ɗokin na wani lokaci ne amma da kansu zasu dawo gare ki.
"Kai ki bari a wannan satin kam sai na durza bakin ƙanwarshe fiddausi"
Ayshe har yanzu hakuri zan baki, ina nan ina kan shiri nan da kwana biyu zan je na zauna miki in ba danna ƙirji nayi miki ba abin ba zayyi kyau ba.
Zeenat ta ce
"Gaskiya kin kyauta ki je cen ɗin yanzu ma da na biya ta gidan ta ƙadan ta mari Yayar shi, muna zaune ta shigo wai ko anƙi ko anso sai ankawo Amaryar mubi duk bokan da muka daman bi, tamu ba ta Allah ba"
Uhm gwada da baku tanka musu ba, ina yaran ne?.
Ayshe ta sauke numfashi tare da cewa
"Sunbi Yaya Ammar zuwa waje, ni fah nazo da Abinci ko ci ban nutsu nayi ba muje ɗakin ki Yaya Hamrah mu ci na kwanta ko naji sanyi"
A tare suka fito zuwa ɗakin Hamrah, suna shiga suka mimmiƙe Hamrah ta fito zuwa kitchen anan aka ajiye abincin, ta tadda Maryama tana zuba abinci Hamrah ta soma zuba nasu a babban trey jollof rice ne wacce ta ji kayan spices, sai dandarun jan nama, ganin irin rainin dake kan Maryama yasa ta ce
Maryama, kina bani mamaki ta yadda rayuwar duniya ke rud'an ki, wannan halin da kika ɗaurawa kanki wallahi babu inda zai kai ki, bansan meyake sanya ki fuzgar kai ba, amma ina mai baki shawara ki bi duniya a sannu.
Turo baki da kuma ɗaga hanci tayi ta ce
"Ai kinfi kowa sanin dalilin da yasa nake haka in kema baki sauya daga ƙiyayyar da ki ke nunawa habibina nima bazan daina abin da na keyi ba, kin nuna banbanci sakanina da Zeenat bacci ni dake mun fi kusanci....
Ya isa, Maryama kada kiga ina biye miki ki ɗauka tsoron ki nake ji, a'a tausayi ki ke bani sbd kin ɗauki dala ba gamo ne, shi Alay Shatteema ne ya ce dake bana son shi ko kuma ke ce ki ke ganin hakan? To ki sani shi rashin mutunci riga ce kowa ma yana iya arota ya sanya ta kuma ya yi, amma kuma ganin rigar ba mai kyau bace shiyasa ake gudun sanya ta, amma in ba haka ba Maryama kin yi kaɗan kimin na ɗauka.
"Ai ko shi Alay Shatteema bai faɗa ba ni ai kin min na gani, kina ɗaya daga cikin waɗanda basu son aurena dashi ko kin manta ne da abin da ya faru a wancan lokacin, sannan haka still ya sake faruwa a ranar sunan Waleed, dan haka duk wanda ya ce baya son mijina to nima bazan yi dashi ba"
Murmushi Hamrah ta yi su sai ta ce
Au sai yanzu na fahimta wato dai kin fi son mijin ki da danginki to ya yi amma ki sani ba a takama da gidan miji amma anayi da na uba, ki yi indai zai miki kyau Allah bada sa'a.
Tana kaiwa nan ta ɗauko abincin ta nufi dakinta dashi tana jinjina lamarin, lallai Maryama ta na dab da zubar da hawayen dana sani in dai akan Alay Shatteema ne. Allah shi kyauta.
Nan suka zauna suka soma ci, yaran sun dawo ma ɗakin Ammar suka wuce dan fita ya yi dasu su kayo siyayya. Bayan sun kammala cin abinci ne Zeenat ta kalli Hamrah tare da cewa
"Yaya Hamrah na rasa gane kan uwar gida ta, ta hanani sakat a gidan ke numfashi ma so ta ke ta hanani, shima kanshi Alay Gana kamar tsoronta yake da ta ƙirashi har rawar jiki yake duk ya kiɗime"
Uhm Zeenat, daman duk wacce tazo a mace ta biyu a gidan miji sai tayi hakuri, duk abin da za tayi ki kau da kai in kince sai kinyi magana babu wanda zai goya miki baya cewa za ayi kin sameta a gidan dole kice za kiyi hakuri.
Zeenat ta sauke numfashi ta ce
To ai Allah ne ya ƙaddara sai na auri mijinta, dan meyasa zata ja da hukuncin Ubangiji abin da ma zai baki haushi shine tana da ɗiya a gidan miji yadda na ji ma ta kusa haihuwa amma ta ke takuramin"
Ayshe da tayi shiru tun ɗazu ta ke jin nata takaicin ta ce
"Ai ya zame muku dole ki bi tsarin da muka ɗaura mazajen mu akai ta yaya zaku shigo ku mulke mu, ai ba zayyu ba wallahi"
To fah sun rabawa Hamrah kai abin ya koma kowa so ta ke a goyi bayan ta da ƙyar Hamrah ta shawo kan zancen aka sauyata zuwa kayan da zasu ɗinka na fitar bikin nan da kwanaki biyar, sun zazzaɓa akan Ayshe zata karɓo sai ta kaiwa telan ta, nan Hamrah ta sanar dasu zuwan Alhaji Sama'ila, ai ko suka saka murna suna Alhamdulillah Allah ya ƙarɓi addu'ar su, su kayi ta bata shawa akan ta amince mashi su sha biki. Fira ta sauya an koma na bikin hamrah, ita dai bata ce komai ba sai binsu ta ke da kallo, a haka har suka wuni sai yamma lis suka tafi da yaran baƙi ɗaya aka bar Hamrah da kaɗaici, ta dawo ta zauna jin ana kiran sallah magrib yasa ta miƙe ta shige toilet ta ɗauro alwala ta fito ta idar ta jima tana addu'a akan in Alhaji Sama'ila alkhairi ne gareta Allah ya tabbatar in kuma ba alkhairi bane Allah ya sauya mata da mafificin alkhairi har aka kira sallah ishai ta idar sannan ta fito zuwa wajen Daddyn ta dake zaune a farfajiyar gida tana isowa ta zauna kusa dashi tare da yi mashi barka da dare, ya amsa tare da cewa
"Da man akan batun wannan mutumin ne, wanda Mommyn ku ta faɗa min akan shi ne zaɓinki a matsayin wanda zai aure ki, shin ɗan ina ne kuma a wacce unguwar ya ke menene sana'ar shi, waye iyayen shi?"
Jikin Hamrah ya yi sanyi sosai ta rasa ta inda zata fara amsa tambayoyin nan ita kanta bata san a salin labarin shi ba kawai dai Ammie ta yi saurin sanar da shi ne , a hankali ta ce
Sunan shi Alhaji Sama'ila, ba mazaunin nan garin Maiduguri bane wasu ayyuka ne suke kawo shi, a Abuja state yake da zama.
Sauke numfashi Daddyn su ya yi tare da cewa
"To ke likita ya za kiyi ki aure mutumin da baki san asalin shi ba, shin ma har tsawon yaushe haka ku ke tare har yasa baki san sana'ar shi ba?"
Kanta na ƙasa a hankali ta ce
Daddy bamu jima da haɗuwa ba baifi sati biyu ba jiyane dai yazo nan ya ke sanar dani cewa yana so ya turo magabatan shi.
"Kayya! Wannan ai bai nuna ba har yanzu zancen danyene ace daga zuwan shi na dauke ki na bashi ce mashi akayi ke kaya ce, ko ko mun gaji da ke a'a ba zayyu ba sai nayi bincike kanshi, kada ki yi gaggawa kema kin ji ko in shi ba zai jira ba ya tafi Allah zai kawo miki wani"
Sauke numfashi Hamrah ta yi to yanzu Ammie zata ce bakin ta ɗaya da Daddyn ta ya zata yi kenan, a hankali ta ce
To Daddy na gode.
Ta miƙe ta shigo ciki nan ta tadda Mommyn ta a tsaye tana jiran shigowar ta, aiko tana ganinta ta jeho mata da tambayar ya suka yi nan Hamrah ta sanar da ita amma ina ranta ya matukar ɓaci ta ce
"Ban gane ba sai kun fahimci juna yanzu mutum ya taso daga wata uwa duniya yazo shine za a ce ba mutumin kirki ba sai anyi bincike to shikenan sai ki zauna muyi ta gogan kafaɗar juna cikin gidan"
Ita dai Hamrah bata ce komai ba kanta a kasa sai ga Daddyn su ya shigo ya tare shi da zancen ya kalleta ya ce
"Hajjiya Batula ni kam me wannan yarinyar ta tare miki ne, yarinya da ko magana bata yi kuma da ta fita tun safe sai yamma ta ke dawowa ko kuma ta fita da yamma ta dawo da safe, to wai ma sbd ta jima bata yi aure ba shikenan daga zuwan shi sai mu bashi ita ba tare da mun san shi ba, ni na faɗa bazan mata auren gaggawa ba, in zai jira zuwa wani lokaci sai a sanya ranar amma daga zuwa ya ce wai har ya yanke lokaci ba tare da ya zauna dani ba ko mun zauna da mutanen shi ba"
Ammie ta birƙice musu lokaci guda da ya sanya Hamrah sorata ta miƙe da sauri zata bar wajen ta ji ta ce
"Na gaji Alhaji, na gaji ka fito kawai ka faɗamin cewa akwai wata manufa a ƙasa shiyasa, yarinya shekaru sun ja manema sun fito amma kuma kace sai ka zaɓa ka ɗirce is she a diamond, ina itama kamar sauran ta ke haihuwar ta akayi, to muddin tana son mu zauna lafiya ta fidda miji ta yi aure, in dai ba wata manufa ta daban cen ba....
"Hajjiya Batula, meya kawo wannan zancen, me ki ke nufi da wannan Hamrah ɗiyata ce ba zan taɓa barin a cutar min da ita ba shiyasa na ke son na aura mata mutumin da zai riƙemin ita da amana, dan haka sai na duba na tantance kuma magana ta zauna, in kuma kin shirya son rashin zaman lafiya cikin gidan to shikenan"
Sauri Hamrah ta yi ta faɗa kan bed ta fashe da kuka me Ammie ke nufi ne...
In ba wata manufa ba, to me hakan ya ke nufi kenan? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun......
Comments and share
MUJARRABI
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 15 & 16
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_________ tsit babu mai magana cikin motar, sai ƙamshi da sanyin AC dake ratsa dukkanin jikin su, ko da bata ɗago ta kalli inda yake ba ta san yana kallon ta sbd yadda ta jita bata cikin nutsuwa, haka kawai take jin mutumin na yi mata ƙwarji. A daidai ƙofar gidan su ya yi driver parking hakan ya dawo da Hamrah daga tunanin da ta keyi. Shatu ce ta fara fitowa driver ya taimaka mata suka sauke kayan, Hamrah na ƙoƙarin fitowa sai ya yi saurin dakatar da ita ta hanyar cewa
"Umm bani time na ki mana kaɗan muyi magana"
Ta sauke numfashi a hankali ta yi magana ba tare da ta kalleshi ba ta ce
Yamma tayi gashi sallah la'asar ma ta wuce mu, zamu je mu gabatar, amma ba ƙin tsayawa nayi ba.
Murmushi ya yi yana jinjina kanshi ya ce
"To ki ce da Malama nake tare to shikenan amma let's exchange our number"
Ta sauke numfashi tare da amsar wayar shi ta sanya number ta sannan ta fito ya ƙira ta yi saving da Abuja, sukai sallama suka shigo cikin gida shi kuma driver ya jashi suka tafi. Suna shiga ciki Shatu ta daka tsalle tana murna, daman gulma na cinta ta rasa yadda zatai tun ɗazu ta kagu ya tafi ta ce
"Wayyo ƙawata sanar dani good news Allah ya sa ya ce yana son ki"
Murmushi ta yi ta ce
Ke to bai faɗa ba, ya so muyi magana amma kuma na ce dashi munyi missing lokacin sallah la'asar za mu je mu gabatar, to shine fah ya karɓi number ta.
"Yeee Allah yasa ya ƙira muji alkhairi"
To in kuma wani zancen na dabanne fah.
"Kai ƙawata ai ga dukkan alamu ma ya kamu"
Dariya su kayi suka shige ciki, kasancewar Hamrah tana da night duty yasa suna idar da sallah ta hau shirin tafiya. Bayan sun fito ne Shatu ta wuce gida sbd kayan dake hannunta bata yiwa ƙawarta rakiya ba zuwa bakin titi. Hamrah ta iso bakin titi ta tari ɗan sahu ya kaita bakin Hospital ta shige ciki, kamar yadda ta saba ta ƙimtsa komanta kan teburi sannan ta kunna system ɗinta yau kam ta ɗan makara bata iso da wuri ba taji ana kiraye² sallah magrib ta tashi ta idar tana kan dardumar aka ƙira ishai nan ma ta idar sannan ta fito da niyyar tafiya general ward sai taji muryar Dr Mahmoud yana
"MD na neman ki yana cikin office nashi"
Kamar ba zata juyo ba amma jin MD yana nemanta shiyasa ta juyo ta dawo ƙofar office nashi har lokacin bai daina kallonta ba, ita kam ko kallon inda yake ba tayi ba tayi nocking ya bata izinin shigowa ta shiga, ta tadda shi zaune ya ɗaura ƙafarshi kan ɗaya ya kishingiɗe jikin kujera ya lumshe idanuwan shi.
Afternoon sir.
Ya buɗe jajayen idanuwan shi ya zuba mata su ya ce
"Have a sit"
Ta zauna ta maida kallon ta gefe, mutum a gaida shi ba zai amsa ba wannan wane irin hali ne ya jima yana kallon ta sannan ya ce
"Dr Aliyu an mai dashi bangaren yara sbd ana bukatar irin shi gogagge ta fannin aiki a wajen, shine naga ya dace da ke da Dr Mahmoud kuyi aiki tare shine yanzu zai zamo messenger na sannan kuma PA nki ina so ku haɗa kai kuyi aiki tare, kamar yadda ku keyi da Dr Aliyu, Please i don't want to see or hear anything from both of you da ya shafi ƙoraf, muna bukatar ku haɗe kanku"
Sauke numfashi Hamrah ta yi ta juyo ta kalleshi kamar yadda yake kallon ta tace
Amma sir, in dai da mutunci ai yakamata ayi shawara dani akan wannan kafin a yanke hukunci, sannan ni na fi son aiki da Dr Aliyu ba a shawar ce ni ba aka ɗauke shi sannan kuma Dr zalihat ce wacce ta dace a haɗa mu ba wai Mahmoud ba, kai ma kasan aikin mu ba zai taɓa tafiya daidai ba kuma kasan halin shi sarai ba son zuwa aiki yake ba shine za a haɗani dashi sbd ni na ɗau nawin aikin shi, Please a kanza shi da Dr zalihat.
Shuru ya yi na wani lokaci sannan ya ce
"HAMRAH, you always challenged me at anything, kina nufin ban san me nake yi bane ke kin fini sani, kada kiga OG ya baki office ki ɗauka dani da ke kanmu ɗaya I'm bigger than you in everything yanzu ma na kiraki ne sbd na sanar dake ba wai shawarar ki nake nema ba.....
Turo ƙofar Dr Mahmoud ya yi ya shigo, yana ganin su ya tabbatar hali ya motsa, duk girman kai ne dasu ko wannensu yana son girma, shiyasa basa jituwa cikin tashi salon munafunci yace
"Ranka shidaɗe, an kammala duba patients ɗin ka"
MD ya washe baki ya ce
"Weldon Dr you are trying fa, thank you"
"Noted sir, ai in dai kai ne komai ma zan iya yi maka shi"
"Yauwa zauna ga Dr Hamrah nan muna magana akan aikin ku ne ku haɗe kai kuyi aiki tare"
"Ai ba komai ai in shaa Allahu.....
Akwai, ni ba zan yi shiru na cuci kaina ba, bana son aiki da kai Dr Mahmoud dan haka a sauya min shi da wata.
"Haba Dr Hamrah, i have changed fah wlh na kanza ba zaki sami matsala dani ba"
Uhm.
Kawai abin da ta ce, sai tayi maganin shi tun da ya ɓata mata suna a wajen Dr Aliyu sai ta sa ya yi regretting, ta miƙe tare da kallon wayar hannu ta lokaci ya ja gashi yau babu patients ɗin da ta duba, ta yi musu sai anjima ta fice, kai tsaye ta wuce general ward nan ta duba su sannan ta dawo ta kwanta, ta jima tana ta tunani kan rayuwa sannan ta kwanta. Gari na wayewa ta dawo gida.
_Bayan kwanaki biyu_
Kasancewar yau morning gareta hakan yasa tana dawowa daga wajen aiki ta faɗa toilet ta watsa ruwa ta shirya cikin doguwar riga mara nawi ta zauna Jin ana kiran sallah magrib yasa ta tashi ta idar har da ishai sannan ta kunna tv tana kallo Ammar ya shigo ya tadda ta zaune tayi zurfi cikin tunani har ya ajiye mata leda ya ɗauki remote ya kanza channel zuwa MBC Bollywood, ana film ɗin student of the year. Ya juyo tare da dan taɓa ƙafarta ta sauke numfashi tare da kallon shi, ya yi mata alamun na tane ta ɗauka. Ta dauko leder ta buɗe ta, roasted fish ne ya kawo mata da moltina sai kuma choculate kala biyu, ta kalleshi tare da cewa
Na gode Ammar yau kuma har da choculate sai ka ce yarinya.
Murmushi ya yi kai Hamrah akwai son girma, ya ce
"Yarinya ce ke mana"
Hararar shi tayi, ya yi dariya sbd ta tsani wannan kalmar ta yarinya ta ce
Kada kasa na fasa cin abin da ka siyo.
Ya yi murmushi ya ce
"Allah baki hakuri babbar yaya"
Nan ta yi murmushi ta soma ci sai ta ji wayar ta na ringing tana dubawa ta ga mutumin da tayi saving da Abuja ne, sai da ta sinke ya sake ƙira ta ɗauka cikin sanyayar muryar ta tayi sallama, har tana jin yadda yake suke numfashi ya amsa tare da cewa
"Ranki shidaɗe, Allah yasa ba bacci ki keyi ba na tada ki"
Ta sauke numfashi cikin sanyin murya ta ce
A'a na kusa amma.
"To ashe dai ban yi laifi ba, daman na ƙirane mu gaisa kuma na nemi alfarmar ko zuwa gobe ne nazo sai muyi magana"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Eh to da yake ina fita aiki kuma gobe ina da morning duty sai yamma zan tashi.
"Wow, fantastic! Do you mean ke likita ce?"
Yes of course.
"Masha Allah, that's good, ki ce nima ina dab da warkewa"
Baka da lafiya ne?.
Eh.
Ya faɗa, sannan ya ce
"To zuwa yaushe ki ke gida sai nazo"
Jibi.
"Ok Allah ya kaimu"
Ameen.
Sukai sallama, ta sauke wayar ta ɗan ɗago ta kalli Ammar wanda ya zuba mata na mujiya tun da yaji da na miji ta ke wayar ta sauke numfashi tare da cewa
Menene?
"Waye ne?"
Me ka ke nufi.
Kai tsaye ya ce
"Wa ya ƙiraki, me yake nufi da wannan kiran?"
All questions for me, ban isa a ƙirani bane yaya Ammar?.
"Da gaske nake fah, kamar da na miji ki ke magana, kuma kina ce dashi yazo jibi me zai kawo shi?"
Ta tattare ledan ta saka a dustben sannan ta wuce toilet ta wanke hannunta ta fito, ta sameshi ya yi tagumi a hankali ta ce
Sunan shi Alhaji Sama'ila daga Abuja yake, to mun haɗu ne ranan na yi mishi kwatancen gidan Alay SHAREEF mai nema takaran House of reps, shine kuma kwanaki biyu da suka wuce muka haɗu a wajen shopping shine ya kawo ni gida, yanzu kuma cewa ya yi yana so yazo akwai abin da ya ke son muyi magana akai.
Sauke numfashi Ammar ya yi ya ce
"To yazo muji da me yake tafe, amma kuma daga jin sunan shi tsoho ne, in kuma da gaske hakan ne gaskiya ya yi gaba"
Murmushi tayi ta ce
To cewa fa ya yi magana zamu yi, ba wai so na yake ba.
Bayyi magana ba ya ci gaba da kollon shi, ta yi murmushi ta ce
To ai naga son na yi aure kowa ya ke to menene kuma na waɗannan tambayoyin?.
Ya sauke numfashi tare da cewa
"Haka ne muna so ki yi aure amma kuma mun fi son kiyi auren kwanciyar hankali, shiyasa sai mun tantance wanda zaki aura"
Dariya ta yi ta ce
Ƙanina na kaina, kada ka damu da yardan Ubangiji zan yi dace.
Sun jima suna fira sannan ya yi mata sai da safe ya fice, ta yi addu'an bacci ta kwanta.
Washegari bayan ta kammala shirinta, ta fito tayiwa Ammie sai ta dawo bata kulata ba ta fice zuwa wajen aiki, tana isowa sai ga motar Dr Aliyu ta shigo har ya yi parking ya fito yana kallon ta, ta shige ciki ta buɗe, bayan ta kammala jera komata ta zauna tare da sauke numfashi, turo ƙofar ya yi tare da sallama yana isowa ya zauna tare da cewa
"Good morning my partner"
Bata ɗago ba ta ci gaba da danne² wayar ta, ya ce
"Nazo ne mu tattauna akan abubuwan da zamu gudanar wunin yau"
Ai ni tun kan na fito na ke gama daily plan ɗina.
Murmushi ya yi ya ce
"Amma kin san yanzu ni PA kine so, we will work together, kuma dole nasan duk wani abin da za kiyi"
Ta juyo tana kallon shi, shima ita yanke kallo, ta ce
Bai zama dole kasan komai na ba, do you work.
Ya sauke numfashi ya ce
"Dr Hamrah let's work together, bazan sake yi miki abin da baki so ba, na canja fa"
To Allah yasa ba tuban muzuru ka yi ba.
Ya yi murmushi ya ce
"To dame zamu fara?"
Akwai patients a VIP rooms dukkanin su maza ne kai za kaji dasu yau, nima kuma zan duba mata a general ward.
Dariya ya yi sosai ya ce
"What that means?"
Kawai.
Ya jima yana kallon ta sannan ya yi murmushi ya fice, ta yi ajiyar zuciya, shi Dr Mahmoud ya yi amfani da Dr Aliyu wajen neman kusanci da ita shi kuma MD yana so ya yi amfani da Dr Mahmoud wajen tattaro bayana daga wajenta, uhmm tayi ajiyar zuciya.
5:00pm na yi ta tattaro yanata² ta yo hanyar gidan, sai dai kuma wani tunani ya bata ta shiga gidan su Shatu su gaisa a tsai tsaye ko ba komai ita tana zuwa mata amma ita bata da time na kanta ma ballantana ziyara, tana shiga a daidai lokacin kuma Alhaji Yusuf yana ƙoƙarin fitowa Mommyn shatu tana yi mai rakiya cikin girmamawa ta gaidasu ya yiwa Hamrah kuri da idanu har ta shige ta girgiza kai a ranta ta ce Allah ya shirya. A palour ta tadda shatu aiko tana ganinta cikin murna ta ce
"Ƙawata kamar kin san ko kina raina daman cewa na yi koman dare zan shigo"
Murmushi Hamrah ta yi tare da cewa,
Aiko ba zan ma jima ba a gajiye na ke zan wuce, daman mu gaisa ne.
"Duk da haka sai na shafa miki labarin"
A lokacin Mommyn ta tashigo tare da cewa
"Hamrah ki zauna mana"
A'a Mommy daga wajen aiki na ke zan wuce ma.
To Shatu yi mata rakiya ko.
Shatu ta miƙe suka fito, Hamrah ta ce
Kamar Mommy ta sauko kin yi yadda muka tsara ne?.
"Eh na yi tun washegarin ranar na baiwa Mommyn hakuri dashi kuma Daddyn sai dai jikin shiya yi sanyi amma bai fahimci komai ba"
Ai ba zai fahimta ba sai nan gaba.
Dariya sukai suna fira har ta rako Hamrah kusan gidan su Hamrah ta ce
Yauwa ƙawata wannan mutumin na Abuja mun yi dashi gobe zaizo.
"Kai amma na ji daɗi ki ce na shigo mu haɗa beta na taran baƙo"
Ke rufani ki sayani, a da ma da nayi yarinta ke ɗibata yanzu kam ba wanda zan mai wata beta in ya yi mutunci na bashi ruwa, ballema shi wani abun ne zai kawo shi innayi beta ma sai yaga rashin hankalina.
Nan sukai dariya sannan suka rabu, Hamrah ta shigo gida a lokacin ma Ammar ya dawo yana tsaye yana waya ganinta yasa ya kashe ya ce
"Ashe baki shigo ba sai yanzu, na yi tunanin kina ciki ai"
Murmushi ta yi ta ce
Gidan su Shatu na shiga, me akwai ne naga kamar da labari.
Murmushi ya yi ya ce
Muje ki girka mana abincin ki mai daɗi.
Ta ɗan buge shi a kadaɗa tare da cewa
A gajiye na ke yau sai dai ka siyo mana a bin taɓawa a waje.
"To ƙanwata kada ki damu harda choculate ma zan siyo"
Hararar shi ta yi ta ce
Ko mutum zayyi ya ya dai girma an fi shi.
Ta yi hanyar ciki ya yi dariya ya bi bayanta. Ɗakin Ammie ta shige ta gaidata amma bata kulata ba ta wuce ɗakin ta har dare tana kwance, Ammar ya shigo masu da kayan ciye² ya ajiye tare da kunna tv suka soma ci sai suna fira sai da suka kammala sannan ya tafi ɗakin shi. Wannan ɗabi an tun suna yara su keyinta har suka girma basu daina ta ba, shiyasa akwai kyakkyawar fahimta a sakaninsu kuma basa ɓoyewa junan su sirrin su.
_WASHEGARI_
A hankali ta buɗe idanuwan ta tare da ƙurawa farin slink ido, tunowa da tayi yau Friday ne yasa ta sauke numfashi ta miƙe ta gabatar da sallah asubah ta ɗan taɓa karatun Alkur'ani sannan ta koma bacci bata farga ba sai wajen 10:00am da ƙyar ta iya tashi ta ƙimtsa dakinta sannan ta wuce kitchen ta dafa indomie ta zauna a kitchen ta ci, ta wuce ɗakin Ammie ta zauna a lokacin Daddyn su yana shirin fita, suka gaisa ya fice ta kalli Ammie a hankali ta ce
Ammie, anjima akwai baƙon da zaizo ya ce yana son magana dani.
Ga mamakinta sai taga Ammie ta saki fuskar har da ƴar murmushinta ta ce
"To
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 19