Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
biyu tun ɗazu nake ta jiranki ki zo ki karya ku yi wanka ke da Toye, sai mu ka ji shiru kuma" Kujera na samu na zauna duk illahirin jikina babu inda baya yi mini ciwo, kuma babu inda bai yi mun tsami ba, zazzaɓi ne kau a jikin nawa ma, ga jiri da ke damuna. Ke dai bari, aikin abincin bikine bai bani damar zuwan ba. Kinga ko karyawa ma ban yi ba. Bara'u ina kwana ya akaji da taro?" Na faɗa kaina a ƙasa. "Lafiya lau Iyaa Toye Tsuntsun soyayya, ya jiki_ jikin?" Alhamdulillah. Na dubi Gwadabe nace. Ekaro oromi ( ina kwana mai gida?) Ajjiyar zuchiya ya sauke kana yace. "Kin tashi lafiya, ya jiki_jikin naki? Wato kina ta aiki bayan kinsan likita ya hanaki aiki mai wuya ko? Gobe ma kowa zai watse daga yau biki ya ƙare, tunda yau za'a kai Amarya ɗakinta ai" Boyayyar ajjiyar zuchiya na sauke, dan jina nake tamkar a ƙaya wallahi. Zame jiki Bara'u da Sakina su ka yi su ka bar mana ɗakin. Suna fita Gwadabe ya dawo kusa dani ya zauna. "Iyabona" Ya faɗa muryarshi na rawa. Kuka na fashe mishi dashi. Gwadabe na roƙeka da girman Allah ka sauwaƙe mun zuwa taron biki ko suna na danginka. Ba ƙaramin muzanta nake yi ba. Ka ware mana wasu lokutan domin ziyarar danginka, amman ba lokacin wani sha'ani ba." Shiru yayi yana kallona idanunshi suka kaɗa su kai jawur. "Ki ƙara haƙuri bisa wanda kike yi da dangina Iyabo. Nasan kina takura sosai, kuma kina shan baƙaƙen maganganu marasa daɗin saurare. Amman ni ko na so barinki a Kano, kinsan ba yarda Babala zata yi ba. Kuma hakan zai ƙara haddasa wata fitinarne. Iyabo bana son kukan ki, ki share hawayenki gobe da wuri zamu bar Takai ki yi haquri kinji?" Sai na ji tausayinshi ya kuma kamani, ga ɓoyayyar damuwa ina gani shinfiɗe a fuskantar shi, duk da yana ta ƙoƙarin ganin ya ɓoye mun halin da yake ciki. Amman na san Tatsuniyar gizo bata wuce ta ƙoƙi. A hankali na furta. Gwadabe na ganka a cikin damuwa meke damunka, kar kayi yinƙurin ɓoye mun, dan bama ɓoye ma juna damuwarmu. A kai nane ko Gwadabe?" Ajjiyar zuchiya ya sauke, tare da kamo hannayena dukka biyun ya ɗan matsesu kaɗan. Idanu na lumshe ina cike da tsantsar tausayin aurenmu. MRS BUKHARI *DAN ALLAH KUIMUN AFUWA NA SAURARI ƘORAFE_ƘORAFENKU AKAN KU WATA BIYU YAYI MUKU YAWA. AYIMUN AFUWA MU BARSHI A WATA BIYU, NA SAKE TURO WANNAN PEJINNE DOMIN IN MUKA DANNAR ƘIRKI DASHI. NAN DA WATA BIYU ZAKU JINI DA CI GABAN LABARIN NAGODE*🙏🏻🙏🏻 https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU. ROMO ƊANYE BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI Lamba ta uku "A game da abinda ya faru a gida can Kano ne kafin mu tawo. To da Yaya Hambali, da su Yaya Harisu duk sun amince akan Yaya Hambali ya tashe mu a gidanshi mu yi nesa dashi. To Babala tace dai a barta tayi shawara da su Goggo Iyatu. To kinsan Goggo Iyatu kusan ita take sake zuga Babala akan ki. Sabida Laila ƴar wajenta da Allah bai yi mun yi aure ba kamar yanda suka tsara tun muna tsumman goyo. To kinji abinda ya ɗaga hankalina kenan, tunda nasan bani da kuɗin da zan iya kama mana ko ɗaki ɗaya, balle ciki da falo." Ƙur na zuba mishi idanu. Gwadabe duk abinda Allah yayi a kan mu me kyau ne. Allah ba zai ba danginka ikon tozarta mu ba da ikon Allah. Kayi haƙuri jarumina duk a akaina ake yi ma hakan." Murmushi yayi gwanin tausayi yace. "A tunaninsu matsa mun lamba da zasu ci gaba da yi, shi zai sa aurenki ya sire mun. Billa aurenki kullum sake zame mun yake yi kamar yau aka ɗaura iyabo na. Kema ki ƙara haƙuri wata rana sai labari . Sannan ina da babban albishirin da na cancanci garjejen farin goro ɗan shagamu. Allah ya nufa nima na zama matuƙin Babbar mota na tashi daga karen mota. Ma'ana an mallakamun mota." Sakina ce ta shigo hannunta riƙe da langa da kofin silver ta dure shi a gabana. "Sakko ki ci abinci ki yi wanka mu samu mu koma gidan biki, yau biki zai ƙare Amarya zata kwana a ɗakinta" Godiya na yi ma Sakina. "Gwadabe Bara'u yana ƙwar gida wai kaje ku tafi" Da sauri ya miƙe, mu kai sallama ya fice dan yanzu za'a ɗaura auren ƴar autar tasu. Ni ko a gurguje na karya na yi wanka zuchiyata fal murna na san a ƙalla zamu samu sassauci daga talaucin dake addabarmu. , Sakina ta yi ma Toye wanka. Leshin ankon bikin Bose da mu ka yi wata shida daya wuce na saka. Leshi ne me tsada, dan ko sanda aka fitar da leshin na cire raina da yi, amman Gwadabe sai da ya je ya ciyo bashi yai mun domin ya fitar dani kunyar dangina, leshin ya sha ɗinkin buba da zani, na saka sarƙa fashion me kyau wacce Gwadabe ya siya mun a legas da suka je. Mayafina da takalmina ma sababbine wanda matar Tamu ta aiko mun daga Habuja, da naso in bari sai na haihu in yi fitar suna dashi. Gwadabe ne ya ƙi yarda yace lallai sai dai in sa a bikin gidansu nima in fito da kyau, dan su Yaya Haula suma sun yi ɗinke_ɗinken biki kala uku_uku. Ni kuma bamu da kuɗi leshin da na sa basu san na ɗinka ba, tunda mu ka yi bikin na ɓiyeshi a ƙasan akwati abunka da tattali irin na talaka. Fitowa nayi shar dani har ƴar hoda da jan baki na murza. Toye kuma riga da wandon Atampa na saka mishi da hular ashoke irin na yarenmu. Sakina ta riƙe mishi hannu muka nufi gidan bikin. Ƙofar gidan taƙi wutuwa sabida tsabaragen dandazon maza ƴan ɗaurin Aure, sai maƙota muka faɗa akan in an sassauta ma shiga cikin gidan. Sai wajajen kusan azahar ƙofar gidan ya sarara da mutane muka samu muka shiga cikin gidan. Da Laila na soma haɗa idanu, sai naga ta shiga ƙarame kayan jikina kallo har kirjinta na hawa da sauka irin na tashin hankali. Ni mamakine ma ya kamani. Ban bi ta kanta ba kai tsaye shiyyar Babala na wuce domin in sake gaishesu. Kowa na cikin ɗakin kallona yake yi baki a sake, Yaya Haula kuwa tsabar kallona da ta shagala tana yi sai da ta zuba ruwan miya a ƙafarta mai zafi kafin ta dawo hayyacinta. Koddibuwace babba a jikinta, amman leshina ya tsole mata idanu. Yaya Halima kuwa wuyana take ta kallo kawai. A tsarge na gaggsishesu bi da bi, suka amsa a daddaƙile in da sabo na riga dana saba tuni. Na ɗan zauna jim sai ga Amarya ta shigo ɗakin ita da ƙawayenta su su biyu. Ta tsugunna ta gaisa da kowa amman kallo wannan ban isheta ba. Sauwama Amarya an sha kyau" na ce mata ina ɗan yaƙe. In kun tanka yarinyarnan ta tanka. Abunda ya kawota ta yi ta fice da ƙawayenta. Bayan na zauna kamar na awa ɗaya haka sai na koma tsakar gida, dan naga atana alwalar sallar azahar. Ɗakin ƙanwar mahaifiyar Sakina anan nayi Sallah, mu ka ci tuwo da Sakina, na koma tsakar gida muka shiga rabon tuwo ka'in da na'in. Ban zauna ba sai da aka gama rabon abinci kab tukunna. Zuwa bayan laa'asar kuma dangin ango suka tawo da fantimotin aure, daga nan kuma zasu tafi da Amarya. Ayarin su Asiya na bi mu kai ta fita da kayan ɗakin Amarya ana sakawa a mota. Su Yaya Haula da Zuwaira harda su a ƴan kai Amarya, mutane sai da suka cika Bus guda, sai ƙaramar motar Amarya da ƴan ƙawayenta. Muna shiga cikin gida muka tsaida sanwar tuwon dare ba mu muka nitsa ba sai wajen takwas na dare, sai lokacin na samu kaina na galabaita sosai, marata ciwo take yi mun tun rana haka na kwana da ciwon marar nan. Da sassafe muka kuma tashi da aikin gyaran gida da karin kumallo. Kokko da ƙosai mu ka yi, bayan an kammala karyawa baƙi suka shiga haramar komawa garinsu, sai wanka akeyi. Sai da mu ka yi wanke_wanke muka share wajen tas kafin na samu bokiti na samu ruwan wanka mu ka yi ni da Toye. Gwadabe ne ya neme ni a tsakar gida ya same ni. "Ki hanzarta ki shirya yanzu zamu kama hanyar Kano. Ana mun lodi a mota zamu kai kayan Legas." Ajjiyar zuchiya na sauke nace. A shirye nake ni kam tsab. "To ki shiga ki yi sallama da matan gidan, sai ki same ni a ɗakin Babala" Yana faɗar haka ya juya da sauri. Ni kuma na shiga bin ɗakuna inai musu sallamar zamu koma, har na iso ɗakin Babala na shiga da sallama. Su Yaya Hambali duk suna ɗakin, waje guda na samu na raɓe. Babala dake magana taci gaba da magana. " Kai wannan yaron ka yi haƙuri ka bar Gwadabe ya zauna a tare da ku. Dan ina buƙatar a dinga sa mun idanu akan dukkan motsinshi. Amman ya dinga biyanka haya a shekara, in yaso sai ka kama shago da kuɗin ka dinga tara dabinon naka a ciki. Kai kuma Gwadabe duk shekara ka dinga bashi nera dubu ashirin kuɗin hayar ɗakinshi. Dan in ma baka bashin ba akan matarka zai ƙare. Gara ka ba ɗan uwanka dan babu irin hidimar da bai ma rayuwarka ba. Shi ya cicciɓaka har ka kai wannan matsayin. Ke kuma Iyabo zan gargaɗeki duk randa kika sake yi musu gwale a tsakar gida, ni na basu umarnin su watso miki da kayanki waje. In shi kin shanyeshi sai abunda kike so yake yi, to ni na sha tabara na sha yaseen ke har da lahaula duk na haɗa na sha na fi ƙarfin Oremi ma uwar bokayen yarbawa balle ke karan kaɗa miya. Ni dai kaina na ƙasa numfashi mai ƙarfi na saka fesarwa, in tashi in fita ina jin tsoron fassarar da zasu yi mun, in ci gaba da zama zuchiyata ta buga, hawaye na soma zubarwa. Yaya Hambali da su Harisu ransu yai fari fes dan jin irin hukuncin da Babala ta yanke mana. "To Shikenan Babala dan kin sa baki ne zan barsu su biya haya, amman da ko hayar basu isa na basu ba, dan dubu ishirin ɗaki ɗaya zai iya kama musu. Babala ki faɗa mishi na bashi sati ɗaya ya biya kuɗin haya, dan haya zata soma daga yau. Ban yarda kuma a sake sa mun kaset ɗin yarbawa a gidana ba." Ni sabida tsabar mamaki daskarewa nayi a zaune ina jin ikon Allah. Gwadabe kuwa kasaƙe yayi in wannan yayi magana sai ya juya ya kalleshi, har sai da suka gama maganar tsab yace. "To na ji Babala zan dinga biyan kuɗin hayan kamar yanda kika gindaya mun in sha Allah. Yaya Hambali kayi haƙuri a bisa dakatar da kai da na yi. Kuma in sha Allah in akwai wata doka ma da kakeson gindaya mana, zamu yi ƙoƙarin ganin mun bi, ai kai ubane ba wa a gareni ba. Babala shikenan inason mu tafi ana ma motarmu lodi legas zan wuce a yau ɗinnan?" Babala ta yi murmushi tace. "Me kake ci na baka na zuba, yanzu zan sallameku ai." Baki ta kada ta kira Laila har sau biyu kafin ta amsa daga uwar ɗakin Babala. Fitowa tayi tana wata irin tafiya ta jan hankali. Kallonta nayi inason in karanci yanayinta, ita kuma idanuwanta akan Gwadabe suke. "Kin gama haɗe kayan tafiyar naki dai ince?" Babala ta tambayeta, sai da ta yi murmushi har da sin da kai kafin tace. "Na gama haɗawa tun jiya Babala" "To ki fito da fantimotanki zaku wuce yanzu ko?" Laila ta kalleni muka haɗa idanu kafin ta koma uwar ɗakin. Babala kuma tace da Gwadabe. "Ga Laila zaka tafi da ita ta zauna a hannunka. In kun daidaita kanku falillahil hamdu, mu haka muke so dama. Kai na ɗauki amanar Laila na ba, sai ka kula da'ita yanda ya kamata. Ka kuma tuna ƴar uwarka ce, gyatumarta ni na saki nono na bata" Ba ƙaramin razana nayi da jin wannan zance mai kamar saukar aradu ba. Meke shirin faruwa dani ni Iyabo a wannan karon? Ta ya za'a bamu riƙon gansamemiyar bazawara irin Laila. Lailan da ada mijina ita zai aura, kuma har yanzu data fito naga son Gwadabe a idandunanta. Tabbas an shirya hakanne dan a nuna mun iyakata, ai mun kora da hali. In zan iya ɗaukar duk irin samfurin wulaƙancin da dangin Gwadabe suke yi mun, bazan iya jurar wannan ba, tabbas sai dai Laila ta mayema Gwadabe gurbina dan tafiyata zanyi gidanmu, abun ya isheni haka" "Babala taya zan iya riƙon Laila ina ƙarami alhalin ga Yaya Hambali, ga Yaya Harisu, sannan ga Sukairaju. A tunanina su yafi cancanta su rike Laila tunda sune a gaba dani. Sannan Babala..." "Ya isheka nace. Na riga da na yanke hukunci kai baka isa ka koya mun yanda zan yi ba. Ka tashi kawai ku wuce in ba so kake ranka yai mummunan ɓaci ba" Cikin faɗa sosai Babala take yin magana, har muryarta tana rawa. Ba shiri na miƙe har wani jiri nake gani tsabaragen kishi. To Babala zamu koma, sai mun sake zuwa kuma. Amarya Allah ya zaunar da'ita lafiya a gidanta" A mugun fusace Babala tace. "Ameen in da gaske kike yi baƙar muguwa kin rabani da abunda na haifa. Kema in sha Allah haka wata zata rabaki da ɗanki kiji in da daɗi" Bance uffan ba na ja hannun Toye muka fita bana ko gani da kyau. Ji nayi duniyar na juyawa dani, kaina na wani irin saramun tamkar zai rabe biyu. A ƙofar gida na nemi dakali na zauna jikina na rawa. Tsawon shekaru shida ina shanye dukkan abunda dangin Gwadabe suke yi mun. Amman ji nake yi kamar ma zamana da Gwadabe ƙarshe yazo kawai. Wallahi bazan iya dai dai da kwana ɗaya a ɗaki tare da Laila ba. Gara ni in matsa sai su aura mishi ita zaifi. Wasu zafafan hawayene suka gangaro a kumatuna. Ƴar ƙaramar wayata ce ta soma kuka, wayar da tunda nazo ba wanda ya kirani sai yanzu. In zaro wayar a jakar na kasa sabida tsabar turirin da zuchiyata take yi. Laila ce ta fita kici_kici da fantimotai guda uku hawan hawa, harda wata ƙatuwar jaka. Sai fara'a take yi tamkar wacce akaima bushara da gidan aljanna. Kawar da kaina nayi dan bana ƙaunar sake ganin fuskar Laila. A sanyaye Gwadabe ya fito daga cikin gidan. Duk yanda yaso mu haɗa idanu naƙi bashi damar hakan. Bara'u da Sakina ne suka katse mana tunaninmu. Gwadabe ya janye Bara'u zuwa gefe. Sakina ta zauna a kusa dani hannunta riƙe da baƙar leda. Laila tana daga gefe tana amsa kiran waya. "Meke faruwa Iyabo duk na ganku a birkice haka, naga Laila da fantimotan aurenta?." Hmm Babala ce ta danƙa amanarta a hannun Gwadabe, suna nufin tare da kishiyata zan zauna, bayan ta gama sanin sirrina sai a bashi umarnin aurenta." A hasale nayi maganar kuka na tunkuɗo kanshi. Sakina ta riƙe haɓarta tare da sakin baki cike da ta'ajibi tace. "Danƙari maƙari. Kika ce me, Lailan ce zaku tafi da'ita ta zauna a wajenku? Lailan da duk ƙauyannan ba wanda baisan irin son da take ma Gwadabe ba. Ke a wata ruwayar fa cewa akayi sabida Gwadabe ta kaso aurenta. Haka naji a wajen Goggona, kuma hakanne Bara'u ma ya sani. " Kaina ne naji yayi wata iriyar buɗewa, gabana yaci gaba da harbawa. Zuchiyata ta shiga watsa jini bisa rashin ƙa'ida, take na soma haki tamkar numfashina zai dakata. Yawu nake so in haɗiya in jiƙa maƙoshina da nake jin tsabar bushewa ya shiga daddarewa. Kika ce me Sakina?" Da ƙyar na jawo numfashi daga huhuna zuwa cikin bakina, harshena kuwa da ƙyar na iya sarrafashi. "Wallahi Allah kinji na rantse Laila sabida Gwadabe ta kaso aurenta, kowa ya sani." To gata ga Gwadaben, dan ni muna isa zan tattare inawa inawa in bar musu filin ɗakin, tunda dama abinda suke so kenan. Wallahi Sakina bazan iya zama inuwa ɗaya da Laila ba, gidanmu zan koma" Hawayena yaci gaba da zuba a kan kumatuna. Dafa kafaɗata Sakina tayi tace. "Bazan ce kar ki ƙwaci ƴancinki ba Iyabo. Haƙiƙa kin shanye abubbuwa masu yawan gaske tun daga aurenku kawo iyanzu. Amman barma Laila gidanki ba mafita bane Iyabo. Kiyi tunani kafin yanke hukunci, kar ki aikata aikin da zai jefa ki cikin dana sani marar amfani." Murmusawa kawai nayi dan banji akwai abinda Sakina zata faɗa yai tasirin hanani barma Laila Gwadabe ba." Gwadabe Yana fitowa ya dubi inda Iyabo ta zauna, zamanta kawai ya duba yasan tana cikin damuwa mai yawan gaske. Amman da zata tona taga irin damuwar da yake ciki zata san damuwarshi ta dame damuwar da take ciki ta shanye. Ya jima akan Iyabo yana son su haɗa idanu domin karantar yanayinta amman fur taƙi yarda ta ɗago. Dama muddin Iyabo na cikin ɓacin rai bata yarda ta ɗago kanta, sannan bata iya furta kalma. Isowar su Bara'u ce ta dawo dashi hayyacinshi. Gefe guda abokin nashi ya jashi. "Wadannan fantimotan ba na Laila bane Gwadabe. Kano zaku tafi da'ita ko me? Kasan zamanta gida ɗaya da matarka ba zai haifar da ɗa mai ido ba ko? Iyabo fa tasan irin soyayyar da Laila take yi ma, a lokacin da take ƙarƙashin inuwar auren waninka ma, ta kasa barin zuchiyar Iyabo ta nutsa, balle yanzu da nayi imanin farautar zuchiyarka zata je yi. Gwadabe ya kamata su Babala da Goggo Iyatu su ƙyale Iyabo ta nutsu, ta sha ruwa a gidanka. Yarinyace mai hankali da biyayya, gata da tausayinka, son da take yi ma mai tsananine. Shin ko dan so da ƙaunar da take yi ma ba hujja bane da zai sa Babala ta haƙura ta barku kuyi rayuwar Aminci ba?" Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke yace. "Ni bansan da wanne idan ma zan kalli Iyabo ba. Kar kaso kaji irin cin fuskar da Babala ta gama yi mata yanzu. Ba wanna ba Bara'u kasan ni Babala ta ba riƙon Laila a ɗakina zata zauna? Bayan hakan har tana ƙarawa da faɗin in mun daidaita kammu su hakan suke so. Ina cikin tsaka mai wuyar fita, ina jin nauyin Iyabo sosai, tana haƙuri da yawa da dangina." Bara'u ya dafe ƙirji tamkar wata mace yace. "Gwadabe kace Babala ce da kanta ta baka riƙon Laila, alhalin tasan ɗakinka ciki da falone kuma ƙananu, a haka take so ku zauna da Lailan duk abinda kuke yi tana jiyowa? Zaman ma bazai yi kyau bane Gwadabe kuma in akace an yi hakan to tabbas an zalinci Iyabo kuma an shiga hakkinta. Tana da damar yi maka bore ko tawaye. Kuma itama Babala dole ayi mata biyayya a matsayinta na uwa. Amman Gwadabe kar in tsayar daku kuje. Ni kuma zan shiga in samu Babala mu tattauna wala Allah zata fahimcemu. In yaso Laila ta zauna a wajen Haula tunda ita babbace kuma tana da ɗakin ƴan matan yaranta. Duk da hakan zaman ba kyau zai yi ba, amman in muka samu hakanma dama_dama. Dan Allah ka ba iyabo haƙuri ni wallahi kunyarta nake ji ma" Kai Gwadabe ya ƙyaɗa yace. "Kar ka wahalshar da kan ka da yawun bakin ka Bara'u. Ni nasan ko sama da ƙasa haɗewa zata yi, Babala ba zata saurareka ba balle ta fahimceka. Ko kasan yanzu haya zan dinga ba Yaya Hambali har nera dubu ashirin a shekara, ina nake da irin wannan kuɗin Bara'u?" Jijjiga kai Bara'u yayi yace. "Maganar tana da tsayi, da girma Gwadabe. Ungo Bakonnan shinkaface, da masara, sai kuka da daddawa, da gyaɗa da Sakina ta saka muku, ku kama hanya. Zanzo da zaran ka dawo daga legas, sai mu tattauna. Ta yi haƙuri ita Iyabo kafin mu tsayar da mafita. Muje suna jiranmu" Iyabo:. Ni dai ina zaune kamar mutum mutumi . Ita kuma Sakina sai gargaɗi take yi mun akan duk rintsi kar in kuskura in bar Laila taci nasara a kaina, kana kar in kuskura tasan logona na zafin kishi dan zata wahalani dashi. Jinta kawai nake yi, dan banga abinda zaisa in zauna inuwa ɗaya da Laila mu gauraya numfashi a ɗaki tare ba. Duk wannan abinda akeyi Laila na tsaye a gefe da Samarin cikin gidansu Gwadabe tana hira, duk da nayi imanin hankalinta na garemu. Su Bara'u ne suka nufo mu. "Tsuntsun soyayya to shikenan Allah ya tsare hanya. Aita haƙuri duk abinda yai farko ƙarshenshi yana tafe ko mu jima, ko mu daɗe. Allah ya yi miki albarka bisa bin mijinki da kike yi mun gode, in Allah ya saukeki lafiya Sakina zata zo da wuri ayi komai da'ita. Kuma a miƙa mun saƙon gaisuwa zuwa ga Iya Debisi, da Debisin" Ameen nagode sosai." Iyakar abunda nace kenan dan muryata shaƙewa tayi." Mashin Sakina ta tarar mun na hau, ta ɗaura mun fantimotina a gaba, ta miƙo mun ledar hannunta. "Amshi Atampa ce, kya ɗinka ki ƙara a kayan cin suna" Kafin in mata godiya har ta shige gidansu Gwadabe. Gwadabe ya hau mashin shi da Toye, da jakar kayanshi. Itama Laila ta hau nata aka ɗaɗɗaura mata kayanta muka wuce. Ina zaune akan acaɓa tunani duk ya addabeni, na rasa inda zan tsoma kaina. In na bar gidan Gwadabe na tafi gidanmu, bani da tabbacin Iya Debisi zata amsheni, kuma ko bata amsheni ba, sai ta yi mun kwakwazo da tonon sililin da kab ƴan gida sai sun sam halin da nake ciki. Ƙauyan da mahaifiyata take Aure kuma sau ɗaya na taɓa zuwa, shima a lokacin ina da shekara goma sha biyu ne. In wuƙa za'a ɗaura mun bisa wuya ko sunan ƙauyan bazan iya tunowa ba. Kuma har ga Allah bazan iya zama da Laila a ɗakina ba. Ajjiyar zuchiya na sauke wanda yayi dai_dai da isowarmu inda zamu hau mota. "Cikin gari ne, Alhaji, Hajiya kuzo ga mota" Cewar ma'aikatan tashar, suka yo kanmu suna rige_rigen sauke mana kayanmu zuwa wata cinyayyar Bus wacce ta ga duniya. Ni dai ina biye da mijina. Waje ya sama mun na zauna, Laila kuma ta zauna a jerin kujerun farko. Sai ajjiyar zuchiya nake faman yi. Ina hango Gwadabe ta taga yana biyan kuɗin motarmu, bayan ya biya ya shigo cikin motar. "Ga waje na samama kamar zaifi cikin sanyi ko?" Cewar Laila, tana yi tana kashe muryarta kamar tsohuwar karuwa. Tsaki ya ja bai ce mata uffan ba ya wuto inda nake a baya, yana riƙe da Toye. Zama yayi a kusa dani baice mun komai ba, amman naji jikinshi yayi zafi kau halamun zazzaɓi. Idanu na lumshe hawaye suka zubo mun suka diga a tsintsiyar hannunshi, kasancewar a mugun matse muke a motar. Ɗagowa yayi ya kalleni, ni ko kaina na kallon waje. "Iyabo so kike ki ƙarasa sukurkutamun lissafi kenan, ni da zan kwana a hanya ina tuƙi. Shin in ban samu sassauci a wajenki ba ina zan shiga in ji daɗi? Dubi yanda kike asarar hawayenki ke da baki da ishasshiyar lafiya" Da raɗa_raɗa yai mun maganganun. Zuchiyata ta tsinke, sai naji sababbin hawaye suna gudu a kumatuna. Allah ya gani bazan iya zama da Laila ba zaman da bansan irin sharrin da aka tanadar mishi ba tunda abun shiryayyene. Hawayena na share dan in sama ma Gwadabe ƴar nutsuwa. Amman sai na kulle idona kawai kamar mai bacci. Har motarmu ta fice a tasha, ta ɗauki hanya ban buɗe idandunana ba, banda niyyar buɗewa. Amman idanuna biyu zuchiyata na faman yi mun turiri. Ina jiyo muryar Toye yanai ma Gwadabe yarbanci, yana bashi amsa da yarbancin. Duk da ba iyawa yayi sosai ba, amman yana ƙoƙari wajen koyo, dan lokaci mu ka saka na musamman a tsakankanin magriba ruwa isha, ina koya mai yana maimaitawa in ya haddace sai ya rubuta. Wasu kalmomin da ƙyar yake iya furtasu. Muna nishaɗi sosai dan dariya muke yi sosai har tsakar gida ba za'a rasa jiyomu ba. A tsakanina da Gwadabe rayuwa muke yi mai aminci, muna ƙoƙarin bama junanmu farin ciki, da bama juna cikakken lokacin juna. Wannan irin zaman ke ƙaramun so da tausayin Gwadabe a ko wanne daƙiƙa. Shima hakan ke ƙara mishi sona.

Chapter 3 of 16