Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
duk haɗin gidane. Ko akwatin Amaryar Nazifi baa'a kaiba, ance in aka kawota sai kawai a miƙa. Akwatuna masu taya suna nan a ɗakin Yaya Haula, ina dai gani matan waje sunata shigowa kallon kaya. Ni ko da nake gidan babu wanda ya neme ni da in zo in ga kaya, nima ban ɗaɗa kaina ba. Bayan azahar maza ƴan ɗaurin aure suka dawo tare da bataliyar maza ƴan Takai. Da yamma lis kuma sai ga jerin gwanon tsofaffi da Amarya an tawo da'iya. Harda Sakina aka tawo, suma sun sha ankonsu na Takai. Muma duk mun ci namu ankon na cikin gida, shaddace mai ruwan toka na iyaye, sai wani yaɗi haka na ƙawayen Amarya dai. A haka taro ya watse, duk da ina kaffa _kaffa sai da Yaya Halima ta ci mun mutunci a cikin mutane, daurewa nayi na shanye dan a ranar ma Takai zasu komai. A dangina babu wanda yai mun kara yazo, Uwani ce dai na matsama bata da yadda zata yi shi yasa tazo. A kwana a tashi asarar mai rai. Wasa wasa ƴan biyu shekararsu guda, har suna dabo, Toye kuma yanata zuwa makaranta. Fitinar gidanmu kuma babu abinda ya ragu sai ƙaruwa, dan sau huɗu Gwadabe na biyan kayan da aka sata. Na huɗun ma har ƙarƙashin kujerata akazo aka saka mun, da suka shigo bincike suka zaro. Nayi imanin Laila ce ta aikata mun hakan ba kowa ba, dan tuggu da munafurci iri iri take haɗawa, tsaraicinta da aljanun ƙarya fa babu abinda laila ta dena, a wannan shekara guda ɗin abubbuwa masu dama sun faru. In baku mance ba nace ina yaye ƴan biyu zan bar gidan, to maganar tana ɗamfare a zuchiyata. Ga zawarawa kullum a cikin sallama da' Laila suke, tare da kawo mata ƙwalam da maƙulashe, amman mayyar tana kan bakarta ita sai Gwadabe. Gwadabe ne yaita bani haƙuri nima ganin na kusan yaye in barshi ma baki ɗaya shi yasa ma ban yi tafiyata ba na haƙura na zauna, na cire damuwar kowa da komai a raina. Kamar wasa wata ranar juma'a sai ga Oga Lurwanu shi da karen motar Gwadabe sun riƙo gwadabe ko iya taka ƙafarshi bayayi, suka shinfiɗe mun shi a doguwar kujera. "Gashi nan kin ganshi, mota ya shiga, amman wallahi sai zaro shi akayi ƙafa taƙi takuwa. Muna kyautata zaton sammu akayi mishi. Dama in dai a raba mutum da kafa ko hannune a harkar tuƙi ba kanshi farau ba. Sai ku dage mishi da maganin gargajiya" Hannu na ɗaura aka ina kuka, shima Gwadabe kukan yake yi yana girgiza mun kai halamar in yi shiru. "Ki gode ma Allah ma, da ba haɗarin mota akasa yayi ba ya ragargaje ba. Dan shima anayi kana tsaka da tuƙi sai kaga zaki ko kura, kana ɗauke hannunka magana ta ƙare. Wasu kuma teku suke gani a gabansu duk sai su dibibice" Ni dai sai mamaki da tsoron sha'anin mutan Duniya duk ya kamani. Nera dubu biyar ya ajjiye mun. "Mu kam zamu koma Gwadabe Allah ya ƙara sauƙi" Su kai mana sallama suka tafi. Kifewa a jikinshi nayi ina kuka kamar fitar rai. "Iyabo ki yi ta mun adda'a Allah zai bani lafiya, ta Allah ba dai ta mutum ba. Ni na ɗauka wannan jarabawace ubangijina ya jarabceni dashi. Bazan ɗaura hakkin akan kowa ba Allah yana madakata yana ji da ganin kowa. Ki yi ta mun adda'a. Kafin in amsa shi Yayyen nashi su kayo sallama suka shigo. Baban Nazifi yace. "Gwadabe haka abun ya faru? Ni ina kasuwa ma shigowata kenan mata suke sanar dani wai an shige da kai a hannu baka tafiya, haɗari ne ya afku kome? Koma dai menene Allah ya kyauta gaba. Ke bamu waje ko?" Ya juyo yana mun kallon tsana, ƴan biyu na kwashe dan kar su damu Babansu. Ina daga uwar ɗaki na kira Iyaa nake sanar mata halin da Gwadabe yake ciki. Halin ko in kula ta nuna, tsaki ma tayi ta kashe wayarta, sai Burodami kokodeen da Burodami Debisi na kira na sanar musu, sai ƙawar arziki Uwani. Su Baban Nazifi sun daɗe sosai a falon kafin daga bisani suka tafi, ni da yaran muka fito. "Iyabo inaso zan ɗaura alwala, gashi ina jin fitsari ma. Zaki iya kuwa?" Murmushi nayi ina hawaye lokaci guda nace. "Ai ko ɗaukarkane kacokam zan iya mijina. Nice a haƙƙu in yi maka duk abinda kake da buƙata" Miƙewa nayi na kai yara uwar ɗaki na kulle, falonma na kulle na tawo da ƙaton po mai murfi, cikin dabara na zamo Gwadabe izuwa kan po ɗinnan. Yayi fitsari na mai tsarki, na sake mayar dashi kan kujera. Daga ni har shi sai muka fashe da kuka na faɗa jikinshi. Allah kenan mai yin yadda yake so da bayinshi. Mutum ya fita da ƙafafuwanshi amman yanzu jibeshi a kwance, abunda yafi ƙarfi yanzu ya fi ƙarfinshi. Su Baban Nazifi daya kamata ace su zasu mai duk wannan amman kowa ya tafi ya barmu. Gwadabe kayi haƙuri kuka ba namu bane fa. Akwai Allah shi zai yi mana sakayya. Ka rungumi ƙaddararks sai Allah ya kawo maka ɗauki. Zaka warke bi izinillahi rabbi" "Iyabo ki duba dangina jinina yanda suka nuna halin ko in kula da abunda ya sameni, babu wanda ya tambayeni ko ina jin wata lalura. Yanzu ko Da'u da ba sai ya zauna ya kula dani ba?"... A'a Gwadabe kar ka ɗaura musu nauyin da ba nasu ba. Ni ya kamaci da in jinyata maka. Karma ka sake tada wannan zancan. Ga bawo kayi alwala." Shi da kanshi yayi alwala ni kuma na wanke mishi ƙafafuwanshi. Gwadabe ka daure in kai ka kan gado kaji, sai kayi zamanka acan. Yanzu nan anjima kaɗan Laila zata tashi kwanciya." "Ba zaki iya kaini ba Iyabo, ki je ki kira Da'u ko Nazifi ɗayansu yazo ya kaini, ko du su biyun." Bana so in mishi musu da To" Na amsa mishi, na fita da po ɗin da yayi fitsari na zubar, sai da na mayar ƙarƙashin gado sannan na je kiran Nazifi da Da'u tare da sanar dasu saƙon dake tafe dani. Abun mamaki ko da suka kinkimeshi su biyun dukkansu sai mitar yayi nauyi suka dinga yi, ƙafarshi ɗaya ma basu kama ba sai janta su kai kii. Ni ko ina durƙushe ina hawaye har suka fice ina kuka. A wajen su Yaya Haula suka shigo suka sameni idanuna sun ƴi luɓu_luɓu dasu. "Ohh ni ƴarnan mutum ba a bakin komai yake ba, yau_ yau ɗinnan Gwadabe ya zama musaki sai an kwantar sai an tayar. Sannu Iyabo kinji sannu" Kalmar musaki data faɗa ya dafani sosai. "Kaimu muje mu yi mishi sannu ko. Laila sai ki kwashe kayanki ki ko ɗakin su Halima da Ƙauwama sai ki koma kinga ƴan zuwa dubiya zasuita sunturi kuma dole falo za'a dinga fito dashi" Ni dai gaba nayi suka biyoni. Suka gama gaisheshi suka fita. Ni kuma ina gefenshi ina tofa mishi adda'a a ƙafar tashi, shi kuma yana kallon silin yayi wani irin sanyi" "Iyabo kinga irin riƙon wulaƙancin da Da'u su kai mun? Kinga yatsan ƙafata ya fashe. Daga kwanciya lalura yau _yau harna soma fuskantar wulaƙanci, sai kace ba ciki ɗaya muke ba. Wannan ƙiyayyar dame tayi kama, ki duba fa yanda su Yaya Hambali suka zo suka dubani wallahi babu damuwar komai a fuskokinsu, sai cewa su kai nima karambanine yasa na shiga sana'ar da bani da ilimi a kanta. Wai sana'ar hatsari gareta." Hawayene suka gangaro daga idanunshi izuwa fuskarshi. Rarrashinshi na dinga yi, a ƙoƙarina na ganin na faranta mishi rai, wala Allah ya samu sassauci. Ruwan ɗumi na zuba a bawon na tsoma tsumma na ɗan gargasa mishi yatsan nashi da yake jini. Ya samu yayi sallah, na bashi abinci a baki da kaina, ina bashi ina sake yi mishi nasihu masu ratsa jiki, akan ya gode Allah ma da ba hatsari yayi yaji raunuka masu yawa ba, da izinin Allah muddin muka dage da adda'a koma sammunne Allah zai bamu nasara, amman zuwa gobe zamu je asibiti. "Babu ko ficika a jikina Iyabo, kuma kinga asibiti sai da kuɗi Iyabo" Haba Gwadabe, zan siyar da atampopina in samu ɗan kuɗin da zamu riƙe a hannunmu, mu gode ma Allah muna da abinda zamu ɗaga mu siyar ma. Ina zuwa da zafi_zafi akan daki ƙarfe. A zabure na miƙe na shiga zaro atamopin sunan ƴan biyu, kala goma na fitar na zuba a bako. Gwadabe bari in je shagon me sai da atampopinnan ta bakin titi yarenmun nan, bazan jima ba, ga yara a falo" Ban tsaya jin abinda zaice ba na fice, sai dai kunsan mutane in suka ganka cikin matsuwa ka fitar da abu zaka siyar, sai su dinga yi maka tayin wulaƙanci. Dubu goma sha biyar ta taya atampopinnan kuma manyan atampopi harda Holland, da ƙyar muka ƙarƙare a sha bakwai da ɗari biyar. A cikin daren yau daga ni har Gwadabe kusan kwana mu kai muna Sallah muna adda'a, wallahi har akai sallar asuba bama ko jin digon bacci sai jarababben ciwon kai daya jarabeni. Ana fitowa Sallah na jiyo sallamar maza a ƙofar ɗakinmu. Baban Nazifi ne yake sanar dani dattawan unguwane suka zo duba Gwadabe. Hijabi nasa kafin nace su shigo. Gaggaisawa mu ka yi dasu, tare da yi mun jajen abinda ya faru, daga bisani kuma suka shiga ciki dubo shi. Ni dai jigum nayi a wajen na rasa me ke yi mun daɗi, a wajen suka fito suka taddani, su kai mun sallama suka fita. Ruwan wanka na juyo a bokiti na shiga da sallamata. Na samu Gwadabe yayi jigum yanata aikin tunani, na sani ban isa na hanashi tunani ba, domin jiya uwar haka da lafiyarshi ras ya fita. Gwadabe bari in ɗan goggoge maka jikinka da tawul sai ka yi asuwaki mu samu mu je asibitin ko?" Sai da ya sauke nannauyar ajjiyar zuchiya yace. "Na yi ma Yaya Hambali magana kan batun asibiti da muke son zuwa. Bai goyi bayan hakan ba, yace ciwon yafi kama da sammu, tunda babu inda yake yi mun ciwo, sai nauyi da ƙafafuna su ka yi, kuma Oga lurwanu ma yace sammu ne" Hakane Gwadabe, amman zuwa asibitin ai yana da amfani, in muka je suka auna basu ga komai ba shikenan sai a yi na gargajiyan "E haka na ce mishi nimaa. Ya dai ce Da'u zai tsaya mu tafi asibitin tare." Goggoge mishi jikinshi nayi tas, na saka shi a po ya rage mararshi, yayi asuwakin zamani, kana na bashi tea da burodi, da ƙyar yaci burodi yanka ɗaya, ni ko iyaka shayin kawai na kurɓa, mu ka jiyo sallamar Uwani. Miƙewa nayi na fita falon ina sharar hawaye, ita kanta uwanin kuka take ta faman yi. Muna cikin haka Da'u da Nazifi suka shigo, basu kula mu ba, ciki suka wuce abinsu. Ni kuma na sallami Toye ya tafi makaranta. Fitowa dashi suka yi, Da'u sai tsaki yake yi. Mu dai bayansu muka bi, ashe sun kira tasi tana tsaye a ƙofar gida. Asibitin Murtala muka wuce, ganin halin da muke ciki sai wani likita yace bari ya bamu gado ayi duk binciken daya dace a tsanake zaifi. Hakan kuwa akayi aka bamu gado a Ward ɗin maza, Da'u da Nazifi kuma jin an riƙe mu a asibiti sai suka yi tafiyarsu. Hawaye kawai nake sharewa, likita yace mu zauna daga waje. "Yanzu tsabaragen ƙiyayya yana ciwon ma ba zasu taimaka mishi ba, a lokacin da yafi buƙatar taimakonsu ba. Tafiya fa suka yi Iyabo" Takaici da damuwa duk suka taru su kai mun yawa sosai. Muna zaune aka fito da Gwadabe a keken da ake tuƙa guragu zasu tafi ayo mishi hoto. "Baiwar Allah ya kamata ace akwai wani namiji da zai tsaya tare da marar lafiyan ba ke mace ba, kinga da su zasu sashi a keke, kuma su tuƙashi zuwa ɗakin hoto. " Nurse ɗin daya tuƙo Gwadabe ne ke magana. Gwadabe na kalla, shima ni yake kallo ya dafe kanshi da hannun dama, idanuwanshi tamkar garwashin wuta. To mun gode, suna hanya masu kula dashi ɗin." Na faɗa mishi haka, kafin ya miƙo mun wata takadda. "Ki je wancan tagar ki biya kuɗin hoto, in mun fito sai ki bari in mun dawo ki bani" Karɓa nayi jikina na rawa, su kuma suka wuce. Kuka na fashe dashi babu ƙaƙƙautawa, Taiwo da Kahinde suna ganin ina kuka suma sai suka soma kukan. "Iyabo kije ki dawo, wannan kukan ya isa haka kinga ga yara suma sun soma. Jakata na kinkima na je na biya kuɗin hoto na dawo. A taƙaice sai da muka wuni zumbur babu wanda yazo daga dangina ko na Gwadabe, Hafizu mijin Uwani ne ya kawo mana abincin da muka ci, da naga magriba na shirin yi na dubi Gwadabe nace. "Inaso zanje gida in dafo ruwan zafi, in tawo da tabarma." A'a su Babala suna hanyar zuwa. Ɗazu da likita ya kiraki Yaya Hambali ya kira ni a waya" Baima gama bayanin ba sai gasu sun iso dukkansu, harda Yaya Haula tana riƙe da filas na ruwan zafi da kular abinci. Da sauri na tashi a kujera na ba Babala waje ta zauna. Abu na farko daya fito daga bakinta shine. "Ba ga irinta ba, akan son gwanance mace kaje ka kai kan ka mahallaka. Waya sani ma ko daga danginta ne aka bugo maka wani agumun. Duk da sammu a tsakanin direbobi abune mai dogon tarihin gaske muma munsan tarihin. Gwadabe bazan yi maka baki ba, amman kaji na rantse maka da girman wanda yayi ni yayi ka buwayi gagara misali. Kana tashi zaka sallami wannan matsiyaciyar ka auri Laila, in ba haka ba sai in tsine maka ka bi duniya uban kowa ya rasa ka. Banga riba a aurenta ba sai ci baya da koma baya da rayuwarka tayi. Ke kuma na dawo kan ki, ki zauna da shirinki, Allah na tasan kafaɗarshi ƙarshen zamanki kenan dashi, ya'isa haka, inason yarona ya dawo yanda yake. Kin shigo cikin zuriyarmu kin tarwatsa mun kan yara." Da kuka taƙarashe zancen, yaranta na bata baki kan ta dena kuka. Baban Nazifi ya ɗaura da cewa. "Ya zame mishi dole ya rabu da'ita matsawar mune danginshi. In kuma zai sake iyaye da ƴan uwane sai mu gani. Sabida wannan baƙar kadarar matar tashi marar asali yasa na kasa tallafama Gwadabe Babala, amman a baya wanne irin so ne banyi mishi ba." Wannan yace wannan, wannan yace wancan kowa sai da ya tofa albarkacin bakinshi. Mu dai mun yi shiru kamar ruwa ya cinyemu. "Babala kima Allah kar ki zama silar rabani da Iyabo, son gaskiya take yi mun, bazan iya samun macen da zata soni rabin nata ba. Iyakar zamana da'ita babu abunda ta taɓa yi mun na assha." Miƙewa Babala tayi tace. "To gaka ga Iyabo. Ta maye maka gurbina dana ƴan uwanka da baka da tamkarsu. Ta zauna tayi jinyarka, ni kuma babu ni babu kai. A cikinku duk wanda ya tsaya ya kula dashi ban yafe mishi ba, ko ya cire dukiyarshi ya ba Gwadabe. Haula ɗauki abincin da kika kawo mu koma dashi. Da gudu nasha gaban Babala ina haki nace. Babala kiyi haƙuri ni nayi miki alƙawarin Gwadabe na warkewa a ranar zan bar gidanshi rabuwa irinta har abada. Bazan iya tafiya in barshi a wannan halin bane, ko babu komai uban Ƴaƴanane, kuma a zamanmu bai taɓa cusgunamun ba. Nima dashi da aurenshi ya fice mun a raina, wallahi ko baki ce ba ya zama dole in rabu da Gwadabe dan ba shi bane autan maza ba, kuma ba mutuwa zanyi ba. Amman fishinki masifa ne, yana buƙatarku yaya Harisu, Babala Gwadabe na buƙatar adda'arki" Duk wannan maganar cikin dimuwa nake yinta. Majinyatan dake kwance, da masu jinyarsu kab hankulansu a kanmu yake. Tsawa Babala ta daka mun. "Gafara dallah. Ke baki da uwa dama da sai in ce ki je kisa ta mai adda'ar mana. Tunda akan ki wannan ciwon ya same shi, ke zaki yi mishi jinya dan ubanki" Fuu suka fita suka barni. Bansan sanda na durƙusa a ƙasan ɗakin ina salati ba, Allah nake ambato a lokacin wani irin duhu ne ke mamaye mun idanuna. Uwani ce ta ɗaga ni. "Tashi Iyabo meye haka kike kuka kamar ƙaramar yarinya, ɗakinnan kab ke suke kallo. Rabuwa da Gwadabe shi ya fiye miki." Jaye ni tayi ta zo ta zaunar dani a kujera. Gwadabe yana kwance idanunshi a buɗe suke amman yayi zurfi a cikin tunani hankalinshi baya tare damu. "Bara in fita bakin asibiti in siyo muku ko da tuwo ne. Zan yi ma Hafizu filashin in ya kirani zan sa ya kawo ruwan zafi." Bani da niyyar bata amsa, itama bata buƙaci amsar tawa ba ta fice. Ƴan biyu suna ƙasa na shinfiɗa musu ɗankwalina suna bacci. Har Uwani taje ta dawo ni da Gwadabe babu wanda ya tanka ɗan uwanshi. Tayi yin duniya muci abinci mun ƙi yarda, damuwar da take gabanmu ta wuci a tsaya ana saka lomar tuwo a baki, ni in banda ɗaci babu abunda bakina yake yi. Mijin Uwani ma yazo yayi roƙon duniya kan mu ci abinci, ni ko magana na kasa, Gwadabe ne ma yake iya cewa a ƙoshe yake. "Iyabo ki taso mu je gidana, in yaso Hafizu zai kwana gobe mu ma dawo" "Ku barta tare dani, ina buƙatarta a kusa dani, damuwar zata yi mun yawa" Cewar Gwadabe, sai lokacin hawaye suka surnano da idanun Gwadabe wasu sirara. Uwani ta tattare yaran su kai mana sallama suka tafi. Da ƙyar ma'aikatan kiwon lafiya suka barni zan yi jinyar Gwadabe kasancewar ward ɗin na maza ne, akwai wata mata itama ita take ma mijinta jinya, sai muka zama mu biyu. Shiru wajen ya ɗauka na kasa rarrashin Gwadabe shima ya kasa rarrashina. Wannan daren na ba makaranta gari ku hasaso da kawunanku. Washe gari sassafe aka sake zuwa aka fita da Gwadabe zuwa wani hoton. Kafin a dawo dashi sai ga Yemisi da Burodami Debisi, da Lekan. Hannunsu riƙe da lodoji. Shigowarsu ke da wuya aka shigo da Gwadabe. Da Burodami Debisi aka kinkimeshi zuwa gado. "Sannu Gwadabe ya jikin, ashe abunda ya faru kenan?" Cewar Burodami Debisi. "Jiki sai godiyar Allah, Iyabo likita yace yana son ganinki" Tashi nayi na nufi ofishin likita. "Duk binciken mu ya tabbatar mana komai nashi lafiya suke. Mun yi hoto har sau biyu bamu ga komai ba. Mun sallameku inaga ku nemi na gargajiya zaifi. Ina mai baku shawarar ku sai mishi keken tuƙa marasa lafiya, yafi muku sauƙi da a dinga kinkimarshi. Ga takaddar sallama, kije ki biya Allah ya ƙara sauƙi" Sai da na share hawayena kana na amshi takaddar bance mishi komai ba na fita. Kuɗin hannuna sai da suka ƙare tas ban tsira da ko ficika ba. Burodami Debisi da Lekan su suka taimakeni wajen ɗaukar Gwadabe muka samu Taxi ta kaimu har ƙofar gida. Baban Nazifi da Yaya Harisu suna tsaye a ƙofar gida su Lekan suka zo suka shige da Gwadabe, na mara musu baya. Tunda muka dawo maƙota sukaita tururuwar shigowa gaishe da Gwadabe, su Iyaa Debisi ma sun tawo kusan dukka gidan, sun kawo abinci da dubu biyar, haka mu kaita karɓar jaje daga mutanen arziki. Babala kuwa a bakin Gude nake jin wai ta koma Takai Laila ma ta je ganin gida. Atampopi na na ɗura a buhu kab harda ma ɗinkakkun bar bari ba, kala huɗu na ware kawai, na ɗauki buhunnan na fita hankali da nutsuwata basa tare dani sam. Siyan wulaƙanci sosai akaima kayan, amman biyan buƙata yafi godon buri, Gwadabe mutum da ɓari ne a wajena. Keken ɗaukar marasa ƙafa ko tsofaffi na siyo ta hannu akan nera dubu ashirin da biyar da ɗari takwas. Ina shigowa gidan kallo ya dawo gareni, ni dai babu wanda na kalla takaina kawai nake yi. Ko Gwadabe yasha ruwan mamakin ganina da wannan wul ciya sosai. Ni dai bance uffanba na tallafeshi na sashi a kan wul ciya ɗinnan. Hawaye ya soma sharewa, ni kuma ina mishi murmushi. "Mala'ikun Allah ku shaida na sama rayuwar Iyabo albarka, kuma na ɗaga mata ƙafafuna domin ta shiga aljanna. Allah yai miki albarka ya kawo mana mafita akan jarabawar da take kanmu" Ameen Gwadabe, ka dena kuka. In sha Allah tunda ina nan kafi ƙarfin zubar da ruwan hawaye." Daga haka muka shiga suntirin bin masu magungunan gargajiya, mu ke nan kullum a tafe, amman babu canji kullum jiya e yau. Tafe tafe sai da mu ka kwashe tsawon wata uku muna abu ɗaya. Dangina da suke ɗan tallafamun suma suka gaji suka watsar. Babala sau biyu kaɗai tazo ta duba Gwadabe, amman ƴan Takai kam sun zazzo sosai. Sakina da Bara'u kam mayar da gidanmu su ka yi kamar aje kasuwa a dawo. Duk wata jigilar zuwa nemo maganin makarin sammun da akaima Gwadabe, tare da Bara'u da Sakina muke zuwa. Abincin da zamu ci Bara'u ke kawo mana. Ayashe da Tamu suma sun mana ƙoƙari sosai. Babbar damuwata ɗaya ce tak har yanzu babu wani sauƙi da aka samu." MRS BUKHARI 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAWU ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 10 Duk wannan ƙibar tawa da kuka ji labarinta, wallahi ta zuge sosai, na gama ramewa na fice a hayyacina sosai. Shi kanshi Gwadabe yafi tausayina fiye da kanshi. Bara'u kullum a cikin jinjina ma ƙoƙarina gami da amanaa suke yi. A kullum roƙona shine Allah ya ba Gwadabe lafiya, ya yanke mishi wannan zaman. In zaman cikin ya isheshi shi da kanshi yake tuƙa kekenshi ya fita ƙwar gida ya sha iska. Mun gama siyar da komai namu kuɗin ya ƙare a magani, ɗakina goduwar kujer da kafet kaɗai ya rage, sai tarkacen kwanuka da katifa , itama sabida Gwadabe na barta Wata rana ina zaune ina wankin kayana dana yara sai ga Uwani ta shigo, Gwadabe kuma yana ƙofar gida ya ɗan fita shan iska "Uwar biyu wanki kike yi ne?" Wallahi kuwa, daga ina haka na ganki afujajan?" Na tambayeta tare da kallonta. Sai da ta cire mayafinta kana tace. "Hmm wata harkar arziki na samo Iyabo. Kin ganni daga cikin gari nake gidan Hajiya salamatu, wata matace dake kai ƴan mata da matan aure ƙashashen larabawa ko ƙasashen turawa. Amman kafinnan na samo miki maganin karya sihiri garanti, daga cikin ayayoyin Qur'ani mai girma. Bari in karanto miki, muddin kuka riƙe wannan da izinin Allah kuka yazo ƙarshe a cikin kwana na bakwai Gwadabe zai miƙe da ƙafafuwanshi." Ina jin haka na zabur na saki wanki. Na juyo na zuba mata idanu. Dan Allah faɗi ina saurarenki Uwani" Dariya tayi tace. "Ɗakko biro da takadda ina faɗa miki kina rubutawa, da izinin Allah waraka ta zo." Da sauri ba shiri na yago takadda, na ɗakko fensirin Toye na dawo. "Da farko zaki samu ruwanki mai tsabta. Sai ganyen magarya koraye bushewar inuwa guda bakwai. Sai a karanta suratul fatiha a cikin ruwan da aka zuba magaryan, a dinga karantawa numfashin baki na komawa cikin ruwan Sai a karanta Ayatul kursiyyu ( aya ta 255 na cikin suratul baƙara). Sai a karanta suratul a'afaaf daga kan aya ta 106 zuwa kan aya ta 122. Sai a karanta yunus daga kan aya ta 79 zuwa kan ta 82. Suratul kafirun ƙafa ɗaya. Falaƙi da nasi ƙafa uku_uku Sai a karanta wannan adda'ar. Allahumma rabban nas,azhibil ba'as ashfi wa antash shafila shifa'a illa shifa'uk shafi'un la tugadiru sakaman Ƙafa uku za'a karanta. Sannan za'a iya karawa da wannan adda'ar "Bismillahi urkika min kulli shai'in yu'uziyaks wa min sharri kulli nafsin Allahu yashfiyka, bismillahi urkika Shima ƙafa uku In sha Allah ta'ala idan aka karanta wadannan kuma mutum ya dinga sha sau biyu a rana safe da yamma, yana kuma wanka dashi a waje mai tsabta, ko kokuma a jiƙa tawul a goge jikin marar lafiyan da ruwan maganin. Da izinin Allah cikin sati ɗaya mutum zai warke in dai sihirine a jikinshi. ( Kuma zaku iya jarabawa.

Chapter 9 of 16