Tasi'u yayi yace.
"Ana maganar kayan gado dasu katifa yayi kuɗi. Ku ta ango ma kuke yi ko? To kuje dai wajen Antynku Badi'a zata baku atampopin ta siya muku, dan ni ban bata ko sisi ba. Kunga ni an hutasheni, sai in yima Mamana" Nan suka yi mishi godiya. Baba Fhatsima tace
"Ai Babannan ( haka Take kiranshi, kasancewarshi ɗan fari kuma mai sunan Mahaifinta) Babu abunda zamu ce da Badi'a sai dai muce Allah ya saka mata da Alkhairi. Tana yi mun abinda ko su Hadiza iyaka kenan. Yarinyace adala. Ina ma su Auwala fatan Allah yasa yaran da zasu auro mana su kasance masu hankali. Sai kaga zumunci ya sake ƙarfi sosai. Kuma naji daɗin yadda Malam ya yanke hukuncin ware su wadannan yaran a gida daban. Ƙila suma kansu su Sabitu su daure ayi zumuncin duka tare da matansu. Kuma kuyi ƙoƙarin haɗe kawunan yaranku waje guda, kar ku sake a raba muku kan yara. Ni bana jin daɗin irin yanda kowa yake jaye ɗanshi jikinshi kaɗai." Auwala yace.
"Tabb ni kuma Baba gani nake yi wannan haɗemu da za'yi waje guda ba zai haifar da ɗa mai ido ba. Sabitu da baya ko iya gaishe da mutane cikin daɗin rai. In fa zai gaishemu kamar zai haɗiyi zuchiya haka yake yi, dan ƙaniyarshi dan yasan kashi zan bashi in baiyi gaisuwar bane. Ni wallahi bana son wannn haɗemun da za'ayi" Yaya Tasi'u yace.
"Gaskiya ne za'a iya samun rikici sosai, musamman dag ɓangaren su matan da za'a auro bare. Mun tattauna da Malam sosai akan matalolin da ka iya faruwa. Mum kuma yi magana akan irin nasarorin da zasu iya faruwa. Dan a wannan karon Malam ya shirya ɓatawa da duk wanda ya nemi ƙetare umarnin abinda zai gindaya. I zuwa yanzu ya kamata ace an watsar da duk abinda ya shige, a fuskanci rayuwa. Malam bashi da wani buri daya wuce yaga kan iyakanshi a haɗe. To matsalar Baba Asshi itace zata fi kawo matsala acikin lamarin. Amman Baba shi fa malam so yake filin Ɗan Abhuja dake jikin filin da malam ya bayar a gina, ya siya a faɗaɗa harni da Usman, da Jamilu duk mu koma can, sai ya ware ku kuma daban, muma daban. Ni a matsayina na babba sai in kula dasu baki ɗaya" Cikin damuwa da tunanin rashin yiyuwar haɗin kai ga iyalan Malam Baba Fhatsima tace.
"Tab aikin da Malam ya ɗebo babbane sosai. Kuma abun zai yi matuƙar wahala asamu abinda akeso. Sai dai zamui ta adda'a kamar yadda muka kwashe shekaru sama da hamsin muna yi. Malam ya matsantama kanshi da damuwa, da tunanin abinda zai dawo mishi da farin ciki da haɗin kan iyalinshi. Akan ɗan wani dalilin da bai kai an kirashi dalili ba duk wannan abun yaketa faruwa, har waɗanda aka auro a baya_baya suma suka shigo da nasu fitinar. Amman in sha Allah komai zai zo ƙarshe a kwana a tashi" Sun jima sosai anata tattaunawa sai kusan sha ɗaya su kai sallama da Baba Fhatsima, su Auwala suka nufi shashensu, Yaya Tasi'u ma ya nufi nashi ɓarayin.
A daren wannan rana Gwadabe ya kasa runtsawa, duk da tarin gajiyar wahalar aikin daya kwaso. Kwakwalwarshi sai hasko mishi hotunan ƴan matan gidan kawai take yi. Da wannan tunani ya wayi safiya, suna kan shirin fita Hadiza ta kawo musu abincin karin kumallo. Kunu ne a jug, sai ɗunamen tuwon ɓula da lafiyayyar miyar kuɓewa ɗanya. Da idanu Gwadabe ya bita bayan ta gaishesu tana shirin ficewa.
"Hadiza" Auwala ya kirayi sunanta hakan yasa ta dawo cikin ɗakin. Komanta da sanyi take yi, kuma yanayinta na nuna halamar kunya tsantsa.
"Ga kayanmu kala bibbiyu ki wanke mana, Gwadabe bata kuɗin sabulu, ko kai ko Mammada" Gwadabe ne ya zaro sefa ya miƙa mata, tasa hannu ta amsa. Auwala kuma ya bata kayan nasu daya cusa a cikin wando ɗaya.
Kafin su dawo Hadiza ta wanke musu kayannan tas, harma ta yi musu kwalima ta haɗa da zannuwan katifunsu du ta wanke. Dama su kan yi ma yayyen nasu hakan lokaci zuwa lokaci. Wanki dama suke yi musu kasancewar su basu da lokacin kansu.
Yau samarin gidan a mugun gajiye suka shigo sharkab_sharkab da zufa, hakanne ma yasa basu shigarma Baba Fhatsima ɗaki a haka ba suka nufi shashensu. Anan suka tarar da sabitu yana kutuntumama Hadiza zagi tare da faɗin kalma marar daɗi a kanta.
"Ƴar iska dama naji labarin ƙazamin kishine irinna gado yasa aka sakoki ai. Dama yaushe zaku iya zaman aure, yara an sangartaku, an ɗaure muku ƙugu, an ɗauraku akan bigiren kishi" Karab a kunnen su Gwadabe. Sabitu na ganinsu yazo da sauri zai wuce, Auwala yayi zafin naman riko hannunshi ya fincikoshi ya dawo gabanshi.
"Ai ba ka zazzageta ka tafi a kyauta ba. Dan Allah sai munje gaban Malam yaji duk abinda ya haɗaku har ka zaɓi cin zarafin mahaifiyarmu da shi kanshi Malam ɗin. Kai dai Sabitu baka ƙaunar buɗe idanu ka ga muna rayuwa kyakkyawa. Wannan ciwon hassadar ne ya hanaka ci gaba sam, kuma gashi munfi ƙarfinka nesa ba kusa ba. Hadiza wuce muje gaban Malam. Da ƙarfin damtse Auwala ya figi Sabitu suka ratso tsakar gidan iyayen nasu, duk suna baje a tsakar gida suna shan iska. Baba Asshi taga Auwala riƙe cab da Sabitu, ba shiri ta cire hannunta a cikin abincin da take ci ta bi bayansu har da gudunta, daga ita sai fallen zani babu ko ɗan dires a jikinta. Baba Fhatsima ganin harda Hadiza aka fita yasa itama ta miƙe ta rufa musu baya."
Anan na kawo ƙarshen free page.
Wasa farin girki, labarin yana da tsawo ainun, dan ba mui komai ba. Sannan akwai tarin rikita_rikita da abubbuwa da dama na darasi, kar ki yi sake ayi wannan tafiyar babu ke.
Akwai tarin abubbuwa da zasu biyo baya.
Sannan akwai kyautuka da zan rabama masu yin dogon sharhi na musamman.
Ki biya kuɗinki kisha karatu.
Wasu suna roƙon in buɗe VIP
To 1000 ne VIP ɗin normal group 500 ne. Nagode sosai da soyayya
Nagode nice taku a kullum Mrs Bukhari. Mu haɗu a paid group dan jin yanda zata kasance.
+22785548912
Ƴan Nijar ga number da zaku turama da kati nan nera 500 a kuɗinmu na najeriya.
Nagode
3064127935
Buhari Ibrahim Ladan
First bank
Sanya nera 500 ɗinki kuɗin karatu anan. Wannan asusun gudauniyarmu kenan.
Ki sani in kika siya wannan littafin tamkar kin taimaki iyayen marayune, dama su kansu marayun
Kuzo mu yi tarayya cikin aikin lada. Ƙarƙashin Amila Foundation gidauniyar da muka buɗe ni da megidana domun iyayen marayu, ko tainakon marasa lafiya.
Waɗanda suke cikin group dina mai suna (NAMA YA DAHU ROMO ƊANYE)
300 kacal zasu iya kuɗin karatu
*Ƴar uwa ina fatan baki mance da kayan ƙamshin Mrs Bukhari gidan ƙamshi ba ko? Ƴar na gata ba take haye ba, Kanuri gidan ƙamshi. Matso kusa ƴar uwa ina da turarukan wuta nau'i daban_daban. Turaren kaya da zaki turare gidanki ƙamshi ya riƙe miki surura, sannan inada kabbasiyya turaren ruwane da ake fesama sutura a yayin da ake turara kaya a kabbasa, kana inada turaren wadrop da ake saƙawa a tsakankanin kaya.
Turarukan wutana kuwa in kika turara gidanki yana sati guda yana ƙamshi. Inada turaren turara jiki gangariya wanda yake kama fata.
Akwai kulaccam ta matan aure mai sirrin rikita maigida, ga gyaran fata. Akwai kuma kulaccam ta gashi, haɗe da turaren fesawa a gashi.
Mai gayya mai aiki humrata ta matan Aure mai sirrin ƙara dankon soyayya, kiga oga na shinshinarki kamar mage taji ƙamshin kifi ɗanye.
Inada humrori kala_kala.
Ina da room freshener, da mopping mix mai sirrin ƙamshi.
Kar in ta lissafo muku duk wani nau'in ƙamshin da kikeso in kika samu Mrs Bukhari ƴar mutan Maiduguri kin samu ƙamshi.
( Albishirinku akwai package na musamman dana tanadarma masoya wannan littafi nawa. Package ne mai ɗauke da abubuwa huɗu manya kuma a kan kuɗi ƙalilan karki bari garaɓasarnan ta wuceki zaki ciji yatsa kwasha_kwasha nayi da kayana domunku)*
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 16 Chapter of 16