Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

yau da tunanin Amadu a raina shine nace bari dai in je shi ma ya sami lada na...." Baffa ne ya shigo da sallama, kaka tace "Ikon Allah, har da kai Umaru, to me ya faru ne wai? Ba fa kai kadai na haifa ba da xanyi ta xama gidanka, shkkn kuma shi Amadu ba mutum bne da baxan dinga xuwa nasa gidan ba, Kar ka xama me son kanka mana Umaru, ka so ma d'an uwanka abinda kake so ma kanka, shima ka barsa ya dinga samun ladan uwarsa" Baffa yace "Nayi tunanin ko an 6ata maki rai ne ai Baaba" Da sauri kaka tace "Aa wllh, baku ta6a min komai ba, idan nace ma kun mun sai Allah ya kamani, matan ka ai mutanen kirki ne tun ma ba Mai jidda ba, tamkar ynda xa su yi ma iyayen su suke min, to sae in masu sharri ince sun min wani abu?? Aa kawai ni dai na xo gidan Amadu ne shi ma ya samu lada...." Kallonta kawai junaid yake with surprise, Mumy da hawaye ya cika idonta tace "Amma fa kaka cewa kika yi kwai suka soya maki duk karni sannan basa baki abinci da wuri kawai sun gaji da ke ne...." Kaka ta saki salati tace "Yau naga abinda ya isheni jama'a, Maryam ke da wa ku ka yi haka??? Lalacewar ta ki ta kai haka bani da labari? To ke ina ruwanki ko danyen kwai suka kawo min, ba gwara su sun kawo min kwan duk karni ba, ke me barina da yunwa fa??" Baffa yace "Toh kaka tunda dai bbu wani matsala shkkn sai dai mun yi waya" Kaka tace "Bbu ko wani matsala Umaru Allah yyi ma kai da matanka albarka..." Baffa ya amsa da Ameen ya fita....Mumy dai hawaye ya ki tsaya mata, Hajiya Hauwa sai danne dariyar ta take, daga karshe ita ma tayi ma Kaka sallama ta fita haka ma Hajiya Amina, Mumy ta bi bayansu xuciyarta na tafarfasa, Junaid dai kansa na kasa, kaka tace "Ka ji min mata dai xata min sharri da rai na" Tuwo da miyar egusi Sajida ta kawo ma kaka, Kaka tace "To ba gwara ke ba kan wannan mata da Rakiya ta dauka aiki duk wari.... Tafi ki kawo min flet da cokali" Mai aikin ta fita sae gashi ta dawo, Kaka ta amsa ta bude warmer din tuwon ta diba, ta ajiye ma Junaid, Junaid yace "Kaka ni fa a koshe nake" Kaka tace "Aa ni ba ruwana gashi nan ka ci, kana da Inda xaka je ka ci abinci ne da ya fi nan...." Ta kalli Heedayah tace "In xuba maki kema" Heedayah tace "Na koshi" Kaka tace "To wlh baxan baki Kai da kafar Kazan ba ma" Heedayah ta mike xaune kamar xata yi kuka tace "Toh in ci da Yaya" Kaka ta kalli junaid, Tashi yyi ya koma kusa da ita da plate din tuwon yace "Toh mu ci" Kaka ta ta6e baki tana xuba nata, Heedayah ta d'an fincili tuwon bayan ta laluba plate din ta kai baki, Kaka tace "Wllh haramta maka tuwon xata yi, meye kuma na mintsilin tuwo kamar kaza??" Dariya junaid yyi ya deba a cokali kadan ya tabbatar ya huce sannan ya kai bakin Heedayah, Jin cokali a lips dinta ta bude bakin ta amshi tuwon, a haka suka dinga cin tuwon, aka bude kofa sai ga Shuraim ya shigo, kaka tace "Shureen wai xaka dinga koyon turanci gun Deedayah" Shuraim ya kalli Heedayah da ta tankwashe kafa a gaban Junaid, ajiye ledan hannunsa yyi nan gefe ya fita dakin, kaka ta kalli Junaid tace "Kila kunya ya ji, da ban masa magana a gabanka ba" Dariya sosai Junaid yyi... Sai kusan karfe tara yayi ma Kaka sallama Heedayah har da kukanta wai xata bi sa, ya samu dai ya lallabata ya fita, Kaka tayi tagumi tace "Toh wai a gidan ubanwa kika ta6a sanin Junaidun idan ba gulma ba?? Sai kace shine Amadu? Ai ni da Amadu ne dolen ki..." Wajen karfe sha daya Mami ta shigo da eye drops din Heedayah, Kaka da har ta kashe wuta tace "Kinga Rakiya, abinda xai faru ba sai kin dinga ba kanki wahalan shigo mana tsakar dare ba mun fara bacci, kawai ki nuna min ynda xan dinga sa mata a idon, Amadu fa ya fi awa daya a dakin nan sannan ya fita, tun daxu ya kamata ki xo ai, ni na xata kin gaji kin kwanta ne" Mami tace "Aa ban kwanta ba" kaka tace "To nuna min ynda abun yake in dinga yi mata da kai na" Mami ta nuna ma kaka ta tabbatar ta gane din tana kuma tsaye ta diga ma Heedayah dake bacci drops din dare sannan tayi masu sai da safe ta fita... Har kaka ta kashe wuta aka sake bude kofa, Mumy ce ta shigo kaka ta kunna wuta tace "Amma dai bakwa tsoron Allah matan gidan nan, bakin cikin baccin ake mani cikin daren ma" Mumy tace "Yi hakuri kaka, naga baki bacci da wuri ne ban san kin kwanta ba, kankana na yanka ma Barrister shine na dibar maki" kaka tace "Ki sa min a firiji, amma wnn ae shiga hakki ne, meye kuma kankana tsakar dare jama'ah kamar ana yunwa" Mumy ta bude fridge dake dakin ta ajiye tana kallon eye drops dake ajiye saman fridge din, lkci daya ta kwashe su tace "Toh sae da safe kaka" bata jira cewarta ba ta fice daga dakin, kaka ta ja tsaki ta kashe switch din wutan.... Har wani murmushi Mumy take ta wuce dakinta da sauri, bandaki ta shiga da wayarta ta doka ma Sadiya kira, Sadiya na dagawa tace "Toh ga dai eye drops din na samo Sadiya... Kin yarda Allah na tare da ni?? Wllh cikin ruwan sanyi na samu, ban ta6a xaton hka ba...."




Heedayah isn't free, do not read for free, subscribe and read happily....

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍


Hajiya Sadiya dake sauraren Mumy tace "To kin dauko cikin ruwan sanyi maidawan fa Maryam?" Mumy tace "Aa ni maidawan ba wani damuwa ta bace, minti nawa ne, abinda dai ba makulli take sa wa a dakin ba...." Sadiya tace "Toh shkkn, amma wajen bude maganin kiyi ta ynda fa baxa a gane ba, a nutse xaki yi komai" Mumy tace "Toh shkkn sai mun yi waya Sadiya" Daga haka ta katse wayar ta fito, handbag dinta ta nufa ta bude ta binciko wani kwalba irin na magani dake karkashin jakar ta ciro sannan ta rufe jakar, kokarin bude eye drop din ta dinga yi amma ta kasa, tayi tayi amma ya ki buduwa, wuka ne ya fado mata ta Kalli agogo taga sha biyu saura, ta d'an yi murmushi ta ajiye drops din a drawer ta nufi saman gado ta kwanta tana jiran karfe daya yyi don wnn lkcn ta tabbatar kowa na gidan yyi bacci, tana ta kwance idonta kyar ko digon bacci bbu har agogo yyi struck din karfe daya dai dai, ta mike a hankali ta saka hijab dinta har kasa sannan ta dau drops din da kwalbanta ta fita daga dakin, cikin Hijabin nata ta boye hannunta me dauke da eye drops da kwalba, kitchen ta nufa direct ta kunna wutan, sannan ta juya baya ta ciro abubuwan cikin hijab dinta ta dau wuka ta fara gwada bude eye drops din a nutse, she was so careful kar saman yyi shaidar da xai sa a gane an bude, bude kofar kitchen din taji anyi, a rikice ta boye komai cikin Hijab, muryar Shuraim taji yace "Baki kwanta ba Mumy, what are you doing" kin juyowa tayi ta dinga kawar da plate da cups din karya duk a rude, amma lkci daya ta dake tace "Me ya hanaka bacci har war haka??" Yace "Shayi xan hada" Mumy ta hade rai sosai tace "Wannan shan shayin dai ya xame maka jaraba, wani shayi ne baka sha ba tun wayewar garin Allah sai tsakar dare kamar maita ka tashi wai xaka sha shayi? Shayin me? idan baka sha shayin ba mutuwa xaka yi ko me da baxaka hakura ba tunda dare yyi" Shi dai bai ce mata komai ba, har sannan hannunta daya na boye hijab dinta, ta nufi kofa a fusace ya bi ta da kallon gefen ido, cup ya dauka ya bude flask ya debi ruwan Lipton ya bude kayan shayin xai hada, Mumy tayi still ganin kaka a parlor, lkci daya gabanta yyi mugun faduwa kaka ta karaso Inda take tace "Amadu yyi bacci ne?" Cikin rawar baki Mumy tace "Lafiya Kaka, me ya faru?" Kaka tace "Ina fa lafiya, idonsa biyu ko yayi bacci?" Mumy da hankalin yyi mugun tashi don cikin d'aga murya kaka ke magana tace "Kaka ban san ko yyi bacci ba daga kitchen...." Abba ne ya fito parlon jin muryar mahaifiyar tasa, Kaka na ganinsa tace "Amadu wannan wani bala'in ka kawo wa mutane gida, ya xa a dinga shiga hakkina Ina bacci, to gata can ta hanani bacci wai shayi xata sha, meye kuma shayi kamar buxuwa tsakar daren nan" Mumy bata san lkcn da ta sauke wani bayyanannen ajiyar xuciya ba, Kaka tace "Ni dai ba ruwana, tun wayewar gari bata gama shaye shayen shayinta ba sai ynxu bayin Allah na hutawa, kawai ta cuceni ta tasheni" Abba dai bai ce mata komai ba, kaka tace "Ga ta can xaune kamar yar mage ta ki bacci wai shayi, to ni siyar da shayi nake xata tasheni ta dameni" Abba yace "Kiyi hakuri, bari a maida ta gun Rahinah" Kaka ta kallesa da sauri tace "A maida ta kuma? A kan me? To sai kayi ta maida ta din ae, daga tace xata sha shayi sai a maida ta gun Rahilah" Duk wnn abun Shuraim na tsaye rike da cup din shayinsa yana kallonsu, Mumy tace "Kiyi hakuri kaka bari in hado mata shayin yanxu" Shuraim ya karaso cikin parlon Kaka na kallonsa tace "Waye wnn kuma?" Mika mata cup din hannunsa yyi ta amsa tace "Toh ba shkkn ba dai, amma xaka wani ce a maida ta gun Rakiya, meye hadinta da Rakiya, Kuma waye bai san yaro ba Allah na tuba" Daga haka ta wuce dakinta rike da shayin, ta gefen ido Mumy ta dinga hararan Shuraim da ya juya ya wuce dakinsa shi ma, Abba ya girgixa kai ya koma bangarensa. Mumy ta tabe baki don har yau ba wani shiri take da shi ba, dakinta ta koma ta sa makulli ta ci gaba da aikinta, da kyar ta bude drops din ta wuce bandaki ta tattular da maganin ciki ta dauraye empty container din da ruwa a nutse sannan ta dawo daki, kwalbanta ta bude ta xuba content din ciki wanda kalansa shi ma fari ne a robobin eye drops din, snn ta rufe gam da murfi... Ta ajiye robobin su bushe a gaban madubi tana yi tana kallon agogo, sai biyu da kusan minti goma ta kwashe magungunan ta bude kofarta a hankali ta fito parlor, kwance ta ga mutum saman kujera yyi rub da ciki, duk da wutan parlon a kashe yake amma wutan compound ya d'an haska har cikin parlon, ta yi still a Inda take don ta san baxai wuce Shuraim ba tunda ya saba kwanciyar parlor, yawanci ma nan yake kwana, tana daga Inda take tsaye ta dinga leka fuskarsa a hankali taga bacci yake, tayi tiptoeing har xuwa hanyar dakin kaka sannan ta bude kofar very careful don ma ko kadan kofar baya kara, fridge ta nufa ta ajiye eye drops din ta juyo da sauri ta fita ta kulle kofar, sannan ta sauke ajiyar xuciya, tana isa cikin parlor ta kara lekan Shuraim da ko motsawa bai yi ba, ta wuce dakinta hankali kwance tana gode ma Allah. Sbda baccin da Mumy bata yi ba da wuri sai kusan karfe takwas na safe ta tashi duk da ta tashi sllhn asuba, taga har su Khadijah sun wuce makaranta, bandaki ta fara shiga sannan ta fito ta tafi parlor, dai dai nan Kaka ta fito, Mumy na murmushi tayi kasa tace "Sannu kaka, fatan kun tashi lfya?" Kaka tace "Wani lafiya an shigo an sace ma yarinya magani, a kira min Amadu" Kasake Mumy tayi tana kallon kaka, kaka ta nufi bangaren Mami tana cewa "Bari inji ko wnn matar ce ta shigo ta kwashe magungunan yarinya sbda ta nuna min ban isa da ita ba" Kaka ta shiga buga kofar Mami, Mami na fitowa kaka tace "Rakiya Ina maganin da kika shigo kika kwashe?" Da mamaki Mami tace "Magani kuma kaka?" Kaka ta saki salati tace "Toh wllh barawo ya shigo ya sace maganin da kika kawo jiya, ba a kan friji nace ki ajiye ba??" Mami tace "Ehh nan kuma na ajiye" Kaka tace "Toh ko sama ko kasa, dakin na can na hargitsa wai ko ma ya shige wani lungun ne amma wllh ban gani ba, Ina Amadu" Mumy dai ta kasa motsi inda take, Mami ta kalleta na yan sakwanni sannan ta dauke kai, Kaka da kanta ta tafi ta kwankwasa ma Abba kofa yana fitowa tace "Amadu barawo ya sace maganin Deedayah, wllh da shi muka kwanta muka tashi ba shi" Da mamaki Abba yake kallonta, tace "Wllh ba xancen wasa ba kana kallona" Mumy dai fa an kasa motsin kirki sai imagining take to ko dai cikin mafarki ta mayar da maganin bata mayar a xahiri ba, Shuraim ya sakko downstairs jin muryar Kaka ya cika gidan, ya karaso yana kallonta yace "Me ya faru?" Kaka tace "Shureen maganin Deedayah aka rasa wanda ya dauke, ni kuwa yau xan ga 6atar nono a kirjin budurwa...." Kallonta kawai Shuraim yake with surprise, can ya kalli Mumy dake tsaye sai wurga ido take, Kaka tace "Al-qur'an kira xan yi in sa a ja min Yasin, in dai ba a fito min da maganin yarinyata ba sai na kai kudi an ja min yasin" Abba dai bai ce komai ba, Mami na tsaye just watching everybody, Kaka ta nemi kujera ta xauna tana hada xufa tace "Ka ji min dai, to wllh ba ruwana sai dai cikin mutum ya kumbura, me Deedayan ta tsare maku da xa a dauke maganinta, ko uban wani ne ya siya mata maganin banda Amadu???" Abba yace "Junaid ne ma ya siyo ba ni ba" Kaka ta mike da sauri tace "Au Junaidu ne ma, to dama idan ba kai din ba ko shi wa gareta da xai siya mata, wllh Amadu ka ja su daki kayi masu magana cikin nutsuwa su fito min da maganin yarinya kar abu ya baci tsakanina da su, xan fa mance sanin da na masu in sa a ja masu Yasin" Tana fadin haka ta juya ta nufi dakinta fuska daure, Shuraim ya bi ta da kallon gefen ido, Cike da karfin hali Mumy tace "Ikon Allah...." Mami ta ta6e baki ta juya ta koma dakinta, Mumy tace "To magani kafafuwa garesa da xa a nema a rasa?? Anya kaka ta san Inda ta ajiye maganin kuwa?" Abba na kallon Shuraim yace "Xan sa Junaid ya tura maka sunan eye drops din, sai na maka transfer ka tafi pharmacy ka siyo su" Shuraim yyi kasa da kai, Abba yace "Ko baxa ka samu xuwa ba..." Kafin yace komai Mumy tace "Baxai samu ba mana, shi da yake fita aiki Barrister, Ina ji fa ranan Baffa ke fadan baya wani xuwa aikin sai ya ga dama to idan ba matsala kke son ja masa gun Baffan nasa ba ina xai je samo wani magani ynxu da safe" Tun da ta fara magana Abba ke kallonta keenly, can ya gyada kai ya wuce bangarensa, Shuraim dai bai iya ya daga kansa ba, Mumy ta hade rai bayan tafiyar Abba murya can kasa tace "Did you know anything about the missing eye drops Aliyu??" Ya daga kai da sauri yana kallonta yace "Ni kuma Mumy, ni ban ma san da wani eye drops a gidan nan ba, I know nothing about it, ban ma san kalarsa ba" Mumy ta kauda kai tana naxari to wai ko dai mafarki tayi ta mayar da drops din dakin kaka?? Ganin Shuraim ya fara wucewa ta kara daure fuska tace "Wait, ko da wasa kar ka fita gidan nan da sunan tafiya siyo ma tsinanniyar yarinyar nan magani.... I'm instructing you not to do so" Da mamaki ya tsaya yana kallonta, can yace "Toh idan Abba ne yace in je fa Mumy?" Rai bace Mumy tace "Ni kuma nace baxa ka je ba, ko tsallake maganata xaka yi??" Yace "Amma ai baxan iya ce masa A'a ba kamar ynda kema baxan iya ce maki A'a ba" tace "Wannan ya rage naka kai da shi, ni dai nace idan ka fita gidan nan siyo maganin makafi to ba da yawuna kayi hakan ba" Fitowar kaka ya sa ta ja bakinta tayi shiru da sauri, Kaka dake sanye da hijab hannunta rike da Heedayah tace "Ga shi na fiddo dubu daya ta xan je siyo maganin idon a kemist, daga can kuma xan tafi gun da xa a ja min yasin na tsakani da Allah...." Mumy tace "Haba kaka yanxu fa nake cewa xan shiga a sake duba dakin da kyau ko...." Kaka ta katse ta a fusace tace "Tunda kinga alamar na fara makancewa kamar Deedayah ba, wllh tllh baxan yi kaffara ba wani algungumin ne ya shiga ya dauke maganin nan, to ni abinda har yanxu ban gane ba a nan shine, bakin ciki ake ma yarinyar kar idon ya warke ko me?? Anya wasu xa su gama da duniya lafiya kuwa, Junaidu ya cire kudi domin Allah ya siyo mata magani amma wani mara tsoron Allah ya bi dare ya sace, tunda nake ban ta6a ganin irin haka ba sai gidan Amadu, gidan Umaru basa haka kwata kwata, in haka ne lauyancin karya Amadu ke yi kenan, lauyancin karya mana tunda ya kasa kama wanda ya sace ma Deedayah magani, ita ma amaryar da naji ance lauya ce ashe ta karya ce, lauyoyi biyu a gida a tafka wnn uban sata amma a kasa kama barawon har war haka?? Aa ba ruwana gwara inyi ta kai na, dubu daya da dari biyar dina ya biya min bukata, dubu daya in bada a kemist su bani maganin guda biyu, dari biyar kuma in tafi gidan Ta salla ta rakani inda xa a ja min yasin...." Shuraim was trying hard not to laugh sai sunkuyar da kansa yake yana shafa gashin kansa, Fitowar Abba yasa ya daga kai yana kallon Abban nasa, Abba yace "Ina kuma xa ki kaka?" Tace "Ina ne kuwa baxan je ba Amadu, Kai baka san wnn yar amana ce Allah ya baka ba xaka barta ta walakanta a gidanka, wani axalumi ya sace mata magani kayi shiru" Abba yace "Xan je siyo maganin ai ynxu" Kaka tace "A'a ai tunda nayi niyya sai na siya ga dubu dayana xan je kemist da ita ynxu" Abba ya tsaya kallon kaka kafin yace "Ae ko wani daya ya kusa dubu ashirin da biyar" Kaka ta gwalo ido tace "Me din?" Abba yace "Bari ynxu xanje in siyo in kawo maku" Shuraim dake kallonsa a hankali yace "Abba I will go..." Abba yace "Noo, Kar ka damu" Shuraim yace "Amma kace I should get it" Yace "Ehh na canja shawara, you don't worry" Daga haka Abba ya fita, Shuraim ya bi sa da kallo, Mumy ta kyabe baki, Kaka na kallon Heedayah ta dunguri kanta tace "kin dai ji nawa ake siyar da maganin d'an cikin roban nan, to idan ba tsoron Allah ba uban me muka hada da ke xa mu dinga kashe maki kudi haka, kin ji fa wahalan da d'a na yake, dubu hamsin xai kashe da safen nan a kan lalurar ki, to wa xai saka masa kuwa banda Allah? Ba dangin iya balle na Baaba fa" Mumy tace "Abinda ke damuna kenan kaka daga karshe ma a saka ma mutum da sharri" Kaka ta kalleta tace "Toh Ina ruwan ki, kudin ki ko na Amadun??" Kaka na fadin haka ta ja hannun Heedayah suka koma daki.... Mumy ta wuce nata dakin don duba drops din ko bata mayar da gaske ba, Mumy ta tsaya da mugun mamaki a gaban madubinta tana naxarin to waye ya shiga dakin kaka ya dauke maganin nan, kaf ta duba dakinta bbu, ita dai tana da yakinin ta mayar wajajen karfe biyu da wani abu na dare ba wai mafarki ba, hankalinta yyi mugun tashi don gashi an kara wargaza wnn plan din ma, ta dau wayarta rai ba dadi ta wuce bandaki. Har Mami ta gama shirin fita office hankalinta ya kasa kwanciya, she is so disturb, ko kadan bata ji xuciyarta yyi na'am da komawar Heedayah gun kaka ba, ko ma waye ya dauke eye drops din nan yyi hakan ne da wata manufa na cutarwa, cuta kuma me girma ba karami ba, bata san ta ina xata fara billowa kan a bar Heedayah wajenta ba, gaba daya taji bata yi trusting kowa na gidan ba, they all look guilty, both mother and Son, sannan masu aikin ma haka kawai taji hankalinta bai kwanta ba bata yrda da su ba, sannan Rabi'ah da Khadijah ma halin uwar garesu bbu abinda suka mance nata, kaka kuma from many indications taga baxata cutar da Heedayah ba balle kuma a je ga wanda yyi sanadin xuwanta gidan wato Abba, dauke Heedayah daga wajen kaka isn't going to be easy but she will try, ynda take jin Heedayah bata jin xata bada space a cuceta a gidan nan sai iya inda karfinta ya kare, da haka ta fita xuwa parlon Abba sanin bai fita ba, Yana parlon nasa da Shuraim dake xaune kasa, Abba na kallonta yace "Xaki tafi office...." Tace "Yes, but barrister har yanxu baka ce komai ba a kan the missing eye drops.... This is a very serious issue to address to with immediate effect, Sannan nasan ka fini sanin koma wanene ya dauke eye drops din nan ya dauke sa ne da manufa biyu xuwa uku which I won't mention cos you know...." Abba dake kallonta yace "Gaskiya ne, I will see to that" tace "And pls ko xaka yi ma kaka magana Heedayah ta komo wajen??" Abba ya d'an yi shiru, sannan yace "Will see to that too" Mami tace "Alright thank you, sai na dawo" daga haka ta fita, Shuraim ya bi ta da kallon gefen ido, dakin kaka Mami ta tafi, ta samu kaka ta hada ma Heedayah shayi me kauri ga ledan bredi guda ta ajiye mata, Kaka tace "Har xa a fita kenan" Mami ta xauna kusa da Heedayah tace "Ehh kaka, Ina kwana?" Kaka tace "Lafiya lau, kawai sai muka wayi gari da alhinin an sace maganin Deedayah" Mami tace "Allah dai ya kyauta...." kaka tace "Ameen fahhh, ga dai sabo Amadu ya siyo ya kawo na boye, ita kanta Deedayan ma baxan bari ta san Inda na boye ba balle wani" Mami tace "Yauwa gwara haka kaka" Kaka tace "Ni fa sai nake ga kamar Maryam ce ta dauke, ke baki ga duk ta rude ba??" Mami ta d'an yi murmushi bata dai ce komai ba tana gyara ma Heedayah gashinta, Kaka tace "Toh wllh sai dai ta cuci kanta ba dai Deedayah ba, me yar yarinyar ta tsare mata" Mami

Please Login or Register in order to submit comment