Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na shiga ɗakin yaranta, sai da na goge kayayyakin dana wanke tas kafin na miƙe lokacin anata kiraye_kirayen sallar azahar. Na jera na yaran a sib ɗinsu, na Alaja kuma na kai mata ɗakinta na saka mata a sib. Na gyare mata ɗakin tas. Kafin nayi salla kuma. In idar da sallah sai na tsinci kaina da rashin aha'awar komawa gida. Sai na tsiri gugar kayan da Hajiya ta bamu, tunda a wanke suke, sai ƙamshin turare mai daɗi suke yi. Dana gama wajajen biyu da rabi dai dole na fito daga ɗakin yaran ina riƙe da buhun kaya da Toye. Robar da take zuba mun abinci ta miƙo mun, da wata farar roba babba mai murfi tace. "Miyar ganye ce a cikin robar nan, ta ɗan jima a firji ne bazan iya amfani da'ita ba bansan ko kina so ba?" Karɓar ledar nayi nace. Inaso Alaja. Aidupe ( Nagode) Nayi mata sallama muka kama hanyar komawa gida. Ga buhu a kaina, ga leda a hannun hagu, ga Toye ina riƙe dashi, ga uban ciki mai tsini a gaba, ina tafe da ƙyar duk jikina ciwo yake yi mun. Da sallama na shiga gidan, tsakar gidan tsit kamar ba gidan hayaniya da shewa ba. Turus na tsaya a daidai tagar ɗakina bakina a sake, furucin Laila na ƙarshe a waya ne ya daki kunnena. "Ai in sha Allah na shigo kenan sai dai ta fita ta bar mun ɗakin, Gwadabe nawane halak malak" Sai ta saki Dariya. Murya a daƙile nace. Salamu Alaikum. Nasa ƙafa na shiga, tayi saurin kashe wayar da take yi. Na ƙare mata kallo da kyau. MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU.. ROMO ƊANYE BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI. Lamba ta biyar (5) Saye take cikin shuɗiyar atampa, ta ci kwalliya da jan baki da hoda, fararen idandunanta rambaɗe da kwallin daya sake fito da hasken fatarta. Sai wani ƙamshi take yi ita da falon. Haƙiƙa na tsorata da Laila da muguwar nifaƙar dake tafe da'ita. Amman in ta san wata ai bata san wata ba. Wanda ya riƙe Allah shi ke da gagarumar riba, nasara tana biye dashi. Dan duk nisan jifa dole ya dawo ƙasa. Kallon dana cikata dashi shi ya jefata cikin taraddadin daya kasa ɓoyuwa a fuskarta. Murmushin dole na sakar mata na yi shigewata ɗaki, na zauna daɓas a kan gado ina sauke numfashi kawai. Tagumi na zuba ina tunani. Na jiyo murya a falo kamar ta Burodami Debisi. Da hanzari na leƙo ai kuwa shi ɗinne a tafe da abubbuwan arziki. A guje Toye yaje ya ɗafeshi, shi kuma yayi maza ya rungumeshi tsam a jikinshi. Ɗagowa yayi ya ƙuramun idanunshi, nima shi nake kallo. Burodami barka da zuwa" Na faɗa tare da ƙoƙarin kawar da kallon da yake yi mun. Hijabi na zura , ban fito ba sai da na zuba mishi abincin dana dawo dashi daga aiki. Jallof ɗin taliyace ta ji bushasshen kifi, na zuba ruwa a kofin roba, na ɗaura a tiran roba, sai na fito. A gabanshi na dire tiran, na sake komawa na zubo ma Laila da Toye abincin bai yi ragowa ba, ga raina ya biya ina fatan Burodami Debisi ya ci ya rage in samu in lasa. Miƙoma Laila abincinta nayi, Toye ma na zaunar dashi a leda ya soma cin nashi. Ekabo Burodami ( sannu da zuwa Yaya) Ya gida, wa ni Iyawo re bawo ni ebi re? ( Ya Iyaninka) Murmushi yayi mun yace. Awon ti wani ol atanran. Bawo ni o se wa ( suna lafiya, ya kike?) Ohh mowa daa_daa ( lafiya Ƙalau) Ga abinci kaci karya huce. Abincin ya kalla nima ya kalleni, saurin kawar da kaina na yi gefe guda. Murmushi yayi tare da girgiza kanshi. "Ba zama nazo yi ba. Kuma in naci abinci anan, in na koma gida Emisi ba zata ji daɗi ba in nace mata na ƙoshi, dan na barota tana ta faman dakan sakwara" Wani yawu ne na jarabar kwaɗayin masu juna biyu ya tsinko mun jin an ambaci sakwara, muƙut na haɗiyeshi kawai, dan bani da yanda na'iya. "Ga TV da dvd, da kafet na kawo miki, na sauya ma Emisi kayan ɗakine shine na raba muku tsofaffin. Yanzu haka daga gidan Simbin Maman Kokodeen nake na kai mata labulaye da kujeru" Har ƙasa na tsugunna ina ragargazo mishi godiya, dan nayi farin ciki sosai, a cikin gidan ni kaɗaice bani da kayan kallo. Wataran matan gidan suna haɗuwa a ɗakin mutum ɗaya su harhaɗa kuɗi a yo renting ɗin kaset sai dai in jiyo sauti, muna dai da rediyo da muke sauraren labarai, harma wataran in saka kasetin waƙar yarena, dan Allah yayi ma yarbawa baiwar iya waƙa da son rerata, dan ko karatu zamu yi da waƙe muke yinshi, gamu da son sha'ani a taru taci asha ayi ashobi. Dubu biyu ya zaro ya ajjiyemun mu kai sallama ya fice. Kinkimar komai nayi na shigar ɗaki, na dawo na ɗauki abincin nayi shigewata, Laila na zaune bakan a zaune tayi tsit da halama saƙa take yi da mugun zare a ranta. Da daddare Gwadabe ya kirani mu ka ɗan taɓa hira ba mai yawa ba dai haka, yai mun albishirin ƙila jibi ko gata ya dawo da izinin Allah. Fatan alkhairi nayi mishi, tare da samun alkhairai. Washe gari ma kamar jiya ina gama komai na tafi wajen aiki abina. Ina dawowa tun daga bakin zaure na fahimci masu waje sun dawo mai tabarma dole ya naɗe, dan muryoyinsu har waje nake jiyosu ana mayar da yanda akayi da yanda za'ayi. Da sallama na shigo amman babu wanda yaji balle su lura da shigowar tawa. Karab a kunnena na jiyo Laila tana faɗin. "Ai ku baku ga irin kallon soyayyar da take ma farkan nata ba. Wai ni zasu ninke baibai. Ya kawo TV da dvd harma da kafet ƙato, ga kuɗi fa. Bai tashi zuwa ba sai da ta ga ba idanun Gwadabe" Yaya Haula tace. "In banda abinki Laila yarbawa ai sun saba iskanci wannan ba wani abu bane. Su da suke zaman wa jo ko, yarinya tana gaban iyayenta saita koma ɗakin saurayi, wai da sunan gwajin mahaifa, sai ya ɗirka mata ciki zata dawo gidan iyayenta. Kiga anata murna abu yayi kyau zata auru. In kuwa juyace shikenan an shata musulla. To su da suke haka har dan tsohon kwarton Iyabo ya biyota ɗakin aurenta wani abunne?" Ƙirjina take naji yana fat_fat_fat take numfashina na soma jin yana karkatsewa. Ban yi aune ba na jiyo muryar Gude tana cewa. "A can gidansu ma fa ɗakinsu ɗaya akace, tare suke gwamutsuwa su yi baccinsu, kinsan yarbawa dai sai a hankali basu cika hankali ba. Ni dai na rasa uban abunda Gwadabe ya gani a jikin beyerabiya wacce ƴar uwarshi Bahaushiya bata dashi. Ita ba kyauba, sai gandar baki da kayan ɗuwaiwaka ɓaka_ɓaka iyakar abinda matansu ke dashi kenan fa" Dariya suka saka dukkansu. Da Suwaiba muka haɗa idanu ina tsaye kasaƙe ina jin irin sharrikan da ake bina dashi. "Ahh kin dawo ne Iyaa Toye shine ba ko sallama?" Ta kula ni ne domin ta ankarar da abokan gulmar tata tai musu isharar wanzuwata. Ai kuwa sai su kai kamar ruwa ya cinyesu kawai. Hmmm e nadawo, ai nayi sallamar hira ce tayi daɗi shiyasa baku ji ni ba. Sannunku da hanya." Ina kaiwa nan na yi wucewata zuwa ɗakina. A saman kujera na zauna ƙirjina na soya mun. Da ƙyar na iya sa abinci a bakina, salla ma a daddafe nayi, kawai sai na ji na zama marar lafiya gaske. Sai tubka da warwara nake yi a zuchiyata hakanne ya hana ni sukuni da numfashi me kyau. Tun dawowar su Yaya Haula daga Takai, al'amuran gidan suka sake jagwalgwale mun. Sabon gulma da tsigudidi aka buɗe sabo. Laila kuwa irin ado da kwalliyar da take yi yana firgitani sosai. A tsakar gida suke wuni gulma da shewa, a gabana suke yi ma Laila adda'ar samun damar warce zuchiyar Gwadabe, tana amsa musu da Ameen. Ranar da Gwadabe ya faɗamun zasu shigo Kano da safe ina zaune ina wanki a ƙofar ɗakuna, ina ɗan waƙe_waƙenmu na yarbawa. Baban Nazifi ya fito daga banɗaki, dake banɗakin gidan a kusa da ɗakinmu lungun yake. Har ya wuce sai ya dawo da buta riƙe a hannunshi. "Wadannan randunan naki, da gayyar tarkacen robobinki, da wannan kwantenar da kike girki a ciki sun tsushe hanyar wucewa ban ɗaki. Sabida haka ki tattare komai a wajen ki sam inda zaki ajjiye, irin wannan tarkace suke lalata gida. Yana gama faɗar hakan ya wuce yana mita. Sukairaju wanda fitowarshi daga ɗaki kenan yace. "Yaya Hambali magana kake yi ne?" Ya tambayeshi. Cikin ɗaga murya dan in ji yace. "Da wannan masu kwalo_kwalon nake yi, kasan yarbawa da ƙazanta gasu ta tarin shirgi, ca nayi ta kwashe randunanta sun tare hanya." Harisu dake ɗaki sai ya amsa da cewa. "Yaya Hambali ai nima fa na jima ina son ince tarkacen lungun su Gwadabe yayi yawa, in zaka je banɗaki sai ka ta ture bokatai kafin ka wuce" Kaina na sauke ƙasa kawai. Gabaki ɗaya akan wannan maganar sai da kowa ya tofa albarkacin bakinshi. Ni dai da zafin zuchiya na gama wankina na nufi bakin rijiya zan ɗebi ruwa. Laraba ƙanwar Nazifi ƴar Yaya Haula kenan, tana bakin rijiyar tana ɗiban ruwa. Laraba ɗan zuba mun ruwa guga biyu nayi ɗauraya bayana ya riƙe" Ai ina rufe Baki Suwaiba ta iso inda muke da bokatanta da bahunanta itama zata ɗebi ruwa. Da safe duk matan gidan muke ciccika kayayyakin aikinmu, da randunanmu da ruwa. Buɗar bakinta tace. "Harda su kaza acin danƙo. Akanme yarinya uwarta ta sata aiki, zaki dakatar mata da aikin da aka sata kice ta zuba miki? Laraba in kin gama bani gugar" Ina tsaye Laraba ta gama jan ruwanta ta tsab sai ta miƙo ma Suwaiba guga. Ni ko nasa hannu na warce gugar a hannun Laraba. Na zura a rijiya. Suwaiba ta nemi kamani da kokawa a bakin rijiya, ai kuwa na dubeta nace. In ki kai wasa zan miki hajijiya in jefaki cikin rijiyarnan Allah, ki shiga taitayinki ba fa tsoro nake ji ba, ina dai son mu zauna lafiya ne. Da sauri Suwaiba ta matsa dan ni ɗin ƙatuwace tubarkalla masha Allah, kun dai san matan yarenmu akwai ƙiba babu laifi, gani da mazaunai a sama ɓaka_ɓaka masha Allah. Nan matan gida su kai mun ca a kaina, kowa na tofa albarkacin bakinshi, Gude har tana zunguremun kaina. Mazajen gidan a lokacin sun fita nema. Ni dai har na gama kab aikina na tsakar gidan, basu dena kwashena iyayena da dangina albarka ba. Ina shinfiɗa kafet ina hawaye harna gama shinfiɗawa, na saka tv da dvdn a inda ya dace, ɗakin sai ya sake sosai. Randunana na kwasosu na saka ɗaya a bayan ƙofar falo, ɗayar a uwar ɗaki, bokatan na ɗaurasu akan randar falo, bahunan kuma na ɗaura a saman randar uwar ɗaki, na fita na share wajen tas na shigo ciki. Duk fa wannan aikin ina jin ciwon mara da nake kyautata zaton haihuwace. Ina ninkin kaya na ji ciwon na ƙaruwa mun, ina jiyo ɓuruntun Laila a falo. Waya na ɗaga na kira Uwani Tabalbalin ,da Bose na sanar musu ina naƙuda, Bose kuma ta kira gida ta sanar, a cikin ƙasa da awa guda sai gasu dukkansu afujajan. Gashi ko reza bamu ajjiye da sunan haihuwarba, ta abinda zamu sa a bakin salati muke yi. Zaman dirshan nayi a ƙasan leda, sai zufa nake yi, ina ɗan nishi sama_sama su nai mun sannu. Ana cikin haka sai ga Yaya Mulka matar Burodami kokodeen, babban ɗa a gidanmu ta iso. "Yaya jikin nata Bose? " "Gashi nan dai tana ta fama, ko dai zamu kaita asibiti ne? Ƴan biyu ne fa a cikin ina tsoro" Ni da naketsakanin rayuwa ko mutuwa na shiga ɗaga musu hannu, ina musu nuni da su barni bazan je asibiti ba. Amman da ciwon yai tsanani gashi harna soma galabaita, babu shiri suka ɗaukeni, Burodami kokodeen ya zo da mota ƙofar gida. Matan gidanmu sai gani su kai an rirruƙoni mun fita. Sai faɗi suke "Au naƙudarce mu da muke cikin gida bamu sani ba, sai danginki kika kira? Yarbawa munafurci a jininku yake. Wannan ai iskanci da rashin daraja dangin mijine" Bansan wacece ta yi maganar ba, amman babu wacce ta tanka mata. Uwani maza je ki rufo mun uwar ɗakina. Na ƙarashe faɗe ina nishi. Tabalbalin:. A guje ta shiga gidan, tana shiga ɗakin Iyabo taga matan gidan a ɗakin cirko_cirko. Turus tayi da ta gansu, suma kansu sun dibibice da ganin Uwani. A zatonsu babu mai dawowa, sun shigo gulmar ganin gyara. Tsaki Uwani tayi ta shige ciki tare da cewa. "Aikin banza wallahi duk matar dana fito na sameta uwarta zanci danni ba Iyabo bace." Karo taci da Laila a cikin uwarɗakin gaban sib ta ɗauko sabuwar atampa tana hannunta. "Sata ce ta shigo dake ɗakin kenan? Iko sai Allah wai na kwance ya faɗi. Amman dai su Kulu anyi asara, an yi faɗuwar baƙar tasa, ko kuma ince ƙarkon kifi daga ruwa izuwa wuta, ayi dai mu gani in tusa zata hura wuta." Laila kuwa ba bakin magana ai da kunya an kama uwar miji na sata a ɗakin suruka. Fisge Atampar Uwani tayi. Sum_sum ta fice, Uwani kuma ta rufo ƙofar ta fito ba kowa a falo, tsakar gidanma data fito duk sun yashe. Abundai ba haka akaso ba, wai an yi gulmar uwar miji ta ji. Tana shiga motar suka ja sai asibitin nasarawa." Asibitin Nasarawa. Da taimakon Allah, na haifi yarana biyu, mace da namiji da kaina, sai ƙari da akaimun kaɗan. Tubarkalla yaran manya kamar ba ƴan biyu ba. Sai dai fa ina sauka ma'aikatan kiwon lafiya suka soma tambayar dangina kayan da za'a saka ma jarirai, da abubbuwan da ake buƙata. Ko allura bamu da'ita. Burodami kokodeen ne ya ba matarshi Antimi Mulka kuɗin dukkan abinda ake buƙata aka kawo babu ɓata lokaci. Cikin ƙasa da awa guda yarana an kintsasu tsab a cikin seti me ruwan toka, sun yi kyau sosai. Ɗakin hutu aka dawo dani. Da iyaa Debisi na soma haɗa idanu, tayi kicin_kicin da ranta, da gani kasan ta cika ta batse ƙiris take jira. Ko ma dama can haka take, kullum a cikin faɗa da kumfar baki take. "O ye koju ti e ( Kinji kunya) Ki duba kin haihu a wulaƙance, babu mijinki, babu dangin mijinki, babu kayan jarirai, ba kuɗin asibiti, jibi ramarki. Da ace kinji abinda aketa faɗa miki daba haka ba, da ɗan uwanki kike aure yarenku da kin fi haka daraja, kuma babu mai ƙyamatarki, ballema ya tsangwameki." Duk wannan maganar da yare take yi mun. Tana yi tana buga cinya, tana ɗaga murya tamkar faɗa, bil haƙƙi ita ba faɗa take yi ba maganarta ce haka, ko kuma ince mafi akasarin yarenmu suna da ƙarfin murya, da ihu a cikin magana. Ni dai bani da bakin cewa, dan nasan Gwadabe na ƙoƙari sosai, banso zuwa asibitin ba sabida gujema tashin hankali da tarzoma irin wacce ta afku lokacin haihuwar Toye, an yi ɗauki babu daɗi sosai. Dan ranar suna anci dambe an gode Allah. Burodami kokodeen ne ya katse Iyaa Debisi ta hanyar cewa. "Yarinyar nan Iyaa Debisi ya kamata a barta haka, ko dan rabon dake tsakani, ni ina ganin dukan yayi mata yawa" Miƙewa tayi tsaye, ta tafa hannu tace. "Ahhhh Ahhhh kokodeen Oya were ( baka da hankali)" Nan fa ta sake shiga wani babin, ta inda ta shiga ba tanan take fita ba. Shigo da yaran da ma'aikatan kiwon lafiya suka yi ne yasa ta yi shiru. Ɗakin kuwa Hausawa sai kallonmu suke yi. Iyaa Debisi take ta soma rera waƙa tana rawa na murnar zuwan jikokinta. Suma su Burodami kokodeen nan suka soma rawa suna mata tafi. Tana rera waƙar yarenmu ta musamman da akema ƴan biyu. Gabaki ɗaya ɗakin hankalinsu yana kanmu. Murmushi kawai nayi musu, Uwani kuwa sai zolayar Iyaa Debisi take yi dama sun saba. Taiwo Iyaa Debisi ta riƙe, Burodami kokodeen kuma ya karɓi Kahinde. Sai murna suke yi, domun a ƙabilarmu babban abune haihuwar ƴan biyu, mun ɗaukesu a matsayin wata babbar baiwa da Allah ya bamu. Kuma yarenmu su kansa yaƙinin rayuwar ƴan biyunnan mai albarka ce. Ni dai a haka baccin gajiya ya kwasheni, bani na farka ba sai jefin la'asar. Ƴan uwana sun cika asibiti danƙam sai tayani murna suke yi. Ga abinci iri_iri an kakkawomun. Burodami Debisi ya zubo mun amala da miyar ewodu, da miyar wake, da jar miya dukka, ga ganda haka_haka. "Ga abinci kici ko zaki samu ƙwarin jikin naki, gida zamu tafi" Karɓa nayi na mishi godiya. Ƴan uwa kuma aka shiga yi mun ya jiki, tare da murnar zuwan Taiwo da Kahinde duniya. ( Hassana da Usaini ) Amalata naci nayi ƙat na kora da kunun akamu me zafi, take naji na yi gyatsa mai ƙarfi, bana jin komai garau nake jina tamkar ba ni bace na haifi ƴan biyu ba. Wajajen shidan yamma aka sallamemu muka fito asibiti mota biyu. Duk tare muka ɗunguma mazanmu da matanmu zuwa gida. A tsakar gidan muka tarar da matan gidan kamar dai kullum ana zaman gulma da kace_nace. "Ahh ƴan biyu aka samu kenan? Kai masha Allah barka da arziki Iyabo." Cewar Yaya Haula. Yauwa sannunku" Iyakar abinda nace kenan. A ƴan uwana kuwa babu wacce ta kulasu, suma basu kula kowa ba, mu kai shigewarmu ciki. Mazan a falo suka zauna, mu kuma muka shige cikin uwar ɗakin. Anty Mulka tace. "Abun girkin ki na ganshi a falo. Anan zan dafa miki ruwan wankan ne, ko zan iya fita ƙaddararren tsakar gidan naku?" Sai da na ja numfashi nace. Zaki iya fita dashi ki sa ta gefen ɗakina, kafin Gwadabe ya zo ya kawo itace" Sai lokacin Bose tace. "To wai shi gogan bai san kin haihu bane?" Kafin in yi magana Uwani tace. "Na kirashi na sanar dashi. Yana hanyar dawowa daga legos ne, da ƙyar ma na samu wayar tashi ba sabis. Amman yace abokinshi Bara'u zai tawo daga ƙauye, duk abinda ake buƙata zai yi kafin shi ya iso, dan yace mun zasu iya kaiwa ma ɗayan dare basu shigoba, wata ƙila sai Asuba ma zasu shigo kanon." Tsaki Iyaa Debisi tayi tace. " Isokuso asan. ( Banza marar amfani)" Haƙiƙa naji zafi ainun, kuma maganar ta dokeni, ai ko banza Gwadabe uban ƴaƴanane." Anty Mulka ta fita bakinta a taɓe. Bose ta fita da zanin jini da muka dawo dashi daga asibiti, Uwani kuma ta ci gaba da mun gyaran ɗaki, sauran ƴan uwa kuma suka fita falo wajen su Burodami. Zuga su Yaya Haula su ka yi, suka shigo da sallamarsu, Iyaa Debisi ce ta basu izinin shigowa. Suna shigowa ta miƙe ta koma falo" "Iko sai Allah, Iyabo dama kunsan ƴan biyu ne a cikin naki, ko kuwa sai da kika haihu tukunna?" Cewar Gude uwar son jin ƙaƙa aka haifi mutum. A'a dama tun cikin ma yana wata huɗu da akayi mun sikainin akace ƴan biyu ne. Kun gansu mace da namiji. Taiwo da Kahinde kenan" Yaya Haula tace. "Au suma sunan yarbawan za'a liƙa musu, babu ko karar a saka sunan Mahaifin shi Gwadaben, ita kuma macen asa sunan Babala, sai wani Taiwo da Kahinde?" Uwani ce ta juyo tace. "Ba tana nufin sunan yarbawa za'a saka musu ba. Taiwo da kahinden yana nufin Hassana da Usaini kamar yadda muke cewa a Yaren Hausa. Tunda ai kunsan ba ko waɗanne ƴan biyu bane ake sake musu suna ba, ko a cikin hausawa " "To wannan ko dole a sake musu wallahi. Kun mayar da Gwadabe sai kace sususu kawai" Cewar Yaya Haula wacce da gani ta fusata. Uwani ba kanwar lasa bace na santa sarai shi yasa na katse zancan dan gudun kar su kira mun ruwa, dan ƙyas su Bose suka ji wata hayaniya zasu shigo ayi ɓatacciya, dan kowa cike yake da haushin kowa, sai kace ba Allah ɗaya muke bautama ba. Ya'isa haka Uwani dan Allah. Yaya Haula Gwadabe na da ikon ya zaɓama jininshi duk sunan da yake da buƙata. Ni bani da ikon sashi yayi abinda baya so. Ko Toye ma shi ya zaɓi ya saka domin yai na mahaifina Allah ya jiƙan rai takwara" "Tunda ya kasa yi ma nashi Allah ya ji ƙan ran takwaraba. Ai baki zo kin ganshi da mahaifinshi a raye ba. Dama yarbawa akuyarku ai tayi kuka wajen juya miji da jarabar bin baba lawo" Ta sake faɗa da karfi . Na riga da nasan tarzoma take son tayarmun, ayi rikici su sake kafa hujja akan jarabar yarbawa, da ƙin zaman lafiya. Haka dai suka fice a ɗakin bayan sun yi mun barka. Ni dai ban basu yaranba, dan a al'adarmu bama ba da yaro jariri ga mutane aita jagwalgwalashi. Suma sun sani tun a haihuwar Toye, kuma sun yi rantsuwar ko yara ɗari zan haifa ba wacce zata sake yinƙurin ɗaukar jaririn. Cikin ikon Allah a ƴan uwana babu wanda yaji kace_nace ɗin data faru, bayan fitarsu Uwani tace. "Iyabo sai fa kin yi da gaske dangin Gwadabe zasu iya barinki kici gaba da rayuwa a gidannan, wannan ƙiyayyar ta yi yawa. Wallahi ko ahalul kitabi ce ke ya kamata su sarara miki haka. Duk da su kansu Iyaa Debisi sunƙi su zubar da makaman yaƙinsu. Amman ɗazu fa kinsan ina dawowa rufe miki ƙofa da kikace. Su Haula suna falonki suna kallon ɗakin. Ita kuwa baƙar kadararcan a Uwar ɗakin ki muka ci karo tana miki bincike a sib, har ta ɗakko wata atampa mai ruwan malmo, kai gaskiya kina cikin wani yanayi." Shigowar Sakina ne ya katse mana hirar. Ah Sakina kune a tafe da yamma sakaliya haka? Maraba" Na faɗa ina dariya. Uwani tace. "Kaga uwar gida, kuma Amarya a gidan Bara'u, Sakina lale." Cewar Uwani. "Lale Uwani, ashe Iyabo uwar biyu an samu kai. Sannu fa mai jego. Bara'u yana falo yace a kawo mishi yarin zai musu huɗuba." Miƙewa nayi na saka mayafi, Sakina ta riƙe Taiwo ni kuma ina riƙe da Kahinde muka fito falon. Bara'u yana kujera shi kaɗai, babu kowa a falon, duk yanda akayi su Burodami kokodeen sun tafi gida ne, ko sun je su dawo. Sakina ta miƙa ma Bara'u Taiwo. Ina wuni Bara'u. Da wannan yammar Gwadabe ya taso ku?" "Haba dai ai Gwadabe ya wuci haka a wajena. Kuma dama muna shirin shigowa cikin garin jikin Babala yaƙi yanzu haka tana asibitin Murtala. Yaya Hambali da Sukairaju suna wajenta, amman ƙila ba gado za'a bata ba dai." Allah sarki, ai ban sani ba. Zan shirya in je zuwa bayan magriba in dai basu dawo ba." Sai Sakina tace. "Ke da kike fama da kan ki kuma?" Bara'u daya fita sanin dawar garin yace. "A'a in dai akayi magriba sai ki rakata ta je ta dubo jikin ai dai ba za'ace bata nuna kulawarta ba ko ba gaskiya ba" Huɗuba yayi ma yaran da suna Hassana da usaini kamar yadda yace Gwadabe ya bashi umarni. "To yara na yi musu huɗuba da asalin sunayen da ƴan biyu suke zuwa dashi, wato Hassana da Usaini. Taiwo da Kahinde a yarenku kenan. Sabida haka a ɓangarenmu Hassana da Usaini suke. A naku ɓangaren kuma Taiwo da Kahinde Allah ya raya su da imani" Miƙo mun yaran yayi na amshi ɗaya Sakina ta amshi ɗaya muka shiga ciki. "Me za'a ɗaura na dare ne Iyabo magriba ta kawo kai ma?" Cewar Uwani kafin in bata amsa Iyaa Debisi ta shigo da ruwa a bawo na wankan yara ta dasa kujera. "Fun mi ni omo ( Bani yaron) Ta furta ranta a mugun haɗe. A sanyaye na miƙa mata ina fatan kar a kuma samun matsala makamanciyar ta haihuwar Toye. Uwani ai inaga ba sai an yi girki ba, ga Amala a kuka da faten wake, ai ya ishemu, gobe a ɗaura girkin." Nabata amsarta. Anty Mulka ce ta leƙo tace dani in je in yi wanka ta kai mun ruwan. Wanka nayi na gargasa jikina sosai na ji daɗi. Ina fitowa Su Anty Mulka suna shirin tafiya gida Burodami kokodeen yazo zai kaisu gida. Godiya nayi musu sosai, mu kai sallama suka fita ni kuma

Chapter 5 of 16