shine ganin ya doshi ɗakin wannan yarinyar da ake kira da Fateemah, kamar zan bi bayan sa kuma na fasa na dawo ɗakina na kwanta cike da mamakin me ya kaishi ɗakinta ina cikin tunanin naji ya shigo a lokacin awansa 1 da rabi, kamar zan tambaye sa amma nayi shuru. Gari ya waye na fara observing nasu sai kuma nake fahimtar wani abu na daban yana yawan kallonta su sakarwa juna murmushi, a daren ranar na ce kai sai naga me suke nufi ne kuma me suke ƙullawa na, yana fita da 10 minute's nabi bayansu. A hankali na tura kofar abin da naci karo dashi ne ya gigitani kusan 5 minutes brain nawa ya daina aiki jikina da a lokacin za a saga dako ba za a sami ko da ɗigon jinine na matukar kaɗuwa, ina karanta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun, sannan na fara dawowa daidai. Mijina kwance kan ruwan cikin Fateemah suna aikata zina a gidana a kuma ɗakina da kuma gadona, wata zuciyar ta ce na watsa musu ruwan zafi. Wata kuma ta ce na kashe su na huta, amma kuma da ikon Allah na sake daurewa na fito cikin tashin hankali na komo ɗakina ina ta sake² cikin raina na irin matakin da zan ɗauka, sai kuma wani tunani ya faɗo min na cewa in kuma sun san nasan me suke aikatawa suka kasheni fah suke ɓarayi ne suka shigo, to in dai Ahmad zai shigo da dadironsa cikin gidana babu abin da zai hanashi kasheni...
Ina cikin wannan tunanin ne ya shigo ya wuce toilet ya watsa ruwa ya shirya ya dawo ya kwanta ganin idanuwana biyu yake tambaya ta me ya hanani bacci kamar na shake sa ya mutu amma na daure na bashi amsa da eh. Washegari na shirya na ce ta rakani muje gidan iyayensa amma fir ya ce bazata je ba sai dai ni kaɗai na tafi, nan na gama fahimtar komai sai na shiryawa mahaifiyarsa da ƙannensa waleema na ce suzo ba tare da ya sani ba, kawai kwasam sai yaga sun diro cikin gidan ......
"Hamrah magrib ya kawo kai ya kamata mu tafi"
Cewar Shatu ta katse Rahama da labarin da take baiwa Hamrah wacce tayi suman zaune da jin wannan labari, ta sauke numfashi cikin sanyin jiki ta kalli Shatu ta ce
Gani fitowa.
Shafu ta koma Hamrah ta ce da Rahama
Zan dawo nan da kwanaki biyu sai ki ƙarashe min.
"Ba komai a gaida gida"
Hamrah ta amsa sannan ta fice zuwa palour. Nan su kayi musu sallama suka fice akan sai zuwa nan da kwana biyu zasu dawo Hamrah suka dawo Shatu ta wuce gida.
_Bayan kwanaki biyu_
Hamrah ce tsaye bakin titi tana jiran ɗan sahu zata shopping na mayyukan gashin kanta, daman sunyi waya da Shatu akan zata biya mata su wuce, har ta tari ɗan sahu kuma sai ga kiran Abuja ya shigo tayiwa mai a daidai yayi hakuri ya tafi da hannu tayi masa alama, ta koma gefen hanya ta ɗauka tare da sallama ya amsa ya ce gashi zuwa gidansu ta sanar dashi tana hanyar tafiya shopping ya ce ta jirashi nan ta sake sanar dashi ya bari zuwa gobe zata wuce gidan ƙawarta Shatu amma ya nace sai yazo haka ta hakura yazo ya ɗauke ta suka wuce gidan su Shatu, ta kallesa ta ce
Bari na shiga sai mu fito ko?.
Kai ya gyaɗa mata alamun to. Ta shige ciki suka fito da Shatu cikin girmamawa shatun ta gaida shi ya amsa cikin fara'a tare da cewa
"Yauwa yau na haɗu da kawar matata wacce zamu dinga shawara game da bikin"
Murmushi Hamrah da Shatu suka yi shatun ta ce
"Aiko nima nayi farin cikin haɗuwa da mijin bestie nah"
Suka shige motar ya tada ta yake tambayar su wane shop suke son zuwa nan Shatu ta sanar dashi amma kuma sai ya kaisu wani babban shop a tare suka shigo sukai siyayya ya dinga jido musu kaya kamar babu gobe, suka fito bayan ya biya ya riga su fitowa tare da wani ma'aikacin wajen ya taimaka masa ya fito musu da sauran kayayyakin. Shatu da Hamrah na ƙoƙarin fitowa sai su kayi kicibus da su yar gold, cike da mamaki Zee ta ce
"Aminai an fito siyayya kenan?"
"Uhm fah Zee kuma ku kayi balle kuma mu"
Bata fahimci abinda Shatu ke nufi ba Hamrah ta ce
Da mutum muke tafe kada ya jiramu yaga mun daɗe.
Juyowa suka yi lokaci guda, suna kallon motar cike da mamaki ƴar gold ta ce
Kamar nasan wannan motar............
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 41 & 42
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_________ Kallonta Hamrah keyi tun da ta shigo ta ganta ta soma bala'i bata ce komai ba sai dai tayi mamaki a ina taji zancen za tayi aure ita Hamrah ba wasu kawaye ne da ita ba ballantana zancen aure ya bayyana kuma ba wasu ƙannene da ita ba waɗanda za a ce su suka yaɗa sbd yarinta, ƙannenta duk sunyi aure kuma ba masu yawan yawace² bane. Bata so ƴar gold ta san da zancen aurenta ba tafi son ayi sa cikin sirri har ta kammala abin da take so cikin kwanaki kaɗan amma ba komai ko a hakan ma tasan za tayi nasa ko bajima ba zasu gano gaskiya su dawo kan turɓa madaidaiciya. Ta sauke numfashi a daidai lokacin da ƴar gold ta ƙaraso ta zauna ta tsareta da idanuwanta ita a dole anci amanar ta, murmushi Hamrah tayi ta ce
Ƴar gold, sannun ki da gajiya ban ma jima ba da shigowa, Rahama ke faɗa min kina hanya....
"Dakata Hamrah ki fara bani amsar tambaya ta wai shin da gaske this week za a Daura aurenki?"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce
Eh Hauwa'u abin da ma ya kawo ni kenan...
"Ba wani pretty daman cen da wata manufa a ƙasa, yaudarar mu ki ke son yi, in ma ita ce to ki sani ko da aurenkinne ma za ki ci gaba da wannan harkar"
Uhm.
Cewar Hamrah, Zee ta ce
"To ai daman tasan da hakan kawai dai auren da za tayi a matsayin kariya ce daga idon al'umma"
Rahama zaune duk jikin ta yayi mata sanyi da abinda Hamrah ta faɗi mata, a hankali ta ce
"Ai aure ba matsala bane muma ai yana kanmu kuma muke harkar, zata iya fitowa ayi da ita kawai a bata sati kan cin amanar ci tana gamawa sai ta fito"
"To na ji wannan shawarar amma tunda taji sirrin mu ya zama dole ta zauna ayi harkar tare amma cewa zata bari bazata ga daidai ba"
Cewar Hauwa'u Jibrin, ita dai Hamrah bata ce komai ba, bata jima ba ta fito ta dawo gida, a ƙofar gida ta tadda Alhaji Sama'ila a tsaye a kofar gida yana gingine cike da mamaki ta iso inda yake yana ganinta ya sauke numfashi cikin sanyin murya ya ce
"Wayar ki bata shiga duk na damu, tun ɗazu nake nan na rasa wanda zan aika shi cikin gidan ya kiramin ke"
Ajiyar zuciya Hamrah ta sauke tare da ciro wayar ganin network ne ya ɗauke ta ce
Wayar a kunne take service ne ya ɗauke.
"Ok shigo mota"
Ta zagaya ta shiga suka zauna jikinta duk yayi sanyi ta zauna cikin sanyin murya ta ce
Amma lafiya ko?.
Ya juyo sosai yana kallon ta na wani lokaci sannan ya ce
"Em nazo ne na baki kuɗaɗen da zasu isheki, sannan kuma kinsan ba a garin nan zamu zauna ba a cen Abuja ne, dan haka bana son ƴan rakiya dake kaɗai zamu tafi kuma bana son tarkacen kaya ina da komai cikin gidana"
Ta sauke numfashi cikin sanyin murya ta ce
To zanje muyi shawara da yan'uwana duk yadda mu kayi sai na sanar maka....
"A'a Hamrah bana son hakan shiyasa tun farko na faɗawa maneman auren cewa bana bukatar komai daga wajenku sbd bana son yawan magana ne kawai muyi maganar nan a sakanin mu, ke ba yarinya bace da zamu tsaya muna cece kuce kawai maganar ta zauna a haka"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce
Gaskiya, maganar gaskiya wannan ba al'adar Maiduguri bace kamar yaya zan yanke hukunci da kaina, bayan bani ce zan aurar da kaina ba, zancen akaini babu kayama bai taso ba dole sai amin duk abinda ake yiwa ko wacce amarya. In yaso ko daga baya ne sai akai min cen ɗin. Amma menene dalilinka na son na tafi babu kaya kuma babu ƴan rakiya?.
Ganin ranta ya tsoma ɓaci yasa ya rage murya ya ce
"Shikenan ayi miki kayan, amma daga baya sai a kawo miki, bani account number ki sai na tura miki kuɗi"
To.
Ta faɗa ta bashi sannan ta shigo cikin gida bayan sunyi sallama, mai Alhaji Sama'ila ke nufi ne. Har ta shigo cikin nan ta tadda Ammie a palour tana zaune tana ta shirya kayayyakin da tasa a kawo. Zama Hamrah tayi cikin sanyin murya ta gaida ta
Ammie barka da yammaci?.
"Barka dai Hamrah kinga yanzu babanninki suka tafi kalli abin arziki da suka kawo min nan, kai amma sunyi ƙoƙari sosai"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce
Ammie, yanzu Alhaji Sama'ila ya tafi.
"Ah to madalla.
Amma fah ya ce wai baya son a haɗani da kayayyaki komai akwai acen, kuma babu ƴan rakiya, Ammie na fara jin tsoro.
Murmushi Ammie tayi tare da cewa
"Ke zolaya ce, giyar wake muke sha da za ace a kaiki babu komai shima kawai faɗa yayi ai sai anje anga masaukinki"
A hankali Hamrah ta sauke numfashi jin abin da Ammie ta ce, dan haka ta miƙe ta shige cikin ɗakinta, ta watsa ruwa ta gabatar da sallah magrib tana kan dardumar sallah har aka kira ishai ta idar ta kwanta. Cikin dare ta farka duk tayi gumi taba sauke numfashi zuciyar ta nata harɓawa sbd mummunar mafarkin da tayi, ganinta tayi cikin daji ita kaɗai dajin naci da wuta babu kowa tana ta neman masu cetonta amma babu har wutar ta kusa dab da isowa inda take shine ta farka ta sauke nauyin ajiyar zuciya. A hankali ta furta
Mafarki ba gaskiya bane.
Ta tashi ta ɗaura alwala tayi addu'ar bacci ta kwanta.
Washegari tun da ta tashi ta idar da sallah asubah ta koma bacci. cikin bacci taji ana tattaɓata ta buɗe ido little Hamrah ce ke zaune kusa da ita da murmushi ta rike hannunta tare da cewa
Namesake saukar yaushe?.
Turo baki little Hamrah tayi ta ce
"Da Mommy na muka zo tana ɗakin granny"
Turo ƙofar da sallama Ayshe tayi ta shigo ganin little Hamrah ta ce
"Au nan ki ka shigo ina ta duba ki"
Hamrah dake kwance ta miƙe ta zauna cikin sanyin murya ta ce
Aiko ita ta tadani da ko yanzu ina ta bacci.
"Kema ki shirya yaya Hamrah ki fito mai gyaran jiki ta iso zaku fara tun kan rana tayi zafi"
Uhm kai Ayshe wane gyaran jiki kuma, ai bikin da saura.
"Wane da saura this coming Saturday nefa yau kuma Sunday please get ready, muna cen baya sai kin fito"
Ayshe ta ɗauki little Hamrah suka fice. Hamrah ta shige toilet ta yi brush sannan ta fito tayi inda suke. Anan suka wuni akaiwa Hamrah gyaran jiki wuni daya tayi matukar kyau sai sokanata suke tana murmushi har suka watse. Biki saura kwanaki uku duk ƙannena ta suka tare a gida, gida kam cike yake da baki kamar aranar ce za a daura ƴan kauye ma duk sun hallara. Hamrah tayi matukar kyau kamar ba ita ba Ayshe ce tayi mata rakiya zuwa saloon aka gyara mata gashin kanta sbd ba zai kitsu ba yana da yawa da tsawo da kuma tsantsi. Ana washe gari biki akayi mata kunshi da kuma lalle tayi matukar kyau.
Zaune suke bayan sallar la'asar suna fira su Ayshe sai sokananta suke wai ta Alhajin Abuja mai komai dozen, ita dai sai murmushi take yi, suka ji daga waje ana marhaban mutanen ABGANISTAN. Aiko su Ayshe, Zeenat da Maryama suka fice daga ɗakin Hamrah sbd yiwa yayansu oyoyo sai da da fitarsu suka dakata tare da tsayawa kallon shi, sbd yadda yayi wani haske da kiɓa kamar wani Balarabe ko ba India ya koma tamkar jarumannan na indiawa masu faffaɗan ƙirji da shanyeyen ciki, sanye yake da riga read da kuma ba Black trouser sai kuma bakin agogo, fuskar nan ta fito rau da kwantaccen saje da size box, gashin kannan yasha gyara kamar na larabawa. Murmushi ya sakarwa kannensa ganin yadda suka tsura masa idanuwa suna tantama shine ko ba shi ɗin bane. A hankali cikin silent voice ya ce
"Ina amaryarmu take?"
Suka ƙaraso tare da cewa
"Ya Ammar tana ciki"
Suna tayi masa sannu da zuwa kai tsaye ya shige ɗakin Hamrah ya tadda tana zaune kasan carpet ganin shigowar sa yasa ta sake baki tana kallon sa irin kallon nan na saukar yaushe. Murmushi yayi ya iso ya zauna kan kujerar gaban mirror ya ce
"A jinki ba zanzo bikinki bane ai ko in bana nan baza a ma daura ba sai na zo"
Dariya tayi ta ce
To alwalina, tunda kazo barka. Ya hanya?.
"Alhamdulillah, ya shirye shiryen biki kuma?"
Anayi.
Sun ɗan taɓa fira ya miƙe ya wuce ɗakin sa ya watsa ruwa sannan ya fito ya wuce wajen Daddyn shi sbd tattaunawa kan yadda zasu tsara gidan sbd taron da za ayi na ɗaurin auren.
Har dare su Ayshe na ta sokanar Hamrah abin da ya basu mamaki shine yadda gidan ya cika makil da mutane har da wasu ƴan uwan su da basu taɓa gani ba, Hamrah tun tana gaisawa dasu har ta gaji duk tayi laushi, ta zame jikinta ta dawo ɗakinta ta zauna. Ammar ne ya turo ƙofar ya shigo ganin sa yasa ta tashi ta zauna. Zama yayi bakin bed tare da cewa
"Baki kwanta ba ashe, nima sai yanzu na shigo ina cen wajen Daddy wani abu naji wai meke faruwa ne me wannan Alhaji yake nufi da wai baya buƙata ƴan rakiya ya turo wani dattijo wai gobe da yamma za a tafi dake masaukinsa kuma wai baya buƙata ƴan rakiya a ina aka taɓa yin hakan?"
Sauke numfashi Hamrah tayi tare da cewa
Ya turo da wani kuma Ammar?.
"Eh Hamrah, ba kuyi magana bane"
Ta sauke numfashi ta rasa gane kan Alhaji Sama'ila meyasa baya bukatar ƴan rakiya me kuma na cewa ita kaɗai zata je masaukinsa wane masaukin kenan yake nufi shin ya tanada mata inda zai ajiye tane ko kuma menene...
"Ya kinyi shiru?"
Ammar munyi magana amma na ce dashi ba zayyu ace babu ƴan rakiya ba shine ina ga ya tura wani.
"Gobe zan yi mashi magana kamin a ɗaura auren"
Sun jima suna fira sannan ya fice zuwa ɗakin shi.
_WASHEGARI_
Gida ya kauraye da hayaniyar hidiman biki sai kaiwa da komowa ake yi su Ayshe kam sai rawar jiki suke ana auren babbar yaya, an kashe Naira iya Naira bikine wanda ba a taɓayi ba Daddy ya buɗe bakin aljihunsa yana zubda Naira karfe 11:00 am aka ɗaura auren Hamrah da kuma Alhaji Sama'ila, akan sadaki 15 million, wuni akayi ana hidima har 4:00 pm aka kawo kayan akwatin Hamrah dozen biyu dukkanin su cike da kayayyaki na gani na faɗa da key mota a cikin kid na dankunnayen gold nan akayi ta murna ana ta sanya albarka. Sai dab magrib motar tazo kwalli ɗaya wai anzo ɗaukan amarya nan hankalin kowa ya tashi akace ba zayyu ba sai anga inda zai ajiye ta, aka kirasa ya ce a hotel zasu kwana da safe zasu hau jirgi su wuce Abuja amma akace ba zayyu ba da ƙyar aka amince masa shima sbd yace da safe masu rakiya su shirya sai azo a ɗauke su. Hamrah kuka kaman ranta zai fita Ammie ce ke rarrashinta tare da banbaki, ganin Ammie ta sanya baki yasa ta ɗan sagaita kuka ta shirya aka fito da ita aka sanyata cikin motar abin da ta bata mamaki shine babu kowa a cikin motar sai driver kawai tana shiga ya tada motar kai tsaye sai a hotel ya direta ta baya yayi mata jagora suka shige ta tadda Alhaji Sama'ila zaune cikin manyan kaya sai ƙamshi yake yana ganin ta ya miƙe ya riko hannun ta zuwa bakin bed ta sudda kai ƙasa tana wasa da zoben gold ɗin dake hannunta ya rike hannunta tare da ɗago dashi ya ƙurawa lallen ido yana jujjuya tare da shafawa. Ta sauke numfashi a lokacin da ya janyo ta cikin jikin shi tare da ɗago da habarta ya kura mata idanuwa, a hankali ta sauke nata idanun sbd ba zata iya jure ganin nashi jajayen nan ba duk a tsorace take. Babban yatsan hannun sa yakai kan bakinta yana shafawa a hankali, ta ɗago ta kallesa zuciyarta na harbawa, idanuwanta sun ciko da kwallah kamar zatai kuka murmushi ya sakar mata tare da cewa
"I'm sorry dear"
Bata fahimci mai yake nufi da kalmar ba a hankali tana kokarin zamewa daga jikinsa ya sake riketa gam tare da zame mata ɗankwalin lace ɗin kanta, bayyanar gashin ganta da yayi yasa ya sauke numfashi tare da bin gashin yana shafawa hannunsa ya soma rawa abin da bai taɓa yi masa ba. Gaskiya wannan lady special ce, kokari zuge mata zip na rigar ta da yake yi ne yasa ta rike hannun sa tare da yin magana muryarta na rawa ta ce
Ba muyi sallah ba kamar yadda ake yi.
Lumshe idanuwan sa yayi ya buɗe tare da sakar mata da murmushi ya shafi gefen fuskar ta yayi jin laushinsa yasa ya sauke numfashi tare da cewa
"Yanzu na idar da sallah kuma na sanya ki cikin addu'a so no need sai mun sake yi"
Daram ƙirjinta ya buga me yake nufi, ita dai tasan ana yin raka'a biyu na godewa Ubangiji kafin a kwanta amma meyasa Alhaji Sama'ila yaƙi suyi, ba tayi aune ba taji ya zuge zif na rigar ta tare da sanya hannu ya cire mata rigar da kuma kunce zanin. Jikinta ya tsoma rawa yayi saurin kai bakinsa kan labbanta ya soma tsosa kamar tsohon maye. Tsoro da fargaba yasa jikinta rawa, ga yunwar dake addabar ta wunin ranar ba abinda ta saka abaki anyi² taci abinci ta kasa ci. Sosai yake sarrafa ta ita dai banda rawar da jikinta keyi ba abinda tayi. Ya miƙe ya barta kwance ya cire dukkanin kayan jikinsa ya tsaya yana kallon ta duk ta tashi hankalin ta ganin ƙaton tumbinsa da kuma manyan nonuwansa kamar mai shayarwa yasa ta fara zubda ƙwalla a tunanin ta zai kashe wutar ɗakin ne amma taga ya hayo kan bed ɗin ya kai mata danƙa kamar a old hungry Lion, a hankali bakinta na rawa ta ce
Dan Allah, kayi min a hankali ban taɓa yi ba wallahi tsoro nake.....
Kan ta karasa ya rufe bakinsa da nata yana masa shan rake a tunaninta horo man ne yana so ya zuƙi jininta. Nan ta fara kokarin kwatar kanta a hankali ya zame bakinsa ya kalleta da jajayen idanuwan sa ya ce
Hamrah wai meye haka ne?. kinsan dogon lokaci da na naɗauka ina jiran wannan ranar, bana son haka ki barni na dirji kuɗina in kuma ki kayi kaddama ke jikinki zai gayawa"
Bakinta na rawa ta ce
Dan Allah...
Amma yaki saurara mata, yana dab da shigar ta kuma hakan yazo daidai da kusan ta shiɗe sai taji ya dakata ya ɗanyi shuru na wani lokaci sannan ya dago da fuskar ta yana mata kallon mamaki tare da yin magana cikin rawar murya ya ce
"Are a virgin?"
Kirjinta ya kara bugawa daman me ya ɗauketa cikin sanyin jiki tare da rawar murya ta kaɗa masa kai alamun eh. Ya sauke numfashi tare da cewa
"I'm really sorry"
Daga nan bata sake sanin inda take ba sbd sumar da tayi.
10:00am, a hankali taji kamar ana tattaɓata ta buɗe idanuwanta da su kayi mata nawa da ƙyar tana bin inda take da kollo a hankali komai ya dawo mata, ta ɗan juyo taga Alhajin da yake ƙoƙarin tada ta kuma sai taga akasin haka, ta sauke idanuwan ta kan wata ƴar budurwa sanye take da jan riga polo da kuma bakin skit sai face cap. Da alamu ma'aikacinya ce a wannan hotel ɗin a hankali tayi magana sbd yadda zazzaɓi ya rufe ta da kuma ciwon kai da yunwa ta ce
"Kina son abu ne?"
"A'a turoni akayi na gyara wannan room ɗin sbd akwai wanda ya kama zuwa yamma zai iso"
Cewar wannan ma'aikaciyar. Cike da mamaki Hamrah ta sake waro idanuwanta tana kallonta ta ce
Inaga ba nan bane, dan da mijina nake, ki bari ya shigo inaga ya ɗan fita ne in yazo sai kuyi magana.
Gyara tsayuwar ta ma'aikaciyar tayi cike da mamaki ta ce
"Baiwar Allah miji kuma, ai wanda ya kama ɗakin tun safe ya sake daman kuɗin dare ɗaya ya bada, yanzu ma manager ne ya turoni na gyara ganin ki kwance kuma yasa nayi mamaki.........
_________________________
Alhamdulillah yanzu aka fara wasan. Daman nace tun daga farkon PG ɗin zuwa PG kafin wannan shimfida ne to yanzu labarin ya soma.
Ayi hakuri da typing errors bana samun time na gyarawa ne.
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 39 & 40
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
____________ Da mamakin su suka bi inda ƴar gold ke kallo, ƙurawa motar Alhaji Sama'ila idanu tayi tana rarrabe su, tana so ta san a inda ta taɓa sanin motar, Hamrah ta sauke numfashi tana mamakin ina kuma ƴar gold ta san shi, Shatu ce tayi magana cikin sauri tare da yin gaba ta ce
"Ah to kisawa ranki cewa ba wanda kika sani bane wannan special man ne"
Tayi gaba abin ta, Hamrah tabi bayanta bayan ta ce da yar gold
Sai nazo ko zuwa nan da kwanaki biyu.
Sukai sallama ta wuce cikin motar Alhaji Sama'ila ta tadda sai fira suke shida Shatu, ta sauke numfashi da ya sanya ya juyo ya kalleta itama ta ɗago ya ce
"Ya dai gajiya ne?"
Uhm to dashi ɗinma, 2 days ban huta ba.
"Kin kusa ki huta ma ai daga fita aikin, let it be next week, kawai kiyi bankwana da aikin kinga za ki sami hutu kamin ki fara hidimar bikin"
Ta sauke numfashi ko ita daman haka take son tayi zuwa next week ta sami OG suyi magana akan zata sake aikin, a hankali ta ce
Inna samu na kammala wasu abubuwan zan sake aikin.
"Ok it's better kam"
Shuru ya ratsa har suka iso ƙofar gidan su Shatu yayi parking tare da cewa
"A'isha mun iso bari na buɗe boot ki ɗauki kayanki ko"
"A'a duk siyyan Amaryar ka ce babu nawa a ciki"
Cewar Shatu tana kokarin fitowa Hamrah ma ta fito tana cewa
Akwai wani white lada naki ne ki ɗauka.
Alhaji Sama'ila ya fito mata da kayayyakin ta, da ƙyar ta amsa tana godiya ta shige ciki bayan sunyi sallama da Hamrah. A nutse ta shigo cikin motar ya tada ta suka nufo gida, shuru babu mai magana a sakaninsu daman ita Hamrah bamai yawan magana bace har suka iso kofar gida yayi parking, juyowa tayi zata mai godiya taga ya kafeta da idanuwansa masu kwarjini sai ta kasa magana, shiru suna kallon junansu cikin sanyi jiki ta janye nata idanun tare da sauke numfashi, shima ajiyar zuciya yayi ya ce
"Kina bukatar wasu abubuwane da suka shafi biki nan kusa?"
Kai ta gyaɗa alamun a'a, murmushi yayi ya ce
"A'a buɗe baki za kiyi muyi magana ai yanzu mun zama ɗaya, babu batun ma wata kunya ko jin nawi na"
A'a yanzun dai gaskiya bana buƙata komai.
Ta faɗa cikin sanyin murya ta sake ɗagowa a karo na biyu ta kallesa har yanzu shina idanuwan sa na kanta yana kare masa kallo duk sai taji ta takura ta ce
Ɗazu a bakin shop mun haɗu da wasu ƙawayena ɗaya daga cikin su ta ce ta sanka.
Murmushi ya sakar mata sosai yana yinsa ya ce
"Menene sunanta?"
Ƴar gold, Hauwa'u Jibrin.
"Ƴar gold"
Ya maimaita yana jinjina sunan, a hankali ya kai hannunsa zuwa kan nata hannun dake kan ciyarta ya rike tare da matsesa cikinta, ya sauke numfashi tare da kiran sunanta
"Hamrah"
Hannunta ne ya tsoma rawa, ta sudda kai ƙasa tana kokarin kwato hannun amma yaki sakewa cikin sanyi murya ya ce
"Are you doubting me"
Ta ɗago cikin sanyin jiki tana kallon sa sai kuma taji kunyar abinda ta faɗa ta girgiza kanta alamun a'a, murmushi ya sakar mata ya ce
"I don't know her, did you agree"
Ta sake gyaɗa masa kai, ya sake hannun nata ya fito ya buɗe
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 15 Chapter of 19