Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
toilet ba wajen dauro alwala ta fito taga harya shimfida darduma Bayan sun Gama ne sunyi addu,oi Sannan ibrahin ya miqe ya nufi falo bai jimaba ya dawo da wani qaton flask da plates Naman kazane banqararra sai huci take sannan ya koma ya dauko kayan sanyi. Ya aje a gaban afnan din Sannan ya cire Mata hannu ya cire Mata tagumin datayi Tana kallonsa. Yace haba afnan wannan ranar ranacefa ta farinciki. Amman dubi yaddah duk kikabi kika damu kanki Haba afnan koko dai so kike ki batamin daren angoncin nawa? Afnan din taja wani murmushi qarfin Hali ta girgiza Kai sannan tace masa, a!a yace to bani abinci naci Da sauri ta dago Kai tana kallonsa Suka hada ido. Duqar da kanta tayi qasa sbd wani irin knyarsa data sauko mata Yace kinajin kunyata ko afnan bari na kashe wutar abar marar hasken. Ya yinkura da niyyar miqewane yaji ana bugun qofar tasu. Da sauri da sauri kamar ana shirin balle kofar. Afnan ta miqe da sauri don hantar cikinta harta kada Ta zare masa idanu ya bita da kallo yace kamar bugun qofa nakeji. Waye yanxu cikin darennan bari na duba Afnan tai saurin kalllon agogon Dakin qarfe sha daya dayan mintuna tai saurin kallonsa yai murmushi yace ina zuwa dear bari na duba Yana shirin tashi ta rirriqo hannunsa ta rirriqe tamkar mai shirin kuka. Tace nidai uhm /uhm. Karkaje inajin tsoro Yai murmushi gamida shafan gefen kuncinta yace tsoron me kuma afnan? Babu abinda zai faru Kiyi zamanki ina zuwa Ta rirriqeshi jikinta har rawa yake tace a,a ba zaki barniba saidai muje tare. Yace to muje tunda tsoro kikeji kada wani abu ya cinye miki miji ko? Bugun qofar ya shahara kamar za,a balle kofar gate. Din Cikin daga murya ibrahim din yace wai Waye annan? Shiru ba,ai maganaba ya sake cewa wai waye? Nanma ba,a tankaba saima ci gaba da dukan gate din da akeyi. Wanda idan za,a kwana ana duka bazaiyi ko gezau ba Ibrahim ya fusata ya nufi hanyar gate din don yaje yaga ko waye afnan ta rigoshi jikinta na rawa tace, a, a ibrahim ka kira yan sanda Yaja murmushi yace karki damu babu abinda zai faru mai dear ya shafi kanta sannan yasa hannu ya Bude gate din Kamar afnan din ta saki fitsari sbd Bude gate din da yayi saidai yana budewa wata mace ta shigo babu ko hijab a kanta ballentana gyale Hakan yasa kirgin afnan yaci gaba da bugawa Ibrahim din ya kalleta ido waje yace Maryam maiya fito dake cikin darennan? Ban saniba amsar data bashi kenan har tana watsa masa miyon bakinta To jama,a. Akwai rikici kenan Don Jin kodame Maryam din taxo cikin tsohon Aure. Kan. Aure Chapter33. End ov. B00K3 Ta riqe kugu tana dan iska munafiki wato amanata zakaci ko? Kenan ni inacan ina haukata a banza kaiko kananan ko a jikina ko? To wlh duk danda ya hana uwarsa barci to ko rintsawa bazaiyiba Ta juya tai cikin gidan a guje ibrahim ya bita yana Kiranta Maryam Maryam. Afnan ma ta rufa musu baya Nanfa rigima ta kaure tsakanin Maryam da ibrahim Maryam taci damara da dankwali Gashin kannan duk ya tattashi tsaye sbd masifa Chaiii. Fadi take na rantse da Allah yau saina kunnama gidannan wuta. Wlh bazan mutu ni dayaba macuci mayaudari munafuki kawai Kaida a mafarkinka har kana zaton zaka kwana da wace mace bayann nine? Ibrahim ya daka Mata tsawa yace ke Maryam Kinada hankali kuwa? Kanki kalau kuwa wace irin fitinace wannan kikeson kunnamin ayau daren angoncina? Ta tafa hannu tana fadin ohh lallai su angonci manya Aiko za,ai angwanci yau cikin farinciki Ta juya zata shga bed din afnan din ibrahim ya riqota yace babu inda zaki wlh ficewa zakiyi kibarmin gida yanxunnan Cikin zafin xuciya tace sakeni nace kafin ya ankara tayi wani kukan kura ta qace hannun nata ta fada bangaren afnan din. A guje Afnan din dashi har rige rigen binta suke don suga hukuncin ubangiji Tana shga tai Karo da naman kajin da basu somaciba da kayan sanyi tasa qafa tai fatali dasu. Sannan ta dauki wuqar dake wajen ta nufi kan gadon ta dinga farfarka zanin gadon da katifar Ibrahim na shgowa yai saurin nufarta domin kwace wuqar tai saurin dagowa idanuwanta sunyi jajir. Kamar wata mahaukaciya Tace na rantse Maka da allha kana qarasowa inda nake saina yankeka da wuqarnan Ba yaddah ya iya haka ya tsaya yana kallonta kaman wani dolo Ta suri lokar dake jikin gadon da makata Akan madubin dake tsakiyar Dakin. Madubin ya tarwatse ibrahim yai saurin binta kanin abin nata bana lfy bane Ta nunoshi da wuqar hannun nata tace kana nufoni zan Maka illa na tabbata Cikin zafin rai yace so wat kimin din Maryam kin Dade bakimin illar ba hakanne zai tabbatarmin da ke cikakkiyar mahaukaciyace Ganin yaddah yake yinkurin kamota dukda wuqar da take kare kanta dashi. Yasa ta kwasa da gudu ta finciko hannun afnan din suka fice falon da gudu Yana yinkurin biyosu Maryam din ta rufe Dakin da key din dake jikin qofar sannan tahau afnan da duka Afnan ba gwanar fada bace asalima ku cacar baki bata iyaba Don haka ba qoqarin ramawa takeba qoqarin Qatar kanta kawai take Maryar ta janyo wuqar take hannun nata tana qoqarin yankar afnan din afnan din ta dinga ja da baya harta qureta I zuwa bakin bango Tabi wuqar dake hannun Maryam din da kallo tace innalillahi bata da mafita illa ta runtse idanunta kawai Kamar a mafarki taji tana fadin yar iska munafuka ai tunda kikace gonata zaki shiga to wlh sai naga bayanki Kamar daga sama taji saukar wuqa a goshinta afnan din ta kurma wani uban ihu takai hannu ta shafi goshin nata Jinine sosai kamar an watsa ruwa Afnan Tabi hannun nata da kallo ido waje tana qoqarin kuka Maryam din ta sake Kai Mata wata yankar cikin zafin nama ta kauce ta yanki bango sannan ta rirriqeta suka kaure da kokawa Maryam na qoqarin saita yanki afnan din kuma na qoqarin amshe wuqar gaba daya sunjima kansu ciwo Hannuwansu kuwa sau zubar da jini yake Afnan ta samu ta kwace wuqar a Lokacin data watsar da Maryam din gefe guda ta baje ita kuma ta kwasa a guje Ta Bude Dakin da Maryam din ta kulle ibrahim din Fitowa yai hankalina a tashe yaddah yaga afnan din ke zubda jini ya riqota saidai bai samu tabuka Mata komaiba yaddah yaji Maryam din nata ta! adi a falon Ta dauki dvd ta buga a jikin TV din dake manne na bango komai ya tarwatse. Teburin dake tsakiyar falonma ta kakkarya shogilas din dake gefen kusurwan Dakin duk kwalaben humran dake ciki suka watse kasa suka tarwatse Cike da baqinciki ibrahim din ya ture afnan din ya nufeta yana fadar Maryam ya isheki haka yar iska marar mutunci kawai bai Gama qarasawaba shima ya tasa kwalba cikin kwalaben da Maryam din ta fasa ta lume cikin qafarsa Sosai. Wata irin gigitacciyar qara ya saka ya Fadi qasa warwas Afnan ta kwala ihu tayi kansa ta riqe qafar jinine sosai ke fita sosai sai kace an yanka wata qaramar dabbar Ta saki wani irin kuka mai hargitsa zuciya Ibrahim ya runtse ido sbd azaba afnan takai hannu domin zare masa kwalbar da sauri ya janye qafar yana girgiza kai Afnan tabi qafar da kallo harta kumbura tausayinsa ya kamata. Don ita batama damu da nata ciwonba Ta miqe ta nufi bed din nata Wanda Maryam ta Gama tarwatsa komai wayarta ta zaro ta lalubo numbar adnan Kota ya akai ta samu numbers oho Nima bansaniba@admin Ringin daya biyu ya dauka bata tsaya fada masa komaiba tace ka taimakeni yaya adnan kada na rasa mijina yaya........ Cikin tashi hankali yace lfy maiya faru dashine cikin wannan daren? Bata iya amsa masaba ta saki wayar tai waje a guje Sbd qarar ibrahim din data jiyo har ilokacin Maryam bata daina Mata ta,adi da bannata Mata kayan cikin gidan ba Ashe garin ya dingisa ya tashine ya saje taka wata kwalbar dalilin daya sake kurma ihun kenan Afnan ta rude ta shga matsanancin tashin hankali Ta riqe hannunsa tama rasa me zatai rage masa radaDin da yakeji Bata damu da nata ciwonba da kuma yaddah Maryam keta Keta rusau a cikin falon nataba Tana riqe da hannun ibrahim din taji saukar qarfen shogilas din akanta afnan ta dafe Kai ta sulale qasa bata iya ko motsi Ibrahim bai wata wataba ya yayibo qafar Maryam din dake kanta ya watar kanta ya bigi wani dan qaramin tebur. Saidata shede Cikin tsananin takaici da nadamar saninta da yayi ya nunata dadan yatsa. Yace Maryam na sakeki saki uku ban buqatar sake hada idanuna da naki Yar iska jaka akuya kawai Allah yai wadaran dake tirr dame irin halinki Gaban afnan yai mummunan faduwa dajin sakin da yai anan take. Saidai dishi dishi take gani Kamar Maryam din na jira ta tashi ta shaqi wuyar. Afnan din Tana fadin na rantse daah saidai kowa ya rasa ibrahim din na rantse kasheki zanyi Adaidai Nan adnan ya fado falon kafin kowa ya ankara ya dire inda Maryam din take ya fizge hannunta daga wuyar afnan din ya. Wanka Mata wani irn Marin da saida tai Sakan talatun tana ganin jajayen taurari. Lol Bama farareba. Hmmmm Tana qara dawowa hayyacinta ya qara dauketa da wani wawan Marin haQu da dama har Saidata kifa Sannan ya nufi afnan din Jikinsa sai rawa yake ya tallabata ya kwantar a Jikinsa Muryarsa da Jikinsa sai rawa suke yace lfy adnan Waye yai miki wannan danyemn aikin? Bata iya maganaba saidai numfashinta dake fita da sauri da sauri Adnan ya dubi ibrahim baima lura da cikin jinin da yakeba Cikin takaici yace ammandai Kai kaji kunya wlh tirr dame irin halinka yanxu me afnan tai Maka da har zaka taimaka wajen salwantar da rayuwarta? Ran ibrahim cinkushe da baqin ciki musamman dayaga afnan din kwance a jikin adnan din a jikin qirjinsa. Ta lafe tamkar wata mage saidai maida numfashi da take sama sama lol Cikin tsananin zafin kishi yace bansaniba Waye Kai da har zaja fadomin cikin gida babu ko neman izni? Adnan yace aikai kafi kowa sanin koni Waye sannan rashin gaskiyarkane yasa na shgo cikin gidan naka ba tare da izniba Ibrahim yace wacce rashin gaskiyace wacce ta wuce shgomin da kayi cikin dare ashe kenan bibiyata kake to lallai yau hukumace kawai zata rabamu dakai Afnan yace kamar yaddah na fara sanar da hukumar kafin naxo ba Ya kalli afnan wacce ta fara dawowa cikin hayyacinta ya shafi ciwon dake goshin nata yace Kiyi haquri afnan muje nai miki dressing din ciwukan naki Wohoho. Wato idanda zaka daura hannunka kan kirgin ibrahim a wannan Lokacin aradu zaka iya konewa sbd tiririn Da yake. Tsabar kishi kawai. Ita kanta afnan din ta lura da irin kallon da ibrahim din ke musu ganin haka yasa ta zame jikinta tace tsaya yaya bari nai Maka bayani Bai tsaya saurarentava ya janyo hannunta hakan yabama ibrahim damar. Harde qafafun adnan din babu abindaya tareshi yai taga taga har saida yai Karo da bangon dakin Ji kake kuuuuuuuuuum afnan ta kwala ihu tayi kan adnan Din. Tana jijjiga Jikinsa tana Kiran sunansa amman ko Motsi bayayi. Babu alamar numfashi a Jikinsa Afnan tasa ihun kuka tana na shiga uku na lalace shikenan ka kasheshi. Ta kife akansa tana wani irin kunjin kuka Maryam ma dake tsaye ta soma tafa hannunta tana fadin wannanma yayi min daidai ibrahim yayi kyau daka kasheshi Akan idona wlh ka biyani Ta nufi inda adnan din yake tasa hannu taji ko yana Motsi ko baiyi taji shiru baya numfashi Ta daura kanta saman ruwan cikinsa nanma shiru tasa hannunta ta daga hannunsa nanma ya Fadi ragwab Maryam ta miqe tana wata irin dariyar mugunta Tace haka nakeso don haka kaga itama yanxu saina kasheta Inyaso a hadamu ni dakai a kaimu. Gidan yari mu qarasa rayuwarmu acan Wata irin zazzafab zuface ta soma lullube ibrahim Ya soma girgiza Mata Kai alamar kartai haka Ko kallon inda yake bataiva ta dauki wuqar dake qasan ta nufi kan afnan din cikin zafin rai Afnan din cikin firgice. Da tsoro ta soma ja da baya. Mai zai faru mu hadu a book4 Danjin yaddah zata kaya shin adnan din ya mutune ko kuwa? Maryam nacin nasaran kashe afnan din? Oho taya za,ai na sani mu hadu a book4 Danjin yaddah wannan lamari zaai kasance Aure. Kan. Aure. Book4 Chapter34 Cikin tsoro take ja da vayan cikin ikon allah kuwa taci Karo da wuqar da Maryam din ta yanketa dazun tai saurin duqawa ta dauka Maryam na qarasowa afnan din ta runtse idonta saiji akai Maryam ta. Kurma uban qara ashe runtse idon da afnan tayi. Yanka takaima Maryam din da wuqar dataci Karo da ita din cikin ikon allah kuwa tai sa,ar yankanta a fuska Wani irin wakakeken yankane afnan din tai Mata tun daga gefen hanci har zuwa wajen kunne Nanfa Maryam ta duqa tana kururuwa adaidai Lokacin yan sanda suka shgo suka zagaye falon afnan ta saki uqar hannunta tana cije lebe don bataso yan sandan sukaxiba don A Lokacin yaddah zuciyata ta qeqashe so tayi ta. Yayyanki Maryam din don itama taji yaddah taji Yan sanda suka zagaye falon mai camera ya soma daukar hoton adnan dake kwance shame shame Sannan aka hada hannun afnan Dana Maryam ala datsa musu ankwa yan sanda suka tasa qeyarsu sannan Wasu daga cikin yan sandan suka tallabi ibrahim din shima sukai waje dashi Dan sanda daya yasa wuqar da afnan ta saki a cikin farin qalle sannan suka tattara harda gawar adnan din suka fice Aka garqamama gidan qaton kwado basu wuce ko inaba sai police station inda aka wuceda ibrahim da adnan asibiti Cikin dan qanqanin lokaci akaima ibrahim din dressing din qafar tasa aka cire masa kwalbar sannan akai afishing yan sandan dashi inda shi kuma adnan din suka barshi anan domin likitoci suci gaba da bincike akansa idan zai tashi Ibrahim ne da afnan tare da Maryam a. Ofice din. D. P. 0 Yana zaune cikin kujeran dake gaban tebiirin dake office din da biro a hannunsa yana jujjuyawa yace Yace Kai malam ibrahim kace yau aka daura Maka aure? Yace eh wlh. D. P. O yau aka daura mana aure kuma yau matata ta tare wannan yar iskar matar tazo ta haddasa mana fitina a cikin gida Maryam ta sako baki tace ba wani Nan yallabai a kan idona ya shaqare bawan allah ya kasheshi da hannunsa D. P. O ya kalleta ta cikin baqin gilashinsa yace to yanxu kena tambaya tai shiru yace lallai zaki fuskanci fushin Hukuma. Inhar kika qara sako mana baki bayan ban tambayekiba Sannan ya maida kallonsa kan ibraheem Wanda shi kadaine ke zaune sbd ciwukan dake qafarsa Yace inajinka ibrahim kuma wace hujja ce zata tabbatar mana da yau aka daura Maka aure Yace iyayena duk zan bada number su aka kirasu kuma matannan da kake gani anan dukansu Mata nane Wannan itace uwar gida dan har yaya ke garemu waccan. Kuma amarya yau dinnan ta tare a gidana kuma ko wacce da gidanta daban Nanfa ya zaiyane masa abinda ya faru tun daga A to z Sannan. D. P. O ya koma wajen Maryam yace wane daliline ya kaiki gidan amaryar mijinki a ranar data tare? Tace malam takalata akai kaga wannan mutumin da kake gani yaudarata yayi yau kusan kwana bakwai kenan ban sashi a ido ba babu cin yau babu na gobe duk inda nake tunani zan ganshi abin yaci tura don haka yau na saneshi a gidansa D. P. O yace da musalin qarfe nawa?tace qarfe tarane batama qarasaba Yace dawa dawa kika samu a cikin gidan tace shida matarsa Sannan ya juya ya kalli ibrahim yace ibrahim misalin qarfe tara na dare kana ina?yace ina tare da abokina a gidansa bamu isa gidan amaryaba sai goma na dare kuma Muna isa abokin nawa ya dauki matarsa suka wuce Qarfe sha daya kuma Maryam taxo D. P. O yace to Waye mutmin da muka samu kwance rai a hannun allaha gidan naka? Yace saurayin amaryatane. Dr adnan aleeyu musawa Wanda yaxomin har cikin gidana ba tare da izininaba ya shgo har cikin falona. Ya dinga yinma matata rungumar da ni kaina tunda aka daura mana auren ban mataba a cikin daren ankwancin nawa Ganin haka yasa nasa qafa na haurar dashi tsautsayi yasa kansa ya bugu da bango ya Fadi qasa warwas D. P. O yace kace kishi ne yasa kayi kisan kai? Ibrahim din yace a,a Bawai kasheshi naso naiba Abinne kawai yaxo da tsautsayi amman na rantse har yanxu banji nadamar yin hakan ba Yace yallaba ka kwatanta abi akanka. Matarka tsohon mijinta ya shgo Maka gida a ranar daren angoncinku harya dinga rungumarta kuma a gabanka kana kallo in kaine wane mataki zaka dauka? D. P. O yaja dogon murmushi can kuma yace hukuma kawai zan sanar mawa domin kuwa daukar doka a hannuna bata tasoba Saidai kuma kasan kafin. Dr adnan ya shga gidanka saida ya sanarma hukumar yan sanda cewa yar uwarsa ta kirashi Akan yaxo ya taimaka Mata gidanta babu lfy kuma ya bamu adress din gidan ba tare daya jiramuba yai gaba kafin mu iso Ibrahim yace yar uwarsa kuma wacece yar uwarsa? Cikin kuka afnan tace gani Nina kirashi nace yaxo gida babu lfy D. P. O yace samun sauqinka daya shine adnan ya farfado don kuwa inhar rai yai halinsa adnan ya rasu to kaima kasan Tabbas. Hukuncin ratayane zatahau kanka don kasan hukuncin wandaya kashe shine akashe ido waje Yace wattt ratayafa kace yallabai. D. P. O yace yes Tabbas Don haka yanxu haka daga Kai har matan naka tsareka anan Zamuci gaba daya har sai result ya fito Akan kwaje kwajen da akema. Dr. Adnan din. Tir qashi muje zuwa Aure. Kan. Aure Chapter35 D. P. O yace itama wannan shu,umar matar taka kotu zamu turata kawai a yanke Mata hukuncin daya dace Nan take. D. P. O ya kira iyayen afnan Dana ibrahim ya sanar dasu duk abinda ke faruwa Ba,a dauki tsawon lokaci ba saiga. Abban afnan dinnan ya iso aleeyu daga bisani kuma mahaifin ibrahim shma ya iso tare da matarsa Bayan sun hallarane. D. P. O ya sanar dasu duk abindaya faru. Dukkansu sunyi al,ajabin abun Hajia iklima kuwa sallallami ta fara tana tafa hannu tace kwarai kuwa ai duk Wanda yaqiji bayaqi ganiba Meye ban makaba Akan karka qara aurennan ka zauna da matarka daya amman kaqiji wannan tsinannan yarinyar zata sakaka cikin ba,ai daga kawota harta fara tara Maka mazaje a gida Da sauri suka kalleta su duka sannan alhaj ashiru ya daka Mata tsawa Ke ya isa haka Kinji ko ya isa haka banson shirme Nan taja bakinta ta tsuke sai girgije girgijen masifa take Ana cikin hakane sako ya shigoma. D. P. O cewa ai Adnan zai iya tashi akodawani lokaca. Sassanyar ajiyar zuciya afnan ta saki. Zuciyarta shar shima ibrahim din ba qaramin dadi yajiba don bazaiso a ce yayi kisan kaiba kasancewar ko kaza bai taba kashewa ba Ananne abban afnan ya roqi alfarmar a saki ibrahim yaje yai jinyar qafafunsa tunda komai yaxo da sauqi Ba musu suka sakeshi sannan sukace itama Maryam suna neman alfarman a basu belinta D. P. O yace! A a hakan bazai samuba koda kuwa su mutanen sun yafe dole abar doka tai aikinta Hajia iklima ta sako baki tace ai kuwa saidai suma su tafi da yar tasu har sai randa aka sako ita Maryam din Babu Wanda ya kulata Nan sukayi sining din da zasuyi Sannan yan sanda Mata suka tasa qeyar Maryam din zuwa cikin cell . Lol Alhaj asshiru yabama Abban afnan haquri gamida cewa insha Allahu hakan ba zata sake faruwa ba. Sannan gaba dayansu suka wuce asibitin da aka kwantar da adnan din Alokacinda suka isa likitocine duqufe akansa tsawon awanni hudu kenan. Don haka suka nemi waje suka zauna Wata nurse ce taima afnan dressing din ciwukan dataji Tsawon awanni shiddah likitoci nakan adnan sannan suka fito da hanzari alhaj ashru da abban afnan suka miqe Gamida nufa inda likitan yake yace su biyoshi office Nanne yake fada musu sakamakon buguwar da adnan din yayi yasa memory dinsa ya dawo bayan sun bashi taimakon gaggawa Don haka zai iya farfadowa daga yau zuwa gobe Godia abban afnan din ya shga yin masa Akayi lissafin duka abinda zasu biya sannan suka fita suka biya abban afnan ya tilasta ma alhaj ashiru tafia tunda sunga yaddaha lamarin ya kasance Abban ibrahim din da kansa y dauki su afnan din amotarsa ya ajesu a gidan nasu inda ya dudduba barnan da Maryam din tai musu ya girgiza Kai gamida cewa yarinyarnan bata kullama kanta arziqiba hajia iklima tace ai komai tayi janta akai don haka ni banga kaifintaba wlh da subiyunsu suke zaune tayi hakan?alhaj ashiru ya bita da harara sannan yace wuce muje Kinji karkisa raina ya qara baci Yai gaba sumi sumi tabishi a baya Afnan tai musu rakiya. Sannan yace tayi haquri zuwa Anjima zai turi da wadanda zasu sake shirya Mata komai na cikin gidan nata shi zai biya Tayi godia sannan ta dawo cikin gidan tana kallon iri varnan da Maryam tai Mata saidai rabin tunaninda da hankalina nakan. Da tunanin halinda yake ciki Sannan ta shge ciki Kai tsaye kichin ta nufa ta bata lokaci wajen hada musu break mai rai da lfy sannan ta dibesu ta wuce darect bangaren nasa inda ta sameshi kwance kan doguwar gujera ya daura qafafunsa kan tebur din dake tsakiyar falon Ta aje komai a gabansa sannan ta dubeshi tace bismillah Ya kauda Kai tashi tayi ta koma wajen da yake ta daura kanta kan kafadarshi muryarta a sanyaye tace ka tashi muyi braek tuba nake ranka e Dade mai gidana na kaina Bai tanka mataba hakan yasa ta riqo hannaynsa ya sauko ta zuzzuba masa komai ya qureta da idanu ko kiftawa baiyi Lol mayae kawai Afnan ta tallabe fuska tana kallonsa tace yanxu ya kakeso nayi da rayuwatane eye ta tashi da kanta tana bashi abincin a baki harya qoshi shi kansa yayi mamakin irin abincin dayaci bayan ta Gama tasa tissue ta goge masa bakin nasa Zata tashi kenan ya jonyota Jikinsa ya rungumeta gamida cewa me kike nufi ke bazakici komaina? Tace nawa yana kichin ya qureta da idanu yace kina nufin ba tare zamu dinga cin abinciba sbd me? Yaddah ya qarashe maganar har saidayaso ya bata tausayi don haka ta zauna domin taci yace a!a wannan aikinane da kansa ya soma bata har saida ta ture hannunsa alamun ya isheta Bayan ta kwahse kwanukan takai kichin ne. Takai kicinne ta Kawo masa magungunan da aka basu a asibiti yasha itama Tasha nata sannan ta miqe Yace ina kuma zaki ta lumtse idanuwanta sannan tace barci nakeji zanje nayi Ya miqa Mata hannu itama ta miqe ya janyota Jikinsa Gamida qanqameta yace babu inda zakije kiji dadin barci a yanxu sama danan. Don haka yi kwanciyarki anan Babu yaddah ta iya dole ta lafe a qirjin nasa tun tana sake saqe har barci mau dadi ya sureta Bata tashi farkawaba sai bayann sallar azahar Tana tashi taganta manne a girjinsa shima barcin yake sunyi filo da. Hannun kujera Zame jikinta tai ta nufi sashinta. Ta fada toilet ta watso ruwa duk kuwa da zafin da ciwon nata ke Mata bayan ta Gama wankanne ta dauro alwala tai sallah tana gamawa taji ana sallama Ma,aikatan da daddyn ibrahim din ya turo ne don haka tayi musu iso sannan ta koma sashin ibrahim din shima ya farka yana sanye treequarter da wata tshirt fara qal Ta zaro ido tace Kai ya akai gurgunnan yai qafa yace ej shiyasa kika sulale kika barni ko don kinga banda qafafun binki ko? Cikin sigar wasa tace ba haka bane kwalliya naje nayo makaba Yace dadin abinma aii bakiyi kyau ba Ta zaro ido tana fadin da gaske ya daga Mata gira ta nufi Qofa tana fdin aiko saina sake wata yanxunnan yasa daria Yana ke dawo ni wasa nake miki ta waigo a shaagwabe tana kallonsa tace. Ni allah ka barni na sako wata Yace zo kije dan qaraso taa zuwa ya janyota Jikinsa yace kinyi kyau matata kyanda Mata dari zasu kalleki su kauda kai Kinsam Mata sunada kishi basuson ganin macer data fisu Kyau taja dan dogon haancinsa tace to sarkin iya kalamai gafa masu aikin can daddy ya turosu yace to lfy lau kice musu su soma aiki kawai Tace angama yallabai ta fice insa tai musu izni Akan su fara aiki kawai Bayan ta Gama kichin ta fada domin hado musu nagartaccen abinci bayan ta Gama ne ta jera Akan tire ta Nufi falon mai gidan nata suka zauna suna ci gamida hira mai ban sha,awa kamar babu abindaya damesu Anan sukai sallar la,asar ibrahim ya kira musty abokinsa yace yaje ya dauko masa yaransa a gidan Maryam Mustafan ya tambayeshi lfu? Yac idan ka kawosu kaji yace to an Gama Bayan sallar magrib aka kammala Mata komai Dakin nata gunun ban sha!awa amman dukda haka baikai da kyau ba kasancewar kayan da suke nada din duka na qasar wajene Amman wannan dinmaya bada ma,ana Afnan na kichin tana hada musu abincin dare musty ya shigo alokacin ibrahim na babban falo Itama ta fito tai masa sannu da zuwa Saidai ganinsa da yara yasa ta qaraso tana fadin ina ka samomin yara kuma? Musty yace dubesu dakyau kiga dawa suke kama? Afnan ta dafa kafadun yaran tana kallonsu kamar ta sansu saidai ta. Rasa a inda ta sansu din Ta dubi musty tace na Baka gari fadamin a inda ka samosu Daria yai yana fadin juya ki kalli mijinki Afnan din ta juya ta kalli ibrahim Wanda ke kishin kide yanacin ayaba tace Tabbas dashi sukai kama Ta kalli musty fuska dauke da fara,a tace wai nashi ne? Yace ba gashinan a gabankiba. Taja hannun yara suka qarasa gabanshi take ku dubi wannan wai abbankune da gaske? Suka daga Kai afna tai daria tace ku zauna a jikin abbanku kunji mai kukeso na dafa muku? Babbar ta kalli qaramin su duka suka kalli mahaifin nasu akai sa,a kuwa shima kallon nasu yake sukai shiru Tace yadai sai kallon kallo kuke Musty dake shirin zama yace ai indai har suna gaban. Ibrahim be basa iya magana Babu Wanda ya motsa cikinsu sai kallon ibrahim din suke itama shi take kallo ya wani hade rai Yace ku tashi mana sai alokacin yaran suka tashi Afnan ta hadiyi wani numfashi ba tar data tamka masaba taja hannun yaran suka nufi kichin Afnan ta dubi babbar macen wacce itace babba tace aqallah zatakai shekara tara tace meye sunanki Tac sajidah ta dubi qaramin Wanda bai wuce shekara shiddah ba tace Kai kuma fa yace salim Ytai murmushi gamida cewa ashe dai Kuna magana amman mai yasa bakwayi a gaban abbanku gabadayansu Kallonta suke ba Wanda ya bata amsa a cikinsu Tai murmushi. Itama ba tare data takura musu Akan hakanba tace Zaku tayani girki suka daga Kai alamar eh tace to ku matso Nan ahaka taita jansu da wasa da daria har suka kammmala suka shirya komai Akan dinnif table sannan ta qarasa wajen dasu ibrahim din suke tace yallabai ina kayan yaran? Ya nuna Mata trolling bags dinsu a gefe taja. Gamida Jan hannun yaran sukai gamida fada musu ga abinci can a dinng idan kun shirya bata saurari amsar da zasu bataba tai ciki Bayan yaran sun Gama cin abincin nasune ta duba cikin kayan nasu ta dauko musu kayan barcinsu Bayan ta musu wanka suka saka bata Gama shiryasuba tajiyi mustafa na fadin zai tafi don haka Ta Sanyo abayarta ta xo suakai sallama Bayan sun Gama yin sallamarne ta koma wajen yaran ibrahim na kishingide Akan kujera yaji zaman ya isheshi Don haka ya zaro wayarsa ya tura Mata da text Ta soma karantawa Wato kin samu yara kin manta dani konaci ko karnaci ko? Tai murmushi itama ta tura mishi da Wanda kaci Kaida Abokinka fa? Ya turo Mata. Waya gaya

Chapter 13 of 16