ITAMA HAKA TAKE FUSKANTAR ƘALUBALE A CIKIN AURENTA. ITA KANURI TAKE AURE TANA BEYERABIYA)
Lamba ta bakwai (7)
Saye nake da doguwar rigar leshi, ɗaya daga cikin kayan da aka bani a gidan aiki. Toye na kwance a kan bargo a ƙasa yana bacci. Ƴan biyu kuma suna kan gado suna baccinsu sun sha overoll farare tas. Yaran ya zuba ma idanu da kyau sai murmushi yake faman yi. Zama yayi a bakin gadon ya ɗauki Taiwo dan tafi kusa dashi. Zama nayi ina fuskantarsu yayi kyau da yarinyar a hannunshi.
Rabon yarannan ne yasa iyayenmu suka amince da aurenmu bisa dole, dan wannan rabon ka iya ajalin duk wanda ya kafe ba zamu auri juna ba. Gwadabe ina alfahari da aurenka, ina alfahari da soyayyarka gareni. Hakanne yake sa in mance da kyara, tsangwama, ko ƙyamata daga danginka. Domin kai kam ka zame mun komai, ka cike duk guraben dake da giɓi a rayuwata madallah da samun miji nagari irinka"
" Ifemi ( masoyiyata) Na gode da soyayyarki, ina jinjina juriya gami da haƙurinki, samun mace irinki abune da sai an tona shi a wannan zamanin, musamman a ƙabilarku da matan yarbawa suke da zafin rai da saurin faɗa. Mala'ikun Allah ku shaida ni Gwadabe na ɗaga ƙafafuna Iyabo ta shiga aljanna, ku sake shaidawa ita da kishiya sai ta gidan aljanna, a can ma itace shugabar su " Dariya mu ka yi dukkanmu kafin ya ja fasali yace.
"Ina da tarin tulin tambayoyi kin shirya?"
Ahaf ni dama nasan ba zaka barni ma zuwa gobe ba. Tambayeni in baka amsa, amman kafinnan bari in kawo maka abinci, kana ci kana kora koka kola zai fi. Miƙewa nayi abincin na gefen sib a tiran silver ɗauke da duk abun buƙata. Tuwon shinkafane miyar bushasshen karkashi wacce ta ji kayan cikin rago, iyakar kayan Cikin miyar shine iyakar rabon da muka samu a raguna biyu tiƙa_tiƙa. Zuba mishi nayi na matsar gabanshi, Ajjiye Taiwo yayi tare da sakkowa ƙasa, ya tanƙwashe ƙafarshi yanata kallo ina hidima dashi. Lomar tuwon farko a bakina ya sauke mun, tare da yankan saifa.
"Bani labarin tv da kafet tukunna, dan dasu na soma cin karo" Sai da na saisaita nutsuwata, na sake tausasa muryata kafin nace.
Burodami Debisi ne ya sake ma Yemisi kayan ɗakinta, shine ya bibbimu da tsofaffin"
Kafeshi da idanu nayi ina karantar yanayinshi, dan Gwadabe bashi da daɗi sam ta wajen kishi. Ya zafafa kishinshi sosai akan Burodami Debisi. Alhalin shi babu ni a zuchiyarshi sam, bana mance lokacin da Iyaa tace zata haɗa aurenmu ayi tuwona maina. Har hawaye Burodami Debisi yayi ma iyaa dan ta tausaya mishi ta janye maganar auren. Ba dan ƙiyayya ba sai dai kawai bana daga cikin jerin kalar matan da yake burin rayuwar aure dasu. Ni ina da ƙiba sosai, gani da cikar kumatu dan har idanuna da hancina sun shige ciki, ga mazaunai masha Allah. Shi kuma baya ra'ayin mace mai irin zubina. A cewarshi siriraya doguwar mace yake so, wacce zai iya bi da gudu ta zura ya rufa mata baya. Akan wannan dalilin ya kafe dole cikin fishi da hasala Iyaa ta janye batun aurenmu dole ta ɗauki idanu ta zuba mishi, har kwsnciya jinya ssida yayi. Bayan aurena da shekara biyu ya auri Yemisi ƴar ƙawar Iyaa.
"Me yasa daya kawo baki bari na zo kin nuna mun ba?" Kai na sauke ƙasa ganin yanda fuskar Gwadabe ta sauya launi.
Ka yi haƙuri in karɓar da nayi ya ɓata maka rai. Amman ba roƙa nayi ba, har gida ya kawo mun. Gwadabe ka rage ƙiyayyar da kake yi ma Burodami Debisi, dan shi ya ɗauki ɗawainiyar rayuwata tun daga yarintata har tasowata. A matsayin wa nake ganinshi, shima bani da wani matsayi a wajenshi daya wuce na ƙanwa"
"Ki tsahirta mun haka nan Iyabo. Ai nasan wanki ne, sai dai ai wa ne irin wanda akwai aure a tsakani. Danni na kasa gane menene manufar Debisi sonki yake yi ko tausayinki" Zim naji jikina yayi, ba wannan bane karo na farko da Gwadabe yake ƙumaji sabida debisi ba, kuma ba fa zargina yake yi ba ni na ɗauka a matsayin yana tsare mutuncina da nashi ne baki ɗaya.
Gwadabe..." Hannu ya ɗaga ya dakatar dani. Ya soma cin abincinshi zuchiyarshi cunkushe da kishin Debisi har ya gama tsakanin ni dashi babu wanda yayi ko tari, sai ja da sauke numfashi da muke yi.
"Batun kuɗin asibiti kuma shima Debisinne ya biya ko, so kike ya samu hujjar ganin kamar bana ƙoƙari a kan ki ko? Bayan kinsan komai da irin tsanar da ake nuna mana. Kina fa gani ƴan uwana ma bana neman taimakonsu"
Nasan idanun Gwadabe ya rufe da kishine, shi yasa nayi murmushi nace.
Ashe na fika dauriya da haƙuri tunda har na iya haɗa ɗaki da matar da akeson a aura maka. Matar data baro gidan mijjinta sabida kai. Haba Gwadabe in hankali ya gushe hankali ake turawa ya nemo shi. Ko da Burodami ne ya biya kuɗin asibitina bai kamata ace an yi fishi dashi ba, ballema Burodami kokodeen ne ya biya komai da komai." Shiru yayi mun, yasha jinin jikinshi, dan maganata tamkar na ɗaureshi da jijiyoyin jikinshi ne.
"Kiyi haƙuri da fishin dana nuna, kishinki ne yai mun yawa. Amman nasan har ga Allah kin fini dauriya da mayar da komai ba komai ba. Mala'ikun Allah ku shaida na sa ma rayuwar Iyabo albarka." Ajjiyar zuchiya na sauke tare da yin dariya. Shima dariyar yayi.
"To leshi da kika ɗinka mana shi kuma ta ina kuɗin ya ɓullo?"
Labarin yanda akayi na tara kuɗin na bashi tare da kayan kwancen da aka bani a gidan aiki. Miƙewa tsaye nayi na ɗebo mishi duk kayayyakin da na samu na suna, da duk kuɗaɗen da aka babbani.
Ka gansu duk albarkar haihuwa ne, kasan ƴan biyu akwaisu da farin jini" Dani dashi mu kaita wauware kayayyakin muna kallo, muna hirarmu ta yaushe gamo, ina bashi labaran abubbuwan da suka faru shima yana bani labarin yanda suka kwashe da Babala kan batun sunan yara da ya saka. Da ankon leshi da muka yi, ashe Babala har kuka saida tayi, wai Gwadabe ya zama beyeraben dole.
"Kaya sun yi kyau an gwangwajeki da kaya gaskiya, babu abinda zance sai Allah ya amfana. Sunan yazo mun da sauƙi wallahi ko da yake ance ko wanne yaro da arzikinshi yake tafe"
Gaskiya ne kam. Allah ya ƙara rufa mana asirinmu fid duniya wal akira"
Gwadabe yace.
"Ameen dai Maman ƴan biyu. Toh yanzu me kike ganin ya dace kiyi da kuɗinnan tunda kinga suna da kauri, in yaso sai ki haƙura da zuwa gidan mutane aiki, dama ba asan raina kike zuwa ba, tunda na samu aiki ƙwaƙƙwara a hannuna kema ki miƙe ƙafarki ki huta kamar yadda ko wacce mace take hutawa ko?"
Miƙewa nayi na tattare kwanukan daya gama cin abinci na fito falo dasu. Abun mamaki Laila na gani a laɓe tana sauraren hirarmu da Gwadabe. Tana ganin fitowata tayi kamar maiyar da aka kamata ƙiri_ƙiri tana lashe kurwar surukarta, har wayarta tana faɗuwa a ƙasa tsabaragen kaɗuwa. Tsaki nayi mai ƙarfi na harareta. A cikin bahun na zuba kayan wanke_wanken na rufe da bahun na yi komawata ciki. Gwadabe ya sake dawo da maganar sana'a tsabaragen ɓacin rai yasa ban iya ce mishi komai ba, na tuɓe kayan jikina na zura doguwar rigar baccina, nayi hayewata gado na juya bayana ina hawaye." Cikin ɓarin jiki Gwadabe ya hayo gadon yasa hannunshi a kafaɗata, yayi amfani da ƙarfi wajen juyo dani, hawayen da yaga yana tsiyaya ta gefen idanuna ne yasa ya kasa magana. Cikin rishin kuka nace.
Yaushene Laila zata bar ɗakinnan Gwadabe ka sanar dani a darennan, wacce hanya ka sama mana ta yanda Laila zata bar gidannan? Ni da ɗakina Laila bata Isa ta hanani zaman lafiya ba, nagaji Gwadabe ni gidanmu zan tafi" Na ƙarashe zancen da rushewa da kuka mai gunji, ji nake yi zuchiyata na yi mun tuƙuƙi. Rungumeni Gwadabe yayi tsam a ƙirjinshi yana rarrashina, amman fur naƙi rarrasuwa. Ana cikin hakane muka jiyo wani ihu daga falo mai razanarwa, wanda yai sanadiyyar farkarmun da yara daga bacci suka saki kuka a tare. Kafin in ɗaukesu muka sake jiyo ihun a karo na biyu. Da sauri Gwadabe ya fita na mara mishi baya da ƴan biyu a hannuna. Me zamu gani hmm Laila muka gani a kwance tana burgima tsaraicinta na fitowa, sai ihu take kwarmayawa. Har ɗan diras ɗinta muna hangowa fari sol dashi, da sauri Gwadabe ya kawar da kanshi gefe. Kafin kace me matan gidan sun cika ɗakin, Laila na ganin haka saita soma kwaɓe suturarta tana fatali da'ita. Ba shiri Gwadabe ya fice a ɗakin. Sai adda'a aketa faman tofeta dashi ita kuma tana ta surutai. Mamanta na ƙurama idanu farare sol dasu luwai_luwai ko wacce mace nayi imani zata so dama itama mamanta haka yake. Kuma Gwadabe fa ya ga maman nata, dan sai da ta yar da rigar maman kafin ya fita har yana tuntuɓe hawayena na share dan nayi imani babu wata iskar dake damun Laila tsagwaron iskanci da makircin data riƙa a matsayin makamin da zai fitar dani daga ɗakina ita ta maye gurbina kenan. Ina tsaye a gefe na kasa daidai da motsawa jiri ne ke shirin zubar dani, da zanyi gigin ɗaga ƙafata tabbas da jiri ne zai kwasheni ya zubar a ƙasa tim.
"Sannu Laila Allah ya baku haƙuri. Haula kawo ruwa a bata tasha, ƙilama wani agumun aka mata danta bar gidan a haukace, tunda mu a iyakar saninmu Laila bata da iska." Cewar Yaya Halima wacce take riƙe da kafaɗun Laila. Gude ta ɗauki zani a kujera ta suturta mata ƙirjinta dashi. Ni dai ina tsaye ina kallon bariki. Ruwa aka bata tasha, Babala tace ta kwanta ta rufe idanunta. Ta ko kwanta ta rufe idanta ruf.
"Toh Allah shi kyauta, Allah yasa ba mayu bane ma suka kama mata kurwa ba, kunsan jiya an yi taron na ayya"
Cewar Babala wacce take hanyar ficewa daga ɗakin. Ina tsaye duk suka watse suka barni, sai muryoyinsu nake jiyowa a ƙofar ɗakina. Rigar maman Laila na bi da idanu kawai na yi ƙuta tare da shigewa ɗaki na kwantar da ƴan biyu da suka koma baccinsu nima na kwanta ina share hawaye mai zafi. A wannan dare Gwadabe ya sha rarrashi sosai, dan birkice mishi nayi kamar lalatacciyar besfa, da ƙyar ya iya shawo kaina a wannan dare.
Washe gari muka wayi garin babu walwala sam daga ni har Gwadabe, dan shi kanshi ina ankare dashi da damuwar da tafi tawa ya kwana. Bayan sun dawo daga sallar asuba ya shigo, sai yace
"Bari in ɗan kwanta kaina saramun yake yi sosai, zazzaɓi ne ma yake son kamani"
Sai jikina yayi sanyi, a tausashe nace dashi.
Allah ya ƙara afuwa, sannu inka karya ina da fanadol sai in baka ka haɗiya" Har ya kwanta sai kuma ya tashi, ina shirin ficewa a ɗakin kenan zan juyo ruwan wankan ƴan biyu.
"Dawo ki zauna Iyabo mu yi magana " Babu musu ko kafiya a tsakaninmu, cikin saurin bin umarninshi na zauna ina fuuskantarshi.
"Wallahi Iyabo ko tsirara Laila zata yi a gabana ba zata taɓa burgeni ba, domin bana daga cikin mazan da suka fifita kyawun mace, ko dirinta. Ni kyawun halinki, da haƙurinki ya fi ye mun komai. Ai mace ta gari farin cikin rayuwar duniya ce. Zance na gaskiya bani da wata hanya da zan bi in kori Laila a ɗakinnan. Ina gudun yawan fishin da Babala take yi a kaina. Dani dake mu yi haƙuri ki taya ni mu yi mata biyayya ta zauna ɗin,in taga dama ta zauna har mahadi ya bayyana, zata ɓata ma kanta lokaci a banza, dan ko matan duniya sun ƙare Gwadabe ba mijin Laila bane. Iyabo na ƴar duma_duma mai hanci a tsakiyar kumata itace nutsuwata. Kiyi haƙuri nasan na danneki da yawa" Shiru nayi kawai ina wani tunani, har ga Allah Ni kam ina yaye Taiwo da Kahinde aurena da Gwadabe yazo ƙarshe ma, nasan ina tafiya babu makawa Laila burinta zai cika na mallakar Gwadabe a matsayin miji. Iyakar son da zan yima Gwadabe kenan in zama tarihi a cikin labarinshi, ko dan ya samu rabauta, dan fishin iyaye bala'ine babba akan yara musamman fishin uwa al'amarin da girma yake"
"Baki ce komai ba Iyabo" Ɗagowa nayi muka haɗa idanu nace.
Babu komai Gwadabe, zan tayaka biyayya ma Babala ka samu aljanna ta hannunta, Laila taci gaba da zamanta kuma in sha Allah bazan sake asarar hawayena akanta ba. Dukkan wata ƙaddara ko jarabtar da zata samu bawa daga Allah ne, dukkannin wani tsanani baya dauwama face sauƙi ya samu." Ina gama faɗar hakan na miƙe na fita cikin dakiyar zuchiya muka gaggaisa da matan gida suna tsakar gida anata hada_hadar aikin daya zamema mata jiki a rayuwa. Ɗakin Yaya Haula na shiga na durƙusa a gaban Babala na gaisheta, saida nayi baki biyu kafin ta amsamun a yatsine. Yaya Halima kuwa ciki ciki ta amsa, ni banji sautin muryar tata ba ma, sai dai labɓanta da naga sun motsa. Har zan fita Babala tace.
"Zo ki zauna Iyabo inason magana dake" Dawowa nayi na zauna kaina a ƙasa ina wasa da gezar majanyin ashoke dana goye Taiwo da Kahinde dukansu a gadon bayana.
"Ba komai bane yasa nace kizo ba dama. Kuɗi nake son ki bani kamar dubu talatin haka, inason zan sai taki in tafi dashi, nayi magana da Baban Nazifi hidima tayi mishi yawa, ke kuma naga kin samu kuɗi a wajen suna sosai"
To Babala bari in kawo miki"
Na miƙe na fita ina jinjina wannan lamari. Nera dubu talatin cib na ƙirgi na kai mata, tako sa hannu ta amshe ba sannu bare madallah. Harna yi ma ƴan biyu wanka na shiryasu ina ta'ajibin wannan al'amari. Toye na ja muka fita tsakar gida nayi mishi wanka a ƙofar ɗaki ya shigo. Ban gusheba sai da na ɗauraye kayan da ƴan biyu suka cire da wanda nasa naci suna, da wanda nasa jiya, dana Gwadabe duka. Kafin in gama wankin matan gidan suka cike igiyoyin da shanya tsab. Sai mayafi na yafa na shiga gidan maƙota na yi shanyata. Ɗaki na shiga na shinfiɗe ƴan biyu a gado, Toye kuma na shafa mishi mai, yasa kaya. Ina juye ruwan wanka na mayar da ruwan kunu kan wutar. Ina fitowa na dama kunu na juye a jug ɗin silver na mayar da ɗumamen tuwon jiya. Ɗaki na shiga na shirya tsab cikin jar atampa sabuwa fil ɗinkin dai buba da zani, yana cikin kayan suna da Iyaa ta hado mun dashi, na murza kwalli da jan baki, na bi jikina da body milk na Mrs Bukhari, na shafa har a ƙasan mamana kunsan masu jego sai da ta'amali da ƙamshi. Ina gyaran falo Gwadabe ya fito daga ɗaki. Murmushi nayi mishi, shima murmushin ya sakar mun.
Yallaɓai ka tashi, ya kan naka?" Bai amsa ba sai da ya haɗe jikinshi da nawa, Laila fa duk abinnan tana naɗe a doguwar kujera tana bacci.
"Lafiya lau Iyabo, sai kewarki a shinfiɗata. Irin wannan kyau haka Babbar mace kenan, cinyar sa maganin mai haɗama"
Dariya muka kwashe dashi kamar babu matsalar dake damun mu. Inason in ji Gwadabe ya kirani da Cinyar sa maganin mai haɗama, ko Babbar mace, daya faɗa sai in jii ƙibata ta sake burgeni, barenma in nai kwalliya, dan kwalliya tafi amsar masu jiki irinmu.
To yanzu dai karyawa zaka soma yi ko wanka?" Ido ya kashe mun yace.
"To ba sai ki zaɓar mun ba kawai, tunda dai ni mijin Hajiya ne"
Ina dariya ciki_ciki nace.
To ka soma da wankan, zaka fi jin daɗin karyawar. Ina faɗar haka na fita, har na juye mishi ruwan a bokiti zan je rijiya in sirko, sai ya riƙe hannun bokitin ƙarfen yace.
"In banda fitina irin taki kina jego ina ke ina aiki, gafara cus kawai."
Ya ɗauki bokitin yayi bakin rijiya dashi. Baban Nazifi dake zaune a turmi yana rage ƙasumbarshi da aska, ya ja tsaki yace.
"Allah wadaran naka ya lalace, Laila da majnun ma ƙarshen tarihin soyayyarsu sam babu armashi a ciki. Gwadabe kayi asara shanyayye fitsararre"
Ya ci gaba da askinshi, ni kuma na shigewata ciki. Ina haɗa mana abun karyawa a tire mandiya hamshaƙiya ta tashi. Tsaki ta buga, ta fice fuu. Ni kuma na girgiza kai kawai na dure mana abincin a gefe, ni na tattare mata kayan rufarta na sa mata a saman akwatunanta. Na kunna turaren tsinke na Baba flora ɗakin ya biɗe da ƙamshi. Ina zaune ina kallon wani kaset ɗin yarbawa, shiru_shiru yau Gwadabe zai shigo, gobe ne, har goman safe bai shigo ba. Ni kuma yinwa sai sasiƙata take yi, abinci na zuba na soma cin abuna. Ina kan ci wayata na jiyo kukanta daga uwar ɗaki, da sauri na shiga ɗakin. Wata number ne ba suna, ina karawa a kunne na jiyo muryar Gwadabe.
"Nine Iyabo. Kiyi haƙuri muna asibiti tare da Babala. Na je dubata na tarar zasu koma asibiti shine muka tafi tare, muna gamawa zan dawo. Kici abincinki kinji? Zan tawo da cefane"
To Shikenan Gwadabe Allah ya ƙara mata lafiya, sai kun dawo. Dan Allah ka gaisheta sosai da jikin."
"To shikenan Babbar mace zata ji, ki kula mun da kan ki" Mu kai sallama na ajjiye wayar. Ina gama karyawa sai na shige ɗaki har bacci ya soma ɗibata sai naji ana tattaɓani kamar a mafarki naji ana kiran sunana. Ina buɗe idanu naga ashe Uwani ce."
Kai Uwani irin wannan duka haka" Na faɗa ina miƙewa zaune.
"Ke dai bari Iyabo, damuwace ta ciyo ni shine na kasa haƙuri sai da na tawo. Amman kafinnan akwai abinci a gidan in ɗan sama cikina, tun duku_duku na bar gida babu abunda naci"
Ki fita falo zaki ga tire akwai dumamen tuwo da kunu"
"Yanzu kuwa zaki ji labari Iyabo in na take cikina"
Fita tayi sai gata da tuwo shaƙe da kwano da kununta cikin ƙaton kofi, bayan taci ta yi gyatsa tace.
"Tun safe ni da matan gidanmu muka fita muka bazama gari neman aikin yi yinwa na shirin halakamu da yaranmu. Da ƙyar muka samu aiki mu huɗu. Wani sabon asibiti da aka buɗe a bakin titin layinmu to anan ni na samu nawa aikin na wanke bayangidun asibitin, Hafizu kuma Allah ya so shi ya samu gadin get da ƙyar wallahi, a hakanma saida nayi mishi jan ido ya karɓa, gani yake shi yafi ƙarfin gadi, matar gidanmu kuma nata aikin shara da goge gogen ƙasa ne. Iyabo albashin bashi da yawa sam wannan rayuwa ni nama rasa yadda zan tsoma kaina a ciki ga matsalar gidan haya. Shaddarmu fa wata biyu kenan data rufza me gidan yace bazai gyara ba mu da muke haya a gidan mu zamu gyara. To mu bamu ci ba balle har mu iya gyara masai sai dai fa ko wacce mata tayi kashinta a po ta ɗauka taje ta watsa. Gabaki ɗaya gidan sai wari kawai"
Jigum nayi ina saurarenta, yinwa bata da daɗi sam ni kaina a baya mun sha kwana da yinwa mu wayi gari babu abinda zamu ci sai ruwa.
Uwani rayuwar ta zama sai a hankali, gashi mutane basa son taimako daga ƙwauri sai guiwa kowa nashi ya sani. Amman a ƙalla aikin zai rage muku sosai, sai ku gina rayuwarku akan albashin da kuke ɗauka kusan yanda zaku tsara komai. Allah yasa dai mu dace kawai amman rayuwarma wataran sai kaji duniyar ta fice maka fit a ranka in matsaloli suka haɗu suka cakuɗe maka. Jiya da kinga irin tashin hankalin dana faɗa da daddare da kin tausaya mun sosai" Nan na kwashe labarin iskancin Laila na bata.
"Kusun uwa kuma baki yi kukan kura kin dira a wuyanta kin narki shegiya ba?"
Kai na girgiza tare da cewa.
Hmmm motsi ma wannan na kasa. Ni da nake zaune a ɗofane Uwani ai ina taɓata zata jijjigemun auren nawa ne, kinga burinta ya cika ai ko?" Sai kuma ta sakko tace.
"Sai dai dan hakan amman in ba haka ba wallahi da saita gane kuranta. Amman ke haka zaki zuba ido kuci gaba da zama da'ita ko yaya kike so?" Miƙewa nayi tsaye na ɗauki Taiwo na saɓa a baya, na sake sa hannu na ɗauko Kahinde sima na sashi a kusa da ƴar uwarshi, na ɗamaresu tamau da zanin goyo na bisu da majanyi. Hijabina na zura, na saƙa hannu a ƙasan kayana dake jere a wadrop na ciro kudaɗe na soke a giyo.
Mu je ki rakani in yo cefane kinji in ɗaura abincin rana, dan Gwadabe suna asibiti da Babala, bansan ko gado za'a kuma basu ba, ko zasu dawo gidaba, ya kamata in gama abinci da wuri" Fita a gidan mu ka yi muna tafe sai tauna matsalolin dake ci mana tuwo a ƙwarya muke ta ta faman yi. A wajen wata beyerabiya mai kayan miya da niƙa na sai tumatiri da albasa da attaruhu, rabi na gyara a wajen na wanke ta niƙa mun, dama mun fito da robar fenti, rabi na ƙunso abina na sayi ɗanyan kifi shawa da su maggi a wajenta, Uwani ma na sai mata haɗin kayan miya na ɗari da hamshin, maggin hamsin, man hamshin, sai kifi ɗanye na hamsin, sai murna da godiya take yi mun. Muna dawowa gida na shiga aikin abinci, ni ina jajjage Uwani na yi mun tsintar shinkafa. Matan gida sai shewa suke yi, ko wacce tana girkinta a ƙofar ɗakinta, Yaya Haula kuwa kajine cikin tukunya take ta aikin musu jar suya gidan ya karaɗe da ƙamshi, Suwaiba kuma kifi take soyawa sukumbiya ɓula_bula, ga jajjage kayan miya tana yi, ga alayyawo ta baje akan tabarma. Kullum su kam a cikin cin daɗi suke kullum baren ma Yaya Haula tunda mijinta kusan shine mai kuɗin familyn baki ɗaya ma. Tukunya na ɗaura na zuba mai na jefa ɓararriyar tafarnuwa guda, man yana yin zafi na zuba jajjagena, na wanke kifina tas na tsaane a kwando, ai sai matan gidan baki ɗaya kallo ya dawo gareni kawai dan hakan sabon abune a tukunyarmu gaskiya, barmu dai da yin fara da mai, ko tuƙa amala da miyar ewodu ko mai babu. Yaya Haula tace.
"Lallai bana abun arziki muma ya biyo ta layin gidanmu har mun samu, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta" Sai suka saki shewa dukkansu, ni kuwa ko in kula na gama tsayar da sanwar girkina nasa ma uwani hannu muka ci gaba da tsinta. Sai bayan azahar girkina ya sauka na juye tumaturina a tukunya na mayar kan gawayi. Waya na ɗauka na kira Burodami Debisi nace inason nama na dubu biyu dan Allah ya turo yaro dashi. Bayan mun gama cin abinci sai ko ga yaro da nama cikin ƙaramar baƙar leda dam harda kayan miya cikin leda mai zane, yace kuma in bar kuɗin naman. Allah sarki ɗan uwa mai daɗi kiranshi nayi na dinga yi mishi godiya, ina ajjiye wayar sai ga kiran Gwadabe ashe sun dawo Yana ɗakin Umman Nazifi. Abinci na tafi musu dashi, na gaishe da Babala da jiki, na ɗan jima a ɗakin kafin na fito."
MRS BUKHARI
3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank
Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya.
Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE)
300 kacal zasu iya kuɗin karatu
NAMA YA DAHU...
ROMO ƊANYE
GAWURTATTU UKU
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
8
A kwana a tashi A haka rayuwarmu tai ta garawa, yau fari gobe tsumma, babu laifi Alhamdulillah yanzu kam munfi ƙarfin abinda zamu saka a bakin salati. Koda yaushe Gwadabe a cikin tafiye_tafiye yake, duk garin da ya je yakan siyo mana tsarabar garin, su bushasshen kifi, manja, doya, wake, gawayi duk yana siyowa ya kawo. Babala ta jima sosai a gidan sai data warke tsab, ana gobe zanyi arba'in ita kuma ta tattara ta koma ƙauye. Irin ƙoƙarin da taga Gwadabe nayi a kanmu sai ya sake dagula komai. A tsakar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 16