Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
nata ta koma ciki ta rasa amsar da zatabama yaran Kamar daga sama taga qafafun mutun akanta tana daga kai taga adnan ne Muryarta na rawa tace Yadai malam lfy kafin ta gama rufe bakinta ya dauketa da wani gigitaccen mari ya nunata da dan yatsarsa yana cewa Ke qaramar yar bariki ki saurareni inba hakaba zakisha mamaki Ki sanar dani abinda nai miki da har Wadannan yaran Muryarsa ba sassauci yace meye kike buqata idan dukiya kike nukaqata ko nawane ki sanar dani wannan ba matsalata bace Amman sunana dakikeson batawa ya isa haka ya isa ki ganeko? Ya qarashe maganar ccikin daga murya Gashi jama,a har sun fara tarata suna fadamin wai ashe inada Wasu yaran to ya isheki haka niba dan iska bane Kamar yaddah kike tunani Marin ya ratsa afnan har taso rudewa daqar ta iya shanye Marin tana masa kalln takaici Tace lallai adnan wuyanka ta isa yanka yau nice ka mara da yatsunnan naka Ta girgiza kai gamida cewa lallai ka cika. Butulu mayaudari maha,inci Kuma na baka asignment kaje ka bincika Waye aleeyu musawa a cikin garin kano Koda qaramin yaro yasan wayeshi sannan ka bincika wacece yarsa afnan Idan ka Gano saimu gane Waye me qallen uba Waye me taqama da uban wani ta kama yaranta taja hannunsu tace kuxo muje Yaja wani dogon tsaki yana fadin sakarya kije ki kwashi ciki a titi ki haife sannan ki rasa da sunan da zaki liqa musu sai nawa Aslim ya bishi da kallo cikin tsawa yace daina kallona shege marar uba Da sauri afnan din tajasu ta turasu cikin mota ta rufe ita kuma ta koma mazaunin direba maimakon ta tada motar sai kwantar da kanta tai Akan sitiyari tana kuka marar sauti yaran suka janyo kansu suka kwanta Jikinta suma kukan Suke babu mai lallashinsu Saidata gaki don kanta sannan ta soma lallashin yaran daqar ta samu Sukai shiru Sannan ta kunna motar ta Jasu a hankali tajejan motar harta kama hanyar gida Kamar daga sama aslim yace wai da gaske Momy mu shegu ne? Ji tayi tamkar ta saki sitiyarin motar Sbd firgici ta shafi kan yaran tace a,a kuba shegu bane Shegu sune wadanda basu da uba kukuwa ai kunada uba Abba aikin sanshi ko Yaron ya daga ka Taslim tace amman mommy.... Ta daka mata tsawa tace ya isa haka ganin yaddah ta taso musu yasa suka tsuke bakinsu Sukai shiru Zuciyata sai azalzalarta take ji take Kamar tasa hannu akai tauta ihu Ba yaddah ta ida kodata aje yarana a gida office dinta ta wuce. Dukda kanta na mata wani irin azababben ciwo amman kodata isa office din nata Ta Gaza katabus Zainab ce ta turo office din nata ta shgo afnan ta dago da jajayen idanuwanta Ba tare data damu da yanayin yaddah takenba don daman tun a Makarantar yaran ta lura da yanayin nata Taja kujera ta zauna gamida cewa wai meke faruwane afnan Afnan din tai wani murmushinda zamu iya kiransa da yaqe Tace damuwace kawai zaiban Zainab din tace nasan da haka amman da Zakiji shawarata da kin manta da batun adnan kin Bama ibrahim dama domin bayyana miki abinda ke cikin zuciyarsa Tundadai yarane Allah ya rigada ya raya miki su Afnan taja wani dan murmushi taje zaiban kenana aini tuni nabar adnan Kamar yaddah babvar cikin mahaifiyata Kuma na fita harkarsa sannan abinda yaimin na barshi da Allah saidai ban isa na hana zuciyata takaici da kuncin rabuwa da adnan dinba Tace dole zuciyata tai kuka amman nikam na daina na idanu Zainab din tace aiko dakin kyautama rayuwarki saidai inason don Allah kibama ibrahim dama ibrahim mai sonkine so na haqiqanin gaskia don tun randaya fara ganinki ya damu zuciyarsa da zancenki adnan Ibrahim abokin mustapha ne. Tun suna. A. B. U. Inda aka tura ibrahim bautar qasa zuwa inugu shikuma mustapha akwaibom Kinji Yaddaha akai suka rabu Bayan sun gamane kowa ya dawo gida sai Iyayen ibrahim suka hada shi aure da yar uwarsa shi kuma mustapha ya aureni dan dama tun ina secoundry muke tare Don ko,a. A. B. U lokacin da suke shekara qarshe a lokacin na shga 100level don haka na qara saninsu da abotarsu gamida sanin halin kowa. Wlh ibrahim mijin marainiyane don matarsa Maryam da kike gani batada hali kona misqara zarratan Ni kaina shaidane ibrahim mutum ne mai haquri don ba ko wane namiji bane zai Iya zama da wannan annamimiyar matar tasaba in takaice miki yanxu haka yaransu uku kuma har yanxu yanna tare da ita Tunda nake ban tabajin ibrahim yace zai Qaro aureba don ko an mishi maganarma cewa yake ba wannanne a gabansaba mace dayama na neman gagararsa inaga ya Qaro Na rantse miki ibrahim mutum ne na gari salihi marar hayaniya Dan Allah afnan ki bashi dama koda na yini dayane na tabbatar da zaki fahinceshi please Afnan tai. Murmushi tace zainab kenan lallai da yar siyasaceke da jakija zama,A Da wannan bakin naki Zainab tace ba haka bane afnan gaskia na fada miki ki yarda dani Afnan tace shikenan zanyi tunani zainab tace wane tunani kuma yanxu haka yana office dina a zaunefa don Allah afnan ki taimaka kar yaga gazawata Tace kai keko zainab kin cika naci jeki shigo dashi ai inanan Cikin murna tace tanx afnan ta fice da saurinta afnan din ta bita da kallo Zuciyata na mata saqe saqe saidai jiyo sallamarsa tayi da hannu tai masa nuni da wajen zama ya samu waje ya zauna Yayi kyau sosai yana sanye da qananun kaya Yaja kujera ya zauna yace godiya ta tabbata ga sarkin sarakuna sarki Allah Yabo ya tabbata ga shugaban so da masoya annabi muhammad (s. A. W) Afnan bansan irin farinciki da godian da zan miki kasancewar saurarata da kikaiba Daqar ta iya qirqiro wani daria da bai kai xuci ba Yacu gaba da cewa da alamun damuwa a tare dake Da zaki ban dama Dana dawo miki da farin cikin da kika rasa Afnan ta dubeshi tace taya baqincikina da damuwata zasu ragu idan har na baka dama? Yace abune mai Sauqi afnan Tunda har sonki ya fasa qirjina ya tsaga zuciyata ya shge gamida samama kansa mazauni Tabbas babu abu mafi siddabaru a duniya daya wuce kancewar so a zukata Lallai idan ba ubangijiba babu Wanda ya isa ya qaddara wannan Afnan zan dawo miki da murmushinki da kika rasa a baya zan dawo miki da fara,arki da kika rasa a baya sannan na dawo miki da farin cikinki a duk inda yake namiki wannan alqawarin Afnan ta ja wani gajeranmurmushi a lokacin data tuna da kalaman adnan din da yake ce mata. Afnan inasonki ina qaunarki sonki zai kasjeni idan harna rasaki mutuwa zanyi Ta girgiza kai tace. Hmmmm maza kenan yau kuma tanan aka bullo wato zan dawo miki da murmushinki fara,arki da kuma farincikinki Tace yanxu idan nace duk zancennan tsarine sai kace bada gaske bane ba ko? Yace karkda zuciyarki ta raya miki haka afnan wlh sonda nake miki sone Bawai Irin son da kike tunani bane ki yarda dani afnan bazan taba cin amanarkiba Ina miki sonda zan iya sadaukar da raina akanki ki yarda dani Tace Indai afnan ce ta baka dama ibrahim domin taga gudun ruwan soyayyar taka Wani murmushi Yaja sannan yace wannan ruwan afnan bashi da qarshetashi tai tana kallonsa tace yanxu dai gida zanje jibi ina gayyatarka gidanmu don daman ai ka Dade da cusa kanka wajen mahaifina Shima miqewar yayi yana fadin irin wannan zuqeqiyar matar idan nai sanya ai Sai Naga sanya daria tayi dukkansu suka fice a daidai inda masinja ke zama ya miqa mata wata takarda yace gashi hajia akace wai na baki Ta amsa sukaci gaba da tafia tare ba tare data duba takardarba Zainab yarsa ido tana maqale a ofice dinta tana leqensu tace hofa daga farawa da iyawa afnan tai saurin amsar ta da cewa to yarsa ido ni. Gida na nufa Tace to saimunyi waya kenan tare suka wuce ibrahim ya rakata har bakin motarta yace abani dama na kaiki har gida mana madan Tace a,a ka barshi in Allah ya yarda zan isa gida lfy yace to shikenan Allah e kiyaye sannan ki gaishemin da yarana Murmushi kawai tay sannan ta fada motar ta figeta saidata bace da gani sannan ya juyo daga inda yake tsayen Tunda afnan ta dawo gida kasala da ciwon kai suka rufeta don haka bata samu damar warware takardar da masinja ya batabawashe gari batai niyyar zuwa office ba don haka wata jallabiya kawai ta saka mai dogon hannu Bayan tayi wanka Har zata fice ta hango takardar tasa hannu ta janyota takardar sanmacice daga kotu idanuwa waje tace shin masinja mantawa yai ya bata kokuwa yaya? Tambayar da Taima kanta kenan ta warware takardar ta soma karantawa Tabbas tatace sammaci ita akaima qirjinta yai mummunan bugawa tace tabbas adnan ya debo ruwan dafa kansa wato ita yake qara a kotu Abinda ta fada kenan Sannan tai saurin juyawa ta nufi saShin abban nata da sauri hannunta Har kyarma yake Yana zaune a saman kafet yana break Bayan ta nuna masa takardarne cup din dake a hannunsa ya aje ya dago kai yana murmushi yace wato adnan dinne ke qararki a kotu?adnan kenan ciwone kawai ya hargitsashi kuma wannan wani damace dazai gane koshi Waye Gyara zamanki ki karya Allah e kaimu ranar zan tanadar miki shaidu ki kwantar da hankalinki Batace masa komaiba ta zauna Sukai break din tare Bayan sun gama break din tace amman Abba kafin zaman kotun inason zuwa abuja Na Gano momy kwana2 dinnan ina yawan tunanina ga fadiwan gaba dake damuna kullun idan na kwanta sainayi munanan mafarki akanta Yace tashi kije sha kuruminki afnan in Allah ya kaimi ranar asabar zamuje ki ganta Tunda zaman kotun naku ranar Monday ne cikin jin dadi tace yauwa daddy kaima zakaje yai murmushi yace nima zanje. Hardasu inna da taslin da aslim cikin jin daddy tace na gode daddy Tana fita sashinsu. Inna ta nufa ta samu yan tsofaffin nanfa aka bude shafin Hira Don tana matuqar jin dadin Hira da yan tsofaffin nata Adnan nne zaune a falonsa Kamar mutum mutumi yana cikin matuqar damuwa tun jia da abinnan ya faru Shinn wai mai yasa yarinyarnan ke masa hakane duk mazan dake fadin duniyarnan ta rasa Wanda zata riqama yaranta saishi Koko don taji ya samu matsalar memory dinsa shine zatai masa wannan Toce mata akai hauka yake? Yana cikin tunaninne yaji an dafa kafadarta Bai rasazana don yasan ko Waye don haka ko juyowa baiyiba ta zagayo ta zauna a kusa dashi Cikin murmushi tace Yadai my love badai tun abin jiyane ke damunkaba? Haba adnan inhar kayi mata abinda nace kai mata wlh ba zata sake shga harkarka ba Adnan ya dago dara daran idanunsa wanda suka kada Sukai jajir Sbd tunani ya cigi lebensa da haqoransa da qarfi yana girgiza kai Yace abin ya damenine sady fiye da yaddah bakya tunani bafa qaramar matsala bace matsalace babba matarnan ba qaramin abu ta shiryama rayuwatabada alamar tanada. Babban shiri akaina anya ba raina suke nemaba kuwa Wlh na fahimci yarinyarnan wani abu take shiryawa babba akaina To nidin wani mai arziqine da suke shiryamin wannan abun Ady tace aiko kai mai arxiqine Tunda ka mallaki manyan kudi gaka da asibiti da gidan mai Naka na kankin kanka Kana Tunanin qaramin mai arziqine zai wannan Adnan ya girgiza kai gamida cewa dole naima tufkar hanci Domin harna shgar da qara kotu Gaban sady yai mummunan fadiwa Wanda har saidata dafe qirjinya hannunta har kyarma yake tace kotu kuma adnan gaskia ban yardaba Wannan ai tonon sililine ka kaisu kotu kace wai kasan abinda suka taka Ai ina ganin Kamar mtsalar cikin gidane wannan Adnan ya bita da kallo yace wannanne matsala ta cikin gida? Baki da hankali sady Ganin yaddah duk ya birkice mata tasan abin nasa bamai sauqi bane Tace to kaje ka fadamasu baba sai Kaji abinda zasuce Miqewa yayi yace banson na tada musu da hankali shiyasa bannson fada musu Nafison na magance matsalar ni daya don banson wani ya zargeni Da aikata fasiqanci Sady ta fusata ta miqe tsaye tana jijjiga jiki ban gane bakason kowa ya shga cikin lamarinba shin babu alamun gaskia a ciki ne?kodai yayankane adnan Tambayr data rudar da zuciyarsa kenan ya vita da wani irn kallo cike da takaici Yace amman nayi mamakin wadannan kalaman naki sady daman na tabason wata mace kafin rashin lafiyata ko Bayan rashin lfyr tawa Bayan ke? Ta kifta idanu tana fadin to inba hakaba mai yasa bakason iyayenmu su shga cikin lamarin! Cike dajin haushinta yace haka naso kuma na tsara kema da kikafi kowa sanin halina kin fara zargina inaga su Don haka duk Wanda kika kira kikaima wannan Zancen na rantse miki a bakin aurenki cikin firgici tace abakina aurenafa kace adnan yace abakin aurenki so wat Ya fada cikin daga murya sannan yabar falon Cike da tashin hankali sady tace nashiga uku Hmmmm lol baki shga ukuba zama ki shgane Aimin afuwa yau banyi post da wuriba makara Aure. Kan. Aure Chapter29 Mun tsaya inda tsakanin adnan da sady suke kace kace inda har adnan yaimata furucin saki. Idan harta kuskuea ta fadama wani shirinsa nakai afnan kotu da yayi So muje zuwa Nan ya barta inda sady ta tsaya cikin tashin hankali Tace mai yasa tun farko bata canja masa takardunsaba ta canja masa sunansa gaba dayaba Ta daura hannu akai tana qoqarin rushewa da kuka Afnan ce zauna kan dressing mirro ta dau kwalliya ba qaramin kyau tayiba sannan ta tashi ta nufi falon da aka sauke ibrahim Sannu a hankali take tafian cikin kwarkwasa tana lallatsa wayarta Yana zaune Akan daya daga cikin kujerun tayi sallama idansa kur akanta. Ta sakar masa wani lallausar murmushi idanunsa kirr akanta ta zauna Akan kujeran dake fuskantarsa Shima ya qara zama yana Mata murmushi yace Tsarki ya tabbata ga mahaliccin wannan surar Allah ka qaddara nine Wanda zan dinga kula da ita don zatinka afnan tai daria tace dakata malam duk kyanka na kaika ne Riqe baki yayi ya zazzaro idanuwa yace waneni afnan amman kin kashe kanki aike kyawunkine ke fitarda adonki Bawai adonkine ke fitar da kyawun nakiba Sannan duk iya adon mutun idan. Idan yaxo gabanki saiya rude Shin wai akwai. Wanda ya tava fadamiki cewa. A duk sanda kikai murmushi kinfi kyau? Wlh ke kyakkyawace dubi yaddah fuskarki ke qalli sai kallon fuskata nake a ciki Wani qayataccen murmushi taja sannan tace maza kenan Tace ibrahim mai yasa kasan irin kalaman da nakeso a fadamin magana ta gaskia da kuma mai kama da tatsuniya? Yace ki yarda dani afnan Wlh a rayuwa bani da Wani buri daya wuce na mallaki zuciyarki dake kanki gaba daya Yace Wlh ina cikin damuwa afnan tsorona daya karkice ba zaki amince min na zama mijinkiba Afnan ta girgiza Kai tanajan Wani gajeran murmushi sannan tace. Hmm Ibrahim kenan dondai kawai inajin tsoron halinku na mazane in banda haka danace na baka zuciyata da komai nawa To kudinne dai lamarinku sai allah Amman ina mai tabbatarma da idan na shirya aure yanxu da babu Wanda zan aura sai kai Tuni zufa suka karyoma ibrahim ya sulale qasa saman gwiwowinsa ya zama abin ban tausaya Murya kamar zaiyi kuka yace Haba afnan ki tausaya ma radadi gamida zogin sonki dake addaban zuciyata mana Ki tausayama lamarin dake hananin sukuni dare da rana daman ance kama da wane ai bata wanie a zahiri nayi kama da maza ta hanyar halitta amman ba zai kasance ace zuciyoyinmu sun zama iri dayaba kowa da irin tasa zuciyar Wlh inhar kika aureni ba zakiyi nadamaba afnan Ina mai tabbatar miki da saukin manta da duk Wani baqin ciki dake cikin duniyarnan Saina dawo miki da farincikinki duk inda yake Saina Nemo miki shi Hmmm maza kenan abinda ta furta kenan ta miqe Ba tare data sake kallonsaba tace Zan sanar da Abba ka turo da iyayenka cikin satinnnan a tsaida ranar aurenmu wohoho Wani dadine ya rufeshi yaji kamar ya goyata don murna yace godia marar adadi afnan don Allah idan kika shga ki turomin da taslim da aslim Tace to tana fita falonta ta nufa tana isa ta iskesu suna game suka rugo da murnansu suka rungumeta suna don Allah mommy muje ki Siya mana ice cream Tai murmushi ta shafi kan yayan nata tace kuyi haquri yanxu yammah tayi ku bari sai gobe kuje inda ake sauke baqi dadynku nacan yana jiranku Tsalle sukasa yaran suna murna suka fice zasu ganin abbansu Wani murmushi afnan din tayi Wanda ya tsaya iya labba Yaran basu suka dagowa sai bayan magrib suka shgo da gudu suka haye jikinta tace oyoyo my twinsss ina kuka shgane kuda daddyn naku har hankalina ya soma tashii Sukace bako ina momy ai munce masa ma zamu bishi yace a,a mu bari sai an mana hutu sannan zaizo ya daukemu afnan din tace da gaske cikin murna Sukace da gaske momy yanxuma ya tafi Afnan na zaune bayan taci kwalliya ta hade cikin wata danyar shaddah. Inka ganta zaka rantse kace wannan budurwace danya sharaf. Ita kadaice a falon nata tai shiru ko tunanin me take oho Can kuma ta tashi ya nufi sashin mai kula da yaran nata Tana isa taga yaran suma ana shiryasu tsaf cikin Wasu sababbin kaya kala daya na namiji Dana mace Don haka taja hannunsu suka fice kowa ya Gama shiryawa don haka qatuwar jeep din daddyn nata shga shga harda shi daddyn nata. Don haka direba ya jasu A. G. R. A. Suka tsaya Suka dauki kausar sannan Suka Kama hanyar abuja ba hira suke sosai ba don kowa da abinda yake saqawa a cikin ransa Ibrahim ya kira afnan suka gaisa bayan sun Gama gaisawanne yace abama su taslim yanason Jin muryarsu ta basu wayar inda ita kuma ta maida kanta jikin kujeran motar Can tajiyo ibrahin da yaran hira ta barke a tsakaninsu tun tana sauraronsu har. Tunani ya rinjayi zuciyar tata misalin azahar suka isa garin abuja Kai tsaye gidan yari suka nufa ba tare da bata lokaciba aka sanar dasu cewa tana medical hospital Don haka aka rubuta musu takardar ganinta suka nufi asibitin jikin afnan har rawa yake wurin shga Dakin da aka kwantar da mahaifiyar tata Ji take kamar tai Mata Wani laifi tunaninta daya batasan sa idon da zata kalli momyn nata ba Ji tayi an riqo hannunta abbantane she harsun shige ita tananan a tsaye Yana janye da hannunta har suka isa Dakin da momyn nata ke ciki afnanan tai matuqar kidima ganin halin da mahaifiyar tata ke ciki Har kusan kifewa tai sbd matuqar kidima saidata dafa qarfen gadon da maahaifiyar tata ke ciki Idanunta suka. Ciko da kwalla duk an jirkita halittar mahaifiyar tata ashe ciwon sashin jikine ya kamata Ta riqe hannunta sashi daya daya mutun tace Momy haka rayuwa tai dake? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun ta kasa boye kukan dake fuskar tata hajia nafin dake kwance ta daura dayan hannun nata dabe mutunba Akan afnan din Itama hawayen take ta soma magana amman maganar bata fita kamar mai kwaranci Cikin kuka afnan ta dago tana kallon mahaifin nata idanu jage jage da hawaye Tace abbah ban fahimtar abinda takecewa yace cewa tai kinga yaddah Allah ya maida ita duk ta sanadiyyyar alhakin jama,a dake kanta Sannan tace ki roqar Mata mutane Akan su yafe Inhar ta mutu a haka alhaki bazai bartaba. Balle har tasa ran samun rahmar uban giji Afnan ta kifa kanta a kan momyn nata tace momy na yafe miki kuma nasan duk Wanda kika zalunta zai yafe miki inhar yaga halinda kike ciki Hakan yasa hajia nafin taci gaba da magaba saidai a yanxu babu mai fahimta don haka itama taci gaba da kukan don babu bakin da zata fadi abubuwan da takeson fada musu din Aleeyu yasa hannu ya janye afnan din daga jikin nafin ya girgiza Mata Kai alamun kukan ya isa haka Hakan yasa su kausa inna da malam suka qarasa inda take sukai Mata ya jiki basu fahimcvi abinda take fadaba sai aleeyune ke fada musu Wasu kalaman nata idan shima ya fahimta Gaba daya Dakin babu Wanda baiyi kukaba sai aleeyu da Mala wadanda keta tofa Mata addu,o,i Su taslim ma saida sukai kuka ganin momyn nasu na kuka nafi tai musu nuni alamun suxo sukaqi saida aleeyu yajasu yaje ya hada hannunsu da nata yace kin gansu jikikonkine yayan da afnan ta haifa Runtse idanunta tayi tana Wani irin kuka mai ciwo da alamun abin nacin zuciyarta Basu Wani jimaba sukai Mata sallama. Saidaya biya da yan jikokin nasa super market yai musu siyayyah sannan suka nufo hanyar kano Bayan shin shga Wani restaurant mai rai da lafiya kowa yaci ya qoshi. Sannan sukayo hanyar gida A yanxu afnan ta daina kukan da take saidai ajiyar zuciya akai akai don haka kausar ta janyota ta kwantar da ita jikinta gamida lallashinta Dukda tana kallon wayarta dake qara ta Gaza dauka Dukda tasa mai Kiran ibrahim ne Basu isa kanoba sai bayan sallar magrib ta gidansu kausar suka fara sauka sukayi sallah sukaci abinci sannan suka wucto gida Tun daga bakin gate afnan ta hango motar ibrahim yana kwannce a saman boot din motar kansa na kallon sama suna tsayawa su taslim suka kwasa da gudu suna ga daddy ga daddy Aleeyu yace subhanallah yaufa ashe mukai da iyayen yaronnan zasuxo Allah dai yasa ba zuwan yammah sukai ba Tace ba zasuyi zuwan yammabh ba tunda aina fada masa cewa zamuje abuja. Aleeyun yace yauwa Da sauri ya sauko daga motar ya rungume yan yaran yana dagasu sama Ganin abban afnan din ya nufo inda yake yasa ya saukesu ya zube yana kwasar gaisuwa Cikin nuna kulawa aleeyun ya bashi hannu sukai musabaha yace Allah dai yasa bamuyi muku African tyme ba yace a,a suma. Nanda minti talatin direba zai kawosu aleeyun yace masha Allah Sannan ya wuce ciki afnan dake tsaye wajen tace Kai kumai maiya kawoka? Ya lankabe Kai muryarsa tayi laushi yace hankalinane yaqi kwanciya afnan don na kiraki yafi sau hamshin amman kinqi dagawa Ta yaya hankalina zai iya kwanciya afnan? Saidayadan bata tausayi don bataga alamun wasa Ko zolaya daga idanun nasaba su taslim kuwa sai tsalle suke jikinsasuna fadin sudai ice cream zasusha Cikin kakkausar murya tace Kai ku shigaa gida mana Ibrahim din ya janyosu yace a,a afnan karki korar minsu har Cikin jinina nakejin yarannan don Allah ki qyaleminsu Ki fadamin meya hanaki daga wayata alhalin kinsan muryarkice kawai ke kwantarmin da hankali? Ko bakyasonane Wani qayataccen murmushi taja tace haba ibrahin aida bana sonka da tun farko ban kulakaba don haka bai kamata ka dingamin wannan zarginba Dubekafa babu ta inda Allah ya rageka kanada kyau ga zati uwa uba kwarjini Ga haquri sanin ya kamata aikai abin alfaharine ga duk macen data sameka a matsayin mijinta kuma uban yayanta Ka yarda dani Wlh ina sonka da duk zuciyata wami sanyin dadine ya ziyarci zuciyarsa Har yakeji tunda yake a. Duniya bai tabajin kalaman da sukai masa zaqi kamar wadannan a xuciyaba Bakinsa yaqi rufuwa yace Allah sarkin dadi inji barawontakanda abinda ya iya cewa kenan sannan yace Afnan Wlh bazakiyi Dana sani miqamin saoyayyarki da kikai gareniba nai miki alqawarin saina shayar dake gidauniyar farinciki Afnan din ta lumshi ido tana murmushi dadin kalaman nasa na ratsa zuciyarta Tace na gode bari na shga gida yanxu muka dawo so nake na watsa ruwa nadan kwanta yace ni kaina yanxu sulalewa zanyi karsu alhaji suxo su sameni anan suce zaqewar tawa tai yawa San sukai sallama Ta fada gida cike da begeb juna Qarfe takwas daidai iyayen ibrahim suka shgo suma attajirai ne sossai akai kudin a qasa Don haka aka karramasu sosai Basu rabuba saida suka aje sadaki naira dubu dari uku da kuma naiman auren afnan ga ibrahim don Haka malan ya tsaida ranar daurin aure nanda Sati biyu masu zuwa A. Kotu Washe garin ranar itace ranar data kama ranar litinin tanar dasu afnan zasu zauna a kotu inda suka Gama shirya qwararan hujjoji Akan adnan Don haka a shirye shuke kotun Ta cika matuqa kamar kullun Alqali na shigowa aka tashi domin diban gaisua bayan mai gabatar da qara ya tashi ya gabatar da qara kowa ya koma ya zazzauna Alqali ya buqaci lauyoyi dasu gabatar da kansu Barister muqaddam ya gabatar da kansa a matsayinsa na lauyan dake kare Wanda ke qara Mutum ne mai kwaxo da sanin aiki yakai maqura wajen sanin haqiin dan adam Lauyan kasuwane amman kuma Mai tsadar gaske Yana zama zaina sufwan ilyasu zee . Zee qawar afnan ta miqe itama ta gabatar da kanta Akan itace Lauyar dake kare Wanda ake qara Bayan ta zauna ne baristar muqaddam ya miqe ya nemi izni a wajen Alqali kamar haka Yace ya mai girma mai shari,a inason kotu ta bani dama Dana taso da Barister afnan aleeyu musawa domin nai Mata Wasu yan tambayoyi Alqali yace an baka dama Afnan ta miqe ta nufi kan yar kantar da aka tanada Don tsayiwar Wanda za.aima tambaya ko tuhuma Tana qarasawa Barister muqaddam ya qarasa gabanta yace malama ko zaki iya fadama kotu Sunanki da kuma asalinki? Afnan tace nidai asalin sunana shine hafsa. Ana kirana da afnan ne sbd sunan kakata ta wurin ubane da naci Kuma ni yar asalin garin kano ce don. Anan aka haifeni Lauyan yai saurin jefo Mata tambaya yace Ke yar asalin garin kanoce kuma kike amfani da musawa ko zaki iya fada mana ta inda kika samo hakan? Afnan tai murmushi tace musawa asalin garin mahaifinane shi acan aka haifeshi karatune ya kawoshi. Garin kano Lauya yace amman gaki kamar budurwa kuma kike iqirarin kinada aure Afnan tace kwarai kuwa. Niba matar aure bace kuma ba budurwa bace Barister ya zaro ido gamida cewa woot me kike nufi da keba budurwa bace kuma ba bazawaraba ??? Hmmmmm jama,a ku biyoni a next chapter donjin yaddah kamarin zai wakana And. I will like to. Apologist again. A lot ov ppl zasuyi tunanin kaman wulaqancine ko hakanne kawai yasa ban muku post kwana biyu ba da kuma. Jia da nace muku zanyi post banyiba so dan Allah Aimun haquri kuma aimin uzuri. Banason trust dina dake gareku ya samu tankarda ku yarda dani hakanan bazanqi yin muku post ba. Jiyanma naso nai post din. Ba yadddah zanyi. Aure. Kan. Aure Chapter30 Barister yace kamarya keba matar aure bace kuma ba budurwaca inda muka tsaya kenan Good Ta gyara tsayuwarta tace sbd bayi aure shekaru hudu da rabi da suka uce harda yaya biyu. Aslim da taslim Don haka ni bazawarace Lauyan yace ko zaki fada mana waye kika aura? Tace dan uwana na aura adnan aleeyu musawa da kakana da nasa uwa daya uba daya suke Tun adnan na yaro mahaifinsa ya rasu bayan yabar mahaifiyarsa da ciki itama wajen haihuwar ta rasu. Hakan yasa kakata ta dauko adnan da niyyar ta riqeshi kasancear Yanxu babu yaro a gabanta Don bata sake haihuwaba tun daga kan mahaifina Alokacin da mahaifina yaje musawane duba iyayensa yaga Adnan ya daukoshi domin ya samu ingattaciyar Ilmi a Birni don shima a lokacin babu yaro a gabansa domin bai haihuba mahaifina ya dauko wacce zata raineshi kasancewar mahaifiyata ba iyawa zataiba Ya kawo baba hauwa ita ta riqeshi da aka haifenine ta hadamu ta riqe gabaki daya Bayan Mun girma yaya adnan har qasar London mahaifina ya turashi karatu Yana dawowa aka hadamu aure dashi saidai abin yaxo da matsala. Kasancewar mahaifiyata batason auren Wai ita tsohon. C. G. A. Takeson na aura wato tsohon comander genaral na sojoji ni kuma bana sonsa Hakan yasa mahaifina ya jajirce Akan sai an dauramin aure da adnan Wanda aka daura a. Musawa. Daga baya kuma akazo akai musu sharri Akan wai suna safarar hodar koken da qananun yara. C. G. A ya kama mahaifina da mijina ya daure inda yaketa azabtar dasu Ananne shi mijin nawa yai lossing din memory dinsa shi kuma mahaifina ya kakkarye Don haka na nemi taimakon qawata wacce mahaifiyarta aminiyar mahaifiyatace tana a matsayin . D. G. P. Ne a garin abuja ta taimakamin matuqa wajen shigar da qara kotu kuma ta tsaya tsayin

Chapter 11 of 16