Bama iya ɓoye ma juna dukkan wani sirri. Haka naita tunane_tunanen daddaɗan zaman da muke gudanarwa da Gwadabe na. Zamanne danginshi basa so, sabida na fito a ƙabilar da ba tasu ba." Nasha wuya da wannan tsohuwar Bus sosai. Kafin mu sauka jikina yayi likib. Muna sauka muka samu abun hawa ya kawo mu har ƙofar gidanmu. Ni dai ana isowa na sauka abuna, ɗan mabuɗin ƙofar na ciro a jakata na buɗe gidan. Dukkanmu ko wacce ita da mijinta suna da safaya ki da mijinta. Ɗakina na buɗe na shaga, ban zauna a falo ba na shige uwar ɗaki na rufo ƙofar garam. Zama nayi a bakin gado, kamar am tsikareni na miƙe. Cikin ƙarfin hali na buɗe akwatina na soma loda kaya, ina jin Gwadabe yana kiciniya da fantimotan Laila .
Da gudu Toye ya shigo yana dariya, rungumeni tsam yayi. Tunda muka tafi Takai sai yanzu da muka dawo gida yaron ya sake. Dariya nayi mishi nace dashi.
Keeni ( Menene)? Na tambayeshi da yare.
"Kiyasi (Ba komai) Ya faɗa cike da nishaɗi. Muna cikin haka Gwadabe ya shigo da sallama.
Hirar sama data ƙasa na haɗe.
Ku meye shawarar da zaku ba Iyabo. Shin ta zauna da Laila a ɗaki ɗaya. Ko kuma tayi tafiyarta su Babala burinsu ya cika, shin inta koma gidan kuna ganin zaman zai mata daɗi. Sannan inta zauna tare da Laila me zai faru?
Ina saurarenku
MRS BUKHARI
https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm
NAMA YA DAHU...
ROMO ƊANYE
BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Lamba ta huɗu (4)
*(SANARWA DUKKAN WAƊANDA SU SAYI WANNAN LITTAFIN TAMKAR SUN TAIMAKAMA MARAYUNE DA IZININ ALLAH. DOMIN KUƊIN KAI TSAYE ZAI TAFI ASUSUNMU NA GIDAUNIYATA MAI SUNA AMILA FOUNDATION NE. GIDAUNIYAR TAFI ƘARFI WAJEN TALLAFAMA MARAYU, DA TAIMAKON MARASA LAFIYA, SAI KUMA TALLAFAMA ZAWARAWA DA JARI MUSAMMAN WAƊANDA MIJI YA MUTU YA BARI DA ƳAƳA. SIYAN WANNAN LITTAFIN TAMKAR TALLAFAMA MARAYU DA IYAYEN MARAYUNNE. KUZO MUYI TARAYYA AKAN AIKIN ALKHAIRI)*
*( KAR KU MANCE INA SAIDA TURARUKAN WUTA DA HUMRORI, DA DUK DANGIN ƘAMSHI MASU INGANCI NA MATAN KANURI. KANURI MUNE ƘAMSHI MEDUGURI GIDAN ƘAMSHI)*
Ƙur yai mun da idanunshi wanda suka kaɗa su kai jawur.
"Toye Wa Nibi ( zo nan)" Da gudu Toye ya je wajenshi. Murmushi yayi mishi yace.
"L'o pade Anty re ( Je ka samu Antynka) Ya turashi zuwa falo. Yana fita Gwadabe ya mai da ƙofar ya rufe. A gabana ya tsugunna.
"Ifemi (masoyiyata) me kike shirin yi, ɗakin ki kike son bari, Gwadaben naki kike son gujema? Duk irin juriya da gwagwarmayar da muka sha a baya bai sa mun rabu ba, sai dan akan Laila banzar bazara?. Ifemi ( Masoyiyata) kema kinsan dole zanyi wani abun ko dan samo mana mafita. Na fiki jin zafin tawo da Laila da mu ka yi. Iyabo kar ki yarda shaiɗan ya rinjayi zuchiyarki. Ki tuna Gwadabe ne naki wanda kikai mishi Alƙawarin mutuwace kaɗai zata iya gibtawa a tsakaninki dashi, ki rufa mun asiri ki zauna a ɗakinki"
Shiru yayi yana jiran abunda zance.
Gwadabe a gaskiya bazan iya zama da Laila a ɗaki ɗaya ba. Bayan tana ɗakin mijinta ma bata dena turo maka da saƙonnin ƙauna ba. To ka sani in ba baka san na san sabida kai Laila ta kaso aurenta ba, to na sani. Dan haka bazan zauna da kishiyata ɗaki ɗaya ta gama gane mun sirrina ba, in aurenta zaka yi basai an turota yimun c.i.d ba."
Yanda nake maganar ina haki yafi komai ɗaga ma Gwadabe hankali ƙuri yayi mun da idanu yasan tabbas naje maƙura dan tsakaninmu yi nayi ne, bari na bari. Kafin ya tuno lafazin da zai rarrasheni dashi akayo kiran wayarshi, ya zaro a aljihu. Oga Lurwanu naga an rubuta, shine ogan Gwadabe wanda yake ma karen mota. Da sauri ya ɗaga, murya a sanyaye yace.
"Oga Lurwanu yanzu na shigo Kanon, zan tawo yanzu in sha Allah, an gama lodinne?"
Daga cikin wayar Oga Lurwanu yace.
"Ka hanzarta Gwadabe, an yi rabin lodi, ana gamawa zaku kama hanyar Ikko da izinin Allah. Karen motarka yana nan tare dani tuntuni."
"To Oga Lurwanu abinda zan barma iyali fa? Wallahi ɗari ukune a jikina da zanyi kuɗin motar zuwa inda kuke. Kuma a gidan babu komai. Kasan lamarin sai godiya"
Oga Lurwanu yace.
"Wannan babu wata matsala. Kai dai ka tawo ɗin. Ko yaro ka ba saƙo ya ajjiyema Iyalan. Kai muke buƙata yanzu"
A haka su kai sallama da juna. Yana sauke wayar a kunnenshi ya dubeni. Hawaye nake ta faman sharewa.
"Iyabo gashi bani da lokaci a halin yanzu. Kina jina da Oga Lurwanu. Abinda zance miki shine ki tausayama masoyinki ki yi zamanki a ɗakin ki, ki toshe kunnuwanki, ki ɗauke idanuwanki daga gani ko jin komai. Dana dawo zan nema mana mafita, amman in sha Allah Laila ba zata zauna tare damu ba. Ki kuma kwantar da hankalinki Laila ba zata taɓa samun gurbi a zuchiyata ba. Ba zata iya ruɗata da komai ba, a gabana ta yi wasan ƙasanta. Ni naki ne ke kaɗai Iyabo. Nasan kishi ke nuƙurƙusar zuchiyarki. Kinga hanya zan hau, taya hankalina zai kwanta in na barki kika koma gida. Sannan ke kan ki in kin koma gidan wani sabon damuwarce kika jefa mu a ciki. In ci albarkacin soyayya haba tauntsun soyayya"
Duk wannan kalaman cikin sigar so gami da rarrashi yake yinsu. Gabaki ɗaya sai jikina ya mace mus. Ance tsakanin mata da miji sai Allah. Duk da ina jin bazan iya zama da Laila ba. Amman ya kamata in ma mijina uziri tunda shima umarni aka bashi, kuma bazan so akan faranta mun ya saɓama wacce tai sababin zuwanshi duniyar ba. Ajjiyar zuchiya na sauke kana nace.
Kana da girman daraja a guna. Kaje Allah ya tsare maka hanya. Ya kareka da sharrin ƙarfe da sharrin hanya. Allah yasa sai dai ka ajjiye motar da hannunka ba dai ta ajjiyeka ba. Allah yasa a soma a sa'a, Allah yasa ƙarshen wahalarmu ne yazo. Ka kular mun da kan ka Gwadabe, dan akwai tarin tulin maganganu marasa daɗin ji a kan ku direbobin manyan motoci, sunan masu sana'ar tuƙin manyan motoci yayi ƙauri, sun san sirrin ajjiye daduro ni bana zarginka amman ina tunatar dakai jin tsoron rabbissama wati wal ardi. Kar ka zama daga cikin irinsu dan Allah, duk da a ko wacce sana'a akwai nagari, akwai na banza." Murmushi yayi ya rungumeni dani da ƙaton cikina yace.
"Kamar yadda kika faranta mun raina, Allah ya faranta miki kema. Mala'ikun Allah ku shaida na ɗaga ƙafafuna domin Iyabo matata ta shiga Aljanna" Dariya mu ka saka dukanmu.
Ka hanzarta jiranka akeyi dai kar ka shagaltu"
"Wallahi kuwa. To ni zan tafi, zan aiko da ɗan kayan abinci da kuɗin da zaki riƙe a hannunki. Ki kula da kanki da abinda yake cikin ki. Da zaran kin soma jin naƙuda ki sanar ma Bose, nima ki yi gaggawar sanarmun, Bara'u sai ya zo ya tsaya. Ballema ina roƙon Allah yasa sai ina nan zaki haihu. Sannan ki kula sosai, Laila ɓarauniyace ta bugawa a jarida, ko ɓera bai kaita iya sata ba, kuma bai fita dabarun iya sace abuba, har hannu take sawa a wandon jeans na maza a kasuwa ta yashesu, gidan biki ko suna kuwa sata take yi tamkar tana bacci dan sauki. In zaki je gidan aiki ki kulle uwar ɗakin ki kar ki sake ki bar mana ƙofa a buɗe. Dan komai ɗauka take yi" Sumbatata yayi a baki, tare da riƙo hannayena muka miƙe tsaye a tare.
To in sha Allah zan kiyaye, Allah ya tsare. Mu je in rakaka" Tare muka fito zuwa falo. Laila na tsaye a gaban hoton aurenmu dake manne a falon. Na ci lace da gwaggwaro. Gwadabe ya sha rigar asheke da hular ashoke kai ka rantse beyerabe ne shima. Jin motsinmu ne yasa ta zauna a kujera mafi kusa da'ita.
"Fita zaka yi ne Yaya Gwadabe?" Ta furta da zazzaƙar murya ba irin tawa ba, dan muryata tana da ɗan girma gami da kauri.
"E tafiya zanyi ma. Ni sai na dawo. Iyabo ki koma ki kwanta ki huta zuwa azahar kya tashi ki yi wanka ki yi salla." Kafin in ce wani abun muka jiyo sallamar Uwani Tabalbalin ƙawata tun ta ƙuruciya, ƙawarda banda madadinta.
"A maraba lale Tabalbalin kece a tafe? Ai kuwa kinci sa'a dawowar ƙawar taki kenan daga ƙauye" Cewar Gwadabe daya tari Uwani da fara'a sosai. Cikin dariya tace.
"Gwadabe na Iyabo ikon Allah tsuntsun soyayyar daya tashi daga kan Debisi sai ya hau kan Ɗan hausawa. Fita zaka yi ne?"
Dariya muka saka dukkanmu, wannan suna yaƙi fita a bakunan waɗanda suka san gwagwarmayar da muka sha kafin aurenmu.
"Wallahi tafiya zan yi ma zuwa Ikko. Ya yaran, ina Hafizu Oga ba?" Dariya mu ka yi duka.
"Hafizu na baroshi a majalisarsu"
A wajen mu kai sallama da Gwadabe ya fita, mu kuma muka koma uwar ɗaki ni da Tabalbalin.
"Ashe tafiya kuka yi Iyabo. Kaddai bikin ƙanwar mijinnan naki marar kunyar nan, wacce ta watsa mun miya a zani lokacin sunan Toye kuka je?" Zama na yi a bakin gado. Na yi shiru kawai dan batun zaman Laila na ci mun tuwo a ƙwarya. Zama Uwani Tabalbalin ta yi a kusa dani tace.
"Akwai wata matsalar ne Iyabo? Nasan ai ba zata wuce irin wulaƙancin da dangin Gwadabe suke yi miki ba ko. Balle kunje ƙauye an shiga taron biki"
Wallahi da shine ma da sauƙi Uwani. Ai kinsan Laila tsohuwar budurwar Gwadabe, ƴar uwarshinnan wacce kwanakin baya muka samu saɓani?" Kai ta gyaɗa tace.
"Na ji na ji. Wacce take turo da saƙon batsa tana gidan wani ko, ai kece banza da baki zaune ƴar banza ba. Halan wani abun tayi miki a cikin taro?"
Itafa ƙawata. Ana baki kina karɓa Tabalbalin"
Bata labarin abinda ya faru nayi kab ina share hawaye.
Uwani da ba dan in na koma gidanmu tamkar na tozarta aurena bane, da wallahi kafin Gwadabe ya dawo na bar gidannan."
"A'a kar ma ki soma. Dan in ma kika je Iya Debisi sai ta kusan illataki banda kwakwazon da za tai ta yi miki, maƙotanku ma sai sun ji meke faruwa. Amman gaskiya kar ki kuskure ki yarda kici gaba da zama da'ita ɗaki ɗaya maganar gaskiya. Ba zata zo har ɗaki ta iskanta miki miji ba. Amman ko da wasa kar ki sake ki bar ɗakin ki, yo kin bata dama ta kwace miki miji cikin sauƙi kenan ma. Nifa dani Gwadabe yake Aure da tuni na seta kan ƴan uwanshi. Ki kwantar da hankalinki tunda Gwadabe yace zai samo muku mafita kema kinsan bazai barki haka ba. Ya kika baro Sakina da mijintannan nata mai barkwanci Bara'u?"
Ajjiyar zuchiya na sauke nace.
Suna lafiya lau Uwani, ya Hafizu da yaran?" Shiru tayi na ɗan lokaci tace.
"Iyabo yau haka muka wayi gari ko lomar da zamu kai bakinmu babu wallahi. Yaran sai turasu gidan Hajiyata nayi nasan ko ba komai ba zasu rasa abinci ba, tunda Hajiya na yin ɗanwaken saidawa. To mu ɗin bamu ci komai ba, ga ni da ciki na wata uku ban baki labari ba, wallahi bansan ina da cikin ba. Ga hayarmu ya ƙare gobe mai gidan zata zo karɓar kuɗinta, ko ficika bamu ajjiyeba, babu wanda muka ba ajjiya. To shine na sha maganin zubar da ciki cikin ya zube yau ɗinnan, Iyabo bazan iyaba, Hafizu bashi da zuchiyar nema. Ni rayuwarma ta isheni Iyabo, Talauci masifane ƴan uwanka ma sai su gujeka su ƙi taimakonka" Kuka ta fashe dashi kawai. Ban hanata rera kukan ba, domin kusan ni na fita sanin zafi da raɗaɗin talauci da wayar gari babu abinda za'a saka a ciki. Tunda Hafizu da yana da rufin asirinshi direban ƙaramar motane yana lodin Kano to Gomber, da Bauchi. Motarshi ce tayi haɗari ta yi rugu_rugu. Har yanzu bai samu wata motar ba. Shi kuma ya ɗaurama kanshi girman kan neman wata sana'ar. Daga haka ya ɓige da zaman kashe wando. Shi yasa rayuwar ta ɗaure musu. Amman ni dama a haka na shigo gidan Gwadabe na sameshi. Dama bashi da cikakkiyar sana'a duk abinda ya fita ya samu yi yake yi kawai. Numfashi na ja kana nace.
Kiyi haƙuri Uwani da sauyin rayuwa. Mu yi ta yi musu addu'a babu dare ba rana. Ubangiji rabbissama wata wal ardi zai bamu mafita, zamu ji daɗi a gaba komai lokaci ne. Tashi mu je mu hura wuta, ga ɗan abinci mun samo daga ƙauye, ko fara ce in dafa mana, ina da yaji, mai ne babu dai." Tire na ɗakko na zuba shinkafa ƴar hausa Gongoni biyar, Uwani ta karɓa ta fita. Kurfot ɗina na zaro a ƙarƙashin gado da ƙullin gawayin hamsin a kai, nima na fito tsakar gidan. Wuta na hura da leda, Uwani na zaune a kujera tana tsintar shinkafa tace.
"Ji gidan shiru kamar ba shi bane mai tarin hayaniya da bataliya ba" Yatsana nasa a leɓena nai mata nuni da tai shiru sabida Laila. Dole mu ka zama kuramen dole. Tashi nayi na ɗakko tukunya na buɗe randata dake bakin ƙofa cike da ruwa na zuba ruwan a tukunya, na ɗaura a wuta. Ruwan na tafasa Uwani ta wanke shinkafar ta zuba. Alwala muka ɗaura dukkanmu muka shiga ɗakin. Da sauri Laila ta ajjiye kwanon samira dake ajjiye a gefe guda. Kallonta nayi itama ta kalleni. Kai na girgiza na nufi hanyar shiga ciki.
"Am Iyabo a ina zan ajjiye fantimotaina naga kamar basu dace su zauna a falo ba" Kallonta nayi na ƙara.
To a ina kike ganin ya dace ki ajjiyesu in ba falon ba?" Na bata amsa cikin danne fishi, dan ji nake wallahi kamar in dira a wuyanta.
"A uwar ɗaki mana, taya zan ajjiye kayana a falo?" Ta faɗa a gadarance irin ta dangi miji dan halinsu ne wannan kam. Cikin cusa haushi nayi dariya nace.
Haba Laila, ai uwar ɗakina mallakinane tafi ƙarfinki, iyakar taki a falo take. Uwani mu shiga ko?" Na yi shigewata ciki na bar Laila tana surutai ni bansan ma me take cewa ba. Abinci na zuba mana a tire. Na zuba na Laila a kwanon silver, na zuba ma Toye nashi. Wani ƙaramin kwano na jawo a ƙasan gado, ragowar manjan miya ne a ciki nama mance dashi na tsiyayama Laila da Toye ragowar na ajjiye a gaban uwani danta soma cin abincinta ma gaya abunta. Falo na fita da zummar in ba Laila abincinta na tarar bata cikin falon. Ajjiye mata nayi a inda na barta. Na jawo hannun Toye yanata wasanshi muka shiga ciki na zaunar dashi. Kabbarar Sallah nayi. Ina cikin sallah muka jiyo sallamar namiji. Uwani ce ta fita dan dubawa. Sai da na idar sai gata da leda mai zane, da kuma baƙar leda da kuɗi dubu biyu.
"Saƙone Gwadabe ya aiko miki. Gwadabe akwaishi da ƙoƙari akan komai ma, gaskiya ki sake gode ma Allah. Gwadabe ya riƙe miki amanar ƙaunarki. Iyabo kar ki kuskura wannan mai idanu a tsakar kan ta rabaki da mijinki."
Tabalbalin sai na dage da tsaiwar dare. Domin tsorona bansan da wanne irin shiri tazo ba. Nasan kyanta, ko farinta, da kyan durinta bazai taɓar ruɗar Gwadabe ba. Na yarda da irin son da yake yi mun. Kuma na yarda yana ganin kyauna a hakan da nake, ko babu komai yakan yabeni ya kurantani. Kuma yasan da'itan ya tsallaketa ya auroni. Ni dai da sallar dare zan dage kar su je su nemar mun miji ta hanyar asiri. Uwani ina cikin damuwa sosai wallahi. Ke dai mu ci abinci kinji.
Muna hirarmu muna cin abinci, anan na ba uwani labarin abinda ya faru a cikin gidannan ranar da zamu je Takai, da kuɗin hayar da zamu soma biya. Uwani tayi mamaki ainun ta jinjina irin ƙiyayyar da dangin Gwadabe suke yi mun. Sai bayan la'asar Uwani ta shiga haramar tafiya. Shinkafa da taliya, da kayan miya, da ɗanyen kifi, manja, maggin da Gwadabe ya aiko yaro ya kawo duk sai dana ɗibar mata, na bata ɗari biyar. Bata tafi ba sai da ta ɗoramun miyar tumatur a gawayi, da kanta ta leƙa ta kai mun niƙan maƙota. Sai da na rufe uwar ɗakina sannan na rakota. Mun fito mun samu Laila tana cin gurasa da lemun koka kola, abincin dana ajjiye mata kuma ta tureshi gefe guda, ƴar ƙaramar rediyo ta kunna tana jin waƙat barmani choje, waƙar gwarne ikon Allah. Tana yi tana karkaɗa kafaɗarta. Wucewa muka yi jiki duk a sanyaye. A sanyaye mu kai sallama da Uwani tana sake jan kunnena kar in kuskura in bar gidana sabida wata. Ko dana dawo ban shiga falon ba, a tsakar gida na zauna ina tsintar shinkafa ina shaƙar iskar ƴanci. Dan da masu gidan na nan, da ananan ana zubar mun da habaici, gami da maganganun cin fuska marasa daɗin saurare. A taƙaice dai ko dana gama girkin dare na sake zuba ma Laila a wajen ta sake bar mun. Ta fita ta siyo tea da biredi. Ni ko tunda na janye yarona na shige ciki nasa sakata, ban sake sanin halin da Laila take ciki ba.
Misalin ƙarfe goman dare sai ga kiran Gwadabe ya shigo wayata. Cike da zumuɗi da kewa na ɗauka. Daman a zaune nake dan tunda cikina ya tsufa ban fiye samun baccin dare ba. Allah sarki Gwadabe da yana nan da yanzu yana matsa mun ƙafafuna.
Amincin Allah ya tabbata a gareka gwarzon gwaraza. Barka da hanya, da fatan kana cikin aminci?"
Murmushi yayi mun yace.
"Barka sa dare sarauniyar zuchiyar Gwadabe, da fatan kina cikin ɗakinki na sunna cikin aminci ko?" Farin ciki ne ya lulluɓeni bansan sanda na lumshe idanuna ba.
Ina lafiya, sai kewarka dake nuƙurƙusar zuchiyata. Ya hanya fa?"
"Ba daɗi hanya. Kin ganmu a Tafa mun tsaya cin abinci da Sallah. Shine nace bari in ji lafiyarki. Ina Toye?"
Gashi nan yayi bacci.
"To masha Allah babu dai wata matsala da Laila ta baki ko?" Baki na taɓe kafin nace.
Babu wata matsala a halin yanzu. Amman abincin rana dana dare dana bata duk bata ci ba. Fita tayi ta sai abunda ranta yake so" Faɗa ya soma yi akan karma in ƙara saka mata abincin in nayi tunda abun iskanci ne. Ni dai nace.
Ba za'ayi haka ba. Ai da duk take_takenta so take in ƙi zuba mata a kafa mun hujjar na hanata abinci ita da gidan ɗan uwanta. Kai dai ka yi tunanin nemo mana mafita kawai. Dan wallahi Allah bazan zauna da gansamemiyar bazawara kamar Laila ba." Dariya Gwadabe ya dinga yi mun yana tsokanata kan na fiye kishi. Nima da dariyar na bishi kawai. A haka mu kai sallama dashi. Bacci bai zo ma idanuna ba, ƙarfe sha ɗayan dare na ɗaura alwala a cikin bahun babba. Na raba dare ina neman tsarin Allah ga dukkan masu son cutar dani da mijina, da masu son ganin bayan auren. Na roƙi Allah yai mun katangar ƙarfe da Laila ya karemu da dukkan sharrin data kwaso. Gwadabe kuwa alkhairi duniya dana lahira na roƙar mishi. Sai zaman lafiya, da jin daɗi wanda bana gajiyawa wajen sake roƙa mana, kusan duk addu'o'in maimaicine ba dare ba rana. Sai dai yau na ƙarama adda'ar tsawo da wasu salon roƙon. Sai wajajen jefin assalatu bacci ya kwasheni ina daga zaune. Amman ana kiran sallar farko na buɗe idanuna. Yinƙurawa nayi na tashi na buɗe ƙofata na fito da bahun ɗina na fice. Laila na saman doguwar kujera tana bacci saye da wandon bacci iyakarshi guiwa, rigar wandan mai shara_ shara ne har kan mamanta ina iya ganowa. Gabana ya doka da ƙarfi, kifiyar kishi ta soki tsokar jikina. Kai kawai na girgiza domin nasan tabbas dama a rina. Laila da kyan sufa da launin fata take son Jaye Gwadabe daga gareni. Dan tana da kyau tubarkalla masha Allah. Kuma ko a ƙauyen ita idanta a buɗe yake tar. Fita nayi na kama ruwa, na ɗaura alwala na koma ɗakin. Dai _dai da farkawar Laila tana tsaye tana miƙa. Na ƙarema wandon baccinta kallo shima shara_sharenne ina hango zaratan cinyoyinta farare luwai_luwai dasu.
Ya kamata ki sani cewar nan ɗakin matar wanki ce, ba ɗakin aurenki ba. Wannan shigar a ɗakin mijinki kaɗai ya dace ki yita ba anan ba. Zan iya lamuntar komai, banda shigar banza mai nuna tsaraici, ki kiyaye sosai"
Hararata Laila tayi tare da yin shewa tace.
"Ashe ana tsoron iya inji ƴaƴan maiya. Babu rami me ya kawo rami Iyabo? Ashema baki yarda da nagartarki ba a matsayinki na mace ba."
Murmushi nayi mata kawai domin bani da lokacin misayar yawu da'ita.
Bayan na idar da sallah na yi azkar da adda'a, na jima sosai ina tunanin yanda ƙarshen zaman Laila a cikin ɗakina zai kasance. Ta yaya, kuma ya za'ayi tabar ɗakinnan alhalin Babalace ta bata umarnin zama, kuma dani da Gwadabe duk a ƙarƙashin ikonta muke. Wata zuchiyar tace.
"Ai matsawar ba barin gidan kikayi ba Iyabo. To tabbas Laila babu inda zata fita taje. Babu makawa Gwadabe sai ya aureta. A daddafe na miƙe na shiga gyaran ɗaki, sai da na kintsa komai, na fitar mana da wankin kayayyakinmu na soma wankewa inayi ina rera waƙar yarbawa, amman wani shashe na zuchiyata a cike yake da tsoro da fargabar zamana tare da Laila. Kafin takwas na safe na gama komai har shara da wanka duk mun yi. Abinci na ɗunɗuma mana, kamar jiya na sake zuba ma Laila nata dai na dire mata. Ina gama karyawa na fito cikin shiri, na yi kaye_kayen kayana masu amfani na kulle uwar ɗakina. Laila na falo tana cin abincin dana ajjiye mata na yi ficewata ina jaye da hannun Toye, har zuwa bayan layinmu gidan da nake yin aikin shara, wanke_wanke, da goge _goge, sai wanki amman injinne yake wankewa, ya ɗauraye, ya busar gogewa ne dai nawa, sai in jera a sib, sai kuma girki amman shi ba ko da taushe bane. Babu wanda yasan ina yin wannan aiki, domin yana daga cikin sirrinmu ni da Gwadabe. Matan gida dai suna gutsiri tsomarsu akan fitar da nake yi tun safe, bani zan dawo ba sai azahar, har Gwadabe Yaya Hambali ya tara da zancan dan a tunaninsu gantali nake zuwa kawai. Yaya Haula kuwa cewa tayi bin gidajen maƙota nake yi yawon tsogumi, dan babu wanda ya kai yarbawa gulma da munafurci a cewarta. Da sallama na shiga madaidaicin gidan. Matar gidan tana ciki, dan na hango ƙofar falon a wangale. Bayan sallama kai tsaye na shiga falon. Tana zaune tana duba wasu kayayyaki da take ta warewa na maza da mata.
"Yauwa Iyabo ashe kin dawo. Kar ki so kiga yanda wanki ya taru mana, kinsan yara da ɓata kaya" Dariya nayi cikin girmamawa da ɗan risinama wanda kake mutuntawa wanda ya zama ɗabi'a mai kyau ga ƙabilar yarbawa nace.
Ina kwana Alaja ya yaran?"
"Lafiya lau, an yi biki lafiya dai ko? Yau da Toye akazo bai je makaranta bane?"
Wallahi kuwa bai je ba sai dai zuwa ƙarshen wata. Wannan kayan har da su a wankin Alaja?" Na tambaya ina kiciniyar kwashesu tace.
"A'a kayane muka fitar na kwalima, za'a tura ƙauye a buhu zaki zura mun su. In akwai wanda kike so sai ki ɗiba" Baki na washe nace.
Ahhh
irin na yarbawa"
Alaja nima inaso, bari in tsakura tunda mabuƙatan muna da yawa. Amman duk sanda akayi a dinga cira mun. Alaja tace.
"To ki kwashe duka wannan na matan ki bar na mazan, ai ban gama kwaso kayan ba ma" Ba shiri na tsugunna ina ta faɗin.
Ahh_Ahhh_Ahh
Alaja na mazan ma inaso in da hali, zan bama mai gidana shima yana da ƙarancin suturu' Shiru tayi tana kallona, mamaki na bata ko tausayina taji sai Allah, sai da ta sauke ajjiyar zuchiya tace.
"To ki haɗa duka ki kwashe, zan fito da wanda na ware a ɗakina sai ki zuba mun a buhu. Akwai takalman maza ƙafa biyu a dokin ƙofa ki haɗa dasu in zai ma me gidan naki, ni zam shiga ciki."
Ahhh Olorun bukun fun o ebi re ( Allah ya albarkaceki, ya albarkaci iyalinki) Na faɗa da yaren yoruba. Na fassara mata da hausa dana tuna bata jin yaren. Da "Ameen_Ameen" ta amsa ta yi shigewarta ciki. Bayan na tattare kayan na shiga aikin share_share ka'in da na'in. Ina yi ina wanki a injin. Bayan na ƙalƙale ko ina kuma sai
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 16