Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

a kawota nan ba" Kaka ta gwalo ido tace "Toh ni kuma bata dakina yanxu, ban ganta ba wllh" Kasa cewa komai Mami tayi tana kallon Kaka baki bude, kaka ta saki salati ta tafi bangaren Abba da sauri shi ma ta tado sa, yana fitowa tace "Amadu kai ka shigo ka dauke Deedayah dakina muna bacci?" Abba na kallonta da mamaki yace "Heedayah kuma, ba xuwa kika yi daxu kika tafi da ita ba" Kaka ta kara Rafka wani uban salatin ta daura hannu a ka tace "Wllh farkawa nayi ban ganta a dakin ba Amadu, don Allah a rufa min asiri a dudduba ko taje ta shige wani wajen ne ba a sani ba, kasan makaho" Kaf gidan bbu inda ba a duba ba amma bbu Heedayah bbu alamarta, su Rabi'ah duk an tasosu su ma, Mumy da hankalinta ya fi na kowa tashi ta rakube kitchen tafara kiran waya, ana dagawa tace "Kai oga Salahu ku dakata an nemi yarinyar ko sama ko kasa bbu a gidan ba a san wanda ya dauketa ba, ku dakata xan kira ku, ku dakata tukun" Bata jira cewarsa ba ta katse wayar tana xufa.... Duk iya duban da xa ayi a gidan nan anyi har tare da masu gadi amma ba a ga Heedayah ba, daga karshe kuma aka ga second gate din gidan a bude, kaka ta rushe masu da matsanancin kuka tace "Wayyo na shiga uku yanxu cewa xa ayi tayi a dakina ta 6ace, don girman Allah a rufa min asiri a nemota, idan hukuma ma suka ji haka ba kyaleni xa su yi ba, duniya duk a dauka ace na sace makauniya, wllh farkawa nayi naga bbu ita sai pillow...." Abba dai na tsaye ya ma kasa cewa komai, ya rasa tunanin da xai yi but xa a iya ganin tashin hankalin fuskarsa, likewise Mami dake ta kallon gate din da ke bude, Mumy kuwa salati ta dinga yi tana cewa "Anfi shekara uku ba a bude kofar nan ba, a ina ma aka samo makullin aka bude?? Innalillahi wa Inna ilaihi raji'un.... does it mean we are not longer safe cikin gidanmu kenan, waye xai dauke wnn yarinya ni Maryam" Mami tayi mata wani kallo sannan ta shige cikin gida, kana ganinta kasan she is not going to let this, daren ranan nan dai bbu wanda ya rintsa a gidan, Kaka kuwa ta lula cikin anguwa neman Heedayah, bbu yanda Abba bai yi da ita kan kar ta fita dare ne amma taki sauraran kowa tayi ficewarta tana kuka... Gaba daya Mumy ta rasa irin tunanin da xata yi, amma hankalinta ya fi na kowa tashi, can sai ga kaka ta dawo wujiga wujiga da takalma da Hijabi a hannu wai karnuka sun biyo ta... Karfe hudu Shuraim ya shigo gidan ta dalilin kiransa da Abba yyi, Kaka ta fashe masa da wani sabon kukan ta rikosa tana cewa "Wllh tare muke kwance Shureen wai farkawan da xan yi naga bbu ita, an sungumeta...." Shuraim dai ya kasa cewa komai sai kallon kakar tasa yake, can ta sake sa ta koma gun Abba tana Kuka wai ta shiga uku kar hukuma su daure ta, Shuraim ya jingina da bango a hankali ya rungume hannunsa, he looks disturbed also, Ana kiran sllh dama Mami ta bar gidan.... Bayan an idar da sllh sai ga Baffa da Sudais sun shigo gidan, Baffa ma is speechless just as his brother, Kaka dai tun hawaye na xuba har ya daina xuba yanda take kukan kai kace yarinya ce, Sudais ko karasowa cikin parlon ma ya ki yi yana tsaye daga bakin kofa, at the end kawai ya fice daga gidan gaba daya, Baffa na kallon kaka yace "Don Allah kiyi hakuri Baaba, in sha Allah xa a ganta, bbu abinda xai sameta" cikin rawan murya kaka tace "Toh kai sai kayi fatan abu ya sameta dama? Wllh wanda ya saceta cikin gidan nan yake, dama kaf gidan banda ni da Rakiya bbu me sonta, ko shi Amadun bamu san xuciyarsa ba" Abba ya kalleta ta gefen ido bai dai ce komai ba, Baffa yace "Da karfe nawa kika lura bata dakin?" Kaka tace "Daya saura minti goma, Ina fitowa parlo kuma Maryam na fara sanar ma cewar ban ga Deedayah ba" Abba ya kalli kaka yace "A ina kika ga Maryam din" Mumy ta amshe da sauri cike da karfin hali tace "Na fito shan ruwa kitchen muka hadu" Abba ya kalleta, ya dauke kai ya sake kallonta sai kuma ya mike ya wuce bangarensa, Shuraim dai kansa na kasa, Mumy na daga xaune amma duk cikinta ya hautsine da kyar take xaune har lkcn, ba a dau lkci ba Abba ya fito yana kallon Baffa yace "Mu tafi Dr" Mikewa Baffa yyi, kaka ma ta mike da sauri rike da hijab dinta tace "Ae da ni xa aje duk Inda xa a je tunda a dakina komai ya faru, salon in ki bin ku a xargeni ace dama ni na sace ta, gwara duk inda xa ku in bi ku" Sai bayan fitarsu Mumy na kallon Shuraim cikin karfin hali tace "Aliyu wa xai dauke yarinyar nan, wllh ni dai ban san komai kan wnn lamarin ba, naga kuma kowa kallona yake, dama ni na dauketa baxan damu ba, amma wllh ba ni bace, kaga kallon da barrister yyi min irin kamar da sa hannuna gun 6atar ta" Hankali tashe take maganan, shi dai Shuraim kansa na kasa, can ta mike ta wuce bangarenta, yana rike da car key dinsa ya bar parlon ya tafi gun motarsa dake waje.... Hajiya Sadiya da kanta kasa cewa komai tayi, Cikin rawar murya Mumy tace "Sadiya ni fa ban ta6a shiga rudani irin wnn ba, sannan kuma abun mamaki gate din bayan ma a bude na samesa....." Sadiya ta d'an yi shiru snn tace "Shuraim na gidan kuma koh?" Mumy tace "A'a baya nan, tun tara da wani abu ya tafi night duty ba sake shigowa gidan ba sai Asuba uban ya kirasa ya dawo..." Sadiya tace "Kaiii, wnn lamari akwai lauje cikin nadi....." cike da damuwa Mumy tace "Ni ki saurareni Sadiya, ta ya xan wanke kai na cikin lamarin nan, wllh sai kinga, ko magana xanyi sai inyi ta rawan baki... Ni nasan kowa ma ni yake xarga, ni kuma ba a ma kai ga xuwa dauke yarinyar nan ba aka nemeta aka rasa.... Ga dai abun farin ciki amma bbu daman farin cikin tunda ni ake xarga" Sadiya tace "Bari xan kira ki yanxun nan" daga haka ta katse wayar..... Cikin bacci Heedayah ta ji hannu a kanta, ta bude idanuwanta da kyar ta kamo hannun tace "Mami I want to ease my self"




For those sharing and reading this book for free I know I can't stop u from doing so, but that's ur business, burden, and cup of tea, the book is just for a while, while the above mentioned is for everr, but do not edit my write up plss, leave it the way it is and read....😇

Heedayah is 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍




Abba yyi kasa da murya yace "Noo Rahinah, ba sai an kai ga haka ba, this is almost a family issue, ni nasan me xan yi, in sha Allah Heedayah will be back home...." Mami ta katse sa ta mike tace "Family issue barrister? ni fa I've already made up my mind, allow me to do what I am suppose to do, matarka knows Heedayah's Whereabout, ta san komai a kan bacewar yarinyar nan, so why do we all have to pretend, sorry to say, ba ruwana da wani family issue I am doing my work tunda kai baxa ka iya ba, idan 'yan sanda suka je suka daukota they will interrogate her ta fada masu inda aka kai 'yar mutane, period!!!" Abba ya mike yace "But you can't look into my eyes and tell me xaki sa ayi arresting matata Rahinah" Mami tace "I am sorry barrister, I've got no other option, yanayin aikin ne haka kai ma ka sani, nima gobe idan nayi abinda ya cancanci ayi arresting dina, allow them to arrest me..." Kallonta kawai yake, Kaka dake can wani gefe cikin haraban police station din tare da Baffa ta fyace majina tace "To ni dai yunwa nake ji, kar wata cutar taje ta kamani a banxa in cuci kai na, ko 'yar yagwat da nama ai ya kamata ku siyo min in xauna in ci daga nan, shi ciki ina ruwansa da 6atar mutum, Karfe takwas fa ake nema yanxu ban karya ba.... su kuma wa encan xancen me suke har yanxu kamar 6atar yarinyar bai damesu ba?? Ai ko d'an mage ne ya 6ata sa nuna damuwar su, amma tun daxu suna ta hira ka duba fa" Baffa ya kalli Mami da Abba bai dai ce komai ba, Kaka tace "Su ma shegun 'yan sandan ca suke 'yar kaza ce ta 6ata da baxa su maida hankali ayi abinda ya kamata ba, ni ba ruwana shiga xanyi in fada masu gaskiya...." Baffa ya dakatar da ita yace "Xa mu je can gidan ne dasu ynxu, yanxu duk xa mu wuce..." Kaka tace "Atoh gwara dai mu je din, ni dai tunda na biyo ku ai bbu wanda xai xargeni dai ko?? ita kuma wancan matar dake ta shiga da fice kamar Yan uwanta ne 'yan sandan Allah ya sa...." Shiru tayi ganin Mami da take magana a kai ta nufo su, Kaka tace "Ya ake ciki Rakiya? Ni fa hakurina ya soma karewa, basu da taimakon da xa su mana ne, in je gun Ta salla?" Mami tace "A'a xa mu je gida ynxu da 'yan sandan kaka, iya bincike ya nuna bbu wanda ake xargi kan bacewar Heedayah sai Hajiya Maryam...." Kaka ta wani tabe baki tace "Lallai!!! To da baxa a xargeta ba? muguwa ce fa, a jiyan da daddare ma daga waje naga ta shigo bansan uban me taje yi waje tsakar dare ba.... Idan ba rashin gaskiya ba menene wannan din??" Kaka ta fashe da kuka sosai tace "Kilan lkcn ta mika Deedayan ta dawo... Dama tun ba yau ba kowa yasan Maryam bata da Imani, Kuma axxaluma ce, akwai wata mai aiki da tayi da dadewa sai da ta kusa kashe mata ido daya, da kyar Amadu ya shawo kan kess din, sannan ta ta6a aiken Mai gadi mota ta kwashe gantalalle a titi ya karairaye, shi ma dai Amadu ya shiga ya fita aka rufe kess din, sannan kwanaki shi ma da dadewa taje gidan kitso tasu ta hado su da matar wani babban mutum, Maryam ta tattakure ta sharara ma mata mari, in takaice maki dai awowin Maryam uku a seff, da kyar Amadu ya shiga ya fita aka yi belinta sannan ya kashe kess din, Kinga kuwa ai Maryam takadiriyar mace ce, mu dai kawai muna xaune da ita ne saboda su Shureen" Mami dake ta sauraronta tace "Yanxu ma ita xa a je daukowa don ita ce first suspect kan 6atar Heedayah...." Kaka ta saki kabbara da karfi tace "To da pa?? ai dama ita ce ni dai tunda ba a xargeni ba Alhmdllh, a xargi kowa ma, har shi Amadun...." Mami ta juya ganin Yan sanda biyu sun fito ta nufi motarta da su, kaka ta bi bayanta da sauri tana cewa "To dama idan ba ke ba wa xai tsaya kan maganan nan, Amadu dama tun yana karami wani solobiyo ne, lauyancin ma Allah ne ya basa ba wayonsa ko dubara ba" duk wannan abun Abba na tsaye daga inda yake yana kallonsu, haka ma Baffa da ya ki cewa komai, Baffa ya sauke ajiyar xuciya ya nufi d'an uwan nasa.... Heedayah ta daga kai jin an amshi cup din shayin da take sha, tace "Ban shanye ba ai tooo" Yana rike da hannunta suka fito parlor, tace "Tell me who you are.... Yaya that gives me chocolates? Or Yayana, yayana din Farida?" Jin bai bata amsa ba, ta tattaba hannunsa tana turo baki tace "Ka ji mana, tell me" Jan bakinta taji anyi ta kai hannunta da sauri tace "Ouchh, me na yi?" Bai ce mata komai ba, ta warce hannunta tace "Nasan waye" ya tsaya yana kallonta, can ya durkusa kusa da ita ya jawota dabb da shi ya kai bakinsa kunnenta, murya kasa sosai kamar me rada yace "Waye?" Tayi shiru kamar tana son gane muryan, can ta fara komawa baya a hankali tace "I don't know you" jawota yyi ta fasa ihu tace "Maminaa" ya dauketa kamar yar baby suka fita parlon har kofar gida inda yyi parking, front seat ya bude ya sata ciki ya daura hannu saman lips dinsa yace "Shiiiii" he could see how afraid she is, hawaye ya kawo fararen idonta tace "Plss take me back to Mami, ban san ka ba" rufe motar yyi ya tafi ya sa ma gidan makulli sannan ya dawo ya hau motar ya bar layin... Wayarsa ne ya fara ring, ya kalli wayar ganin me kiran sa ya samu waje me kyau yyi parking sannan ya dau wayar ya fita waje don amsa kiran, bayan few mins ya dawo cikin motar ya d'an kalli Heedayah sannan ya ci gaba da driving dinsa..... Rirrikesa Heedayah tayi jin alamar wucewa xai yi ya bar ta bayan ya saukar da ita daga motar, cikin kuka tace "Don Allah don't leave me ka kai ni wajen Mami da Abba first, plsssss..." Ya cire hannunsa daga nata ya koma gun motarsa walking very fast, within a twinkle of an eye ya bar anguwar... Heedayah ta fashe da kuka sosai jin tafiyar motarsa ta dinga kwala ma Abba kira tana yarfe hannu, Mumy ce ta fito daga cikin babban gidan a rikice bayan kiran da Abba yyi mata yace ta bar gidan, hijab ne har kasa a jikinta ko kayan kirki bata sa ba da makullin mota a hannunta, tsabar rudewa mancewa tayi da motar a compound ta fito bakin gate da kafa, karo ta kusa ci da Heedayah dake kuka sosai tana laluba inda take, Mumy ta ja baya a d'an tsorace tana kara kallonta, lkci daya ta saki salati ta riko hannunta tace "Kee wa ya ajiye ki a nan, wa ye ya dawo dake???" Heedayah ta dakatar da kukan da take jin muryarta, Mumy na kalle kalle kamar munafuka tace "Nace wa ya ajiye ki a nan?? Ina yake???" Heedayah dai bata ce komai ba sai shessheka take, Mumy ta kwalo ma mai gadi kira a rikice, ya fito da gudu yana amsawa, tace "Isiyaka wa ya ajiye yarinyar nan bakin kofa, daga ina ta fito?" Ya matso da sauri yana kallon Heedayah da kyau yace "Ikon Allah ba ita ake nema ba Hajiya?" Mumy ta daka masa tsawa tace "Cewa nayi wa ya ajiye ta a nan kana tambayata tambayar banxa, waye ya dawo da ita" Yace "Wllh wllh Ina ciki Hajiya ban san daga Inda ta fito ba, Banda yanxu da kika kirani ni ban san ma akwai mutum a nan ba" Mumy ta fashe da kuka sosai tace "Kai shaida ne isiya yanxun nan na fito na ganta tsaye bakin gate din nan, ni ban san daga Inda ta fito ba, ban san wa ya ajiye ta ba" Isiya ya rike ha6a yace "Ikon Allah, to waye ya maido ta kuwa?" Mumy na goge idonta tana kalle kalle kamar munafuka ta marairaice tace "Amma kaga ba lallai kowa ya yrda a bakin gate muka ganta ba isiya... Ni dai kai ne shaidana fitowata kenan daga cikin gida na ganta, yanxu ka shiga da ita ciki ni xanje can in dawo, maxa ka kai ta ciki" tana fadin haka ta kara gaba da sauri tana hade hanya, isiya ya bi ta da wani kallo kafin ya ta6e baki yace "Da dai ba a san ki bane Hajiyaa, Lallai na yarda Allah na fitar da me kyau cikin mara kyau...." Yana fadin haka ya girgixa kai ya kama hannun Heedayah ya shigar da ita cikin gidan yace "Allah dai ya kubutar dake yarinya, da yake baki da hakkinta sai gashi Allah macecin ki, irinta macecin ki" sai da Mumy ta tabbatar ta shiga adaidaita sannan ta kira Abba, yana dagawa ta fashe masa da kuka sosai tace "Wllh barrister ka ga gashi an maido yarinyar nan kamar daga sama, ni dai ban san komai kan lamarin nan ba ban san wa ya dauketa ba ya sake maido da ita yanxu, Ina fitowa bakin gate muka ci karo da ita wllh wllh iyakar gaskiyata nake gaya maka isiya ne shaida na, tare muka ganta rakube gate tana kuka, Mu dai bamu san ta yaya ba" Abba da ke xaune mota tare da Baffa suna dawowa gida da farko kasa ce mata komai yayi, can dai yace "Yanxu ke kina ina?" Tace "Ga ni a adaidaita xan tafi gidan Aunty Zuwaira" yace "Toh ki tafi can din, Heedayar na gida yanxu haka?" Mumy tace "Wllh kuwa, tana can na baro ta tunda kace in bar gidan" Abba bai ce komai ba ya katse wayar, Abba ya jinginar da kansa da kujeran motar yyi shiru, Baffa da ke jin duk yanda suka yi da Mumy a waya da yake a hands free Abba yasa, ya sauke ajiyar xuciya, Abba yace "Ba Maryam ta dau yarinyar nan ba...." Baffa yace "Ba ita ta dauketa ba, amma she knows everything about it...." Abba ya kallesa yace "Not much, matata ce na san when she is lying and when she is not, nasan Maryam bata son yarinyar nan xa ta ma iya sawa ayi abinda ya fi dauke Heedayah, but this time around ba ita bace, I will have to go deep into this matter" Baffa dai bai basa amsa ba.... Salatin da kaka ta saki bakin kofar parlor ya sa Mami ta karaso da sauri 'yan sanda biyu na biye bayanta, Heedayah suka gani xaune saman kujera a parlon ga Karime da Sajida da su Rabi'ah duk a parlon, Shuraim na tsaye daga wajen dinning ya rungume hannunsa, Kaka tace "To ni dai Allah ya isa cutan hanjin ciki na da aka sa nayi na bar su da yunwa basu ji ba basu gani ba, tunda uwata ta haifeni ban ta6a kai wa karfe tara ban karya ba sae da wnn yarinya ta 6ata, gashi yanxu har wani jiri nake ji kamar xan kwanta gadon asibiti...." Bbu wanda ya kalli kaka, Mami ta karasa gun Heedayah dake xaune tayi shiru hawaye bushe a idonta, kafin tace komai daya daga yan sandan yace ce "Ita ce yarinyar?" Mami ta mike so surprise ta girgixa kai tace "Ita ce, she is the one...." d'an sandan yace "We are going back to the station with her, but before then a gidan nan suspect da xa mu dauka take??" Mami tace "Ehh nan ne" Shuraim ya kalli Mami ta gefen ido, Kaka ta nufi bangaren Mumy tace "Mu je in kai ku dakinta, ko ba Maryam ba...." Yan sandan suka bi bayanta xuwa bangaren Mumy, bbu kowa parlon da daki da ma bathroom, Kaka har da duba karkashin gado da cikin press din kaya, ta dudduba bayan labule, bata yarda ba sai da tasa suka dage katifar gadon, Kaka na hada xufa tace "Ta tsere, kaga ta sa an maido da yarinyar ta gudu, to Allah ya isa wahal da mu da tayi, Allah yyi mata abinda tayi mana...." Yan sanda suka fita dakin, nan dai suka dudduba sauran dakunan cikin gidan amma bbu Mumy, Kaka na kallon Shuraim tace "Toh Shureen ga uwarka dai ta dawo da Deedayah ta gudu...." Calmly yace "Ita tace maki ita ta dauketa??" Kaka ta nufesa da sauri tace "Kar ka min rashin kunya, kana min xan sa 'yan sandan nan su casa min kai yanxun nan su tafi da kai caji ofis" Khadijah ta sunkuyar da kanta tana dariya kasa kasa, Kaka tace "Atoh, ka yi mana, ya naji kayi shiru, xageni mana" Su kansu 'yan sandan sai da suka yi murmushi, Mami dai ko kallon kaka bata yi ba, Yan sanda suka dau Heedayah tare da Mumy xa su koma station, kaka ta dauko Hijab ta bi bayansu, Mami na kallonta tace "Kaka kiyi tsayawarki ki k'arya mana...." Kaka tace "Ce maki nayi yunwa nake ji, a fara abu da ni kuma sai a ki karewa da ni" Mami bata kuma ce mata komai ba ta bi bayan 'yan sandan suka fita, Kaka na biye da su da sauri. Hajiya Sadiya ta rike ha6a tana kallon Mumy da tayi tagumi tace "Ikon Allah, wllh wanda ya dauketa a gidan yake, bbu shakka ya gano komai ne yyi hakan, kuma ba kowa nake xargi ba illa Shuraim" Mumy ta dago da sauri tace "Shuraim?? Shuraim dai, A'a Shuraim baya ma gidan hakan ya faru, yana can asibiti" Hajiya Sadiya tayi wani dariya tace "Dai dai ma kenan tunda baya gidan, wato shine ya bi dare ya sadado ya dauketa...." Mumy ta mike tace "Haba Shuraim baxai ta6a yin haka ba, Bai san ma komai kan wannan plan din namu ba, to idan ma ya sani Allah na tuba meye hikimar dauketa balle bai sani ba, he has nothing to do with the blind girl a gidan, ko kallonta ma shi bai yi, Yan gidan ma yaushe ya samu lkcn yi masu magana balle makauniyar? Bai ta6a kallon inda take ba ma" Hajiya Sadiya tace "Wllh ko rantsuwa nayi baxan yi kaffara ba Shuraim ne ya dauke yarinyar nan, idan ma xaki yarda ki yarda, wnn d'an naki baki san kyar yake kallon ki ba ko? to wai idan ba shi ba Aljanine xai shigo ya dauketa? Ke ki duba lamarin nan fa, sannan kince a bude kika ga gate din bayan gidan ba wai 6allawa aka yi ba, waye yasan wani inda makulli yake?? Gwara ki ajiye wnn batun na cewa Shuraim baya kula kowa a gidan, Kuma in har yaron nan naki na gidan nan bbu abinda xa a yi ma wannan yarinyar...." Mumy dake tsaye ta kasa cewa komai tace "Shuraim Kuma, Shuraim????" Hajiya Sadiya ta ja tsaki tace "Ai sai ki yi kuma, kema kinsan duk shirunsa shegen wayo ne da shi snn kinsan he is never in support of anything bad.... Tsaf shi xai dauketa sannan ya maidota bayan yaga duk an watse a gidan" Mumy dake xufa ciki da waje tace "To kuwa xan ci ubansa la'ada waje, xan ji ko shi ya haifeni ko ni na haifesa" Hajiya Sadiya tace "Atoh wnn dama dai ta wuce kuma, sai mu tari gaba, ga asara, ga xargin ki da kowa ke yi a gidan, ga kuma 'yan sanda na nemanki..." Mumy ta fashe da matsanancin kuka tace "Ni wllh da ma ni na dauketa ko a jikina, amma bani bace sannan gashi kowa kallon ni na dauketa yake min, ga dai ta nan na hadu da ita a gate da xan fito amma sbda tashin hankali ko tunanin cutarta ban yi ba, kai a lkcn ji nayi na fi kowa farin ciki da dawowarta don wnn ba karamin case bane gashi kaka ta ga shigowana daga waje, da dai kattin sun shigo sun bubbuge kowa ne sun dauke yarinyar da Rabi'ah kamar yanda muka shirya daga baya sai su sako Rabi'ar ai kinga bbu shegen da xai xargeni, to ba a kai ga hakan ba aka nemeta aka

Please Login or Register in order to submit comment