Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

baki algungumi, Ina ruwan ka da inda xa ni??" Ya kwantar da murya yace "Kinga Baaba, tafiyar ma an fasa har sai an maki visa sai duk ku tafi tare" Tace "Oh oh ba ruwana su yi tafiyarsu, kada wanda yace min komai, ni dai an walakanta ni an cuce ni, Allah ya hada mu a kiyama gaba daya kawai...." Xaunawa Baffa yyi saman kujera ya jinginar da kansa yana kallonta, Abba dai bai ce komai ba, Junaid ne ya shigo parlon da sallama, Kaka ta saki jakarta tayi mitsi mitsi da ido tace "Junaidu ashe dama uwarka bata da kirki ban sani ba, Ashe sai a hada baki da ita a cuceni ban sani ba, ni tunda nake Maryam bata ta6a min abinda Rakiya tayi min ba wllh" Da farko tsaye yyi bakin kofar, sai kuma ya karaso yace "Me ya faru kaka?" Kaka ta sakar masa kuka tace "Da hadin bakinta aka yanke shawarar baxa a je India da ni ba wajen gyaran idon Deedayah" Junaid ya d'an bude ido yace "Aa kaka ai dole ma xa ki je, ga visa nan ana maki, idan ya so bayan an gama ni da ke sai mu bi su daga baya, nima ai ba binsu xanyi ba ynxu..." Ta marairaice tace "Toh ai su basu ce min haka ba cewa suka yi ban da ni kawai, wani har ce min yyi nima kai na cutar ce me xai kai ni India, wato wai nice cuta, har da ce min wahalalliya, abinda ni dai nasan ubansa ya xaga ba ni ba" Junaid yace "Aa kiyi hakuri don Allah, tafiya kam xa ayi da ke in sha Allah, kawai dai daga baya ne xamu bi su" Kaka tace "To da wa da wa xa a tafi din yanxu?" Yace "Mami da Shuraim" Mumy dake dinning har sannan ta sakko xuwa cikin parlon cike da gadara tace "Nace Babu inda Shuraim xai je, a nemi wani amma ba shi ba, indai har ni da na haifesa ban cancanci xuwa ba to shima bai cancanta ba, kada a sake ambaton sunansa a masu tafiyan" Kaka ta bude baki tana kallonta tace "Waye wannan kuma? Daga gidanku kika xo da Shuraim din da xaki nuna mana iko a kansa ko kuwa shakiyanci ke damun ki? Kaji min jarabbiyar mata dai, to wllh sai an je da Shuraim, Kai idan xuciya ta debeni ma sai ince shi kadai xai kai ta gyaran idon kada wanda ya bi su, ke a wa xaki ce baxai je ba wahalalliyar mata kawai, nan nan kanwarki ta xo nan gidan ranan kamar abun arxiki amma sbda tambadewa na samu labarin ba a gidan take kwana ba sai ta fita da daddare ta dawo mana da safe, to gidan ubanwa take kwana, baki dau mataki kan wnn lamarin ba sai don ance Shureen xai je indiya da Deedayah? " kaka ta kalli Abba a fusace tace "Kai Amadu da wa da wa xa a tafi goben?" Yace "Rahinah da shi Shuraim, daga baya sae ke da junaid ku bi su" kaka tace "Toh dole da Shuraim xa a tafi, idan ma kowa bai je ba sae Shuraim yaje wllh" Mumy tace "Ohk, ya tafi bakina ma ya ishesa ai" Kaka ta nufeta tana tafe hannu tace "Bakin ki na banxa na hofi, bbu abinda bakinki xae mashi, ae ubansa xai yi ma biyayya don hka a gantale bakin ki xae xaga duniya ya dawo ya fada kanki ba dai kan jikana ba, gantalalliya kawai" a nutse Mumy tace "In har Shuraim ya taka ya fita gidan nan xuwa wani kasa wllh sae na tsine masa" tana fadin haka ta bar parlon kamar xata tashi sama, Shuraim dai na tsaye gefen Abbansa, kaka tace "ke kuma tsinuwar Allah ya tabbata a kan ki ba na mutum ba, xan ga uban da ya isa ya hana Shuraim xuwa India" Abba da gaba daya ransa ya gama baci ya bi bayan Mumy, Baffa dai ya ta6e baki bai ce komai ba, kaka na kallon Junaid tace "Ni dai ko xaka kai ni gidan kawun ka ynxu, wllh raina baci yake idan Ina ganin mutan gidan nan, Ka kai ni can ko xa a kwantar min da hankali" yyi murmushi yace "Toh mu je kaka" tace "Amma ae abun ba hauka bane bana kai masu katon akwati ba bari in bude in dau kayana kala ko goma ne" Shi ya ja mata akwatin har dakinta tana biye da shi tana goge guntun hawayenta... Washegari da asuba Mami ta gama duk shirinta, ta shirya Heedayah, suka fita xuwa parlon Abba, Abba da ya gama hada duk medical report din Heedayah a envelope ya mika ma Mami yace "Amma xa mu tafi ku yi ma Kaka sallama tukun koh" Mami ta amsa tace "In sha Allah" Abba ya kalli agogo yace "We need to hurry up, sbd kar ku yi missing train din" Mami tace "Haka ne" Abba ya dau wayarsa yana mamakin rashin ganin Shuraim a masallaci don bai dde da shigowa daga masallacin ba shi ma, Dialing number sa yyi ya ji switched off, ya kuma kira a kashe, Mami dai kallonsa kawai take bata ce komai ba, Abba ya dinga kallon wayar tasa, can ya mike yace "Mu tafi kawai in kai ku gidan Honorable din daga can Junaid ya kai ku Train station" Tace "Shuraim din fa?" Yace "Don't worry about that" Mai gadi ne ya shigo ya dau kayan Mami da Heedayah ya sa bayan motar Abba, Mami tace "Toh baka yi ma daughter din taka Addu'a ba Allah ya sa ayi aiki a sa'a" Abba yyi murmushi yana kallon Heedayah dake sanye da kananun kaya sai baby Hijab dake kanta tana rike da hannun Mami, kamo hannunta yyi yace "Safe trip dear, Allah ya kai ku lafiya ya sa ayi komai a sa'a, ya baki lafiyan idon ki" Ta kamo hannunsa a hankali tace "Abba xan fara gani nima?" Yana murmurshi yace "In sha Allah Dear" ta d'an yi shiru sai kuma tace "Toh baxan fara ganin Ammi na ba?" Abba da Mami duk suka yi shiru suna kallonta, hawaye ne ya kawo idonta tace "Tace min ita xan fara gani fa" Abba ya jawota jikinsa yace "Xa ki ganta in sha Allah daughter, Mami ma ai Ammin ki ce" Ta gyada masa kai, ya share idonta suka nufi gun mota Mami na biye da su a sanyaye, Sai bayan da ya shigar da Heedayah motar Mami tace "Baxa ayi ma matarka sallama ba?" Yace "No, rabu da ita" Mami bata kuma cewa komai ba ta bude front seat ta xauna suka fita gidan xuwa gidan Alhaji Imran Baffansu Junaid, Dakin da aka sauke kaka Mami ta shiga da Heedayah bayan sun gaisa da Hajiya Zuwaira a dakinta, kaka na xaune ko haske gari bai yi ba ga kayan karin kumallo iri iri a gabanta tana hada shayi cikin katon mug, Mami ta xauna saman carpet tana murmushi tace "Ina kwana kaka" Kaka tace "Lafiya lau, to Ina xan samu haka a gidanku??" Murmushi Mami kawai take, can tace "Toh mu kaka xa mu tafi ayi mana addu'a, Allah yasa mu je a sa'a ayi a sa'a, ku kuma Allah ya kawo ku lafiya" Kaka tace "Toh Allah ubangiji ya kai ku lafiya, ya sa wnn marainiya ta fito lafiya, Allah kar ya bamu kunya yasa idanuwan nan su rufa mana asiri su budu" Mami ta yi kasa da kanta tace "Ameen" Kaka tace "Toh matso da ita in yi mata addu'a" Mami ta maida Heedayah kusa da kaka, kaka tayi duk suran da ta sani da su ayatul qursiyyu da Amanar rasulu duk ta tofa mata tace "Allah ubangiji ya sa ayi aikin a sa'a, ya rufa mana asiri ki fara ganin kowa kamar yanda ake ganin ki, daga karshe kuma Allah ya bama d'a na ladan uban kudin da ya kashe maki, Allah yayi masa albarka yasa kema ki ji k'an sa wataran kada ki yi mana butulci..." Heedayah dai tayi shiru staring into space, kaka tace "Kaji gantalalliya, baxa ki ce Amin ba, ko kina da niyyar butulcin ne ya sa kika yi shiru bamu da labari" Mami tayi murmushi tana kallon Heedayah tace "Say Ameen daughter" a hankali Heedayah tace "Ameen" Kaka tace "Toh maxa ku tafi kada jirgin ya tafi ya bar ku ba mutunci ne da su ba haka suka so min xuwa umrana na karshe Allah ya fi su" Mami tace "Toh Kaka, mun gode da addu'a, baxa ki fito ku gaisa da barrister ba" Tace "Waye kuma Barrister? Don Allah ki rabu da ni kada raina ya baci, yyi ta kansa inyi ta nawa kawai" Mami ta mike tace "Toh Allah ya sada mu da alkhairinsa kaka" Kaka tace "Kiyi addu'a sosai kafin ku hau wnn bala'in na bature wai jirgi" Mami tace "In sha Allah" kaka tace "Da Shuraim din dai xa a je koh?" Mami tace "In sha Allah" Kaka tace "Toh duk Allah ya tsare ku, yayi maku albarka, ya sa ayi wnn aiki a sa'a sai mun xo ni da Junaidu" Mami tace "In sha Allah kaka" daga haka ta fita dakin, Abba na xaune parlor da Alhaji Imran, Ganin Mami yace "Lkci fa na wucewa kada kuyi missing train" Mami tace "Ka samu Shuraim din?" Abba yace "No tare da Junaid xa ku tafi" Shiru Mami tayi, Ya mike yace "Yeah, na kira junaid din ya shirya ynxu" Mami ta xauna tare da Heedayah, Alhaji Imran yace "Allah ubangiji ya tabbatar da alkhairi a tafiyar" Mami tace "Ameen Baffa" Ba a dau lkci ba sai ga Junaid da traveling bag dinsa ya sakko kasa, Abba na kallonsa yace "Hope baka ce ma kaka komai ba" junaid yace "Aa ban shiga ba" Abba yace "Good" Har motar Abba dake parke waje Alhaji Imran da matarsa suka raka su, Alhaji Imran na kallon junaid yace "Nayi maka transfer yanxu Incase da bukatar wani abun a can, Allah ya kai ku lfya, ya sa ayi aikin a sa'a" Junaid yace "Toh Baffa Allah ya saka da alkhairi" Abba yyi ma Alhaji Imran godiya haka ma Mami sannan suka dau hanyar train station na Hayin rigasa, Junaid na xaune back seat da Heedayah, ta kwantar da kanta saman shoulder dinsa a hankali tace "Good morning...."


Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍



Har suka isa train station din bbu wanda yace komai cikin motar, Abba yyi parking duk suka sauka suka shiga ciki with their luggages, shi dai Junaid na rike da hannun Heedayah, Abba bai bar tashan ba kuma sai da ya ga tashin train dinsu xuwa Abuja.... Kasancewar sai tara na dare flight din nasu na Qatar airways xai tashi kamar yanda aka sanar masu bayan sun je airport din, hotel kawai Junaid ya kama masu kusa da Airport din, Bayan Azahar Mami ta idar da sllh ta shirya xata tafi gun step sister dinta da ke nan garin Abuja, shigowar Junaid kenan daga masallaci yana kallonta yace "Ina xa ku Mami?" Tace "Xan je gidan Asiya ne in dawo yanxu" yace "Ohk..." Mami ta ajiye ma Heedayah dake xaune saman gadon hotel din takalminta ta kamo hannunta tace "Sauka ki sa takalmin ki" Heedayah tace "Mami da Yaya xa mu je?" Mami tace "Aa ina ruwanki da wani Yaya" Tace "Mami mu je da shi plss" Mami ta saka mata hijab dinta tana rike da hannunta ta nufi kofa tace "Sai mun dawo" junaid ya bi su da ido, sai kuma yace "Mami ko xa ki bar ta ki je ki dawo" Mami ta juya tana kallonsa tace "For what reason?" Da sauri yace "No naga kamar bata son tafiya ne" Wani kallo tayi masa ta bude kofar ta fita, Heedayah dai kamar xata yi kuka take bin Mami.... Har la'asar Mami na gidan yar uwarta da Heedayah suna hiran yaushe gamo, Hajiya Asiya na kallon yar uwarta tace "To amma me yasa ba ku taho tare da Junaid ba? Mun kwana biyu ba mu hadu ba" Mami tace "Muna sauka daxu da safe yace min xai je gidan kawunsa so bna son ya kasance bai je ba, but in dai ta nan xa mu dawo xai xo gun ki in sha Allah...." Hajiya Asiya tace "Toh shkkn, Allah ya kai ku lfya ya dawo da ku lfya, ita kuma wannan yarinya Allah ya sa ayi aikin a sa'a" Mami ta amsa da "Ameen" karfe shidda saura Mami suka bar gidan, babu yanda Hajiya Asiya bata yi ba su tafi da abinci hotel din Mami ta ki amsa, Hajiya Asiya ta sa driver dinta ya sauke su hotel din nasu. Karfe tara da few minutes na dare jirginsu Mami yyi take off direct xuwa kasar India without stopovers, tafiyar kusan awa tara da minti arba'in da takwas, kafin tashinsu kuma sai da Mami ta tabbatar ta kira Abba ta sanar masa xa su tashin yayi masu addu'a yyi wishing dinsu smooth trip.... Tare Junaid da Heedayah suka xauna a jirgin, Heedayah na laluba hannunsa tace "Yaya me yasa Abba bai biyo mu ba" Junaid yace "He is very busy" tace "To kaka fa?" Yace "She's old to journey with us" tace "To ya Sudais fa?" Yace "Shi ma he is busy amma xai xo...." Heedayah tayi shiru sai kuma tace "Dama bana son Shureen ya biyo mu" Murmushi yyi yace "Why?" Ta girgixa kai tace "Bana son sa" Junaid yace "Don't tell anybody that" Tace "Why?" Ya ja hancinta ya kwantar da ita jikinsa yace "Sleep Lolly...." Lumshe ido tayi nan da nan kuma bacci ya dauketa throughout the rest of the journey. Bakwai saura na safiya Jirginsu ya sauka Indira Gandhi international airport new Delhi, Amma sai karfe goma saura suka shiga Indraprastha Apollo Hospitals da xa ayi ma Heedayah aiki, don sai da suka fara sauka hotel dake nan kusa da hospital din suka huta, Bbu bata lkci aka yi admitting din su a babban asibitin a ward dinsu su kadai, ba laifi ward din na da d'an girma, amma kana gani kasan dai kudi ne kawai aka kashe ba kadan ba.... Kamar yanda Abba yayi tunani haka ne don sun daura Heedayah kan allurai na sati daya, sai kuma some diet da aka daura ta kai, Likitar dake ma Mami bayani a office dinta da harshen turanci ta sanar ma Mami irin Disorder din Heedayah da ake kira da Congenital Blindness, sannan ta sanar mata Novel Gene therapy xa ayi mata to correct the disorder, probably through luxturna, Mami da duk jikinta yyi sanyi tace "But is there much chances of her gaining her sight?" Likitan tace "Hopefully, though it's a rare disorder but we will try our best" Mami tayi ma likitan godiya ta mike ta fita office din ta koma ward dinsu. A kwanaki bakwan nan Mami kusan kullum sai ta tashi sllhn dare tayi addu'ar Allah ya sa ayi nasara a aikin da xa ayi, har ranta take tausayin Heedayah take kuma fatan Allah ya bude mata idanuwanta, bata san yanda xata ji ba idan aka yi aikin nan Heedayah bata yi gaining sight dinta ba, she can't just imagine that, a hotel din da suka fara sauka na kusa da hospital din Junaid ke kwana, amma throughout the day yana asibitin tare da Heedayah da Maminsa, sai dai kawai ya fita ya siyo masu Nigerian dishes safe rana da daddare, ko kuma ya fita xuwa yin sllh... A kullum sai Abba ya kira ya sa a ba Heedayah waya sun yi magana, complain dinta kuwa a ko da yaushe shine idonta suna mata ciwo, don a hankali fararen idanuwanta masu kyau suka fara sauya kala xuwa ja kuma tayi ta sosa su, Sudais ma kusan kullum sai ya kira Mami ta ba Heedayah sun yi magana, ana haka har suka cika kwana goma cif a asibitin ya rage kwana biyu a shigar da Heedayah theatre.... Junaid na xaune tare da Mami ana gobe xa ayi operation din wayarsa ya fara ring, dauka yyi saman table dake kusa da shi yana kallon screen din dake nuna masa Beauty, to waye haka? ya dau lkci yana tunanin waye yyi ma saving da haka, sai kuma ya daga kafin ya katse ya kai kunne, Daga daya bangaren aka yi sallama cikin siririn murya, sai bayan kusan second biyar ya dau muryar ya amsa sallaman, Salima tace "Haba Jayyy shine bbu ko sallama kayi tafiyar ka India, to gani a new Delhi din nima, yanxun nan jirginmu ya sauka daga Nigeria wllh" junaid ya d'an yi shiru da mamaki, can dai yace "Ke da wa kika xo new Delhi?" Tace "Wllh wani saurayi na ne ya xo business trip shine kawai yace in rakosa, a hotel din kusa da Airport xa mu sauka ynxu.... Ku kuna wani asibitin ne?" Yace "Toh ki huta tukun xa mu yi waya" tace "Toh shkkn Jay, sai anjima dama duk na gaji, wanka xan yi ma yanxu" Yace "Alright" daga haka ya katse wayarsa, Mami na kallonsa tace "Wacece?" Ya kalleta da sauri sai kuma yace "Ohk wata coursemate dita ce from Nigeria...." Mami tace "Ya aka yi tasan kana India?" Yace "I told her I will be coming to India tun last week" Mikewa yayi ganin Heedayah xata sauko saman gadon ya nufeta yace "What happened?" Tace "I want to ease my self" Tashi Mami tayi ta kama hannunta xuwa toilet dake ward din. Washegari da asuba aka shigar da Heedayah theater, a asibitin Junaid ya kwana ranan, coz shi ma he is so tensed, he just don't want to imagine the operation won't be successful, haka ma Maminsa da bata yi wani bacci daren ranan ba, ita kanta Heedayah duk son baccinta bata yi baccin ba daren don idon na damunta sosai, Mami taji tausayinta ba kadan ba, har karfe goma na safiyan Mami na xaune saman darduma hannunta rike da carbi, Junaid yace "Mami baki yi breakfast ba, pls take something" Tace "Toh" Tea ya hada mata a cup ya mika mata ta amsa, Mami bata wani sha shayin ba ta fita ta xauna saman kujeran dake jere gaban theatre din da aka shigar da Heedayah.... Karfe sha biyu likitoci biyu suka fito theater din sanye da gown din operation, Mikewa Mami tayi wanting to hear something from them, da turanci daya likitan yace mata ta kwantar da hankalinta all will be well, daga haka ya wuce, Mami ta koma a hankali xauna, bayan minti talatin wasu likitocin uku suka fito su ma din dai haka suka ce mata, ita dai gaba daya hankalinta ya kasa kwanciya, daga karshe nurse biyu suka fito, Mami ta kara tashi ta nufesu, su ma dai xancen daya ne suka yi wucewarsu. Sae kusan azahar aka kai Heedayah ward dinta tana bacci, Mami na xaune kusa da ita sai kallonta take an rufe mata idanuwanta da white eye pads, gaba daya she is disturbed and tensed, Junaid dai na tsaye daga gefen gadon ya rungume hannunsa shi ma yana kallonta, wayar Mami ya fara ring ta dauka ganin Abba ne ta daga a sanyaye ta kai kunne, gaisawa suka yi tace "Yanxu aka fito da ita, but akwai eye pads a idanuwan...." Daga daya bangaren Abba yace "Toh Allah ya sa an dace, can I speak to her now?" Mami tace "Bacci take" Abba yace "Toh I will call back later" daga haka suka yi sallama ta ajiye wayar tana kallon junaid tace "Toh baccin me take haka, ko anaesthesia da aka yi mata ne?" Yace "No, anaesthesia din da aka yi mata iya aikinsa bangaren idon, she is not unconscious bacci take" Mami tayi shiru bata ce komai ba.... Har karfe hudu na yamma Heedayah bata farka ba, Junaid ya tafi yyi sllh ya dawo ya tadda Mami na sallahn ita ma, ya xauna kusa da Heedayah ya kamo hannunta yana kallonta ganin sai motsi take, a hankali cikin rawar murya ya ji tace "Mami idona na min ciwo" Ya dafa goshinta still holding her hands tight yace "Xai daina dear...." Ganin xata mike xaune ya dagata ta xauna ta kai daya hannunta idonta, da sauri ya rike hannun ganin cire pads din take son yi yace "Noo don't...." Ta fashe da matsanancin kuka xata kwace hannunta tace "It's paining me" ya ki sake hannun yace "Zanyi tafiyata in bar ki ke kadai a nan if you don't stay still now...." Ganin kukan da take ya rungumeta yace "Toh yi hakuri xa a cire maki yanxu, ki daina kukan, I will call the doctor now" cikin rawan murya tace "Yana min xafi sosai" Mami na idar da sllh dama fita tayi kiran likita don yace idan ta tashi a sanar masa, yana shigowa allurai biyu yyi mata ya sa mata drip ya fita... Ba a dau lkci ba kuma tayi bacci junaid na rike da ita har sannan, Mami ta sake komawa gun likitan don jin abinda ake ciki, nan ya sanar mata nan da kwana uku xa a cire eye pads din a duba idon with hope that tayi gaining sight dinta clearly, kafin kwana ukun kuma xa ayi ta mata injections xa kuma ta dinga shan magunguna, Mami tace "But is there nothing to do about the pain pls?" Yace "The pain will subside before tomorrow...." Mami tace "Are you giving me hope that the operation is successful Doctor?" Likitan ya girgixa kai yace "We are also hoping it's successful, but if it's not, then we will try anoda operation.... The last" Mami ta kasa ce masa komai, can ta mike tayi masa godiya a sanyaye ta fita. Tana komawa ward din Junaid ya kwantar da Heedayah ya mike yace "Xan je in dawo yanxu Mami" Mami tace "Ina xa ka?" Yace "I want to get something, ba dadewa xan yi ba" tace "Ohk, ka siyo fresh milk when coming back" yace "Toh" daga haka ya fita, nan kuwa tun safe Salima ta ishesa da kira shine yyi deciding kawai ya tafi ya sameta inda tace masa take ko xata daina kiransa. Yana tsaya gaban hotel din ya kirata, tana dagawa yace "Ina waje ki fito" tace "Haba ka shigo ka jirani a reception mana Jayy..." Yace "But I can't come in, ki daure dai ki fito Ina sauri ne" tace "Wllh tun safe kai na ke ciwo a kwance ma nake ynxu, bbu ynda Suraj bai yi in raka ba na ki fita, ka daure ka karaso ko reception ne plss Jayy" yace "Alright" daga haka ya katse wayar ya shiga cikin babban hotel din, Yana reception din ya kirata, sae ga ta ta sakko sanye da riga da wando sai black veil da ta daura a kai, shi duk wayar da suke ya kasa yrda da gaske tana India sai ynxu da ya ganta, ta sakar masa murmushi tace "Welcome, mu shiga ciki in daura after dress mu tafi hospital din, tun safe na damu Ina son xuwa wllh" yace "Aa ba a barin mutane fiye da biyu and yau ba visiting day bane" lkci daya mood dinta ya canxa tace "To yaushe ne visiting day din?" Yace "Nan da 3 days" Ta tabe baki tace "Toh mu je ciki" yace "No, na gaisheki, xan koma ynxu coz I need to get them food" Ta marairaice tace "Haba Jayyy, ae ba cewa nayi ka shiga ka dade

Please Login or Register in order to submit comment