Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
kuma zan baki abin da zaki shekaru 10 kina amfanuwa dashi, Shatu ki yarda dani babu wanda zai ji wannan sirrin daga ni sai ke" Ya matso kusa dani yana lallaɓani akan na amince, rufe idanuna na yi na kwalla ƙara wanda yasa shi yin baya ya kuramin idanuwan shi wanda suka kaɗa su kayi jajir, numfashi na ke sauke shi on on na ce Alhaji Yusuf, ka buɗe min ƙofa na fice ko kuma dagani har kai duk muyi mutuwar kasko yanzu wlh yanda na ke ji kamar na kashe ka.... Ji na yi ya danƙo ni ya yi min riƙon mutuwa tare da janyo ni ya yi cikin ɗaki dani ya wanke ni da mara, tare da sa hannu zai yage min riga, na samu na ja da baya ina nishi, na ɗauko gwalbar wine da na gani a ajiye na yunƙura zan maƙa mashi ya saurin riƙe hannuna tare da sake jefani kan bed ya danne dukkanin hannayena ya kura min idanuwa yana sauke numfashi, cikin wata iriyar murya ya ce "Kin aikata babban kuskure wajen ƙirana da Alhaji Yusuf ba Daddy ba, kada kiga ina lallaɓa ki yi tunanin tsoron ki na ke ji, to ki sani ko kusa, kawai ni na fi son muyi alaƙar cikin kwanciyar hankali hakan zai fi faranta min, amma na kula ba zan taɓa samun hakan ba cikin kwanciyar hankali da lallami sai na nuna miƙi karfi na" Eh na faɗa Alhaji Yusuf, kai da bakin ka ka ce kai ba asalin mahaifina bane kuma ba zaka taɓa zama ba, to gwamma na kira ka da sunan ka.... Shaƙo ni ya yi tare da ɗauke ni da mari ya ce "Yau sai kinyi da kin sanin zuwanki duniya" Nan ya soma cire min kayana, na samu na kai mashi cizo, na miƙe tare da ɗaukan kwalbar na makamashi a kai na fice da gudu jiri na ɗibana ta window na samu na fito sbd kulle ƙofar da ya yi, da ƙyar na iya kawo kaina gida ina shiga ciki na tadda Mommy bata nan na tattara duk abin da zan buƙata na ajiye ta dawo da yamma na sanar da ita gobe zan tafi Cameroon nan hankalin ta ya tashi wai sam sai na gaya mata dalilin yin hakan, cewa na yi kawai zan tafi haka muka kwana wai bazan tafi ba, ban samu na tafi a ranan ba sai washegari shine har na shigo na ke sanar da ke. To bayan na tafi da wasu satika ne Mommy ta biyo ni wai Daddy ne ya ce ta je ta taho dani, nan fa na ce ba zan dawo ba, sun yi² na faɗa musu dalili amma naƙi daga ƙarshe dai muka zauna akan a shiga sakanina da mijin mahaifiya ta nan aka ce to na yi harka ta ya yi nashi. To bayan na dawo kuma zaman ya koma babu daɗi yanzu haka Mommy fushi ta ke dani wai bana girmama mijinta har ta kaiga ko gaishe ta na yi bata amsawa abinci ma sai dai ni na girka iya cikina ita ta keyiwa ƙannena, shikuma bai fasa bibiyata ba shine nazo wajenki ki bani shawara na sanar da ita ne ko kuma na yi shiru mu" Sauke ajiyar zuciya Hamrah ta yi da ƙarfi tare da share hawayen dake bin ƙuncinta, ta matukar kaɗuwa da abin da Shatu ta sanar da ita, what mijin uwa ya ke bibiyar ɗiya, wannan wane irin tashin hankali ne, wane irin zamani aka zo ne, tabbas ƙarshen duniya yazo, a hankali ta ɗago ta kalli Shatu da ta ƙura mata jajayen idanuwan ta, ta ce Shatu na tausaya miki akan wannan al'amarin tabbas wannan babban tashin hankali amma da yardan Ubangiji komai zai wuce, sanar da mahaifiyar ki kai tsaye zai sake haifar da wani tashin hankalin ne abin da ya dace shine ta ganshi yana yunkurin aikata hakan shine kawai zai sa ta amince sbd na fahimci ta miƙa masa dukkanin yardan ta babu yadda za ayi ta fahimce ki. "Kina nufin na bari har sai ya yi yunkurin aikata hakan, to ta yaya kenan in kuma ya aikata ba daidai ba fah yazama too late kenan?" A'a Shatu zamu ɓullo masa ta inda ya ɓullo miki sannan kada ki manta ba ke kaɗai ce yake yiwa hakan ba tayu akwai waɗanda ya yi musu kammin ke, to yanzu abin da na ke so dake shine ki koma gida ki sami Mommyki ki bata hakuri ki ce kin fahimci ke ce da kuskure kuma kin gane dan haka ta yi hakuri shima Daddy ki bashi hakuri a gaban ta ku koma yadda ku ke a cen baya daga wannan lokacin mu kuma zamu fara namu plan ɗin dan ina da tabbacin bazai taɓa ja da baya ba zai sake gwada sa'ar shi, abin godiya ma shine baya haihu dashi ba. "Zan yi in shaa Allahu sai dai sai na kai zuciya nesa wlh bana son ganin shi kwata kwata" Ƙawata kada ki damu komai zai wuce, ke dai ki aikata abin da na ce in shaa Allahu, Allah zai bamu mafita. Hamrah ta yi ta kwantar mata da hankali har aka kira la'asar suka tashi suka shige ciki suka isar tare da cin abinci, Hamrah ta shirya kar fe 5:00pm suka fito, Hamrah ta shige ɗakin Ammie ta tadda zaune ta sake yi mata ya jikin sannan ta fito zuwa wajen aiki. A hankali suke takowa a layin unguwar su suna ci gaba da fira, Shatu ta ce "Ni kam ƙawata yakama muje shopping gobe tun da kina gida mun jima fa bamu yi siyayya ba" Uhm gaskiya kam dan nima ina son abun da dama amma kuma ba time haka nake hakura. "Ai sha'anin aikin ku sai an jure, shiyasa ki ka ga gwamma business da na ke yi bazan iya aikin Hospital ba" Murmushi Hamrah ta yi ta ce Ni kuma gaskiya ina sha'awar aikin ko sbd ceton rayukan al'umma, yauwa ban faɗa miki ba kwanakin baya fa na haɗu da Hauwa'u. "Wacce ce kuma hauwa'u?" Hauwa'u Jibrin ƴar kyale² wacce muka yi secondary School mana, tana ma tambayar ki. "Wai ki ce ƴar goal kai naso ganin ta ko ya ta koma" Aiko tana nan yadda take. Suna fira har suka iso bakin titi Hamrah ta hau ɗan sahu ta wuce wajen aiki ita kuma ta dawo gida. Akwai shaƙuwa sosai sakanin su tun suna yara haka suke basa rabuwa har suka girma suna tare kuma dukkanninsu ba su yi aure ba. Hamrah ta iso cikin Hospital ta wuce office na ta kai tsaye office na MD a kulle na Dr Mahmoud ne a buɗe ta shige ciki, a nutse ta fiddo da duk abin da zata buƙata sannan ta kunna system ɗinta ta jima tana aiki a ciki sannan ta rufe tare da lumshe idanuwan ta, sai ta ji babu daɗi da bata sanya Dr ALIYU cikin idanuwan ta ba cikin kwanaki biyun nan sai ta ke jin kamar ba lafiya ba, shigowar shi ko da babu komai tana ƙaruwa da shi kamar yadda yake ƙaruwa da ita sannan akwashi da zolaya. Ta sauke numfashi zata je cen bangaren yaran ko zata samu ta ganshi su yi magana ko ba komai anyi zaman tare. Ta fito ta wuce general ward nan ta ci gaba da duba patients ɗin ta ta jima a ce jin ana kiran sallah magrib ne ya sa ta fito ta dawo office na ta sai bayan ta idar da sallah ishai sannan ta fito ta wuce bangaren yara, bata sha wahala ba ta sami office na shi, cikin sanyin jiki ta turo ƙofar ta shige tare da sallama sai dai kan ta ƙarashe sallamar taga abin da ya firgita ta, wani irin tsawa Dr Aliyu ya daka mata cikin ɓacin rai "Me ya kawo ki nan, ko nan ɗin ma kin zo ne shima ki rushe min shi kamar yadda ki kayi min a wancan bangaren" Cike da mamaki ta ke duban shi what, ita yau Dr Aliyu ke dakawa tsawa akan wane dalili kenan sannan kuma meyake nufi da cewa wai ita ta saka aka kora shi daga wancan bangaren, ta danne zuciya tare da cewa Dr Aliyu, yau ni ka ke wa tsawa sannan ka ke neman ɗauramin laifin da ban aikata ba, ka fi kowa sanin na tsani wannan abu biyun da ka yi min, tsawa da kuma ɗauramin laifin da ban aikata ba ya fi komai ɓata min rai da shiga kunci, sannan ka sani ni ban san abin da ka ke cewa ba dan haka kada ka kuskura ka daura min laifi. Ta faɗa tana sauke numfashi cikin ɓacin rai. Ido cikin ido ya ke dubanta cikin ɓacin rai idanuwan shi sun kanza sunyi jajir kamar ya yi marisa ya fito mata a asalin ALIYU HAIDAR zaki, ya ce "Dr Hamrah kada ki mai dani sakarai nasan abin da na ke yi kuma na ke faɗi, kina da sanya hannu zundum cikin abin da a kayi min sannan kuma ke ce silar faruwar komai, dan haka you have stopped acting like a good to everyone bcoz nasan komai yanzu kin bani mamaki ina kallon ki da daraja da mutumci ashe ..... Ya isa! Na ce ya isa Dr Aliyu ka fara wuce gona da iri, ka gyara kalaman ka, kasan me ka ke faɗi ya zaka dunga ɗunkule zance kana jifata da munanan kalamai akan wane dalili?. "A kan alaƙar da ke sakanin ki da Dr Mahmoud daman can kuna mummunar alaƙa ki ke nuna min bakya yi baki ma son shiga sabgarshi ashe ba gaskiyar bane to ki sani na san koma nasan asalin fuskar ki, dan haka ba za ki ci gaba da raina min hankali ba sbd nasan ke fasuƙa........ Saukan lafiyayyen mari ya ji kan fuskar shi sai da shatin zarazaran yatsun ta suka kwanta kan fuskar shi cikin ɓacin rai ta nuna shi da yatsa Dr Aliyu mind your tongue, ka wuce gona da iri amman ka bani, na yi tunanin in da wani ne ya faɗi hakan a kaina you are the first person da zaka kareni shine yau ka buɗe baki har ka ke kirana da ƙazamin suna, lallai ɗan Adam na iya ƙanzawa i won't prove my self but abin da na sani shine you'll regret and be shame at the last. Tana kaiwa nan ta fice cikin ɓacin rai ta nufo bangaren su kai tsaye ta wuce office nata ta shige tare da dukan teburin dake gabanta tana huce, ansha yi mata irin haka amma kuma jin hakan daga bakin Dr Aliyu ya dameta sai ta ji tana so yasan gaskiyan lamarin ya zama dole ta nemo hanyar da za ta yi exposing halin Dr Mahmoud da MD ta yadda zata kawar da zargi da shakka da kuma kokonton da Dr Aliyu ke yi akanta kuma ta sa a dawo dashi wannan bangaren, ta jima tana sake² cikin ranta sannan ta wuce general ward ta ci gaba da kula da patients nata, sai kusan to 1:00am ta dawo office ta ɗan kwanta sai bacci ya ɗauke ta. Da asubah ta farka ta hau shirya kayanta bayan ta idar da sallah sannan ta fito ta ɗau hanyar gida, ta shigo gidan shuru babu motsin kowa ta nufi ƙofar ɗakinta jin miryar Ammie ta yi ta kira sunanta "Hamrah" A hankali ta juyi, cikin sanyin murya ta ce Barka da safiya Ammie ya ƙarfin jikin?. "Hamrah da na buɗe ido na ganki nake jin bakin ciki da takaici bani da damuwa a duk fadin duniyar nan irin na ki, bana iya bacci bana iya cin abinci cikin kwanciyar hankali in na tuna kin ɗabi shekaru a gabana babu aure shin ki sanar dani da akwai abin da ki ke aikatawa ne da ya sanya baki son aure na sani na kuma san irin matakin da zan ɗauka ko kuma kawai so ki ke na mutu da bakin cikin ki" Kanta a kasa tana kwalla tana jin zuciyar ta na yi mata zafi, to in dai mahaifiyar ta bata yarda da ita ba kuma ba zata iya shaidan ta ba kenan duk wanda ya yi mata hakan bai kamata ta ji babu daɗi a hankali ta furta Ki yi hakuri. "Hakuri a cikin shi nake kawai na fahimci ni ɗin ce baki son farin ciki na kin fi son ayi ta zance na cikin dangi da ƴan unguwar ace na ajiye ki naƙi aurer da ke kina duk abinda da ki ka ga dama, to ki sani ina gab da ɗaukan hukunci akan ki ko ni ba bar miki gidan ko ke ki bar min gidan sai ki je in da zaki ji daɗin ci gaba da abin da ki ka ga dama" Jikin Hamrah ya soma rawa ta ɗago tana kallon Ammie anya waɗannan maganganun daga bakin Ammie suke fitowa, meyasa Ammie ke faɗin haka da tana da yadda za tayi da ko ta yi ko dan ganin farin cikin ta, meyasa Ammie ta tsaneta sosai ne, anya kuwa ba wani abin da bata sani ba ...... "Na faɗa miki har yanzu ina kan bakata zuwa ƙarshen wannan watan komai zaizo ƙarshe" Ta juyo ta fice, da ƙyar Hamrah ta iya ɗaukar kafarta ta shigo ɗakinta, ta zaune daka ƙasan bed ta saki wani maraitaccen kuka wanda da ƙyar ta ke iya yin shi cikin tashin hankali a wajen aiki babu sauki a gida ma kuma babu sauki ina zata sanya ranta taji sanyi me, shasheƙar kuka take yi da tana ajiyar zuciya....... "A'a Hamrah Please stop crying, kuka zai haifar miki da matsala.... Ture shi ta yi ta juya mashi baya tana ci gaba da kuka, hankalin Ammar ya matukar tashi ganin ta cikin wannan yanayin ya sake matsowa kusa da ita cikin muryar rarrashi ya ce "Ki yi hakuri Hamrah, kada hakan ya dameki ni na yarda dake kuma ko da duk duniya zasu juya miki baya ni ba zan yi ba, ke mutuniyar kirki ce Ammie na gulma da segumin mutane ne ya yi mata tasiri, amma itama a hankali zata daina, kin ji I'm with you" Sauke numfashi ta ɗago tana kallon shi duk ya tashi hankalin shi jikin shi har rawa yake idanuwan shi sunyi ja, ta ƙirƙiro murmushin dole ta ce Ba kukan abin da Ammie ta faɗa ba nake kaina ke min ciwo. Ajiyar zuciya ya sauke ai ko mahaukaci ne yaga abin da ya faru zai fahimci komai balle kuma shi da ya ke da cikakken hankali, ya ce "To na ji, faɗamin me ki ke son ci?" Duk abin da akwai. "To ina zuwa" Ya tashi ya fice, bai jima ba ya shigo ɗauke da trey ya ajiye a gaban ta ya haɗa mata tea ya miƙa mata ta soma ƙurɓa a hankali ya buɗe pepper soup na jan nama ya ɗeba mata cikin plate ya miƙa mata ta ƙarɓa ta soma sha, ta ya kura mata idanuwa a hankali tace Kai fa ba zaka sha bane?. Ya sauke numfashi a hankali ya ce Zanje na watsa ruwa sai na nayi breakfast sannan na tafi office na Daddy. Okay, thanks. Ya miƙe ya fice, ta kammala ta buɗe drower ta ɗauko da emzor ta haɗiye sannan ta kwanta bacci ta jima tana bacci sannan ta farka, ta watsa ruwa ta ƙarashe shan raguwar pepe soup ɗin ta ji ana kiran sallah azahar ta shige toilet ta ɗauro alwala ta fito ta idar kenan ta ji sallamar Shatu ta ɗago ta kalleta Shatu ta ce "Ba dai kin mance fitan da zamu yi ba?" Sauke numfashi Hamrah ta yi ta ce Na manta fa amma a shirye nake zamu iya tafiya. Daman ta gaji da kwanciyar suka fito ta shige ɗakin Ammie ta shaida mata zata siyayya bata ce da ita komai ba ta fice jiki a sanyaye, a daidai layin unguwar su suka tadda ɗan sahu, suka hau ya kai su GUMALTI nan suka kammala shopping sun fito da lader niƙi² a hannu sai suka ji ance "Hamrah" A lokaci guda suka juyo cike da mamaki Hamrah ke binshi da kallo mutumin nan ne da ya taɓa tambayar ta a layin unguwar su, cikin sakin fuska ta ce Barka da yamma ci. "Yauwa barka dai ranki shidaɗe da fatan dai baki bance fuska ta ba?" Murmushi ta yi amma bata mance fuskar ma sai dai sunan shi da ba zata iya tunawa ba.... "Alhaji Sama'ila" Murmushi tayi, Shatu ta ce "Bari na nemi ɗan sahu kamin nan sai ku gaisa" "Sannun ki" Ya ce da Shatu. Ta amsa da "Yauwa sannunka kaima" Ya yi murmushi ya ce Ba sai kin nemi ɗan sahu ba nima arean ku zan bi sai nayi dropping na ku ko" A'a ba komai Alhaji zamu ƙarasa ai. Cewar Hamrah, amma ya dage sai da yasa drivern shi ya shigar musu da kayayyakin su sannan ya buɗewa Hamrah gidan baya, ta juya ta kalli Shatu ta yi mata alamun ki shiga, sannan ta shiga itama Shatu ta shiga ta zauna a mazaunin gaba ita da driver, Hamrah da Alhaji Sama'ila a bayan mota suka ɗau hanyar dawowa gida. Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 17 & 18 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _________ Ajiyar zuciya ya sauke da ƙarfi, idanuwan shi sun sauya kala, duk duniya ya tsani ganin yayar shi cikin tashin hankali ko cikin damuwa baya son ganin ɓacin rainta, shiyasa ya ɗau wa kanshi alkawarin samo mata farin ciki, ita ma taji daɗin rayuwa kamar yadda kowa keyi ta daina zubda ƙwalla, shi dai kawai hankalin shi bai kwanta da wannan mutumin ba, amma zai yi zurfi bincike akanshi, a hankali ya ɗago yana kallon ta ganin duk hankalin ta a tashe ya ce "I'm sorry" Ta sauke numfashi jikin ta ya yi sanyi ganin lokaci guda kuma ya dawo cikin hayyacin sa ta ce Bana so, kada ka sake yi min haka, sannan ko ba komai shi babban mutum ne ya kamata ka girmama shi. "Ina yin hakanne don farin cikin ki, bana so ki aure shi dan farin cikin Ammie na fi son ki yi aure cikin so da kuma ƙauna" Ta sauke numfashi, na ji kuma na gode amma kasani dan kaina zan yi ba dan Ammie ba, dan haka ka maida hankali ga shirye shiryen tafiyan ka. Ya sauke numfashi ya ce "To shikenan" Ta fice ta fito compound na gidan ta tadda Alhaji Sama'ila har ya shige cikin mota, ta iso ya buɗe mata ta ciki ta shiga, a hankali ya tada motar sbd shi kaɗai yazo, shuru ya ratsa har suka fito daga layin unguwar su, mamaki ta ke irin na mujiyar da ƴan layinsu suka zubawa motar har suka ɓace. Sauke numfashi Alheri Sama'ila ya yi tare da cewa "A wacce Hospital ki ke aiki?" AL'UMMA SPECIALIST HOSPITAL. "Ok, kin san ba wani sanin kan garin na yi ba, sai kin taimakamin da kwatance" Suna tafe tana nuna mishi hanyar da zai bi, har suka iso nan ya sauke ta cikin girmamawa ta mai godiya ta shige ciki. Office ta sanyawa key ta buɗe ta shige a nutse ta shirya komanta kamar yadda ta saba. Turo ƙofar Dr Mahmoud ya yi ya shigo tare da sallama, ta amsa ya zauna tare da cewa "Yau kam kin makara, in ce dai lafiya?" Alhamdulillah. Kawai ta ce, ta ɗauko white eyes glass nata ta saka tare da buɗe system nata tana duddubawa, ya yi murmushi ya ce "Can we be friends?" Ɗagowa tayi ta kalle shi tare da girgiza kanta ta ce Friend's, how was that be possible, ni fa mace ce kai kuma na miji ta ya ya za muyi abota. Ya yi murmushi ya ce "Ana yi ai, shi ya fi komai sauki" Uhmm, ni bana yi. Ya yi murmushi ya fice sbd ƙiran sallah da ake yi. Ta sauke numfashi ta miƙe ta shige toilet ta ɗauro alwala ta idar sannan ta fito ta wuce general ward, ta jima a cen sannan ta dawo. Tana zaune ita kaɗai ta ji wayar ta na ringing ta duba Abuja ne suka gaisa nan suka taɓa fira sannan sukayi sallama. Sai ƙiran OG ya shigo ta ɗauka cikin girmamawa ta ce Barka da hutawa OG. "Yauwa barka dai Dr Hamrah, ya ƙoƙari?" Alhamdulillah. Yauwa haɗamin file ɗin da ki ke haɗamin da sauran document ɗin zan shigo on Monday around 10:00am akwai abubuwan da zan yi" In shaa Allahu, zan haɗa su OG Allah ya nuna mana jibin. "Good, ameen" Su kayi sallama. Ta miƙe ta fara haɗa su, daman haka ta keyi duk record yana office nata, shiyasa ido yake kanta, kuma akwai sirri a sskaninta da OG shiyasa yake ɗaura ta kan ragamar komai, bata da yawan magana, kuma bata wasa da aikinta, ta kammala haɗasu ta ajiye su cikin loker ta sanya key, sannan ta kwanta. WASHEGARI a nutse ta haɗa kayanta ta fito babu mutane da yawa sbd Sunday ne yawan ci ƴan visiting ne a farfajiyar Hospital ɗin ta fito ta tari ɗan sahu ta dawo gida, a filin gida ta tadda Daddyn su ta iso gareshi, cikin girmamawa ta duka ƙasa ta gaida shi Barka da safiya Daddy Ya ɗago daga danna wayar shi da ya keyi da alama sako yake son turawa ya ce "Likita barka dai, kin dawo?" Eh Daddy na dawo. "To madalla a huta gajiya" Na gode Daddy. "Yauwa likita Ammie ta faɗa min da akwai wanda yazo jiya kuma yana son ya turo magabatan shi, to anjima da daddare ki sameni sai mu yi magana" Jikin Hamrah ya yi sanyi, anya Ammie bata yi saurin sanar da Daddy ba, da ta bari sun ɗan fahimci juna dashi, amma daga zuwan farko. Ta sauke numfashi tare da cewa To Daddy Allah ya kai mu. "Ameen" Ta miƙe ta shigo ta wuce side na Ammie ta taddata kwance nan ta gaidata ta amsa "Lafiya" Har zata miƙe kuma ta ji muryar ta "Nayi magana da Daddyn ku ya ce za ki iya ce masa ya turo magabatan shi" To. Shine abin da ta ce sannan ta fito ta tadda Ammar yana shirin fitowa cikin sanyin jiki ya kalleta tare da cewa "Kin dawo?" Eh na dawo, fita za kayi?" "Uhm magana Daddy ke son yi dani akan tafiyar mu, an matso dashi nan da satin sama zamu tafi" Ta ɗan yi murmushi ganin yana magana yana kallon gefe ta ce Ina so zamu yi magana anjima ni da kai. Ya sauke numfashi tare da cewa To. Ya fice ta dawo ɗakinta duk jikinta a mace ta watsa ruwa ta sanya riga da wondo na material sannan ta hau kan bed nata ta kwanta, bata jima ba bacci ya ɗauke ta, ta jima tana bacci ta ji alamun an taɓata buɗe idanuwan da tayi ne ta sauke su kan namecynta ta sakar mata da murmushi tare da miƙa mata hannu, ta riƙe ta janyota kan bed suka kwanta, Little Hamrah ta ce "Good morning" Hamrah ta shafa kanta tare da cewa Morning cutie, da Mom ki kazo?. Ta gyaɗa kai alamun eh. Suka ji sallaman su Nazeer suka shigo suna gaidata ta amsa musu nan ta hau raba musu choculate daman bata rabuwa dashi, suna murna suka fita itama ta fito ta dawo ɗakin da suke sauka, tana shiga ko duk suna nan, ta zauna Maryama na ganin ta shigo ta fice Zeenat ce ta ce "Yaya Hamrah duk da ina fushi dake amma bazan ƙi gaida ki ba, ina kwana" Murmushi Hamrah ta yi ta ce Amin afuwa duk da bansan laifin da na yi ba, lafiya ta kalau. "Kin ƙini baƙi ɗaya, ko ƙira ballantana ziyara gani da tsohon ciki ƙafata ɗaya a duniya ɗaya a lahira" Oh sorry Zeenatu na, kin san Allah kina raina tun last week na ke son biya ta gidan ki amma Allah bai nufah ba, ya kuke ina uwar gidan ki?. "Ni dai bazan hakura ba har sai kin je min, uwar gida tana nan fah, sai abin da ya ƙaru a halinta yau ma nazo ki bani shawara" Hamrah ta sauke numfashi tare da cewa Ikon Allah, ita bata sanin ta girma, to Allah shi kyauta. Ameen. Ayshe ta ce "Zeenat ki yi wa Yaya Hamrah uzuri ko dan irin aikin ta, Yaya Hamrah barka da safiya?. Bata ma bari mun gaisa ba" Lafiya ta lau uwar gida, ya shirye shirye?. "Alhamdulillah suna yi, dan ni ko kallo basu isheni ba" Hamrah ta yi murmushi kishi ya motsa ta ce Kuna yi dai ba suna yi ba. "Uhm ke dai bari ashe haka ake ji in za ayi wa mutum kishiya kai abin sai an daure, fisabilillahi duk yadda muke da ƴan uwan shi amma suka juya min baya suka koma gindin Amaryar tun basu shigo ba" Ayshe ki nutsu ki kwantar da hankalin duk wannan

Chapter 6 of 19