ba, amman babu yanda ta'iya dole haka mu kai sallama.
"Iyabo ni ko duk randa na dawo daga Canada, zan zo Iyaa ta bani adireshinki ko a bangon duniya kike zan ziyarceki. Sannan dan Allah ki kwantar da hankalinki ki rungumi ƙaddararki da zaran kin samu mane mi kiyi aurenki kema ko Allah zai sa ki samu nitsuwa."
Nagode sosai Allah ya ƙaddara saduwarmu. Kya dinga leƙa yaran in kin samu lokaci."
Na sake magana a raunace.
Basu suka tafi ba sai wajen taran dare su kai mana sallama bayan sunci Amala. Inayin sallar isha na naɗe a gado bana son ma Iyaa ta cakaleni da faɗa ko hargaginta, fruit ɗin da Burodami ya kaqo mun shi naci. Wajajen goman dare Alfa Kulle ya kawo mun adireshin rugar da mahaifiyata take da inkiyar shi mijin nata da take aure Mahaifin su Baɗɗo.
"Tashi ki zauna Iyabo mu tattauna kinga gobe asubar fari ya kamata ki kama hanya dan tafiyarki mai nisan gaske ce. Kece baki sani ba, sanda muka je ƙauyannan kina yarinya ƙarama"
Miƙewa nayi daga kwance na zauna kamar yadda ta uwarceni.
"To tunda kin nace sai kin koma hannun mahaifiyarki ai shikenan, bazan hana ki ba. Amman fa...."
Sai tayi shiru akwai abunda take son sanar dani, amman kuma kamar bata son faɗe ko nauyi yake yi mata ne ni dai ban sani ba. Sai kawai ta ɓige da yi mun nasiha tare da cewa.
"Mijin Uwarki ance jarababbene sosai, dan haka sai ki kula kar ki je ki haɗata rigima dashi a wannan gidan yawa, ga kishiyoyi"
Ni dai da Toh" kawai nake amsata harta gama na koma na kwanta. Tsawon wannan dare tunanuka ne barkatai sukaita kai komo a ƙwaƙwalwata da tunanin irin rayuwar da zan fuskanta a rugar da mahaifiyata take, da irin karɓar da shi kanshi mijin nata zeyi mini. Gefe ɗaya kuma tunanin Gwadabe da yaran duk ya addabeni, wayata a can gidan na baro mishi abarshi dan bana son damuwa. Washe gari sassafe na kintsa tsab, Iyaa ta ɗan harhaɗa mun tsarabar Kano, da ƴan canjina. Iyaa Kokodeen kuma ta kawo kuɗin mota nera dubu biyar ta ce in ji Burodami kokodeen yace a bani na mota. Matan gida mai ishirin mai hamsin sai aka gagganɗa mun, nayi musu sallama. Ina fita sai ga Burodami Debisi a mashin bespa, hawa nayi ya kaini tashar mota inda na samu motar Adamawa, na ci sa'a ma motar zata shiga har ƙaramar hukumar GIRAI, daga girai in na sauka sai in kuma hawa motar wata rugar kuma, kafin na sake hawa motar asalin rugar da Dada take Tafiya ce bata wasa ba a gabanmu. Dubu biyar Debisi ya bani tare da miƙo mun wata jakar leda.
Nagode sosai Allah ya bar zumunci. Allah ya ƙaddara saduwarmu" Idanu ya lumshe yace.
"Ki gaishe mun da Dada sosai. Sai na zo in sha Allah " Sallama mu ka yi ya figi besparshi ya fice. Hanyar da yabi na bi da kallo ni kaina bansan tunanin da nake yi ba. Mu biyu ne rak a motar ni da wata bafulatana mai yara biyu, kuma a seat ɗin tsakiyar Bus muke, Bus ɗin babbace sosai mai layi huɗu ce zata ci mutum goma sha huɗu harda direba. Ga motar ragwargwajajjiya ce soai. Mu dai muna zaune jigum. Ita bafulatana ta kusa dani sai wasa take da yaranta suna yara yaren fullanci. Sai lokacin hawaye ya ɓalle mun dana tuno da nawa yaran. Shikenan su da hawa jikina kuma ya ƙare, haka suma zasu taso ba a hannuna ba, kamarr yadda nima na taso ba'a hannun mahaifiyata ba. Suma haka zan haifo musu ƴan uba ko? Kamar yadda Dada ta haifo su Baɗɗo. Kukane sosai ya ciyoni, dole na saka fuskata tsakankanin cinyoyina na yi mai isata ba tare da Bafulatanar kusa dani ta san halin da nake ciki ba. Shigowar wasu fasinjojinne yasa na share hawayena na ɗago. Suma fulaninne amman maza, harda sarƙar fulani mai duwatsu kala kala a wuya da hannunsu, ga gashi sun tara sosai a kawunansu, ga sandunansu da takalmin roba, sai ƙosai da biredi suke ci suna korawa da lemun limca na kwalba. Murmushi ne ya suɓuce mini kawai. Da ɗaya da ɗaya aketa taruwa a cikin motar, kujerar da nake zaune naci sa'a duk mata ne mu huɗu a kujerar, dukkansu da gani fulanin usil ne, gasu da yara a hannu ga goyo raɓe_raɓe, tun kafin motar mu ta tashi suke ta aikin ciye_ciye. Kasancewar sammako duk muka bugo a tashar duk suke takaryawa masu abincin tasha sai ciniki suke zabgawa. Ni ko ko ruwa bana sha'awar sha balle inci abinci, yinwarma da kanta ta hutasshe da tumbina. Sai da rana ta fito ƙal kafin motarmu ta cika tab, nan aka shiga binmu muna biyan kuɗin mota. Dubu ɗaɗɗaya da ɗari biyar kuɗin motar haka muka bayar, waɗanda suke zaune a injin ɗari biyar. Motarmu ta fita daga cikin tasha ta hau lafiyayyen titi. In banda hayaƙi da jijjiga babu abunda motarnan take yi. Ji kake tututu_tuturtu, gashi bata da gudu sam. Kaina na bakin taga ina kallon mutanen dake tafe a ƙasa ɗaiɗaiku. Wasu kasuwannin ƙauye da gani zasu je ciyo kasuwa, yayinda wasu kuma suka fito neman kuɗi, wasu tallace a kansu maza da mata, yara da manya. Tun ina ganin mutane har na soma ganin bishiyoyi. Jama'ar motarmu kuwa sai hirar nishaɗi da jin daɗi suke yi, yayin da wasu suke gyangyaɗi, a yayin wasu suke ciye_ciyensu, wasu kuma suna kame kamar ni haka. Tafiyace miƙaƙƙiya mu kai ta ta faman yinta. Da azahar tayi muka tsaya a wani gidan mai mu kai sallah a masallacin gidan man. Aka firfito kowa na sayen abunda zaici, dan direba yace ba zai sake tsaiwa ba sai mun isa inda zamu sauka. Masu fitsari nayi, masu ba haya nayi. Gurasa da ƙuli na siya na ashirin, na sha ruwa a randar masallaci, nayi komawata cikin mota. Kai mun ɓata lokaci sosai a wannan gidan mai kafin mu ka kama hanya. Mune har bayan la'asar bamu isa ba, sai yamma sakaliya sai gamu a ƙaramar hukumar girei Allah ya iso damu. Ƙauyan abun sha'awa, fulani makiyaya sunata wucewa da garkunan shanayensu zasu koma gida, shanayen manya lafiyayyu gwanin sha'awa, masu tallar nono mata suma sai wucewa suke da ƙoransu a ɗoɗɗore a kawunansu. Sakkowa mu ka yi kowa ƙafafuwa a kumbure. Matar da muka zauna waje guda na tambaya.
Baiwar Allah a ina zan samu motar Jere Banyo?" Cikin kwaɓaɓɓiyar hausa tace.
"Nima can zani, mu je daga can gaba zamu samu mota sai mu tafi" Ajjiyar zuchiya na sauke, na bi bayanta tiryan_tiryan har zuwa wajen akori kurar dana ga ta cika ta batse da mata da mazan funani. Duk masu tallar nononnan da sukaita wucewa ashe duk can zasu je. Iko sai Allah tafiya mabuɗin ilimi kenan. Haka na haye akori kura na biya nera ɗari, a cakuɗe muke da maza, motar an cika mutane har bana iya shaƙar numfashin kirki, baka jin komai sai warin hammata da ƙarnin nono. Ga hanyar babu kyau, haka mu kaita cuccurewa waje guda da mazan da matan. Na sha ɗan karen wuya ainun kafin mu isa Jere Banyo. A mugun galabaice na fito, ina mayar da numfashina.
Masu acaɓa ne naji suna ta ihun faɗin.
"Jaɓɓi lamba zaki je, kuzo mu je" A galabaice na isa gaban acaɓar nace.
Jaɓɓi lamba zani, nawa ne?"
"Nera hamsin ne, hau mu je"
Hawa nayi ya ja muka nitsa. Ya Allah birni ma rahamane, kwazazzabo muka dinga shiga, acaɓarnan tana sama tana ƙasa damu tamkar zamu kifa. Ƙarafan acaɓar na riƙe dam, na runtse idandunana inata karanto adda'a,. Ga ƙurar jar bushasshiyar rairayi data cika mun idona da hancina dam. Wallahi na ɗauka kafin in sauka daga acaɓarnan zamu rikito mu afka wani ƙaton ramin, babu kwalta ko guntu. Bani na buɗe idona ba har sai da mai acaɓa yace.
"Mun iso madakata fa" kana na buɗe idanuna a hankali na ganni a tashar ƴan acaba. A mugun gajiye na sakko daga acaɓar tare da sallamarshi. Jarabawar dana samu duk yaro ko yarinyar da na tambayeta inane gidan Modibbo Yuguda mai nagge. Sai dai su bini dana mujiya basu iya yaren hausa ba, ni kuma ban iya fullanci ba. Ga duhu ya soma doso kai. Wata baiwar Allah ce ta ja hannuna zuwa gidan wani dattijo. Bayan sun yara yaren fullanci mai daɗi da garɗin saurare sai ya fuskanceni cikin gurɓatacciyar hausa yace.
"Gidan Modibbo Yuguda mai nagge kike nema ko yarinya? Dan Ɓingel tace iyakar abunda ta gane a bayaninku kenan"
E gidanshi na zo Baba. Ni ƴar wajen matarshi Daso ce, yayar su Ɓodɗo ce daga birnin Kano " Baki ya rike tare da girgiza kanshi, ya dubeni da mamaki maɗaukaki yace.
"Kika ce ke ƴar Daso ce kuma daga birnin Kano, to Daso dama tana da wata ƴa?" Take naga ya sauya kala daga fara'a zuwa kicin_kicin. Wata dattijuwar fara sol ɗin bafulatana mai yala yalan gashi ya kirawo ta shiga dani cikin asalin gidan. Bayan yace mun zai tura yanzu a tawo da Dadan. Cikin wata bukka aka shiga dani, sai da na sunkuya sosai kafin na iya shiga cikin bukkar, irin gidajen da suke dashi kenan a rugar . Ban taɓa ganin ɗakin gargajiya a zahirance ba sai yau, ɗakin ya burgeni ya ƙayatar dani. Jeren ƙorene kyawawa masu zanen tsuntsaye da masu zanen ƙadangare gasu nan iri iri an mammanna su a jikin bangon bukkar. Daga kusurwa biyu kuma wasu ƙwaryane hawan hawa a jejjere ko wanne anyi mishi murfo da faifal mai kala_kala. Ɗayar kusurwar kuma jeren kwallane masu hoton tsuntsaye da korayen ciyayi, ga wasu tukwanen ƙasa a kikkife a gefe. Abun al'ajabi baya ƙarewa sai gani ga gadon ƙasa da katifar yayi. Ƙasan cikin bukkar kuma buhune aka ɗinka aka shinfiɗa a matsayin ledar tsakar ɗaki. A gefe na zauna ƙuri ga duhu_ duhu a cikin ɗakin. Wannan dattijuwar ce ta shigo hannunta rike da fitilar aci bal_bal, akwai wani ɗan gini da akayi a saman ɗakin kamar anyi gininne musamman domin ajjiye wannan aci bal_bal ɗin. Bayan ta ajiye sai tace dani.
"Use ɓilgel ( sannu yarinya)" Sai naga ta fita. Inaso ince zan yi alwala in yi sallah amman bansan me zance ba, dole haka nayi gum. Can bayan duhu ya mamaye sararin samaniya duniya tayi baƙi ƙirin sai na jiyo muryar Dada. Murya mai zaƙi da siranta, muryar dake raunata zuchiyata take kara mun so da tausayin uwata. Cikin bukkar ta shigo da sallama. Tana saye da wata iriyar jemammiyar atampar dana taɓa sai mata a shekarun baya. Sai ɗan wani yalolon tattararren mayafi mai ruwan ƙwai. Ƙafafuwanta kuwa duk ƙura. Idanu ta ƙura mun ƙur, sai naga guraben idanunta tab da ruwan ƙwalla.
"Jabu kece a Jaɓɓi lamba a darennan? Kinsan fa kin tambayeni zaki kawo mana ziyara nace miki a'a. To me yasa zaki yi gaban kanki ki zo, ita kuma uwar taki ta barki bacin tasan...."
Sai ta ja bakinta ta tsuƙe tare da sauke gwauron numfashi.
"Tawo mu tafi to, kawo jakar in riƙe miki"
Ta kai hannunta zata ɗauki jakata nayi wuf na ɗauka.
A'a Dada zan ɗauka. Kuma kiyi haƙuri dole ce tasa na zo gareki, dole ce tasa Iyaa ta barni nazo, ba a san ranta na tawo ba" Duk fa maganganunnan da yarbanci muke yinshi. Babu dai abinda tace dani sai naga ta sunkuya ta fice. Bayanta nabi muka fita, muna tafe a jere da juna abinda bamu taɓa yi ba kenan. Tiryan_tiryan mu kaiya tafiya, muna wuce samari da ƴan mata. A yadda na lura kab garin gidajensu iri ɗaya ne, gidajen bukka zagaye da jinka, basu da dangar gini ko da na laka ne. Wani gida muka shiga ƙatoton gaske, mata da yaran gidan nono_nono kowa ya ja zugar abokan hirarshi. Ga aci bal_bal kashi kashi, sai fullanci akeyi ana dariya. Mijin Dada yana zaune akan tabarmar keso da rediyo a gabanshi yana ji, ga abinci da kofi a gabanshi. Sallamar Dada yasa wani yaro namiji da ƴar budurwa suka nufota da sauri suna faɗin.
"Use Dada" ( Sannu Dada)
Mijinta ya juyo ya dube ni, ya dubi Dada dana fuskanci tun shigowarmu jikinta yake rawa.
"Je ki gaishe da Babanku gashi can" Ta dubi wannan ƴar berar da tazo ta tareta sai tai mata yare. Shi kuma namijin sai ya amshi jakar hannuna, ita ƴar budurwar kuma tai mun jagora zuwa wajen mijin Dada, gashi ni ban iya Fullanci ba. Haka dai na durƙusa a gabanshi gaisuwar dai ta kurame mu ka yi, sannan muka zo mu ka tarar da Dada tsaye inda muka barta ta nausa a cikin tunani mai nauyi, har sai da ƴar rakiyata ta jijjiga hannayenta.
"Dada am"
Tace kafin Dada ta dawo cikin nutsuwarta, bayan ta ja fasali sai ta dubeni tace.
"Mu je in kai ki ki gaisa da abokan zamana" Binta nayi a baya ta nuna musu ni, nai musu gaisuwar kurame biyu a cikinsu suna ɗan jin Hausa sai muka gaisa da kyau. Daga cikin ƴan mata da yaran gidan ma suna jin Hausa hakan yasa na ɗan ji sanyi. Amman bansan me Dada tace dasu a kaina ba ni dai. Zungul_zungul na bi bayanta har cikin bukkar da nake da tabbacin nata ɗakun kenan. Babu komai a ɗakin sai tarkace kawai, sai gadon ƙasa da katifar yayi taji zanin gado. A bakin gadon tace in zauna. Bayan na zauna Dada sai ta fita. Wannan budurwar kuma tana wajen tulu tana ɗebo mun ruwa a ƙoƙo, bayan ta bani na sha, sai nace.
"Inason zan shiga bayan gida, banyi sallar la'asarba ƙila isha tayi ma ko?"
"E muma mun yi sallar Isha. Muje in kai ki"
Cikin gurɓatacciyar hausar da ba ko wacce nake ganewa ba tayi maganar. Muna fitowa tsakar gidan sai muka tarar da Dada da abokan zamanta a tabarmar da mijinsu yake zaune. Sai faɗa yake zubowa yana ambaton Daso_Daso. Jikina tuni ya bani a kaina ake tattauna maganganu, da jin ƙarfin muryar kuwa ba magana bace ta daɗi. Na sake gasgata hakanne da na ji muryar Dada na rawa, da kuma irin yanda kab yaran gidan su kai ciko_cirko kuma suka ƙura mun idanu kamar maye yaga jariri.
MRS BUKHARI
NAMA YA DAHU....
ROMO ƊANYE
BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
Lamba ta sha biyu (12)
Da jan ƙafa na bi wannan ƴar budurwar da nake kyautata zaton kanwata ce uwarmu ɗaya. Wani waje ne aka ɗan keɓeshi aka zagaye da kara, nuni taimun da hannunta halamar nanne ban ɗakin. Ruwa ta zuba mun a buta ta miƙo mun nasa hannu na karɓa, tare da shiga ban ɗakin. Ƙasace a ban ɗakin , sai ɗan gefe guda da akayi daɓe inaga a wajen suke wanka, sai ramin shadda a gefe. A ƙyamace nayi bawali na fito, inda zan ɗaura alwala ta nuna mun, naga gidan kamar komai da tsari suke yinshi. Nayi alwala muka fito a tare. Har zuwa wannan lokacin Ina jiyo muryar Dada tana magana. Da ƙyar nayi sallolin da ake bina nayi jigum akan buhun da aka shimfiɗa mun nayi Sallah. Abinci wannan budurwa ta kawo mun a cikin ƙwarya an rufe ƙwaryar da faifai.
Ya sunanki ne?" Na tambayeta ina ɗan fara'a.
"Sunana Cubu"
Kin sanni?" Na sake jefo mata tambaya.
Sai ta girgiza mun kanta halamar A'a. Sai na yi ɗan murmushi nace.
Ke yarinyar Dada ce?"
Sai da tayi dariya sosai kana ta bani amsa ta hanyar ɗaga mun kanta halamar e" Kwaryar abincin na buɗe tuwone da wata miya baƙa ƙirin ba koriya ba, sai wani irin ƙamshin ganye take yi marar daɗi, amman dake ina jin ɗan karen yinwa ba shiri na nutsa hannuna a cikin tuwon. Wallahi da ƙyar na iya haɗiye tuwonnan, ko da na haɗiye dambe mu kai ta tayi, yana shirin dawowa ni kuma ina ƙoƙarin mayar dashi, dan gudun kar suce na ƙyamacesu. Inaga Cubu ta fuskanci bazan iya cin tuwon bane, sai ta miƙe ta kawo mun madarar shanu. Dana kafa kaina sai da na shanye madarar tas. Ina sauke kofin nayi gyatsa, sai ga Dada ta shigo tana sharar hawaye cikin dabara, dan ita a tunaninta ma bamu ganta ba. Zargina ya tabbata akwai wani babban abu da aketa ɓoyemun tsawon shekarunnan da ba'ason ni in sani. Ni kuma ina ganin lokaci yayi daya kamata in sani. Bakin gado ta zauna kanta a ƙasa kamar yadda ta saba tace.
"In kin gama cin abincin Cubu ta rakaki gidan Ɓoɗɗo acan zaki kwana, ƙanwatace a gidan itace uwar mijin Baɗɗo uwarmu ɗaya ubanmu ɗaya babu wata matsala. In Allah ya kaimu gobe na dawo tallan nono zan biyo gidan in same ki. Cubu ƙanwarki ce ƙanwar Ɓoɗɗo, yar Yusuf. Amma. Akwai Amaduyal shine a sama da Ɓoɗɗo sai dai shi baya zama, yanzu haka suna togo, sun fita kiwon shanu tsawon shekara biyar basu dawo ba, amman ana jin labarinsu, suna yo aike gida, matarshi Sa'ada tana cikin gidannan, da yaranta biyu" Kai na gyaɗa. mamakin daya kamani shine jin Dada ta ambaci tallan nono, kenan itama tallah take yi kamar yadda na ga wasu guggun mata a Jere Banyo da ƙoren tallarsu? Iko sai Allah ai yaci ace Dada tana zaune ne tana morar haihuwa ba wai ace har yanzu aikin wahala take yi ba. Miƙewa nayi tsaye Cubu ta ɗaukarmun jakar kayana.
To sai Allah ya kaimu goben Dada"
Na yi magana a mugun sanyaye. Cubu da Yusufu ne suke gaba ina biye dasu a baya, ina kallon gari maza suna kwakkwance a tabarma, wasu kuma sunyi da'ira suna cin abinci. Yayinda samari masu jini a jika suke ta sha'aninsu kawai. Ta wani dandali muka zo wucewa nan naga kyawawan ƴan mata farare, da kyawawan Samari. Ƴan mata na waƙa samari na yi musu tafi. Wasu kuma keɓe suke a gefe guda suna musayar kalaman ƙauna. Rayuwar ƙauye akwai ban ƙawa a cikinta, bugu da ƙari akwai nishaɗi sosai. Tafiyace miƙaƙƙiyar gaske mu kayi kafin mu iso gidan Boɗɗo, duk na gama galabaita, ga gajiyar hanya da dama ban huceta ba, ga wannan tafiya me nisa da muka sake yinta. Suna kwance a tsakar gida mu kai sallama muka shiga, mazan gidan kuma kafin mu shigo sai da mukai musu sallama. Da sauri Boɗɗo ta taso ta tare mu." Ina tsaye bansan me Cubu tace da'ita ba. Kawai sai naga ta rungumeni ta fashe da kuka.
"Adda Jabu ashe zan sake ganinki a rayuwa? Cike zukatanmu suke da maraicinki" Ta faɗi hakan da kwaɓaɓɓiyar hausa. Nima hawayene suka gangaro kan kumatuna. Nan Boɗɗo ta shiga dani cikin gida tana ta nunani, ni dai Adda Jabu kawai nake jin tana ambato. Ɗakin Yafendo Kaɓoji ta kaini ƙanwar Dada surukarta kenan. Kanta ta dinga jijjigawa tana nanata sunana. Abunda na fahimta ƙanenane kaɗai sukai farin ciki da ganina. Hannuna Baɗɗo ta jawo muka shiga cikin bukkar data kasance ɗakinta, Su Yusufu na biye damu. Boɗɗo ta kalli su Cubu tace.
"Sunanta Adda Jabu. Yayar Amaduyal ce, Dada ce ta haifeta itace yarinyarta ta farko. Ina tunanin sanadintane ke sa Dada ƙunci da zubar hawayen da tun tasowarmu muka tsinci Dada a wannan halin." Runguma suka kawo mun dukkansu ukun, babu nuna ƙyama ba komai. Hawaye masu ɗumi sukaita zurubtu a kumaruna, hankalina a madadin ya kwanta sai ya sake tashi. Ni kaina na jima ina tausayama rayuwar Dada, na daɗe ina zargin bata jin daɗin rayuwa akwai wani babban lamari data ƙunsa a cikin ranta yake nuƙurƙusar rayuwarta. A wannan daren mun yi hira sosai da ƙannena na yaushe gamo, dan su Cubu sunƙi tafiya a cewarsu sai dai du mu kwana a zaune.
"Adda Jabu ki ce su tafi, Baffa zai yi faɗa sosai, ko ma yazo gidannan a darennan. Gobe Cubu zata kai nono cikin gari, Yusufu kuma zai fita da Shanu kiyo Kuma zata burga madara ta fitar da man shanu da asuba."
Jim na kuma yi jin abinda Boɗɗo take faɗe.
Cubu tunda kinsan hakane, ku yi haƙuri ku tafi gida. Ni ina nan na dawo rugarnan kenan, daku zanci gaba da rayuwata" Da kyar na lallaɓasu suka tafi, suna tafiya sai ga mijin Boɗɗo ya shigo ya miƙo balangu a baƙar leda. Boɗɗo ta gabatar mishi dani a matsayin babbar yayarsu. Cike da jin kunya ya sake gaisheni yana sosa ƙeyarshi shi a dole kunyata ce ta kamashi. Kai fulani a kwaisu da kunya da kawaici sosai. Fitar mijin Boɗɗo ke da wuya mu ka jiyo sallamar wata mata da Boɗɗo ta yo kiranta da suna Hama Ƙwarya ta ajjiye mun a gabana tace.
"Use baƙuwa"
Farar bafulatana doguwa gata da baƙin gashi. Da fara'arta muka gaisa duk da hausar kamar ta yara ƴan koyo suke yinta.
"Adda wannan matar wan su Yuguda ce, mijinta shine Babba a gidannan, yana fita aiki cikin birni.
Allah sarki, sannu Hama nagode sosai da fura" Murmushi ta kuma yi mun haƙoranta kamar ƙanƙara dan haske, a gaskiya Hama kyakkyawar macece banga wata makusa a tattare da'ita ba face ta rashin wayewa, da ƙazanta kuma dan ƙafarta duk faso fasonnan ya ɗebi wata annakiya ya adana. Ga gashi iya gashi amman kitson a furje kuma cike da yayin katifa. Boɗɗo tace.
"Hama wanna itace Babbar yarmu Adda Jabu, ba lallai bane ki san labarinta ba. Nima naci da bin diddigi yasa na san labarinta. Ta taɓa zuwa rugarnan da daɗewa lokacin muna yara ƙananu." Tare da Hama mu ka ci balangunnan mu ka taɓa hira dai haka. Duk da gajiyace ainun a jikina, ga tunane _tunane da suka haɗu suka cukurkuɗe mun rayuwata. Duk wani bugun zuchiyata bugawa yake yi da so da ƙaunar Gwadabe na. Haka tausayin mahaifiyata da son jin matsalarta suma su ka dabaibayeni. Ina fatan in zame mata sanyin idaniya, maganin zubar hawayenta.amman ta yaya tunda mijinta ma bai karɓeni a matsayin ƴa ba, tunda gashi a darennan ya kasa haƙuri ko da kwana guda ne in yi. Ko ma Iyaa Debisi ta faɗa mun yana da faɗa, bauɗaɗɗen mutum ne ainun. Tunani, da zafi, da sauro su suka hanani huce gajiya ta hanyar saka haƙarƙarina a ƙasa, katifar yayin dana kwanta akai sai sossokeni kawai take yi. Babu shiri na miƙe na fito tsakar gidan, duk yawan matan gidan suna kwance a tsakar gida bisa katifun yayi. A kan tabarma na kwanta iska na ɗan hura ni kaɗan. Da haka ɓarawon bacci yayi awon gaba dani izuwa asubar fari, kwaramniya da kukan shanu ne ya farkar dani. Ashe nonon shanu ake ta tatsa, su kuma sai kuka suke yi. Wasu daga cikin matan na gansu suna burga nono da wani itace mai kama da maburgin miyar yauƙi, wasu kuma suna ta aikin dahuwar madarar shanu, yayin da wasu suke sharar garken Shanu, wasu kuma girkin safe suke yi. Ina buɗe idanu Hama dake shara tace.
"Jabu kukan nagge ya tashe ki ko? " Tai maganar tana murmushi. Nima Murmushi nayi mata kawai, na miƙe Boɗɗo dake zaune a cikin jerin matan da suke ta burga nono ta miƙo mun buta, tai mun nuni da ban ɗaki.
Ruwa na kama na fito na ɗaura alwala na shige ciki. Na jima ina roƙon Allah yayi mun mafita, ya kuma sassauta mun soyayyar Gwadabe a ruhina, bazan roƙi ya cire mun soyayyr ba dan abadan Gwadabe bazai gaza samun gurbi a rayuwata ba. Tunano ƴaƴana yasa hawaye suka zubo mun a kumatuna, ba shiri na miƙe na fita. Ɗaya bayan ɗaya na dinga bin matan gidan muna gaisawa, mun shiga ɗakin ƙanwar Dada ma mun gaisa. Cikin garken shanu Boɗɗo ta jani wai in taya ta mu tatsi nonon Saniya ta dafa mana mu sha. A baya na bita zuwa cikin garken shanun a nan muka tarar da Hama a ciki ita da mijinta suna shafa ma wata saniya magani jikinta duk kuraje ya fito.
"Wannan itace baƙuwar tamu Boɗɗo? Ai Hama yanzu take faɗa mun cewar mun yi bakuwa kuma ma ƴar uwa" Cewar mijin Hama wani dogo siririn bafulatani sosai, ga gashi a kwance a kanshi lub, na lura kamar yafi kowa tsayi a gidan, ko dan ya fi kowa sirantane oho.
"E Yaya Hamma itace baƙuwar tamu, Ita ce sama da Amaduyal, daga ita
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 16