zaka iya zuwa ka ɗebi yaranka ka baiwa matarka taci gaba da kular maka dasu. To nasan zaka fi son yarannan a hannunka Gwadabe. Amman sauƙi muke nemar maka kayi haƙuri ni zan tafi da Toye tamu zai riƙe Taiwo da Kahinde, tausayin yaran muke yi a hannun su Babala. Na ji daɗin samuwar lafiyarka, babu abinda zamu ce da Allah zai godiya. Ka yi haƙuri ka daɗa"
Wata wawuyar ajjiyar zuchiya ya sauke mai nauyi yace.
"Bara'u yau ko ni kuka ce zaku ɗauka da kai da Tamu ba yaran ba, bana jin zanyi muku musu. Yarannan naku ne ku yi yadda kuke so dasu. Nagode da soyayya Allah ya bar zumunci. Sannan Bara'u wallahi na rungumi ƙaddarata, ina fatan Iyabo ma ta rungumi tata ƙaddarar. Amman fa ni da Iyabo Allah shi ya haɗa zukatanmu. Ko anan gaba in nayi aure, matar zata tsaya ne kan iyakar matsayinta, bata isa hawa matsayin Iyabo ba. Ita kanta nasan hakanne ta ɓangarenta. Bara'u Iyabo mutum ce har da ɓari"
"Zahiri Iyabo Mutum ce guda da ɓari. Allah yai mata sauyin alkhairi, kaima Allah yai maka sauyin alkhairi. Yanzu mu je mu shirya yaran, tunda jikinka yayi kyau ai sai mu je Abujar tare mu kai ƴan biyun. Daga nan sai mu wuce Takai. Dan Malam magaji ya zo jiya. Inajin su Yaya Hambali basu sani ba tukunna dai"
Ai kuwa haka akayi. Bara'u da kanshi ya haɗa ma ƴan biyu kayansu a jakar buhu, ya haɗa na Toye. Gwadabe ya rufe ɗakin da ko tabarma babu. Yaima su Yaya Hambali sallama kan zashi Abuja daga can zai zarce Takai gaishe da Baba Magaji da yazo. Yaya Hambali yaso jin dalilin tafiyar, amman Gwadabe sai ya ɓoye mishi dan ko fuska bai bashi ba, yana kan turmi Yaya Haula na gasa mishi baki. Bara'u shi ya biya misu kuɗin mota. Cikin Awa shidda sai gasu a Gwagwalada. Da mota Tamu yazo ya ɗaukesu har zuwa dan madaidaicin gidanshi. Bayan sun yi sallah sun huta, Ayashe ta kawo musu abinci Falo ƙanwar Tamu na biye da'ita da plate a hannu. Ayashe ta shiga da yaran ciki, bayan ta jajantama Gwadabe abinda ya afku cike da jimami.
"Kaga Shafs ce wannan data shiga ciki yanzu. Da shine nake tunanin Bara'u ba zan ba Gwadabe Shafa ba kawai. Kaga a matsayin wa kake a wajenta, kuma ta ɗanyi karatunta yanzu haka karatun diploma take haɗewa anan Gwagwalada. Da in ta kammala sai ayi auren ko ya ka gani Bara'u?"
Bara'u yayi dariya suka tafa da Tamu kafin yace"
"Yarinya zuƙeƙiya son kowa, gata budurwa sharab. Shafa a gabanmu aka haifeta. Bana mance taron sunanta, kasan gida _gida mu ka dinga bin abokanmu muna raba musu alawar gaiyata. Kowa yazo da sile da sisinshi. In abun ya tabbata zaiyi kyau sosai "
Tamu yace.
"Wato kai Bara'u baka da mantuwa sam.
Ni ai tunanina in rama halaccin da Gwadabe yayi mini, ko banyi mai daidai da abinda yayi mun ba, in kamanta mishi. Gwadabe na baka Shafa halak malak. Nine maɗaurin aurenta dama. Zan mata bayani duk lokacin da ka samu nutsuwa sai ka neme ta, a hankali tunda ba sauri akeyi ba sai ku daidaita tsakaninku. Yara kuma zanci gaba da riƙonsu ko kun yi auren ma, in sha Allah ni zan aurar dasu da hannuna. Zan kuma so in haɗe su aure da nawa yaran dakan ɗaka shiƙan ɗaka"
Gwadabe bai yi musu jayayya ba bare turjiya. Kwana ɗaya su kayi a garin Gwagwalada suka juya washe gari, bayan Gwadabe yayi sallama da ƴan yaranshi, abinka da yara sun shige cikin yara ƴan uwansu sai adabo ma suke ma uban. Ganin yaran sun sake ne uban ya ɗan ji ƙarfin guiwa kuma.
Ruga
Iyabo:.
Tabarma Daso ta ɗauko ta shimfiɗama Yaya Hamma daga can gefe guda. Jatau ne ya shigo da garken shanunshi guda yana tafe yana waƙar fullanci, hannunshi da ƴar tsaraba.
"Jatau yau kai ka soma shigowa gidan?" Da Hausa tayi mishi wannan tambayar. Shi kuma hankalinshi duka yana kaina, ina son in ɗebo ruwa a randar ƙasa in kawo ma Yaya Hamma.
"Baƙuwa mu ka yi ne Daso?"
"E baƙuwa ce kuma ƴar gida, Yayar su Boɗɗo ce tazo daga birni"
Sai ya washe bakinshi muka gaisa cikin girma da arziki. Na dure ma Yaya Hamma ruwan sha a gabanshi na koma kan turmi na zauna. Jatau da Hamma nan suka kacame da yare, daga bisani Jatau ya wuce da shanunshi izuwa maɗaura.
"Jabu zo ki zauna sabida ke nazo gidannan da yammannan" Daso dake hura wuta tace.
"Ko ni na faɗa a rayina, sabida Jabu ne kazo Yaya Hamma"
Sai tayi murmushi, nima murmushin na mayar mata, na ƙarasa kan tabarmar da Hamma yake na zauna a gefe.
"Na ji labarin mutuwar aurenki ƙanwata. Abun ya dake ni ainun, naji tausayinki sosai. Amman mu zamu baki farin cikin da har sai kin mance da komai a matsayinmu na dangin uwa, muma zamu taka tamu kalar rawar, tunda kika zaɓi ki rayu damu a ruga, kika haƙura da rayuwar maraya duk da acan ki kai wayau. Kiyi haƙuri kinji am?"
Wasu hawaye ne suka gangaro mun. Ban aune ba sai kuka mai gunji ya tawomun babu zato. A tiɓi tiɓi_tiɓi da kayan mazaunai na shige bukkarmu na zauna akan gadon ƙasarnan na shiga sana'ar kuka. Wani tuƙuƙin baƙin ciki da takaici sai yanzu ne komai ya soma dawo mini. Kuka na zage nayi na ban mamaki. Ƴan uwana suka bani sarari na dirji kukana yadda yayi mun nayi shiru dan raɗin kaina. Sai zuchiyata ta ɗan washe ta rage nauyi. Na yi zaman tunani a zaune bansan iyakar adadin ba. Sai shigowar Yafendo na gani kawai. Da sauri na share guntun hawayena ina duban fuskarta. Sai naga fuskarta cike da damuwa, da dukkan alamu damuwa da damuwata ce take yi. Ledar hannunta ta miƙo mun nasa hannu na karɓa kafin tace.
"Ban isa hana ki kuka, ko hanaki damuwa da tunanin yaranki ba Jabu. Kinga Daso tun bayan rasuwar mijinta kullum sai ta yi kuka zuchiyarta babu daɗi. In Hamma yazo gidannanne ma take samu tayi farin ciki. Ni kuwa ban taɓa hanata kuka ba. Rabuwa da miji ciwonshi bashi da misali sam, musamman mijin da kuke soyayya da zaman lafiya. Ace mutuwace tayi muku yankan ƙauna. Ko kuma wata ƙaddararce ta raba ku ba da son rayukanku ba. A lokacin da mahaifinki ya rasu Adda Daso ta shiga wani irin mawuyacin hali. Mahaifiyarki har jinya sai da ta kwanta na tsawon wata shida masu kyau. Har gaban abada ba zata dena tunanin mahaifinki ba. Musamman data haɗu da azzalumin namiji magoki. Da girmansu haka bai bar dukansu ba. Zuwan da ki kayi ma dan kawai ta roƙeshi ya barki ki zauna a wajenta har ki gama kwanakinki ki tafi. A daren zagi da cin zarafi babu wanda baiyi mata ba, har marinta sai da yayi"
Da mugun sauri na ɗago. Wata kibiya ta soki ƙawon zuchiyata, siraran hawaye suka gangaro kan kumatuna masu zafi.
Yafendo yanzu kamar Dada da girmanta da yaranta manya sai mijinta ya daketa harda zagi, a halin da take rayuwa kenan?" Zama Yafendo tayi a kusa dani tace.
"A haka Adda Daso take rayuwa da azzalumin mijinta. Har da tsohon ciki a jikinta dukanta yake yi. Ko a cikin Boɗɗo yayi mata wani dukan da tai ta zubar da jini, duk muka cire rai da cikin. Sai daga baya cikin ya tashi. Amman sai da Boɗɗo ta shekara biyu cir a kwance a cikinta kafin ta haifeta. Wannan kuma ana tunanin da sa hannun uwar gidansu akan lamarin. Kuma ya karɓe shanunta na gado ya haɗe da nashi shanun, Adda Daso bata ribatar komai. Shanune masu tarin yawan gaske, kinga gaa nawa garken can Jatau ya dawo dasu, sai hauhawa suke yi. Ita kuma bata san adadin yawan haihuwar da nata shanun suka yi ba, dan nata mata ne, namijin guda ɗaya ta samu. Ke Jabu in nace zan ta baki tarihin mijin mahaifiyarki zamu kwana mu wuni a nan bamu ƙare ba. Shi yasa ko da yaushe take cike da tunanin marigayi mahaifinki. Soyayya da kulawar daya bata ne, yasa ta fifita soyayyarki fiye da soyayyar duk yaranta. Duk ɗan abinda ta samu burinta ta tara in zata kai miki ziyara ta miki hidima, kinji na rantse miki tun bayan rasuwar mahaifinki ban sake ganin annuri akan fuskar Adda Daso ba, sai yau data zo gidannan tana sanar dani zuwanki garinnan, damma a hakan ta kwana cikin tashin hankali akan mijinga."
Kukane yaci ƙarfina, zuchiyata sai luguden daka take ta faman yi. Ina jin duniyata na wujijjiga rayuwata. Tausayi da zunzurutun kaunar Dada ya sake ɗamfaruwa a raina. Yafendo ta dafa ni nayi firgigit na kalleta.
"Ki tashi ki ɗauro alwala ki yi sallah. Wannan ledar dana baki Hamma ne ya ce a baki. In ki ka yi sallah sai ki fito tsakar gida in gabatar dake ga ƴan uwanki"
Jikina a sanyaye na ɗauro alwala nayi sallah. Na daɗe ina adda'a, a lokacin zazzaɓin dake jikina ya rabkeni ainun, ko idanuna bana iya buɗewa. A halin da Daso ta shigo ta same ni kenan. Abu kamar da wasa_wasa sai na rasa numfashina, jikina kuwa kamar garwashin wuta. Sai da na shafe tsawon wata biyu da kwana goma sha ɗaya cur a kwance babu lafiya, sai maganin gargajiya akeyi mun, hatta ruwan wankana da ganyen magani a ciki, kuma Yaya Hamma suke kawo mun magani da ɗan abinda zan sa a bakina, Yaya Jatau ma yana kawo mun ɗan abun kwaɗayi, matarshi ma kullum zata shigo ta duba lafiyata, kuma in Yafendona, da Daso sun tafi tallen Nono, Hari itace ke zama dani matar Jatau. A wannan jinyar naga gatan dangin uwa. A wannan kwanciyar sai da dangin Dada suka zo kab suka gaisheni da jiki, a lokacin na gansu suka ganni. Dada kuwa kullum cikin suntiri suke ita da su cubu da Yusufu, Boɗɗo kuwa da hama suma kullum babu fashi sai sun zo dubani. " A cikin wata uku cib jikina yayi ƙwari babu laifi, lokacin iddata ta cika cib, lamarin da ya ɗan ƙara jagula lafiyar jikina kenan, sai da Yaya Hamma ya dinga bani baki, tare da lafuzza tausasa, har mamaki nake yi in naji yana furta wasu lafuza masu kwantar da zukata. Da yamman wata asabar bayan Daso ta dawo daga tallar nono muna ɗaki mu na ɗan taɓa hira, fuskarta cike da farin cikin ganin jikina yayi kyau yau. Duk da na rame fiye da tunanin masu karatu, fuskata ta yi fayau. A jinyar dana kwanta na samu kulawar mutane uku da bazan mance da hidimar da su kai mun ba. Daso, Yaya Jatau, Yaya Hamma. Duk kwanan duniya Daso itace mai bani abinci a baki, tare da gyara mun kwanciyata, ko amai nayi itace ke kwashewa. To a wannan kwanciyar jinyar nayi jinin al'ada hatta da tsumman jini da ɗan kamfaina Daso ke wanke mun da ruwan toka ta shanya su, wanda zai maka irin wannan aikin ba ƙaramin masoyinka bane. Yaya Jatau kuma kullum in zai dawo daga kiwo yana kawo mun wani gashasshen hanta mai yaji, shi nake ci da daddare, shi kaɗai ne nake iya ci ba tare da naji tashin zuchiya ba. Yaya Hamma kuwa shi ya dinga bin ƙauyuka ruga_ruga dan sama mun magani, wani gari wani ganye, ko kiwo yaƙi ya mai da hankali akai har sai da ya ga samuwar lafiyata. Kuma kullum a cikin yi mun nasiha da tattausan laffuzza yake. Muna ɗan hirarmu muka ga an buɗe labulen kaban dake ƙofar bukkarmu. Yaya Hamma ne ya shigo hannunshi riƙe da kwano. Daso ce ta miƙe ta karɓi kwanon ta dure a gabana tana dariya tace.
"Nasan ai nata ne ko Yaya Hamma? Shi yasa na dure mata a gabanta" Dariya yayi tare da nunata da yatsa yace.
"Kin ganki akwai zolaya. Ai itace marar lafiya a gidan, shi yasa na kawo mata tasha romo" Sai tace.
"Nima in na kwanta jinya ashe zaka kula dani sosai irin kulawar da ka ba Jabu?"
Dani da'ita duka sai muka kafe shi da idanu. Sai da ya zauna a ƙasa ya tanƙwashe ƙafarshi kana yace.
"Ai kamar ratayayyen hakkine a kaina in kula daku, ko da a gidan mazajenku kuke balle kuma kuna gabanmu.
Jabu ya ƙarfin jikin, yaya haƙuri ds rayuwa, da haƙurin zaman ƙauyanmu mara wuta balle ruwan daɗi?"
Ɗan murmushi nayi nace.
Jiki Alhamdulillah sauƙin yana samuwa sosai. Babu abunda zance sai godiya. Kuma ina godiya da wannan ɗawainiya da kukaita yi dani" Bayan na bashi amsar na sauke kaina ƙasa.
"Ai ya zame mana dole, ki daina godiya ma Jabu"
Miƙewa tsaye yayi.
"Ba dai tafiya ba?" Cewar Daso.
"Tafiya zanyi. Dama abinci na kawo mata. In kuma ƙara ganin jikin nata. Amman dai ku shirya zuwa dare zan zo mu leƙa dandali Jabu taga yadda muke wasanninmu gwanin sha'awa, wala Allah hakan ya rage mata raɗaɗi."
Dariya nayi musu kawai. Aini na rabu da nishaɗi tunda na rabu da Gwadabe, dan nishaɗi na wajen tsuntsun soyayya. Amman a fili saina amsa da cewa.
Allah ya kaimu"
Ko dan in ƙarfafasu tunda burinsu suga na saki jikina na mance komai.
Da haka mu kai Sallama, bamu muka fito daga cikin bukkarmu ba saida mu ka sallaci sallar isha. A tsakar gida muka ci fsrfesun da Yaya Hamma ya kawo mini harda Yafendo da Jatau, dama Hari Matarshi.
MRS BUKHARI ce.
*Ƴar uwa ina fatan baki mance da kayan ƙamshin Mrs Bukhari gidan ƙamshi ba ko? Ƴar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ƙamshi. Matso kusa ƴar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ƙamshi ya riƙe miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake saƙawa a tsakankanin kaya.
Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ƙamshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata.
Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haɗe da turaren fesawa a gashi.
Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ƙara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ƙamshin kifi ɗanye.
Inada humrori kala_kala.
Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ƙamshi.
Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ƙamshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ƴar mutan Maiduguri kin samu ƙamshi.
( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai ɗauke da abubuwa huɗu manya kuma a kan kuɗi ƙalilan karki bari garaɓasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)*
NAMA YA DAHU....
ROMO ƊANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM
14
Muna gama ci sai ga Yaya Hamma ya shigo. Yana saye da wani yadi mai ruwan bula ɗinkin ƴar shara, yadinnan duk ya gaji yayi laushi sosai sai laɓewa a jikinshi yake yi. Wandon jikinshi kuma na koren yadi ya saka ya ɗauko hular tashi ka fiye naci irin hular da fulani suke mugun so ɗinnan ƴar madina mai fara da baƙa a jiki, ƙafarshi kuma saye da takalmin roba mai ruwan bula duk ya fashe, sai ƙamshin wani turare mai gafin ƙamshi yake yi, daya isa wajensu Yafendo dake akwai fitilar aci bal_bal na gango kwalli rambaɗe a fararen dara_daran idanunshi har zazzagowa yayi. Bayan ya gaisa dasu Yafendo yayi ma Baba bayanin yazo ya kaimu dandaline, sai ya fita waje ya bamu sarari dan mu kintsa.
"Daso maza ku tashi ku shirya abun nema ai yau ya samu ko?"
Dariya mu ka yi mata kawai. Ni dai mayafi kawai na ɗauka, saye nake da koɗaɗɗen riga da zane. Saɓanin Daso da sai da ta shafa kwalli harda janbakin majigi tasa ma labɓanta. Cikin zaulaya nace.
Harda kwalliya ko za'a samo mana bazawari ko?" Dariya tayi kawai tace.
"Kayya, ai tunda na rasa Chubaɗo ban sake tsaiwa da kowa ba. Ni abunma wani iri ba fasali yake yi mini"
E dole zaki ji banbarakwai wai namiji da suna Hajara. Amman ya muka iya haka Allah ya zaɓar mana. Fatan shine Allah ya sadamu da mazajen da zasu ji tausayin rauninmu. Gara ma ke Daso mijinki rasuwa yayi fa. Ni fa Gwadabe yana doron duniyarnan rabamu akayi a bisa tursasawar mahaifiya da danginshi" Siraran hawayene ban aune ba suka biyo kan kuncina.
Dafa kafaɗata Daso tayi jikinta a mace tace.
"Mu yi haƙuri kawai mu rungumi ƙaddararmu. Allah yana sane damu, bai mance mu ba. Ta yiwu ya shirya mana kyakkyawar rayuwa a gaba. Ta yiwu kuma wahalar rayuwarmu ne zai fara. Amman duk abinda ya samu bawa ya fauwala shi ga Allah "
Wannan gaskiya ne. Muna fatan kyakkyawar rayuwar a gaba. Allah ya sadamu da mazajen da dan so zasu ji kamar su mallaka mana numfashinsu dan mu daɗe mu yi ƙarko. Mu je mun bar Yaya Hamma a waje yana ta faman jira" Kafinma in rufe baki muka jiyo Yafendo tana kwaɗa kiran sunanmu tana yaren Fullanci. Ba shiri muka fito tare da ficewa a gidan. Ko da muka kama hanya, sai cin karo muke yi da mata da samari suna nufar dandali. Ina gefen hannun daman Yaya Hamma, Daso na gefen hagunshi mun sanya shi a tsakiya. Sai hira yake janmu dashi, Daso ce ke bashi amsar duk abinda ya tambaya. Ni tunanin Gwadabe da yarana, da kuma tunanin ta wacce hanya zanbi dan ganin na sanya Dada a farin ciki dariya da walwalarta ta dawo kawai nake. Wani shashe na zuchiyata sai kawai katsaham yace.
"Me zai hana ki nemi Uwani in dai bata tafi ba, kema tayi miki hanya ki tafi. In kika tara kuɗi ne kawai zaki iya ɗauke mahaifiyarki ki rabata da azzalumin mijinta, ki kuma rabata da tallan Nono. Wannan shine hanya mafi sauƙi. Tunda ba kya kashe mata aure ba tare da kin shirya mata gidan da zata rayu da yaranta ba, kuma ba zaki hanata tallan nono ba har sai ke kin samu abun yi, ko kuɗi a hannunki da zaki ma rayuwarta hidima kamar yadda mahaifinki yayi mata kafin ya rasu" Nan take sai nake ganin kamar ma na samu mafitar cire Dada cikin ƙangin rashin ƴancin da take ciki. Dan a shirye nake ko matakin shari'a ne zan bi muddin yaƙi sauwaƙe mata igiyar ƙaddararran autenshi. Lokacin dana kwanta jinya take yawan sintirin zuwa dubani. Cubu ranar ta shigo da kuka take labarta ma Yafendo cewar Dada tana gida Baffansu ya daketa ya kumbura mata fuska, sabida sintirin zuwa dubani da take yi wai ya isheshi sai kace nice kaɗai ƴar data haifa. Lamarin da yasa ƙannena suka haɗe kansu suna kuka, tare da adda'ar Allah ya kawo ma Dada mafita ya cireta a wannan ƙangin. Daga ranar kullum ƙwaƙwalwata cikin tunanin sama ma Dada mafita nake, ko da kuwa zan rasa tawa mafitar. Sai yau Allah yayi na tuna abinda nake ganin zai iya kawo ƙarshen hawayen Dada. Tafiya Kano ya kamani gobe da izinin Allah, dan bahaushe gwanin iya tsara zance cikin hikima da azanci yakance da zafi zafi ake dukan ƙarfe, ko kuma yace da safe ake kamun fara"
"Jabu tunanin me kikeyi haka mai zurfi har mun iso dandali baki sani ba? Na lura jefa ƙafafuwanki kawai kike yi" Cewar Daso wacce ta kafeni da idanu, Yaya Hamma shima ido ya zubamun, suna sauraren abinda bakina zai furta da sunan amsa. Iska na jawo daga huhuna na furzar kana nace.
Tunanin rayuwa kawai nake yi Daso. Ai baka isa ka raba zuchiya da tunani, ko da ayyane_ayyane ba" Na ja bakina na tsuke. Na kura maa wutar karar dake ci bal_bal a tsakiyan dandalin ido, wajen yayi haske sosai ina iya hango kwalliyar mata da maza. Wutar nake kallo yanda take tartsatsi. Amman abinda zuchiyata take ciki yafi ƙarfin tartsatsin wutarnan, jin zafi nake yi daya wuce doka da oda. Hannuna Daso ta kama muka nemi wani benci da babu kowa muka zazzauna. Ƴan berorin ƴan mata sai wasannin gaɗa da waƙe_waƙen su na fulani suke yi. Samari sun kewayesu sai tafi da ɗaga sandunansu suke yi.
"Kinga dandalinmu ko Jabu?, Allah yasa wasannin al'adunmu sun burgeki?" Cewar Yaya Hamma wanda yake zaune kusa dani. Murmushi kawai nayi mishi na sauke kayina ƙasa ina kallon yatsun ƙafata.
"Jabu tunanin menene ya bujuro miki duk ya sauya kamanninki? Kinga lafiya abun tattalawace ga duk wani rayayye. Me zai hana ki tausaya mana ki dena wannan tunanin ko dan lafiyarki da farin cikin masu son ganinki cikin ƙoshin lafiya?" Kallonshi nayi na mai murmushi idanuna cike da ruwan hawaye. Shima murmushin ya bini dashi, kafin ince wani abun sai ga wani matashi ya ƙaraso gabanmu da sandarshi rataye bisa kafaɗunshi.
"Hamma in babu damuwa inaso ka bani dama mu zanta da Daso. Na jima ina bibiyarta domin ta bani damar ko sauraren abunda ke tafe dani taji amman ta ƙi ya" Yaya Hamma ya dubi wannan matashin, ya dubi Daso wacce ta turɓune fuskarta kamar bata dariya.
"To jeka zata zo yanzu. Kuma ni Hamma na baka damar zuwa zance wajen Daso Manga daga yau kuma yanzu. Daso tashi kije Manga zai yi magana dake" Nasan ganin rashin wasa gami da murtukewar fuskane yasa ta bishi ba dan ranta ya so hakan ba. Tafiyarta ke da wuya Yaya Hamma ya ce.
"Bani labarin abinda yake damun zuchiyarki. Nayi miki alƙawarin magance miki matsalar duk girmanta"
A'a Yaya Hamma babu komai. Ni dai inaso gobe zan je garin Kano. Amman nayi maka alƙawarin kwana biyu rak zanyi zan dawo." Da sauri ya kalleni har tsoron da yake son ɓoyewa ya kasa ɓoyuwa.
"Kano kuma, ba dai wajen tsohon mijinki kike son zuwa ba, ko ganin yaranki ba? Kinsan yin hakan a wannan halin da kike ciku ka iya fama miki ciwon dake zuchiyarki" Da sauri na katseshi da cewa.
Ko ɗaya ba abinda zai kaini Kano ba kenan. Akwai wani shiri da nake son in yi ne a can Kanon. In abun ya tabbata kaine mutum na biyu da zan faɗa ma bayan Daso" Ajjiyar zuchiya ya sauke yace.
"Au ashe Daso ta fini matsayi a wajenki? Sai ta sani kafin ma in sani ko. Nagode" Yanda ya turɓune ƴar kyakkyawar fuskarshi sai ya bani dariya ainun.
Ba haka nake nufi ba. Sabida ita ɗakunmu ɗaya da'itane. Amman kana da matsayi a wajena gaya. Ko tafiyar nan da zanyi gobe babu wanda na sanarma sai kai. Sai mun koma gida zan sanarma da Yafendo" Daɗi yaji sosai, sai kuma naga damuwa ta maye gurbin daɗin.
"Allah yasa ba ƙauyenmu bane ya isheki kike son komawa maraya ba, sai da muka shaƙu dake kike son ki gudu ki barmu da kewa." Daso ce ta dawo ta zauna jagwab a gefena tana rishin kuka.
"Ni Yaya Hamma bana son Manga. Bazan iya rayuwar aure da abokin Chubaɗo ba, gani zanyi kamar naci amanar Chubaɗo ne. Gashi kai kace ka bashi izinin zuwa zance, kuma kab garinnan waye baisan zafin kishin matar Manga ba. Ni ban shirya jefa rayuwata a cikin haɗari ba gaskiya " Dubanta yayi ranshi a bace, ko me ya tuna oho sai ya shiga aikin rarrashinta gami da yi mata nasiha. Mijintane dai ta rasashi har abada, ya zame mata dole yin sabon aure ko ba dan sha'awa ba ko dan tsira da mutunci. Ya ɗaura da cewa.
"Kuma kinsan Baba ba zuba ido zaiyi ya barki kita zama a gabanshi babu aure ba ko. Lokacin da zai matsa miki da fito da miji nake jiye miki, dan in baki fitarba al'ada zata haɗaki aure da wani ɗan uwanki ko kina son hakan, ko bakya so. Ni abinda nake jiye miki kenan. Sannan Manga kab Rugar nan ansan mutumin kirki ne, gashi da yawan shanu, kuma jarumine sosai. Ko wacce bafulatana burinta auren jarumin namiji." Zaman dandalin dai haka muka ƙareshi babu armashi, Yaya Hamma ya mayar damu gida. Muna shiga a daren na sanar ma Yafendo inaso zanje Kano in Allah ya kaimu gobe, kwana biyu zanyi. Sai da ta ɗanyi jim kamar ba zata yarda ba, kamar tana son tambayata Allah ya soni bata tambayeni ba, sai cewa tayi dani.
"Allah ya kaimu goben cikin rayayyu, sai ki shirya da wuri tafiyace mai nisan gaske" Da tunanin tafiyar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 16