Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

seater yana kallon wani action movie da ake yi, Ta gefen ido ya bi ta da kallo, ita kuwa sai kallon dogon kafarsa take, yana lura da ita, idan ta kalli nasa sae ta kalli nata, bude kofar parlon aka yi ta daga kai Junaid ya shigo parlon da sallama, ajiye cup din hannunta tayi a kasa ta tafi da sauri ta rungumesa tace "Yaya ranan nan ban ganka ba muka wuce" Junaid na kallon kayan jikinta yace "Me yasa kika fito da kayan nan?" Ta kalli kayan tace "Mami tace in sa" Tuni Shuraim ya lumshe ido kmr me bacci, Junaid na rike da hannunta suka wuce parlon Mami, Junaid na kallon Mami yace "Mami kayan nan da ta sa ina ga kamar bai yi ba, she shouldn't be wearing this out" Mami ta kalli wando da rigan dake jikin Heedayah tace "Meye rashin yin sa?" Bai ce komai ba, Mami tace "Hijab xan sa mata ta dinga yawo a gidan ko jallabiya?" Nan ma dai bai ce komai ba, Mami ta masa wani kallo ta ci gaba da abinda take yi, ya xauna ya gaisheta a hankali, ta amsa tace "To sai ka siyo mata jallabiyoyi ta dinga yawo da su" shi dai bai ce komai ba, can ya mike yace bari in je in gaida kaka, Tace "Ohk" fita yyi Heedayah ta bi sa da sauri, Bai tadda Shuraim a parlon ba kuma, ya shiga parlon kaka da sallama, hada kayanta ya sameta tana yi a katon akwatin ta, da mamaki yace "Ina kuma xa ki kaka?" Kamar jiran xuwansa take ta gyara xama ta fashe da kuka ta rike kai tace "Wai da barin garin xan yi Junaidu, in tafi can Inda Allah yayi" Ya xauna yace "Me ya faru kuma kaka?" Kaka na Shessheka tace "Ni dai ba fitinanniya bace ni kuma ba rigimammiya bace Junaidu, kaga tunda uwar ka ta dawo gidan nan ta daina sake min fuska, yau kwana biyu da dawowarsu Ina kirgawa, Deedayar ma ta rabata da shigowa nan gaba daya, me nayi mata Junaidu? Daga nace a ba Maryam Deedayah bata san duk haushin ba a tafi da ni India bne shine ta kullaceni, toh ko Karen hauka ya cijen ae bana bari Maryam ta rike Deedayah ba, Maryam axxaluma, ae kamar an ba kura nama ne, to tun daga sannan Rakiya ko ta shigo min minti daya kawai take, ita kuma Deedayar ganinta ma ba abu ne me sauki a wajena ynxu, duk wahalar da nayi da ita sae a rabamu haka kawai ba tsididi ba tsadada?" Junaid dake ta sauraronta yyi kasa da murya yace "Kiyi hakuri kaka, bbu Inda xa ki je" Kaka ta kara rushewa da kuka tace "Da ma kayi aurene sae ka kai ni gidanka in huta da jarabar kowa inyi ta kai na, Amma baka yi ba sai gantali kke, wnn shine rana xafi inuwa k'una, ni dai na gaji" Heedayah da ke tsaye bakin kofa ganin yanda kaka ke kuka ta fashe da kuka ta fita dakin da sauri, Kaka ta xaro ido tace "Kaga don Rakiya tayi xaton wani abun nayi mata in shiga uku in lalace ko?" Kuka sosai Heedayah ke yi bayan ta fito ta tafi can jikin kujera ta rakube har da Shessheka, Shuraim da ke xaune dining ya mike yana kallonta, ya kalli bangaren Mumy da gefen ido kafin ya nufeta.... Tsayawa Junaid yyi bakin kofar dakin kaka ya fasa fitowa ya bi Shuraim da ido.


Nagode sosai da ta'aziyar ku gareni, Allah ya sa mu cika da Imani.... Baxan samu post gobe ba I'm still not home.




Heedayah is 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Shuraim na tafiya xuwa gun inda Heedayah ke xaune tana rusa kuka kamar ance ya daga kai ya ga Junaid tsaye kofar dakin kaka ta jikin TV dake kashe a parlon, yyi saurin dauke idonsa ya wuce Heedayah ya karasa gun TVn ya kunna sannan ya dau remote ya koma saman kujera ya xauna ya shiga canxa channel, Junaid ya karasa fitowa parlon ya karasa gun Heedayah ya duka yace "Why are you crying?" Ta gefen ido Shuraim ke kallonsu yana canje canjen tasha, Ta goge idonta da bayan hannunta cikin rawar murya tace "Toh me yasa kaka take kuka ita ma?" Soft smile Junaid ya sakar mata ya dagata suka mike ya ciro handkerchief yana share mata idonta, Shuraim bai yarda ya sake satan kallonsu ba ya dinga kallon screen din Tv, a hankali Heedayah tace "Yaya bana son kaka ta yi kuka kuma, or is she sick?" Junaid ya kama hannunta yace "Mu je ki bata hakuri kice kar ta sake kuka..." Yana rike da ita suka nufi hanyar dakin kaka, Heedayah ta kalli Shuraim da yayi frowning face ya bi su da wani kallo, wani harara ya jefa mata, ta turo masa baki ta dauke kanta tana biye da Junaid xuwa dakin kaka. Kaka na kwashe tarkacen kayan magungunanta da ta jera gaban madubi tana xuba su cikin katon handbag dinta Junaid ya shigo da Heedayah, Heedayah ta rakube jikin kofa cikin sanyin murya tace "Kaka kiyi hakuri ki daina kuka kin ji?" Kaka ta juyo ta kara rushewa da wani sabon kukan tace "Atoh kaga yarinya kenan ma tana bani hakuri balle kattin matan da Amadu ya ajiye a gidan nan, ko sanin ina yi ma basu yi ba, bbu wanda yace min ci kanki har ynxu, haba jama'ah ynxu ace bare ya fi jin k'an ka a duniya a kan naka, me muka hada da Deedayah banda Amadu da ya jajubo mana ita a bakin titi tana galantoyi, amma ace ta damu da halin da ta gan ni a ciki a kan yan gidan nan, abinda su Rabi'ah basu ta6a min ba kenan, ko kuka nake ina birgima basa ce min komai sai ma mayar da ni fim da xasu yi" Junaid ya karasa cikin dakin, yyi kasa da murya yace "Yanxu dai kiyi hakuri kaka..." Kaka tace "Toh ni abinda nayi ma Rakiya ta fita harkata a gidan nan ne na kasa ganewa har ynxu, ka dubi Allah ka tafi ka tambayo min ita abinda nayi mata yanxun nan..." Junaid yace "Babu abinda kika yi mata kaka, kawai dai...." Kaka ta daga hannu sama tace "Aa ba ruwana ka tafi yanxu ka tambayo min ita kawai, ko gaisuwar kirki fa ta bar min a gidan nan, haka kawai gida duk ya min xafi kamar mayya, ko don an gan ni shiru shiru me hakuri bana son tashin hankali??" shiru Junaid yyi yana kallonta, sai kuma ya juya a hankali ya nufi kofa xai fita suka kusa cin karo da Salima, haka kawai gabansa ya fadi, hanya ya bata tana kallonsa, shi dai bai bari sun hada ido ba ya fice dakin, Heedayah dake tsaye har sannan cikin sanyin murya tace "Kinyi hakuri kaka?" Kaka ta kalleta tace "To uban wa nake takama da shi idan banyi hakuri ba Deedayah? Bani da kowa sai Allah sai ma'aikin Allah, ni a yanxu fa da ni da juya daya nake kallonmu don wa ennan ba 'ya yan nuna ma duniya bane, Atoh in nuna su in ji kunya, bari dai Junaidu yyi aure wllh da kudinsu baxa su gan ni ba, abinda nafi kowa sanin kan iskanci...." Shiru tayi ganin Salima tace "Waye wannan?" Salima na murmushi ta karaso da ledan hannunta tace "Ni ce kaka, Kin dawo lafiya?" Kaka tace "Ke xan ce ma kin dawo lafiya ai Salima, ni da na samu labarin yau watan ki daya baki gidan nan?" Salima ta hade rai tace "In ji ubanwa? To ai gidanmu na koma" Kaka tace "Toh wani man kika samu yake neman kwale maki fuska kuma yanxu" Salima tayi mata wani kallo ta ajiye ledan hannunta tace "Ga fura na gani a hanya sabon yi me kyau na siyo maki" Kaka ta washe baki tace "Toh Allah yyi maki albarka, dama dai ke din ce me kawo min wa ennan abubuwan" Salima ta kalli Heedayah tace "Ita kuma wnn ido ya bude kenan?" Kaka tace "To da fa? Ae har ta fi ki gani yanxu, bbu abinda xa mu yi sai godiya ga Allah, ynxu ma ji nayi suna cewa boding xa su kai ta...." Bude kofar dakin aka yi Shuraim ya shigo, Kaka ta ajiye jakar hannunta tana nunasa tace "Kai kuma kana gidan nan ina gidan nan amma ka shigo ka gaisheni balle ka san halin da nake ciki kake ganin asara, ai abun kunya ne in nuna ma duniya kai ince jika na ne, ba gwara min Deedayah a kan ka ba...." Heedayah ta kalli Shuraim sannan ta kalli kaka a hankali tace "Kaka sunana Heedayah ba Deedayah ba" Kaka tace "Meye kuma Yeedaya?" Heedayah tayi stressing sunan tace "Heedayah..." Kaka tace "Ba ruwana da wnn, ba Amadun da kansa yace sunanki Deedayah ba, meye kuma laifina a nan, Kai Shureen ba Deedayah ake cewa ba dama??" Heedayah tace "Ae Shureen ma bai san sunana ba, Bai iya fada ba" Fixgota Shuraim yyi, Kaka ta taho da gudu tana cewa "Kul kar ka ta6ata wllh, kana ta6a ta watan barin ka gidan nan ya tsaya Shuraim... A kanta xan sa Amadu ya koreka ka tafi duk Inda xa ka" Kallonta Shuraim ya tsaya yi da mamaki, ta kwace Heedayah a hannunsa tace "Uban me ta hada da kai xaka Fincikota haka, dangin uwa ko na uba?? to wllh kar ka kuma, bbu ruwana da ko kai waye, xan mance sanin da na maka in ci maka mutunci a kanta, yarinyar da tun ba aje ko ina ba tana tausayina...." Shuraim na kallonta da kyau yace "Ki ci min mutunci a kanta??" A fusace kaka tace "Wllh tllh, har shi Amadun sai in 6ata masa a kanta balle kai karan kada miya, ba gwara min ita ba akan kai da Amadun, duk me damuwa da danuwarka ae shine naka bbu wani xancen jininka ynxu" Juyawa Shuraim yyi xai fita suka hadu da Junaid bakin kofar, ya basa hanya ya shiga snn yyi ficewarsa daga dakin, kaka tace "Kai ka ji min katon Mutumi ya finciko yar mutane xai duka daga tace bai san sunanta ba, shi Amadun ne ya sa shi wnn danyen aikin ko bala'i ke damunsa? Haka fa ya xuge uban wai su kai ta makarantar kwana sbda tsabar mugun hali" Junaid yace "Makarantar kwana kuma?" Kaka tace "Wllh tllh, Kai ka ga hakan ya kamata?" Junaid ya kalli Heedayah dake ta kallon kaka yyi murmushi yace "Ya kamata kaka, xata samu karatu sosai kuma xata yi wayo, ta iya xaman duniya a duk ynda ya xo mata" Salima dake ta kallon Junaid ta kashe murya tace "Ae kuwa gaskiya ka fada...." Ko kallonta Junaid bai yi ba, Kaka ta kalleta tace "Ki bar tsomo bakin ki a xancen manya Salima, har fa ynxu kin ki aure ko da yake bbu maneman ne ynxu, ke fa kusan sa'ar Shuraim ce, a haihuwar kaji kin haifi Heedayah fa" Mami ce ta shigo dakin da sallama, Kaka ta juya ta ci gaba da hade kayanta ta wani marairaice fuska, Mami ta xauna, Salima ta duka kasa tana kallon Mami tace "Ina yini" Mami ta kalleta tace "Lafiya lau ya kike?" Salima ta d'an yi murmushi tace "Alhmdllh, kun dawo lafiya ya masu jiki?" Mami tace "Alhmdllh mun gode Allah" Mami na kallon kaka tace "Kaka ynxu Junaid ya sameni da wata magana da ban fahimta ba" Kaka tace "Aa bbu abinda baki fahimta ba Rakiya, yau kwana biyu kenan bakya tanka ni a gidan nan ba kya kulani daga na bugi cikin Amadu in ga ko xai iya ba Maryam Deedayah, so nayi inga abinda ke xuciyarsa game da Deedayah dama, don har ynxu bamu san xuciyarsa ba gaskiya, amma shkkn kika kullaceni...." Murmushi kawai Mami tayi tace "Aa kaka, baki fahimce ni bane ni bbu komai a raina, amma kiyi hakuri idan ke haka kika yi tunani, shi babba ae ba a fushi da shi idan ana son wanyewa lafiya...." Kaka tace "Ka ji ki, kowa ma ai babba ne Rakiya, yanxu wa xai ce ke kika haifi Junaidu, duka duka nawa nake xa a dinga ce min babba kamar wata tsohuwa??" Mami tace "Toh ni dai kiyi hakuri baki fahimce ni bane kaka" Kaka tace "Ni komai ya wuce a gu na, amma fa ko shigo min nan Deedayar ta daina yi, ban san ko ke kika hanata ba" Mami tace "Toh xan dawo da kayanta nan din In sha Allah" Kaka tace "Ae dama a nan kayan suke tun xuwanta gidan nan kawoa shaidan ne ya shiga ya fita ya hada mu" mikewa Mami tayi tana murmushi tace "Ina d'an wani aiki ne kaka, bari in je in karasa" Kaka tace "Toh yi tafiyar ki, Allah yayi albarka" Mami ta fita parlon, kaka ta kalli Junaid tayi kasa da murya tace "Ae gwara haka dae mun tura mata aniyar ta ko?? Gashi ta shigo tana ta borin kunya, amma ae baxan nuna mata na gane ba" Murmushi kawai Junaid yyi yace "Xan je anjima in dawo kaka" Kaka tace "Toh Allah yyi maka albarka" Heedayah tace "Are you going with me Yaya?" Ya kalleta yace "No...." Bin sa tayi da kallo har ya fita dakin, Salima ta mike ta bi bayansa, Kaka ta bude baki ta bi su da ido can tace "Tabdiijam, toh me wnn yar duniyar ke nufi? Son Junaidun take Koko? Naga har kasa ta duka ta gaida Rakiya abinda ko Amadun bata ta6a dukawa kasa ta gaishesa ba balle ni da na haifesa" kaka ta ta6e baki tace "Toh sai mu xuba ido mu ga gudun ruwanta, karuwa ce fa, meye dalilin da xata makale ma Salihi irin Junaidu" ta kuma ta6e baki ta kalli Heedayah tace "Maxa tattara ledojin nan ki kai masu kitchen can ki watsar ki dawo ga sauran mantina na ajiye maki, yau xaki ga ynda nake wanke bandaki ciki da bai, ba a xuba maki ido ki lalace ba baki iya komai ba" Heedayah ta duka ta kwashe tarkacen ledojin Kaka ta fita da su, har lkcn Shuraim na xaune parlor sai dai bbu abinda yake, ta tafi bakin kofar kitchen ta watsar da ledan ta juyo suka hada ido da Shuraim, calmly yace "Koma ki kwashe su" Ta make kafada tace "Ae Kaka ce tace in ajiye a nan" tana fadin haka ta wuce abun ta, ya mike yace "Keee" tsayawa tayi tana kallon eyeballs dinsa, ya daure fuska sosai yace "Koma nace ki kwashe su" Ta wani xare masa ido tace "Ni baxan kwashe ba, ai kaka ce tace in wurgar a nan" Bude baki yyi yana kallonta, ta nufi dakin kaka tana waigosa har ta shige dakin, Kaka tace "Ga wasu nan ki tafi ki watsar" Kwashe sauran tayi ta nufi kofa xata fita suka ci karo da Shuraim, kamota yyi ta ji kawai ya tsula mata abu me xafi, ta fasa ihu a tsorace jin shegen xafi, kaka ta saki xanin gadon hannunta tace "Auxubillahi waye wnn?" Ko kallonta Shuraim bai yi ba ya juyo da Heedayah yana kallonta da kyau yace "Ki ka ce min baxa ki kwashe ba?" Bai jira amsar ta ba ya kara tsula mata dorinar hannunsa a jiki, ta fasa wani karan a rikice tana sosa wajen tana rusa kuka, Kaka ta fashe da kuka tace "Nace waye wannan??" Shuraim ya murda kunnenta ya sake xabga mata dorinar a jiki, fuskarsa a murtuke yace "Nace maki ina wasa da yara ne? Daga yau kika sake kallon Inda nake a gidan nan sai na fasa maki ido na cire su..." Yana fadin haka ya tura ta ya fita dakin, Heedayah ta kankame kaka tana kuka sosai tana kiran Mami, Mami ta fito xata wuce kitchen taji ihun Heedayah da sauri ta shiga dakin kaka, Kaka na ganinta ta kara rushewa da kuka tace "Hada mu yyi ya xane Rakiya, Ashe dama Shuraim d'an da6a ne bani da labari, dorina fa me baki biyar ya dauko yayi ta tsula ma yarinyar nan bata masa komai ba, har cewa yyi xai fasa idanuwanta ya kwakule to kungiyar yan shan jini ya shiga ne bamu sani ba??" Mami ta dinga kallon kafan Heedayah da shatin dorina ya kwanta, juyawa tayi ta fice daga dakin direct dakin Shuraim ta nufa, tsaye ta samesa dakin nasa, a takaice tace "Shuraim a kan wani dalilin ka doki Heedayah?" Bai ko juyo ba balle ya tanka ta, rai bace tace "Am I even supposed to ask why? How dare you? Ka fara hauka ne? Ko ka fara shaye shaye? To wllh daga yau ka sake gigin mata kallon banxa balle ka kai hannunka jikinta xaka sha mamaki na a gidan nan, Wait... Are you mad?" Daga kai yyi ya kalleta ta madubi jin yanda tayi stressing mad din, still bai ce komai ba dai, tace "To kayi na farko kayi na karshe wllh, ko me Heedayah xata yi a gidan nan naka kawai ido, kada ka sake kai min hannunka jikinta" tana fadin haka ta fice daga dakin, Can tsakar gida kaka ta kai ma Me gadi wayarta ya kira mata Abba taji ko kungiyar yan shan jini Shuraim ya shiga ba a da labari a gidan, daga karshe dai me gadi ya jogale waya fitina ya koma kansa ta tara masa mutan anguwa. Tun daga wnn ranan Heedayah ko fitowa tayi main parlor ta ga Shuraim sae ta koma daki da gudu, ko da kuwa tare da Mami take, wani irin tsoronsa na musamman ta fara yi a gidan, ko dakin kaka ya shigo idan ma a xaune take sai ta rufe ido wai tana bacci, idan a kwance take ma haka, ko karatu suke da mu'allimar da Abba ya dauko mata a waje tana ganinsa xata daburce kai kace mala'ikan mutuwa ga gani, Mumy kuwa kullum idan ta fita da safe sai yamma take dawowa kamar ma'aikaciya nan kuwa tuggunsu kawai suke hadawa da Hajiya Sadiya, kudi kuwa ta kashe ya kusa dubu dari biyu.... Kaka na xaune parlon Abba bayan isha, Abba yyi shiru yana sauraronta, Mumy kuma na hada masa fruit salad, Kaka tace "Toh shine nace bari in xo in ji dalilin hanata xuwa gidan nan da tayi bayan sun yi hutu..." Abba yace "Kaka ba ita xata hanata xuwa ba, sai dai Baffan nata yace ta xauna can gidan, kinsan duk makaranta daya suke tare da yaransa, to da aka daukosu daga makarantar dole can gidan xa a kai su ai...." Kaka tace "Toh shi Baffan wiwi ya sha da xai hanata xuwa gaida mahaifiyarta har ynxu? Ni sai in iya xuwa in samesa in gaya masa gaskiya, ko don Rakiyar bata magana? In dan ta nine ma Faridar ta dawo nan gaba daya kawai" Abba yace "Ni dai bbu ruwanki da wnn kaka, ai dole kafin su koma makaranta na san xa ta xo nan din, tunda hutun da saura har ynxu" Kaka tace "Idan an koma tare xa su koma da Deedayah kenan?" Mumy ta saci kallon Abba ta ji me xai ce, Abba yace "In sha Allah" kaka tace "Toh Allah dai ya kai mu lafiya, nafi son yarinyar ta xo nan ne su yi ta sabawa da wnn yaro...." Satan kallon Mumy kaka tayi sai kuma tayi shiru, Abba yace "Wani yaro?" Kaka tace "Su saba da Deedayar wai" Abba yace "Ohk" Abba yyi kasa da murya yace "Dama kuma Ina son xuwa in sanar maki kaka, Shuraim ya samu Soja...." Kaka ta dafe kirji tace "Sojaa???" Abba yace "Ehh" kaka ta saki salati tana tafe hannu tace "Naga abinda ya isheni, uban waye ya masa sha'awar soja ni Patuu, yyi ta harbe bayin Allah kenan basu ji ba basu gani ba? Yana xaune a mutum dinsa ma ya aka kare da shi balle ace an basa wani soja?" Kallonta kawai Abba yake, Mumy ta wani hade rai tana ci gaba da abinda take, Kaka tace "To waye ya samar masa Soja???" Abba yace "Abokina...." Kaka tace "Baka basa labarin bakin halinsa bane da mugunta, don duk mutum me shiru shiru mugu ne" Abba bai kuma ce mata komai ba, Kaka ta kyabe baki tace "Toh ni dai ba ruwana, shi massers din da yake fa" Abba yace "Xai ci gaba" Kaka tace "To ni dai ba ruwana, Shureen a khakin soja ai abu ya lalace kuma, taka mu kawai xai dinga yi yana wucewa wllh" Abba yace "Kaka an gaya maki ne domin kiyi masa addu'a Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, duk wnn xancen da kike yi ba shi bane kaka" Kaka tace "Toh Allah ya sanya alkhairi, amma wllh ba ruwana wataran idan bamu yi hankali ba duk nuna mu xai yi da bindiga mu shiga uku, Abinda na fi kowa sanin halin d'an nan naka Shureen, kwanaki kana ji cewa yyi xai kwakule idon Deedayah ya kai kungiyar su amma ko mataki baka dauka ba, ni dai ina ta xuba ido in ji tace idonta na ciwo ko wani abu wllh a nan xan rufe ido mu tafi gidan yan sanda in gaya masu abinda Shureen yace" Tana kai wa nan ta fice daga parlon, Mumy dai ta cika kiris ya rage ta fashe sai dai bata tanka kaka tun asali dama, Abba ya sauke ajiyar xuciya ya girgixa kai shi ma bai ce komai ba... Yau Heedayah tana xaune dakin kaka tana kallon cartoon ta cikin glasses dinta dake mata kyau sosai kullum baya rabo da idonta, kaka ta yi mata maganan ta miko mata darduman kusa da ita yyi sau uku amma bata san tana yi ba, gaba daya hankalinta na kan kallon da take, aka bude kofar dakin Shuraim ya shigo, rufe ido tayi da sauri xuciyarta na bugawa, Kaka tace "Algungumar yarinya kawai sai wahala take bani Shureen, tun daxu fa nake mata magana tayi min banxa ta saka kallon jaraba da baxae mata gafara ba a gaba, ni dai wllh na gaji da yarinyar nan, ba ta da aiki fa sai kallon robobin nan da an mayar min tashar wa'axi sai ya canjo min na aljanu, gashi kaf gidan nn bbu wanda ta raina sama da ni, ynxu kuma daga ganinka ta runtse ido ba tsoron Allah, shi boding din har ynxu basu koma bane, naji labarin Farida sun yi hutu wajen Junaidu fa, kawai dai Uwar bata bari ta xo mana nan bane..." Bude kofar dakin aka yi sai ga Farida ta shigo tana kalle kallen Inda xata ga Heedayah, she looks so happy, ganin Heedayah ta saki jakar hannunta ta tafi da gudu ta tsallake Shuraim cike da murna ta rungume Heedayah gam tace "Didi na dawo, Didi I am happy you can see me...."





Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....




Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍


Heedayah ta bude ido a hankali tana kallon fuskar Farida, murmushi tayi ta rungumeta ita ma tace "Farida" sai kuma ta saketa tana kallon fuskarta, ta wara manyan idonta ta kai hannu dimples dinta tace "Kamar na Yaya" Dariya Farida tayi tana kallonta, she is so happy seeing Heedayah, Kaka ta nemi waje ta xauna tace "Allah sarki, jininsu ya hadu wllh, su Rabi'ah da Khadijah dama bakin hali baxae bar su suyi hka ba, uwar tayi kane kane ta hanasu, ko kulata ma basa yi a gidan, ita ma Deedayar ta kanta take" Farida dake

Please Login or Register in order to submit comment