Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gabansu, sai su taso da ganin girmanshi ainun. (Wannan kuskuren namu ne iyaye. Mu guji yin abinda bai dace ba a gaban yaranmu. Shi fa zumunci da haɗin kan haula babu abinda ya kai shi daɗi) Gwadabe yana tafe yana girgiza kai, ciwo yake ji a zuchiyarshi sosai ta yanda zumuncin gidansu ya lalace. A falon Babala ya tarar da kowa da kowa. Babala da nata tawagar haka ma ƙannenta su Goggo Iyatu Baba Magaji yana tsakiya. "Gwadabe kaine tafe da yamma haka?" Cewar Baba magaji. "Nine Baba Magaji. Mun same ku lafiya?" Gwadabe ya bi kowa da gaisuwa Babala da Goggo Iyatu fur su ka ƙi amsawa. Baba Magaji yace. "Zauna nan." Ya nuna mishi kusa da Yaya Hambali. Yana zama Yaya Hambali ya matsa, har yana share sangalalun hannunshi inda jikin Gwadabe ya gogeshi. Da mamaki Gwadabe ya dubeshi, shi kuwa ya zuba mishi Uwar harara. "Marar kunya ji yanda kake ƙare mishi kallo sai kace sa'anka" Cewar Yaya Halima da bata fiye son a zauna lafiya ba dama" Baba Magaji ya yi mata daƙuwa tare da cewa. "Ungo naki Yau ga mutuniyar banza. Shi Hambali baki ga share hannunshi yake yi in da jikin Gwadabe ya goga ba? Sai kace wani karfa. To magana dai ta ƙare kai Gwadabe meye hujjarka na nuna zafin ƙiyayyarka ga ƴar uwarka Laila? Dan naji labarin komai" Gwadabe ya ɗago kanshi yace. "Ba ƙin Laila nake yi ba, face ƙin munanan halayanta abun ƙi. Na farko Laila babu wanda bai san ɓarauniya bace. Ko yanzu a taronnan in ba'ai da gaske ba sai ta raba wani da abunshi. Sannan da aure a kanta bata dena bibiyata tana turo mun da saƙonnin ƙauna ba. Wannan manyan dalilan yasa bazan taɓa iya auren Laila ba" Kafin ya rufe baki Goggo Iyatu da Laila suka fashe da kuka wi_wi. Ganin haka yasa Babala soma shessheƙar kuka itama. Baba Magaji yayi tsam yana bin kowa da ido ɗaya bayan ɗaya yana karantar yanayinsu. Yaya Hambali cikin zafin ranshi yace. "Uwar ƴaƴan naka ma naga ɓarauniyace. Wacce iriyar sata ce bata tabka mana a cikin gidaba? Ai kai kasan komai tunda kai ke biyan kuɗin duk abinda ta sata. Ita ka zauna da'ita sai Laila jininka ce ba zaka iya aura ba?" Gwadabe yace. "Wallahi ko tsinke Iyabo bata taɓa sata ba. Duk wannan kitumurmurar Laila ne. Ita ke satowa ta jefa ma Iyabo a ɗaki. Ni kuma ina biya ne dan ba son ganin ana tashin hankali nake yi ba" "Babu shakka Gwadabe " "Duk ya isheku haka ku saurara mun. Iyatu ku yi mun shiru ya isa haka nan" Sai da ɗakin yayi shiru kana yace. " Duk wannan kumfar bakin da kuke yi ba daidai bane sam. Layla dai kowa yasan mai dogon hannuce, tunda har maraɗi wajena Iyatu ta kawota ai mata magani. A lokacin hekarunta baifi goma ba. Sata kuwa da ta dinga yi a ƙauyannan abun yayi muni. Ina bayan Gwadabe na ƙin amincewa da auren Laila. Tunda kunce satarta shafar aljanune sai ku dage ku nema mata magani. Kuma da ace ni nasan irin tsangwamar iyalin Gwadabe da kuka yi da tuni nayi ma tubkar hanci tuni. Ko yanzu ma dan saki ukune a tsakani da ko kun ƙi ko ku so sai ta dawo tunda itama musulmace ahalul kitabi ma aurensu akeyi ballantana ita musulma gaba da baya." Falon yayi shiru sai hawa da saukar numfarfashi kawai. Baba Magaji yace. "Yaran dasu ta tafi ne Gwadabe?" "A'a Baba Magaji bata tafi da su ba. Shi Toye yana hannun Bara'u Sakina zata ci gaba da kulawa dashi, za'a sa shi a makaranta. Su kuma ƴan biyun na kaisu wajen Tamu a can Abuja shi ya buƙaci hakan" Baba Magaji ya jijjiga kai yace. "To Allah ya saka musu da alheri. Faɗuwa tazo dede da zama ni zan tafi da Gwadabe maradi yaje ga su Auwala can suna aikin haƙar zinariya, yaje shima ya jaraba wata ƙila arzikinshi yana can. Akwai ƙannenka mata ma a cikin gida, in kuka daidaita da ɗaya daga cikinsu kaga sai ayi tuwona maina ku yi zamanku a can. In ma aikin haƙar zinariyar bai maka ba akwai aiyuka da zasu dace da kai" Ajjiyar zuchiya Gwadabe ya sauke kuma yaji daɗin hukuncin da Baba Magaji ya zartar, shi kanshi yana da buƙatar yin nesa da danginshi ya fita neman na kanshi. Kuma yaji aikin haƙar zinariyar ya kwanta mishi a rai. Ya je can maraɗi ya samu sababbin ƴan uwa da zasu so junansu. Babala ba haka taso taron ya watse ba, amman bata da ikon cewa komai. Haka tana ji tana gani washe gari Gwadabe da Baba Magaji suka wuce maraɗi a bisa jagorancin Bara'u zuwa tashar mota. Wannan shine dalilin barin Gwadabe Kano, ya koma maraɗi hannun wan mahaifin Babala" JIHAR MARAƊI DAKE CIKIN JUMHURIYAR NIJER Cikin unguwar Ali ɗan tsoho. GWADABE:. Bayan saukar su Baba Magaji a abun hawan da suka hau zuwa layin Ali ɗan tsoho. Duk inda Baba Magaji ya sauke kafarshi nan Gwadabe yake ajjiye tashi turyan_turyan har zuwa ƙofar gidan Baba Magaji mai ɗauke da cikowar almajirai yara da ƙananu. Almajiran malam suna hango malam magaji, wasu gardawa biyu suka taso suka nufo su. "Malam maraba da dawowa sannu da zuwa baƙo? Malam baƙin gaddi mu ka yi ne" Baba Magaji yayi Dariya ya dafa wanna gaddi yace. "Ba baƙin gaddi bane. Ɗan wajen ƙaunata ne cikin ummata. Amman da dare zai zauna ya dinga biɗar karatu, da kuma Asuba. A karɓi jakar hannunshi ku shige dasu wajen Fhatsima." Gwadabe ya bi bayan Gaddawannnan biyu har zuwa cikin gida. A tsakar gida suka tarar da matan malam Magaji su hudu reras ko wacce da abinda take yi. Haka yan matan gidan, wannan na sukola, wannan na girkin abincin siyarwa, wannan na dakan fura, duk dai gasunan. "Almu baƙi mu ka yi ne, cewar Baba Fhatsima. Wanda ta kira da suna almu yace. "Malam ne ya tawo da shi ya. Kuma yace mu kawo shi wajenki." Fhatsima ta yi murmushi tace. "Yaro shiga wannan ɗakin ka zauna. Ke I'ne zo ki kai ma baƙo ruwa ya sha" Gwadabe har ƙasa ya durƙusa ya gaishe da matan Kawun nashi. Babu dai yabo babu fallasa suka amsa mishi, cikin su ukun babu wacce ta yi mishi kallon arziki. Baba Fhatsima tace. "Tashi yaro kaji ka shiga daga ciki, za'a kawo maka ruwa" Jakar Baba Magaji ya amsa a hannun Almu da ɗan kunshin kayanshi kala biyu wanda Bara'u ya ƙunshe mishi. Ɗakin ya shige da sallama. Wata budurwa tana kwance a ƙaramin gadon bono ta juya bayanta ta yanda mai shigowa ba zai ga fuskarta ba. Kayinta babu ɗankwali sai baƙin madaiaicin gashi mai walƙiya da yai ma kan nata ado. Ba gashi bane mai yawan daya wuce misali ba. Gashi ne wanda bai ko kai tsakiyan bayanta ba, iyakarshi gaba da kafadunta kaɗan. Gashin dai ya sha gyara sai walwali yake yi. Gwadabe ya ɗauke idanunshi daga kallon gashin ya bi ɗakin da kallo, ɗakin ya sha labule mai ɗawisu zagaye da bangon ɗakin dukka. Ga ɗan katakon kwalliyar labule zagaye da ɗakin, a saman labulen an yi jeren kwanukan sulba ƙananu sai ɗaukar idanu suke yi. Ga gadon bono ga gado mai rumfa maulidi, ko wannne gado ya sha lallausan zanin gado mai geza da heart a tsakiya. Kasan ɗakin kafet ne ja mai kwalliya malale takota ina. A gefen gadon bonon an ajjiye babban tulun ruwa mai fenti, an rufe bakin tulun da faifayi. Ga wasu manyan kumbuna da kwallaye anyi ado dasu, banda wata kwaba mai ƙofofin tangaran ita kuma kwabar an ƙawatata da kwanuka da fileti na tangaran nau'i daban daban. Sallamar da Gwadabe ya ji ne yasa ya nutsu ya dena ƙarema ɗakin kallo. Wata farar doguwar yarinyace ta shigo, hannunta riƙe da kofin sulba mai murfi ƙato. A gabanshi ta dure kofin, ta zauna harda lanƙwashe kafarta kamar mai ɗaukar karatu. "Ga ruwa Yaya ka sha kafin abinci ya nuna sai ka ci" Murmushi Gwadabe yayi mata. "To nagode ƙanwata" Kofin silban ya buɗe ya kafa bakinshi a kofin ruwan ga sanyi, Gwadabe sai da ya sha fin rabin kofinnan kana ya ajjiye ya rufe kofin. "Gidanku Malam ya je, ko kaima almajirci kazo yi?" Ta jefo mishi tambayar, kafin ya bata amsa suka jiyo ana kiranta. "Ine ke dibo fito ku tafi ga musa mai baro yana jiranki" Zumbur ta miƙe ta dubi Gwadabe tace. "Zan fita tallen abinci, amman ba jimawa nake yi ba. In na dawo ma ƙarashe hirarmu" Da idanu Gwadabe ya bita kawai, ta fita cikin hanzari. Tana fita Baba Magaji ya shigo, Baba Fhatsima na biye dashi. A ƙasa Baba Magaji ya zauna, Baba Fhatsima kuma ta zauna a bakin gadon bono. "Fhatsima kin gane ɗana Gwadabe kuwa, ɗan wajen ƙaunata Babala, yaro mai yawan ƙuraje?" Baba Fhatsima tace. "Ohh naji naji, shine haka ya zama babban mutum haka? Oh Gwadabe rabona da saka ga idanuna shekara talatin baya, kana yaro kyatunarka na yawan kawo mana ziyara a lokacin kana goye a bambunta" Gwadabe sai murmushi kawai yake yi yana sinne kanshi ƙasa. Wata budurwace doguwa itama mai jiki ta shigo hannunta da kwanon abinci ta dire mishi a gabanshi. "Wannan Ƙaunarka ce Habi kenan. Ashirin ga wanga wata za'a ɗamra amrensu su bakwai cib. Habi wannan wankine Gwadabe." Gaisheshi Hari tayi da ladabi, ya amsa cike da fara'a, ta saka kai ta fita. "To Fhatsima ga Gwadabe na damƙa amanarshi gareki, ki zame mishi uwa tunda kece babba a cikin gidannan. Rigingimu ne na dangi su kai yawa shine na yanke hukuncin tawo dashi in gameshi da su Auwala suna tafiya haƙan zinariya. Sauran bayanin in kwananki ya zagayo zan zaunar dake mu tattauna. Labulen ɗakin aka ɗaga. Wata baƙar dattijuwa mai zanzana ce tsaye ɗayan hannunta riƙe da faranin silba shaƙe da kwanonin silba a kai. Ɗayan hannun kuma riƙe da labulen ɗakin. Dukkansu suka ɗago suna kallonta. "Abincin ɗakin Yaya zaka ci, ko in kai shi turaka?" Babu yabo babu fallasa tayi maganar. Sai da malam ya girgiza kai, Baba Fhatsima kuma tayi murmushi tace. "In banda abinki kema kinsan ai a turaka zaici. Me zai sa yaci abinci a ɗakina ke da ranarki" Guntun murmushi tayi tace. "To wa ya sani abu a dubu Yaya." "Ki kai mun turakata gani nan zuwa" Malam ya bata amsa da kaurin murya da halamun ɓacin rai tattare da shi. Tana sakin labulen ya miƙe ya fita. Baba Fhatsima tace. "Kaci abincin, sai a nuna maka shashen samarin gidan ko?" "To Baba Nagode " Gwadabe ya bata amsa a dalabce. MRS BUKHARI B4B GIDAN 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu *Ƴar uwa ina fatan baki mance da kayan ƙamshin Mrs Bukhari gidan ƙamshi ba ko? Ƴar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ƙamshi. Matso kusa ƴar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ƙamshi ya riƙe miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake saƙawa a tsakankanin kaya. Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ƙamshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata. Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haɗe da turaren fesawa a gashi. Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ƙara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ƙamshin kifi ɗanye. Inada humrori kala_kala. Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ƙamshi. Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ƙamshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ƴar mutan Maiduguri kin samu ƙamshi. ( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai ɗauke da abubuwa huɗu manya kuma a kan kuɗi ƙalilan karki bari garaɓasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)* NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI CE 16 Kwanon da aka ajjiye mishi ya jawo. Tuwon ɓula ya gani da miyar bushasshiyar karkashi. A tsanake ya soma ci, wannan tuwo ya bashi mamaki matuƙa dan a ido bashi da kyan gani, amman a baki akwai daɗi sosai. Zama ya gyara yaci gaba da kantara loma. Wannan budurwar dake kwance a gadon bono ce ta yi miƙa ta tashi zaune tana salati. Wankar tarwaɗace kyakkyawa ma'abociyar siririyar fuska da siririn hanci, laɓɓanta suna da ɗan girma kuma a ɗane suke, haƙorinta biyu manya na gaba a waje suke ko da bakinta a rufe yake. Masu irin wannan haƙorin ana ce musu masu haƙorin zomo. Leɓenta baƙine wukul duk da ya fahimci duk mata da yaran gidan bakinsu duk baƙaƙene kuma kamar wani abun suke yi dan leɓen ya zama haka. Bata da idanu manya ƙanana ne idanunta kamar an huda sakwara, ga gashin ido da yaima idanun rumfa, in ba zaro idanun tayi ba ma baka isa ka ga ƙwayar idanun ba." Ganin Gwadabe a zaune yasa ta rarami mayafi ta rufe jikinta ruf. "Kayi haƙuri bansan kana ciki ba" Ta yi magana muryarta na rawa. A gaggauce ta gaisheshi ta fita. Itama doguwace mai kauri yar duma_duma fatar jikinta luwai_luwai dashi gwanin ban sha'awa, ga mazaunai ɓaka_baƙa. Iyabo ce ta dawo mishi rai, da irin yanda in ta yi walliyar ɗinkin buba da zani take burgeshi, da yanda in ya kallli tudun mazaunanta ta bata yake ɗimaucewa. Ajjiyar zuchiya ya sauke a fili yace. "Ina miki fatan samun namiji lafiyye wanda zai kula dake, ki huta a gidan mijinki irin hutawar da kika rasa a gidana. Allah ka sa jin daɗi da nutsuwa a rayuwar Iyabo ta gaba. " Gabaki ɗaya abincin sai ya fice mishi a kanshi ma, rufe kwanon tuwon yayi ya sha ruwa. Yana zaune ƙwalam wannan basamudiyar budurwar ta sake shigowa dan doguwace ingarma. "Baba tace in ka gama in raka ka shashen samarin gidan ka je ka yi wanka ka huta" Ledar ɗan kayanshi kala biyu ya cacuma ya soke a hammata, baice mata komai ba ya biyo bayanta suka fito. Iyayen gidan basa tsakar gidan, sai tsirarin yara matasa masu wasa kawai. Tiryan_tiryan yana biye da'ita har zuwa wata ƙofa da suka shiga yaga ɗakuna kusan bakwai a jere, da ba haya mara ƙofa sai labulen buhu yana kallosu, sai durom biyu na ruwa, da ƴan butoci, da bokiti. Wani ɗaki ta tura ta shiga. "Bismillahi ka shigo" Bayanta yabi zuwa cikin ɗakin. Katifun yayi ne guda huɗu a jere, sai akwatunan ƙarfe suma guda huɗunne, ginine na jar laka, ba fulasta ba komai, ƙasan ɗakin ma ba daɓe ba komai, rairayin ƙasa ne takota ina sai ƴar tabarma da ke shimfiɗe, saman ɗakin kuma jinka ce, sai ƙwan lantarki guda ɗaya jol. "To bayan gida yana waje, akwai botiki, da ruwa zaka iya watsa ruwa. Lokacin sallah ma yayi sai ka sami malam a waje" "Nagode sosai, sai dai bansan sunanki ba har yanzu." Ya faɗa yana ƴar dariya. "Sunana Hadiza" "Ke yar Ine ce?" Ya tambayeta. "E yarta ce ni" Sallama tayi mishi ta fita. Shi kuma ya shiga kewaye yayi wanka tare da ɗauro alwala. Farin yadi ya saka, wanda ya cire kuma ya saka a botiki ya zuba ruwa, kafin ya fita waje wajen Malam. A ƙofar gidan Malam yai musu limanci. Bayan an idar da sallah almajirai sai suka soma karatu. "Gwadabe ga allo da tawada ka iya rubutu ko?" Sai da Gwadabe ya amshi allo da tawada da alƙalami yace. "E na iya Baba, a can Takai ma makarantar allon mu ka yi, sai dai karatun baiyi zurfi ba, banfi izifi huɗu ba" "Hakane na sani Gwadabe. To yanzu daga farkon izifi huɗun zamu soma. Yau ka bar rubutun kayi muraja'a yau da gobe, jibi kuma sai ka soma rubutun allo. Bana son wasa da karatu. Sannan ka zama jajirtacce sai Allah ya dafa maka. Na sani mahaifiyarka bata da daɗi, iyayenmu kansu sun sha yin kuka da'ita. In banda fitina ta Babala ina ita ina kafewa sai ɗanta ya auri ɓarauniya sabida Allah fa?" Ana cikin haka sai ga su Auwala, da Mammada. Baba Magaji ya gabatar musu da Gwadabe, sannan ya mikashi ga Auwala akan zuwa gobe zai soma fita tare dasu. Su Auwala suka karɓeshi hannu bibbiyu, kuma su kai maraba da shi. Baba Magaji yaranshi maza su rai goma sha ɗaya ne ras. Uku daga ciki sun yi aure, suna cikin gidan tare da iyalansu, tara kuma kowanne yana neman kudi, amman shida a ciki kowanne da budurwarshi da tsayayyar magana. Ukun yarane. Washe gari Gwadabe yabi zugar su Auwala zuwa can garin Ɗan Issa inda anan ya ga dandazon dubban al'umma masu haƙan zinariya. Tun daga nesa dai ya hango tudun laka kawai, sai da suka isa wajen ya ga dubban al'umma. Da rijiyoin haƙon zinariya sama da ɗari. Mammada ne ya ja hannun Gwadabe ya kaishi ga shugaba mai kula da ƴan ƙwadagon wajen ya sanar dashi malam ne yace a kawo shi ya dinga ganin aiki kafin a hankali kuma ya shiga ayari. To Alhamdulillah haka rayuwar Gwadabe taci gaba da tafiya, da safe su hau abun hawa zuwa ɗan Issa, da yamma su dawo gida, su ɗau karatu daga magriba zuwa taran dare, da asuba bayan sun yi sallah kuma zasu yi muraji'a kafin kuma su karya su tafi nema. Duk dabdala a ɗakin Baba Fhatsima Gwadabe yake yinta. Mace mai kawaici da son jama'a kenan. A cikin sati guda da Gwadabe yayi a gidan Baba Magaji, ya fahimci ana buga kishi sosai da sosai tsakanin matan Baba Magaji, yaran ma suna taɓawa dan ko wacce ta jaye yaranta, sun haɗe kawunansu isu_isu. Ko wani abune ya faru da ɗan wani ɗakin, sai aita rurrufewa sai dai in na alkhairi ne, ko dan fahari a fito tsakar gida a faɗeshi. Baba Suwaiba da Amaryar Malam sune suka fi gwabza kishi a tsakankaninsu, kasancewar sunfi Baba Fhatsima da Baba Asshi karancin shekaru, sune Baba Magaji ya aura a baya_baya. Dan Amaryar malam yarinyace da bata wuce shekarun Hadiza ba. Yaranta uku duk maza, sune ƙananu sosai a gidan. Fitinarta tafi ta kowa a cikin matan Baba Magaji, sabida tana ganin ai itace Amarya. Su kuma sauran matan kishinsu yafi tsananta akan Baba Fhatsima da yaran ɗakinta da suka kasance manya, masu jam ragamar komai a gidan. Yaya Tasi'u shine Babban yaron Baba Magaji, babban ɗan kasuwane da yake harkar riɗi da gero, kuma yana kiwon tsuntsaye masu darajar gaske, dangin su ɗawusu, da gigs, da Aku, da dai manyan tsuntsaye na ƙasashe da dama. Kasancewar shine Babba shike ciyar da iyalan gidan baki ɗaya, kuma shi ke yi ma yaran gidan Aure, da duk abinda uba yake yi ma ƴaƴanshi. To kasancewar Yaya Tasi'u ya fito a ɗakin Baba Fhatsima sai yaran ɗakin Baba Fhatsima suka zama yara daban a cikin gidan, yana basu kulawa ta musamman, Baba Fhatsima kullum a cikin shigar daraja take. Kuma matar Yaya Tasi'u mai Suna Badi'a tana yawan yin dabgen kaza ta ciko kwano ta kawo ma Baba Fhatsima. Ko Shi Yaya Tasi'un yasa ayo mata miyar kaji cikin tukunya, sai dai su dinga ci, dan ko abincin ɓarayin bata ci, daga can barayin Yaya Tasi'u ake kawo mata ishasshen lafiyayyen abinci. Ko da Sallah Yaya Tasi'u shi ke ma su malam da iyayen nashi mata layya. To ko akan ragon layyar duk shekara sai an samu yamutsi kan na Baba Fhatsima yafi na saurn matan gidan girma da ƙoshi. Haka dai ake wannan rayuwa a wannan gida. Ranar da Gwadabe ya cika sati guda bayan sun tashi daga karatun dare sai Malam ya zaunar dashi. "Gwadabe banyi maka batun mace bane dama nace bari in bari ka nitsa. To kaga akwai ƴan mata a gidana da yawa, duk da bakwai daga ciki am sa lokacin bikinsu. To shine nace ga Hadiza nan ina ganin kamar tafi sauran yaran hankali kasancewar bazawarace ita. Wata biyar kenan da mutuwar auren nata. A halin yanzu dai bata soma fita zance ba, in dai kana ganin tayi maka sai kayi ƙoƙari ku sasanta kanku. In kuma batayi ba, kar kaji nauyi ka faɗamun wacce tayi ma kai ko wacce tayi ma tana cikin waɗanda za'a aurar ne, zan iya baka ita, shi wancan yayi haƙuri. In kuma dukka basu yi maka ba to Shikenan sai in taya ka da adda'ar Allah ya kawo maka wacce zata zame maka alkhairi. Duk da dai mun soma maganar da Fhatsima, Tasi'u da kanshi sai yayi sha'awar maka Hadiza tunda dukkanku Zaurawane. Amman kaje kayi tunani. Gwadabe take zufa ta keto mishi, zuchiyarshi ta shiga harbawa da ƙarfi. Shi a halinnan da yake ciki na alhini da damuwar rashin Iyabo. Ina shi ina wata soyayya? Ta ina ma zai soma wata soyayya, baya jin akwai wata mace da zai iya bata zuchiyarshi harta samu gurbi. To taya zai kuɓutar da kanshi daga wannan tayi na Baba Magaji? Kuma ko yaya ya nuna baya son ko ɗaya daga cikin yaranshi tabbas bazai ji daɗi ba. Kuma shima nauyi da kunyar Baba Fhatsima zata iya hanashi zaman ƙasar. Gashi har ya soma sakewa, ya soma jin daɗin sabon wajen aikinshi, kuma Alhamdulillah shima harya soma shiga rijiyar tono, duk da yanda akaita tsoratashi, da irin yanda ake samun haɗarin ɗaruruwan mutane su rasa ransu ta dalilin rubtawar ƙasa, amman yasa a ranshi tunda anayi, shima zaiyi in sha Allah sai yayi kuɗi. Tunda yanzu zumuncin ma sai kana da hannu da shuni akeyi da kai. "Gwadabe kar ka damu, na baka sati ɗaya kaje ka yi tunani da kyau. Kuma ka kalli yaran da kyau ka zaɓi ka darje, in yaso shekara mai zuwa sai a haɗa auren naku dana su Mammada ayita ta ƙare. Akwai babban filina gashi can, a cikin filin almajiraina suke wanki, da duk wasu harkoki. To anan zaku zauna dukkanku, Tasi'u zai gina ma kowa ciki da falo_falo" Da haka Gwadabe ya tafi ya bar Baba Magaji akan zasu haɗu nan da sati mai zuwa yaji wacce ya zaɓa. Jikinshi a mace ya shiga cikin gidan. Ɗakin Baba Fhatsima kai tsaye ya shiga. Anan ya tarar da Auwala da Mammada suna zaune da abinci a gabansu, da dukkan halama shi suke jira su ci abinci, dan tun zuwansu suke cin abinci a tare. Hadiza, da Ine suma abincin suke cii daga can kusa da gadonsu na bono. "Yaya Gwadabe ya aikin?" Cewar Ine kenan. Sai da ya gaishe da Baba Fhatsima kana ya amsa Ine. Hadiza ta kalleshi da murmushi a fuskarta tace. "Yaya Gwadabe da safe naje nemanka ɓarayinku ban sameku ba yau kun fita da wuri ko?" "Sa hannu Malam muna ci kana amsa musu tambayoyinsu. In wanna yaranne sai mu kai sha ɗayan dare ba mu ci abinci ba" Dariya duka suka yi, dan Auwala baya wasa da harkar cin abinci. Baba Fhatsima tace. "Ato da gaskiyarshi ai. Maza kuci ku samu ku yi wanka sai ku kwanta. Allah dai ya sama nema albarka." Suna cin abincin ana hira baki ɗayansu a haka dai suka ƙare cin abincin. Sai ga Yaya Tasi'u ya shigo. "Kuna nan ba? Anzo a cinye ma Baba ɗan naman nata ba? Baba Yarannan ya kamata a matso da maganar aurensu, a samu suma su mallaki iyalansu, su dena zuwa suna cinye miki kayan daɗi" Ɗan darawa su ka yi, duk suka miƙe suka gaggaisa, Yaya Tasi'u yace. "Gwadabe ya ciwon jikin? Mammada ya faɗa mun ranar daka shiga rijiyar haƙon zinariya kasa bacci kayi, jikinka yaita ciwo?" Kai Gwadabe ya sosa yace. "Wallahu Yaya Tasi'u ai naji jiki sosai. Amman dai yanzu ina ɗan taɓa aikin, ciwon jikin yana ja baya" "E dama a hankali zai bi jikinka. Kama yi ƙoƙari ni naga jarumtarka sosai, dan wannan aikin bana malalata bane." Baba Fhatsima tace. "Ni kaina na ga juriyarshi sosai. Allah yayi muku albarka dukanku Allah ya baku abinda kuke nema duniya da lahira" Da "Ameen" Suka amsa dukkansu. Hadiza tace. "Yaya maganar kuɗin angon baka bamu ba, kar mu rasa ɗinkin" tsaki Yaya

Chapter 15 of 16