An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
NAMA YA DAHU....
ROMO ƊANYE"
GAWURTATTU UKU
DAGA ALƘALAMIN BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
MARUBUCIYAR LITTAFIN NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA (LABARIN SHANONO DA OGA KAILA.
NA SAKE DAWOWA DA WANI LABARIN MAI ƊAUKE DA DARASI, DA BAN TAUSAYI, SADAUKARWA, TSAGWARON ZUNZURUTUN SOYAYYA DA ƘAUNA, FARIN CIKI, BAƘIN CIKI DUK A CIKIN WANNAN LITTAFI MAI SUNA A SAMA. KU BIYONI KU SHA KARATU.
ALƘALAMINA BAYA RUBUTA ABINDA BAZAI AMFANAR DA AL'UMMAR ANNABI BA.
KAMAR YADDA NA SABA WANNAN LABARIN SHIMA YA FARU A GASKEN GASKE, KU BIYO NI DA HANKICI DOMIN SHARE HAWAYEN DA ZASU ZOBO A GURABEN IDANUWANKU. KU GYARA ZAMA DA KYAU KU BI LABARIN SANNU_SANNU ZAKU FAHIMCI INDA YASA GABA.
Lamba ta 1
JIHAR KANO:
Kano na ɗaya daga cikin manyan birane a ƙasar Hausa. Kano itace cibiyar kasuwanci ta Najeriya gaba ɗaya. Jihar ta Kano tana da ƙananan hukumomi guda arba'in da hudu. Kana gari ne da yake da masarauta mai ɗunbun tarihi, mai kwarjini a cikin kasashen Hausa da kewayenta. Haka zalika Kano gari ne babba wanda mazauna cikinta ke magana da harshen Hausa. Itace gari mafi yawan jama'a a Najeriya baki ɗaya.
Kanon ta yi suna wajen kasuwancin da ta bunkasa a kai, har ya zamana ana cewa da ita Cibiyar Kasuwanci. Haka kuma tarihin Kano ya nuna daman can tana da suna wurin cinikayya tsakaninta da mutanen gabas ta tsakiya.
Yawan mutanen da suke garin na Kano sun haura kimanin mutane miliyan goma (10.000,000) a ƙidayar da aka yi a shekara ta alif dubu biyu da shida. Jihar Kano tana da matuƙar tasiri a yawan mutane Najeriya, saboda ita ce ta fi kowacce jiha yawan mutane daga ko'ina a faɗin duniya, tun daga na kudancin Najeriya, har zuwa ƙasashen dake maƙwabtaka da Najeriya,hakq kuma za ka tarar da mutanen sin ( wato china) da kuma na ƙasashen larabawa har da turawan yammacin duniya mutanen Kano sun shahara wajen addini sosai.
ƘOFAR MATA.
Cikin wani layin masu rangwamen arziki na shiga. Duk da kasancewa safiya ce sosai. Hakan bai hana ganin yara suna kai kawo a cikin unguwa ba. Wasu suna kan layin siyan ƙosai, wasu suna kan layin siyan fanke. Wasu yaran da gasarar kokko na gansu a hannunsu. Kasancewar baifi ƙarfe bakwai da rabin safiya ba. Anata hada_hadar shirin karya kumallo. A bakin wani madaidaicin gida na tsaya marar fenti, mai ɗauke da ƙatuwar bishiyar durumi a ƙofar gidan ƙosasshiyar gaske. A ƙarƙashin wannan bishiyar na hango motoci biyu a fake, ɗayar golf 3 ce, ɗayar kuma Vectra ce. Da dukkan halama motocin ta masu gidance. Wani matashine ya fito daga gidan hannunshi riƙe da bokitin ƙarfe cike dumbul da ruwa, ga soson buhu a ɗayan hannun nashi. A gaban motocinnan ya ajjiye bokitin, nan take ya soma watsa ma Vectra ɗinnan ruwa. Daga cikin gidan dai na jiyo hayaniya na tashi kuma muryar namiji nake jiyowa, har da kukan mace daga bisani na jiyo. Ba shiri na faɗa cikin gidan dan ganin meke faruwa haka.
Abun mamaki ashe gidan babbane sosai daga ciki, gashi da yalwar tsakar gida. Ɗakuna kuwa gasunan a jejjere kamar a zangon baƙi ( Hotel). Maza da matan gidan, harma da yaran gidan na tarar a tsakar gidan. Wani babban mutum na gani yana ta faɗa, muryarshi ce take fita har ƙofar gida. Babbane a shekaru, dan har da furfura a gemunshi da sumar kanshi. A gefenshi na hango wata doguwar fara kyakkyawar mace a tsaye jikinta sharkab da ruwa har ɗiga take yi tsabaragen jiƙewa, kuka take yi ƙaƙas tamkar wacce akayi ma mutuwa, gata ita dai ba yarinya bace. Wannan Dattijon cikin murya mai amon ɓacin rai yace.
"Haula ki dena kukan ya'isa ki bari su fito inji in shi Gwadabenne yasa matar tashi ta watsa miki ruwan kashi sai in ji. Ke da gidan mijinki babu wanda ya'isa ya takura miki wallahi, zan ture zumunta in kori Gwadabe da iyalinshi a gidana, wannan ƙazanta ta buskuta samodarar matarshi ni ya isheni. Ina mai takaici da baƙin cikin haɗa zuriya da matar Gwadabe da mu ka yi" Ya ƙarashe maganar yana huci kamar zaki."
Gwadabe:.
Da sauri ya fito daga ɗakin nashi rigarshi a hannu, shimi ce a jikinshi da koɗaɗɗen wandon jeans wanda akayi ma wanki sama da sau saba'in, duk yayi yaushi, ya sake kala daga turarren bulu, izuwa kalar sararin samaniya.
"Yaya Hambali kayi haƙuri dan Allah. Kema Yaya Haula ki yi haquri. Iyabo ba da saninta ta watsa miki ruwan kashi a jiki ba. Bata san kina banɗakin bane, amman kiyi haƙuri dan Allah, kuma zata kiyaye " Gwadabe ya faɗa cikin sigar kare iyalinshi, duk da abinda ya faɗan gaskiya ne. Amman dake a hasale suke da Iyabo shi yasa maganar take ƙoƙarin zama babba. Dama ƙiris suke jira ta kuskure su dirar mata a wuya, sabida tsantsar ƙiyayyar da suke nuna ma Iyabo wacce har idanuwansu suka rufe wannan ƙiyayyar tashafi ɗan uwansu gudan jininsu Gwadabe. Harisu wanda ya kasance wa ga Gwadabe, ƙani ga Hambali, ɗa na uku a wajen mahaifiyarsu yace.
"To ita shafaffiyar da mai bamu da matsayin da zata iya fitowa ta ba Yaya Hambali da Yaya Haula haƙuri kenan ko yaya akayi ne Gwadabe?. Nifa na kasa gane wannan baƙin sha'ani naka da iyalinka kanka kalau yake kuwa" Yaya Hambali wanda maganar Harisu ta kasance tamkar zuga a gareshi yace.
"Ta fito ta ba da haƙuri kuwa Harisu? alhalin ba ganinmu da gashi take yi ba. Gwadabe ya gama watsar mana da darajarmu a idanunta. Allah wadaranka Gwadabe ka cucemu daka cakuɗa mana iri da Iyabo, ba zamu taɓa yafe maka cutarwar da kayi mana ba."
"Ya'isa haka Yaya Hambali dan Allah mana. Wannan maganganun tamkar cin fuskane a wajen Iyabo. Sannan ni banga aibu ko laifin Iyabo dan ta kasance Beyerabiya ba. Ni da ku, da iyabo duk musulmaine,kuma duk mutanene Allah ɗaya muke bauta ma, kuma kamar yadda muke sallah, da azumi haka take yi itama" Azabure Hambali yayi kanshi a zafafe yana shirin dukan ƙirjinshi. Harisu ne yai musu iyaka ta hanyar shiga tsakiyarsu dukan ya sauka tabb a tsakiyan gadon bayan Harisun tsabar zafin dukan saida ya gantsare. Jikin Yaya Hambali har rawa yake yi yana ganin Gwadabe kamar yayi mishi rashin kunyane. Barinma yana ganin Gwadabe tamkar shi ya tsugunna ya haifeshi tsabar girme mishi da yayi. Mutum huɗu ne a tsakaninsu kafin Gwadabe. Akwai Yaya Halima wacce ta kasance itace Babba a cikin ummansu, sannan shi Yaya Hambalin, ga Harisu, sannan ga ɗan Fodiyo, ga Sukairaju. Shi Gwadabe daga shi sai Da'u, daga Da'u sai Zakari, sai ƴar Auta Sauwama." Shi kanshi Gwadaben har cikin ƙoƙon ranshi baiji daɗin yanda yayi ma Yaya Hambalin ba, ko babu komai ya girme mishi, kuma shine makwafin uba a garesu baki ɗaya, gashi cikin ummanshi. Yaya Hambali ya bauta musu sosai, kasancewar tun suna ƙananu Allah yai ma mahaifinsu rasuwa. Shi ya maye musu gurbin uba, shine noma, shine kiwo, Fataucin dabino kuwa shi ya gaji mahaifinsu, yayi musu dukkannin wani gata har Allah ya cicciɓesu suka kai matakin mallakar hankali da girman jiki, dana haihuwa.
"Lallai Gwadabe baka da hankali ba'acikin hayyacinka kake ba, matarka da danginta sun gama mallakeka, imma ka yarda, imma ka ƙaryatani, tunda ka soma sa'insa damu shingin duka ya rage.Yaya Hambalin kake mayarma da magana?" Cewar Ɗan Fudiyo wanda ya cike da mamakin ɗan uwan nasu Gwadabe" Yaya Hambali kuwa tsai yayi yana kallon Gwadabe, tare da ƴan uwanshi da suka dira mishi a ka, kowa na tofa albarkacin bakinshi a kan abunda matarshi Iyabo ta yi, da abunda ya aikata yanzu. Gabaki ɗaya Gwadabe sai ya dibibice, kasancewar ba halinshi bane raina na gaba an yi mishi wannan kyakkyawar shaidar sosai. Ya fusata ainun ne da yanda suke cin zarafin iyalinshi ba dare ba rana, ba tare da ta yi musu laifin zaune ba, balle laifin tsaye. ana cikin haka Sai ga Iyabo ta ƙaraso wajen a kidime, jikinta har rawa yake yi dan tasan Gwadabe ba karamin ruwa ya kirawo mata ba"
Iyabo:.
Tunda Gwadabe ya fito jikina yake ɓari, domin nasan danginshi kab ba ƙaunata suke yi ba, kuma ƙiris suke jiran kuskure na. Sai gashi yau azal ta hau kaina. Daman daren jiya cike na kwana da fargabar zuwa ƙauyansu Gwadabe da zamu je yau biki. Ina tsoron Allah ina tsoron abinda zai haɗa taron biki, ko suna a ƙauyensu Gwadabe ace kuma zanje nima. Ina muzanta, da takura fiye da tunani. Furucin da Gwadabe ya fesarma da Baban Nazifi ya fi firgitani fiye da dalilin rikicin. Ba shiri na buɗe labule na fito ina tura tsohon cikina gaba. Saye nake da leshi riga da zane. Rigar ɗinkin buba, zanin kuma ciki da alako irin ɗinkin yarenmu kenan. Idanu mu ka haɗa da Gwadabena tausayinshi ya sake dirarmun a zuchiyata, har nake jin ko ratayeni danginshi zasu yi, ni da Gwadabe mutu ka raba. Dan shi ɗin cikakken jarumin masoyine na haƙiƙa tunda ya aureni bai sake samun kwanciyar hankali da salama ta ɓangaren iyaye da dangi ba. A zamantakewata dashi kuma haƙiƙatan bai taɓa yi mun wani abun ashsha ba, riritani yake yi, gami da tarairayar zuchiyata tamkar ƙwai, hakanne yake ƙaramin ƙarfin zuchiya da jumurin shanye duk abinda danginshi suke yi mun. Sai dai irin zaman bashi da daɗi, yana raɓa rayuwata da dukkannin farin cikina. Damma Gwadabe na ƙoƙarin sharemun dukkan hawayena.
Dan Allah Baban Nazifi kayi haƙuri. Umman Nazifi dan Allah ki gafarceni wallahi bansan kina cikin banɗakin bane, ban watsa miki da ganganba" Na faɗa ina mai ƙoƙarin haɗiye kukana tare da shanye fishina. Idanu Gwadabe ya lumshe mun cikin sigar ban haƙuri, nima nawa idanun na lumshe mishi cikin bashi amsar shima yayi haƙurin. Idanunshi ya rufe ya buɗesu tare da ɗan zare su, halamar ya samu sassauci a zuchiyarshi. Dukkan wannan maganar kuramen masoyan dake gudana a tsakaninmu babu wanda yasan me muke nufi, amman dai suna kallonmu, idanun kowa a kanmu yake.
"Ke Iyabo kar ki sake zubar mana da kashi ta magudana, nan ba gidan yarbawa bane, dama ku yarbawa a cikin ƙabilu wama ya kaiku ƙazanta, da ɗaukar kashi ba abun ƙyama ba?. In banda ƙazanta yama zaki zubar da kashi ta magudana. Mu dai ana cutar damu da wannan kafirar ƙazantar ta yarbawa." Cewar Gude matar Yaya Sukairaju Kenan. Dama tafi kowa tsanata da caccaɓa mini maganganu kaifafa. Na ji zafin abinda ta faɗa a kan yarbawa, dan ina kishin yarena ina kuma alfahari da kasancewata Beyerabiya."
"Gwadabe da mun dawo daga Takai biki ka tattare matarka da ɗanka ku bar mun gidana, na gaji da ganinku dukkanku." Da sauri na dubi Gwadabe, shi kuma ya kalli Baban Nazifi. Ba mu kaɗai mu ka jijjiga da furucin Baban Nazifi ba, sauran yayyen Gwadabe da matayensu, harma da yaransu wanda suke fahimtar abunda akeyi sai da su ka girgiza.
"Haula mu je ki sake kayanki mu kama hanya banso takwas ta yi mun a gida ba. Sukairaju ku kama hanyar tafiya muma yanzu zamu kama hanyarmu" Take kowa ya watse ya barmu jijjunanmu a sanyaye sosai. Hannuna Gwadabe ya ja a hankali mu ka koma ɗaki. Muna shiga na zauna a kujera daɓas sai da kujerar ta yi ƙara kasancewata mai ƙiba da ɓaka_ɓakan mazaunai. Kuka mai gunji na fashe dashi. Gwadabe ya zauna a kusa dani ya dafe kanshi da hannu bibbiyu, idanunshi yayi jawur. Ya kasa furtamun kalma sai tubka da warwara kawai yake yi, tare da neman tudun dafawa. Mu da mu ke cin abinci da wuya ta ina zamu iya kama hayar muhalli? Dama dai burin dangin Gwadabe su ga mun tagayyara ne yau na sake tabbatarwa.
"Ki yi haquri Iyabo da duk abubbuwan da kike gani, kike ji, da wanda zaki sake ji in mun tafi Takai. Ina mai ƙara baki haƙuri kuma ki sani ni Gwadabe ina tare da sonki, ina sonki Iyabo fiye da son da uwa take ma ɗan cikinta. Ina mai baki haƙuri Iyabo bisa abinda dangina da naki dangin suke yi miki duk sabida Aurenmu. Ina alfahari da soyayyar da ni Gwadabe nake yi miki. Wallahi Iyabo kece sanyi da farin cikin ruhina. Ki share hawayenku mu kama hanyar Takai Sukairaju ya ɗakko mana bus zamu tafi baki ɗaya." Hawayena na share jikina a mugun mace murus, kalaman Gwadabe sun kashe mun jiki. Haƙiƙa Gwadabe na yi mun soyayya mai yawan gaske. Amman ko ƙafar inda nake son shi bai kama ba, gashi a kullum zuchiyata sake jarabtuwa da Gwadabe take yi.
Gwadabe yanzu in Baban Nazifi yace mu bar mishi gidanshi wanne tudu zamu dafa, ina zamu bi mu ga haske? Ka duba ka gani abinci da ƙyar muke ci. Wanke_wanke da sharar da nake zuwa yi albashin nera dubu biyu ne a wata, kuɗin ba yawa bane dashi. Kai kuma ba ko da yaushe oganka yake samun lodi ba balle mu samu ɗan kuɗin sallamar iyali da ake baku. Gwadabe ya zamu yi dan Allah?"
"A'a Iyabo Allah zai yi mana mafita. Zamu tattauna maganar a gaban Babala in mun je Takai. In ta goyi bayan Yaya Hambali kan mu tashi mu bar mishi gidanshi. Ba makawa zamu tashi duk da nasan bani da ko ficikar da zan iya kama mana haya. Dukkanmu a ƙasanta mu ke tunda ita ta haifemu, kinga tsohon ciki gareki damuwa da kuka ai ba naki bane ƴar yarbawata. Oh Allah yayi ba Debisi bane mijinki, ni ɗin dai da basa so ni na yi sa'ar samun ki, Alhamdulillah. Ko mutuwa na yi nasan na zaɓarma yarana uwa ta gari, ba zasu tuhumeni ba." Dariya nayi harda ƙyaƙyatawa, shima dariyar yake yi. Muka shiga tuno gwagwarmaya da muka sha kafin mu kawo wannan matakin. Duk da dai har gobe tsugunne bata kare mana ba. Tuni nasa ƙafa na shure matsalolin dangin Gwadabe na miƙe na shiga ciki dan ɗakko mana jakar kayanmu. Toye yana kwance sai baccinshi yake yi a shirye yake tsab. Mayafi na ɗauko na jawo ƙaramin akwatin kayanmu da jakar kayan Toye. Ni banso tafiya ma dashi ba naso in Kai shi gidanmu, sabida nima fama nake da kaina cikina wata bakwai amman girmanshi yasa ake mun kallon haihuwa ko yau ko gobe. Toye shekararshi shida da haihuwa sa'anninshi na gidan duk sun shiga makarantar islamiyya mu bamu da kuɗin saka shi a makaranta, in yaje ma ana koroshi kuɗin laraba, inna samu ko ni ko Baban sai mu biya. Amman da zaran laraba tayi bamu biya ba ake koroshi, sai Gwadabe ya yanke hukuncin ni na dinga koya mishi Abacada, Gwadabe kuma yana koya mishi baƙin arabic. Shigowa yayi ya saɓa Toye a kafaɗarshi ya zari akwatin kayanmu.
"Zaki iya ɗaukan jakar kayan Toye ko in kai wanna in dawo?" Murmusawa nayi na ɗauki jakar kayan da jakar hannuna, na bi bayanshi. Gaba su ka yi, ni kuma na tsaya na kulle ƙofata na biyo bayanshi. Da ƙyar fa nake tafiya gashi duk na yi kumburi, ga hawan jini na masu juna ina fama dashi. Ko da muka fito, sai muka tarar Bus ɗin ta cika duk sun ɗaura yaransu a kan kujerar sun babbake.
"Motar ba zata isaba Gwadabe abinda za'ayi ku je ku hau motar haya zaifi." Cewar Sukairaju yana gama faɗar haka suka ja motar fu, Bus ɗin na gaba motar Baban Nazifi na biye, kana motar Harisu ta rufa musu baya. Yawu Gwadabe ya haɗiye muƙut jijiyoyin kanshi suka fito raɗa_raɗa.
"Mu je tasha Iyabo" A daƙile yayi maganar. Ni kam ina biye dashi ko gani bana iya yi sosai tsabaragen tashin hankali da damuwa. Shikenan na yi sanadiyyar raba kan wannan zuriyar masu son juna da son zumunta? Gwadabe tunda ya aureni ya zama saniyar ware a dangi. Ina jin rashin daɗi da na zame mishi silar zama mujiya a cikin dangi. Har mu ka isa tasha banji Gwadabe ya ce komai ba, hakan ya sake damuna ainun gashi muna hanya babu damar in rarrasheshi ko zai samu ɗan sassauci. Ga wani ruguntsumin ma yana jiraye damu a Takai. Mota ya sama mana Bus ni da shi ne a can baya ta ƙarshe wajen window, Toye yana rungume a jikinshi yana baccinshi. Yaron na ƙura ma idanu ina mai cike da tausayinshi da abunda yake cikina ta yanda zasu rayu cikin rashin gatan dangi ɓangaren uwa da uba, Toye ko cikin yaran gida ya shiga bashi da damar yin wasa dasu, yaran zasu shiga yi mishi waƙar da iyayensu suka saba rerawa a tsakar gidan. Suna tafi suna cewa Yarbawa masu kwalo_kwalo da ɗuwawu suke tuƙin tuwo. Toye sai yai ta kuka abunka da yarinta, wataran ma da gudu yake dawowa ya faɗa jikina. Ta bangaren dangina ma suna adawa da aurena da Gwadabe sosai da sosai kasancewar shi Bahaushene ba Beyerabe ba. Rabon ƴaƴane da ƙudurar Allah ya tabbatar da aurena da masoyina Gwadabe.
"Tunanin me kike yi haka Iyabo mai zurfin gaske. Kaddai akan furucin Yaya Hambali ne akan mu bar mishi gidanshi? Iyabo ni kaina inaso mu tashi a gidan ba tun yau ba. Ko dan kema ki samu yancin yin rayuwar ƴanci irin wacce ko wacce mace take fatan samu. Na yi imanin dangina ba zasu zo har gidanki su takura miki ba, ko zasu takura miki ba kamar in gidanmu ɗaya ba. Ni da na zame musu dole zanyi zumunci dasu..."
A'a Gwadabe wannan ba zai ma yiwu ba. Babala ba zata bar Baban Nazifi ya tozartamu ba. In muka bar gidannan ina zamu shiga a ina zamu dinga samu kuɗin da zamu biya haya? Sannan yarannan zasu sake rasa dangin mahaifansu ta dukka ɓangarori biyu. Amman in dai muna taren a gida ɗaya su Toye zasu taso da sanin lallai su Nazifi ƴan uwansu ne danginsu ne, a gida ɗaya akayi tarbiyyarsu. Kar ka mance Babala ma burinta kenan ganin kun haɗe kawunanku da na iyalinku baki ɗaya. Ka yi haƙuri da batun tashinmu,madamar ba Babala bace ta goyi bayan Baban Nazifi akan tashin namu ba. Kasan sai ka ƙara mun baƙin jini a wajen danginka" Idanu ya lumshe kawai sai girgiza kanshi yake yi. Ɗan guntun siririn hawayen daya surnano mun na yi maza na share gudun kar Gwadabe ya buɗe idanunshi ya ga zubar hawayena. Har Bus ɗinmu ta cika muka fito daga tasha bamu sake magana ba. Ko wanne cikinmu aikin tubka da warwara kawai yake yi a zuchiyarshi. Motarmu sai gudu take shararawa bisa titi, tun muna wuce titinan cikin gari muna wuce manyan gidajen sama, da manyan shopping mall har mu ka soma wuce ciyayi da fasassun kwalta, jagab_jagab ɗin hanya ne yasa Gwadabe yai ta mun aikin sannu har muka shiga cikin ƙaramar hukumar Takai.
TAKAI TA KAWO TA SABA DA SAUKAR BAƘI
Takai ƙaramar hukumace take jihar Kano. Yanki ne wanda Allah ya albarkace shi da ruwan sama a sanadiyyar hakanne mutanen yankin su ke noma da kiwo da kasuwanci gashi Allah subuhanahu wata ala ya albarkaci garin takai da bishiyun dabinai masu yawan gaske, dabino ya wadaci jama'ar Takai sosai mota_mota ake fita da dabino domin kasuwancinshi. Garin Takai yankine wanda ya yi nesa da birnin kano da tsawon kilomita 80, yayi kusa da yankunan ƙasar Bauchi, yankin da yake yawan kawowa ƙasar kano farmaki a lokacin sarkin kano (Babba Zaki) Sanadiyyar hare_haren da yake yawan kaima birnin kano, Sarkin Kano Babba Zaki ya yanke shawarar a kafa ƙasar Takai, kuma ayi ganuwa a garin. Hakanne yasa ya tura mayaƙa domin su zauna a garin. Bayan an kafa dausayin yaƙi a garin Takai, Sarkin Kano Babba Zaki ya gina gidan sarkin kano a garin Takai kuma ya so ya koma garin Takai ɗin da zama." Muna sauka daga mota mu ka hau mashin ya wuce damu Unguwar Dibinai unguwa mai dogon tarihi kenan a garin na Takai. Dai dai ƙofar gidansu Gwadabe acaɓanmu ya tsaya, ƙofar gidan cike maƙil da maza, mata kuma sunata shige da fice. Bara'u Abokin Gwadabe ne ya tarbeshi da fara'arshi, yasa hannu ya amshe Toye ya rungume.
"Madam Iyabo barka da isowa tsuntsun soyayya" Dariyar dole na yi mishi, dan muddun muka haɗu dashi sai ya furta wannan suna daya raɗa mana.
Bara'u barka dai da gida, ya yara da Sakinar?" Dariya yayi yace.
"Sakina tun safe tana cikin gida sun zo taya aikin biki. Yaran naku ma zaki gansu a ciki" Ɗan murmusawa nayi, Gwadabe ya dubeni yace.
"Iyabo ki shiga ciki, zan gaggaisa da ƴan uwa da abokan arziki. Gasu Yaya Hambali can a ƙarƙashin bishiyar dabino suma "
To shikenan sai mun haɗu, ka kawo akwati da jakar to" Dan nasan matsawar ban karɓa ba da ƴan uwanshi sun ƙilla ido suka ga akwatinan a hannunshi to zan sha habaici da maganganun banza" Bara'u yace.
"Bashshi ki yi fama da kanki, yara zasu shigo miki dashi" Gwadabe yace.
"Kaima ka faɗa mata, da ba dan bikinnan ya zame mata dole zuwanshi ba, ai da bama zata yi doguwar tafiya da ciki haka ba, baka ga wuyar da tasha a hanya ba wallahi. Bikin Auta guda in bata zo ba kai kasan akwai ƙura" Ni dai a wajen na yi shigewata cikin gidan na barsu a tsaye suna tattaunawa, Gwadabe bashi da aminin daya shallake Bara'u a wajenshi, tare suka taso, su kai wasan ƙasarsu, har shayi tare akayi musu. Komawar Gwadabe Cikin birni bai rage amintakarsu ba sam, dan Sakina matarshi tasha zuwar mana ita
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 16