sakanina da shine.
Tana faɗin haka ta shige cikin general ward, tana mamakin gulmar ma'aikatan wannan Hospital ɗin musamman ita wannan Nurse mai suna Laraba akwai kai kawo sakanin ma'aikata. A nutse take gaisawa da patients ɗin ta jima a wajen su, sannan ta dawo office nata, Dr Aliyu ya shigo tare da sallama yana
"Good morning special Doctor"
Cikin sakin fuska ta ce
Morning doctor Aliyu, ya ƙoƙari?.
"Sai godiya kam"
Da akwai abin da kake buƙata ne?.
"Eh Dr Hamrah akwai patients nawa taƙi na duba ta shine na ce ko zaki duɓa min ita, kin san yawanci mata in ba a dole ba ba sa son maza su duba su, ita ma wannan haka taƙi"
A hankali ta katse abin da take yi a system nata ta ɗago, ta ce
A wane ward take?.
"Tana vip 3"
Ok ba matsala a tare suka fito, Dr Mahmoud yana daga bakin ƙofar office na shi ya kura musu idanu ganin su tare kuma su biyu yasa ya haɗe rai har suka ɓace wa ganin sa. Dr Hamrah ta wuce vip shi kuma ya wuce wani bangaren, tana shiga ta tadda patient ɗin ta dubata sannan ta fito ta iso office nata. Dr Mahmoud da kuma MD suna tsaye suna tattaunawa har ta iso ba tare da tayi magana ba ta buɗe office ta shige ta zauna, ta kunna system nata ta ci gaba da aikin ta. Taji an turo kofar a hankali ta ɗago MD ne ya ƙaraso ya tsaya yana karewa cikin office ɗin kallo cike da mamaki ta kallon shi mutum ko sallama ba zayyi ba da girmansa....
"Hamrah who are you?"
Ta sauke numfashi, bata yi mamakin wannan tambayar ba dan indai bak'ar magana ce ya iya yinta kuma duk yanda yaso haka yake yinta ta ce
I'm human like everyone.
"Saboda jiya nayi miki magana shine kika ɗau gaba dani?"
Ta sake kashe system nata ta ce
Subhanallah gaba kuma MD, a'a ni bana riƙe kowa a raina kuma mema zai sa na yi gaba da kai?.
Eh wato duk iya shegen sa akwai wacce ta fi shi, murmushi yayi har jajayen hakwaransa suka bayyana ya cire glass na idon shi ya ce
"To me yasa da kika ganni da Dr Mahmoud ki ka wuce ko gaishe ni bakiyi ba?"
Ta sauke numfashi ta ce
Oh i got it, nayi tunanin kuna tattaunawa ne shiyasa bana son katse ku.
Nan ma ya ce
"Hamrah i need to know more about you"
This time murmushi ta yi ta ce
I'm nobody but I'm somebody.
"What that means"
Uhm sir, nothing.
Mamaki yake yi tabbas akwai abin da take takama da shi, koma menene zai bincika ya gani sannan kuma nan da kwanaki biyu zata gane kuren ta.
Ya juyo ya fice ta ci gaba da aikin ta. Ita sam taki jinin yawan magana musamman ma akan abin da bai da muhimmanci shiyasa sai suke ganin kamar girman kai gareta, amma she's so simple sai dai ba zata juri wulakanci ba, sannan tana girmama duk wanda ya kama girman shi.
5:00pm nayi ta fito, bayan ta kulle office nata, cikin nutuwa ta iso bakin gate na Hospital ta samu ɗan sahu ta mai kwatancen unguwar Ayshe amma ta ce dashi ya tsaya tayi shopping a bakin babban titi. Nan tayi siyayyar tsaraban yaran sannan ya kaita ta sallame sa.Turo gate ɗin tayi ta shigo ta hango yaran suna wasa a compound na gidan hankalin su kwance sai wasan su suke jin ƙarar turo ƙofar ne yasa suka juyo aiko suna ganin ta su kayo inda take suna
"Oyoyo Mommy Hamrah"
Cikin farin ciki ta rungume su tana cewa
Oyoyo, ya kuke?
Nazeer, shine ɗan fari a wajen ƙanwarta Ayshe ya ce
"Mommy Hamrah muna lafiya, ina grandma and pa?"
Tayi murmushi ta dafa kan nazeer ta ce
Suna lafiya kalau suka ce a gaida ku.
Cikin murna suka rakota ciki, a hanyar ta shigowa ciki ne ta hango sabuwar mota dal anyi parking nata a area park. Suka shigo ciki tana sallama tayi trus ganin an kanza komai na palour, tana ƙarewa wajen kallo yaran kuma su kayi ciki da gudu suna kiran sunan maman su cewa Mommy Hamrah ta shigo. Mamaki take ya a kayi Ayshe ta samu ta kanza set nata bayan sunyi magana da ita, ta ce bata da halin kanzawa. Zubawa sabon show glass din idanu tayi yadda aka jera kwalaben turaren wuta da humaira da culacham a ciki yayi tsari, ikon Allah duk wannan a 2days a kayi shi, sai kuma babban plasma ta dake kan tv stand saɓanin nata da kwanaki ƙarami dake manne jikin garu, tabi kujerun da kallo sunyi kyau cikin yadi golden color....
"Yaya Hamrah"
Ta ɗago ta kalli Ayshe dake ɗauke da murmushi kan fuskar ta, ga dukkan alamu tana cikin farin ciki, itama murmushin ta yi ta ce
Bakuwa babu sanarwa ko?.
Murmushi Ayshe ta yi ta ce
"A'a ai nan gidan ki ne zaki iya shigowa a duk lokacin da ki ka ga dama"
Murmushi HAMRA tayi taji daɗin abinda Ayshe ta faɗa mata ko ba komai ta mutunta ta shiyasa tasu tafi zuwa ɗaya ta ce
Nayi kewar yarana ne naga a weekend amin rowar su.
"Uhum kin ganni nan kwana biyu ban zauna ba yanzu hake ke nake bi a raina, ina ta son na kiraki kuma ina tunanin kina Hospital shine na bari in kin koma gida muyi waya, sai ko gaki ƴar halak"
Nima haka fa, tun jiya nake son kiranki amman ban samu na kira ba na ce kawai inna tashi wajen aiki sai na biyo na duba ki na shigo kuma naga abin duniya.
Dariya Ayshe ta yi ta ce
"Uhmm ke dai bari ƴar'uwa, bari na fara baki ruwa ki sha"
Ayshe ta shige ciki, yaran kuma suka fito suna sake mata sannu da zuwa so biyar ne ƙaramar cikin ita ce takwarar HAMRA suna kiranta da UKHTY ( ƴar'uwa), HAMRA ta rike hannunta tare da zaunar da namecynta kan cinyarta tare da ciro musu da tsara ta basu sai murna suke, ta ce da namecynta
Takwarata, how was skul?.
"So good"
Ta faɗa cikin siririyar muryar ta, yarinyar ce ƴar shekara 3 kyakkyawa da ita kamar HAMRA ce ta haife ta saboda kamanninta ta ɗauko, HAMRA ta sake ce mata
Da anyi hutu zan aiko Uncle AMMAR yazo ya taho dake kinji?.
Cikin murna ta ce
"To"
Suka shige ciki tare da tsarabar su suna murna, Ayshe ta shirya abincin kan Dining table dake Dining area ta dawo palour wajen yayar ta. Zama tayi ta ce to kinga an fara kiraye² sallah magrib mu idar tukuna"
Murmushi HAMRA ta yi sosai rabonta da taga ƙanwarta cikin wannan farin cikin har ta manta, ta ce
Ayshe na kagu naji menene dalilin wannan farin ciki haka.
Itama Ayshe tayi dariya ta ce
"Aiko zaki ji, muje bedroom mu idar da sallah tukuna"
A tare suka shige cikin, Ayshe ta ce da ita ta shige toilet ta ɗauro alwala, HAMRA ta shige ta ɗauro ta fito itama Ayshe ta shiga. Kusan lokaci guda suka idar, amma Ayshe taki bata labarin ta ce su ci abinci tukuna, HAMRA dai ta taɓe baki suka fito tana ganin mulki, sun kammala cin abinci su ne suka dawo palour suka zauna, a lokacin mijin Ayshe ya shigo tare da sallama ganin Hamra zaune yasa jikin shi sanyi ya ɗan tsaya jim kamar ya koma kuma sai ya yi wani tunani ya karaso ya zauna, murmushi Hamra ta yi da taga abin da ya yi, ta san ya san cewa ta sami labarin ƙarin auren da zayyi shine yake jin nauyinta, ta ce
Ina wuni Babana?.
Daman sunan da take kiran shi da shi tun ranar da ya saka mata takwara.
"Lafiya kalau, ya kwana biyu, na ke tambayar mamar ta ki kin ɓuya kwana biyu, ta ke ce min aiki ne ya ɓoye ki"
Sauke numfashi ta yi ta ce
Eh fah ai Sunday ne kaɗai nake hutawa, shiyasa fita unguwar ma bana samun yi yanzun ma na ce zan yi sqwizing time nawa na biyu na duba yaran.
Ah aiko kin kyauta, ai sha'anin aiki sai an jure abin ba a cewa komai, yana magana yana sunkuyar da kanshi ƙasa, ita dai sai murmushi take to menene yake wani abu so gulty to dan zayyi aure ai babu mai hana shi.
Abin da yasa yake jin nauyinta sbd ya sha wahala kamin aka ba shi Ayshe kusan hauka ya dinga yi musu, HAMRA ce ta shige ma shi gaba wajen Daddyn su aka ba shi hakan ma sai da ta haɗa da wani aminin Daddyn su sannan Daddyn na su ya amince saboda shi Daddyn a lokacin akwai wanda babu ya ya kawo kuɗin aure sannan a zo da wani zance ya ce baza a mai dashi ƙaramin mutum ba, to haka dai Hamra ta yi ta rokon sa da ƙyar ya maida musu kuɗin auren da suka kawo, saboda shima yaga tijarar da Alay Bukar yayi har fa kwana yayi a ƙofar gidan su, kuma anyi ruwa a wancan daren yayi mishi duka har sai da ya kwanta a Hospital, daga karshe dai aka bashi ita sosai ya riƙe sunyi soyayyar da sai da kaf familyn su suka sani suke sha'awar su, har ta kaiga ya saka mata takwara, saboda sake kulla zumunci, ranar suna ko anyi bidirin da ba a taɓa yin irin sa ba dan hamra tayi wasan Naira. Sauke numfashi Hamra ta yi ta ce
Amma a hutu zan aiko da Ammar ya ɗauko min takwarata.
"Babu komai ai, sai yazo ɗin in ma bai samu zuwa ba da kaina zan kai miki ita"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Na gode.
Cikin sanyin murya ya ce
"Yaya HAMRA"
Sunan da yake kiranta dashi a lokacin da yake cikin giyar son ƙanwarta duk da ya girme ta amma yake bata girma a matsayinta ta yar matar sa, cikin sanyin murya ta ce
Na'am Alay Bukar.
Daman Allah ya ƙaddara zan sake wani auren, kin san rabo babu yadda ka iya dashi, wai aka ce rabo ajali, to a takaice dai next week za a ɗaura min aure"
HAMRA ta so tayi dariya da wannan dogon zancen da ya ɗebo tun da dai aure ba fashi ai ba wani ɓoye² ta ce
Masha Allah, to Allah ya sanya alkhairi ya baka ikon yin adalci a sakanin su.
Ya washe baki yana
"Ameen wlh Daughter"
Uhm maza kenan halin su sai su. Wato fa in sun ce sai sun yi to sai sun yi ɗin. Ya miƙe ya shige ciki ya bata da zancen zuci, sai da suka idar da sallah ishai sannan ya fice ya basu waje Hamra daman a ɗaki suke HAMRA ta ce ta bata labarin wannan farin cikin, murmushi Ayshe ta yi ta ce
"To yanzu ko zaki ji........
(Sakanin mata da miji sai Allah) To sai ku biyo ni dan jin wasu hanyoyi Ayshe ta bi har wannan Alay Bukar nata ya kanza mata set. To uwar gida taho, biyo ni da gudu zuwa next pg dan jin wannan sirrin. Na san wata zata harare ni ta ce ba set ba koma menene za a kanza ba zata yarda a yi mata kishiya ba💃🤣
Allah yasa dai ana fahimtar littafin MUJARRABI 😃
Comments and share
[1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
PG 9 & 10
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_________ Tana tsaye har zuwa wannan lokacin tana kallon yanda ake fidda da kayayyakin dake office na Dr Aliyu, cikin wulakanci suke fiddawa shiyasa ma sauran kayan suke faɗuwa suke da farfashewa, lallai MD ya cika mara imani, duk da bata fahimci manufar shi ta yin hakan ba amma tasan da wata a ƙasa. Ba abu ne mai wuya ba ya ɗauke duk wanda yaga dama ya kaishi wani bangaren yanzun ma tasan wani ɓangare na daban zai kashi, shiyasa ake kiran shi da transfer master sbd yadda yake juya Nurses kamar waina, a ce ba zaya bar ma'aikata su yi aiki cikin kwanciyar hankali ba kullum cikin farga suke. Ta sauke numfashi kamar zata juyo ta komo cikin office nata sai ta hango shi yana tahowa ya turo ƙaton tumbi sai bubbuɗawa yake yana hura hanci yana taunar goro ya iso ko kallon inda ta ke bayyi ba ya wuce cikin office na Dr Mahmoud, ta juyo ta shigo ta ɗau white coat nata ta sanya tare da sanya white eyes glass nata, ta fito tare da sawa office nata key, ta wuce general ward, a nutse ta ke duba patient na ta wacce ke fama da jiki, sai da ta kammala duba ta sannan ta juyo zata fice Dr zalihat ta ce
"Dr Hamrah, neman ki ma nake, jira nake ki kammala ashe har kin kammalan kina shirin fita"
A hankali ta juyo tare da cire glass dake maƙale kan idanuwanta tana kallon Dr zalihat tare da murmushi ta ce
Dr zalihat, sannu da aiki ya ƙoƙari, nema ta ki ke yi, to Allah yasa ba laifi nayi ba.
Murmushi Dr zalihat ta yi daman akwai wasa a sakanin su ta ce
"A'a Dr Hamrah, ni a suwa, ai ku bakwa laifi, daman akan zancen ɗauke Dr Aliyu da a ka yi ne a wannan ɓangaren naga abin ba daɗi, sbd yana taimakawa sosai sannan babu ruwan shi harkar gaban shi ya ke y kuma nan ɗin ya fi dacewa dashi amma a ce MD ya dawo kusa da office naki, abin bai wani tsari ba"
Cike da mamaki Hamrah ke duban Dr zalihat, MD zai dawo office na Dr Aliyu akan wane dalili kenan, to menene amfanin shi wancan office nashi tabbas ruwa baya tsami banza amma ba zata yanke hukunci ba sbd zato zunubi ne ta ce
To ikon Allah, shi kuma Dr ALIYU ina aka kaishi?.
Eh to ɗazu nake jin nurse Laraba tana cewa wai cen bangaren yara aka kaishi kuma an yi mashi iyaka da wannan bangaren"
Sauke numfashi Hamrah tayi, tana jinjina maganar, iyaka da wannan bangaren akan menene kenan there must be something under, ta ce
To Allah yasa hakan shine mafi alkhairi.
"Ameen"
Ta fito ta tadda sauran nurses ɗin suna ta zance tayi wucewar ta, ta iso office na ta, a lokacin ake shigowa da sabbin kayayyakin MD, sai ganin Dr Mahmoud ta yi ya tsura mata idanuwa yana kallon ta ko kifta su baya yi, ta ɗauke kanta ta shige ciki.
Tana ciki har azahar, sai da ta gabatar da sallah sannan ta fito a lokacin babu har an kammala shigar da kayayyakin cikin office na MD an jera su sai ganin Dr Mahmoud ta sake yi yi ya fito daga cikin office ɗin bata kulashi ba ta wuce cen wajen patients ta zauna sai la'asar ta dawo ta idar, tana zaune kan dardumar sallah ta ji alamun shigowar mutum tare da sallama cike da mamaki ta shafa addu'ar da take yi ta juyo sbd ta sake tabbatarwa shi ne ko kuma wani ne daban, ganin shi ɗinne yasa ta ɗauke kanta, murmushi ya yi da yake ɗan duniya ne ya yi kamar ba abin da ya haɗa su, kamar bayyi mata laifi ba, ya rage tsawon shi cikin sanyin murya ya ce
"Hamrah, meyasa ki ke son zama ke kaɗai cikin.....
Dr Mahmoud, faɗi damuwar ka sbd ina da abin yi.
Murmushi yayi ya ce
"HAMRA kenan, kamar kina gudu na....
Eh ina gudun ka, sbd dabi'un ka ba masu kyau ba ne, sannan ina sake gargaɗin ka a karo na ƙarshe ka fita cikin rayuwata kuma kada ka sake shigo min office is better for you to stay a side.
"Uhmm HAMRA da an ganki za a ɗauka ke wata wayayya ce amma kuma da an bincika za a famin ci duhun kai gare ki, meyasa ba zaki bari na shigo cikin rayuwar ki ba na wani lokaci kinga za...
Tsawa daka masa cikin ɓacin rai ta ce
Mahmoud, get out. I said get out, tun kan naya maka rashin mutunci ka fita harka ta, wlh hawainiyar ka ta kiyayi ramata and this should be the last time da zaka shigo min office.
Kafeta ya yi da jajayen idanuwan shi, yana kallon ta yana kuma sakar mata da murmushi tare da kurawa coca cola shape nata idanun ba abin da yake muraɗi irin jikin ta, cikin sanyin murya ya ce
"This is the beginning, yanzu ma na fara, kuma ban taɓa neman abu na rasa ba dan haka ina da tabbacin cewa sai na biya bukata dake, ki ka baiwa wasu gajoji ma ballantana handsome iri na, wanda mata ke mararin so amma nake kin kulasu shine ni zaki wulakanta to ki sani shi saurayin ki ma mun kaishi ƙasa balle ke da ki ke mace, ni zuba ido ki gani"
Yana gama faɗin haka ya yi ƙofar fita cikin ɓacin rai da tashin hankali ta ce
Kun cika marasa imani, sai Allah ya saka mashi akan zaluncin da ku kayi mishi, amma kuma sai dai kun manta akwai Ubangiji kuma ya fiku shi zai ƙwato mashi hakkin shi. Sannan kasani ni Hamrah na fi karfin ka nesa ba kusa ba kuma ba zaka taɓa cin galaba a kai na ba, it will be the last not the beginning.
Murmushi ya juyo ya sakar mata irin na zancen ki ke so, sannan ya fice, ta daki teburin dake kusa da ita zuciyar ta nayi mata raɗaɗi, wannan wacce iyar rayuwa ce, meyasa duk inda take ake samun matsala, meyasa bata samun farin ciki sai bakin ciki, to yaushe zata jita cikin farin ciki kamar yadda kowa ke yi?. Ta sauke numfashi tare da rumtse idanuwanta wani tunani ne ya faɗo mata akan to ta bar wannan aikin mana, sai kuma ta sake sauya tunanin da cewa in kuma ta bari me zata yi, zaman gidan da Ammie bata so kuma tayi ta tunani ko kuma fita shan iska waje ƴan unguwarsu su sami abin faɗa a hankali ta furta
Nothing will happen in shaa Allahu.
Ganin time yaja yasa ta sauke nauyin ajiyar zuciya ciki sanyin jiki ta kammala shirya ko manta ta fito sbd tafiya gida ta tadda duk office na su a kulle ta fice ta iso bakin titi ta tari ɗan sahu ya kawo ta layin unguwar su, ta sauka tare da takowa zuwa cikin layin, jin tsayuwar mota tayi an parker ta sannan aka fito bata kawo komai cikin ranta ba, ta cigaba da tafiyar ta.....
"Assalamu alaikum"
Kamar ba zata juyo ba amma dan jin anyi mata sallama yasa ta ɗan juyo tare da amsawa ganin babban mutum ne kuma sanye yake da tufafi ta mutunci yasa ta ɗan saki ranta ta furta
Amin wa alaikassalam.
"Tambaya nake son yi miki in dai babu damuwa"
Ta ɗago tana kare masa kallo cike da mamaki, yana da tsawo sannan shi ba baki cen ba yayi shiga ta babbar riga wacce ake kira da gare, da kuma hula, shaddar dark green ce, ta sauke numfashi tare da cewa
To ina jin ka Allah yasa na sani.
Ya sauke numfashi da yasa ta sake ɗagowa ta kalle shi, ganin haka ya ce
Ba ƙone ni sauka ta kenan daga airport nayo nan, wani gida nake nema gidan Alay SHAREEF wani ɗan siyasa mai neman takar house of reps, to na shigo ne kuma nake ta tantama kamar ba wannan ne layin ba, shine ganin ki yasa na ce da driver ya tsaya na tambaye ki"
Ta sauke numfashi ta juyo tana karewa layin su kallo ganin ga majalisu ga kuma shaguna a buɗe ana ta siyyayya bai tambayi kowa ba sai ita da mamaki ta sake juyowa tana kallon shi, dressing nashi sak na garin Maiduguri amma kuma baya shige ko kama da mutanen nan da alamu yarene, to meyasa ya zaɓi da ita yake son tambaya.....
Ajiyar zuciya da ya sauke ne yasa ta sudda kai kasa, ya ce
"Menene, kina mamaki ne sbd na tambaye ban tambayi mutan da suke layin ba"
Ta yi saurin ɗagowa tana mamakin ya aka yi yasan abin da take tunani kenan...
"Abin da yasa na tambaye ki shine, bana son shiga cikin mutane sbd wani dalili na, amma da fatan hakan bai bata miki rai ba"
Ta sauke numfashi ta ɗago tare da cewa
Gidan Alay SHAREEF ba a wannan layin yake ba yana layin baya gida na biyar kofa milk color painting jikin gidan coffee brown ne.
"Na gode sosai, kin san yawanci old GRA layin na kama shiyasa kuma ni bako ne ma'ana mata fiyi, da wannan zuwana na uku kenan garin Maiduguri, ina jin labarin karamcin ku ban taɓa yarda ba sai da ki ka nuna min"
This time ta yi murmushi ta ce
Wannan ba komai bane.
Ta juya ta soma tafiya ta ji ya ce
"Ko zan iya sannin sunar mallamar, saboda ko wata rana zamu iya haɗuwa na sake gode miki"
Hamrah na ke.
"Masha Allah, HAMRAH, nice name, i Alhaji Sama'ila by name from Abuja state"
Ta sauke numfashi tare da jinjina kai tayi wucewar ta sbd na mujiya da ƴan majalisan matasa da suka zuba mata shikenan yau da chapter ta za a kare zama, ta iso kofar gida ba tare da ta juyo ba, bata san ko mutum ya tafi ba ko kuma yana tsaye ba sai ta taji horn na mota, ta juyo sai ganin motar Ammar ce ke mata horn ya ɗaga mata hannu alamun ta buɗe masa, ta ce
Kai da wannan motar ta ka one door ka ke min mulki, to baza a buɗe ba.
Dariya ya yi sbd yana jin abin da ta ta ce, wani yaro ne da gudu ya yi cikin gida ya boɗe mashi ya shiga ya yi parking ya fito yana
"Likita kada ki damu da zaran na dawo daga ABGANISTAN za ki ga na siyo dan kareriyar mota"
Uhm Ammar kenan ce maka a kayi da ga dawowa za kayi kuɗi ai sai ka ci kwakwa tukuna.
Ya yi murmushi ya ce
"Ai ni da kafar dama na shiga kin san ina da babban kwali kuma certificate biyu gare ni na nan da kuma na out side kada ki yi mamaki na samu genaral"
Dariya ta yi tana nufo kofar palour tana
Su genaral manya.
Ya yi murmushi ya biyo bayan ta yana
"In shaa Allahu, duk abin da aka ce Allah an gama komai"
To Allah ya sa.
"Ameen"
ta wuce ɗakin Ammie, shi kuma ya wuce dakin shi. Tana shiga ta tadda Daddyn su na zaune ta gaida shi yake tambayar ta wajen aikin su ta ce dashi Alhamdulillah, ya ce
"Kamar na ji tsayuwar motar Ammar"
Eh Daddy ya dawo yana ɗakin shi.
To madalla ya yi kyau, shima yanzu fama yake da jama'a kin san kasuwanci sai an jure saboda har ka ce ta mutane amma kuma yana complain a kan su"
Uhm hakane Daddy sai anyi hakuri, to in ma ba abin UMAR ai harkar jama'a sai an yi hakuri balle kuma customers sai da lallaɓa"
Daddyn su ya yi dariya ya ce
"Wa Ammar ne zai lallaɓa customers ai ko cewa ya ke in dai tsari ka zo yi ka sara ko kuma kayi gaba, baya ɗukan nonsense"
Uhm gashi kuma sun kusa tafiya training.
"Eh na kammala haɗa masa duk abin da zai bukata kuɗin shi ma yana account"
Masha Allah Daddyn mun gode.
Ba damuwa ai....
Ammie ce ta shigo ta zauna Hamra ta gaidata ta amsa sannan ta wuce ɗakin ta.
Faɗawa toilet ta yi ta watsa ruwa sannan ta ɗauro alwala ta fito ta shiryar ta gabatar da sallah magrib tana kan dardumar sallah ta na lazimi aka kira ishai ta tashi ta idar yunwa ta ke ji, ta fito ta shige kitchen yau ko ruwan zafin haɗa tea ɗin ma nata dashi tana kan ɗaura ruwan zafi cikin electric cattle ne AMMAR ya shigo, ta juyo tana duba me zata dafa cikin ƴan mintina ta rasa ya ce
"Likita nima yunwa na ke ji a dafa dani"
Ba tare da ta juyo ba ta ce
To ai abin da zan girka ne ma ban sani ba.
"To ki dafa indomie mana"
Kai baya raina, kuma dole ke sa na ci, bari na duba cikin store ko na samu abin da zai kwanta min a rai sai na dafa shi.
Ta shige cikin store ta duba ganin tayi kwana biyu bata ci macaroni ba yasa ta dauko shi ta dawo dashi nan ta soma haɗashi jollof na shi, ta soma pa_boilling nashi ta zuba shi cikin matsiyaya sbd ruwan jikin ya tsami sannan ta soma haɗa souce ya ɗan ji wuta sannan ta zuba kifi da nama a ciki sannan ta juyi macaroni a kai ta yi ta juya shi komai ya haɗe ta kashe gas tana kammala shi
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 4 Chapter of 19