Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
Wasu malaman sun ce yana da kyau wanda yake da lafiyarshi ma yayi, domin hakan ka iya zama rigakafi kafi magani kareshi. Wallahu mista'al) Wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke tare da yaƙinin sauƙi ya zo ma Gwadabe. Duk da abaya masu magani sun bamu wasu mayuka tare da tofin ayoyin Allah a ciki mun yi amfani dasu da dama. Wasu kuma mu da kanmu muka zubar dasu, dan ganin shirka ta shiga cikin lamarin, amman wannan sai naji na samu nutsuwa dasu ainun. Nagode sosai ƙawata Allah dai ya bar zumunci. Bari ki ga da zafi zafi ake dukan ƙarfe bari in wanko ganyen magaryana, ina da ruwan sama cikin robar fenti sai in yi dashi. Sai fa na gama zan samu nutsuwa." Da sauri na je na ɗebo ganyen magarya adadin na buƙatar na wanko, na kinkimo ruwa da Qur'ani izu shittin. "Af na mance sai an daddaka ganyan magaryar ake zubawa." Cewar Uwani kenan. Da haanzari na ɗauko turmi na daka na zuba a cikin ruwan da bismillahi. Sai da muka kammala na samu nutsuwa har na sauke ajjiyar zuchiya. Daki na kai ruwan maganin na adana kana na fito." "To bani labarin abinda ya kai ki gidan Hajiya Salamatu, uwar shige_shige Uwani" "Wallahi Iyabo ƙasar zan bari zan tafi nemo kuɗi. Amman shekara biyu kawai zan yi in dawo" Zare idanu nayi ina dubanta da mamaki. Ƙasar fa kika ce, to aurenki da yaranki a hannun wa zaki barsu Uwani?" Ajjiyar zuchiya ta sauke tace.."Hafizu zai lura dasu Iyabo. Wannan talauci namu yayi yawa. Duk abinda Hafizu fa ya soma babu albarka sam a ciki. Kuma shi ba jari ba. Ke yanzu haka maganar da nake yi miki ma ina gidanmu fa da yaran. An koremu a gidn haya ko ince miki an watso mana kayanmu tsakiyar layi da ranar Allah. To Hafizun ma shi ya bani shawarar ko zan nemi aikatau na ƙasashe da ake zuwa, ƙanwarshi ma yanzu haka tana Canada a gidan aiki, shima in ya samu tare zamu tafi. Ni fa Iyabo wallahi tafiya zanyi. Su Hajiya ma basu san me ake ciki ba. Babbar damuwar shine ita Hajiya Salamatu tace sai dai in ajjiye dubu Hamsin da kuma ni zan yi ma kaina fasfo. In kuma ba haka ba duk zata yi mun amman zan kai wata shida kafin in gama biyan kuɗin da duk ta kashe mun. In kuma na yi fasfo na ajjiye dubu hamshin, da zaran na tafi a cikin wata biyu zan gama biyan kuɗin girji" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. To amman babu wani haɗari a cikin tafiyar dai ko. Kuma ina fatan bata ɓarauniyar hanya za'a tura ku ba Uwani, kuma kin tabbatar Shekara biyun zaki yi ki dawo, kuma zaki iya kare mutuncinki a matsayinki na matar aure, bahaushiya ƴar Najeriya, najeriyarma Arewa?" "To Iyabo ina kyautata zaton hakan. Ke kinga mata aure masu tafiya kuwa? Wallahi sun fi ƴan matan yawa, harda dattijai fa baki gani ba. Kuma ba ta ɓarauniyar hanya zamu bi ba, ta hazo zamu keta " Shiru nayi ina ɗan nazari. Kafin ince da'ita wani abun sai ga Gwadabe ya shigo akan kekenshi. Wannan dalilin yasa dole muka katse hirar tamu. Uwani tai mana sallama ta tafi. Tun daga ranar na soma ba Gwadabe ruwan addu'o'in nan safe da yamma, haka kullum sai na goge mishi jikinshi da ruwan maganin. Allah al Hakim cikin kwana na tara da rana kawai sai ƙafar Gwadabe ta motsa kamar da wasa. "Iyabo ƙafata na motsawa" Na ji ya faɗa cikin zabari. Kafin ma in ƙaraso inda yake harya miƙe tsaye. Suddajar godiya ga mahalicci mu ka yi a tare. Muna ɗagowa Gwadabe ya rungumeni tsam a jikinshi yana shafar bayana, tare da sama rayuwata albarka. "Iyabo kinga ikon Allah ko? Haƙiƙa na sake tsinkewa da lamarin Ubangiji Allah. Allah na gode maka daka bani lafiya. Ya Allah dukkanmin mai ruwa da tsaki akan wannan rashin tafiyar tawa ya Allah ka nuna mishi iyakarshi" Ni kuma sai amsawa da ameen nake yi. Ko yara da suka shigo suka ga Abbansu akan ƙafafunshi sai suka shiga murna harda tsalle. Rungumesu yayi dukkansu. Farin ciki da jin daɗi bazai misaltuba, bazai rubutu ba balle har mai karatu ya fahimta" Bara'u shine mutum na farko daya samu labarin warakar Gwadabe. Ni kuma ta ɓangarena Uwani na soma sanarma, kafin na sanar da gida. Na leƙa tsakar gida duk suna tsakar gidan ko wacce tana aikin girki nace. Ku ta ya mu murna Allah ya ba Gwadabe lafiya, ciwo ya warke" "Warkewa fa kika ce Iyabo?" Cewar Gude, kafin in bata amsa Gwadabe ya fito tsakar gidan. Ai sai suka riƙe bakinsu. "Allah ya bani lafiya haka tace. Gani akan ƙafafuna. Godiya ta tabbata ga Allah" Yana faɗar haka ya koma ciki riƙe da ƴan biyu. A masallaci abun sha'awa Gwadabe yayo sallar magriba, bashi ya shigo gida ba sai bayan isha sabida mutane sun baibayeshi ana mishi barka. Hatta su Baban Nazifi a masallaci suka haɗu da Gwadabe, kamar yadda ya labarta mun sun yi mamakin ganinshi akan ƙafafunshi. Ƙafa mai daɗi yau sai ga Gwadabe a bayan gida yana yin wanka da kanshi, Allah abun godiya ne A daren ranar Gwadabe yasha labarai sosai. Hira mu kai ta zabgawa muna murna da farin ciki. Furucin Babala yananan ɗamfare a zuchiyata ya zame mun ciwo. Na yi alkawarin washe gari zamana a gidan Gwadabe yazo ƙarshe kenan. Har yayi bacci idanuna biyu ina tunanin inda zan nufa in na bar gidan Gwadabe. Wata zuchiyar tace mun. "Ga mahaifiyarki da kike ganin kamar tana da wani ciwo a zuchiyarta me zai hana ki koma hannunta da zama. Tunda yanzu kin mallaki hankalinki?" Idanuna na lumshe wasu siraran hawaye suka gangaro kumatuna. Na jima ina karanta wasiƙar jaki kafin na daure na taso na fito falo na ɗaura alwala na soma Sallah. Bani na tsagaita da sallar ba har sai da naji kiran sallar farko tukunna. Takun fitowar Gwadabe na jiyo. Ƙura ma ƙofar ɗakin idanu nayi. Shine ya fito yana saye da jallabiyya fara. Idanu ya ƙuramun yana sakarmun murmushi me kyau da tsayawa a rai. Take zuchiyata ta sake yin rauni ainun. Ruwan hawaye suka ɓallo daga idanuna zuwa kumatuttukana. Tsugunnowa Gwadabe yayi a gabana, ya shiga share mun hawayen nawa. Abun mamaki ruwan hawayen sam sun ƙi ƙarewa. "Iyabo na yi tunanin hawayen farin cikin ganina akan ƙafafuwana kike yi ai. Amman na fahimci akwai ciwo mai raɗaɗi dake damun ruhinki. Faɗa mun menene matsalar? Naso in kwanta dake daren jiya, ko dan kewar juna da muka yi, amman na rasa gane dalilin da yasa kika kasa bani kan ki, mu raya daren da yake cike dam da farin ciki. Daren da babu daren da zai iya tureshi a ƙwaƙwalenmu" Kuka na fashe dashi mai gunji, na rasa yanda zan yi da raina. Zugi zuchiyata take ta tayi mun. Gwadabe cike ruhina yake dam da farin cikin samun warakarka. Gefen zuchiyata kuma cike da fargabar yanda rayuwata zata koma bayan rabuwarmu. Gwadabe ya zama dole mu rabu, muddin muna son juna so na gaskiya. Mu ɗauka rabuwarmu itama ƙaddarace. Har abada sonka zaita wanzuwa a cikin rayuwata, kullum sake halittar sabo za'ayi. Ta yiwu rabuwarmu ka iya kawo ƙarshen numfashina, ko ya zama silar kamuwa da wani ciwon da zai ta cin naman jikina har sai ya kaini ga kushewa. Amman Gwadabe na sani har duniya ta naɗe ba zaka manta da gudunmawar dana ba rayuwarka ba....." Tashi nayi ina shirin shigewa uwar ɗaki domin soma shirya kayana. Gwadabe kuwa duk illahirin jikinshi rawa kawai yake yi mun. Cikin kaurin murya irin ta cikar mazantaka yace. "Iyabo..." A maimakon in tsaya sai na shige ciki da gudu na saka sakata. A jikin ƙofar na jinjina ina jawo numfashi daga cikin huhuna da ƙyar. Iyabo ki buɗe ƙofarnan dan Allah na roƙe ki kar ki sa zuchiyata ta buga." Ya faɗa hakan a mugun raunace, tsabar ɓarin da jikina yake yi ma na kasa ko da motsawa, jin za'a shiga Masallacine yasa ya fita dole, ina jiyo rufo mana ƙofar falo da yayi. Sai da na haɗa ƴan tsunmokaraina a ƙaramin akwati, na ajjiye gyalena a saman akwatin kafin na tada kabbarar sallah. A lokacin ƴan biyu sun tashi daga bacci. Ina idarwa saina gyara zama na soma azkar, ina yi ina kallon yarana. Toye yana tsakankanin ƴan biyu yana wasa dasu. Sai dariyarsu suke yi. Yara kenan su basu da matsalar komai. Iyaka su yi bacci su tashi su ci abinci. Ku sakko ku je ku yi alwala ku yi salla, na faɗa musu da yaren yarbanci. Dukkansu sai da suka rungumeni kafin na buɗe musu ƙofa suka fita. Ai sai na kife a dadduma na shiga rera wani irin kuka na tashin hankali. Inayin kukan nan ban mance da ambaton Allah ba. Jin hucin mutum nayi a gefe na, Gwadabe ne nasan babu makawa. Riƙo hannuna yayi gam, ya rarrasheni ya kasa, yayi magana wallahi ya kasa. Duk dauriya da irin shanye abu na Gwadabe yau zuchiyarshi a tsinke take. Shima hawayen yake fitarwa a gidanunshi. Mun fi minti goma a haka, yara dai ban sake jiyo ɗuriyarsu ba ma. Sai can Gwadabe yayi ajjiyar zuchiya kana yace. "Iyabo yanzu me kike so in yi, ina alƙawarin da muka ɗaukarma kawunanmu zai kwana, babu rabuwa a tsarin da muka tsaroma rayuwar gidan aurenmu...." Dakata Gwadabe, kar so ya rufe maka idanu, ka kai rayuwarka ga halaka. Wallahi zaman mu babu alkhairi, kuma ba zamu taɓa ganin haske ba. Tunda Babala ko da yaushe a cikin zubar da hawaye take. Ta yiwu bijerema iyayenmu da mu ka yi ne ya jefa mu a cikin halin da muka shisshiga a baya. Siraɗi nawa muka tsallake Gwadabe? Ka tsayar da zuchiyarka kul sona ya ruɗeka, uwa tafi gaban a tsaya ana jayayya da'ita wallahi. Dukkanmu ba zamu so yaranmu su yi mana taurin kan da mu ka yi ma namu iyayen ba, Gwadabe mun zuba taurin kai sosai da sosai. Allah ya jarabcemu da talauci sosai da sosai sakamakon fishin iyaye da muke ciki. Ka daure ka sake ni kawai in tafi" Cikin dashasshiyar murya yace. "Ko dai har yanzu da ragowar soyayyar Debisi a zuchiyarki ne Iyabo? Ni fa bazan iya rayuwa babu ke ba. Da maraici kike so yaranmu su taso ne?" Cikin jin haushi, gami da tausayinshi a haɗe na dubeshi. Nayi mishi uziri dan tabbas a cikin tsaka mai wuyar fita yake, dole nice dai zan lallaɓashi ya sauwaƙe mun. Billa babu ko sofanen son Debisi a zuchiyata. Mutumin daya gujeni sabida halittar ƙibar da Allah ya hore mun, to shin me zan yi dashi a cikin rayuwata. Ka sake ni kawai, domin cika umarnin Babala da cika alkawarin da nayi mata. Ce mata nayi a ranar daka samu lafiya ko kwana da igiyoyin aurenka bana kumawa" Mun fi awa guda muna tataɓurza tsakanina da Gwadabe. Muna cikin haka, Allah da ikonshi muka jiyo sallamar Babala a cikin falo, tana tambayar Toye ko muna ciki ne" Jijjunanmu a mace muka fita falon, ita da Baban Nazifi ne, sai Yaya Harisu. Gurfana nayi a gabansu cikin rawar baki na gaishesu, babu wanda yayi yinƙurin amsawa. "Rana bata ƙarya sai dai uwar ɗiya taji kunya. Gwadabe yau zan yi bacci harda munshari sabida wannan jikar oduduwan zata bar gidannan, igiyoyin aurenka zasu sauka a kanta. Kuma bari kaji danginta ne su kai ma Agumu ( sammu) ba kowa ba, domin ba ƙaunarka suke yi ba. Wajen malamai har biyar muka je, duk maganar ɗaya ce dai. Maza saketa ta kama gabanta yanzu_yanzu. Ko wallahi in tsine maka" Idanuna na runtse bakina, harshena suna kakkarwa kunnena na baza ina jiran kalmar saki. Kamar saukar aradu naji ya furta. "Na sake ta saki ɗaya Babala" Wani wuji_wuji naji yana dibata, take mashashshara ta saukar mun. Ajjiyar zuchiya Babala ta sauke kana tace. "Cikace mata ya zama uku ɗan albarka" Na sake ta saki biyu, in aka haɗa dana baya dana yi uku kenan." Ya faɗa muryarshi a mugun dashe kamar wanda aka shaƙe. Miƙewa nayi tsam, duk da jirin da nake gani, amman bazan iya jure shaaƙar numfashin Gwadabe ba. Uwar ɗaki na shiga, Toye da ƴan biyu suna katifa suna wasansu. Ganina yasa Toye cewa.. "Mama kinga Kahinde yana dukan Taiwo ko, bayan itace yayarshi" Sai da na zari jakata kana nace. Kahinde ka dena dukanta, yayarka ce. Kai kuma Toye ka kula sosai da maraicin ƙannenka. Zan yi wata ƴar tafiyar da bansan yaushe zan dawo ba" Duk da yaron yana da ƙarancin shekaru amman sai naga yayi jigum kamar mai tunani. Kayukansu na shafa tare da saka musu albarka, na fito daga ɗakin a sanyaye, har na kai bakin ƙofar fita na jiyo muryar Babala tana cewa. "Yaran wa kika barma, wa kike tunanin zai riƙe yaran yarbawannan? Maza koma ki kwasosu..." "A'a Babala yara kam zan rayu dasu, ni yafi dacewa in kula dasu tunda dana aurota iyayenta ita gayanta suka bani, kiyi haƙuri dan girman Allah " Gwadabe ya katseta da hanzari. Kai nasa nayi ficewata daga ɗakin. Matan gidan duk suna tsakar gida da yaran gidan, suna hangoni ko wacce ta sau abunda take yi kallo ya koma sama wai shawo ya ɗau giwa. Ni ko murtuke fuskata nayi sosai ta yanda ba wacce zata iya samun fuskar tambayata, nayi ficewata zazzaɓin dake jikina sai tsananta yake yi. Ko da na shiga Bus ɗin unguwarmu na kifa kaina a bayan kujerar dake gabanku ban ɗago ba har sai da muka iso. Duk wannan abun babu ko ɗigon hawayen daya sake zubo mun tunda kunnuwana suka saurari kalmar saki. Ko gidanmu ma bansan ya akayi na iso ba, ganina kawai nayi a ƙofar shagon Iyaa. " Ahh ahhh ahh Iyabo kini o ti sele? ( Me ke faruwa )" Iyaa ta faɗa cikin kwakwazo da kuzuzuta lamarin. Kafin in mata amsa sai ga Iyaa Kokodeen ta fito daga cikin gida, itama ganina ne yasa ta nufo ni. "Iyabo lafiya da sassafe haka harda jaka a hannunki?" Jin haka yasa Iyaa fitowa a kidime zaninta na suɓucewa. "Ahhh ahhh ya sake ta ba? Ai dama mu munsan zaki dawo, ba riƙe aure suke yi ba saki ko da yaushe, da laifi ba laifi saki. Kinga abunda muke guje miki tun ba'aje ko ina ba har ya faru. Da yarenki kika aura da kin samu kwanciyar hankali. Ai sai ki shigo mu ci gaba da zama kafin Allah ya ɓullo miki da wani. In ce dai babu wani ragowar igiyar da tai saura? Dan wallahi kin bar komawa wannan auren, an yi na farko, gana ƙarshe yayi." Duk wannan maganar cikin yare take yi, tana yi tana buga cinya tare da tafa hannaye. Jiyo muryar ta ne ya tilastama su Iyaa Beji fitowa da sauri. Suna fitowa ni kuma na shige cikin shagon Iyaa na ɓulle cikin gida abuna. Ina shiga ɗakin Iyaa na tarar da Yemisi a kwance a ƙaramin gadonmu a kwance da dukkan halamu itama a gida ta kwana. Zama nayi a ƙasa jiɓur. Zaman nawa ke da wuya sai ga su Iyaa sun shigo da duk matan gidan, suka tutsiyeni kan sai na faɗi silar mutuwar auren. Daga masu cewa gwara da aka rabu, sai masu cewa zasu je su ɗebo yaransu su girma a cikin yaren mahaifiyarsu. Ni dai suka sak sani a tsaka mai wuya. "Ki buɗe baki kiyi magana mana kin ma mutane shiru" Babu abunda ya haɗa ni dashi.mahaifiyarshi ce ta bashi umarnin ya sake ni. Igiyoyin auren sun ƙare duka" na faɗa a sanyaye. Da hanzari Yemisi ta tashi zaune zumbur kamar wacce aka tsikara. Idanu muka haɗa, dan na riga na gane manufarta na wannan zabura haka. Iyaa ce ta katse mun kallon Yemisi da nake yi dafe da kirjinta. "Sai da kika gama mishi jinya tas ba, iyayen nashi ba ke suka bari da ɗawainiyarshi ba? Kika kaɗar da kayan ɗakin ki tas komai ya ƙare a nemo lafiyarshi, to ga sakamako kin gani. Wanne irin bijere mana ne baki yi akan Gwadabe ba, amman shi gashi ya nuna miki yafi son uwarshi sama dake" Cewar Iyaa da take magana a tsawace. Iyaa Kokodeen ce tace. "Ahh ki barta haka ta ji da zafi gami da raɗaɗin mutuwar aure, daga baya ayi wacce za'ayi." Da ɗaya da ɗaya suka watse ɗakin ya rage daga Iyaa sai ni da Yemisi. Da ƙyar Yemisi ta amsa gaisuwata har tana hararata. Ni abunda yake damuna shine a gabana da ta kwantar da hankalinta ma ƙila wannan itace gamuwata da'ita ta ƙarshe daga ita har mijinta. Dan a wannan karon garin Kano ta yi mun zafi ainun, na fi son in je rugar mahaifiyata in zauna a cikin danginta da ƙannena nima. Ina cikin zancen zuchi sai ga sallamar Debisi ya shigo. Irin kallon daya watso mun da dukkan halamu Iyaa ta labarta mishi abinda ya faru dani. Kaina a ƙasa na gaisheshi cike da ladabi. "Lafiya lau Iyabo. Sai kuma naji mummunan labari marar daɗin sauraro?" Ɗan murmushi kawai nayi kaina a ƙasa. "To Allah yasa hakan shine a'ala gareku baki ɗaya. Allah ya fito muku da waɗanda za su yi dai dai da rayuwarku. Kar ki saka damuwa a ranki. Shi aure rai gareshi nasan kin sani" Duk wannan maganar da yayi yana tsaye a kaina yake yi. Shigowar Burodami kokodeen, da Anty Mulka, da iyaa, da iyaa Debisi, da duk masu ruwa da tsaki na gidanmu ne yasa Burodami Debisi ya nemi waje ya zauna. Alfa Kulle shine ya shigo a ƙarshe, Wa yake ga mahaifina, ƙani ga Iyaa Debisi cikinsu ɗaya. Kuma ya kasance shine mai ƙarfin faɗe aji a family kasancewar shi kaɗai ne namiji da yai ragowa. Gidanshi yana jikin namu gidan. Amman iyalinshi suna Ibadan da zama, sai dai duk shekara yana kai musu ziyara. Burodami kokodeen ne ya buɗe taron da adda'a kafin Alfa Kulle ya tambayeni cikin yaren yarbanci. "Meye silar rabuwarki da mai gidanki?" Murya na rawa na labarta mishi a taƙaice, sai Iyaa tayi carab tace. "Dama tun auren a difane fa take a gidan auren. Dangin miji kullum cikin ƙyamatarta suke suna aibanta mata yarenmu. Buradomi Kulle meye kai baka zaunar da yarinyar nan ka faɗa mata ba, ba ƙafa tasa tashure ba, sabida ganin ba mu muka tsugunna muka haifeta ba, ƙasa ta rufe ma Toye idanu. Cikinmu nan babu mai son wannan auren " Alfa Kulle yace. "Ta faru ai ta ƙare. Ba shikenan ba auren ya ƙare kan kat ba. Sai. Ki zauna zuwa lokacin da Allah zai ɓullo miki da wani mijin. Inason in koma Rugar mahaifiyata can inda kowanta yake. Dan Allah kar ku hanani wallahi bazan iya zaman Kano ba" Ina jiyo ajjiyar zuchiya da Yemisi ta sauke mai ƙarfi. Iyaa kuma ta dire akan ban fa isa in bar hannunta ba. Sai da kowa dake wajen ya sa baki kafin ta amince sai zubar da hawaye take yi. Burodami Debisi kuwa ya kasa cewa komai. Zahiri bai ji daɗin amince mun da kowa yayi akan komawata ruga ba. "Zuwa yaushe kike son tafiya Iyabo?" Burodami kokodeen ya tambaya. A sanyaye nace. Zuwa gobe in Allah ya kaimu" A haka dai taron ya watse, duk yanda Burodami Debisi yaso keɓancewa dani Matarshi ta hana shi wannan ƙofar. MRS BUKHARI 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI LAMBA TA SHA ƊAYA (11) *ASSALAMU ALAIKUM MASOYAN IYABO MUNA MIƘA SAƘON GAISUWARMU A GAREKU. IYABO TACE IN SANAR DAKU TANA GODIYA DA KUKA TAYA TA JIN ZAFIN RABUWARTA DA GWADABE. TANA MIƘA ƊUMBUN GAISUWA GAREKU* *(Na sha ƙorafi akan in yi haƙuri inyi har asabar da lahadi. To duba da irin son da kuke nuna ma labarin ƙorafinku ya karɓu a yanzu. Amman da zaran free page ya ƙare zaku dinga samun posting ne daga monday zuwa alhamis kaɗai, juma'a asabar lahadi na hutune. Kuyi mun afuwa kunsan bana wasa da yin posting ina da lalurar idanune shi yasa. Amman zaku samo readmore masu yawa in sha Allah nagode)* Duk yanda Burodami Debisi yaso ni da shi mu samu keɓewa Yemisi ta kulle wannan ƙofar a tsakaninmu. Ta cikin idanunshi nake iya karanto labaran dake cikin zuchiyarshi. A haka na wuni cur a waje ɗaya tamkar mutum mutumi. Maƙotanmu da ƴan uwanmu yarbawa su kai ta shigowa jajanta ma Iyaa. Da ƙyar cikin tursasawa da lallami Burodami Debisi yasa na sa lomar abinci a bakina. Har zuwa wannan lokacin hawaye bai zubo mun ba fa, face ruhina dake gasuwa, haƙiƙa kuka rahamane. Sai dab magriba Burodami Debisi ya shigo hannunshi riƙe da baƙar leda shaƙe da yankakkun kayan marmari ya miƙo mun. Harara matarshi ta watsa mana ta dubemu daga sama har kasa ta buga tsaki. Hannu nasa na amshi ledar nayi godiya ciki_ciki, dan wallahi ko magana akayi mun sai in ji kamar in sa hannu a ka inta kwarmata ihu. Ga mita da Iyaa take ta faman yi da kutuntumama Gwadabe da Babala ashariya. Dan da ƙyar Alfa Kulle ya hanata wai ita sai taje ta ɗebo yara ta dawo dasu. Ni kuma wallahi a wannan lokacin har yaran bana son gani, da duk abinda ya danganci Gwadabe. Iyaa ce ta shigo tai ta ma Yemisi faɗa ita da Burodami ashe saɓani suka samu har ta kai da duk haƙurinshi da kau da kanshi sai da ya ɗaga hannu ya mareta. Ita kuma tana taƙamar soja ce ita shine ta rama, rikicin daya tilasta mata baro gida a daren jiya. Nasiha tayi musu sosai, ya ɗauki matarshi suka koma gida. Fitarsu ke da wuya sai ga uwani da Hajiyarta sun yi sallama idar da sallana kenan ban tashi akan sallayar ba ma, ina jan carbi na amsa sallamarsu. "Hajiya kune da magriba haka a tafe, lamarin Iyabo ya tasoki ko?" Cewar iyaa dake gyara zamanta. Hajiya ta kalleni cikin tausayi tace. "Yanzu sai da aka sako yarinyarnan Toyosi duk irin faɗi tashin da tasha, amman dangin mijinnan nata sai da suka ɗauketa akan yaranta?, jiya Tabalbalin take faɗamun samuwar lafiyar mijin fa." Baki Iyaa ta taɓe tace. "Ai tsuntsun da yaja ruwa shi ruwa kan duka. Ni Hajiya ina murna da mutuwar aurennan, domin in banda wahala babu abunda take sha a wannan gida. Sai da ta game mishi jinya ta sai da komai nata ɗakinta daga robobi sai tukwane fa, shine zai sako mana ita. Ko da yake kiyi haƙuri Hajiya ku Hausawa baku fiye riƙe aure ba" Gaggaisawa mu ka yi, Uwani ta matso inda nake, su Iyaa ma suna hirarsu ta manya. "Yanzu a wanne hali shi Gwadaben yake sai Allah. Nayi imani duk inda yake cike yake da tashin hankali babu mamaki in akace yana gadon asibiti ma. Amman Iyabo me yasa kika baro su Toye? Kinsan fa wuya zasu sha ƙila ma a mayar dasu ƙauye kinga shikenan an kashe musu rayuwa" Inata ƙoƙarin ganin ƙwalla ta zubo a idanuna amman ina, abu yaci tura, idona ya soye. Sai da na sauke ajjiyar zuchiya nace. Gara su yi zamansu a dangin mahaifinsu zai fi. Wuya bata kisa Uwani da wuya na kisa mu yaran yarbawa da tun muna ƙanana zamu dinga mutuwa, ke kinsan irin gwale_gwalen da muka sha. Gobe asubar fari garin zan bari, kinga in na tafi bazan sake waiwayo garin Kano ba, na barta har abada. Kinga zanyi irin tafiyarnan ai bai dace in tafi da yaran mutane ba. In Gwadabe ya ga yaran a kusa dashi a ƙalla zai ji sanyi" Na ƙarashe maganar a raunace. Ƙirji Uwani ta dafe tace. "Ni Uwani Tabalbalin ina zaki koma to iyabo?" Can Adamawa wajen mahaifiyata nake son in je in rayu cikin ƙannena, domin in samu kafaɗar da zan jingina in yi kuka. Ita kanta Dada akwai wata boyayyar damuwa wacce take cin ruhinta ainun, tun tasowata da wannan ƙuncin nake ganinta. Baki ga yanda take ta ramewa ba Uwani" Uwani dai bata so

Chapter 10 of 16