fi sha'awan ta aure saurayi ko da wanda ya ja shekaru ne amma Alhaji Sama'ila girma ya gama bayyana a gareshi yasan dududu ba zai ƙara shekaru goma kan nashi ba a duniya, a hankali ya yi magana cikin sanyin jiki
"Hamrah, farin cikin mu shine kiyi aure, kema ki sami farin ciki kamar kowa, ba wai bamu son Alhaji Sama'ila bane a'a ba haka bane, kamar yadda Daddyn ya ce babu wanda yasan asalin shi, sannan ba a san sana'ar shi ba, ba zayyu a dauke ki a bashi ke ba, ba tare da anyi bincike akan shi ba, bai ce min komai ba sannan bai bani amsar tambayoyin da na yi mashi ba kawai ya girgiza kai ne wanda i don't know what that means shine na ji shakku akan shi, amma kuma in dai zai aure ki ya baki farin ciki muna maraba dashi"
Ta sauke numfashi tare da tashi ta zauna ta naɗe ƙafafuwanta ta ce
Ga dukkan alamu mutumin kirƙi ne, sannan in kayi duba da lokaci guda ya ce yana so na da aure hakan ya nuna kamilalle ne, sannan next time idan ya zo zan tambaye shi labarin shi kaga zamu sami duk amshoshin mu.
Ya sauke numfashi ya ce
"Allah shi kyauta, me ki ke so na kawo miki zan fita bakin hanya na dawo"
Ta fahimci baya son maganar ne shine ya sauyata, ta ce
Ni bana ma sha'awar komi duk abin da ka siyo ka kawo ina so sai dai amma abin ya zamto mara nawi.
"To shikenan sai na dawo"
Ya miƙe ya fice, ta sauke numfashi ta shiga zancen zuci daman haka sha'anin aure yake da zaran an fara zancen yin sa sai an sami tangarɗa amma baza ta bari wannan damar ta wuce ta ba ta ɗau tsawon shekaru tana jiran irinta, ai kuma duk wanda ya ce yana son ka kuma yana son haɗa zuri'a da kai to ya fi wanda zai ce ba ya son ka..... Ringing wayar ta tayi tana duba ba sai ganin Abuja ta yi yana ƙira ta ɗauka tare da sallama ya amsa tare da cewa
"Likita bokan turai in ban nemeki ba ke baza ki neme ni ba, shariyar ta yi yawa"
Ta yi murmushi ta ce
Yau na wuni da ɓaki shiyasa ban samu sukuni ba sai yanzu shi ɗin ma kwanciya na yi sbd na samu na miƙe.
Ya sauke numfashi ya ce
"Ni dai nasan har yanzu ban sami gurɓi cikin zuciyar ki ba"
Murmushi tayi ta ce
A'a ba haka bane, na faɗa maka uzuri na.
"To shikenan ranki shidaɗe, da fatan kina lafiya?"
Alhamdulillah.
Suna fira Ammar ya shigo jin da Alhaji Sama'ila ta ke wayar yasa ya ajiye mata ledar bai ko waiwayo ya sake kallon inda ta ke ba ya fice abinshi, ta yi murmushi tare da girgiza kanta suka ci gaba da firar su, yake sanar da ita gobe zai wuce Abuja zayyi kwana biyu kafin nan ya dawo ta ce dashi Allah ya kiyaye hanya su kayi sallama ta buɗe ledar ta ci gashashiyar kazar da ya siyo da fresh milk sannan ta kwanta.
Tun da ta farka sallah asubah bata koma ba ta hau shirin tafiya wajen aiki tea da bread tasha ta ɗau jakarta ta fito ɗakin Ammar ta yi nocking jin shuru yasa ta turo kofar ta shiga sai ganin shi ta yi yana Sallah ta duba a gogo a lokacin 7:00am, ya sallame tare da juyowa ya kalleta tana zaune bakin bed ya ƙarashe addu'o'in shi sannan ya ce
"Good morning likita?"
Ta sauke numfashi ta ce
Ammar yaushe ka daina sallah asubah kasan kuwa karfe nawa yanzu?.
Ya sauke numfashi tare da cewa
"Makara na yi jiya ban kwanta da wuri ba"
Ammar ai ya kamata ka sanya Alarm, Kai ba yaro bane da za kayi ta bacci sai lokacin da kaga dama ka tashi ka idar, sannan ko yaro ma an fi son ya dinga yinta har ta shige jikin shi amma gaskiya ka gyara hakan ba daidai bane.
Ya sauke numfashi ya tashi ya iso kusa da ita ya zauna ya ce
"Na gaidake baki amsa ba"
Lafiya ta kalau, Please ka dinga tashi da asubah kana sallah akan lokaci.
"Na faɗa miki makara nayi amma zan gyara"
Wannan ba hujja ba ce kace ka makara amma tunda kace zaka gyara that's good. Sallar asubah itace mafi alkhairi fiye da Bacci, ka rage bacci don ka ribanta da goben ka.
Bacci amsawar zuciya ne ita Kuwa sallah amsawar kiran Ubangiji ne.
Shi bacci mutuwa ne ita kuwa sallah rayuwa ce.
Shi bacci hutu ne na gangar jiki sallah kuwa hutu ne na ruhi.
Bacci da mumini da kafiri duk suna yinsa ita kuwa sallah musulman kwarai sune kadai ke yinta.
Masu tashi lokacin ketowar alfijiri sun rabauta, fuskarsu kuma ta haskaka, goshinsu kuma yayi Haske da Kyalli, lokacinsu kuma yayi albarka, idan kana cikinsu toh Ka godewa ALLAH da Ya Fifita ka, Idan Kuwa baka cikinsu toh Ka roki ALLAH Ya saka Cikin su.
Farillarsa {Sallar Asuba} zata Saka ka Acikin Kulawar Ubangiji
Sunnarsa (Rak'ataanil fajr) tafi Duniya da abinda ke cikin ta.
Ita sallar asubah da Mala'iku masu aikin dare da Mala'iku masu aikin safe duka suna halartar ta, kasani duk wanda ya rayu akan wani aiki toh akansa zai mutu, wanda ya Mutu kan wani aiki kuma akansa za'a tashe shi.
Jikin Ammar ya yi matukar sanyi, ko shi bai ji daɗi ba da ya tashi a makare amma ba ɗabi'ar shi bace ya ce
"Na gode da tunatar dani da ki kayi, har kin shirya ko?"
Eh bari ma na wuce kada na makara.
Ya miƙe tare da yi mata rakiya suka fito, ya koma ita ta wuce ɗakin Ammie ta same su da Daddy suna faisa sannan ta fito ta wuce wajen aiki, baya ta ɗan a daidaita ya sauke ne tashigo ganin yanda ake kai kawo yasa ta tabbatar da sun ji labarin OG zai shigo tayi murmushi a ranta ta ce duniya ba gaskiya ba zasu yi aiki sakanin su da Allah ba sai dai suyi dan mutum, Allah shi kyauta. Ta buɗe office ta shige tare da fito da duk wasu abubuwan da zata buƙata tana cikin hakan ne Dr Mahmoud ya shigo.
Ɗauko white coat nata ta yi tare da sanya white eyes glass ta ɗau wayar ta tare da sanyata cikin aljuhun rigar tana ƙoƙarin fitowa ya yi saurin riƙe ƙofar ya hanata fitowa ya ce
"Amma ai kin ga shigowa ta shine zaki fice wannan bai dace ba"
Ɗagowa ta yi tana kallon shi da fararen idanuwanta ta ɗan waro su ta ce
Dr Mahmoud i think you have nothing to do, so bani hanya na je na duba patients ɗina lokaci na tafiya.
Ya sauke numfashi yana kallon pretty face nata ya ce
"Yaushe zaki daina min wulakanci, sbd kinga na damu a kanki ne ki ke min haka, to ki sani badan MD ya haɗa mu muyi aiki tare ba, ba ki isa ki wulakanta ni ba"
Murmushi Hamrah tayi ta ce
I need to go.
Ya ɗan matsa ta buɗe kofar ta fito tare da ce mashi
Zan kulle ƙofar.
Ya fito ta rufe ta kama hanyar tafiya general ward shi kuma yana biye da ita har suka shigo tare suka duba so ya rigata barin wajen ita kam ta jima sannan ta dawo, zata shige ciki ne taji muryar MD ya kirata ta shigo tare da gaidashi ya amsa ya ce
"OG zai shigo nan da 30 minutes so, you should get ready with the all records, if possible ma i have to see them before ki kai mashi ko ki faɗa min me da me yake buƙatar"
Ta sauke numfashi a ranta ta ce, tasan wannan abin ne ya kai Dr Mahmoud office nata ɗazu ganin basu sami wani kwakkwaran dalili bane yasa ya yi kiranta da kanshi ta ce
Sir, akwai abubuwan da zan sake dubawa bari na tafi.
Ya buɗe jajayen idanuwan shi ya zuba mata ya ce
"In kin kammala ki kawo na gani"
To.
Ta faɗa sannan ta dawo office nata, a nutse ta fiddo su ta shiga dubasu kamar yadda ta keyi nan ta shirya komai ta kammala tsarawa ta ji ana nocking ta bada izinin shigowa Dr Laraba ce ta ke shaida mata OG ya iso an hallara a ɗakin meeting ta fito in ji MD, ta ce da ita tana fitowa.
A nutse ta fito ganin office na Dr Mahmoud da MD a kulle yasa ta sauke numfashi tare da furtawa
Thank God.
Ta iso a lokacin OG ma ya shigo ana gaisawa ta gaida shi, sanye yake da suit baƙi koman shi baki hatta eyes glass dake idanun shi ma baƙi ne, yana da haske ba cen ba ya cire glass ɗin ya ce
"Dr Hamrah lafiya kalau ya kokari"
Alhamdulillah sir.
Ta ajiye mashi komai ta ɗan kalli MD shima ita yake kallo sabar haushi kamar ya shaƙo ta badan OG ne ya ƙirashi ba da ko sai ya karɓi document ɗin ya sauya komai ya tafi daidai da na office nashi kada ya banbanta. Ya sakar mata da harara ta yi kamar bata ganshi ba ta yi murmushi ƙasa² ta ce cikin ranta da saura jira akwai wasan da baka san dashi ba yanzu za a fara buga shi.....
"Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yake bamu ikon akan komai, ina mai farin ciki da jin daɗin yanda ku ke gudanar da aikace-aikace a wannan asibitin kuma ina jin yadda jami'a ke yaba ku, Alhamdulillah, musamman ma Dr Hamrah tana na mijin ƙoƙari kuma ina alfahari da ita"
Cewa OG sai da ya kai aya ya yi shuru yana duban su sannan ya kai hannu ya fara duba document dake gaban shi a nutsu ya ke dubawa sai da yazo kan list na staff da partner su sai yaga na list da kuma office dake cikin document da MD ya bashi daban ya ke da wanda ya ke wajen Dr Hamrah, cike da mamaki ya ce
"Ya naga banbanci sakanin list of staff's and there duty's partners ya banbanta me yasa haka?"
Saurin miƙewa MD ya yi ya ce
"With do respect sir, ni ne na sauya sbd ci gaban wannan Hospital ɗin naga ƙanzawa shine zaifi kuma zai kawo cigaba"
Sauke numfashi OG ya yi ya ce
"To ya aka yi yasha banban da na Dr Hamrah, sannan kuma meyasa ka yanke hukunci ba tare da neman izinina ba"
Nan wuta ta ɗaukewa MD ya juyo da jajayen idanuwan sa yana kallon Hamrah ganin haka ta ɗauke kai kamar bata san yana yi ba ya sauke numfashi tare da cewa in kin san wata baki san wata ba, cikin ranshi ya faɗa a fili ya ce
"Eh na manta ne banyi comparing da nata ba but all this ya faru ne sbd rashin bada haɗin kai da bata yi ba"
Sosai OG ya ke kallon shi sannan ya ce
"For what reasons ta ki bada haɗin kai?"
Kai tsaye MD ya ce
"I don't know kawai bata girmama ni ne"
Murmushi Hamrah ta yi bata ce komai ba sai da OG ya kalleta ya ce
"Hamrah meyake faruwa ne, shin gaskiya ne MD ya ke faɗi?"
Cikin girmamawa ta ce
Eh sir amma ina da dalilina na yin hakan.
Ya kalleta tare da cewa
"Menene dalilin?"
Yana da ikon yanke hukunci amma kuma duk da haka ya kamata ya shawarce ni wajen kanza min partner kawai kwasam sai dai jin na yi ya ɗauke Dr Aliyu ya kaishi bangaren yara, sannan kuma ya sauke mishi albashin sa, a kullum neman ci gaba ake ba wai baya ba sannan hakan da ya yi takura ce da kuma jefa shi cikin damuwa shine naga hakan bai dace ba wannan ne dalilin da yasa naƙi bashi goyon baya.
Shiru wajen ya yi ya kalli MD tare da cewa
"Haka ne abin da ta faɗa?"
Ya tsosa keyarsa ya ce
"Haka ne amma.....
"Ya isa haka, na yi cansel na wannan transfer from office to another office dan haka kowa ya koma nashi office ɗin na da sai mun zauna zamu sauya"
Yana gama faɗin haka ya fice, MD ya daki teburin dake wajen yana huce wai always Hamrah, Hamrah, Hamrah. Ya fice a wajen ya wuce office nashi yana huce Dr Mahmoud ya shigo amma ya ɗaga masa hannu alamun ya fita, ya fice ya ci gaba da tunani zuci ya akayi ya faɗi a wannan lokacin amma yasan yanda zai bollowa al'amarin.
Hamrah cikin farin ciki ta dawo office nata, ko ba komai Dr Aliyu zai dawo office nashi ya ci gaba da aikin shi, tana so ta wanke kanta daga ganin cewa da ita aka haɗa baki aka cire shi daga cikin office nashi....
Turo ƙofar Dr Aliyu ya yi ya shigo cikin sanyin jiki, bata ɗago ba jin turo ƙofar yasa ta ke tunanin Dr Mahmoud ne ko MD har yanzu idanuwanta a lumshe suke ....
"Dr Hamrah"
Jin muryar Dr Aliyu ne yasa ta buɗe idanuwanta ta kalle shi, bata yi mamakin zuwan shi ba dan tasan zaizo amma kuma bata yi farin cikin ganin shi ba, har ya ƙaraso kusa da teburin ya zauna tare da cewa
"Dr Hamrah....
Dr Aliyu i don't need any word from you, please step out.
Sauke numfashi ya yi kamar zayyi kuka yana bukatar ta saurare shi amma yasan abu ne mai wuya sbd irin ci mata mutunci da ya yi, cikin sanyin jiki ya miƙe a hankali ya fice da nufin da ta sauko zai sake dawowa.
(Ji na da ku kayi shuru 2days rasuwa aka min naje na dawo. Masu addu'oi da kuma waɗanda suka ƙirani da waɗanda su ka yimin magana duk ina godiya, Allah ya bada ladan ta'aziya) littafin MUJARRABI labari ne mai ɗauke da sakonni daban daban ta ko wanne fanni kuma tafiya ce mai ɗan tsawo sai dai ina tabbatar muku cewa baza kuyi nadamar bibiyar labarin ba. Har yanzu muna cikin shinfiɗa asalin labarin na nan zuwa.
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 19 & 20
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
__________ Da ƙyar ta ke iya fidda numfashi tana sauke ajiyar zuciya on on zuciyarta na yi mata zafi sai gumi ta ke haɗawa, tana jin kanta na tsara mata zazzaɓi na neman rufe ta cikin ƙanƙanin lokaci. Ta juya tare da jan blanket ta rufe jikin ta tare da rumtse idanuwanta waɗanda suka kasa fidda kwallah sbd damuwa, a kullum sai tayi tunanin meyasa hakan ke faruwa cikin rayuwarta, yaushe zata ji ta cikin farin ciki kamar yanda kowa ke ji, yaushe iyayenta zasu daina faɗa a kanta, yaushe za a koma cikin farin ciki irin na rayuwar baya, yaushe, yaushe, yaushe?. Amma da ta tuna cewa ko wane bawa da irin ta sa jarrabawar sai taji sanyi cikin ranta, duk abin da ya yi farko yana da ƙarshe kuma duk tsanani yana tare da sauki kamar yadda bata taɓa zaton zata riski wannan lokacin ba haka bazata cire sammanin samun sauki nan gaba ba.
"Hamrah"
A hankali ta buɗe idanuwanta sbd jin muryar Ammar da ya ƙira sunanta, ta haɗiye damuwar ta tare da sauke numfashi ta fito da fuskar ta tare da ɗan kishingiɗe jikin bed ta ce
Ammar, na yi tunanin ka kwanta ai, shiyasa nima na kwanta sbd gobe Monday kuma morning duty gareni.
Ya sauke numfashi sosai ya ke kallonta, duk da tana ɓoye damuwarta kada ya gane amma tun shigowan shi ya riga da ya gane sannan yaji abin da iyayensu suke cewa, ko shi kanshi baya son irin yadda su keyi, sun daina jituwa da juna zaman lafiyar ma yanzu ba sosai suke yin ta ba, abin damuwar ma shine yanda Ammie ta ke ɗauka hot akan maganar, babban tashin hankalin shi shine tafiyar da zayyi ya bar Hamrah, yasan za tayi ta shiga damuwa gashi kuma zayyi nesa da ita babu mai kwantar mata da hankali. Ya sauke numfashi a hankali ya ce
"Ban kwanta ba ina chatting ne muna online meeting, muna gamawa ne na ce bari nazo sbd ɗazu kin ce kina son magana dani"
Ta kwakulo murmushi dole tare da cewa
Ammar, shin menene laifina akan zaɓar Alhaji Sama'ila da nayi, meyasa ka ke ganin bai dace na zaɓe shi ba, shin akwai abin da ya faɗa maka ne?.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kura mata idanuwa na wani lokaci yana jin tausayinta yasan tana yin wannan ne saboda ta sami kulawar Ammie ta samu ta sauko su koma daidai kamar yadda suke a cen baya har ake ƙiransu da ba a shiga sskaninsu sbd yadda suke shawara da juna koman Ammie Hamrah. Sai dai ya fi sha'awan ta aure saurayi ko da wanda ya ja shekaru ne amma Alhaji Sama'ila girma ya gama bayyana a gareshi yasan dududu ba zai ƙara shekaru goma kan nashi ba a duniya, a hankali ya yi magana cikin sanyin jiki
"Hamrah, farin cikin mu shine kiyi aure, kema ki sami farin ciki kamar kowa, ba wai bamu son Alhaji Sama'ila bane a'a ba haka bane, kamar yadda Daddyn ya ce babu wanda yasan asalin shi, sannan ba a san sana'ar shi ba, ba zayyu a dauke ki a bashi ke ba, ba tare da anyi bincike akan shi ba, bai ce min komai ba sannan bai bani amsar tambayoyin da na yi mashi ba kawai ya girgiza kai ne wanda i don't know what that means shine na ji shakku akan shi, amma kuma in dai zai aure ki ya baki farin ciki muna maraba dashi"
Ta sauke numfashi tare da tashi ta zauna ta naɗe ƙafafuwanta ta ce
Ga dukkan alamu mutumin kirƙi ne, sannan in kayi duba da lokaci guda ya ce yana so na da aure hakan ya nuna kamilalle ne, sannan next time idan ya zo zan tambaye shi labarin shi kaga zamu sami duk amshoshin mu.
Ya sauke numfashi ya ce
"Allah shi kyauta, me ki ke so na kawo miki zan fita bakin hanya na dawo"
Ta fahimci baya son maganar ne shine ya sauyata, ta ce
Ni bana ma sha'awar komi duk abin da ka siyo ka kawo ina so sai dai amma abin ya zamto mara nawi.
"To shikenan sai na dawo"
Ya miƙe ya fice, ta sauke numfashi ta shiga zancen zuci daman haka sha'anin aure yake da zaran an fara zancen yin sa sai an sami tangarɗa amma baza ta bari wannan damar ta wuce ta ba ta ɗau tsawon shekaru tana jiran irinta, ai kuma duk wanda ya ce yana son ka kuma yana son haɗa zuri'a da kai to ya fi wanda zai ce ba ya son ka..... Ringing wayar ta tayi tana duba ba sai ganin Abuja ta yi yana ƙira ta ɗauka tare da sallama ya amsa tare da cewa
"Likita bokan turai in ban nemeki ba ke baza ki neme ni ba, shariyar ta yi yawa"
Ta yi murmushi ta ce
Yau na wuni da ɓaki shiyasa ban samu sukuni ba sai yanzu shi ɗin ma kwanciya na yi sbd na samu na miƙe.
Ya sauke numfashi ya ce
"Ni dai nasan har yanzu ban sami gurɓi cikin zuciyar ki ba"
Murmushi tayi ta ce
A'a ba haka bane, na faɗa maka uzuri na.
"To shikenan ranki shidaɗe, da fatan kina lafiya?"
Alhamdulillah.
Suna fira Ammar ya shigo jin da Alhaji Sama'ila ta ke wayar yasa ya ajiye mata ledar bai ko waiwayo ya sake kallon inda ta ke ba ya fice abinshi, ta yi murmushi tare da girgiza kanta suka ci gaba da firar su, yake sanar da ita gobe zai wuce Abuja zayyi kwana biyu kafin nan ya dawo ta ce dashi Allah ya kiyaye hanya su kayi sallama ta buɗe ledar ta ci gashashiyar kazar da ya siyo da fresh milk sannan ta kwanta.
Tun da ta farka sallah asubah bata koma ba ta hau shirin tafiya wajen aiki tea da bread tasha ta ɗau jakarta ta fito ɗakin Ammar ta yi nocking jin shuru yasa ta turo kofar ta shiga sai ganin shi ta yi yana Sallah ta duba a gogo a lokacin 7:00am, ya sallame tare da juyowa ya kalleta tana zaune bakin bed ya ƙarashe addu'o'in shi sannan ya ce
"Good morning likita?"
Ta sauke numfashi ta ce
Ammar yaushe ka daina sallah asubah kasan kuwa karfe nawa yanzu?.
Ya sauke numfashi tare da cewa
"Makara na yi jiya ban kwanta da wuri ba"
Ammar ai ya kamata ka sanya Alarm, Kai ba yaro bane da za kayi ta bacci sai lokacin da kaga dama ka tashi ka idar, sannan ko yaro ma an fi son ya dinga yinta har ta shige jikin shi amma gaskiya ka gyara hakan ba daidai bane.
Ya sauke numfashi ya tashi ya iso kusa da ita ya zauna ya ce
"Na gaidake baki amsa ba"
Lafiya ta kalau, Please ka dinga tashi da asubah kana sallah akan lokaci.
"Na faɗa miki makara nayi amma zan gyara"
Wannan ba hujja ba ce kace ka makara amma tunda kace zaka gyara that's good. Sallar asubah itace mafi alkhairi fiye da Bacci, ka rage bacci don ka ribanta da goben ka.
Bacci amsawar zuciya ne ita Kuwa sallah amsawar kiran Ubangiji ne.
Shi bacci mutuwa ne ita kuwa sallah rayuwa ce.
Shi bacci hutu ne na gangar jiki sallah kuwa hutu ne na ruhi.
Bacci da mumini da kafiri duk suna yinsa ita kuwa sallah musulman kwarai sune kadai ke yinta.
Masu tashi lokacin ketowar alfijiri sun rabauta, fuskarsu kuma ta haskaka, goshinsu kuma yayi Haske da Kyalli, lokacinsu kuma yayi albarka, idan kana cikinsu toh Ka godewa ALLAH da Ya Fifita ka, Idan Kuwa baka cikinsu toh Ka roki ALLAH Ya saka Cikin su.
Farillarsa {Sallar Asuba} zata Saka ka Acikin Kulawar Ubangiji
Sunnarsa (Rak'ataanil fajr) tafi Duniya da abinda ke cikin ta.
Ita sallar asubah da Mala'iku masu aikin dare da Mala'iku masu aikin safe duka suna halartar ta, kasani duk wanda ya rayu akan wani aiki toh akansa zai mutu, wanda ya Mutu kan wani aiki kuma akansa za'a tashe shi.
Jikin Ammar ya yi matukar sanyi, ko shi bai ji daɗi ba da ya tashi a makare amma ba ɗabi'ar shi bace ya ce
"Na gode da tunatar dani da ki kayi, har kin shirya ko?"
Eh bari ma na wuce kada na makara.
Ya miƙe tare da yi mata rakiya suka fito, ya koma ita ta wuce ɗakin Ammie ta same su da Daddy suna faisa sannan ta fito ta wuce wajen aiki, baya ta ɗan a daidaita ya sauke ne tashigo ganin yanda ake kai kawo yasa ta tabbatar da sun ji labarin OG zai shigo tayi murmushi a ranta ta ce duniya ba gaskiya ba zasu yi aiki sakanin su da Allah ba sai dai suyi dan mutum, Allah shi kyauta. Ta buɗe office ta shige tare da fito da duk wasu abubuwan da zata buƙata tana cikin hakan ne Dr Mahmoud ya shigo.
Ɗauko white coat nata ta yi tare da sanya white eyes glass ta ɗau wayar ta tare da sanyata cikin aljuhun rigar tana ƙoƙarin fitowa ya yi saurin riƙe ƙofar ya hanata fitowa ya ce
"Amma ai kin ga shigowa ta shine zaki fice wannan bai dace ba"
Ɗagowa ta yi tana kallon shi da fararen idanuwanta ta ɗan waro su ta ce
Dr Mahmoud i think you have nothing to do, so bani hanya na je na duba patients ɗina lokaci na tafiya.
Ya sauke numfashi yana kallon pretty face nata ya ce
"Yaushe zaki daina min wulakanci, sbd kinga na damu a kanki ne ki ke min haka, to ki sani badan MD ya haɗa mu muyi aiki tare ba, ba ki isa ki wulakanta ni ba"
Murmushi Hamrah tayi ta ce
I need to go.
Ya ɗan matsa ta buɗe kofar ta fito tare da ce mashi
Zan kulle ƙofar.
Ya fito ta rufe ta kama hanyar tafiya general ward shi kuma yana biye da ita har suka shigo tare suka duba so ya rigata barin wajen ita kam ta jima sannan ta dawo, zata shige ciki ne taji muryar MD ya kirata ta shigo tare da gaidashi ya amsa ya ce
"OG zai shigo nan da 30 minutes so, you should get ready with the all records, if possible ma i have to see them before ki kai mashi ko ki faɗa min me da me yake buƙatar"
Ta sauke numfashi a ranta ta ce, tasan wannan abin ne ya kai Dr Mahmoud office nata ɗazu ganin basu sami wani kwakkwaran dalili bane yasa ya yi kiranta da kanshi ta ce
Sir, akwai abubuwan da zan sake dubawa bari na tafi.
Ya buɗe jajayen idanuwan shi ya zuba mata ya ce
"In kin kammala
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 19