Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na koma ciki. Anan naga kayan abincin da su Sakina suka kawo mana, garin tuwon masara, kuka daddawa, busassun kayan miya, albasa, shinkafar hausa, da gyaɗar miya harma da man ƙuli jarka guda, da bushasshen kifi" Godiya nayi sosai gami da yaba ƙwazon Bara'u, ya kuma yi dace da macen da bata hanashi yin aikhairin sai ma taimakonshi da ƙara ƙarfafashi da take yi." MRS BUKHARI https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE. GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI Lamba ta shida Shiryawa nayi cikin doguwar rigar Atampa, ɗaya daga cikin kayan da Alaja ta bani, atampar mai kyauce kuma tana da tsada da gani. Hijabi mai roba_roba na saka kalar atamfar sak. Na ɗauki Taiwo na goya, Kahinde kuma Sakina ta goya shi. Uwani zamu je asibitin Murtala Babala tana can bata da lafiya gara in je kar in yi wani babban laifin. "To sai kun dawo, nima ƙoƙari nake in gama gyare miki uwar ɗakin yadda ya kamata. Gobe za'a zazzo da yawa. A nan ma ni zan kwana gobe na koma gida Hafizu baya nan ya tafi Lahadin makoli mahaifinshi bashi da lafiya. Yaran kuma suna gidanmu " nace da'ita. To Shikenan ma, sai mun dawo to. Sakina muje." Shigarmu ward ɗin mata ke da wuya na hangi su Yaya Haula dukkansu a zazzaune a tabarma da mazajen nasu. Kallona suka shiga yi da suka hangoni. Sannunku Yaya Haula ya mai jikin?" Sai da ta taɓe bakinta tace. "Jiki da sauƙi" Gaishe da su Sukairaju nayi tare da yi musu ya mai jikin. Yaya Harisu cikin murtukewa yace. "Da'u ka kai su wajen Babala su gaisheta" Da'u yayi gaba muka bi bayanshi har bakin gadon Babala, tana zaune ta jingina bayanta da matashin filo. Yaya Halima kuma tana tsaye tana haɗa mata tea. Muna isowa Babala ta kawar da kanta gefe. Sannu da jiki Babala, ya ƙarfin jikin? Na furta muryata har tana rawa. "Da sauƙi" Ta bani amsa ciki_ciki. Yaya Halima kuwa nunawa tayi bata ma san Allah yayi ruwan tsaron mu ba. Gaisheta nayi tare da yi mata ya mai jiki. Babu yabo babu fallasa dai ta amsa mun. Da Sakina ne dai su kai fara'a. Sunto Taiwo nayi na miƙa ma Babala ita, tasa hannu ta amsheta, Sakina ta ƙara matsa da Kahinde. "Ba shakka gashi nan yara sun ɗebo ƙoƙon asali. Kamanninsu sak da dangin uwarsu dai kamar yadda Toye yabi sunanshi." Iyakar abinda tace kenan ta miƙo yaran. Raina ya sosu ainun ko Allah ya rayasu bata ce ba, balle ta yi musu adda'a a matsayinta na kakarsu. Yaya Halima kuwa ko kallo yaran basu isheta ba. Bayan na gama goyo ne ta kalleni sak tace. "Na ji saƙonki na gode da har kike tunanin mahaifinki ya fi mahaifin Gwadabe daraja a wajenshi. Burinki ya cika yaranki uku babu wanda Gwadabe yayi ma takwara a danginshi. Har ni da na ɗau jimirin renon cikinshi na wata goma ya kasa saka sunana ma ƴarshi. Taiwo da Kahinde ɗin dai da kika sanar, shima shi ya jaddada a matsayin sunan yaranshi. Ko da yake dama tuni kun gama tsarin komai tun ma yaran suna ciki." Baki na buɗe inason in ba Babala haƙuri amman sai ɗaga mun hannu tayi. "Kije kawai, bana son ganinki, bana kuma ƙaunar zamanki da Gwadabe, zuchiyata ba zata taɓa samun salama ba madamar kina amsa sunan matar Gwadabe abadan" Cikin razani da tashin hankali mai girma na shiga. Lokaci guda Gwadabe da aurenshi ya fice mun a raina kwata_kwata. Na yi alkawarin inayon arba'in zan tursasama Gwadabe sakina ko dan ya ga haske a rayuwarshi, domin na fahimci har abada Babala ba zata taɓa ƙaunata ni da abinda na haifa ba, wannan shi ake kira NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE. Ko Gwadabe bai sake ni ba, ni kuma zan fice a rayuwarshi.Wata wawuyar ajjiyar zuchiya na sauke a hankali na soma tafiya dan barin ɗakin. In sha Allah ƙarshen aurena da Gwadabe yazo, ko da kuwa soyayyarshi ita zata zam silar numfashina. Fitowa daga ɗakin ke da wuya, na jiyo Harisu yana zagina tare da ƙorafi kan sunayen yara da aka saka. Sai ji nayi na muzanta ko fita ma bazan iyaba. A tsaye Sakina ta iskeni. "Ki ƙara haƙuri dai Iyabo damo sarkin haƙuri. Mu je kinji" Da taimakon Sakina na iya fitowa, amman har muka isa guda ban iya furta ko kalmar A ba, sai ajjiyar zuchiya kawai nake saukewa. In sa abinci a cikina wallahi na kasa sabida tsabar damuwa. Sakina da Uwani sai aukin rarrashina suke yi, amman na kasa ce musu komai. Ni tunanina ya na ga samarwa Gwadabe sauƙi dan fishin iyaye masifa ne, nayi imani fishin da Babala take kwana ta tashi dashi akan Gwadabe shi ya hana shi yin arziki. Kullum cikin faɗi tashi yake, ta hana kowa ya taimaka mishi. Yaya Hambali shago gareshi babba a kasuwa da yake siyar da dabino da gyaɗa, buhu_buhu yake siyarwa yana da yaran shago sosai. Amman Babala ta hana shi ya ɗauki Gwadabe ko da a matsayin yaron shago. Yaya Harisu shi kuma mota yake ja zuwa ƙauyuka a haka ya sai wasu motocin guda biyu ya bayar anayi mishi hayarsu. Sukairaju kifi bushasshe yake saidawa a kasuwa, shine zuwa argungi, shine zuwa maiduguri, da Yawuri saro katan katan na kifi, kuɗi yake samu sosai da sosai Ɗan fodiyo kuma Kafinta ne kuma ogan kanshi ne. Da'u shi kuma Yaya Hambali ne ya buɗe mishi shagon sai da kayan masarufi dangin shinkafar hausa, gyadar miya, masara, wake. Duk wannan matakan sun haushine da taimakon Allah da taimako da jajircewar Yaya Hambali, domin Yaya Hambali guda ne harda ɓari ga ƴan uwanshi, yana musu tsananin so. Ina lokaci yayi da zan fita fit a cikin wannan ahalin, nima in je in yi rayuwa mai kyau. In ba haka ba bala'o'e iri_iri zasu iya saukar mana a sakamakon fishin da Babala take yi da Gwadabe. Abubbuwa nawa Gwadabe ya kama suka lalace, yayi sana'o'e a ƙalla iri huɗu karen mota shine na biyar. Amma tafiyar bata wani nisa sai abun ya lalace, ko mai gidanshi ya koreshi, ko a yi mai wani ƙazafi, ko na sata ko na ƙashin tsiya." "Iyabo ga tea ki daure ki sha, wala Allah ruwan nono yazo miki. Kinga Taiwo da Kahinde kuka suke yi baki ma sani ba. Kar ki kuskura waccan munafukar ta falo ta fahimci kina cikin matsala, yanzu ta shigo. Surukar taki ma an sallamota tana ɗakin umman Nazifi." Hannu nasa na amshi tean hannun Uwani na sha, dan jikina har rawa yake yi tsabaragen yinwar da nake ji. Sakina ta miƙo mun Taiwo da take ta canyara ihu kamar wacce ake zare ma rai. Ga man zaitun da audiga Sakina bani in goge kan mamana in gwada musu ko zasu jawo ruwan yazo" Miƙomun Sakina tayi, na bi kan mamana na goge da man zaitun tas na ba yaran suka soma ja. Cikin ƙudurar Allah sai ruwan nono ya soma zuwa. Nan kuka yaƙare aka shiga tsotseni. A wannan daren bana ce na yi bacci mai kyau ba. Misalin ukun dare sai ga Gwadabe, a lokacin duk su Uwani suna kan gado sun yi bacci ya shigo. Ganinsu ne yasa ya koma falo, ni kuma na ɗebo jariran na biyo bayanshi, yana zaune a kan kujera. Laila kuma tana kwance tana bacci ta yi baje_baje cinyoyinta duk a waje. Miƙa mishi yaranshi nayi yasa hannu ya amshesu yana fara'a. "Maman biyu barka da sauka, ina fatan babu inda yake miki ciwo ko?" Babu, sannu da dawowa" Iyakar abunda na faɗa kenan shima ciki_ciki. Idanunshi yana kan yaranshi yace. "Ya dai akwai wani abu dake damunki ne, ko an yi wani abunne? Iyabo a yanzu ya kamata ace kin saba da komai. Ki toshe kunnuwanki dan abubbuwa da yawa zasu faru kafin ayi suna kema kuma kin sani. Yanzu haka nafi awa ɗaya da shigowa Babala naketa ba haƙuri tayi fishi wai ban mata takwaraba ita da mahaifinmu. Nace mata zan sake yin sabuwar huɗuba in hakan zai bata farin ciki. Amman taƙi fur tace mun in na sake ma yaran suna bata yafe ba, wallahi kar kiji......." Ɗan yatsana nasa a kan laɓɓana nayi mishi halama da yayi shiru, nuni nayi mishi da Laila dake kwance. Ai ba shiri ya haɗeye maganarshi. Mu ka ɗan taɓa hirarmu kaɗan, ya miƙo mun ledoji manya biyu, mu kai sallama dashi zai kwana a ɗakin zaure, ɗakin su Nazifi, Bara'u ma yana ɗakin. Da tunane_tunane na ƙarashe daren nawa, sai jefin asuba bacci mai nauyi sosai ya ɗebeni bani na farka ba sai taran safe lokacin ƴan uwana sun ƙaraso, har an yima ƴan biyu wanka sun fito ras dasu, dan Gwadabe ya kawo kayan jariri kala biyar biyar, sai nawa na fitar suna kala biyu, da takalmi da mayafi, sai sarƙa, dasu nabkin, da paints na yara, da man shafawa, da sabulu. Ɗayar ledar kuma kayan abinci ne a ciki. Ina farkawa Yemisi tace. " Lo we. ( Je kiyi wanka)" O dara ( To) Kawai na iya ce mata na ɗauki zani na lulluɓe jikina dashi na fita. Ina fitowa maƙotanmu suka soma shigowa barka. Matan gida kuwa babu wacce ta leƙo, sai aikace_aikacensu suke yi kawai. Bayan jama'a sun ragu sai na fita zuwa ɗakin Yaya Haula dan gaishe da Babala. A falon na tarar da Gwadabe da Bara'u gurfane a gabanta. Ɗan fodiyo yana gefenta yana ɓallo mata magungunanta. Gaisheta nayi da jiki, da ƙyar ta kada baki ta amsa mun. Ɗan fodiyo na gaishar kafin na gaishe da Bara'u da Gwadabe. Ni dai anan na tafi na barsu. Da tuwon masara miyar kuka da bushasshen kifi Uwani ta tare ni, harda tea mai madara, ina bacci Gwadabe ya shigo da kayan tea. Anty Mulka ce ta shigo ciki tace. "Wai Iyabo su dangiin mijinki basa zuwa taya aikine? Tun sassafe muke ta aiki a tsakar gidanku, amman babu wacce ta taya mu komai. Mun fitar miki da randunanki tsakar gida, wata bushasshiyar mace tazo tana faɗar maganganun banza, har tana dangantamu da ƙazanta. Mu fa ba zamu ɗauki irin wulaƙancin da sukai mana lokacin sunan Toye ba. Bga won ( ki ja musu kunne) sai in zaune mace ni yadda nake da ƙibarnan" Nan Bose da Kauliya suka ɗauka suma sai yare suke ta yi mun. Uwani ce tai ta basu haƙuri ni kam kuka na saka musu kawai. Ganin kukan nawa ne yasa su kai haƙuri. Tun ganin da naima Gwadabe a falon Yaya Haula ban kuma saka shi a idanuna ba. Da rana Iyaa Debisi ta aiko mun da farfesun kan akuya cikin kwano shi naci da rana, su kuma suka dafa taliya. Uwani na kira nai mata raɗar ta zuba ma Babala ishasshe a kai mata. Amman ko da aka kai sai dawo dashi Uwani tayi Babala tace bata cin abincin Yarbawa, da akayi tuwon dare ma na kuma sa Uwani ta kai mata, amman bata karɓa ba. Har magriba babu Gwadabe ba dalilinshi sai wajajen taran dare muna zaune dani da Sakina da Uwani suka shigo shi da Bara'u da ƴar baƙar ledarsu a hannu. Idanu ya zuba mun tare da lumshe su. Na fahimci akwai gajiya da tarin damuwa dake damun Gwadabe. Ko wanne halin zai shiga in na barshi oho, nasan Gwadabe yana sona so mai tsanini, duk da na fishi zurfi a soyayyar da nake yi mishi, jin Gwadabe nake tamkar shine mahaɗin numfashin da nake yi dan in rayu. Amman dole in fita daga rayuwarshi shima ya samu ya nutsa. "Ayi mun afuwa uwar biyu. Abubbuwanne su ka haɗu suka caɓe mun. Mun fita da Bara'u fafutukar yanda za'a samu na abincin suna da abun haƙiƙa a fita kunyar ƴan uwa." Murmushi nayi mishi nace. Babu komai, sannunku da dawowa ina wuninku?" A tare suka amsa duk aka gaggaisa baki ɗaya. Sakina ta tafi kawo musu tuwo. "Tamu ya kirani da magriba madam ɗinshi tana son tayi miki barka, yace ma ana gobe suna zata zo. Bari in kira ku gaisa" Kiran layin Tamu yayi bayan ya ɗaga wayar sai ya miƙo mun muka gaisa tare da yi mun barka. Daga ƙarshe ya haɗa ni da Ayashe itama tayi mun barka tare da faɗin. "Kayan fitar sunan ƴan biyu dana Maman ƴan biyu yana wuyana in sha Allah. Ana gobe suna zan tawo in zo ayi komai dani." Dariya nayi nace. Muna godiya Ayashe Allah dai ya bar so da ƙauna, mun gode ƙwarai" Mu kai sallama na miƙa ma Gwadabe, nan Tamu yake sanar mishi ya ɗauki nauyin rago ɗaya. Mun yi farin ciki matuƙa gaya. Sun jima a falo muna hirarmu gwanin ban sha'awa daga ƙarshe su kai mana sallama, suna fita muma muka tafi kwanciya. Haka dai ranaku sukaita tafiya, duk da kauce ma rikici da dangina suke yi sai da akayi rikici a tsakanin Anty Mulka da Yaya Haula. Wai an jiƙa tsakar gida da ruwan wanki, shine fa Yaya Haula tai ta zage_zage tun su Anty Mulka basu tanka ba har suka tanka. Akaita gwabza rikici har sai da manyan unguwa suka shigo akaita basu baki tukunna. Ni dai ranar naci kuka sosai sabida Babala har ɗaki ta shigo ta ƙaremun tanadi tas. Har ta gama babu wanda ya tanka mata, sai da tayi mai isarta ta fita. Ana gobe suna da yamma sai ga su Gwadabe da raguna tiƙa _tiƙa guda biyu sun ɗaure, da kayan cefanen suna niƙi_niƙi. Daf magriba Ayashe ta ƙaraso da yaranta biyu. Gaskiya ta gwangwajeni da ƴan biyu sosai. Shadda ta ɗinka mun taji aiki sosai, harda mayafi da takalm. Taiwo kuma bulawus mai tsada ta siyo mata irin mai takalmi da abun kai na yara, Kahinde kuma riga da wandon jins ta kawo mishi. Godiya na dinga yi mata. A ranar Bose, da Kauliya, da Anty Mulka a nan suka kwana. Washe gari asubar fari aka shiga aikin abinci. Da asubar Burodami Debisi ya kawo mana nama cikin leda mai zane, Burodami kokodeen kuma ya turo masu rumfa suka kafa runfuna biyu da kujeru. Yasa yara suka shigo da koka kola kireti huɗu. Ƴan uwa masu daɗi, ƴan uwa abun wuya wannan ya kawo nashi wannan ya kawo nashi sai kaga ashiri ya rufu ruf, a gaskiya ba yabon kaiba muna da hadin kai sosai. A ƙofar gida suka kafa murhun girki, masu Amala nayi, masu yin jallof nayi, ga nama jingin anata yankawa ana soyawa, wasu suna gyaran kayan miya. Tun asussuba ni da ƴan biyu muka yi wanka, ina ɗaki a zaune Bose tanai mun kwalliya ta kece raini. Ba yabon kai ba mu yarbawa mun iya kwalliya da sanin darajar kaya masu tsada. Domin mazan yarenmu basu san siyama mace ƙaramin zani ba, ko ashobi zamu fitar muna zaɓar mai tsada mu fitar. Domin matan yarbawa har adashe akeyi na musamman domin kece raini, ko wacce mace tana son asan mijinta na kulawa da'ita. Ko ni duk talaucinmu tun cikina na wata ɗaya nake zubin dashi a shagon Iyaa Beji me shagon atampa da lace ta bakin layinmu. Da kaɗan_kaɗan na tara kuɗin les ɗaya, sai naci gaba da tarawa, in ƴan uwana sun kawo mun ziyara sun ban kuɗi a ciki zan zari wani abu in zuba dashi, da haka na sake tara kuɗin leshi na karɓi lace biyu iri ɗaya na bayar da ɗinkin nawa a wajen Yemi, na gwadabe da Toye na bayar a shagon ɗinkin maza. Lace ɗinne a jikina tun sassafe nasa aka miƙama Gwadabe nashi shi da Toye dan tare suke kwana a ɗakin zaure. Sarƙa Bose ta saka mun a wuyana. "Wannan karon mai gidanki yayi ƙoƙari ba kamar lokacin haihuwar Toye ba. wannan lace ɗin da sarƙar babu laifi ba sui arha da yawa ba, ba sui tsada can can ba. Ga raguna manya_manya" Harara na doka mata, ta kwashe da Dariya ta doki kafaɗata. Dole nima na murmusa, dan Bose a lokacin da nake cikin matsi a gida sakamakon soyayya da Gwadabe, a wajenta kawai nake samun sauki. Yaya Haula ce ta shigo ɗakin da sallama tana wani gatsine, ta sha kwalliyarta da wata shadda mai maiƙo tayi kyau sosai, dan Baban Nazifi yana ƙoƙarin sosai a kan iyalanshi, bama su kaɗai ba harda iyalan ƙannenshi. Turus tayi data ganni na fito shar dani kamar ba ni ba, ba wata kwalliya bace a fuskar tawa ba, hoda ce sai jan baki, sai kwalli da Bose ta ziraramun, ko ja gira banyi ba sakamakon akwai gashi sosai a girata. Ɗan kunne da sarƙar da Ayashe ta tawo mun da'ita ta ba da gudunmawa sosai wajen ƙawata kwalliyar tawa, sannan dinkin buba ɗinkine dake fito da kyawun ko wacce irin mace, musamman masu jiki duma_duma irinmu, kwalliya da ado na fito da masu ƙiba ainun. "Iyabo gashi kayan yarinya na ɓangaren dangin miji." Ta dangwararmun da leda mai zane_zane. Kafin in yo godiya ta ƙara watso mun mugun kallo tace. "Na ga anata aiki babu wacce ta buƙaci ganinmu a wajen. Amman ki sani duk tsiya dangin uba sun fi power fiye da dangin uwa. Amman ke kinfi son duk abunki ƴan uwanki su tsaya a wajen, dan ku aikinku kenan ƙabilanci, tunda kika haihu ake yare a gidannan dan masifa." Murmushi nayi dan har ga Allah bana son cusa ma zuchiyata baƙin ciki a irin wannan rana mai albarka. Ai bansan basu neme ku ba Yaya Haula tunda ni bana wajen." Jijjiga kai tayi tace "Ai ba zaki sani ba tunda dai Gwadabe shi ya baki ƙofar raina danginshi. Babala tana gidannan a kasa zuwa a kiramu mu kama aiki a matsayinmu na dangin miji, ai shikenan hausawa na cewa sai bango ya tsage ƙadangare ke samun mafaka." Tana gama faɗar haka ta fice fuu kamar kububuwa. Ajjiyar zuchiya kawai na sauke na jawo ledar data dire mun. Riga ce ƴar ɗari uku uku guda biyu ta mace da na namiji, sai sabulu sanda biyu da omo mudu ɗaya shikenan abinda ke ciki. Bose ta riƙe baki tace. "Wannan kayan shine kayan dangin miji ke da kika haifa musu ƴan biyu? Lallai Anty Iyabo dangin mijinki basa ƙaunarki.. Ya isheni Bose ki barni in ji da abinda ke damuna dan Allah." Ina faɗar haka na miƙe zuwa uwar ɗaki, na tarar da Ayashe tana shirya Taiwo da Kahinde sun fito sun yi kyau sosai. Dubana tayi tana dariya tace. "Kai masha Allah mai jego kin fito shar dake kamar ba ke ba." Dariya mu ka yi dukkanmu. Simbi ce ta shigo niƙi_niƙi da buhu ta dire a gabana, Sai ga Taufiq shi da Lekan suma sun shigo da ghana most go. Yaran Burodami kokodeen ne Taufiq, Lekan kuma yaron Iyaa Kokodeen ne, Simbi shekararta goma sha takwas haka, wannan shekarar ta game sakandare ɗinta. Taufiq kuma yarone shekararshi sha biyu, yana jss 2. Lekan kuwa saurayine Buhun sobeniya ne na robobi, da kofuna, mafificin roba, moɗa da sauran kayayyakin roba mai manne da sikitar dake ɗauke da sunan Taiwo da Kahinde. Wanda ya ɗauki nauyin yi naga an rubuta Burodami Debisi Adebayo. Ghana most go ɗin kuma shaƙe take dam da kayan jinjiraye da atampopi , omo, sabulu da su nabkin. Hawayene ya gangaro a kumatuna mahaifiyata na tuno tana can ƙungurmin daji, babu waata hanyar da za'a iya sanar mata na haihu balle itama tazo ayi komai a gabanta. Duk da bani da maraicin uwa sam balle uba, Iyaa Debisi itace makwafin uwa a gareni, Burodami Debisi kuma shi ya zame mun makwafin uba. Shi yaita ɗawainiya da rayuwata har tasowata yanzu ma da nake gidan mijina bai fasa turo mun abun alkhairi ba, kuma yana kawo mun ziyara lokaci zuwa lokaci, duk da matarshi na tsananin tsantsar kishin kulawar da mijinta yake bani, sabida alaƙar data tafa gibtawa a tsakaninmu na soyayyar da Allah bai nufi shine uban ƴaƴana ba. Kafin ƙarfe takwas na safe tuni an gama girki tsab an zuzzuba a kuloli, An yanka raguna harma an gyara kayan ciki, kayan cikin dabba ɗaya nace a miƙa ma su Babala su soya da kansu kar suce an musu coge. Abinci ma ni da kaina na tsaya saida aka basu duk abinda ya dace, har sobeniyarsu nasa an cire musu Anty Mulka da Uwani suka kai musu har ɗakin Yaya Haula. Takwas da rabi Alfa Abdulsallam Abdulganiyu ya iso, ƙofar gida, zuwa lokacin ƴan uwa maza da mata duk suna waje a cikin rumfa a zazzaune. Gwadabe ne ya ratso cikin mata yana saye da leshi da hular ashoke, Kahinde ya riƙe Ni kuma ina riƙe da Taiwo, Ayashe da Sakina ne suka mara mana baya har zuwa ƙogar gida inda Alfa Abdulsallam Abdulganiyu ya soma wa'azi. A gabanshi muka gurfana, ya soma ragargazo ma ƴan biyu adda'a tare da roƙa musu alkhairan duniya dana lahira, tare da samun nasara gami da rayuwa mai tsayi, mai albarka. Duk wannan cikin yaren yarbanci yake yi, yanayi da waƙa dukkanmu muna amsawa da. Ameen" Muma cikin salon rerawa kamar masu waƙa. Yaran muka miƙa mishi ya shafa kansu yai musu adda'a ya miƙo mana su. Sannan ni yai mun adda'ar samun lafiyar shayar dasu cikin lafiya, Gwadabe kuma yayi mishi adda'ar samun tagomashi ta yanda zai ciyar dani lafiyayyen abincin da zan raini yarana cikin ƙoshin lafiya. Iyaa Debisi ta fito itama tayi nata addu'o'in, aka miƙa ma Babala abun magana, "Allah ya raya su da imani" Kawai tace shima sabida idon mutanene da taga sun yi yawa a kanta. Iyaa Kokodeen itama ta yi nata, su Burodami kokodeen da Burodami Debisi duk dai kowa yayi nashi.Daga nan kuma akayi adda'a kowa ya shafa. Sai Bose ta ɗauki kwano ta dinga bin mutane ɗaya bayan ɗaya sunata zuba kuɗi, mu kuma muka koma cikin jama'ar suna. Dangina rankatakab ɗinsu ankon atampa mai ruwan kunun kanwa ce a jikinsu maza da matansu. Abinci aka soma rabawa masu kalangu kuma suka amshe fagen. Haka dai akaci gaba da gudanar da shagalin suna bamu muka tashi ba sai ƙarfe biyun rana. Daga nan kowa ya watse, duk wani gudunmawa a wajen aka bani, sai da muka cika bahun biyu da kaya da atampopi, kuɗi kuwa na same shi sosai ƴan biyu sun yi goshi sosai. Bayan mun koma gida sai na sake wanka na kwalliye da shaddar da Ayashe ta bani na fito shar dani. Sai lokacin na samu nutsuwa naci abinci na ba ƴan biyu nasu abincin. Kafin la'asar har an gama soye naman suna tas Anty Mulka ta ƙuƙƙullama duk waɗanda suka dace, ni dai da Gwadabe cikin ƙaramar samira kawai muka tsira dashi a matsayin rabonmu. Ragon ɗaya sukutum aka ba su Babala, ɗayan kuma ni da ƴan uwana duk muka rataya akai, wanda na samun ma Babala ta aiko laraba wai in ƙara mata nama ƙawayenta na Takai basu samu ba. Dan haushi samirar duka na miƙa mata na yi kwanciyata dan in ɗan huta. Washe gari Ayashe ta ɗau hanyar garinsu, da rana su Sakina suma suka wuce. Uwani dasu Bose ne suka gyara mun ko'ina su kai mun girkin dare kafin magriba duk suka watse ɗakin daga ni sai ƴaƴana misalin taran dare sai ga Gwadabe ya shigo furkarshi ɗauke da fara'a, nima murmushi na sakar mishi. MRS BUKHARI 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu NAMA YA DAHU.... ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI INA MIƘA SAƘON GAISUWATA A GAREKU. KHADIJA MAIDOKI MRS BASH MAMANMU (HAJARA ALIYU) MAMAN SAFWAN ANTY YABI YUNUSA JIBRIN ( AZARE) MAMAN ANNUR KHADIJAN MAKAWA UMMU NABEEHA MAMAN YASEER SISTER FARIDA ( ƘAWAR UMMU NABEEHA) MAMAN MUHSEEN RUƘAYYA YAWURI UMMU AFFAN ABUJA UMMU AFFAN SADFAT RAMLEX MMN LAMIDO MAMAN ABDULRAHMAN INNAR BASMA ANTY ZEE MUSA A.A NAFAƊA MAMAN INTEESAR KUNA DA YAWAN DA BAN ISA JEROKU A PEJI ƊAYA BA, A BOYONI BASHI DUK ZAN ZANA SUNAYENKU, INA ALFAHARI DA MASOYANA NA FAƊIN DUNIYA. ( JIYA WATA BEYERABIYA TA KIRANI A WAYA TAKE CEWA DANI TANA BIBIYAR LITTAFINA, KUMA TANA JIN DAƊINSHI SOSAI. SOYAYYAR GWADABE DA IYABO TA BURGETA, KUMA

Chapter 6 of 16