Join Our WhatsApp Group


You Cannot Download this book untill you login but you can read it .


Login Register

ki a titi kina galantoyi, kinga kuwa ai da ruwansa da ke, ni dai ki bar rashin kunya, haka kawai kina fama da makanta kina fitsara, ni ban taba ganin inda aka yi haka ba" Heedayah ta daura kafanta saman gadon tace "Shi ma ba yana maki fitsaran ba kullum.... Kaka gaya min ma yanda yake" Kaka tace "Shureen din?" Ta gyada kai, Kaka tace "Tohh, yana nan dai wani dogo kamar fal waya, wani lagwai lagwai, shi dai baxa a ce masa fari ba kuma baxa ace masa baki ba, Sudess ya fi sa haske, snn a tsaye yake bai dai kai samudawa ba, kinsan da shi da d'an uwan nasa Sudess basu da aiki da sai xuwa gidan karafe suna dagawa, to ynxu duk sunyi hankali, yana nan kuma da kwala kwalan idanuwa kamar dai naki, amma naki ya fi nasa kyau, Inda Allah ya cecesa hancinsa har baka wllh, sannan bakinsa d'an tsut, shi ke hanasa magana kila" Heedayah ta juya ido tace "Toh meyasa sai yyi ta cin xalin mutane, haka ranan ya doki kawata Farida" Kaka tace "Toh wnn kuma sai dai mu ji daga garesa, kinsan yana tsaye bakin kofa... Kai Shureen me yasa kake cin xalin al'umma" Heedayah ta xaro ido tana komawa baya saman gadon kamar xata yi kuka a hankali tace "Kaka yaushe ya xo?" Kaka tace "Tun tambayar ki na farko amma kinga ai baxai yiwu in katse maki hanxari ba tambaya ance mabudin ilimi...." Shuraim sai kallon Heedayah kawai yake ya rungume hannunsa, can ya gyada kai ya juya ya fita dakin, kaka ta rufe kofarta tace "To ni dai ba ruwana Allah ya so ban fadi wani mugun abu a kansa ba, ke kuma kar ki iya bakinki da surutu, wllh karya ki xai yi ba ruwana, ko kanninsa baya wasa da su duk tsoronsa suke, ke kuma gashi har ce masa mugu kika yi kika ce karya yake, ni dai ba ruwana" Heedayah da har hawaye ya kawo idonta tayi shiru tana sauraron kaka. Bayan Magrib Heedayah na dakin kaka har lkcn bata koma bangaren Mami ba, a hankali Kaka ke daukan naman kwanon gabanta tana ci kar Heedayah ta sani balle ta bata, kaka tace "Toh ko uwar ce ta hanata shigowa yau gaba daya bani da labari, da ta shigo fa da ynxu kinga ta gyara min daki ta goge tace xata wanke bayi, yarinyar ba dai tsafta ba gata yar gayu kuma kyakkyawa fara, har da lotsa kumatu gareta, naga kamar ma har waya gareta, 'ya yan Amadu kuma ga su nan dai wasu kolaye kazamai, Kinga da Shureen wani ne ae sai ya nemeta nasan ko don Amadu Rakiya baxata ce A'a ba, to ba a auren aka aureta, shi ma Shureen din ae d'an gayu ne, fess xaka gansa kullum cikin kamshi, ko kadan bai son datti, kinsan ni ya gada amma ba uwarsa ba, Kuma fa wllh auren yake so, ya rasa yanda xai fito ya fada ne amma wnn shiru shirun da yake duk aure ya saka a rai, kinsan indai shirun namiji yyi yawa kawai auren nan yake so wllh" Heedayah dake gefe xaune da plate din shinkafa da miya a gabanta ta ta6e baki tace "Kaka ni fa na san nama kike ci wllh...." Kaka ta fiddo naman da ta kai bakinta da sauri tace "Inji ubanwa, meye kuma nama da xan ci in hanaki kamar wata mayya?" Heedayah tace "Ni dai nama kike ci wllh" Kaka tace "To tashi ki yi ma kanki jagora ki fitar min a daki kada raina ya baci, aniyar ki kuma ya bi bayanki wllh, ni ya kamata in baki nama ko shi Amadun da ya tsinto ki, Kuma wllh ke mace ce ki raba kanki da sa ido gidan wani xaki, meye kuma kinsan nama nake ci, a ina kika ga naman kina fama da makanta" Heedayah ta mike tana turo baki tana ma kanta jagora da hannunta ta nufi kofa xata fita, kaka ta bi ta da harara tace "Aa kifi nake ci ba nama ba tunda Amadu kika ga ya kawo min nama...." Dai dai nan aka bude kofar Heedayah ta ja baya da sauri, Kaka ta saki salati ta mike tace "Junaidu?? Allahu Akbar saukan yaushe??" yana murmushi yace "Daxu kaka...." Yana magana yana kallon Heedayah da ta bude ido sosai, ya daga kanta yana murmushi cikin cool voice dinsa yace "Hey...." shigewa jikinsa tayi ta rungume sa tace "Yaya"




Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....





Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍



Junaid ya dago kanta yana murmushi yace "How are you dear?" tace "I'm fine...." Kaka na washe hakora tace "Ae da ka gaya min kana hanya da nayi maka girki Junaidu, ga dai yara in aika su siyo min kayan miya da yar kaza" yana rike da hannun Heedayah ya karasa cikin parlon ya xauna yace "Aa bana son ki wahal da kanki ne, Ina yini kaka?" Kaka tace "Toh lfya lau Junaidu, to ya hanya?" Yace "Alhmdllh" tace "In ji dai baxa ka sake komawa ba" yyi murmushi yace "Saura kadan in gama kaka" kaka tace "Toh, shima dai Sudess hka na ji yace saura kadan, Shureen dai ne ban san isilin karatun nasa ba, anya ma yana karatun kuwa? Gani nake kamar budirinsa kawai yake a Zaria" Junaid dai bai ce komai ba sai murmushi da yake yi, ta mike ta tafi dauko masa ruwa tana cewa "Toh ko 'yar mantinan nan dai bbu a gidan ynxu, tunda ka tafi fa rabona da wani mantina, hana rantsuwa dai Amadu da Umaru na siya min" Junaid na kallon Heedayah murya can kasa yace "Lolly..." Heedayah ta wara manyan idanuwanta tace "Sunana Heedayah" yace "No Lolly dai" dariya tayi tace "Lolly pop?" Yace "No just lolly" ta langwabar da kanta bata ce komai ba, yace "Where is Farida?" Tace "Tana gun Mami" kaka ta ajiye lemo da ruwan hannunta tace "To ae gaba daya uwar ta hanata shigowa yau, ko ba Farida ba??? Kila don d'an aikin da take min ne ma aka hanata shigowa wa ya sani, kasan bata dade da xuwa hutu daga makaranta ba, shine fa muka sa6a sosai da ita, yarinya me hankali ga shegen aiki a cikinta, ta iya aiki yarinyar wllh" Bowl din naman da take ta ci a boye ta dauko ta dire masa tace "Daxu na sa masu aikin nan suka soya min kayana, nama ce ka ci iya cin ka ba komai ka ji" Heedayah ta turo baki tace "Amma kince min ba nama bane" Kaka ta galla mata wani harara tace "To meye hadina da ke? Ke dai ki raba kanki da kwadayi da sa ido mace kike wllh" Junaid na murmushi ya dau ruwan gora daya ya bude ya fara sha... A boye ya dinga ba Heedayah naman, da kaka ta shiga ciki kafin ta fito xai yanka ya sa mata a baki, da ta aji alamar kaka ta fito sai ta boye fuskarta shoulder dinsa, Daga karshe kaka tace "Ni dai ban ba Deedayah namana ba gaskiya, idan ma ci take ban bata ba gaskiya" Dariya Junaid yyi yana kallon kaka, ita kanta Heedayah dariyar take fuskarta a kafadarsa, kaka tace "Aa ba batun dariya bane Junaidu, ba fa Amadu ya siyo min ba balle ace tana da rabo a ciki, kudin da nake ta tarawa na bada a siyo min daxu, to meye xata wani makale maka tana kwadayi kai kuma kana biye mata? Shegen kwadayi fa gareta wllh" Heedayah ta mike tana turo baki tana ma kanta jagora ta nufi hanyar kofa xata fita, Kaka tace "Yanxu xuwa xata yi ta hada ni da farar matar can..." Heedayah ta bude kofar ta fita daga parlon.... Sai bayan isha Junaid ya shiga bangaren Mami, bayan sun gaisa Mami tace "Me ya hada kaka da Heedayah?" Ya kalli Heedayah dake kwance saman kujera yyi murmushi yace "Ai xa su shirya" Heedayah ta mike xaune tace "Ai baxan sake xuwa ba" Mami tayi murmushi bata ce komai ba, Farida dake xaune kusa da Junaid ta matso kusa da shi a hankali tace "Yaya tell me the truth, sbda birthday din Aunty Shaheedah ka dawo ko???" Ya kalleta kamar baxai ce komai ba sai kuma yace "Eh" Irin kallon da yake mata ya sa ta matsa kusa da shi da sauri tana dariya.... sai wajen karfe tara da wani abu Junaid ya mike xai bar bangaren Mami, don Kaka ta aika Sajida ta kirasa sau biyu kenan, Xai fita parlon Farida tace "Yaya to tsaraban mu fa?" Yace "Tomorrow in sha Allah" yana kallon Mami yace "Sai da safe, daga can xan wuce" tace "Me yasa idan ka xo gidan nan baka son cin abinci?" Ya girgixa kai yana kallon Heedayah dake kwance saman kujera tayi bacci yace "Na ci abinci kafin in taho ne" Mami tace "Toh shkkn, sai da safe" Ya dauke idonsa daga kan Heedayah yace "Allah ya tashe mu lfya, daga haka ya fita parlon, dakin kaka ya tadda Shuraim tsaye daga bakin kofa Kaka na cewa "Ai shi kansa Umarun ya girgixa da bala'i na jiya Shureen, ynxu kuma dama kiransa xanyi ince idan bai mata magana ta janye gantalallen bakinta da ta daura ma bawan Allahn ba nima xan yi Allah ya isa idan shi Umarun ya sake shigowa gidan nan gaisheni, kowa sai yyi ta takama da d'an sa ba shknn ba, amma kan me xata hanasa xuwa gidan nan bayan ga ni kakarsa" Tana ganin Junaid tace "Haba Junaidu har sai furan da nono ya huce, Amadu fa nasa sai ya siyo min, ni ban ga ji abun kunya ba ka xo har dakin nan ka fita baka ci komai ba" Ta gefen ido Shuraim ke kallon Junaid, Junaid ya karasa dakin ya mika masa hannu, Shuraim ya mika masa nasa sannan Junaid ya xauna yace "Kaka na ci abinci fa kafin na xo" kaka tace "Aa kai dai so kawai kke ka tafi kana xagina a ranka ka xo dakina ban baka komai ba" Dariya yyi ya ma rasa abinda xai ce mata, Shuraim xai juya kaka tace "Toh kaji abinda dai ake ciki Shureen, kaya kuma rabi xan ba Deedayah, sauran rabin gaskiya kasuwar 'yan koli xan kai ayi gwanjonsu, to fa bai siya min komai ba ni kamar wanda aka yi ma baki, ko jiya sai da na sake mafarkin nan wai Sudess bai min tsaraba ba hankalina ya tashi sosai" Shuraim yace "Ae dukka ya kamata ki kai ki siyar" Kaka tayi shiru tana kallonsa, can tace "Allah?" Yace "Wllh" kaka tace "Atoh, me xata yi da su ma idan an bar mata su ita ba ido ba, iyaka in d'an debar mata biskit din da swee in ajiye mata" Shuraim yace "Hakan yayi" Kaka tace "Atoh, ga dai Rakiya kullum sutura take mata, bbu abinda ta ragi yarinyar da" Shuraim ya juya xai fita dakin sai ga Farida ta shigo rike da cooler, gefe ya ja ya tsaya, ta wuce ta ajiye ma kaka coolern tace "Kaka gashi Mami tace in kawo maki" Kaka tayi kasa da murya tana kallonta tace "Ita ta hanaki shigowa duk yau koh?" Murmushi Farida tayi tace "Aa fa kaka" kaka ta ta6e baki tace "To da ta hanaki ai ita Deedayar da take tamu ta shigo kuma ta wuni" Farida tace "Wllh Kaka ni ba a hanani shigowa ba kawai karatu nake yi a ciki" Kaka tace "Ayyoo, to ban ji kin gaida Shureen ba, ko baki gansa bane" Farida ta d'an turo baki tace "Ehh ban gansa ba" Kaka tace "Gashi can rakube gefe, gaishe sa" Ta d'an kalli inda yake kafin tace komai ya juya yyi ficewarsa daga dakin, Kaka tace "Au, to yyi ma kansa, Wai haushi yaji nan fa, kema dai in kin gansa ki dinga gaishesa" Mikewa Farida tayi tace "Kaka sai da safe" kaka tace "Toh sai da safe" Farida ta kara yi ma yayanta sai da safe sannan ta fita, kaka na kallon Junaid tace "Kai ka ji fa Junaidu, tsaraba na fitan hankali Sudess yyi ma Deedayah a kasar waje ni kuma ko abun sakace ban gani ba, shine nake tunanin in siyar" Junaid dake saurarenta yace "Aa kaka, ki bar mata su, kar ki siyar" Kaka tace "To ai ba duka xan siyar ba, sai kace wata axxaluma macuciya, 'yan kadan xan deba in siyar in bar mata sauran" Furan da ta dama masa ta ajiye gabansa tace "Kaga dai ko Shureen ban yrda na dibar ma wa ba, kuma yana tsaye na dama wllh" Washegari da asuba Abba na dawowa daga masallaci ya ga kaka bakin kofar parlonsa tana jiransa, yace "Lafiya kaka?" Kaka tace "Ehh to lafiyan kenan, magana nake son yi da kai me muhimmanci, idan na jira sai ka shigo gaisheni bayan ka shirya fita ofiss ba saurarata xaka yi ba sai kace sauri kake" Bai ce komai ba ya bude mata kofar parlonsa ta shiga, ya bi bayanta, ta xauna saman kujera, tace "Kana ji na Amadu?" Xaunawa yyi yana kallonta yace "Ina ji Baaba" tayi kasa da murya tace "Yauwa dama kan maganan Shureen na shigo" yace "Lafiya dai koh?" Tace "Aa lafiya lau, na kawo shawara ne kuma kasan ni bana bada shawaran banxa" Ya gyada kai yana sauraronta, tace "Ni dai kaga yarinyar nan Farida ba karamin burge ni take ba wllh, gata da biyayya iya biyayya, sannan bata da neman fada, uwa uba ga aiki, yini fa take yi dakina tana min share share da goge goge, bata fiye min Deedayah ba sau dubu mai makalewa saman gado? To shine naga gaskiya d'an ka Shureen xai dace da ita duk da mugun halinsa, Kuma da kyar idan ba aure yake so ba, ko kai baka lura ba, a rabu da mutum me shiru shiru kawai, na ciki na ciki, toh kuma shirun ma ai baxai bari ya nemi matar auren ba, shine nake son ayi masa auren, na duba iya dubawa na, na gama hange hangena naga ba kowa xai dace da shi ba gaskiya sai Farida" Tun da ta fara magana Abba ke kallonta with surprise, Kaka tace "Aa ni dai ka daina min wnn kallon kamar warce tace a kashe Shureen, gata fa nayi masa, sannan Rakiya yau watana hudu da ita ko kallon banxa bata ta6a min ba, kwata kwata matar bata da damuwa kaf halinta d'an ta Junaidu ya kwashe, wayayyiyar mata ce sosai, to don me baxan yi kwadayin hada iri da ita ba..." Abba yace "Toh yanxu kaka ni da ba wai ina da iko da Farida bane, ya kike son..." Kaka ta dakatar da shi tace "Aa wllh kai mijin uwarta ce ai, kuma ai a gidan ka take yanxu" yace "Yaushe ta dawo gidan nawa? Ba hutun makarantar kwana da suka yi bane ya sa ta xo? Gidan yayan babanta take fa Baaba" Kaka tace "Toh ni ba ruwana sai in saka gyale a rakani gidan yayan uban nata, Kai sai kayi ta yin abu kamar ba namiji ba meye kuma don ka nema ma d'an ka auren Farida? Ni fa gata nake son yi ma Shureen din don baya magana kuma ni na san aure yake so, kaga kira min Rakiyan yanxun nan ta xo ayita ta kare, Kar ka wani bata min rai" Abba yyi kasa da murya yace "Karatu fa yarinyar take kaka, duka duka ss2 nake jin take yanxu" Kaka tace "To ko Jami'a take ni ina ruwana, karatu na hana aure ne dama bani da labari, ku dai kun cika wahala wllh, cewa nayi ka kira min Rakiyan ta fito, in dai aka ga Shureen bai auri Farida ba to kilan kashe ni ku ka yi kawai" Abba ya kasa cewa komai, kaka tace "To ko in kira Rakiyan da kai na ne Amadu?" Daukar wayarsa yyi, yyi dialing number Mami, tana dagawa yace "Meet me at my parlor now Rahinah" Bai jira ta ce komai ba ya katse wayar.... Da sallama Mami ta shigo parlon, ganin kaka ta xauna kasa tace "Ina kwana kaka?" Kaka ta washe hakora tace "Lafiya lau Rakiya, ya kwanan su Deedayah da Farida?" Mami tace "Alhmdllh" Abba dai bai ce komai ba, Mami na kallonsa tace "Ga ni barrister" Ya kalli kaka yace "Ga ta kaka" Kaka tace "Kai Amadun nan dai wani solobiyo ne wllh, to kai baxa ka yi mata bayanin ba sai ni? To ai duk kai ka cuci Shureen don kaf halinka ya dauka amma banda mugun halin shi wnn na uwarsa ne, Rakiya kina ji na, ba wani abu bane dama ni dai Farida ce ta kwanta min can cikin raina, a gaskiya Ina son yarinyar wllh, shine na xo na samu Amadu Ina neman alfarman a ba ma jikana Shureen aurenta...." Tana kai wa nan ta fara matsar kwalla, Mami da ta bude baki tana kallonta with shock ta kalli Abba tace "I don't get her barrister, as in??" Abba ya sauke ajiyar xuciya bai ce komai ba dai, Mami tayi murmushin karfin hali tace "To kaka ai karatu Farida take yi yanxu, Kuma....." Kaka ta dakatar da ita tace "Kuma me? Ku dai gantalallu ne marasu mafada, karatu ance maku yana hana aure ne, kinga idan na biye ta taku kawai mahakuciya xaku mayar da ni, ni naga dacewan hakan shi yasa nace ayi, ynxu ni ba ni da wata magana da ku kuma...." Tana fadin haka ta mike ta fita parlon, Abba sai kallon Mami da gaba daya mood dinta ya canxa lkci daya yake, can tace "Plss Barrister kayi ma kaka magana, try to let her understand cewar ba mai yiwuwa bane ni bani da iko da Farida wajen yayan Mahaifin ta take, let not make things complicated pls Barrister" shi dai bai ce mata komai ba, kaka na fita dama wayarta ta dauka ta lallaba ta kai ma Farida can bangaren Mami wai ta kira mata Junaid, junaid na daga kiran kaka ta fita da sauri, tayi kasa da murya suka gaisa tace "Kana ji na Junaidu, duk Inda kake ka taho yanxun nan xaka kai ni anguwa ko Rakiya kar ka sanar ma, kana isowa bakin get ka kirani sai in fito" Junaid dake kwance yace "Toh bari in taho kaka" tace "Yauwa Allah maka albarka, Ina jiran ka yanxun nan" daga haka ta katse wayar ta wuce dakinta tana cewa "Gantalallu wa enda basa son abun arxiki, ni bana biye ta taku ba" Kaka na komawa bangarenta sai ga Abba ya shigo da sallama, ya xauna saman kujera gaba daya he look confused, can yace "Kaka yanxu kinga cikin watan nan xa a fitar da Heedayah waje gyaran idonta, so yanxu kinga ai babu wani abu a gabanmu da ya wuce wnn..." Kaka tayi saurin cewa "Haba?? Kuma sun ce idon xai gyaru kuwa? Amma dai da ni xa a je koh? Kasan bata da kowa sai Allah sai ni" Abba yace "In sha Allah...." Kaka tace "Toh yaushe ne tafiyan in fara hada kayana?" Yace "Nan dai da sati uku" Kaka tace "Atoh Allah ya kai mu lafiya, Allah ya dubemu idonta ya bude ni dai" Abba yyi kasa da murya yace "Don haka kaka ki bar ko wani xance yanxu mu ji da gyaran idon da xa a fita yi" kaka ta kallesa tace "Atoh shkkn na bar xancen har sai idon Deedayata ya bude" Abba ya sauke wani boyayyen ajiyar xuciya, ya mike yace "Bari in je kaka, a taya mu da addu'a, ana kan processing din fitan ne" kaka tace "To wani kasar xa aje?" Yace "India" kaka ta washe baki tace "Xa mu ga su Hamita da muganbo kenan Amadu??" murmushi kawai Abba yyi ya fita daga dakin kaka ta mike ta daga hannu sama tace "Allah ka dubi yar marainiyar Allah ka bude mata idanuwanta, ka bude mata ido ya Allah ko son jikinta xai ragu" Karfe takwas dot Junaid ya kira kaka yace yana kofar gida, ta dau Hijabinta ta boye ta fito parlor tana kalle kalle xata fita, Shuraim dake xaune dinning yana shan tea ya bi ta da ido har ta fice daga parlon da sauri, Junaid ya sakko ya bude mata back seat yana gaisheta da ladabi, ta amsa tana washe baki tace "Allah yayi maka albarka Junaidu da bani da kai ai da nayi kuka yau, ni dai wllh ka fiye min kowa ma" murmushi kawai yyi ya tada motar, sai da suka bar layin suka hau saman titi yace "Ina xa mu kaka?" Tayi kasa da murya tace "Yau xumunci kawai nake son yi, kaga ai bai dace ace har yanxu ban san kowa naku ba, to don haka gidan yayan Mahaifin ka xaka kai ni mu san juna" Junaid was so surprise ya dinga kallonta ta madubi yace "Gidan Baffanmu?" Kaka tace "Ehh shi, ai xa a samesa yanxu da safe koh?" Yace "Ehh na bar sa a gida" Kaka tace "To maxa kai ni kar yyi ficewarsa, gwara xumuntakar tamu yyi karfi" murmushi kawai Junaid yyi ya dau hanyar gidan yayan late Abbansa.



Heedayah isn't free, you read for free 🤷🏻‍♀️🤷🏻‍♀️

it's 300 via... Fcmb 3276052019 Hauwa Bello Jiddah

Then you show ur evidence via WhatsApp 07087865788....



Ina masu son kamshi in and out, I mean kamshi irin na manyan mata fa, to ga opportunity, hope dai ba ku mance Innar su Mujaheed da Imaan ba, to ta ce a baku shawara ku siya turaren wutan nan don yana daya daga sirrin kamshin dake tashi a parlon ta kullum, tace me xa ayi da gidan da bbu kamshi, mace bbu kamshi kuma ai bata cika mace ba, daya daga tsatsonta ke hada wnn lafiyayyen turaren wutan da bbu irinsa, for more info contact 08038103096.....

Khaleesat ma dai da turarurrukan take amfani wllh, trust me it's nice and very affordable.... 😍



Parking Junaid yyi a compound din Baffan sa, ya sauka ya bude ma kaka bayan motar, ta fito tana kare ma kantamemen gidan kallo baki bude tace "Nan ne gidan kawun naka?" Junaid yace "Nan ne" kaka tace "Ikon Allah, to mu shiga, Allah ya sa bai fita ba dai...." Junaid ya shiga gaba tana biye da shi yace "Yana nan ai, ga motarsa" Kaka ta kalli motar da ya nuna mata tace "Kamar irin motar Umaru kuwa" Babu kowa parlon da suka shiga, Kaka ta xauna tace "Wato basu tashi ba kenan ana ta bacci" Junaid yyi murmushi yace "Bari in masu magana" daga haka ya wuce sama, kaka ta dinga bin parlon da kallo ta rike ha6a murya can kasa tace "Toh ai masu kudi ne su ma, ba gidan tsiya Shureen dina xai fada ba, ko gidan Umaru bai kai haka ba" Ba a dau lkci ba Junaid ya dawo tare da wata dattijuwa, Ta xauna tana kallon kaka da fara'a tace "Sannu da xuwa Mama, Ina kwana" Kaka ta kalleta tace "Lfya lau wllh, kece matar gidan?" Matar na murmushi tace "Ni ce Mama" Kaka tace "Atoh ya yara, ya gida" Matar tace "Alhmdllh wllh, fatan kun xo lfya?" kaka tace "Toh Alhmdllh, ba ma wanda yasan na fito sai shi Junaidun, nace dai yau bari in xo inyi xumunci ku san ni in san ku, bana biye ta Rakiya da Amadu ba, ko karyawa ban yi ba wllh na fito" Matar tace "Ikon Allah to bari a kawo maki kayan kari yanxu, tashi mu je daga ciki Mama, sannu da xuwa"

Please Login or Register in order to submit comment