da yara, sai su fi sati biyu. Nima dolena in na zo Takai a gidan Sakina nake sauka. Zuwana na ƙarshe wanda daga shi ban sake zuwa ba sai yau ne kawai Babala tace bazan sauka a gidan Sakina ba, a cikin gida zan zauna, kuma ta kafa dokar ta haramta mun zuwa gidan Bara'u in kwana, ba dan komai ba sai dan a sake ƙuntatani.
Gwadabe:.
"Gwadabe lafiya irin wannan ramar da kayi haka?" Cewar Bara'u wanda ya kasa haƙuri sai da ya ja Gwadabe gefe dan su ɗan zanta,bayan ya bi mazan dake ƙofar gida an gaggaisa. Gwadabe ya girgiza kai yace.
"Wallahi Bara'u kai kasan komai al'amuranne sai godiyar Allah kawai. Kasan in akace maka magidanci bashi da cikakkiyar sana'ar kanshi dole hankalinshi bazai kwanta ba. Karen mota nake yi har yanzu dai daka sani. Amman muna sa ran za'ayi mana freedom da yardar Allah muma a bamu mota, in hakan ya tabbata za'a samu sauƙi. A hakanma ban fa zauna ba, buga_buga akeyi babu dare bare rana, muddin akace maka safiya ta yi, to fa in na fice duk abunda na samu yi nake yi. Nine kwashe shara, nine kwashe kwata, nine bin masu Bus na zuwa unguwanni ina karen mota. Kaga duk sana'oene na cin abinci kawai, abincinma bafa sau uku a rana ba. Duk ranar data carke wallahi sai dai in tura Iyabo gidansu ita da Toye dan su samu abunda zasu kai bakin salati, haka iyayenta zasu ci mata mutuncinta in taje musu, to amman ni hakan yafi mun. Ni kuma haka zan wuni neman aikin yi. Babban abunda yake sani cikin juyayi shine a wannan halin da muke ciki ko Bara'u? To Yaya Hambali, da su Sukairaju, Fodiyo, Yaya Harisu kai dukkansu. Su a wadace suke da abinci, dan Yaya Hambali kullum da nama ake miya a tukunyarshi. Ni kuma na sama raina in yinwa ita zata zame mana ajali ni da iyalina sai dai mu mutu. Bara'u bazan sake tambayar tallafi ko taimako a wajen kowa ba. Wulaƙanci wanne ne ni Gwadabe ban gani ba? Yanzu nan yau Yaya Hambali yace mu tattare yamanu_yanamu mu bar mushi gidanshi. Dan kawai Iyabo ta watsa ma Yaya Haula ruwan kashi ba tare da saninta ba, fitintinun gidan kaɗai ya'isa yasa in yi rama wallahi."
Mrs Bukhari ce
Sai mun kasance a cikin wannan kayataccen labarin mai ɗauke da dumbin darasi.
Tafiyar tana da tsayi sosai. Ku shirya tsab kafin fitowata
Inanan tafe ba da jimawaba in sha Allah 👍🏻
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
NAMA YA DAHU..
ROMO ƊANYE
GAWURTATTU UKU
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Lamba ta biyu
Gwadabe:.
Numfashi ya ja, tare da jin wani irin turirin zafi a zuchiyarshi. Yana mamakin yanda ƴan uwanshi suka juya mishi baya sabida Iyabo. Bara'u ya ja ajjiyar zuchiya yace.
"Wannan ja'iba har yanzu barta ta wuce ba Gwadabe?, Aure sama da shekaru shida, ga rabo a tsakani har yanzu basu sauke aƙidarsu akan Iyabo ba? Naga ma ana wanke Arniya a aureta ba tare da ta bar arnancinta ba, kuma addini bai haka hakan ba, ballantana Iyabo wacce take musulma gabanta da bayanta. Shawarata anan Gwadabe shine ka yi haƙuri ka ba Yaya Hambali haƙuri kuci gaba da zama a ƙarƙashin inuwar dukiyarshi. Kuma nima na mara maka baya kar ka sake ka nuna musu ka gaza akan iyalinka, gara ka dinga turata gidan nasu duk wulaƙancin da zasu yi muku. Gwadabe kai mutumin kirki ne sosai, bana mance alkhairanka gareni. Bazan mance ba lokacin kana samu kai ka biya mun sadakin Sakina, ka siyo mun turamen zani har guda biyar aka zuba a famtimoti banda abubbuwa da kai ta binmu mu abokanka dashi na alkhairi. Kai kayi silar fitan Tamu gada cikin garinnan na Takai ya shiga Kano. Ashe hanyar arzikin nashi kenan yanzu ina Tamu? Yana Habuja shi da iyalinshi, sun samu rufin asiri sosai. Allah bazai hofantar da mutum irinka ba, matsawar kaga ka roƙi arziki Allah bai baka ba Gwadabe ka ɗauka cewar arzikin ƙila ba alkhairi bane a gareka. Kar in cikaka da surutu gara ka shiga ka samu Iyabo, wala Allah dangi su sassauta daga tsangwamarta in suka ga kaifin idanunka." Hannu yasa a ajjihu ya zaro nera dubu uku ƴan muttala_muttala ya tura a aljihun koɗaɗɗen jeans ɗin Gwadabe.
"Ka ba Babala gudunmawarka basai kace mun baka dashi ba, ta nuna a jikinka." Hannunshi ya ja suka nufi cikin gidan. Gwadabe sai murmushi yake yi gami da yabon ƙoƙari na Aminin nashi a kanshi. Jifa_jifa Bara'u na yi ma Gwadabe aiken gyaɗar miya, da shinkafa ƴar hausa. Abunda yake nomewa kenan, kuma ƴar gonar tashi ba wata babbar gona bace ga hidindimu masu tarin yawa a kan nashi.
Iyabo:.
Ƙafafuna har rawa suke yi wallahi dana ɗora ƙafata a cikin gidan. Da Yaya Halima na soma cin karo ta tawo ita da ƙawayenta, taci kwalliya, da halamun rakiya zata yi musu. Dariyar dole na ƙaƙaro nace.
Yaya Halima rakiya zaki yi ne. Ina wuni? Na furta da hausar bakina irinta yarbawan da suka ƙware a yaren Hausa. Dan babu kalmar da take bani wahalar furtawa sai dai nakan furtatane da irin Hausar bakina. Harara Yaya Halima ta doka mun, ta ƙura ma titsetsen cikina idanu ƙur. Tsaki ta ja mai ƙarfi suka wuce ni ita da ƙawayenta fuu. Jikina ya sake macewa mus, da jan ƙafa na ƙarasa shiga babban gidan nasu mai ƙofofi huɗu, ko wanne shiyya da ƙofarshi, amman gidan gabaki ɗaya a haɗe yake, ƴan uwane dangin juna da yaransu da jikokinsu a cikin gidan. Babban wan mahaifin su Gwadabe shi ya tara kan wannan dangi a waje ɗaya, kasancewar mahaifinsu Allah ya albarkaceshi da yawan yara (kakan su Gwadabe kenan). Su rai Talatin da uku mahaifinsu ya haifa, matanshi biyu rak. Sai wan mahaifinsu Gwadabe yaji bari ya haɗe kan ƙannenshi su zauna waje guda domin ƙarfafar zumunci. Irin abinda Babala tayi kenan akan Yaya Hambali daya haɗe kan ƙannenshi waje guda suke rayuwa gida ɗaya. Su Baban Nazifi da su Sukairaju kowanne cikinsu yana da ɗakinshi da yake sauka in sabgar biki ta kawomu, akwai katifu da labuleye a ɗakin. Gwadabe ne kawai bashi da ɗakin sauka in mun zo. Hakan ya farune sakamakon ni ya aura ƴar ƙabilar Yoruba bai auri ƴar ƙalibarsu ta Hausa fulani ba. Ina shiga shiyyar Babala naci karo da su Yaya Haula, da Sawaiba matar Harisu, dasu Gude sune ƴan gaba gaban murhu anata tuƙa tuwon jama'ar biki. Duk suka kalleni suka watsar, nasu kam ai na daɗe da sabawa. Ko da nayi sallama ɗaiɗaikun mutanene suka amsani, suma baƙine da suka shigo daga wasu ƙauyukan dan taya iyalan wannan gida murnar biki. A sanyaye na gaishesu har zan wuce Yaya Haula tace.
"Ai kamata yayi ki ci ɗamara da mayafinki ki zo ki tuƙa mana tuwonnan yayi sumul kamar Amala, kinsan dai a gidan surukai kike. Cijewa nayi nace mata.
To bari in gaisa da su Babala sai in zo Yaya Haula" Shikenan iyakar abunda nace, Sai kawai Gude ta daka tsalle tace.
"Lallai Iyabo wuyanki ya isa yanka sosai. Gwadabe ya ɗaure miki kugu sosai. Ke har kina da ta cewa a cikin zuriyarnan, ɗorin dosono dake? Ai da gidanku kika je bikinku na kwalo_kwalo dole ki zage kici aiki dama yarbawa ba'a sanku da hutu ba sai wahala" Hawayen da suke shirin zubo mun nayi saurin mayarwa dan hango Babala tana nufomu. Tana ganina ta zabga mun harara mai muni. Babu shiri na zube a ƙasa ko nauyin cikina banji ba.
Barka da fitowa Babala" Tsaki taja.
" In Kinga dama kin tashi daga wannan tsugunnon naku na gado. Kin shigo garin amman baki iya zuwa inda nake kin gaisheni ba, balle matan yayyena da ƙannena su ci albarkacina a matsayina na mahaifiyar Gwadabe. Sai da kika ganni zaki wani zube a ƙar, ai ni na ɗauka ba zaki barshi yazo bikin ba ma." Hawaye take ya tsinke a idanuna ya soma zuba shar_shar_shar, in furta kalma na kasa, in ɗago in bata hakuri na kasa bakina yayi mun nauyi ainun.
"Haula menene yake faruwa nake jiyo hayaniyarku ne?" Babala ta faɗa cikin ɓacin rai. Abinda Yaya Haula take jira dama kenan ai kuwa sai cewa tayi da Babala.
"Ce mata fa nayi tazo ta tuƙe mana tuwonnan yayi laushi irin nasu yarbawa. Shine ta nemi faɗa mun magana Babala, so take ta fake da ciki ta ƙi yin aiki. Lokacin bikin Rahina ma haka ta kwanta jinya ko tsinke taƙi ɗagawa. Ko a can Kano Gwadabe shi ke mata har shara da wanke_wanke, balle kuma wanki da wankan Toye" Baki Babala ta riƙe tana jijjiga kai kawai.
"Ba shakka ashe har yanzu Yarbawa suna da baƙar zuchiyar yin agumu. Abunda na dinga jiye ma Gwadabe kenan yaƙi ganewa sabida tun ana neman aka gusar mishi da hankali. Ai sunan Gwadabe ya daɗe a hannun Baba lawo ( Bokan yarbawa)" Hawaye kawai nake zubarwa rana zafi inuwa ƙuna. Ana cikin wannan ruguntsumin Gwadabe ya shigo yana rungume da Toye ga jakar kayanmu yana ja, Bara'u na riƙe da jakar kayan Toye. A tsaye suke suna gaisawa da dangin Babala, amman hankalin Gwadabe na kaina yanda yaga ina tsiyayar hawaye gani a gurfane. Ba shiri ya iso inda muke.
"Babala lafiya meke faruwa haka? Iyabo ke ba likita ya hanaki tsugunno ba, tashi tsaye" Ya faɗa a sanyaye. Babala ta sauke gwauron numfashi ta dubi Gwadabe tace.
"Babu shakka Gwadabe, sannu me mata. Wato likita ya hanata tsugunno a tsaye kake so ta gaisheni kenan ko marar albarka? Yayi kyau ai ku sha kuruminku komai ma ya kusan zuwa ƙarshe da izinin Allah" Tana faɗar haka ta wuce fu tana share hawaye. Bansan me akayi mata har da zai sata zub da hawaye ba. A kullum naga Babala na kuka akanmu tsorone yake sake shigata dan kukanta a wajen Gwadabe babbar musibace wacce ko arziki bazai bari yayi ba. Gabana ya yanke ya faɗi, take na ji jiri na shirin kayar dani. Me take nufi da komai ya kusan zuwa ƙarshe to? Ko so take Gwadabe ya rabu dani kenan ya auri Bahaushiya ƴar uwarshi?. A baya haka Babala ta tursasa Gwadabe sai da yai mun saki ɗaya. Sakin daya sake rura wutar rikici tsakanin dangina da dangin Gwadabe kenan, wannan saki ba ƙaramin ta da zaune tsaye yayi ba. Dan Iya Debisi da Babala sai da suka kusan raba abun faɗe a layi. Har an kwashe mun jerena har ga Allah ko ni a wancan lokacin na haƙura da Gwadabe. Allah ne yayi shan ruwan aurenmu bai ƙareba ina dawowa na samu wannan ciki."
"Tashi daga tsugunnon Iyabo ki shiga ciki ke da Toye ki huta. Zan je in nemo miki abunda zaki iya ci, ko in sa Sakina ta yo miki"
Da ƙyar na miƙe tsaye ƙafafuna sun yi tsami ainun. Haula da sauran matan dake wajen duk sai suka riƙe bakinsu akan furucin da Gwadabe yayi. Shi kuwa kamar ya faɗa ne dan ma ya sake cusa musu baƙin ciki.
A'a Gwadabe kar ka nemo mini wani abuncin. Duk abunda na samu zanci, ai jikin nawa da sauƙi." Hannu nasa na sauke Toye daga kafaɗarshi. Ya miƙo mun jakar hannun Bara'u na rataya. Jakar kayanmu kuma nace ya tafi mana da'ita gidan Bara'u tunda acan yake sauka mafiya yawan lokuta. Ina tafe ina jan ƙafata. Sai kallon banza aketa watsomun, harda masu tsaki, da tofar da miyau. Duk inda naga taron mata sai na gaishesu zan wuce, kuma fa saina rusuna mu a al'adarmu akwai wannan tarbiyyar. Wasu su amsa ciki_ciki, wasu ba sa amsaba a haka har na isa ɗakin Babala. Cike dam ɗakin yake da ƙannenta da yayyenta. Yaya Halima ma ta dawo daga Rakiya tana zaune tana cin tuwon shinkafa miyar kabewa sai ƙamshin man shanu take yi. Laila na zaune a kusa da'ita ta ci ado sosai, sai wani hararata take yi. Ina shiga na zube a ƙasa ɗaya bayan ɗaya na dinga binsu da gaisuwa, har Laila dana girma ban bari ba sai da na gaisheta.
"Sai ki tashi maza ki shiga cikin surukan gidannan ki kama aiki, baki ci ta zama ba" Cewar Baba Iyatu ƙanwar Babala. Miƙewa nayi ina shirin fita na jiyo Yaya Halima na cewa.
"Ki tafi da ɗanki babu wanda zai kular miki dashi" Yaron na kalla yayi tsuru_tsuru kamar ba dangin mahaifinshi ya shigo ba. Duk ƙin Gwadabe da dangina suke yi bai shafi abunda muka haifaba sam, amman banda dangin Gwadabe. Hannun Toye na kama muka fito tare. Da Gwadabe naci karo zai shigo ni kuma zan fita.
"Ina kuma zaki je ke da ba ishasshiyar lafiya gareki ba?" Ban ce mishi komai ba gudun kar in faɗi wata kalma da zata zama lefi.
"Aiki zata je ta kama ma su Haula. Ko su zasu girka mata abinda zata ci ne rasa kunya?" Cewar Baba Iyatu. Da sauri na wuce shi ina murmushi wanda yafi kuka ciwo. Shi kuma ina jiyoshi yana musu bayanin hawan jini ne dani, kuma likita ya hanani yawan aiki da zurga_zurga. Ni dai gaba na ƙara dani akaita hada hadar girki har sai da muka gama na zauna a kan turmi ina ba Toye abinci a baki. Sakina ce ta iso inda nake da fara'arta. Nima cikin fara'a na tarbeta. Kwanon hannunta ta ajjiye a gabana.
"Maman biyu ga farfesun kifi Gwadabe yasa nayi miki. Yace shi kaɗai kike iya ci ya zauna" Ɗan murmushi na ƙaƙaro na dubi Yaya Haula bata kallonmu amman kunnuwanta yana wajenmu.
Kai Sakina sai da ya saki wahala? Kinga ga tuwo nan ma ina jira Toye ya ƙoshi ne sai in cinye ragowar, jikin yanzu da sauƙi" Da sauri Yaya Haula ta yi ɓangaren Babala na yi imani wata fitinar zata je ta kunno mun. Ɗakin Goggo Innawo mu ka shiga, ita Goggo Innawo ƙanwar mahaifiyar Sakina ce a gidan take aure. Anan naci kifina muna hirar yaushe gamo.
"Oh Iyabo ashe rabon ƴan biyu ne ya dawo dake ɗakin ki. Irin rikicin da akaita tayi babu wanda ya zaci aurenku zai dawo, sai gashi har da cikin ƴan biyu" Dariya nayi nace.
Sakina kinsan duk abinda ya samu bawa da sanin Allah. Shan ruwan aurenmu ne bai ƙare ba. Duk rikici in Allah ya riga ya ƙadarto a dakin Gwadabe zan ƙare rayuwata, babu tsumi babu dabara ga duk waɗanda basa son tarayyyarmu. Ni aurena da Gwadabe ya ƙara mun tsoron Allah, anan na sake gane ƙudurar Allah. Irin badaƙalar da ta biyo neman auren ai me girma ce, amman da yake Allah ya yarda da haɗin ba gamu ba". Sakina tace.
"Wannan gaskiya ne. Mu kammu ba mui zaton aurenku zai yiwu ba. Duk da dai Gwadabe yana tsantsar sonki da burin son aurenki. Amman bai samu goyon baya a wajen kowa ba sai Bara'u. Bara'u kuma bashi da ikon zartar da hukunci a kan Gwadabe. Ba da ban Baba Magaji ba da yanzu wani labarin akeyi. Ke dai Iyabo ki ta yin haƙuri wata rana sai labari. Ko wacce mace da irin ƙalubalen da take fuskanta a gidan aurenta, muna barma cikinmu sirrinne kawai. Murmushi kawai nayi ina hango lokacin da Gwadabe yake zuwa taɗi ƙofar gidanmu a idanuna. Tun yana zuwa ana barinshi da dai Iyaa Debisi ta ga abun da gaske ne na riga na kamu da son Gwadabe sai aka hana shi zuwa gida wajena. Ni da Gwadabe sai dai mu haɗu a wajen da nake sana'ar tuyan ƙosai da kafa da daddare a bakin titin unguwarmu. Gwauron numfashi na ja kawai mu ka ci gaba da hirarmu da Sakina. Sai da na huta na yi sallar azahar. Muna yin la'asar kuwa aka aiko yaran gidan wai in zo bakin murhu za'a ɗaura sanwar dare. Faɗan irin wuyar da nasha ɓata lokacine kawai, aikin kusan nice ƙarfin yinshi, sukaita zamewa suna barina. Ga tuwon gidan bikin ƙauye ba tuwo bane na wasa, ni na talga tuwonnan na dinga ɗiba da ƙoƙo ina zubawa a tukunya lamba talatin sai juyawa ruwan zafin yake yi. Bayan na gama talge sai na koma wajen su Zuwaira mu ka ci gaba da wanke kwanukan da aka ɓata da rana. Wanke_wanke ne bana wasa ba. Muna tsaka da wanke_wanken Su Yaya Hambali suka zo wucewa ta wajen. Dukkansu suke tafe harda Gwadabe wanda na ga idandunanshi sun kaɗa sun yi jawur. Duk da magriba ta kawo kai akwai ƙarancin haske. Kallona kawai yayi ya girgiza kai suka wuce zuwa shiyyar Babala. Haka kawai sai na tsinci kaina a cikin damuwa gami da faɗuwan gaba, take sai jikina ya mace murus. Cikin dauriya na iya tsaiwa muka kammala duk aikin daya kamata
Gwadabe:.
Tunda ya shiga ɗakin Babala, Babala ta tare shi da ruwan faɗa itace harda kukan ta ji labarin Iyabo ta shanye shi, ta mai sheshi Ɗan aikinta. Duk ta hanyar da yaso ya ɓullo mata dan ta fahimci dalilin da yasa yake mata aiki, amman Babala ta fututtuke. Su Goggo Iyatu suma suka ara suka yafa, mai makon su rarrashi ƴar uwarsu sai ma sake zugata da su kai ta yi.
"Wallahi Kyauta wannan lefinki ne. Dan wallahi da nine Tanimu ya kwaso mun ƙabila da sunan matar dazai aura. In sama da ƙasannan zata haɗe bazai aureta ba. Ki duba yanda ya shure soyayyar ƙanwarsa Laila fa Kyauta. Da ba dan na kai zuchiyata nesa ba da zumuncinmu ai ya taɓu" ( Kyauta sunan da dangi ke kiran Babala dashi kenan. Babala kuma sunan da ƴaƴa da jikoki ke kiranta kenan) Cewar Goggo Iyatu kenan. Goggo Jummalo tace.
"Ai yanzu ma bata ɓaci ba Iyatu. Har yanzu Gwadabe zai iya auren Laila. Tunda har Laila ta iya kaso aurenta domin tana son Gwadabe .Ya kamata a wannan karon ya aureta ko dan dole dan ubanshi a nuna mishi mu muka haifeshi ba shi ya haifemu ba. Wallahi a wannan karon aurenshi da Laila babu wata makawa." Da sauri Gwadabe ya ɗago jin labarin mutuwar auren Laila ba ƙaramin kiɗimashi lamarin yayi ba. Ga wata magana da Goggo Jammalo take faɗe, shi yanzu ina ya ga ta yin aure alhalin abinci ma da ƙyar yake iya kaiwa gidanshi, har yanzu bai soma sana'a a matsyin ogan kanshi ba. Ta yaya ma zai auri Laila? Wannan ma maganace da bata dace ace an ma tare shi da'itaba, duba da irin halin talaucin da yake ciki, da kuma babban dalilinshi na ƙin Lailan a bayan. Da ƙyar Gwadabe ya yakice ya bar ɗakin Babala yana yarfe zufarshi. Yana hanzarin barin shiyyar ya jiyo muryar Laila a bayanshi tana kiranshi.
"Gwadabe ji mana dan Allah " Cak ya tsaya bai juyo ba, bai da niyyar juyowar. Sai itace ta tako har inda yake, ta fuskanceshi.
"Gwadabe guduna kake yi ne?" Kallonta Gwadabe yayi, tare da girgiza kan shi.
"Tayaya zan guje ki kina gudan jinina Laila? Na ga ai mun gaisa ko, ko akwai wani abunne bayan wannan?" Ɗan murmushi Laila ta yi tare da cewa.
"Babu komai. Ka ji labarin mutuwar aurena, da musabbabin mutuwar tashi ko?"
"Ai kina jiyo duk bayanin da su Babala suke yi mun. Allah ya daidaita tsakaninku da mijinki. Laila in da gaske dan ni kika fito daga ɗakin ki, kin tabka babban kuskuren da zaki jima kina cizon yatsan ki. Sam ni Gwadabe bani da ra'ayin ƙarin aure, lafiya lau muke zaune da Iyabo, bata rage ni da komai ba, ta bani dukkan lokacinta da zuchiyarta. Haka zalika ni ma zuchiyata tana gareta. Ina mai baki haƙuri a karo na biyu." Yana dasa aya ya wuce ya barta da jin kunya.
Yana tafe yana mamakin irin ƙiyayyar da su Babala suke yi ma Iyabo, duk da dai shima irin wannan tsanar akayi mishi a gidansu Iyabo. Da dama a cikin gidansu Iyabo basa ko amsa sallamarshi. Bayan sallar la'asar kuma Babala tasa akayo mata kiran kab yaran nata, dan Haula ta tsokata mata abinda ya faru a can gida Kano da safe kafin su tawo. Shine wannan wucewa da Iyabo taga sunyi. Bayan sun gurfana a gaban Babala da Goggo Iyatu, da Goggo Jammalo, da Goggo Takura. Duk waɗannan ƙannen Babala ne, babban wansu Baba Magaji shi yana Maraɗi tare da iyalinshi. Nan Yaya Hambali ya soma yi ma Babala bayanin abinda ya faru, harda ma waɗanda suka wuce.
"Babala Iyabo ta gama mallake Gwadabe, shi yake yi mata komai da kika sani. Wallahi Babala har ruwan wanka sai Gwadabe ya kai mata, haka zaki ga ta fito tana kallon su Haula ɗaɗɗaya. Duk abunda Gwadabe ya samu akanta yake ƙarewa tas. Ai kin ganta sai ƙiba take narkawa, shi kuma yana ƙarewa kamar wanda ake lasa. Ni shi yasa nace su bar mun gidana kawai, dan ba ƙaunar buɗe idanu nake in ganta a cikin gidan ba Babala. Tunda har Gwadabe ya soma takamun burki, wataran sai duka. Kafin akai ga hakan gara su tashi kawai, ina da buƙatar wajen nasu dama zan zuba dabino a ciki. Babala irin taɓarar da Gwadabe da matarshi suke yi a cikin gida kare fa bazaici ba. Wallahi sai ki ganshi da gajeren wando yana barbaɗa mata garin Amala ita tana tuƙawa sunayi suna waƙar yarbawa. Wannan baƙin ciki da mi yayi kama" Yaya Harisu yace.
"Gaskiya ne gara ya kama mata haya a can nesa damu Babala. Ƙazantar da baka gani ba tsabta ce. Dan wannan yaron baya ko jin kunyar idanunmu, wallahi zaki ganshi a tsakar gida yana wanki tana mishi shanya, wataran har waƙar yarbawa zaki ji suna rerawa abun takaicin ya iya waƙar. Gwadabe ya rasa wacce yake so duk dangi, duk cikin ƙabilunmu na Hausa fulani kyawawa, sai wannan buskutar beyerabiyar ce ta ja hankalinshi." Haka ɗaya bayan ɗaya kowa ya goyi bayan Gwadabe ya bar ma Yaya Hambali gidanshi. Shi kuwa gogan yayi ƙuri yana jiran irin hukuncin da Babala zata yanke. Gyaran murya tayi tare da cewa.
"Na ji bayananku kab, kafin ku koma za ku ji hukuncin dana yanke. Zanyi shawara da ƴan uwana, akan batun matarshi kuwa wannan ƙabilar? Alkadarinta ya riga ya kusan karyewa. Ku tashi kuje in Allah ya kaimu gobe zaku ji hukuncin dana yanke" A sanyaye Gwadabe ya bi bayan ƴan uwanshi. Zuchiyarshi cike da ƙuna gami da taraddadin me ka je ka zo.
Iyabo:
. Sai zuwa bayan isha na samu hutu. Duk mun baje a tsakar gida muna shan iska. Ina kwance akan tabarma nayi matashin kai da hannuna. Toye yana zaune a gabana. Ƴan uwa sai hira da shewa suke ta ta yi abun gwanin ban ƙawa, ni kuwa mujiya na kasance a cikinsu, komai a tsorace nake yinshi, bana son in ɓata ma dai_dai da yaron gidan na goye rai. Ina gani ɗazu yarinyar Asiya matar Lawal tana dukan Toye, babu wanda ya kula. Gashi ba sa'arshi bace dan zata yi shekaru tara da doriya ma. Sai da ta gaji dan kanta ta barshi.
Ina kwance barci ya soma dibata Yaya Halima ta zo inda nake tai mun ƙerere a ka.
"Mandiya hamshaƙiya sai ki taso ga can kayan miya da su alayyawo zaku gyara, gobe da asuba za'a aza tukunya" Da sauri na miƙe ina faɗin wash dan wani irin ƙara ƙuguna yayi mun mai zafin gaske. Toye na kwantar ya riga ya soma bacci a zaune. Tunda muka zauna zaman aikinnan ba mu bar aikin ba sai wajajen sha biyun dare, sannan kowa ya kwanta. Da asussuba kuwa washe gari muka tashi da aikin tuwo, dan kafin takwas na safiya mun kammala tuwonnan tas mun malmalashi mun jera a fantekoki. Zuwa ƙarfe sha ɗayan rana gidan biki ya cika danƙam da jama'ar biki, sai haya_haya kawai kake ji. Daga waje ma haka ƙofar gidan take danƙam da maza ƴan ɗaurin aure. Yaron Sakina ne yazo ya kirani.
"Umman Toye wai inji ummata kizo ki yi wanka" Allah sarki ni Iyabo. Kowa a gidan sai wanka akeyi ana kwalliya, yara da manya. Amman ni babu wanda yai mun ta yin wanka. Bin bayan yaron nayi har zuwa gidansu. A falon Sakina na samu Gwadabe da Bara'u suna zaune suna cin tuwon biki. Ƙur ya ƙura mun idanu, take na ji hawaye na shirin zubo mun, har numfashina na karkatsewa. Fitowar Sakina daga uwar ɗakine ya katse kallon ƙudan da muke ma juna.
"Maman
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 16