Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
sai shi, a birni take aure can Kano" Murmushi ya sake faɗaɗawa yace. "Sannu da zuwa, baki tawo mana da yaran ba?" Ɗan murmusawa nayi bayan mun gaisa nace dashi. Na baro yara a gida sabida makaranta" Baice komai ba sai ɗan murmushi da yayi, ya kaɗa shanu sama da talatin suka bi bayanshi da ƴar sandarshi da halama kiwo zashi. Ni dai ina raɓe a bayan Hama tsoron shanun nake yi, ina dai kallo Boɗɗo na tatso nonon wata farar ƙatuwar saniya mai baƙin ido, ita kuma Hama tana dai ta shafama wannan saniya magani a duk jikinta, kuɗa sai damun saniyar suke yi tana ta kaɗa kanta. Fitowarmu daga cikin garken kenan sai ga su Cubu sun shigo gidan, amman ta wata ƙofa da ban ba ta ƙofar da muka shigo jiya ba. Idanu na ƙura musu, su basu da fari can ɗinnan . Yanda duk suke kallona a kunyace su nai mun kallon so da ƙauna shi yafi komai burgeni sosai. A barandar dake ƙofar bukkar Boɗɗo muka zauna. "Adda Jabu wadannan duk ƙannenki ne iyakarmu mu huɗu ne, shi Amaduyal shi baya nan. Iyakar yaran Dada kenan, nasan baki san iyakarmu ba, kamar yadda suma duka babu wanda ya sanki sai ni, nima saninna gani ɗaya ne." Daɗi ya lulluɓeni ganina a cikin ƴan uwana cikin Dadana, kuma sai kirana suke da Adda Jabu fuskokinsu da zuchiyoyinsu a cike da fara'a. Nawa bazai ma musaltuba. Tuwon farar masara aka kawo mana ɗumame da baƙar miya kamar kwalta, ko miyar meye wannan oho, sai madarar shanu mai zafi, tuwon sai ƙamshin man shanu yake yi. Loma ɗaya da nai karambanin sakawa a bakina da ƙyar da maƙyarƙyata na iya haɗiyewa tare da danneshi da Madara mai ɗumi. Muna zaune a wajen ina ɗan musu tambayoyi suna bani amsa, wata hausar ma da ƙyar suke fahimtar me nake nufi sabida tayi musu girma. A bakinsu naji ai kullum Dada tana zuwa cikin bini kai nono, fura, da man shanu. Tsawon tasowarsu da hakan suka san iyayen nasu, su kuma yara maza kiwon shanu suke fita yi, in suka girma har gari_gari suna iya fita kiwon shanun. Boɗɗo tace. "Ko ni ma kullum ina fita tallar nono, mu da kuɗin wannan nonon muka dogara, bamu da wani abunyi sai kiwo. In mace ta siyar da nono, a ciki zasu ci su sha, su yi sutura, har su tara kuɗin magani in wata saniya ba lafiya a nema mata magani dashi. Ƴan mata kuma da ba aure a kansu, da kuɗin tallar nononsu ake yi musu kayan ɗaki da komai da komai, wata ma har ta tara kuɗi itama ta sai ɗan maraƙi da haka har su zama garken da yaranta zasu ci gado suma. Matan ma a wasu gidajen suna fita kiwo. Ko su Cubu suna zagayawa amman da awaki ba shanu ba." Jigum nayi ina ta kallonsu jikina a mugun mace. Dama duk uba uban tsarabar da Dada take yi mun in zata zo ganina da kuɗin tallar nono take yowa?" Sai naji zubar hawaye masu zafi, tare da saka ɗamarar sauya ma Dada wannan rayuwar tallan da izinin Allah. Ana cikin haka sai muka jiyo sallamar Dada ita da wasu mata su su biyu, sai namiji guda ɗaya sun shigo kai tsaye kasancewar gidan duk dangin junane. Ɗakin Yafendo Kaɓoji suka nufa, mu kuma muka mara musu baya zuwa cikin bukkar. "Zo Jabu ki zauna a kusa da Yafendonki." Wata mai kama da Dada ta faɗa. Kusa daf da ƙafafunta na zauna kaina aƙasa na gaishesu cike da ladabi. Suma cikin karramawa da haba_haba suka amsa. "Wannan ƙannenane duka. Ga Yafendo A'i, ga yafendonki mai sunanki kin zauna a kusa da'ita. Zai Baffanku Musa gashi, sai Yafendonki Kaɓoji gata nan itace surukar Baɗɗo,. Ta nuna mun mahaifiyar mijin Boɗɗo. Kafin ta ɗaura da nuna mun su Cubu tace. " Wadannan kuma duk ƙannenki ne kece babbarsu, Amaduyal baya nan shi kuma na faɗa miki tun jiya." Murmushi kawai nayi dan na lura a damuwa Dada take sosai. Yafendo Jabu ce tace. "Zan ɗaukeki in tafi dake gidana, can ma akwai Daso shekarunku zasu yi ɗaya mijinta rasuwa yayi ya barta da yara tara. Zan zagaya dake dangi su ganki, zaki ɗan jima kafin ki koma ko?" A sanyaye nace. Na dawo nan da zama baki ɗaya ne, auren nawa ya ƙare. Kuma dan Allah a hannun Dada nake son zan zauna" Gabaki ɗaya suka kalleni, banda Dada domin ita bata wani gane Hausa har sai da ƴan uwanta su kai mata tafintar abinda na faɗi. Da sauri ta ɗago ta kafe ni da ido cikin yaren yarbanci tace. "Yanzu sai da wannan auren ya mutu, dangin mahaifinki sun ƙi barinki kiyi zaman auren ko? Dama tun farko da dan tani akabi da Debisin dai zaki aura domin shi yafi cancanta da sanin daraja da kimarki. Ita Iyaan taki ce ta amince miki ki dawo hannuna da zama alhalin tasan komai, zamana tare dake Jabu bazai yiwu ba. Tun jiya da kika shigo garinnan ban runtsaba har zuwa wayewar garin yau. Abinda nake so dake shine ki bi Yafendonki ki zauna a hannunta akwai Daso zaku dinga zuwa tallar nono tare, komai ma zaku ringa yi a tare. Amman ina mai baki shawarar ku koma birni inda kika fi wayo ki ci gaba da zama rayuwar Ruga cike take da ƙalubale, kumama ba iyawa zakiyi ba. Nima in kuɗaɗena suka haɗu zan je in dubo yaran naki. A hannun dangin ubansu kika baro su?" Wasu zafafan hawayene suka gangaro kan kumatuna, tabbas akwai matsala shin mijn Dada baya ƙaunar ganina kenan, baya son ya samu ladan riƙon marainiyar Allah, ko da wani abunne wanda ni ake ta ɓoye mun ne? Duka waɗannan amsoshin na adanasu inaso duk lokacin dana samu lokaci mai kyau da Dada zata amsamun, ta bani tarihin mahaifina cikakke. Dan bansan wasu abubbuwa a game dashi ba sosai. Na dai san sunanshi, sai hotonshi babba dake kafe a falon Iyaa, sai hirarshi da watarana ke shigowa cikinn zance haka in su Iyaa na yi a tsakar gida. Baffa Musa yace. "Allah shi kyauta. Ni ina ganin tabi Jabu ta zaunaa a hannunta ko babu komai zasu dinga ɗebe ma juna kewa ita da Daso. Kuma komai zasu iyayi. Dan in hanuna nace ta komo bani da wata budurwar ƴa a gabana ma. Tunda tace tana son zama a zuba mata ido, in taji wuyar da bata sababa da ƙafafunta zata koma Birni aradu" Yafendo kaɓoji tace. "A barta a hannuna tana ganin Boɗɗo sai hankalinta ya kwanta, kuma anan akwai Hama naga tun jiya da tazo suke hirarsu tare, kuma akwai matan ƙannenta a cikin gidan ƙila tafi jin daɗi. Kema Adda Daso zuwa ganinta zai fi miki sauƙi. Zasu dinga zuwa tallar nono da Hama dan kar damuwa ta dameta." Baffa Musa yace. "A'a ki barta dai Jabu ta tafi da'ita can wajen nata. Ita kanta Daso tana buƙatar wacce zasu dinga shawartawa dan gudun damuwa. Ke Jabu ki je ki ɗebo kayanki sai ku tafi, Allah bashi in ita Daso mahaifiyarki ta samu daidaito da Mijinta kya dawo hannun nata, duk da nasan mutumme bauɗaɗɗe ga taurin kai da dagiya. A kan ki meye ba'ayiba a shekarun baya da suka shuɗe. Ita yar mahaifinkiToyosi ai tasan komai yaƙi an yishi" Bani da zaɓi dole haka na kinkimi jakata na bi Yafendona zuwa gidanta, tafiya mu ka yi mai ɗa karen nisa, kamar ma ba ƙauye ɗaya suke da Dada ba, kuma fa a ƙafa su kamar ma basa son hawa Acaɓa. Gidanta kam ita kaɗaice a yadda na lura daga ita sai mijinta da yaranta. "Jabu ga ɗakin Daso ki shiga ki ajjiye jakarki, zan tafi tallar nono yanzu, ki shirya sai in kai ki wajen Daso ku zauna kina tayata miƙa Nono. Mu nan ba'a zama daga masu kiwo sai masu fita tallar Nono " Ɗan murmushi na ƙaƙaro kawai. Bukkar data nuna mun ciki na shiga na ajjiye kayana a gefen gadon ƙasa, a kusa da inda naga jakar kayan da nake zaton na mai ɗakin ce Daso. Taya Yafendo ɗaukar ƙwaryar nono ɗaya da buhun bakonta nayi. Muna tafe muna cin karo da mata da yara kowa da ƙwaryarshi ta nono a ka za'a tafi talla. Maza da samari kuma sai wuce mu da garke_garken shanu suke yi suna shiga jeji kiwo. Rayuwar ƙauyen ta matuƙar bani sha'awa, gasu da tsabta ainun kamar ba ƴan ƙauye ba ma, ƴan ƙazaman basu da yawa. Wannan akori kurar muka kuma shiga cike da mata masu tallar Nono, sai yarata yaren Fulani suke ta faman yi, ni dai ina cikinsu ƙwalam har muka iso babban titin mota inda matafiya ke wucewa, anan naga mata da yara jejjere a titi sai ƙulla Nono a leda suke yi, wasu kuma suna damawa. "Mu je kinga ga can Daso bari in kai ki wajenta, ni cikin gari can nake zuwa tallan nono ni da Daso uwarki" Zungui_zungui na bita har gaban wata siririyar fara sol ɗin mace kamanninta kamar an tsaga kara ita da Dadarmu, har kaminnin ya ɓaci. A cikin yaranta ma babu wadda yayi kamannin da ita irin haka. Dariya Yafendo tayi ganin irin yadda na ƙure Daso da ido. "Daso kenan mai kama da Adda Daso sak. Sanadiyyar kamanninsu ne yasa taci sunanta. Daso ga ƴar uwarki tazo daga birni . Zata taya ki siyar da Nono, in yaso zuwa gobe itama sai ta fito da nata ƙwaryar." Hannuna Daso ta jawo ta matso dani kusa daf da'ita. Sai farin cikin ganina take yi kamar dama can ta sanni. Da Yafendona ta yarata mata wacece ni da yare ai sai ta rungumeni tana mai cike da farin ciki. Nima sai naji zuchiyata ta ɗan yi wasai. Anan Yafendo ta sake hawa abun hawa ita da tawagar wasu mata. Mu kuma duk motar da tazo wucewa sai mu tawo da gudu ana turereniya a tsakani, yayinda kowa ke son asai nashi. Haka suke yin tallarsu. A gefen titin cikin ciyawa mu kai sallar azahar, Daso ta dama mun fura da nono da siga cikin ƙoƙo. Tas na shanye furarnan ga nonon ba tsami sai garɗi. Wajajen bayan la'asar lis muka ɗau hanyar komawa gida, nono da furar da Daso ta ɗauko ya ƙare duka. Ko da muka doso ƙofar gidan sai mu ka ci karo da Yaya Hamma mijin Hama a tsaye a ƙofar gidan hannunshi riƙe da ƴar baƙar ledarshi. Yana ganinmu yayi murmushi. "Yaya Hamma kaine a tafe da yamma sakaliya haka?" Cewar Daso kenan. "Nine Daso, kin ganni na jima ina sallama ashe babu kowa ne a gidan? Jabu har dake baƙuwa aka je tallan Nono, har kin huce gajiyar tafiya kenan?" Kaina na sauke ƙasa ina wasa da zoben azurfar da Gwadabe ya sai mun lokacin muna nema. In ma na zauna Ni kadai a gidan, ba daɗi zanji ba, tunanine kawai zai addabeni. Amman kaga dana shiga cikin mata ƴan uwana sai na ji daɗi." Shiru yayi baice komai ba. Daso tace. "Yaya Hamma mu shiga daga ciki mu zauna ai hirar zata fi daɗi ko?" Bai mata musu ba, ya kutsa kai cikin gidan muka mara mishi baya muma. Kano Gwadabe:. Tun bayan fitar Iyabo daga ɗakinta bayan Babala ta tursasa yayi sakin. Hawaye suka zubo daga guraben idanuwanshi. Yana jin wani zafi da turirin zuchiyarshi, ji yake tamkar rayuwarshi ce aka tsayar mishi. Maganar Yaya Hambali ne ya dawo dashi cikin hayyacinshi. "Shikenan ɗan uwanmu ya dawo mana, kai yau zan zuba ruwa a ƙasa in sha. Babala ni sabida jin daɗin wannan sakin ko? Zan buɗe ma Gwadabe katafaren shagon kayan masarufi, uwar kuɗince kawai tawa amman dangane da riba ko ta miliyan zai samu babu ruwana da kuɗinshi." Murmushi Babala tayi tace. "Ato yanzu ne shi kanshi zai dawo cikin hayyacinshi daya rabu da ala ƙaƙai. Kasan Allah duk abunda Gwadabe yake yi ba'a cikin hayyacinshi yake ba sam yarinyar ta game dabaibayeshi da asiri baya ganin kowa da gashi. To ta faru ta ƙare, ni naso ma ta tafi da yaranta da zai fi, dan babu wanda zai ƙaunacesu, kuma bazan bari Laila tayi wahalar yarannan ba wallahi." Yaya Hambali yace. "Yanzu ma ai sai dai ki tafi dasu ƙauye Babala kafin yayi wani auren sai a dawo ma da Laila su, ki dai yi haƙuri Lailan ta riƙesu" Sai da aka ambaci Laila ne Gwadabe ya ɗago idanuwanshi da suka rine ya kalli Yaya Hambali kallon tsab. Ya dawo da kallonshi ga Babala itama. Ai ko karen haukane ya cijeshi ba ya auro Laila ya ajjiyeta a gidanshi matsayin mata ba. Yarinyar data kasa riƙe amanar aurenta take turo mishi da saƙonnin soyayya da igiyoyi uku a kanta itace zai auro ya ajjiye a gidanshi matsayin uwar ƴaƴa. A ɗauri kashi ko a ɓata igiya. Kab ƙauyan Takai waye bai san Laila ɓarauniya bace, ko ɓera sai dai ta zama yayarshi shi ƙaninta. Bai dai ce dasu uffan ba har suka gama maganganunsu da baya fahimtar komai suka fice. Toye ne ya fito daga ɗaki yace da Abbanshi. "Abba yinwa muke ji" Hannun yaron ya jawo ya ɗaurashi a cinyarshi yana kallonshi. Bakinshi irin na iyabo babu maraba, hawayen dake shirin zubo mishi yayi saurin ɗaukewa da hannunshi. "Bari in kawo muku abinci ko, ina Taiwo da Kahinde suke?" Ya tambayi yaron. "Suna ɗaki sai kuka suke yi" Ba shiri ya miƙe tsaye, hannun Toye ya ja suka shiga ciki. Taiwo ce take ta kuka ta kifa cikinta akan gado. Kahinde sai bubbuga bayanta yake yi yana gwarancenshi. MRS BUKHARI 3064127935 Buhari Ibrahim Ladan First bank Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan. Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya. Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE) 300 kacal zasu iya kuɗin karatu NAMA YA DAHU... ROMO ƊANYE BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI 13 Tausayi gami da ƙaunar yaran ta shigeshi ainun. Harma yake ganin ganinsu ne kaɗai ka iya rage mai zafi da turirin rashin Iyabo. Haƙiƙa yayi rashin macen kirki, macen da tafi kowa sonshi da sanin hamimmancinshi. Ji irin wuya da ɗawainiyar da ta dinga yi a sanadiyyar ciwonshi. Amman ji irin sakamakon da su Babala suka yankar mata na tarwatsa duniyarta, tare da farraƙata akan ƴaƴanta da mijinta. Rungume yaran yayi jikinshi babu laka sam, rarrashin Taiwo yayi har sai da tayi shiru. "Toye zo ka kula dasu bari in siyo muku waina kuci" Yana faɗin haka ya fice, babu ko nera biyar a jikinshi, bashin mai wainar ta bashi na wainar hamsin, ya dire musu suka ci, suka sha ruwa. Fita yayi ya shiga kitchen ɗin Iyabo ya kunna risho ya ɗaura musu ruwan wanka. A kitchen ɗin yayi zamanshi tare da tariyo irin rayuwar da su ka yi da Iyabo, da irin nutsuwa da farin cikin da take samar mishi babu dare babu rana. Yana kitchen ɗin Babala ta leƙo da kwanon abinci a hannunta, ganin yanda yayi tagumi ya tusa risho a gaba ne yasa tayi turus a tsaye da kwano a hannunta. Yaran kuma tana jiyo ƙiriniyarsu. "Gwadabe au so kake yi tunani ya halakamun kai. Alhalin ita tana can hankalinta a kwance?. Yanzu me kake yi a ɗakin girki" "Ruwan wanka nake tafasawa zanyi ma yaran wanka Babala" Harara ta watsa mishi tare da cewa. "Ba cewa nayi maka zan tafi dasu ƙauye ba, ka ganni abinci na leƙo in ajjiye maka fa, sai in ɗebesu danyanzu zan juya yau muna da biki a gidan mai gari" Ajjiyar zuchiya ya sauke, tare da tasowa jiki ba kuzari, kirjinshi kuwa sai harbawa yake yi, zuchiyarshi na watsa jini jikinshi bisa rashin ƙa'ida. Hakanne ya haifar mishi da jin jiri da mashasshara mai zafin gaske, dan har hucin zafi yake ji a fuskarshi. Bakinshi kuwa tamkar maɗaci aka zuba mai haka yake ji. Inda Babala take tsaya ya isa. "Babala yarannan ni zan riƙesu da hannuna. Inaso zasu yi karatu mai zurfi ba zasu yi rayuwa a Takai ba. Kab yaran gidannan a cikin gidannan su ke rayuwarsu, wasu muna tare dasu, wasu kuma sun yi aure. Dan haka nima zan riƙe yarana" Babala tace. "Da kyau Gwadabe. Dama ni dan in tausaya maka in ɗauke maka nauyine a matsayinka na namiji. Amman tunda har kana ganin reno abune mai sauƙi, gaka ga yaran. In sun ga dama suga ƙarshen biro. Duk karatunsu ai basu isa ganin ƙarshen biro ba. Kuma ka shirya sati me zuwa ka tawo zance wajan Laila ka shiga sahun manemanta, dan manema sun yi mata ca a halim yanzu kowa so yake ya ɗauketa, ni kaga tafiyata" Ta dure mishi kwanon abincin nashi ta fice tana surutai tare da kutuntumawa Iyabo da yarenta zagi. Idanu Gwadabe ya lumshe kawai. Shi yaima yaranshi wanka fes, ya ja hannunsu har zuwa islamiyya kasancewar ranar asabar ce babu boko. A hanyar shi ta dawowane yaci karo da yaya Hambali a mota zai tafi kasuwa sai ya ɗan dakata. "Gwadabe daga ina kake haka? Kaga takalmin ƙafarka ɗaya naka ɗaya na matarka ne fa. An ya Gwadabe asirin da dangin Iyabo su kai maka ya gama sakar ka kuwa, sai kace wanda akace ma Babala ta riga mu gidan Gaskiya" Numfashi dogo Gwadabe yaja, ya kai duba kan ƙafafuwanshi, zahiri takalmin Iyabo ya ƙaƙaba a ƙafarshi duk rabin dunduniyarshi a ƙasa yake, takalmin ma kuma mai ɗan tudu. Ɗayar ƙafar kuma takalminshi taka teba ya saka. Allah yana gani baya cikin hayyacinshi balle har ya fahimci ƙafarshi a matse take, ko yaji yafi tuɗu ta ɓarayi guda. Murmushi kawai yayi. "Kaga yara na miƙa makaranta, bansan wari da wari na saka ba, hankali shine gani, idanu ƙululun kawai ne." Kallonshi Yaya Hambali yayi wata ƴar dariya harda shewa kafin yace. "To sai zuwa yaushe zaka soma zagayawa kasuwar, tunda dai sauƙi ya samu, kuma Iyabo data raɓeka ta raba mu da kai ta zama tarihi a rayuwarka. Kaga ai sai ka zo mu ringa tafiya kasuwa, kwanannan kaima zaka sai motar da kake so ka dinga tuƙawa" Murmushin yaƙe wanda yafi kuka ciwo Gwadabe yayi, yace. "Nagode da tayinka Yaya Hambali. Amman bana jin zan amshi wannan tayin naka. In na warware da kyau zan nemi sana'a dede dani in soma. In Allah ya dafa mini sai kaga na yi gida harda mota, yarana sun samu ilimi ingantaccen" Iyakar abinda Gwadabe ya furta kenan Yaya Hambali ya fusata har yana doka sitiyarin motarshi. "Ni kake faɗa ma magana haka gatse_gatse gwadabe? Ka mance sanda nake goyonka muje gona, nake cire kudina in biya maka kuɗin makaranta, in kama hannunka in kai ka makaranta. Kaci kasha naima sutura duk da dukiyata, kuma nake matsayin uwa da uba duka a wajenka? Ko Harisu bai isa faɗa mun maganar banza ba, balle kai wanda a haife na haifeka?" Sai zazzare idanu yake yi yana kumfar baki, Gwadabe dai baice mishi komai ba. Har ya gama hargaginshi. "Hmmm Yaya Hambali kenan. Shagone dai ni Gwadabe bana so bana buƙata. Bana nema a wajenka a wajen Allahn daya baka nake nema, kaima ba dabararka bace ta baka ba ka san da wannan." "To Shikenan na cire hannuna a kan ka tunda dai taimakonka da nake son yi ne baka so. Kaje kayi Abinda kake ganin ya dace da kai ba shikenan ba? Amman in sha Allah dakai da yin kuɗi har abada Gwadabe muddin ina raye baka ba yin arziki da Hambali kake magana, ɗan iska marar kunya fitsararre Allah dai ya kwashe maka albarka" Yana gama faɗan haka fuu ya ja motarshi ya buɗe Gwadabe da ƙura, ya cika mishi idanu fal da kasa. Idanunshi a runtse suke hawayen bakin cikin danginshi na tsiyaya a idanunshi. Shin wai me yasa ƴan uwanshi su ka fi sha'awar ganinshi a cikin halin damuwa da ƙunci ne, anya kuwa Babala itace mahaifiyarshi ta asali kuwa, ko dai shi ɗin ɗan riƙone bai sani ba? Amman da ace ɗan riƙone da dole ƙauye su sani domin a ƙauye kunne ya girmi kaka. A wajen Gwadabe ya ci alwashin bazai taɓa tambayar kowa komai ba, bazai karɓi ko ficika daga hannun kowa ba. Zai fita nema, kamar yadda Yaya Hambali ya fito nema shi shi kaɗai a shekarun baya, kuma Allah ya buɗa mishi. Shima Allah shine gatanshi ba Yaya Hambali ba, zai nuna musu shi namijine mai zuchiya ba mai hangen na wani ba. Idanunshi ya buɗe ya karkaɗe fuskarshi da idanunshi ya ci gaba da tafiya. Haka Gwadabe ya kwana a tsakiyar yaranshi, yanda rana ta kasance mishi haka darenma ya zame mishi. Sai juyi yake yi, yana tunanin irin rayuwar soyayya da kulawar da suka yi da Iyabo. Da irin abubuwan da akaita yi mata, kuma ta shanyesu duk dan ta zauna tare dashi. Amman daga karshen ƙarshe duk kiyayewarta sai da sakin ya afku a kanta. "Iyabo ina roƙa miki Allah ya baki mijin da zai jarabtu da sonki fiye dani, Wanda ya fini komai a rayuwa. Ya Allah ka kai baiwarka Iyabo gidan hutu da jin daɗi, mala'ikun Allah ku shaida ni dai a zamana da Iyabo babu cutarwa, kuma kune shaidar ni dai na ɗaga mata ƙafa dan ta shige aljanna. Allah ka haɗata da abokin rayuwar da zai ɗaga mata tashi ƙafar shima." Sambatu kawai Gwadabe yake ta faman yi kamar zararre. Haka Gwadabe yai ta tunane_ tunane har gari ya waye musu. Kamar jiya bashin wainar ya kuma karɓoma yara su ka ci ya kaisu makaranta Yana shiga gidan ya tadda dangin Iyabo suna tozarci a tsakar gidan. Sun zo dibar ragowar kayanta da yayi ragowa, da suturunta dai da kayan aiki haka. A wannan rana ya yasha zagi da ele a wajen su Iya Beji. Har tukunya Iyaa Kokodeen ta kwaɗa mishi a gadon bayanshi. Da yaga tozarcin ya isheshi sai ya koma ƙofar gida yai zamanshi. Yaya Hambali kuma sai sababi yake yi cewar duk Gwadabe ne sila, daya haɗe musu jini da jikokin oduduwa. Gwadabe na zaune a ƙofar gida ya hango Bara'u tafe. Ƙuri yayi yana kallon tahowar abokin nashi har ya iso gareshi ya zauna daf dashi. Amman fa kafin yace wani abu sai ga su Iyaa Beji sun fito suna zage_ zage Yaya Hambali na biye dasu shima sababin yake yi. Kan kace me unguwa ta ɗinke, mata har ta katanga leƙe suke yi, kunsan mata akwai gulma ko ince son ganin ƙwaƙwaf. basu dena baloƙoƙinsu na gado ba, sai da Yaya Hambali ya cukume Iyaa Beji, a tunaninshi zai daketa. Ai kuwa taron dangi suka haɗu suka yi mishi da ƙyar mazan unguwa suka karɓeshi a hannunsu duk haushin Gwadabe suka saukeshi akan Yaya Hambali. Bara'u da Gwadabe suna zaune suna kallon ikon Allah kawai. Yaya Hambali ya matso kusa dasu Gwadabe a zafafe yace. "Allah wadaran naka ya lalace. Kaji dai kunya Gwadabe ace waɗannan gayyar na aiya gayyar na yadadan sune surukanka. Mu kanmu ka cutar damu daka dage sai da muka haɗa iri da yarbawa. Duk irin matan dake cikin hausa Fulani ka rasa wacce zaka so sai Iyabo. Jibi yadda mata suka dakeni har suka fashe mun baki dan iskanci kuna zaune" Bushasshen yawu Gwadabe ya haɗiye muƙut. Bara'u ne yace. "Yaya Hambali ayi haƙuri. Komai ai ya riga ya daya ƙare. Allah dai ya ƙara rufa mana asiri" "Gafara can. Bara'u ai ko kisa Gwadabe yayi ba zaka iya ganin laifinshi ba. Aikin ɓur in ji tusa" Ya buga kafarshi ta dama a ƙasa, kana ya shige cikin gida. Bara'u ya sauke ajjiyar zuchiya yace. "Kayi haƙuri Gwadabe na roƙe ka da girman Allah. Ka ɗauka wannan ƙaddarace daga cikin sinnar rayuwa. Iyabo kai mata adda'a gaba Allah ya bata miji na haƙiƙa. Ni kuma da nazo da zummar in tafi da yaran duka can wajena Sakina ta haɗe da nata ta riƙe. To ina cikin mota sai Tamu yai kiran wayata Allah da ikonshi na kwashe zance tas na sanar mishi, to sai yace shi zai riƙe ƴan biyun a hannunshi zai sa su a makaranta. In kanaso zaka iya barinsu a hannunshi. In kuma kayi aure

Chapter 12 of 16