Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
gida Babala bata da aikin daya wuce faɗin an ma ɗanta asiri sai wahala nake bashi, ya shiga tarkon yarbawa jikokin oduduwa. In hakan baiyi mata ba sai ta sameni har ɗaki ta ƙaremun tanadi tsab, ni dai zaman gidan gabaki ɗaya ya gundureni, haka naita haƙuri har Allah yasa ta koma Takai. Gwadabe ma haka yasha haƙuri da Babala, damuwa duk ta haɗu tayi mishi yawa, ga matsala da yake samu a wajen ƴan lodi akwai wani bawan Allah da yasa Gwadabe sosai a gaba, domin yawan tashi da motar Gwadabe take yi wajen sufurin kaya, ada yafi kowa ƙwazo a matukan tirelolin har ana mishi kirari da giya dubu, akwaishi da sharara gudu a hanya dandanan sai ya isa ikko, yana isa zai sauke lodi ya sake nauso hanya. To samuwar mota a hannu Gwadabe sai ya doke giya dubu wajen ƙwazo da kazar_kazar bil haƙƙi Gwadabe yake komai. Wata rana ana ma Gwadabe lodi giya dubu shi kuma shigowarshi ƴan lodin kenan, da ya kalli Gwadabe sai yace. "Wata rana ma ba zaka samu ƙafafun da zaka taka mota ba, balle hannayen murza sitoyari in dai muna tasharnan gasa da ni ba daɗi." To daga ni har Gwadabe sai muka shiga damuwa daya dawo yake sanar dani, mu kaita adda'ar neman tsari harda sadaka, ga wannan damuwar ga damuwar Babala abubbuwa suka cakuɗe goma da ashirin. Washe garin ranar da Babala ta tafi muka cika kwanaki arba'in. Ƴan biyu sun yi kuɓul kuɓul dasu gwanin sha'awa. Tun sassafe naketa kaye_kaye dan yau kam a gidanmu zanje in wuni yawon arba'in. Kafin sha biyu na gama duk abinda ya dace, Toye na dawowa daga makaranta, na kwaɓe mishi inifom na watsa mishi ruwa, na shiryashi tsab, naima matan gida sallama. Atampa mai haske nasaka da sabon takalmi da mayafi, ina fita tun kafin in sauka daga kan tudun gidan na soma jiyo hayaniyar muryoyinsu suna gulmar da suka saba. Muna zuwa titi na tari Bus sai ƙofar Nasarawa inda anan gidanmu yake. Cikin layinmu na shiga tun daga titi nake gaggaisawa da mutane, wasu dole ma in tsaya su ga ƴan biyu a haka harna isa ƙofar gidanmu. Gidane mai ɗauke da karamar ƙofa gefe da gefen ƙofar shagunane biyu. Ɗaya na Iyaa Debisi daya na Iyaa Kokodeen. Iyaa Debisi soson danga dasu lagwani, ashana, sitati, gyalu, bula, kayan robibi. Su take siyarwa tana da injin niƙa har biyu dana wuta dana ruwa. A shagonnan mu kai rayuwarmu, akwai ƙofa a cikin shagunan wanda zaka ɓulla babban tsakar gidan namu. Iyaa Kokodeen kuma albo, garin Amala, daddawar kalwa, da bushasshen rogo, garin rogo su take siyarwa harda ma kamun jar dawa. Wannan sana'ar tasu da ita muma mu ka yi wayo muka gansu akai, gashi har yanzu ana takusawa. A bencin dake ƙofar shagon Iyaa Debisi na zauna dan na gaji sosai. Toye kuma yayi cikin gida da gudu. Iyaa Debisi tana zaune a cikin shago taci leshi ɗinkin buba ɗaurin ɗankwalinnan a cukurkuɗe sai gyangyaɗi take ta yi abunta, dama kullum aikinta kenan wannan gyangyaɗi ba'a rabata dashi, kuma a zaune ake yinshi. Iyaa Iyaa!! Na kirayi sunanta tare da ɗan buga benci kaɗan sai ta buɗe idanunta muka haɗa idanu. "Ahhh Iyabo kece da tsakar ranar nan da yara, ku yaran zamani baku da hankali ai mace mai goyo ko ciki bata fitowa sa'ilin da rana ta take. Maza shiga ciki gani nan zuwa. Mahaifiyarki ma yanzu isowarta ko awa ɗaya ba'ayi ba tana ciki" Miƙewa nayi ina fara'a dan na jima banga Mamana ba. Shagon Iyaa Kokodeen na shiga na durƙusa a gabanta na gaisheta , itama tace maza in shiga ciki rana ta take. Ko da na shiga samarin gidan basa nan kowa na wajen aiki, babu ƴan mata a gidan tuni sun jima da aure, Bose ce da aka bari itama gashi tana gidan mijinta. Sai matan ƙannen su Iyaa su su uku Iyaa Beji, da Iyaa Lekan, sai Iyaa Amope. A ɗakinmu na ya da zango mahaifiyata tana tsaye tana sallah goduwa farar bafulata siririya, gata da alkunya da sanyin hali bata iya sakewa tayi hira dani, iyakarta dani gaisuwa da tambayar ya nake ni da mai gidan nawa. Iyakar hirata da'ita kenan saita tsuke bakinta tayi shiru kanta a sunkuye." Tana idarwa ta juyo tace. "Jabu kune a tafe? ( Jabu sunan da dangin mahaifiyata suke kirana dashi kenan, dangin mahaifina kuma iyabo)" Data juyo sai naga ta rame sosai idanunta sun zurma da yawa" Dada kinzo lafiya ina wuni?" Bata amsaba sai miƙo mun hannu da tayi na tashi na sunto yaran na saka mata a cinyarta. Tayi ƙuri tana kallonsu tana musu adda'a. Take Naji hawaye na kwarara a idanuna, Allah ya ɗaura mun tausayinta sosai a zuchiyata. Inna dubeta sai inga kamar tana cikin ƙunci da matsi a gidan aurenta. Dada baki da lafiya ne naga kin rame?" Cikin gurɓatacciyar hausarta ta fulanin daji tace " E jinya nayi kusan wata shida sai dai a kwantar sai dai a tayar, shine dalilin da yasa ban ɓulloku ba." Sai kuma taci gaba da magana dani da yarbanci, dan Hausa mugun wahala take bata, dama da yarbancin muke magana." "Ashe kin samu ƙaruwa Allah ya raya. Ina ɗayan jikan nawa?" Ajjiyar zuchiya na sauke nace. Yana ɗakin Iyaa Beji can na baro shi, ya wajen Baɗɗo da mai gidanta? ( Boɗɗo ƙanwatace a gidan da Dada take aure yanzu, sau ɗaya na taɓa ganinta tal a rayuwata) "Ɓoɗɗo ta haihu tana goyon Daso an yi mun takwara" Sai naji ina kewar ƙannena da dangin mahaifiyata ma, sai naji inason kasancewa dasu. Dada inaso in zaki koma zan tambayi izinin mai gidana zan biki in gano rugarku, inaso lokaci zuwa lokaci in dinga zuwa ziyartarki ke da danginki nima ya kamata yarana su san dangina na wajen uwa su saba" Da sauri ta ɗago ta dubeni tace. "Kar ki soma, kiyi zamanki na yafe miki. Ni zan dinga zuwa ina dubaki kamar yadda na shafe sama da shekaru ashirin ina zuwa ganinki." Ƙur nayi mata da idanu ina karantar yanayinta, duk sai naga ta ruɗe, tashi tayi ta bani su Taiwo ta haye ƙaramin gadon Iyaa ta kwanta ta juya mun baya. Na rasa me ake ɓoye mun ne da Dada bata ƙaunar in ziyarceta, bata son danginta su sanni, to meke faruwa ne tabbas tana ƙasa tana dabo. Iyaa ce ta shigo tana faɗa sosai kamar zata ari baki, tana yi tana dukan cinyarta tanata faman yare. Ashe da Debisi take yi shigowarshi cikin gidan kenan. Da yare yace da'ita. "Kiyi haƙuri Iyaa nifa ba cewa nayi yemisi ta ajjiye aikinta ba, gani nayi ta fifita aikinta fiye da zaman auren da muke yine. Kuma tama ga damar zuwa ta haɗa mun jarfa ne" Ya ƙarashe a sanyaye. Iyaa Kokodeen ce ta shigo ɗakinnan tace. "Haba Iyaa Debisi wannan yaron fa yana da gaskiya kuma ma ai yayi ƙoƙari sosai Ya kamata itama yemisi ta dena zuwa tana yawon kawo ƙararshi wajenki ko wajen mahaifiyarta. Ai ga irinta nan abunda ake hango muku daban abinda kuke hango ma kawunanku daban, ku kun ɗauke mu ba wayayyuba. Dama duk namijin da zai auri soja ai dole sai dai ayi zaman haƙuri." Wannan maganar tamkar ingiza iyaa Debisi Iyaa Kokodeen tayi dama har gobe da mikin ƙin aurena da Burodami Debisi yayi a zuchiyarta. Dan da ƙyar ma aka shawo kanta bayan aurena ta zubar da makaman yaƙinta, macace mai kafiya da binbinni, gata da mita. "Basshi ai duk abinda na guje mishi kenan, shi yasa naso ya auri ƴar uwarshi Iyabo. Musamman dana fahimci ita iyabon tana sonshi. A gida ma ita ke kula da komanshi ina ga ya aurata. Yaronnan ya buɗa mana ƙasa a idanu, dana matsa ya je ya haɗoni da dangin ubanshi akazo aka danneni. To yanzu me yake so ayi mishi? Ai haka zaka je kaita kwashe takaici da baƙin cikin zama da Soja, kuma ban yarda ka sake takurama Yemisi akan batun aikinta ba." Daga ni har Burodami Debisi muka yi tsamo_ tsamo tamkar kazar data faɗa ruwa, ya ɗago mu haɗa idanu ya kasa sabida kunya tare da nadamar abinda ya aikata. Lokacin na shiga tunanowa a zuchiyata, a lokacin da Burodami Debisi ya murtsuke idanunshi yace shi Allah ya kashe shi bazai aureni ba. Ji nayi tamkar alƙiyamatace ta tsaya. Abun bai zo mun da daɗi ba, domin jaririyar zuchiyata da so da tsantsan kaunarshi ta ginu, ban taɓa tunanin zuchiyata zata iya son wani mahaluki bayan Burodami Debisi ba. Ni ban iya sa abu a zuchiyaba, ban iya son abuba. Da wasa da wasa Gwadabe ya maye gurbin dana adana Burodami Debisi a ciki, harya samu matsayin da shi kanshi Burodami Debisi bashi da irinshi. Yanzu kuwa da Gwadabe ya riga ya lasamun giyar sonshi na shiga mayen ƙaunarshi jinshi nake tamkar numfashina, ko kuma bugun zuchiyata, ina ma mijina irin son da har abada bazai iya samun macen da zata so shi kwatan son da nake yi mishi ba. Muryar mahaifiyata ne ya katsemun tunani, cikin ƙwarewa a yaren yarbanci ta soma magana kamar ba bafulatana ba. "Ai aikin gama tuni ya gama. Abinda zai faru ya faru. Jabu tayi aure harda albakar aure. Shima Debisi yayi aure harda ƙaruwar haihuwa. Ni ina ganin Toyosi ki yi haquri ki kawar da wannan batun. Kai kuma Debisi aure ai cike yake da ƙaɗdarori iri daban _daban. Ita kanta Jabu kana ji da ganin irin matsalolin da take fuskanta da dangin mijinta, auren ba daɗinshi take ji ba ana dai zaune zaman yara ko ba haka ba Alima?" Ta kai dubanta kan Iyaa Kokodeen wacce ainihin sunanta Halima, to a harshen yarbanci kuma sukan maiyar da harafin H a matsayin a misali Alima a madadin Halima auwa a madadin Hauwa, Abu a madadin Habu. To itama Iyaa Kokodeen manya da Alima suke kiranta. Ta dubi Dada tace. "Gaskiya ne sosai, mu kanmu wanne haƙurinne ba mu yi ba, namu haƙurinma na mutan da ba irin na yaran zamani ba. " Ranar Burodami yasa mita, sai an kawar da maganar sai can ta dawo da zancan baya. Har Burodami Debisi ya gaji ya bar gidan amman bata sauya zani ba. Haka dai wunina ya kasance bamu muka tashi shirin tafiya gida ba sai da magriba ta kawo kai. Akamu Iyaa Kokodeen ta bani da garin albo dana amala, bata taɓa gajiyawa muddin zanzo sai ta bani. Dada kuma ta miƙo mun ƙunshin bakon da tayo mun tsarabata. Dada yaushe zaki koma, amman zaki zo gidana ko Dada?" Kawar da kai tayi tace. "Me zai kaini gidanki Jabu, ai babu. Jibi zan koma ni kam in sha Allah " To Dada gobe zan dawo akwai saƙo da nake son baki ki ba su Baɗɗo." Kai kawai ta gyaɗa mun. Iyaa kuma ta dire tace ban isa in dawo ba, in Lekan yananan in je ɗakin zaure in kirawoshi in yaso sai ya bini ya amso saƙon" Ba dan naso ba akayi hakan. Da Lekan muka dawo gida. Ƙannena su su huɗu ne, biyu mata biyu maza. Matan na cira musu atampopi guda ɗaɗɗaya sababbi dal. Na cire ma Dada lashi da Atampa coddibuwa, Baffa kuma na cire mishi shadda guda ɗaya ce rak. Na cirama ƙannena mazan kaya kala ɗaɗɗaya a cikin kayan da Hajiya ta bani in ba Gwadabe. Dada na ƙara mata da mayafai da hijabi, da sabon takalmi dan naga takalmin da tazo dashi a ƙafarta takalmin robane duk ya sha liƙi gashi har ɓulewa yayi. Nera dubu goma na zara na miƙa ma Lekan. Yasa hannu kenan zai karɓa Laila ta shigo babu ko sallama. Banji daɗin shigowar tataba sam, bin Lekan da kayan da na soma cusa mishi a bako tayi da kallo. Lekam muje nayi ma bayani a ƙofar gida" Biyoni yayi a tsakar gidanma da idanu yuuu su Yaya Haula suka bini. Baban Nazifi ya daka mun wata tsawa fitowarshi daga ban ɗaki kenan. "Waye wannan sannan wannan kayan da Za'a fita dashi menene a ciki?" Ya jufo mun tambayar bayan ya iso gabanmu. Ɗan fodiyo dake zaune a tabarma suna ƙirga kuɗi shi da Da'u ai sai ya taso yasa hannu ya fisge ledar hannuna ya zazzageta a ƙasa komai suka zubo ƙasa. Ganin matan gidan a gaban kayan Yaya Haula harda salati yasa na fashe da kukan baƙin ciki. Jin amon muryar Yaya Harisu ne yasa na sassauta. "Ina za'a kai kayan. Shi wannan gona_gonan ƙaton da kika shiga ɗakin mijinki dashi alhalin kinsan Gwadaben bayanan fa, ko gwalen naku na yarbawan zaki shigo mana dashi?" Lekan sarkin zuchiya har zai yi magana na dakatar dashi da yarbanci cewar kar ya sake yace komai. Na mayar da hankalina kan Da'u da Baban Nazifi ya bashi umarnin wauwara kayan. Kayan maza da suka gani yasa Baban Nazifi ɗago rigar yace. "Wannan ba rigar Gwadabe bace Iyabo. Wato sace kaya kike yi ƙannenki suna zuwa da daddare suna fitarwa ko? Kenan doguwar rigar Haula data ɓata muna tunanin ruwan sama ne ya gudu da'ita ta rariya ashe kece kika sata? Asirinki ya gama tonuwa a gidannan ƙila harda ƙarshen zamanki " In kada baki in yi magana na kasa. Lekanne yace. "Wannan kayan data samu a sunan Taiwo da Kahinde ne, sauran kuma nata ne na gida, sai kayan mijinta guda biyu. Mahaifiyarta ce tazo daga ƙauye shine ta bayar a kaima ƙannenta, kuna da matsala da hakanne to? Batun sata kuma Antimi Iyabo ba ɓarauniya bace ba'a mana wannan tarbiyyar ba." Salati Gude ta saka tace. "Au ita Iyabon dama tana da ƙanne mu bamu sani ba? Sannan iyakar saninmu uwarta ma ita kanta ba tace ga inda take ba, yasar da'ita tayi tun tana ƙarama ai." Yaya Harisu yace. "To munji babu kayan da zai fita a gidannan. Kai kuma fice mana a gida" Kamar kuwa jira Lekan yake yi ya fita fuu yana sababi da yare. Da manuniya Yaya Haula ta nuna ni tace. "Wabillahillazi huwarrahmanu sai kin biyani doguwar rigata, nera dubu takwas na siyeta , tunda na kama ɓarauniyar rigar." Nan su Gude suka soma tafi tare da yi mun kururuwar naji kunya. Tsugunnawa nayi jikina na rawa na kwashe kayana zan shiga ɗaki dasu, Baban Nazifi ya warce buhun yace. "Har sai kin biya kuɗin rigar da kika sata zaki samu kayanki, Allah wadaran halinki." Tiɓi_tiɓi da kayan mazaunai na tafi ɗaki da gudu na faɗa akan gado na sau rikitaccen kuka irin wanda ban taɓa yin irinshi ba a duniya. A wannan halin Gwadabe ya dawo tafiya ya tarar dani, dan wallahi ko sallamarshi ma banji ba, sai jin hannunshi nayi a jikina, ina ɗagowa da naga shine na kife na sake rugujewa da kuka. A ƙagauce yace. "Wani abunne ya faru da kika je wunin gida ko? Iyabo kiyi haƙuri ki dena kuka akan matsalolinmu dan Allah." Banza nayi mishi da ƙyar ya iya nasarar shawo kaina na faɗa mishi abinda ya faru" Shiru yayi kamar ruwa ya cinyeshi yana riƙe da kumatunshi. Amman naga ranshi ya ɓaci ainun har jijiyoyin goshinshi sun tsaya. "Yanzu kayan suna ina, ina shi Lekan ɗin?" Cikin rawar murya nace. Kayan suna hannun Baban Nazifi, Lekan kuma Yaya Harisu ne ya koreshi." Numfashi ya ja dogo yace. "Ina zuwa ki goya Kahinde da Taiwo zamu fita." Gwadabe na kirayi sunanshi da gaggawa, kulawa ma yabawa dan ko juyowa bai ba. Ina zaune a bakin gado da goyo a bayana, sai na soma jiyo maganganu sama sama ina jiyo tashin muryoyi daga tsakar gida. Ni dai ban ko yi yinƙurin miƙewa ba, hayaniyar sai ƙara tsananta take yi, jin kamar ana titirniyar dambe ne yasa na fito da gudu, aikuwa ƙafafuna suka harɗe na faɗi rib cikina da Manana suka daku da ƙasa. Take wasu hawayen wahala suka wanke mun fuska. Abunka da mai ƙiba sai fa da dabara na miƙe ƙafata naji ta nai mun mugun zafi, a haka na daure na fita. Da'u Gwadabe ya damƙa yake ta kai mishi mahangurɓa, Yaya Harisu na riƙe da Gwadabe ta baya yana jayeshi, Ɗan fodiyo na riƙe da Da'u ga Auwal a tsakiya yayi musu iyaka. Baban Nazifi kuwa yana gefe yana sharce hawaye Yaya Haula tana rarrashinshi kamar wanda jaki ya kada shi da ƙasa. Su kuma matan gidan suna cure waje guda da yaransu maza da mata. "Ni zaka duba ka ce matata ɓarauniyace, me aka kamata ta sata da za a ci zarafinta ita da ɗan uwanta? Kaya kuma ga kuɗin rigarki Haula ku bamu kayanmu" Ban san Gwadabe na da zuchiya haka ba sai yau. Ƴan uwanshi suka rufu a kanshi da zagi da cin zarafina. Baban Nazifi ne ya jefo mana bugun kayan ya sauka a ƙirjina tab, ba da ban ina da ƙiba ba da sai na faɗi. Yaya Haula kuma ta fisge kudin hannun Gwadabe. "Gobe_gobe ku tattare yanaku _yanaku ku bar mun gidana, tunda ba da uwa da uban Iyabo aka haɗa kuɗi akasai gidan ba. Ku kuma ko wacce ta koma ciki ta ja ƴaƴanta" "Kullo ɗakin mu je mu dawo kinji Iyabo?" Ya faɗa yana haki. Da ɗingishi na koma na kullo ɗakin muka fita. Amman fa har muka isa gidanmu babu wanda yace da wani komai. Acanma mun shiga mun samu kab matan gidan da samarin gidan a tsakar gida Iyaa tana ta faman kwakwaso da sababin abinda ya abku. Ai muna shigowa ta dira a wuyan Gwadabe da zagi, har kakan kakanshi sai da ta zaga. Mahaifiyata ta kaɗa kanta ta shige ciki, Gwadabe ya miƙo mun buhun kayan na shiga ɗaki na sameta, na baro Gwadabe na ba iyaa haƙuri amman kamar ƙara ma zigasu yake yi. Ina jiyo sanda Iyaa Kokodeen ta koreshi shima waje. Da ƙyar mahaifiyata ta yarda ta karɓi kayannan, shima sai ajjiyewa nayi a gefenta. Ina gunjin kuka na nufi hanyar waje. Muryarta na rawa tace. "Jabu ki yi ma mijinki biyayya. Muddin shi yana ƙaunarki kar ki sake wannan rikice_rikicen banbanci ƙabila da aketa gwabzawa kice zaki kaso aurenki. Ko beyerabe kika aura ba tsira zaki yi ba. Dan a ƙarƙashin ko wacce igiyar aure akwai ƙalubale, in kika ji na wasu naki ba komai bane. Kice ina gaisheshi bamu samu damar gaisawa ba" Kasa amsata nayi na fice ina dingishi, a ƙofar gida na tad da Gwadabe idanunshi sun rine sosai. Haka muka rankaya gida, a daren dai ɓarawon baccine ya kwashemu muka wayi gari da labarin Baban Nazifi yace dukkansu zasu tafi Takai akwai meeting da za'a gabatar. Ni dai har Gwadabe yai mun sallama ya fita ina sharar hawaye. Ga ƙafata ta aune ta yi him. Tsabar ɓacin rai Gwadabe bai ga ƙafarba bai san ƙafar ta samu rauni ba. Haka na wuni ni dai sukuku ba laka, ƙafa fa kafin la'asar ta sake hayewa da ƙyar nake takawa. Ina zaune akan kujera ina kirɓa sakwara sai ga ƴan Takai sun yi sallama. Gwadabe na ƙura ma idanu sai naga har ya faɗa. Yana isowa ya cafe taɓaryar a ƙoƙarinshi na ganin ya kore damuwar dake cin ranshi. Ya hau dukan sakwara a turmi, dan da nan ya kammala tsab. Durƙusawar da zaiyi ya taya ni kai filas ɗin abinci ciki, sai yaga ƙafata a kumbure. "Me ya samu ƙafarli ta aune haka, kuma kike zaune kina aiki? A'a taso muje maza_maza" Babu shiri muka fice a gidan. "Ɗan iska na mamaji" Cewar Baban Nazifi kenan. Ashe targaɗe naji a idanun sawuna, mai ɗori ya gyara mun muka dawo gida. Bayan sallar isha muna zaune muna cin abinci yke bani labarin yadda akayi a takai. "Abun babu daɗi. Babala dama kinsan sai dai ma ta daɗa kwaye mun baya, gashi Goggo Iyatu tana nan mahaifiyar Laila, itama tai ta kunnawa abun wuta. Mun tsaya akan dukkan abinda ya ɓace a gidannan kece kika sace kuma ni zan biya. Wallahi nayi iyakar yina dan in fahimtar dasu fur sunƙi. Ni dai roƙon da nake yi miki kiyi taka tsantsan kuma ki iya takunki, kisa ma Laila ido sosai, kinsan na faɗa miki ƙasurgumar ɓarauniyace." Kuka na fashe dashi. Kana nufin a haka zanci gaba da zama tare da kai anai mun kallon ɓarauniya, harma duk abinda aka nema aka rasa sai na biya? Gwadabe haƙurina ya ƙare ni na...." "Kul kika bari mala'ilun Allah su yi fishi dake, Allah yayi fishi dake. Iyabo wallahi dukkan wannan abun so akeyi a samu a ukun da da kanmu zamu ji mun haƙura da junanmu, abinda suke so kenan. Nayi duk iya iyawata in kare ki, abun yafi ƙarfinane bazan tsaya ina jayayya da Yaya Hambali ba, domin uba ne, a kafaɗunshi muka girma, Balle kuma Babala da goggo Iyatu. Kiyi haƙuri ni zan dinga biyansu duk abinda suka ce an sace musu." Ya batun korarmu kuma da Baban Nazifi yayi, ba gara mu bar gidan ba, tunda in bana gidan ba mai cewa nayi sata?" Kanshi ya dafe kafin a tausashe yace. "Babala tace ko bayan rants bata yafe ma duk wanda ya bar gidannan ba. Ashe Yaya Hambali da Yaya Harisu sun sai gidajen su Malam Audi, da gidansu Baturiya, wata mai kamawa ma za'a soma aikin fashe katangun a haɗe gidajen. Kinsan bikin Nazifi da Laraba ya ƙarato, nima fa duk yau nake jin labari. Nazifi zai zauna a cikin gidannan da matarshi. Itama Laraban a cikin gidannan zata zauna. Ai kinsan Ilum ɗakin Goggo mai Yaɗiya ko? To shi zata aura, Yaya Hambali zai ɗaukeshi aiki a kasuwa. Ni dai Iyabo abinda nake so dake shine kar ki sake fita tsakar gidannan sai in fita daga gidan zaki yi, ko ban ɗaki zaki shiga. Su girki, wanke_wanke wanki duk kiyi a ɗakinki, kiyi haƙuri damo.." MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI Lamba ta tara (9) "Kinga can wajen tudun?" Gwadabe ya nuna mun da hannunshi. Wani dan tudune karami akayishi a falon kamar wajen cin abici. ( Daining )Amman bashi da girma, a wajen na saka kayan kallona. "To ki fito da kayan kallon gobe zan siyo miki teburi da dirowar da zaki dinga zuba kayan abinci a ciki. Zaki dinga amfani da risho, ke ko gawayinne in kika kunna a ƙofar ɗaki daya ruru ki shigo dashi, ki sa labule wajen ya zama miki kicin. Iyabo bana so ki sake fita na kuma na jajjada miki. Kiyi haƙuri wata rana sai labari. Ki daure wallahi ba'a sona haka ke faruwa ba, naso mu bar gidannan muyi nesa da ƴan uwa Kuka babu irin wanda banyi ba, washe gari kuwa sai ga Gwadabe da tebur, da durowarshi gajera ta kicin ɗin ƴan gayu. Tare muka jera kayan tukwanena da ɗan kayan abinci da nake dasu, har randunana a cikin wajen na jera, Gwadabe ya hau ya kafa mun labele, Laila sai zirga_zirga take yi tsakanin tsakar gida da ciki. Bai fita ba sai da ya ciccika mun randunanan da ruwa tab, kana ya fice kasuwa. Ni kuma na shiga aikace, aikacen gidan. Bani na fita tsakar gida ba sai da na gama komai nawa na fito da ruwa bokiti uku na sheƙar a rariya, bokitin dana shake shi da wanki na fita dashi na je maƙota na shanya. Ina dawowa na yi komawata ɗakina. Haka al'amuran rayuwar su kaci gaba da gudana yau fari gobe tsumma. A kwana a tashi, gashi yau mun wayi gari jama'ar Takai suna hanyar shigowa Kano. Gidan namu shaƙe da matan anguwa suna ta faman taya mu aikace_aikacen biki. Dan Yaya Haula hantsice leƙa gidan Kowa, babu gidan da bata shiga, kowa a layinnan ya santa. Gida ya ɗau fenti, ga girma da gidan ya ƙara, sakamakon gidaje biyu na jere damu da Yaya Hambali ya siya, aka rushe katangun gidan ya ƙara girman gaske, kuma yasha gyara sosai. Ɓangaren Amarya Laraba da Ango Nazifi ya sha gyara na musamman. Wajajen la'asar sai ga ƴan Takai sun iso Bus biyu su da gayyar yara raɓe_raɓe, gida ya kacame da hayaniya, amman nifa babu wanda yazo daidai da ƙofar ɗakina . Washe gari aka shiga biki ka'in da na'in. Ranar ɗaurin aure tun duku_ duku muka game jallof ɗin shinkafa, da tuwon shinkafa, harda masa. Su Gwadabe kuma suka kama hanyar Takai dan acan za'a ɗaura auren kasancewar

Chapter 8 of 16