Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
tafin hannuna In naso ya rayu in kuwa na juya kanbuna a yanxu sai yabar dunia Lallai ina tabbatar miki da Kinyi zaben tumin dare kuma a sannu zaki tabbatar da hakan Don dagake har mahaifin naki sai Ruwan da zaku kurba ya gagareku badai dani zakujaba Ai duk Wanda Yaja dani to shine zaisha wuya kuma na rantse miki saikin dauka ba nine mahaifiyarki Domin kiyayyar da zan nunama babban maqiyina irinta zan nuna miki Kuma a bainin jama,a don nayi rantsuwa duk Wanda ya nemi Rushemin duniyata to tabbas saina fara rushe tasa Kuma na rantse miki Nida ke ta murza yan yatsunta Sukai qara tace kukan kurciya zawabine saimai hankali ke ganewa ta juya ta fice tana musu dariar mugunta ita da mahaifin nata escote dinta suka rufa mata baya Afnan ta sulale ta zauna a qasa hawaye nabin kuncinta tace shin anya kuwa momcy ita ta haifeta itace mahaifiyarta wacce ta dauki cikinta harna tsawon wata tara kuma Tasha whlr nakudarta Ta Dade tana zargin wannan a zuciyata amman bata taba Tambayar waniba amman yau ta tabbatar ma zuciyata Aleeyu Wanda ke kwance duk abinda ke faruwa a kunnensa ake Ya kira sunanta cikin sassanyar murya Afnan kiyi haquri ki daina kuka ki rungumi qaddarar da Allah ya daura miki Insha allahu zakici ribar rayuwa ko Bayan raina karki taba canja halayyarki Na sanki da haquri gaskia da wadatar zuci inhar kika riqe wadannan sune makaman rayuwa Afnan muna cikin jarabawan ubangiji Bawai yin Allah na rainaba afnan Domin shikeda komai kuma mai ikon yin komai a duk sanda yaso Kuma duk abinda yai ba,a tambayarsa dalili Afnan karki zargi mutane da naimansu da laifi afnan ki dauki Kowa mutumin Kirki saidai Wanda ya bayyana mugun halinsa Ki kyautata huldarki da mutane ki cika musu alqawari inya kama tsakaninki dasu ki fada musu gaskia koda kuwa basasone Kiyi haquri da wautar wawaye daga cikinsu. Kiso mutane har cikin zuciyarki Ki jawosu jikinki ki tausaya musu ki taimaka musu ki janyosu ga shirya da qarfinki Da maganarki da dukiyarki Ita duniya ba azzaluma bace duk yaddah ka zabi rayuwa cikinta ba baki takeba Akowane irin hali kikaga mutun a cikinta shiya zabama kansa Mai kyau ko marakyau Babu wani Wanda zamani zai zalunta face shine ya fara zalumtan kansa Babu kuma Wanda zamani zai kyautatamawa face shine ya fara kyautatama kan nasa Karki yarda ki girmama son ranki sabanin gaskia dason Binta a matakan rayuwa Babu wani mai janyoma kansa tsiya da kansa face son zuciyarsa Domin shine wakilinn komi kuma karkiyi Tunanin qoqarinki da himmarki zasu kaiki ga samawa kanki alkhairi a,a dole saida taimakon mahaliccin ruhi da gangan jiki Mahaliccin sammai bakwai qagaggu da qassai bakwai.... Ya kasa qarisawa Sbd kukan dake koqarin kubce masa Cikin murya sarkakkiya yace ya Allah kada ka baini ikon saba Maka a duk Halin Dana tsinci kaina Dadi ko wahala afnan ki riqe maganganunnan nawa tamkar wasiyyah nake baki Nasan ko Bayan raina zasuyi miki amfani Kuka afnan din take sosai Tace Haba Abba mai yasa kakeson tasarmin da hankali kasa na kasa runtsawa Yanzu idan ka mutu dawa zan rayu? Waxan riqe ya zama bangon da zan jingina rayuwata ? Abbah Dan Allah karka mutu ka barni please banda Kowa sai kai ba yaya adnan Ba momcy Abba inna rasaka nima kashe kaina zanyi Yace subhanallah Haba afnan kina nufin duk nasihar da nai miki ta tashi a banza kenan? Ai duk musulmi na gari saiya yarda da qaddara ta alkhairi dama wacce bata alkhairi ba Kuma ita qaddara duk Wanda ya dauketa. Bazaiyi rashin madadiba Sannan banda abinki ai bacemiki nai mutuwa zanba Sannan ki zama mai tawakkali a duk yaddah rayuwa taxo miki Cikin mutyar kuka tace to abbah Yace yauwa kokefa ki saki jikinki da walwalarki insha allahu abbanki zai taka da qafafunsa Ta dago tana kallonsa sukaima juna murmushi Washe gari Tunda safe su inna suka iso don haka afnan ta nemi tranfer zuwa wani asibitin domin kare lfyrsu don haka kai tsaye asibitin yan sanda suka nufa Wanda ke cikin babban headquater Inna da malam sunyi kuka sosai da rana sady taxo din wucewa airport Sun mata godia sosai itama Don haka afnan har filin jirgi ta rakata taaji Inama da ita za,ai tafiyan Tana kuka har sady ta lallasheta da kalamai masu kwantar da zuciya saida jirgin nasu ya tashi Sannan ta dawo asibtin cike da kewar mijinta Jikin aleeyu ya qara kyau don har yana dan iya dogarawa da sanda malam ya dage wajen yin masa addu,a ba dare ba rana Don haka Shima aleeyun zuciyarsa ta rage zafi ganin iyayensa kusa dashi gashi asibitin da suke asibitin mai cike da tsaro Wato police hospital. Ita kanta afnan yanxu tadan rage kadaicin da take ciki Aleeyu yasa afnan ta kira masa mahaifiyar nafi a waya ya sanar da ita duk abinda ke faruwa itama duniyar nemansa take don kuwa su kausar sun fada mata duk abinda ya wakana a wajen bikin nasu afnan din Don haka ana gobe za,a koma zaman kotu suka iso mahaifiyar nafin da kausar sai wani kawunsu A hotel din garin suka sauka don asibitinma saida dare sukaje ba Wanda yasan sunxo Ita kanta sady data samu kwana bakwai a. Germany Da dare ta sauka don haka Tunda safe ta wuce office domin rarrage Wasu yan ayyukan dake gabanta na Wasu takardu dake gaban tebur din nata Tanayi tana duban agogon dake tsakiyar hannunta Taga ashe da sauran tyme don itakeson taje ta dauki su afnan da iyayensu momynta da na daddyn nata duk su rugunzuma zuwa kotun Don haka Hatta kayan break din da aka kawo mata ko kallon inda suke bataiba Kamar daga sama taji an banko office din nata don haka ta daga kai tana kallon mai shigowar don haka cike da qasaita ya janyi kujera ya zauna Sukai facing Dinn juna yana mata wani irin murmushi Yace sadiya muhammed mai nasara kina neman zaremin mutuncina a idon jama,a to inaso ki sani lallai sai Naga bayanki Bata sauqiba a sannu a sannu na rantse sai Kinyi mutuwa kala dubu kafin kiyi ta gaskia yace na lura lallai bakisan koni wayeba Sady ta tashi cikin zafin rai ta nunashi da yatsa tace Wayekai inba tsageran dan ta,addaba Wanda rashawa ta haifoka zuwa wannan duniyar. Ka tuna da oder da kayo ta miyagun kwayoyi Toka tuna munada rahota Akan haka domin kuwa mun rigada mun siye Wasu daga cikin yaranka. Wanda kake taqama dasu sukasan sirrin ka Tasa hannu ta kashe yar qaramar radion da take recoding ba tare daya saniba Ta kwalama. A,s. P. Kira ya shigo da sauri Tace Me zatace Oho nima ban saniba Aure. Kan. Aure. End ov. Book2 Chapter25 Tace yi maza ka kira yan jarida. Ya sawa adnan hodar iblis Shikuma ai maza a loda giya da garwarwakin da aka da Wasu daga cikin mutanensa dasu. A cikin motarsa da zasu tashi nanda minti ashirin In an loda sai a kira yan jarida maza nnanda minti goma A kama mutanen nasa Zaiyi yinqurin tashi Wasu daga cikin yan sandan suka maidashi Suka zaunar tare da jona masa kan bindiga Sady tai tattaki zuwa gabansa tana jujjuya kan yar qaramar bindigar dake hannunta tace Tabbas ka girgiza ranka shidade daga dan wannan Abun harka tsorata? Ina ikirarinka na fadin sai kasa nayi mutuwa kala dubu kafin nai ta gaskia Ta duqa gabansa tana murmushi tace lallai ka tabbatarma duniya kaine kai fitsari a wando Sbd tsoro. Dagamu saikai a office dinnan baka sanar ma Kowa abubuwanka na sirri Sbd baka yarda da mutane saudayawa sukanci Amana kaikuma ka kudurcin ganin bayansu To inaso ka sani yau asdy mai nasara zatayi nasara akanka Kamar yaddah ta saba Don tana tare da babban yaronka Wanda kayi yarda dashi duk a cikin yaranka Abro. Yanxu haka yana tare damu dakaje kotu da karkaje ya rage naka Cike da bacin rai da kunar zuci ya watsar da yan sandan Idanuwansa duk sun kada ya nunata da dan yatsa Karya kike sady baki isa kiga bayana saidai ni Naga bayanki Karki sake Abro ya isa kotu inkuwa harya isa tona rantse sai Kowa rasa ransa Don Dana wulaqanta a duniya gwara nabar ta gaba daya Ya juya a zafafe ya fice ba tare da wani yayi yinkurin hanashiba Sbd tsorata da Sukai da idanunsa don ita kanta sadyn yana fita taja wata ajiyar zuciya Ta Dora kanta saman tebur lokaci daya kuma ta saki murmushi irin na alamar nasara A babban kotun jami,an tsarone a tsaye suna binciken duk Wanda zai shiga da wani abu inhar na cutarwa ne Janar Yaso ya hana saida sady ta kira shugaban qasa sannan ya tsawatar masa Akan ya bari ai duk wani bincike daya kamaata Sbd tsare rayukan al,ummah Hakan bai masa dadiba dukda yana zaton ba,a zo da duk wadanda yake zaton za,a zo dasu ba Don haka Yadan samu natsuwa kadan kotun ta cika tayi maqil Inda mai shari,a ya buqaci lauyoyi dasu. Gabatar da shaidunsu Lauyan Wanda ake qarane ya soma tashi ya gabatar da shaidunsa marasa mafari Sannan Lauyan dake kare. Wanda ke qara barister nasiru adma ya miqe Ya dubi mai shari,a yace yamai girma mai shari,a inason na gabatar da saidata ta farko wato kakannin afnan Alqali yace kotu ta baka dama Inna da malam suka fito Yace malam so muke ka fadamana sunanka da kuma matsayin aleeyu a wajenka Ya fada masa ya tambayi Inna itama ta fada masa. Sannan yace Ko zaku iya fadama kotu yaddah aka nemi auren afnan da adnan? Malam yace tun yaran suna qanana aleeyu ya sanar dani cewa yanason hadasu aure idan sun girma Bayan sun girmane yake sanar dani cewa matarsa naneman Wargaza masa shirinsa. Wai yarta ba zata auri wani matsiyaciba Ya sanar dani Wanda ta kawo sannan yake sanar dani cewa ba mutumin kirki bane Don haka shi bazai bashiba nima na goyi Bayan hakan Don har yake sanar dani suma iyayen matar tasa basu yarda da zabin da uwar tata Taima yar tata ba Don haka mukaja daurin auren zuwa wata daya cif Biki saura sati daya cif yaran suka iso kauyen suke sanar dani mahaifiyar yarinyar ta samarma yarta waliyar ranar alhamis za,a daura auren yarinyar da Wanda takeso jin hakan yasa muka yanke shawara gari na wayewa Bayan sallar azahar Na tara mutane a qofar gida aka daura auren nasu Ranar goma ga watan goma shekara ta dubu biyu dasha biyu Lauya yace mun gode suka koma mazauninsu Yasa aka gabatar masa da mahaifiyar nafi itama ta maimaita Kamar yaddah malam ya zayyano da zuwar da nafin tayi Akan suk zama waliyan afnnan sukaqi mahaifiyar tata ta koreta Barister yace wancan zaman sunce ranar goma sha biyu ga wata aka daura auren afnan da janar. Amman yanxu gashi bincike ya nuna an Riga daura auren Afnan da adnan sannan akaxo aka daura auren afnan da janar aure kan aure kenan Alqaline zai fadamana a yanxu matar Waye Tunda su duka ai musulmai ne Sannan yace yanason akawo masa manyan direrobin janar dayafi ji dasu Aka kawosu jikinsu sai tsuma yake Lauya yace kunsan dai yanxu Kuna hannu dagaku har mai turaku zuwa aikin ashshar kuko? To bakuda mafita yanxu munaso ku fadama kotu sunanku da kuma aikinku Daya yace sunanan victor dayan kuma yace sunana emmanuel Dukkansu direbobine kuma matuqan dake daukan mutane a yayin da yaqi ya afkawa Wasu qasa da sunan masu cetonsu saisu kamasu su harbe daya Bayan Daya. Lauya yace dasa hannun wa duk kuke wannan aikin? Sukace dasa hannun general abdullahi aminu Abba Lauyan yace to mun sannan yan sanda suka kamasu Sukai waje dasu Sannan ya qara cewa inason a kawomin Abro yanxun Janar yai saurin miqewa idanunsa a warwaje jikinsa sai kyarma yake Ya zaro bindiga kamin Kowa ya ankara ya dauke kan Abro din da ake niyyar kawowa Abinda ya jawo Hankalin jama,ar dake kotun kenan kamin kace me hargitsi ya kaure Yan sanda da sojoji suka dinga yunkurin kare rayuwakan jama,a Daqar akayi nasan riqo janar sai rawar jiki yake yana niyyar fixgewa Anan alqali ya dakatar da qarar yasa aka tsare masa janar da nafi da taci uban dress ta kame Jikinta sai rawa yake Kamar tai fitsari a wando lol Aka dauki gawar Abro babban sojane nan Kowa ya watse Sati guda tsakani aka yankema tsohon comander general abdullahi aminu Abba Hukuncin kisa ta hanyar rataya Bayan an cishi tarar kudade masu yawan gaske Ita kuwa uwar gayyah hajia nafi hukuncin daurin shekara ashirin da biyar aka yake Mata a gidan yari da horo mai tsananisbd cin mutuncin addini da tayi tare da mummunan sharrin dake daukar hukuncin rataya ga mutanen da basujiba basu ganiba tare dacin tarar bata musu sunan datayi Tayi kuka Kamar me taita rogon gafarar iyayenta amman Sukaqi kulata Kowa kyamarta yake Sati guda da gama case din aka salllami a aleeyu daga asibiti ya samu lfy masha Allah Dukda kuwa da sanduna yake yawo Don haka suka tattaro suka dawo garin kano Ita kuwa sady daman tun Washe garin yanke hukunci ta wuce. Germany wajen mara lfy inda tace insha allahu inhar ta dawo zata dauki afnan domin taje taga mijin nata kuma ta kula da lfyrsa Akeeyu kuwa kai tsaye gidansa yasa aka wuce dasu gaba daya Iyayensama sawa yaai aka taho musu da duk wani abu nasi da zasu buqata Daga can qauyen nas sannan ya dauko Wasu daga cikin yan uwan nasa yasasu a cikn gidan kasancewarsa qaton gaske Don haka yanxu afnan batada wani kadaici saina mijinta Gashi kwanannan ba abinda take fama dashi sai yawan kasala tashin zuciya da Yawan barci inna na lura da yanayinta don haka tasa aleeyu ya kira likita domin dubata Bayan likitan ya gama yan gwaje kwajensane yake sanar dasu cewa tanada juna biyu Ba qaramin farinciki inna taiba dan daman tun lokacin da adnan ya kebe da afnan ta Fahimci wani abu ya faru a tsakaninsu dan haka ta wayar da kowa Babu Wanda baiyi farinciki a cikinsuba dan kuwa harsun fara fiddah rai da Adnan dan har yanxu babu amo ba lbr Wayarma da ssuke da sady yanxu idan ta kira baya zuwa saidai babu Wanda yeke nuna mata damuwarsa ta rashin dawowar adnan din kasan cewar kartasa ranta cikin damuwa Itama bangarensa tana cikin damuwa saidai ganin Kowa yayi biris da lamarin yasa itama ta daure zuciyata. Taci gaba da rainon cikin nata Wasa wasa har an share wata biyu duk wani qoqari da aleeyu zaiyi Akan ganin ya samu full information Akan sady amman ina abin yaci tura Tun afnan na daure zuciyata harta Gaza taje ta samu abbanta da maganan Ya lallasheta yace Yace insha allahu Zamuji alkhairi afnan inaji ajikina suna lfy Kasa daurewa tayi ta nufi gidansu sadyn har yanxu mom dinta cin duniyarta da tsinke take tasan komai Akan sadyn Amman saita rufe domin cimma wata manufa tasu Da afnan taje ta sameta sai ce mata tayi suma nemanta suke ruwa a jallo Dan haka babbu yaddah ta iya dole ta koma gida qafafu a sake Tun a hanya take kuka harta isa gida Duk gidan sun kasa gane kanta ta kasa cin komai sai kuka kawai Don ita yanxu ta Gano mijinta baya raye Lallashinta kawai suke dan su kansu sun tausaya mata ganin abinda ke gabanta Cikine dan wata biyar amman saika rantse kace dan wata tara ne Don haka malam ya duqufa wajen yin mata Rubutun dangana Kuma anyi nasara don zuciyata ta rage mata radadi da zugin da kalamanda yake mata Wanda suke dawo mata tamkar a lokacin yake furtasu Afnan idan na mutu Sbd ke zanbar tarihin da za,a Dade ana tunawa dani a Duniya Wlh danace na barki gara raina ya zama fansar wannan furucin Ta runtse idanunta cikin kuka tace kayi haquri yayana ni kainabazan iya rayuwaba idan baka ina ka shgane kabar mai sonka? Tambayar da bata da amsar sa sai kuka Cikinta ya shga wata tara babu abinda aleeyu bai siya mataba daga Wanda ta fada harda wandama bata fadaba badon komaiba saidon kawai ya cire mata damuwa amman ina Abun Kamar qaruwa yake Duk kuwa da doctor wajen scanning ya fada mata cewa yan biyune Amman ina tausayin yayan natane ya qara shgarta Don bata taba tsammanin rayuwa zatazo mata a hakaba Kullun tsara yaddah rayuwarta zata kasance ita da mijinta da yayanta take amman abinda bata saniba ashe yayan nata marayu zasu zama Hakan kesa tayi kuka sosai har sai taji ba dadi kuma ba mai lallashinta Nakuda taxo mata cikin sauqi kasancewar tana tare da inna Don haka ta haife yan yayanta mace Dana miji kyawawa masu kama da ubansu Washe gari haihuwar afnan ta karade ko ina Dan kuwa anty kausar dinta zuwa tayi ta tare a gidan domin kula da mai jego da kuma kyawawan baby's dinta Taron suna na gani na fada anty kausar ta hada an gayyaci masu hotuna da videos Yara sunci sunan aleeyu da mahaifiyar nafi macen ana ce mata taslim na mijin kuma aslim anci ansha a wannan suna Kowa sai sha,awar yaran yake daka gansu Kaga afnan da adnan Kamar har taso ta baci Aleeyu ya saukar mata masu raino don haka bata da wani matsala dan ko kukan Dare basayi inhar ba bra zata basu ba Afnan ta soma saki da lamarin sady da adnan don ta tabbbata basa raye Shiyasa ta soma service dinta amman fa ba ruwanta da Hulda da maza harkar gabanta kawai take duk wani abu dazai hadata danamiji Bata kusantarsa Yaran afnan sun fara wayo don harta fara shawarwarin yayesu Amman aleeyu ya hana yace ta barsu su qara girma da kwari don duka dukafa shekarunsu daya da wata biyu Amman girma da wayon da Sukai saika dauka yan shekaru biyu ko biyu da rabi ne Harkokin aleeyu sun bude tako,ina ya gyara al,amuransa abinda ya faru dashi Saima ya qara masa farinjini a idon jama,a Don sai suke ganin kaman abokan adawane Sukai masa haka Da sanyin safiya afnan tana saman capet dinta a cikin falonta da abbanta ya gyara mata fiye Dana da alokacin dama masu aslim salak take Taji wayarta tana ruru Kamar karta dauka Sbd abinda takema yaran Ga gwarancin da suke mata alamun dai sun qosa da susha salak din Saida wayar ta kusa kashewa sannan ta dauka ta Kara a kunne Hello muryar wacce taji tasa takusa barar da abinda take cikin murna tasa ihu tace sady daman kina raye sady ina mijina dan Allah ki fadamin inda mijina yake Ina cikin kewarsa ina buqatarsa kusa dani please sady Sady tace sha kuruminki qawata ina kusa da mijinki yau dinnan zamu dawo nanda Wasu yan awanni Don haka kizo ki tari mai gidanki ke kadai dan Allah afnan kiga yaddah yake cikin qoshin lfy Cikin zumudi tace insha allah sady yanxu zan iso kodai baya maganata ne? Naga baya nemana? Sady tace kedai kin cika shegen dumi ki tashi ki shirya ki taremu a airport dan ban fadama Kowa dawowarmuba ke kadai na fadamawa don zuwan bazata nakeson yinma kowa Jiki na rawa ta miqe tace toto ganinan zuwa. Yanxu ta nufi sashin inna tana kwala Mata kira inna inna inna tace oh ni yasu wannan kiran mafarauta haka afnan Ta rungumeta tamkar ta samu adnan din tace inna adnan yana raye nanda awa biyu Jirginsu zai sauka Inna tace niko kinsan banson qarya yanxu haka wanine keson yaudararki yake tsakonarki da adnan na rayeafnan tai wata daria harda kyalkyalawa tace Haba inna Waye zai jani da irin wannan zolayar inhar ba raina yake nemaba yace anga yaya adnan tace ai inhar naje Naga bashi bane mutuwa kawai zanyi Inna tace. Hmm Allah dai ya kyauta ta miqe da sauri cikin zumudi ta nufi sashinta Domin cancaro kwalliya Kwata Kwata ta manta da batun yaranta da take damama salak tana shga bed dinta toilet ta fada. Ta bata mintuna sha biyar wajen yin wanka Bayan ta fitone taje gaban dressing mirro Bayan ta gama kwalliyar ne Ta nufi wadroff dinta can idanunta suka sauka kan wata doguwar Riga irinta Larabawa tace tabbas yaya adnan Nason kalar kayannan Don duk lokacin datasa inya ganta sai kaji yace kai qanwata kinga yaddah kika hade kika zama jinsin larabawa kuwa ? Wlh qanwata kedin ta dabance gaki kalar indiyawa gaki kalar larabawa sannan In kika sauya saiki koma hausa fulani tsab lallai ni nayi sa,ar samun mata daya Tamkar da dubu Na rantse ina sonki matata Bawai so na wasaba so na gaskia Wanda bashida Algus Tai murmushi gamida hanzarin janyo rigar mai kalar sararin samaniya Wato sky blue Wohoh wani abin sai Wanda e gani. Wato wani madarar kyau tayi alokacinnan duk Wanda ya ganta kai koda maqinyintane saiya yaba da wannan kyan da tayi Ni kaina admin na yaba dandai kawai ban fara love bane amman da saina taya lol Wato ita kanta data dubi madubi ta qarema kanta kallo tasan tayi kyau iya kyau Tace no wander shi yasa duk sanda ta fita maza keyo mata ca ashe kyan nata na dabanne Taja jakarta gamida makullin motarta da wayarta tana fita Sukai karo Da taslim da aslin Duk sun bata jikinsu da salak din sunyi dame dame sai yanxu ta tuna dasu ta dafe kai ta kwalama mai kula dasu kira ta qaraso da saurinta tace maza dauki yarannan kije ki kyarasu dubi yaddah duk suka bata jikinsu Tace to ranki shi Dade ta kwashe su tai hanyar sanshinta dasu Tana kallonsu taji tamkar ta kwashesu ta kaimasa yaransa ya gansu Amman ina shiryasuma yanxu bata lokacine Abakin qofar inna ta tsaya tace ro inna na tafi kimin addu,a don bazan shgoba ki riqeni tai murmushi tace to afnan Allah ki bda sa,a ya kuma kare mana ke Tace amin inna sannan ta juya ta fice abinta Bata dauki direbaba qatuwar jeef din abbanta ta dauka domin taji dadin zubosu da tarkacensu gaba daya taja motar ta nufi filin jirgin aminu kano Lokacin data isama jirgin bai rigada ya isoba bini bini ta duba agogon dake Hannunta ji take tamkar ta yayo jirgin da hannu Cikin ikonn Allah jirgin ya sauka afnan ta dinga ware idanu don ganin ta inda zasu Fito Kamar daga sama ta hangosu cikin jerib mutanen dake saukowa Idanuwan afnan suka sauka kan fuskar data zame mata baquwa ji take tamkar ta kwasa da gudu ta runguMeshi Cikin kyakkyawan girjinsa wacce ke manne da baqar shirt Arainta tace lallai turai ya amshesa ya qara wani kyau da haske kwarjininsa ya qaru Ita gani takema ya sake zama mata wani dan gayu lallai zaman turai ya amsheshi Batayi auneba har suka kusa qarasowa wajenta ta. Tattaro na tsuwar duniyarnan ta daurama kanta ta nufesu fuskarta dauke da fara,a Saidai yanxu kallonta ya koma kan kyakkyawan diyar da sady ta rungumo mai kama da adnan din Don haka koda suka ida yarinyar ta karba hannunta na rawa tace Tace. Sannunku da zuwa sady tai murmushi tace yauuwa afnan Sai yanxu ta lura da wani haske da qibada sady ta qara kyanta ya qara bayyana Tana sanye da shga irinta mutanen turai da Baqin gilashi a hannunta Afnan fara,arta da mamakinta sun kasa boyuwa tace sady a ina kika samu baby haka so beauty? Ta qara murmusawa tana kallon adnan Wanda yaketa yamutsa fuska da alamar duk tsayuwar ta gunduresa Yarkice afnan Afnan ta zaro ido tace yata kuma ta ina? Ta qara murmusawa kamin tace wacce na haifa Nida adnan a zamanmu. A. Turai Bayan an daura mana aure secretly amman ki gafarceni afnan munyi hakanne kawai dan gudun sabama allah Kinsan duk inda namiji da mace suka hadu to shaidanne a tsakaninsu Ma,ana na ukunsu Babu inda baya rawa a jikin afnan Hatta yatsun qafarta hakan yasa sady tai Saurin amsar babyn nata afnan ta Kure Adnan da kallo kallo mai cike da mamaki tsana da kiyayyah Shima kallon nata yake saidai nasa kallon na rashin sanayyah ne Sannan ya maida kallonsa kan sady cikin sanyayyar murya yace wai me kuke tattaunawane hake keda wannan bagidajiyar Woooooot kuuut yau adnan ni yake kira da bagidajiya Wait wait wair wait jama,a shin wai ya manta da itane zaman da Sukai a a turai Basu hadu bane. Koko halin da namijine ohoooooo nima ban saniba mu hadu a Book3. Danjin yaddah zata kaya Zamu xan fara qila yau amman idan Naga. Comment kenan Naku har kullun Abdallah s. Salankzz Wasu na qorafin ba,ayi da wuri kuma a dingayin musu post sau biyu a rana Amsar buqatarku itace. I. Can't. Sbd me. Course. Idan nai post Aure. Kan. Aure Chapter26. @book3rd Muje zuwa admin Zuciyar afnan tamkar ta tsinke qirjinta sai faman rugurguza yake Yaddaha adnan ke mata kallon rashin sani yasa zuciyata qara dagulewa Ta juya da saurinta ta fada motarta ta fizgeta da qarfin tsiya Tamkar mai shirin tashi sama tahau titu idonta ya rufe Itadai tasan tuqi take amman batai auneba saidai ta ganta ta yanki cikin daji Batayi yunkurin dakatar da motarba har sai dataga tayi nisa a cikin dajin wajenda babu wani dan Adam mai giftawa Ta bude ta fice daga cikin motar tamkar wacce bata cikin hayyacinta Ta nutsa cikin dajin tamkar wacce aka datsema kaqa ta fadi a cikin Rairayi Ta duqa a wajen kuka take na Fitan hankali ta rasa lissafin kanta Babu mai lallashin zuciyata ta qara daukar matuqar ruri Kuka take sosai tana kife a wajen har rana ta gama faduwa Duhu ya fara wani iska da sanyi ya fara saukowa irin sanyinnan marar Dadi mai shga qashin nan Saidai ita ba sanyin ya dametaba zafin da zuciyata ya dauka ya zarta duk wani Radadi da zai ratsa jikinta Batada mafita illa ta miqe ta kama hanyar data biyo Tana tafe tana tangadi tamkar wacce Tasha wani abun maye Tayi tafia mai nisa bata iske inda motarta takeba don harma ta fara fiddah Rai da ganin nata. Don lokacin data fita ko key din jikin motar bata zareba Ta soma gajia sosai don haka ta soma neman agaji saidai wayar tata itama tana cikin motar Don haka ta fiddah rai ta soma dibar sayyada can ta hango duhun motar Batayi tsammanin ita din bace sai data ganta a gabannta Ta shga ta dau hanyar gida Zuciyata na mata lissafe lissafe harta isa gidan nasu Lokacin an kammala sallar isha,i. Don haka ta fada cikin gidan Bataso ta samu Kowa a babban falonba saidai hakan bai samuba Domin aleeyu inna malam da yan aiki duk suna cikin falon Hankalinsu a tashe Tana shga sukayo kanta jikin aleeyu har rawa yake. Ina kikaje afnan? Ina kikaje kika tayar mana da hankali? Afnan Waye yace miki kije anga adnan. Iye? Jikin mahaifinta ta fada tana kuka sosai marar sauti. Abban nata ya shga rudani matuqa dama duk Wanda ke falon Inna ta janyeta daga jikinsa ta zaunar da ita a saman kujera Tace ya akaine afnan kiyi magana mana kinga kin jefa mahaifinki cikin tashin hankalifa Dubi jikinki saceki akai? Ganin yaddah duk suka tashi hankalinsu yasa afnan tsagaitawa da kukan Muryarta na rawa tace babu Wanda ya saceni inna yaya adnan ne ya dawo Dan har sunyi aure shida sady qawata Wacce ta taimaki su Abba wacce ta fitar da adnan din qasar waje sunyi aure inna harda yarsu Inna auren sirri Sukai yaya adnan ya mance dani. Ya zareni daga zuciyarsa baya Buqatata a cikin rayuwarsa. Yama mance kamannina yanxu haka nunawa tai Wai bai sanniba har yake kirana da bagidajiya ni inna ta qara fashewa da kuka Duk Wanda ke wajen ya tausaya mata aleeyu yace ban yarda adnan bane Tabbas adnan bazaiyi miki hakaba tabbas saidai idan maqiyane Zasu biyo tanan su rarraba hankalinki Amman adnan bazai taba miki hakaba Afnan ta miqe da sauri idanunta na qara zubda hawaye ta riqe hannun Mahaifin nata ido waje tace. Karkace Haka Abba ko.a cikin maza dubu zan iya tsamo yaya adnan Abba ka yarda dani yaya adnan na gani da idona Abba ya riga Ya manta dani Cikin dakewa irinta manyan mazaje yace bani number da aka liraki da ita Hannunta na kyarma ta lalubo number a wayarta tace ka kira Kaji Abba Bazan Maka qaryaba Ji yai tausayin yar tasa ta qara narkar masa da zuciya. Ya lalubo dakiyar dunyarnan ya daurama kansa bugu daya aka dauka ya fice suna Magaba afnan ta nufi sashinta tana sharar kwalla Kan gadonta ta fada ta bude wani babin kukan tace yanxu shikenan soyayyar da

Chapter 9 of 16