ta ambaci sunanta taga tashin hankali a tare da shi, ta sauke numfashi ta faɗa kan bed, tare da rumtse idanuwanta ta jima tana bacci sai yamma lis ta shirya ta wuce wajen aiki.
Zaune suke ana ta hayaniyar gidan bikin suna iya danginsu ma kaɗai sun cika gidan balle kuma ace da sauran ƴan uwa da ake zumunci, kasancewar ba wani aiki mai yawa suke yi ba sbd contract na komai sun bada ayi musu. Hamrah ta fito daga ɗakin mai jego ta nufo inda sauran ƴan uwan su ke zaune suna yanka cabeji da dai ƙananun abin da ba a rasa ba. Sanye ta ke da riga da skart ta farin lace tayi normal ɗauri tayi matukar kyau, komanta fari ne hatta sarka da ɗankenne da ta sanya masu duwatsu suma dare ne, plat shoe ɗinma fari sai kuma ɗan karamin jaka dake hannunta ma fari ta zauna kusa da Ayshe tare da ɗauro wuka tana kankare carrots tana gaisawa da ƴan uwanta da suka shigo, Maryama ma ta fito ta zauna Aunty maimuna ta kalli Hamrah tare da cewa
"To Hamrah sai a dage a fidda miji abar zaɓe tunda kinga ƙannenki girma ya fara kamasu Ayshe ta zama uwar gida Zeenat kuma ta fara tara yara Maryama ma a ɗakinta Ammar ma yana dawowa zamu aurar dashi, kinga zaki rage ke kaɗai ce"
Hamrah batayi magana ba sai ma murmushi da tayi taci gaba da kankare carrots ɗin, ba wannan bane karon farko da take fuskantar irin wannan daga familyn su dan haka baya damunta. Maryama ce tayi caraf ta ce
"To da wani auren ba gwamma ta shekara dubu a gidan su ba, wasu da su suke ci da kansu da kuma ƴaƴansu kai harda mijin ma, wlh ba zan taɓa ci da gardi ba sai dai ko kasannayi"
Sittt.... Aunty maimuna tayi tasan da ita take mara kunya kawai Indai Maryama ce zata faɗi fiye da hakan, dan kaf gidan itace zakka...
"Ke Maryama babu son rashin kunya da fusara dan tayi wa yayar ki magana akan ta fidda miji itama ta samu rahamar Ubangiji ta dalilin aure aɗaga gawarta sama tayi daraja shine ki ke faɗin haka to kul ki iya bakin ki, ai takai shine take faɗa mata haka me yafi daɗi a duniya bayan aure.
Cewar wata daga cikin dangin Ammie, caraf ko Maryama ta turo baki ta ce
"Oh ni Maryama har dasu kaza a da cin danko in ana magana ta aure da masu jini a wuya ake yi, ba wai waɗanda mazajen su suke tatil da giya ba su lakaɗa musu na jaki kuma su zauna ba, da irin wannan auren ai gwamma batayi saba"
Sittt......... Akayi bakin kowa ya mutu suna kallon Maryama cikin ɓacin rai da ta kuncewa Innarta zani a kasuwa kowa kuma yasan halin da ta ke ciki da ta sani batayi magana ba......
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 27 & 28
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
______Kallon shi ta tsaya yi sbd yanda ya wani firgita da jin zancen yana wani waro idanuwa waje, ta yi murmushi, tana mamakin meyasa Ammar yaƙi jinin Alhaji Sama'ila ne, mutumin bashi da makusa da farko tana jin fargaba a kanshi amma kuma tunda ya faɗa mata wanene shi taji sanyi a ranta, zata aure shi ko dan hankalin Ammie ya kwanta ta daina fushin da ta keyi da ita duk da ba laifin ta bane ƙaddararta ce jinkirin aure, amma tunda Ubangiji ya nufa ta samu mijin aure zata rufawa kanta asiri ta zauna dashi.....
"Wai kina nufin tsohon nan za ki aura da gaske, look Hamrah kada kiyi gaggawar yanke hukunci ki nutsu ki sake fahimtar shi kada kalaman bakin shi su yaudareki"
Ammar munyi magana ya faɗamin cewa yana da mata da kuma yara 7 shi ɗan siyasa ne kuma ita ke kawoshi Maiduguri so no need na sake damun kaina akan sai na sake tambayar shi wannan bazayyi making sense ba, kuma ga shi babban mutum ne.
Sauke numfashi Ammar ya yi ya ce
"Bana ƙinshi ni kawai na fi son ki aure mutumin kirki sannan wanda shekarun shi bai ja ba, amma kuma tunda kin ce ya yi magana da Daddyn mu that's okay, to amma kwa bari ai na dawo daga training ko?"
Eh to maybe.
Ya haɗe fuska ya ce
"What do you mean by maybe kamar ma ɗauki ki ke"
Murmushi ta yi ta ce
Ai ya zama dole ƙanina ya halarci taron bikina, za a jira ka dawo.
"Yanzu naji batu, to me za ki bani na tafiya?"
To mai kuwa zan baka da ya wuce na yi maka addu'ar Allah ya kai ku lafiya ya kuma bada sa'a a bisa abinda aka je nema, a kula da ibada ayi riƙo da gaskiya ban da kanza dabi'a ko tarbiyya.
Ya yi murmushi ya ce
"Na gode babbar yaya amma kuma amin kyauta ta musamman "
Ok, na fahimce ka kace na haɗa maka snacks kamar yadda na keyi in dai za kayi tafiya.
Dariya ya yi ya ce
"Yes, kin gano ashe kin san kuwa daɗin cake ɗin ki na keji kuma yana ɗauke min yunwa"
To zan yi maka sbd kace dani babbar yaya amma badan haka ba, bazan yi ba.
Sosai ya ke mata dariya wato dai wannan son girman ba zai taɓa ƙanzawa ba amma yana son ganin ranar da zata dauki girman ta bada ta dauki ƙanƙanta.
Bayan sun kammala shirya kayan ne suka wuce kitchen ta shiga shirya masa caka, donot greba sun jima suna yi sannan ta samu ta kammala dare ya yi sosai gashi duk sun gaji kuma tana so ta tashi da wuri ta yi mashi rakiya airport sannan ta wuce office a adaddafe ta shige dakinta ta kwanta bayan ta kammala shirya mashi ta bashi ya wuce dashi ɗakin sa.
_WASHEGARI_
Da ƙyar ta iya tashi daga bacci ta watsa ruwa tare da ɗauro alwala ta idar bayan ta shirya ne ta fito ta tadda Ammar, Daddy da Ammie suna zaune a palour suna yi masa nasiha ta gaidasu, sannan suka fito ita da shi da kuma Daddy a tare suka yi mashi rakiya airport Daddy ke driving nasu. Bayan ya yi parking a parking space na airport ne ya fito tare da ce musu yana zuwa ta ɗau waya ta kira Dr Aliyu cikin rawar jiki ya ɗauka ta sanar dashi bazata iso da wuri ba duk abin da ya dace ya yi, su kayi sallama. Ammar ya kalli yayarshi tare da cewa
"Na gode yaya Hamrah da ƙoƙarin ki na jiya i really appreciate it, kuma in dai ina dasu to bana zama da yunwa. Zanyi kewarka ku"
Murmushi ta yi ta ce
Muma zamuyi kewarka, ka kula kaji banda soyayya da masu jan kunne.
Dariya ya yi sosai ya ce
"Ni abin da ya kaini shi zanyi ba wata sabuwar alaƙa ba, burina shine na yi nasara"
To Allah ya dafa muku.
"Ameen"
Suna cikin fira Daddy yazo Ammar ya fito ya wuce suna gani har jirgin ya tashi sama sannan suka juyo Daddy ya sauketa wajen aiki sannan ya wuce nashi office ɗin yau ba Ammar dake taimaka mash.
Kai tsaye office nata ta shige ta fidda duk abin da zata buƙata ta sanya white coat nata tunanin ta baki ɗaya yana general ward, turo ƙofar Dr Aliyu ya yi tare da sallama ya shigo ta juyo ta kallesa ta ce
Dr Aliyu sannu da kokari, na yi rakiya ne da safen nan.
"Lah ai babu komai Dr Hamrah, na kammala duba patients ɗin ma sai dai ko zuwa anjima sai ki sake duba su"
Ok na gode.
Ya fice yana jin daɗi, Hamrah na da saurin fushi kuma bata da riƙo gashi duk abin da ya yi mata ta yafe masa, sai ya ji jikin shi ya yi sanyi. Tunda Dr Aliyu ya ce ya kammala duba patients ɗin sai ta miƙe kan resting chair sbd hutawa gashi daren jiya bata kwanta da wuri ba kuma ta tashi da wuri. Baccin 10 minute ta duk jikinta yayi mata nawi bata sami isasshen bacci ba a hankali ta tashi ta zauna sai kuma taja da baya ta haɗe da jikin kujera tare da waro idanuwa alamun mamaki da kuma tunanin me yake nufi da yi mata sanɗa, lallai wannan mutumin yana wuce iyakar shi, ba laifin shi bane amma za tayiwa tufkar hanci, ta nuna shi da yatsa ta ce
Kai Dr Mahmoud abin naka har yakai kashigo sbd ina bacci, ka aiwatar da nufin ka a kaina to ƙaryarka ta ci ƙarya, to bari na takaita maka kada kaga kana kwalɓewa ana yi maka uzuri wai baka cikin hayyacinka to kasani ba ƙwaya ka ke haɗiyaba ko durum na giya ka ke sha to wallahi baka isa kaci galaba a kaina, tashi ka fice min tun kan na tara maka ma'aikatan cikin wannan Hospital ɗin.
Ta ƙarashe maganar cikin ɓacin rai da kuma tsantsan tsana da kuma ƙyamatar shi, sauke numfashi ya yi tare da kura mata idanuwan shi ya ce
"Ba abin da nasha I'm in my normal sense, ni bana shaye shaye.....
Ka fice min daga office Dr Mahmoud or should I call OG and tell him that, you always interrupting me.
Jin haka yasa ya miƙe sbd yasan zata aikata, ya fice. Ta sauke numfashi tare da lumshe idanuwa ta buɗe ta miƙe ta shige toilet ta ɗaura alwala ta idar da sallah azahar sannan ta wuce general ward.
Bayan ta tashi daga wajen aiki ta dawo gida tana shiga kuma sai jikinta yayi sanyi da ta tuna Ammar bayanan, ɗakin Ammie ta shige ta gaidata sannan ta wuce ɗakinta ta faɗa kan bed ta ɗan miƙe tana washh sbd gajiya, ta ɗan jima a kwance sannan ta tashi ta faɗa toilet ta watsa ruwa ta fito ta shirya ta gabatar da sallah magrib tana kan dardumar sallah har aka kira ishai sannan ta miƙe ta hau kan bed sbd kaɗaici ta hau online ta yi kwana biyu batayi chatting ba, tana hawa ko message ta ko ina tana reply a nutse tazo kan na Ammar video ya tura mata tun da suka shiga ABGANISTAN har zuwa masaukinsu tana ta dariyar abin daga bisani ta kwanta bacci.
Washegari kasancewar bata da morning duty sai night duty yasa ta jima tana baccin safe sai kusa 11:00am ta tashi ta shirya ta fito kitchen ta nufa, breakfast mai sauki ta haɗa ta fito ta ci sannan ta wuce ɗakin Ammie ta shaida mata cewa zataje gidan su Shatu, ta fito ta wuce sai dai kuma wayam babu kowa gidan ma da alamun babu kaya a ciki, ta fito ta komo gida tana mamakin abin ko gate man ma bayanan, tana isowa gida ta zauna a ƙarƙashin bishiyar darbejiya ta kishingiɗe jikinta duk sai taji kaɗaici ba shatu babu Ammar ta ɗau waya ta kira number ta bugu ɗaya ta ɗauka tare da cewa
"Bestie kina wajen aiki ne ko kina gida"
Ina gida Shatu yanzun nan ma daga gidanku na taho.
Cewar Hamrah tana sauke numfashi.
"Gani shigowa"
To.
Sukai sallama, babu jimawa sai gata ta iso Hamrah ta shige ciki ta ɗauko darduma suka zauna ta ce
Ƙawata meyafaru ne naje gidanku babu kowa.
"Uhmm ƙawata ki bari, muna nan muna ta rigima da mijin Mommy na, yanzu haka muna zaune ne a asalin gidan mahaifina"
Ƙawata kin fara bani labarin bamu ƙarashe ba ki ka tafi to ki ƙarashe mun na fahimci komai duk ina cikin damuwa hankalina yaƙi kwanciya.
"Haka ne ban ƙarashe miki ba a ranar sbd ƙirana da lawyer ya yi. A wancan ranar da Mommyna taga jini a guest House har ta tambayi Daddy na sai ya bata amsa cikin tsoro da kuma tashin hankali da firgici dan shi a tunanin shi ya goge komai jin ta ambaci jini yasa ya ƙiɗime da ƙyar ya tattaro nutsuwar sa ya ce
"Jini kuma hajjiya, abu ne ya zube mai kama da haka nasa a goge amma kuma basu gyara mai kyau ba"
Ta sauke numfashi sosai ta ke karewa palour kallo sannan ta ce
"To na wuce sai na dawo"
Har ta kusa isowa ƙofar fita kuma sai ta tsaya sbd ƙarar bugun ƙofar da taji ana yi, ta juyo ta kalleshi sai taga duk ya haɗa gumi, ni kuma ganin haka yasa naci gaba da bugawa da gwiwata, cike da mamaki ta sake dawowa sakiyar palour ta ce
"Alhaji kamar ina jin ana buga ƙofar cen, shin wayene a wajen?"
"Babu komai a cikin store ɗin kayane da kuma ɓeraye"
Zuba masa idanuwana tayi tana karantar shi ya ganin uban gumin da ya haɗa da kuma yadda jikinshi yake ɓari yasa ta fara fahimtar akwai abin da yake ɓoye mata, takowa ta yi zuwa inda yake tsaye ta ce
"Alhaji lafiya mai yasa you are so gulty, meyake faruwa ne...
Jin bugun ƙofar da na keyi yayi yawa yasa, ta iso bakin ƙofar tare da saka hannu ta murɗa handle door amma kuma sai taji ta a rufe, ta juyo ta kalleshi tare da cewa
"Ina key na wannan ɗakin?"
Zuwa wannan lokacin Alhaji ya fara ruɗewa cikin tashin hankali ya iso inda ta ke ta ce
"Na faɗa miki babu kowa a ciki, tunda wucewa za kiyi to ki tafi mana kada ki makara"
"Alhaji akwai abin da ka ke ɓoyemin shin budurwa ce a ciki ka ke ɓoyemin baka so na gani ko kuma wani abin ne na daban"
"Babu dukkan abin da ki ke tunani....
Na sake buga ƙofar tare da cewa
Ummmmm.
Alamun ina neman taimako, cikin ɓacin rai ta ce
Alamun jin kamar muryar mace da taji ne yasa tace
"Da alamun macece, ka buɗe naga wacece a ciki"
Duk ya ƙiɗime ta shige ciki ya ɗauko key ya fito sai dai ganinta riƙe da jakata tana kare mata kallo, ina kallon sa ta wannan ramin ya dafe kanshi tare da jujjuya sa cikin tashin hankali. Mommy ta iso inda yake tsaye ta nuna mashi jakar tare da cewa
"Wannan jakar Shatu ce, ina Shatu, ina ta ke?. Shin itace a cikin nan ɗin"
Bai bata amsa ba, ya sauke numfashi duk ya gigice, tasa hannu ta warci key ɗin ta wuce ƙofar kai tsaye ta buɗe da ɗauri da kuma jinin da ya gama ɓata min jiki na faɗo jikinta, baifi 2mint ba da faɗawa jikinta na tsume ban tashi fargawa ba na ganni kwance kan bed na hospital mommy na a kusa dani tana ganin na farka ta fashe da matsanancin kuka ta kasa magana, ni kam kukan ma na kasayi sai bin ɗakin da kallo nake. Nurse ce ta shigo ta tadda kukan da Mommy ta keyi, nan ta fidda ta waje sbd kada hankalin na ya tashi kuma jikin babu daɗi duk da ba wata rashin lafiya nayi ba amma a wuni ɗaya na kanza kamar nayi jinyan 1week. Kwanana biyu a hospital aka bamu sallama muka dawo gida na tadda ana fita da kayayyakin mu, na kalli Mommy tare da tambayar ta
Mommy ya naga ana fidda kayayyakin mu ina zamu je?.
Bata kalleni ba kuma bata ce komai ba har aka fidda komai aka zuba su cikin manya manyan motoci na ɗeban kaya ta ce
"To Shatu kama ƙannenki ku shige motar"
Na ce da ita
To mommy.
Na tattara su muna shirin fitowa ne Daddy ya shigo ganin abin da yake faruwa yasa hankalin shi sake tashi ya iso inda muke tsaye ya ce
"Babu inda zaku tafi ku wuce ciki ku zauna....
"Ku fice ku shige motar Shatu, bai isa ya dakatar da ku ba"
Cewar Mommy ranta a matukar ɓace, ya iso inda ta ke zayyi magana ta ce
"Alhaji keep you words sbd baza suyi maka amfani anan ba ka jira zuwanmu court maybe suyi amfani acen amma kuma baka isa ka hana mu tafiya ba"
Tana faɗin haka ta hanyar fita amma yayi saurin shan gabanta ya tare ƙofar fita ya ce
"Na faɗa muku babu inda za kuje, ko kin manta ne da aurena akanki in ki ka fita bada izinina ba ban yafe ba"
Dariya Mommy tayi wanda ya fi kuka ciwo ta ce
"Kacika ɗan ta'addan da baya riƙe tokobi, irinka annubane cikin al'umma zama daku bazai haifar da ɗa mai ido ba rabuwa dakai shine mafi alkhairi a garemu, a tunaninka ban san me kake aikatawa bane to ka sani tun ranar da Shatu ta ɗibi ƙafa tabar wannan gidan zuwa Cameroon na san da akwai dalili, kiyayyar da ta ke nuna maka ma ta sake tabbatar min da akwai wani abun amma kuma bani da hujjar da zan tuhume ka, sannan kuma miyar ƙuɓewar da gangan na wareta daga cikin sauran kulolin na ajiye ta ina jiran zata dawo ne tare da driver ko kuma shi kaɗai zai dawo, ganin shi kaɗai ya dawo yasa zargina ya fara tabbata, na fahimci duk sanda ka ce kana da meeting a guest House to a wannan ranar driver da Shatu dawowarsu na banbanta, sai kuma da shatun ta dawo nake kasa gane kanta. Ganin komai a zahiri yasa na sake tabbatar da zargina shine kake ganin zan zauna dakai a matsayin miji to wlh ba zai taɓa yuwa ba sbd kai ba uba bane gare su ko zan shekara da auren ka a kaina gwamma in zauna dashi ba tare da ina ganin ka ba, ka cuceni ka cuci ƴaƴana bazan taɓa yafe maka ba da ka yaudareni da fuska biyu, dan haka na tafi kuma ina jiran takarda ta nan da kwana biyu in kuma ba haka ba na fito na sanar da duniya irin ɓoyayyen halin ka da danginka da kuma ƴaƴanka na sauran matan su sani"
Tana faɗin haka ta tisamu gaba muka tafi, tun daga wannan lokacin yake ta bibiyarta ta yafe mashi amma ta ƙi da dai yaka ta shirya tsaf zata tona masa asiri shine ya tura mata ta kardan saki ta hannun lawyer na wanda da yayi gardama bai aika ba Court zata makashi. Babban damuwata itace BP Mommy ya tashi sbd wannan abin kullum cikin tunani bata cin abinci duk hankalin mu a tashi yanzu haka dai likita ya ɗaurata kan magani tana sha jikin dai za a ce da sauki"
Sauke numfashi Shatu tayi da ta ƙarashewa Hamrah labarin tare da sake fashewa da kuka, ita kuka Hamrah kuka aka rasa mai rarrashinsu sai suka jiyo muryar Ammie daga bayansu tana cewa
"Kuka ba shine mafita ba, ku cire mazan aure kuyi aure shine mafita kuma wannan ne kaɗai hanyar da zaku tsira da mutuncinku kuma kuyi daraja"
Juyowa sukai suna kallonta lokaci guda cike da mamaki kenan Ammie taji duk abin da suke tattaunawa..........
_________________________
Assalamu alaikum fan's jina da ku kayi shiru 2days banyi Update ba kuma nace daku nasami hutu zan dinga yi on on to yau da gobe na hannun Ubangiji, baƙi nayi sun zo min hutu shiyasa bana na samun time na zauna nayi typing amma in shaa Allahu zan dinga squeezing lokaci ina typing.
Ayi hakuri da typing errors bana samun daman yin editing ne. Sannan ina godiya da fan's masu ƙirana da kuma masu tambayata, thanks habibaties 💕 😘 love you all❤️.
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 29 & 30
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_________ Ƙarasowa ta yi dab dasu ta tsaya tana kare musu kallo suka sudda kai ƙasa suna share hawayen dake kan fuskar su. Ɗagowa Hamrah ta yi ta kalli Ammie da ke kallon su cikin sanyin jiki ta ce
Ammie barka da fitowa da abin da zan yi miki ne?
Sauke numfashi Ammie ta yi ta ci gaba da cewa
"Ku zaman ku gabanmu ma ko gunduranku baya yi, fisabilillahi ku duba ƙannen ƙannenku ma sunyi aure sun rufawa kansu asiri sun zauna a gidajen su kuma muma sun rufa mana asiri, amma ku sai dai kuyi ta janyo mana zagi da abin faɗa abin haushin ma ku ko a jikinku baima dameku ba, kuji tsoron Allah ku fidda mijin aure kuyi aure ku tafi cen gidajenku ku zauna, ku kuhuta muma mu huta da gori da kuma nuna mu da ake yi wlh a ta dalilin ki Hamrah na janye jikina daga shiga cikin dangina da kuma dangin Daddyn ku to cewa ake ni ce na hanaki aure alhalin ina bakin ƙoƙarina wajen ganin kinyi amma kuma ke a koda yaushe sai zuba min ƙasa a ido ki ke to bari kuji na faɗa muku kuka da kuke yi yanzu kuka fara indai kun zaɓi zaman gaban iyayenku to ke shatu ba dole mijin uwar ta ƙi ya faɗa a sha'awar ki ba kin kai aure har kin wuce kuma kina gaban shi kina giftawa, duk abin da ya sameku ku kuka ja wa kanku, kun tsaya zaɓi ko to zakuga zaɓe"
Shiru sukai babu wanda yace ƙala mamaki ne ƙarara a fuskar Shatu tana duban Hamrah da ta sudda kai ƙasa tana watsa da zoben dake hannun ta jiki a sanyaye da alamu ba wannan ne karon farko da ta ke fuskantar wannan matsalar ba sai taji Hamrah ta ce
Za muyi in shaa Allahu.
"Haka dai ko da yaushe kuke cewa amma kuma ni banga alama ba to in kuma wani abin ake kullawa to ba a isa ba kuma anyi kaɗan"
Ammie na gama faɗin hakan tayi ciki abinta.
Ikon Allah, cewar Hamrah cikin zuciyata bata ji daɗin faɗin hakan da Ammie tayi a gaban Shatu ba, ai ko ba komai akwai girmamawa da alkunya a sakanin su sannan kuma bata so kowa yasan halin da ta ke ciki bayan ƴan gidansu, sannan kuma abin Ammie kullum ƙaruwa yake kalaman yau sun ɗaure mata kai wane abu kenan ake ƙullawa ko za a kulla....
"Bestie meyake faruwa dake wanda bansan dashi ba ko ince me yake shirin faruwa me kuma Ammie ta ke cewa ban fahimta ba yaushe kuka fara ƴar haka da ita me take cewa ne dake da kuma waye kuke kulla wani abin?"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta kwakulo murmushi cikin sanyin jiki ta kalli Shatu ta ce
Babu komai Shatu kawai dai tana son nayi aurene shiyasa ki kaji ta ke faɗin hakan....
"Look Hamrah kada ki ɓoyemin komai kamar yadda nima bana ɓoye miki nawa, har tsawon yaushe hakan ke faruwa dake kike ɓoyewa?"
Shatu Ammie mahaifiya ce ban isa naja da ita ko nayi fushi da ita ba ko kuma na tuhumeta da wani abun balle kuma na tambayeta wannan dalilin yasa bana magana akan batun.
Sauke numfashi Shatu tayi ta ce
"Hamrah cewa na yi yaushe hakan ya fara kuma menene dalilin?"
Shatu bana ce ga dalili ba amma kuma rashin aure da banyi ba shine dalilin, zan iya cewa hakan ya fara faruwa ne a lokacin da aka sanya ranar bikina da Deeny akan za a haɗa dana Maryama to wannan abin ya farune ranar bikin da kuma a lokacin suka sami matsala da dangin Daddy a haka aka watse ko rakiyar Maryama basu yi ba suka bar gidan sai dai kuma naji suna ambaton sunan wata acikin musayar kalaman da suke yi wai ita HAJARA ban fahimci komai ba har aka watse aka barni da tashin hankali na fashin aurena da akayi bayan na kammala dukkanin shirina to zan iya ce miki tun daga wannan lokacin Ammie ta ɗauke min wuta bata shiga tsabgata, sannan kuma sakaninta da Daddy ma babu jituwa sai kuma kalaman da suke fitowa daga bakinta masu ɗauremin kai amma kuma abin da bansani ba shine dalilin da yasa Daddy ke cewa in ma akan wancan batun ne to tama daina tunanin zai faru. Nayi² na haɗa dukkanin maganganun waje guda na sami amsar su amma na kasa shiyasa ki kaga bansanar da ke ba.
Ajiyar zuciya mai ƙarfi Shatu tayi tana kallon Hamrah tana nazari akan kalaman ta sannan ta ce
"Wacece Hajara?"
Ban santa ba.
Cewar Hamrah.
"Bestie duk abin da ya faru dake mukaddari ne babu kuma wanda ya isa ya kanza hakan, Ammie uwace amma kuma zan iya cewa bata miki adalci ba sbd kowa yasan asalin abin da ya faru ranar bikinki ba laifin ki bane daman cen Allah ya yi ke ba matar Deeny bace. To amma meyasa ta ɗau zafi cikin kwanakin nan"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce
Eh to wannan yana da nasaba da fitowar Alhaji Sama'ila neman aurena, da farko Daddy bai amince ba amma kuma yanzu ya amince sai dai ni ce hankalina bai kwanta dashi ba kuma matsalar na faɗa mata shine take ganin kamar ko auren ne banaso to shine ta ke faɗan waɗannan kalaman dan kada naja da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 12 Chapter of 19