Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
na kwana a raina harma da mafarkin wai naje amman ban samu Uwani ba sai Hafizu mijinta. Washe gari tun asussuba nayi wanka. Ina yin sallah na fito da ƴar jakata ta hannu da kuɗaɗena a ciki. Kaya ko kala ɗaya ban ɗauka ba, nayi musu sallama akan zan biya wajen Dada da Boɗdo mu yi sallama. Daso ce ta fito domin yi mun rakiya. Muna fitowa muka ci karo da Yaya Hamma a zaune a bakin wata bishiyar darbejiya yana kallon ƙofar gida yaga yaushe zamu fito. Ba Daso ba ni kaina nayi mamakin ganinshi a wajen. Dan sai da nayi turus. Tasowa yayi ya nufo inda muke. "Yaya Hamma kaine da sassafe haka a ƙofar gida, zaman me kake yi a wajen?" In ji Daso kenan. Dariya yayi mata kawai kafin yace. "Tunda dai Allah ya ƙaddari ganawarmu ai shikenan. Babu gaisuwa sai tuhuma ko? Da fatan kun tashi lafiya" Muka amsa a tare, sannan mu ka gaisheshi cikin girmamawa. Gidansu Yaya hamma muka soma zuwa. A ɗakin Yafendo muka zauna, a gurguje mu ka gaisa na sanar mata inaso zanje birni amman kwana biyu zanyi. "To Allah ya dawo dake lafiya. Hamma sai ka kaita har tasha ka tabbatar motarsu ta tashi kafin ka dawo. Allah ya tsare. Hama da Boɗɗo suna garken shanu kuje ku samesu ko? Ke kuma Daso kizo in kin taso tallan Nono zamu yi magana muhimmiya dake" Kan Daso a sinne ta amsa da "To Yafendo" A garken shanu muka yi sallama da Hama da Boɗɗo. Sai adda'a su ke yi miki, daga nan sai wajen Dada. Ni da Daso ne muka shiga, Yaya Hamma fur yaƙi shiga yace Baffa faɗane dashi bai fiye son baƙi suna shigar mishi gidanshi ba. Mu ma muna shiga ya taremu harda sanda kamar zai dokemu. "Kai ku tsaya nan kar ku sake ko taku ɗaya a wajen" Ya faɗa da fillanci, Daso ce ta fassaramun abinda yace. Wannan kalma daya faɗa kamar ance Dada ta fito ta duba sai firit ta fito daga bukkarta. Su Cubu kuma da su Yusufu suna tsakar gidan, suna aikin dafa madara. Da sassarfa ta iso inda yake tsaye. Wallahi ɗaga sandar shi yayi kamar almara sai ya kwaɗa mata a goshinta jini ya yayi tsartuwa har a hijabina" Cikin hargagi yake yi mata magana da fillanci. Hannunta ta dafe da goshinta ta yi saurin juyawa, na fahimci umarni ya bata. Yusufu da Cubu ne suka yi kanta Cubu ta riketa zuwa ƙofar bukkarta. "Ku je Jabu. Zan dinga zuwa dubaki. Na mancene ban sanar miki ba ya kafa dokar kar ƙafarki ta tako mishi gidanshi" Da yarbanci tayi mun Magana. Ajjiyar zuchiya na sauke ina hango irin yadda sandar ta sauka a goshinta, ba tare da wani babban daliliba, ko da dalili addini ya bada umarnin a daki mace har a zubar mata da jinine? Ko da ma suna da ƙarancin ilimin addini, rayuwarsu a kiwo da tallar Nono take ƙarewa. Ji nayi na sake jin ƙarfin guiwar hukuncin dana yanke dan cire Dada a cikin wannan uƙubar. Hawayen daya zubomun nake shirin gogewa Baffa ya ɗaga sandarshi ya sauke mun a kafaɗata, zafin ya ratsa dukkan ƙasusuwan jikina kau,. Kafin in tantance tsakanin mamaki da tsoro naji Daso tayi ihu ta jani mun rufa waje a guje. A guje muka wuce Yaya Hamma. Sai biyo mu yayi da sauri yana tambayar ba'asin abinda ya haddasa gudun. Daso ce ta bashi labarin abinda muka tarar. Ni kam hawaye kawai nake sharewa ina kallon mayafina da jinin Dadana a jiki, sanadiyyar zuwa ganinta kawai aka zubar mata da jini. "Jabu kiyi haƙuri. Mu kanmu mun rasa yanda zamu yi mu tsamo Dada daga cikin halin da take ciki a wannan gidan. Amman abinda nake so dake shine dan Allah ki taya ta da adda'a, kuma zan baki shawarar kada ki sake zuwar mishi gidanshi, Dada zata zo har inda kike ta dubaki. Kar hakan yasa in kika tafi ki ƙi dawowa, hakan ka iya jefata a halin da yafi wanda take ciki yanzu. Zamanki tare damu zai iya kawo mata sauƙi sosai, kece babba ke zaki dinga rarrashin ƙannenki, kinga Boɗɗo kullum a cikin kuka da damuwar da Dada take ciki take." Ajjiyar zuchiya na sauke kawai nace. Babu komai, nagode da shawara. Daso ku koma daga nan ni zan tafi" "A'a ai kinji abinda Dadanmu tace dan haka har sai na tabbatar da fitar motarku a tasha. Daso ki koma gida ke" A wajen mu kai sallama da daso. Ni dai har muka gama wannan gwajab_gwajab ɗin fita zuwa gari hankalina baya ma tare dani. Wai duk haka Aure yake cike da ƙalubale kowa da irin nashi? Oh ya Allah ka kawo mafita a zamantakewar aure, ya Allah ka ba ma mata mafita. Har muka shiga cikin babbar tashar Adamawa babu wanda yace da wani ƙala a tsakanin ni da Yaya Hamma, dukkanmu sai tubka da warwara kawai muke yi, tare da karanta wasiƙar jaki. "Fullo Kano ne, ko Kaduna, ko Zaria ga motar Haɗejiya?" Cewar ma'aikatan tashar da suka nufo kanmu har suna rige_ rige. "Kano zata je, nawa ne kuɗin motar?" Cewar Yaya Hamma, tare da cusa hannu a aljihunshi. "Nera dubu da ɗari biyu zata biya" Kuɗin ya zaro ya kirga ya basu, ni kuma ya miƙo mun dubu da ɗari biyar. Ƙin karɓa nayi, ya dubeni rai a ɓace yace. "In baki karɓaba zaki barni cikin damuwa, da kokontan dawowarki rugar mu. Ni kuma dana tuna zaki iya ƙin dawowa, ko zaman rugarmu ya isheki take sai inji fargaba ta dirarmun. Jiya ɓarawon baccine ya ɗebeni shima cike da mafarkai akan tafiyar taki. Ungu kuɗinnan ko tsaraba kya yi musu" Nagode sosai Yaya Hamma, in sha Allah bazaan wuce kwana biyun ba. Kuma dan Allah ka je ka dubo Dada, ko a ɓoye ne ka kai mata magani, kai mata bayani kwana biyu zanyi" Yaya Hamma bai bar tasharnan ba har sai da ya ga fitar motarmu. Sai da motarmu ta yi nisa sosai na dena hango hannun Yaya Hamma a sama yana yi mun Adabo., ban dena waige ba har sai da na dena hango shudiyar rigarshi, Ajjiyar zuchiya na sauke na lumshe idanuna ina tunano yanda Baffa ya kabɗama Dada sanda. Wannan dalilin ne yasa kullum in zanga Dada sai in ganta cikin rashin guzari da rashin walwala, kullum cike take da tunani. Ta haɗu da azzalumin miji mai kafiya, tallar Nono ya cinye mata lafiyarta da kuzarinta. A shekarunta ya kamata ace tana zaune a nutse yaranta na hidinta mata, ba wai tai ta fita tallar nono, kuma mijinta na cin zarafinta harma da fitar mata da jini. Wallahi da Baffa zai iya amincewa in fanshi tallar Nonon Dada, da tuni na famsheta na zama ƴar tallar Nono kamar yadda ya zama al'adar matan fulani musamman mazauna rugage. Ya zame mun dole in yi duk abinda ya dace dan ganin na kawar ma da Dada Ƙwallar data daɗe tana zuba a idanunta. Gaga_gaga haka mukaita cin hanya, azahar, la'asar sai dab magriba muka shiga garin Kano, a unguwa uku muka sauka, ina fitowa titi na samu Bus har ƙofar layinsu Uwani. Na ko yi sa'a tana gida, tana tsakar gida tana kwasar tuwo Hafizu kuma yana shanya kayan yara a igiya. Tana ganina ta sau marar hannunta ta miƙe a zabure. "Iyabo kece haka afujajan?" Tana faɗin haka na fashe mata da kuka a tsakar gidan kamar ƙaramar yarinya. "Uwani jata kuje ciki maza" Cewar Hafizu. Hannuna Uwani ta ja muka shiga ciki, wallahi na fi minti talatin ina kuka take zazzaɓi mai azabar zafi ya rufeni. Uwani da Hafizu suka rufu a kaina suna ta rarrashina da ƙyar na haɗiye kukan nawa bakina na ambaton Allah. Ganin na ɗan samu nutsuwane Hafizu ya fita ya bamu waje. "Kawata lafiya kuwa kinga yanda ki kai baƙi kika rame kuwa? Gabaki ɗaya kin koma wata ƴar ƙauye, meke faruwa haka?" Cikin shessheƙa nace. Labarin da tsayi Uwani, amman bari in rama sallolina sai mu tattauna tunda abinda ya kawoni wajenki kenan" Ina gama faɗar hakan na miƙe jiri na kwasheni na fito tsakar gidansu dan kama ruwa da alwala. Uwani kuma taci gaba da aikin tuwonta, ina kan yin alwala yaran Uwani suka shigo gidan da sallamarsu. Matar gidan buɗar bakinta tace "Wannan wacce iriyar rashin tarbiyyace zaku shigoma mutane gida da gudu, kalan ku zubar mun da miyar da ko kayan ɗakin uwarku in an siyar bazai siya miyar ba?" Yaran su kai turus, ni dama nasan irin matsalolin da Uwani take fuskanta a gidannan shi yasa ban yi mamaki ba, gashi uwani ta kasance kamar zawayi wajen rashin haƙuri ai kuwa nan ta tanka. "Maman Shamsu kenan. Baƙin cikin ki takashinki zai koma da izinin Allah. Ni Uwani nafi ƙarfinki, kuma in mijinki yafi nawa mijin kuɗi, ai ni na fiki more aure tunda mijina bai taɓa zagin iyayena ba. Kuma bai taɓa korata da watan azumin ramadana ba, dan haka ki iya bakin ki" A mugun zafafe Uwani tayi maganar cike da hargowa. Yaran na kaɗa ciki dan gudun kar su kantamo kalmomin da suka shige shekarunsu. Da Uwani da maman Shamsu sun ci uwar sabada har sai da mazajensu suka dawo daga masallaci suka raba wannan ja'iba, dan wallahi na kasa riƙe Uwani sam, har zani Maman Shamsu ta fincike mata ya rage daga ita sai gwari na tsuma ( siket ɗin ciki). Ɗayar matar gidance ta ɗaukoma Uwani zanin ta ɗaura. Baban Shamsu cikin son bin goyen matarshi ba tare da bin ba'asin abinda ya faru ba yace. "A ɗayan biyu ya kamata ko ku ku bar gidannan, ko kuma mu tashi mu bar muku gidan. Wannan bala'in yayi yawa dan watarana wannan jarababbiyar karyar matar taka zata iya illatamun mata'" "Karya kace mata Ƙasimu? Uwani ba karya bace tunda bata leƙen mazan mutane in sun shiga bayan gida. Uwani Iyabo ku shige ciki kar ku tanka musu" Shigewa mu ka yi mu ka barma Hafizu faɗan. Matan gida sai ihu suke yi. Nifa harna rama sallolina ba'a dena gwabza habaice_habaice ba. Wannan ta jefa ma wannan, waccan ta rama, Uwani na tsaye a bakin ƙofa riƙe da labule sai ɓarin zance take ta faman yi. Yara kuma sai cin tuwonsu suke yi a yinwace." Uwani dan Allah ki rabu da Maman Shamsu ki shigo mu tattauna matsaloli" labulen ta saki muka shige uwar ɗakinta duk muka yada zango a kan katifa" Wai Uwani me matarnan take nufi dake ne haka?" "Sharri mana, baƙin ciki take yi mini. Jiya jiya fa na kamata tana barbaɗa mun garin magani a ƙofar ɗakina, kinga ɗauki babu daɗin da mu kaita yi kuwa? Mune har gidan mai unguwa fa. Amman kinga ta sake takaloni" Ajjiyar zuchiya na sauke . Labarin duk matsaloli na ba uwani, da ƙudirina da dalilin zuwana wajenta" "Lallai rayuwar mata cike take da ƙalubale mai tarin yawa. Wata matsalarta uwar miji irinki, wata matsalar ta ƙannen miji, wata jarabawarta maƙotane marasa ƙaunarta irina. Wasu dangin mij, wasu matan maƙota, wata ma abokin mijina, ko matar abokin mijinta sune matsalarta, banda kishiya da shegiya facala su ba'a lissafinsu ma. Na tausaya ma Dada aimun. Kuma ya kamata ku yaranta ku haɗe kai lallai ku nema mata takaddarta. Iyabo amman ramar da kika yi da sauyawarki ta ban tsoro" Hawayena na share. Uwani ƙauyene fa sosai can inda na koma. Babu ruwan famfo, sai wata rijiya guda ɗaya jol anan ake ɗiban ruwa, ba wutar lantarki, babu sabis ɗin waya, ba titi, amman suna da makaranta, sai dai al'ummar cikin ƙauyen aikinsu kenan kiyo, matansu kuma tallar Nono, suna da ƙarancin ilimin addini, ai dole ki ganni haka. Kuma jinya nayi magashiyyan sai an ɗaga sai an ƙwantar" Mun jima muna tattaunawa, sai da mu kai sallar isha mu ka ci abinci sannan Uwani ta zura mayafi muka nufi gidan Hajiya Salamatu. "To naji bayaninku. Amman Uwani kin mata bayanin komai da komai dai ko?" Cewar Hajiya Salamatu tana hakimce taci gwala_gwalai kunne da wuya, da tsintsiyar hannu. "E Hajiya na yi mata bayani. Sai dai itama bata da kuɗi kamar dai ni. Amman Hajiya in muka je can za'a cire a kuɗin aikinmu har mu gama biya. Mu ba ma daɗewa zamu yi a can ba shekara uku ya ishemu, dan da ita Iyabo shekara biyu ma tace" Hajiya tayi dariya tare da girgiza kai. MRS BUKHARI 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundati https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE GAWURTATTU UKU BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 15 Kafin tace. "Ba dai shekara biyu ba, dan a ƙalla ba a ƙasaru ba, zaku iya kaiwa shekara guda kuna biyan kuɗin jirki da duk abinda aka kashe muku. Sai dai in babban gida kuka samu suke biyanku kuɗi da kyau, amman in ba haka ba shekararnan sai kun yita. Babu rufa_rufa sai kun gama biyan kuɗin jirgi zaku samu damar yin aikin hajji da umara baki ɗaya. Amman muddin kuka zama masu hazaƙa da kazar_kazar to gidan da za'a kaiku aiki zasu soku, kuma in dawowarku najeriya tayi, su hadoku da goma sha tara na arziki." A nan na fahimci Saudiyya zata turamu, sai naji hankalina ya ƙara kwantawa. Kafin mu baro gidannan mata da tsofaffi a ƙalla mutane fin ishirin sai da suka shigo, duk akan batun tafiyar. Ni dai mun tsayar da magana akan gobe da safe in zo mu je hajj kam aimun fasfo kafin in koma garinmu, nan da wata ɗaya da kwana goma jirginmu zai ɗaga zuwa ƙasa mai tsarki. Muna tafe muna ɗan tattaunawa har bus ta saukemu a unguwar su Uwani. Muna sauka muka ci karo da mijin Uwani yana zaune a wata majalisar maza ƴan sa ido. Zumbur ya miƙe da ganinmu ya nufomu gadan_gadan. "Ke Uwani daga ina kike?" Ya faɗa a fusace. Tsaki uwani ta ja tace. "Aikin banza aikin wofi, ka dai ji kunya ka kuma yar da zuchiyarka kare ya cinye. Maza majiya ƙarfi masu zuchiya, ka gansu a titi suna aikin sufuri dan su rufa ma iyalinsu asiri. Banda kai Hafizu baka da aiki sai zaman majalisa, duk matar data wuce kuna ƙarema surarta kallo, ka barni da buga_buga mata a layi duk sun rainani" A faɗace take maganar tana yi tana kumfar baki. Shima zabura yayi ya ce. "Duk macen da take fita dai ba da sanin mijinta ba mala'ikun Allah har taje ta dawo suna tsine mata. Shashasha kawai." Tsaki ta buga fuu ta wuce ta barmu a tsaye. Hafizu ka ƙara haƙuri dan Allah. Dama har yanzu irin wannan zaman na rashin daraja kuke yi ma junanku? Ga yara sai sake girma da mallakar hankali suke. Ko dan su ya kamata ku sarara dan kune allon kwaikwayonsu, kai tunda kaine babba ka dena biye mata" "Shikenan Iyabo. Amman Uwani da kike gani bata da daɗi. Kwananta goma cib tana gaba dani, bansan sam abinda na aikata mata ba. Motsi kaɗan sai habaice_habaice" "Iyabo wai ki zo mu tafi kin kuma tsaya wani lallaɓashi" Ƙwafa tayi ta kawar da kanta. Har muka isa gida tana zazzago mun mita. A falo na kwanta ni da yaran, kafin gari ya waye kuwa suka jiƙani shakab da fitsari sai da nayo wanka kamar mai kwanan turaka dan har kaina sai da ya jiƙe da fitsari. Ai kuwa Uwani ta shiga jibgar yarannan kamar Allah ya aikota, haya_haya tsakaninta da Hafizu bai tsaya ba sai da ya gaji ya bar mata gidan tukunna. Ni na fitar musu da katifar na zuba ruwa katifar ta hau yarari tana gudana a tsakar gidan. Uwani kuma ta wanke musu kayan tas ta goge ledarta tsab da ruwan toka, gabaki ɗaya zarnin ya ɗauke. Dumamen tuwo tayi mana bai ma isaba saini na ba da hamsin aka siyi gasara da siga Uwani ta dama mana. Muna karyawa Hafizu ya leƙo "Ki kawo mun abincina ina tsakar gida" Yana faɗa ya saki labulen tare da jan dogon tsaki. Kai mishi abincin tayi ta dawo muka ƙarashe namu, a gurguje muka fita a gidan bayan ta sallami yara ƴan islamiyya. Ni ko Uwani kin je kin dubo su Toye kuwa?" Ɗan murmushi Uwani tayi tace. "Na yi tunanin Hamma ya goge miki tunanin Gwadabe ne ai Iyabo da baki tambayesu ba" Dariya nayi nace. Ko kusa meye tsakanina da Hamma da har zai ture matsayin uban ƴaƴana a zuchiyata? Shi fa Gwadabe Mijinane, shi ko Hamma ɗan uwanene kuma wa a gareni mai kulawa dani. Uwani kinsan Allah son Gwadabe nunkuwa yake yi a duk ranar duniya, bana jin zan iya sauraren wani da sunan aure a zahirin gaskiya" Ajjiyar zuchiya na sauke take ƙirjina su kai mun nauyi. "Naje kusan sau uku dubo ƴan biyu. Allah cikin ikonshi ban samu ganinsu ba, har shi Gwadaben. Sai da mu kai zageni in zageka da wanna figaggiyar matar wan Gwadabe Haula take ko Zuriya oho" Gabana ya yanke ya faɗi nace. Shikenan duk yanda akayi rayuwar yarannan ta koma ƙauye, ni da naso yaran su samu ilimin zamani tunda ni da Baban nasu iyakarmu kammala sakandare. Yarana sun zama ƴan ƙauye shikenan" Kuka na saka a hanya muna tafe kafin mu samu abun hawa. Da ƙyar da siɗin goshi Uwani ta shawo kaina. Amman fa har muka isa gidan Hajiya Salamatu bana cikin hayyacina, muna zuwa aka kwashemu a golf kusan mu tara zuwa hajj kam, anan muka amsa tambayoyi dai haka bamu jima ba duk yawanmu kuma akwai sanayya sosai tsakaninsu da ita Hajiyar. Muna bakin ƙofar Hajj kam ɗin a tsaye Uwani na kuma tausata wata mota fara sol tayi tsaye a gabanmu, ita bata wuce ba, gashi ta tare mana ganin gari" Wani dattijone baƙi mai haiba da kwarjini ya fito. Saye da yadin boyel mai ruwan ƙasa, kansa saye da hular zanna bukar, ga zobe ga agogo, ga takalminshi sau ciki irin na ƴan gayun maza. Abun almara sai muka ga ya tsaya a gabanmu. Gemu mai shi kombineshon ɗin fari da baƙi na kalla "Assalamu alaikum ƴan mata" Ya furta da muryar kamana muryarshi da kauri irinta tsayayyi dakakkun maza, sai buso ƙamshi yake yi" "Ba dai ƴan mata ba. Ko wacce da yaranta, kuma ai ko da wasa ba mui kama da ƴan mata ba" Cewar uwani balbalin kenan, ni ko fa bance komai ba. Wannan dattijo yayi murmushi har haƙorin makanshi fari ya bayyana. "Allah ya ba manyan mata haƙuri. Dan Allah kuna da aure ne?" Ya tambaya, sai naga fuskarshi ta cika da fargaba. "Ni dai ina da aure. Amman Iyabo a kasuwa take" Sai ya sauke ajjiyar zuchiya tare da murmusawa yace. "Alhamdulillah. To Hajiya in ko babu damuwa inaso mu ɗan yi magana a gurguje, dan gudun kar in katse muku hanzarinku" Carab uwani Tabalbalin tace "Babu komai bari in matsa in baku waje" Ai kuwa sai ta karasa wajen matan da muka zo tare dasu tayi tsaiwarta "Sunana Buhari Namoriki. Nazo shiga Hajj kam ne Allah yasa nai tsuntuwa dake. To a gurguje zanso jin sunanki da unguwarku sai in zo gida in sameki yafi mutunci" Ajjiyar zuchiya na sauke. Idanuna suka cika bam da ruwan hawaye, sai nake jin kamar tsaiwa da wani namiji da sunan soyayya tamfar cin Amanar Gwadabe ne" "Malama Iyabo baki ce komai ba" Na ji sunana raɗau a bakinshi. Sunana Iyabo kamar yadda ƙawata tace. Unguwarmu kuma ni ba ƴar garin bace ma, zuwa nayi gobe zan koma ina mai baka haƙuri" Murmushi yayi yace. "Ai mai son ɗan tsuntsu shi ke binshi da jifa. Kuma garin masoyi baya nisa, in kika bani dama ko adireshi zaki ganni" Ba ko wanne garin na masoyi bane baya nisa. Ka ganni ƴar ƙauye ce a jeji nake rayuwata, babu wutar lantarki balle har sabis ya isa mana, gashi ban shirya aure ba. Wallahi ko zan yi aure bazan auri ƙabilar da zata zama tana ƙin ƙabilar dana fito ba" na ƙarashe zancen cikin rishin kuka. Hajiya Salamatu na hango ta fito, a wajen na tafi na bar Buhari a tsaye. Har motarmu ta fice fit yana tsaye yana ƙarema motarmu kallo. Ko da muka isa gida Uwani Tabalbalin ta balbaleni da faɗa akan me zance ma Buhari haka? Ta tambayeni ne na bata labarin yanda mu ka yi. Uwani ai ni da Bahaushe sai dai zumunci. Amman bazan sake auren Bahaushe ba. Bama yanzu zan yi aure ba kin ganni nan. Mu da muke da tafiyar da zamu yi har tsawon shekaru uku, da dakon soyayya kike son inje inyi wanna shekaru? Dame zanji, da mutuwar aurena, ko da mayar mun da yara ƙauye, ko da matsalar Dada?" Da rishin kuka na masifa nake maganar. Uwani sai ita ta sakko, zama tayi ta dafani. "Kina da gaskiya ƙawata. Amman da ba irin rabuwar da kuka yi ba kenan. Rabuwa salamun_salamun yafi, domin bakasan inda rana zata faɗi ba. Batun yaranki da zan baki shawara ki ɗauka da kin sa ƙafa kin yi fatali da sha'anin, domin yafi ƙarfinki. Ba dole sai sun yi karatun boko darajarsu zata ɗagu ba, akwai arzikin da yafi noma ne? Babu shi da noma yaranki maza zasu iya azurta Iyabo, ita mace aure dama ka iya kaita jeji ma, ki bisu da adda'a zata bisu har gadon baccinsu Gwadabe kuma nasan ya cika jarumi, kuma yayi miki halacci. Amman cireshi a zuchiyarki wajibun ne saki ukune a tsakaninku. Ke ko saki ɗaya yayi miki yaci ki haƙura kema kiyi fatan samu sabuwar rayuwa a gaba. Kawo ɗari a siyo taliyar murji mu ɓararraka ina da maggi da ragowar manja. Kullum aikin kenan nike faɗi tashin neman abun rufin asirinmu, ke Iyabo har wanki da guga inayi a cikin gidannan, yawon wanke_wanke a gidajen masu hali ko shagunan cin abinci har ya zamemun jiki" Ɗari da hamsin na bata dan yara ma in suka dawo sa lasa. Ita da kanta ta fita ta siyo, tare mu kai hidimar komai muka baje a tsakar gida, Maman Shamsu tana zaune a kan turmi tana fige kasa tana waƙoƙin neman masifar da ta saba. A tukunyar muke ci, mun ɗebama yara nasu, Hafizu kuwa nayi roƙon duniya ta dibar mishi Uwani tace bai isa yana zaune a majalisa yana aikin bin matan mutane da ido ta ajjiye mishi abinci ba. "Amman iyaa Debisi da shi kanshi Debisin basu san kin shigo Kano ba?" Sai da na haɗiye taliyata na tsotse yatsuna daya jiƙe da romon da ya ji kafi zabo kafin nace. Babu wanda yasan na shigo. Gobe zan daka sammako in koma. Zanje inci gaba da jiran lokaci in Allah ya kaimu. Kuma inaso in tattauna sosai da Dada ta san ƙudurina, ta goyi bayana akan tafiyar da kuma batun Mahaifin su Baɗɗo. Zan soma zama dasu Boɗɗo tukunna mu tattauna in ji ra'ayinsu. Kuma naso in ɗan dinga ba matan Rugar ilimin addini iyakar abinda na sani, ko dan karatun sallarsu ta yi kyau. To basu ma da lokacin kayinsu ne shine matsalar. Amman su ƴan uwan nawa zan tsaya a kansu kafin in tafi in ɗan gyara rayuwar tasu" Washe gari asubar fari Uwani ta rakani tasha, ta ɗan tsintomun kayanta kala biyu da wanda na sauya a jikina uku kenan. Naso in mata turjiya amman taƙi sam dole haka na karɓa. A tashar na ɗan sai maganin ciwon kai, da maganin ciwon ciki, da maganin zazzaɓi , dana rage zugi ko wanne kati_kati. Inaso in bayar a kaima Dada ta ɗan dinga sha, sauran kuma in ajjiye a wajena. Taran safe motarmu ta ɗaga. Gwadabe:. Takai. Tun a ƙofar gida ya hango motar Yaya Hambali a gefe guda, kuma ya ga Nazifi na zance da Nana ƙanwar Layla. "To Gwadabe ni da Toye zamu wuce gida, in kun gama ganawa da Baba Magaji dasu Babala ka sameni a gida" Cewar Bara'u kenan. "To Shikenan sai nazo. Ka isar da saƙon godiyata ga Sakina" Yana faɗar haka ya shige cikin gidan. Da Nazifi da Nana babu wanda ya kalli Gwadabe balle su gaisheshi. Zumunci ya riga da ya taɓu, ana rikice_rikice a gaban yara suna ji suna gani, sai su taso da raini da rashin ganin girman wanda aka watsar a gaban idanunsu. Wanda ake mutuntawa kuma a

Chapter 14 of 16