Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
da suke yi ne ma yasa ta ɗan ji sanyi cikin ranta ko ba komai ta faranta musu, musamman ma Ammie. Tana cikin wannan tunanin ne taji muryar babarsu dake zaune a gefenta ta ce da ita "To mun iso menene kuma abin kin fitowa" A hankali ta sauke numfashi dan ita tayi nesa cikin tunanin zuci bata ma san anayi mata magana ba, ganin an buɗe ƙofar motar da suke cikin ne babarta da kuma Innarta sun fice yasa ta saka kafa ta fito, suna rike da ita har cikin palour nan ko sai guɗa ake ita dai tayi shuru bata ce komai ba, har aka shigar da ita ɗakinta. Kaya kam Masha Allah Daddy yayi mata dan kaf gidansu ta fiso kyaun kaya tun daga na palour, ɗaki zuwa kitchen ba abin da aka saya da farashi mai sauki duk kayan masu sadane. A bakin bed ta zauna tana jin yadda suke yaba gidan suna ta sanyawa Alhaji Sama'ila albarka suna ta musu fatan alkhairi har lokacin tafiyarsu yayi. Nan ko Hamrah sabon kuka ita tama rasa na menene na tafiyarsu ne ko na bakin cikin da take ciki ne da ƙyar Ayshe da Shatu suka yi ta rarrashin ta tayi shuru har suka fice. Ta rabka tagumi a karo na biyu, oh yanzu kuma ko wacce iriyar rayuwa za tayi ita kaɗai a wannan kata faren gidan dan tasan kan ta sanar dasu Daddy sai an dau tsawon wasu watanni dan zuwa wancan lokacin babu sun mance komai hankalin su ya kwanta sai ta sanar dasu. Ta miƙe tsaye tare da yaye gyallen dake jikinta tana bin ɗakin da kallo ganin set na ɗakinta wanda yaji uban kuɗi da kuma kyau sbd ba a Nigeria Daddy ya siya ba order sa akayi a lokacin da za a shigo masa da kayayyakin business na sa. Sauke numfashi tayi gashi anyi mata hidima kuma ace suji wannan mummunar labarin ai dole hankalinsu ya tashi, ta fito ta wuce palour nan ma haka ya matukar haɗuwa da kuma tsaruwa musamman Dining area ya matukar kayatu, ga standard fridge nata haɗaɗɗe da kuma babban plasma. Hawaye ne take ya wanke mata fuskar sai a lokacin taji wani irin kuka ya taho mata nan take ta zube a wajen ta saki kukan tana jujjuya kanta tana kuma tausayawa rayuwarta shikenan ta rabu da farin ciki na har abada kuma ta ɗaukarwa kanta alkawarin babu ita babu aure har aba kawai za tayi ta bautawa Ubangiji in ta kama ma ta zauna a wannan gidan ta karashi rayuwarta..... Jin an taɓata ne yasa ta ɗago a hankali tana sauke idanuwanta kan Ammar dake zaune kusa da ita ya dafata yana girgiza mata kansa alamun ta daina kuka sai dai kuma ina shi kansa ya kasa jurewa nan hawaye suka zubo masa, ji yake da yana da halin ɗaukewa Hamrah damuwar da take ciki da ko ya ɗauke mata ya dawo kansa. Hamrah ganin Ammar na ƙwalla yasa ta tsagaita nata kukan tare da share hawayenta cikin sanyin murya ta ce You have to go back Ammar, dare ya soma yi babu daɗi kana waje kuma... Hannun sa yasa ya riƙe nata da ƙyar ya buɗe baki yayi magana dan zuciyarsa nayi masa tsuya da raɗaɗi ga kuma tausayinta da yake ji a hankali ya ce "Do you think, i can go and leave you hear?. No, I can't" Uhm Ammar, ni ce ya zame mun dole na zauna ana cos i don't have a choice amma kai ba zayyu ka bar gida ba, kuma nasan Daddy zai nemeka. Ajiyar zuciya ya sauke tare da miƙewa ya ɗauko ledar da ya shigo da ita wacce bata ma san da ita ba ya ajiye gabanta shima ya zauna kamar yadda take zaune bisa ƙafafuwanta ya ce "Kin manta lokacin da muke yara in zaki kwana bikin kawarki in Daddy ya hanaki Ammie kuma ta barki sai mu haɗa plan sai Daddy ya shigo na taimaka miki ta saman garu ki fice a tunanin Daddy kina gida to irinsa nayi yau ma. Ya shigo mun gaisa mu kayiwa juna sai da safe shine na biyo ta baya na hawo garu na wuce nayi miki siyayya dan nasan tun abin da ki ka saka a baki tun safe baki ci komai ba" Murmushi tayi duk da yanayin da take ciki sai taji zuciyarta tayi mata sanyi, tuno mata da rayuwar kuruciyarta da Ammar yayi ne yasa tayi murmushi. Ganin tayi murmushi yasa ya buɗe ledar ya fiddo da roasted fish and chicken with souce ya matso dashi kusa da ita ya buɗe mata fresh milk mai sanyi ya ce "To kici abinci ba a fushi da abinci" Uhm Ammar i don't feel to eat anything at all this time.... "Ki daure ki ce kin cin da ki keyi shine ki ke jin kamar baki da lafiya shi wanda ya jefaki cikin wannan halin fah yana cen yana wantayawarsa ko a jikinsa to ke meyasa zaki tashi hankalinki, ki daure ki" A hankali take yanka tana ci kamar ta amayar take ji amma ta daure gaskiya ne bai kamata ta na fushi da ƙaddararta ba, duk da akwai ciwo amma ya zama dole ta yarda da ƙaddarar da ta sameta. Ba laifi ta ɗan sha fresh milk ta koma da baya ta jingine jinjina kujera tana sauke numfashi... "Ga magungunan ki nan ki sha sai ki kwanta" Da mamaki ta kallesa ita ta ma manta tana kan magangana an ɗaurata akan su shiyasa ma ta mance bata dauka ba to amma yaushe Ammar ya ɗauko bata sani ba. Ba tare da ta ce komai ba ta buɗe su ta haɗiye ya mika mata wani sachet ɗin ya ce tasha ba tare da tasan na menene ba ta karɓa ta haɗiye sa, nan da nan ta fara jin bacci ta miƙe ta shige ciki sabar baccin yayi nawi da kayan jikinta ta faɗa kan bed nan take ta bacci yayi awun gaba da ita. _WASHEGARI_ Buɗe idanuwanta tayi ta ƙurawa roba slink, ganin haske ya gauraye ɗakin yasa tayi mamaki wane irin bacci ne tayi har gari yayi haske bata farka ba, a hankali ta sauke ajiyar zuciya, ta tashi ta zauna tare da karanta addu'ar tashi daga bacci. Tayi miƙa ta sauko daga kan bed ta shige toilet ta haɗa ruwan ɗumi ta watsa sannan ta fito ta shirya cikin doguwar riga ta atamfa ta shimfiɗa dardumar sallah ta gabatar da sallah asubah duk da ta makara amma ta jima tana ta addu'oin. Jin ana nocking kuma tasan Ammar ne sbd babu kowa cikin gidan bayan ita sai shi yasa ta miƙe ta buɗe. Murmushi ya sakar mata ya ce "The breakfast is ready" Sauke numfashi tayi tare da cewa Uhm sai zuwa anjima zanci kaci naka. "Kin manta ne kina kan shan magunguna kuma ba zaiyu ki shasu ba tare da kinci abinci ba, kuma ai ya kamata kimin kara ko dan tashi da wuri da nayi na haɗa miki delicious" Fitowa tayi ta wuce Dining area tare da cewa To muje na gani. Ya bi bayanta, ya matukar sharya Dining table ɗin ya matukar burgeta harda wasu flower's da light a jiki suna kawowa su kuma ɗauke tayi murmushi Allah sarki Ammar a dole yana son ta mance komai. Ta iso ta zauna shima ya iso a nutse ya soma buɗe rufaffun plate ɗin da ya jerosu kan Dining ɗin yana nuna mata, murmushi tayi a kan ko wanne plate yayi decorating da abincin wani aresh ne wani kuma fried yam sai kuma ma ɗauke da souce na hanta. Abu dai kala daban daban kuma ba masu yawa ba, ko wanne ya ɗiba ya zuba mata kan plate dake gabanta ya haɗa mata hot tea mai kauri ya bata sannan ya zuba ma kanta. Ta ɗan dauko spoun tana ci kaɗan kaɗan ba laifi ta ɗan ci ya bata magungunan ta ma tasha sai kuma bacci a nan palour kan kujera ta kwanta tayi bacci ganin haka ya fice ya koma gida. Kusan wunin ranar tayi tane a kwance sbd bacci da ta dinga yi babu tantama Ammar maganin bacci ya bata tasha. Bayan ta idar da sallah la'asar ne taji tsayuwar motar ta leka Ammar ne da wani mutum a tsaye ta fito sbd ganin da sabuwar motar ta wacce Alhaji Sama'ila ya siya mata shi ya taho. Tana nan tsaye ya sallami mutumin ya iso inda take ya ce "Ga mukullin motar ki Daddy ya ce na taho muki dashi yana kuma gaidaku" Uhm Ammar, na bar maka motar in ma saida ita za kayi kaje kayi ni bana sonta. Murmushi yayi ganin ta juya ta shige ciki ba tare da ta karɓi kin motar ba, yabi bayanta, ya taddata zaune kan 1sitter shima ya zauna daga gefe ya ce "Babbar yaya fushi ba naki bane sbd duk wannan abin tafe yake da plan naki dole ki amshi motar kiyi amfani da ita har zuwa lokacin da zaki sanar dasu Daddy komai" Ta sauke numfashi tasa hannu ta amshi key ɗin motar tare da cewa Ya mutan gida?. "Yau duk yawanci sun tafi ina ji zuwa gobe zuwa jibi za a ma watse" Alhamdulillah, kaga komai yana tafi kan tsari. Allah ya kaisu lafiya. "Ameen" Sun jima suna fira kusan magrib ya fice, sai 8:00pm ya dawo ya kawo mata abin taɓawa ta ci suna fira ta shige ciki ta kwanta dan shi yace ba zai tafi gida ya barta ita kaɗai ba. Haka rayuwar Hamrah ta kasance har tsawo sati biyu, sai dai zuwa wannan lokacin ba kullum bane Ammar ke kwana a gidanta, sbd kada Daddy ya fahimci wani abin. Hankalin Hamrah ya fara dawowa jikinta ta ɗan sami nutsuwa Zeenat da Ayshe suna kawo mata wuni su koma bata taɓa barin sun fahimci komai ba, haka bestie nta Shatu ita ma tana kawo mata wuni su sha firar su da ƙyar suke rabuwa. _After 1month_ Cikin sauri ta fito ta faɗa cikin motar ta tadata ta fito tayi parking a waje ta koma ta rufe gate ɗin dan har zuwa wannan lokacin basu nemi gateman ba tun bayan sallamar wanda suka tadda yana gadin wajen, sunyi hakanne sbd kada sirrin abin da suke ɓoyewa ya tonu, ta shige motar ta figeta cikin gudu ta hau titi kai tsaye sai Na kowa hospital tayi parking a farfajiyar Hospital ɗin ta shige ciki bata ma ganin gabanta duk ta fita hayyacinta. Tana isowa ta shige cikin office ɗin da zata gamu da ko wacce iriyar likitace, tana shiga ta tadda Doctor da ta duba ta a hotel na washegarin aurenta cikin sauke numfashi ta iso kusa da ita suka gaisa bata shaida Hamrah ba sai da Hamrah tayi mata kwatankwacin wancan ranar ta ganeta cikin sanyin murya ta ce da Hamrah "Kina bukatar wani abu ne?" Ganin office ɗin da mutane ta ce Eh likita amma a sirrance. Ta sauke numfashi suka shige wani karamin room dake cikin office ɗin, Hamrah cikin kuka ta ce Nayi farin ciki da yasa dake na haɗu a yau kuma nasan kin san duk abin da ya faru dani a hotel kwanakin baya, to yanzun ma kusan matsalar tare suke, likita a takaice dai ina ɗauke da ciki sakamakon abin da ya faru, bana son cikin wallahi bana so ba haife shege ko shegiya dan Allah ki rabani dashi. Sosai Hamrah ke kuka kamar ranta zai fita, da ƙyar likitar ta iya rarrashinta ta, ta ce "Abin da ki ke shirin aiwatar wa babu kyau shawarar dan zan baki ita ce ki yi hakuri ki amshi babyn maybe alkhairi ne amma zubda cikin hatsari ne ga rayuwar ki kuma zaki aikata laifi, sannan menene laifin abin da ke cikin shi bai san komai ba kada ki sanya shi cikin abin da ubansa ya aikata miki" Har kasa Hamrah ta duka tana kuka ta haɗe hannayenta biyu ta ce Ni da ki ke gani nima likitace kuma kwararriya nasan illar yin hakan amma kuma hakan shine hanya mafi sauki daga gareni ki taimaka ki zubar barin shi tamkar ruguza rayuwata ce, yau nake fatan komawa gida na sanar dasu abin da ya sameni a ranar bikina na, daga kuma rana irinta yau na sage gina sabon rayuwa sai kuma wannan abin ya sameni dan Allah likita ki zubar min shi..... Kuka take yi kanta na ƙasa, jin shuru da likita tayi ne yasa ta ɗago tana hawaye idanuwanta suka sauka kan Ammar dake zaune a gabanta ya kura mata idanuwansa da suka kaɗa su kayi jajir, baya tayi cikin sauri tana mamakin yaushe ya iso nan ɗin kuma ya akayi yasan tayo nan ɗin?. "Ba zaki zubar da cikin ba Hamrah yin hakan kuskure ne ya zama dole ki haifeshi, the baby was innocent bai san komai ba" Miƙewa tsaye tayi ta nuna shi da yatsa kamar wata zararriya ta ce Bai zama min dole na haifi cikin shege ba Ammar dole ne a fidda min shi ko ana so ko ba aso bazan taɓa haɗa jini da azzalumi ba kuma fasuki ba, in kuma aka dage sai na haifeshi to zan kashe kaina kowa ma ya huta. Hankalin Ammar ya matukar tashi tunda suka taso shi da ita bai taɓa ganin ta shiga cikin ɓacin rai ba irin wannan, duk da yasani da ciwo to amma ba zai bari ta zubda ba. Ya miƙe tsaye shima tare da kai hannu zai riƙe ta sbd ganin kamar nema take ta faɗi ƙasa tasa hannu ta bugesa. Ajiyar zuciya yayi ya ce "Hamrah everything is a matter of time, we should be more patient. If Allah wills, everything will be right. All things must come to an end. Kamar yadda ki ka jure zama da agida na wani lokaci ki kayi hukuri ki ka kau da kai har Allah ya nufa ki kayi aure washegarin bikinki mijinki ya gudu ya barki kika jure hakan to haka ma wannan karon hakuri za kiyi ki kuma jure ki amshi kyautar da Ubangiji ya baki da hannu bibbiyu, dayawa na neman hakan basu samu ba. Kuma bamu sani ba ko da wane irin alkhairi wannan babyn zai zo mana so, Please Hamrah accept it as your destiny" A hankali ta sulale kasa ta zauna kamar wacce aka cirewa laka, hawaye na ci gaba da zubo mata, ta rumtse idanuwanta a hankali take furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Abin ya fara fin karfinta, kuma ya wuce tunaninta tabbas Allah ne mai iyawa bawa ba ya iyawa sai da iyawar Ubangiji, a tunaninta a yau ranar farin ciki ne dan tana murna zata koma gida gaban iyayenta bayan rabuwa da tayi dasu na tsawon wata ɗaya a matsayin tana gidan mijinta ashe abin ba haka bane, kana naka Allah na nashi nasa ne kuma shine dai-dai. To yanzu ya za tayi?. Sunkuyowa Ammar yayi tare da share mata hawayen dake fuskarta cikin tausayawa ya tausasa murya ya ce Tashi mu koma gida. Rike hannunta yayi suka fito a tare har cikin motarta ya sakata ya zaunar da ita a mazaunin gaba, ya koma ya sanyawa motarsa key a inda ya bakata sannan ya dawo shige cikin motarta ya zauna a mazaunin driver yaja ya fice daga cikin Hospital ɗin suka dawo gida yayi parking ya taimaka mata suka fito, ya zaunar da ita a palour. Ita kam ta koma mutum butumi sai ido babu bakin magana ji take sam kamar ba ita bace. Ammar ya fice babu jimawa ya dawo da alamun ba da motarta ya fita ba amma jin shigowar motar yasa ta tabbatar da cewa Hospital ya koma ya ɗauko tasa motar. Shigowa cikin palourn yayi yanda ya barta zaune haka ya taddata, hawaye da bin gefen fuskar ya zauna kusa da ita cikin kulawa ya ce "Ko kina ganin yau mu sanar dasu Daddy abin da ke faruwa in yaso musan irin matakin da zasu ɗauka" A'a. Kawai abin da ta ce. Ya sauke numfashi ganin yanayin da take ciki yasa ya kyaleta ya koma kan 3setter ya kwanta tare da lumshe idanuwansa. Ya akayi kasan Hospital na tafi?. A hankali ya buɗe idanuwansa ya juyo ya kalleta ya ce Nazo ne da niyyar ɗaukanki na kaiki gida kamar yadda mu kayi sbd sanar da iyayenmu gaskiya akan aurenki da Alhaji Sama'ila shine naga kin figi motar kin fice daga layin a daidai lokacin kuma ni ina ƙoƙarin shigowa nayi mamaki ma da baki ganni ba, ganin haka yasa na fahimci ba lafiya ba nabi bayanki sai dai abin da ya bani mamaki shine shigar ki cikin Hospital ɗin me ya kawo ki, kawai nayi parking na biyo ki ciki shine na tadda abinda ki ke sanar da likitar" Ajiyar zuciya tayi a hankali ta sake cewa To ya zanyi da abin da ke cikina shin bayan na haifeshi ina zan kaishi rikesa zanyi ko kuma zan nemo ubansa?. Tashi yayi ya zauna ya kura mata idanuwa na wasu lokuta, sauke numfashi yayi a hankali ya ce "Ai ba zamu baiwa Alhaji Sama'ila abin da zaki haifan ba ya zama namu mu zamu rikesa ko riketa har zuwa lokacin da Ubangiji ya kayyade mana, kuma nasan iyayenmu zasu amshi abin da ƴarsu ta haifa..... Ni bani son abin da zan haifa, dole ne in na haihu a kaiwa ubansa. "A ina kenan?" Abuja. Murmushi mai ciwo Ammar yayi ya ce "Kina da tabbacin a Abujan yake ina da tantama ma bashi da asali. Ni na amince in kin haifa ki bani babyn zan zame masa uwa da uba in kuma lokacin Allah ya ƙaddara nayi aure sai na tafi da babyn gidana mu renesa" A hankali ta ɗago ta kallesa da jajayen idanuwanta ta ce Na mallaka maka tun yanzu ko na mutu ko kuma ina raye na baka babyn ni kuma bayan na haihu, I'll to go far na fara sabon rayuwa. Comments and share*MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 49 & 50 _end of book 1_ *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _MIKIYA mai hangen nesa, mai kuma farin jini wajen al'umma, mai ɗauke da tarin marubuta hazikai kuma fasahai. Kungiyar masu haɗin kai da fahimtar juna. Godiya ban girma ga shuwagabannin kungiyar da kuma members ɗin ta kun nuna min kauna wajen sharing, shawara da kuma ƙwarin gwiwa, i dey with you till.....🤣 You showed me love 💕😘. Much love for you._ _Bana taɓa mantawa dake habibty Bilkisu S fari. Much love for you 😘_ __________ Laulayi sosai cikin ya sanya mata bata iya cin koma sai amai da tofar da yawu duk ta fita hayyacinta, ta rame ga yawan tunani da take yi, bata iya komai daga kwanciya sai zama duk ayyukan gidan Ammar ke yinsa. Kwance take a wannan lokacin ma idanuwanta biyu tana kallon jikin garu kamar me nazarin painting dake jikin mai ɗauke da kyalli² lokaci zuwa lokaci take sauke numfashi. A hankali ya turo kofar ɗakin ya shigo ya zauna kusa da ita ya kura mata idanuwa cikin tausayawa yayi mata magana "Hamrah ki tashi ki sanya abu a cikin ki rashin cin abinci zai haifar miki matsala tare da abinda ke cikin ki, ko bakyaso ki daure ki ci Please" Kamar zayyi kuka yake rarrashinta, a hankali ta yunƙura ta tashi ta zauna da ƙyar ta kallesa kuma sai ta kau da kai gefe, saukowa tayi ta nufi toilet tana shiga kuma sai kwara amai tun tana iya yinsa har ta gagara sbd babu komai cikin cikinta daman ruwa ne gashi kuma ta amayar, nan take ta faɗi sumammiya. Cikin hanzari Ammar ya iso cikin toilet ɗin sbd jin karan faduwar da tayi yasa ya taso dan ganin abin da ke faruwa. Ganin ta kwance a ƙasa yasa ya dinga jijjigata yana tashin ta amma ko motsi bata yi ba yasa ya ɗauke ta chak kamar wata jiririya yayi waje da ita ya sanyata cikin mota ya kwantar da ita a sit na baya, sannan ya wuce ya buɗe gate ya dawo ya shiga ya tada motar ya tukata zuwa kofa yayi parking daga gefe ya fito ya rufe gate ɗin sannan ya koma cikin motar ya tada ta kai tsaye sai Hospital. Da taimakon Allah dana likitoci Hamrah ta farfaɗo aka sanya mata drip bata san inda take ba sai da ta kai kwanaki uku a hospital, ta farka taga ƴan gidansu a kanta binsu take da kallo su kuma suna mata ya jiki, da kai take iya amsa musu, jikin dai tana jin sa da sauke da taimakon karin ruwan da akayi mata. Sai da tayi 1week a hospital sannan aka bata sallama sai dai wannan karon Ammar sam yaki goya mata baya akan ta koma gidanta duk da bai sanar dasu komai ba amma ya ce mijinta baya nan dan haka a tafi da ita main house ta ɗan huta. Haka ko akayi gida aka tafi da ita sai da tayi 3 weeks sannan ta dawo gidanta. Zuwa wannan lokacin kam jikin dama² dan tana iya komai da kanta Ammar ma ya fara fita office nashi na soja sbd kwazonsa tashi guda aka basa matsayi, yakan zuwa da safe sai ya fice sai kuma dare yazo ya ganta wani lokacin ya kwana wani lokacin kuma ya tafi. ************************ Cikin sauri akayi labour room da ita duk hankalin su a tashe sbd bleeding ɗin da take yi, ganin haihuwa ce ta kamata kadan² yasa likitoci mai da hankali akanta sai da aka dau 1hour 30munute sannan ta haifu baby girl nan ko murna da farin ciki a gun ƴan'uwanta ba a magana, ita dai tun da taji babyn ta faɗo ta kama bacci bata san wainar da ake toyawa sai da ta farka ta ganta a side room an shiryata saf kamar ba mai jego ba, ita kaɗai a ɗakin shuru babu motsin kowa. Jin motsin turo ƙofar ne yasa ta ɗan juya ta kalli ƙofar. Amma ta gani a tsaye hannunsa rike da handle door kamar bazai ƙaraso ba a tunanin sa bacci take, ganin idanunta biyu yasa ya ƙaraso ya zauna kan kujerar dake kusa da bed ɗin ya sakar mata da murmushi a hankali yana ci gaba da kallonta sauke numfashi tayi a hankali ta ce Did you tell them the secret?. Kai ya girgiza mata alamun a'a, sannan ya sauke ajiyar zuciya a hankali ya ce "No. I won't, until you agree" Sauke numfashi tayi ta maida idanuwanta ta rufe.... "The baby is pretty like you" A hankali ta buɗe idanuwanta ta kallesa, sai kuma ƙirjinta ya bada rasss, to yanzu kuma ta haihu ko wacce iriyar rayuwa zata sake sintar kanta cikin ta dan wannan karon ba zata iya ɓoye komai ba zata bayyanawa iyayenta komai sbd itama ta samu taji sanyi cikin ranta ta rabu da fargaba, bata ce dashi komai ba shima ganin bata son yin magana yasa yayi shuru har Ammie ta shigo da babyn tana cewa "Lah ashe uwar taki ma ta farka, to taho meje ta baki mamman naki kisha" Hamrah dake kwance ta kalli Ammie dake ƙoƙarin ƙarasowa da babyn, ta sauke numfashi tare da tashi ta ɗan kishingiɗe da jikin bed ɗin, Ammie ta mika mata babyn tana "ki bata tasha yunwa sai addabar take tun da ta taho duniya bata sha nono na sai ruwan zamzam da dabino" Sudda kai ƙasa tayi tasa hannu ta amshi yarinyar ta kura mata idanuwa tana kallon yadda ta sanya babban yatsar ta cikin bakinta tana sosa alamun yunwa take ji, fara ce kal wanke hannu ka taɓa duk da jaririya ce kyawunta bai buya ba wasu kwantantun gashi ne saman goshinta, idanuwanta farare tas da su roung face gareta hanci ɗil dashi da ɗan ƙaramin bakinta mai ɗauke da jan laɓɓe, sai wusili wusili take da idanu. A hankali Hamrah ta sauke numfashi tana jin tausayin yarinyar na shigar ta sosai tana jin ƙaunarta... "Oh ni yaran zamani, ki bata tasha shine ki ka zuba mata idanu yunwa fa take ji" Cike da kunya Hamrah ta buɗe rigarta ta fidda nono ta sanyawa yarinyar a baki nan da nan ta kama sosa tana sha, a hankali ta ɗaura hannunta saman kan yarinyar tana shafa gashin kanta mai laushi da tsantsi baki wuluk dashi. Jin ajiyar zuciya da Ammar yayi ne yasa ta ɗago ta kallesa kura musu idanuwana yayi yana kallon su ko kiftasu baya yi, sun matukar burgesa mamaki yake Hamrah na feeding baby lallai rayuwa kenen. Harararsa tayi da ya sanya ya saki murmushin da ya fito da

Chapter 18 of 19