ta shafa kanta tare da cewa
Namcy yau kam zamu sha fira ko?.
Little Hamrah ta gyaɗa kai alamun eh.
Ayshe ta fito ta tadda Ammar zaune suna gaisawa da Zeenat ta ce
"Lahh ya Ammar kai da kanka lallai yau gidana ya yi farin jini"
Murmushi ya yi ya kalleta tare da cewa
"Na sameku lafiya?"
"Lafiyanmu kalau, ya shirye shiryen tafiya?"
"Alhamdulillah, week ɗin da zamu shiga ma zan tafi"
"Kai Ya Ammar ka ce tafiyar tazo?"
Cewar Zeenat tana gingina kai, ya ce
"Eh fah Zeenat kuyi ta sanya ni cikin addu'o'in ku"
"Zamuyi da yardan Ubangiji"
Ayshe da Zeenat suka faɗa lokaci guda, sun jima suna fira Ammar ya yi musu sallama ya tafi baima jira abinci ba, har dare ana hidima ƙafa bai yanke ba mutane sai shigowa suke kamar yau ne ranar bikin, ko da shike Ayshe akwai ta da zumunci. Hamrah tana zaune a palour tana shan fruit salad Zeenat ta fito itama ta zauna an watse baifi mutum biyu zuwa uku bane a ɗakin Ayshe, suna fira Alay Bukar ya shigo ya tadda su, zama shima yayi suna gaisawa ya ke tambayar Hamrah ya aiki ta amsa mashi da Alhamdulillah, ta tambaye shi ya shirye shiryen bikin ya ɗan tsosa keyar shi ya ce
"Daughter ya ƙoƙari?"
Murmushi ta yi ganin ya dawo mata da tambayar ta ce
Alhamdulillah.
Ayshe ce ta fito ganin ya shigo yasa ta fice daga palour duk sai ya ƙiɗime yabita da kallo, ya miƙe ya shige cikin ɗakin shi bai jima ba ya fito ya fice a lokacin ta shige ciki, Hamrah ta girgiza kai tana mamakin irin kishi na Ayshe ta miƙe ta shige ciki ta samesu nan su kai ta fira har lokacin kwanciya ya yi suka kwanta.
_The next day_
Washegari kasancewar Friday ne short day yasa tunda suka tashi basu kwanta ba suka hau hidiman biki, gida ya cika da mutane musamman side na parents nashi sai shige da fice ake, Ayshe duk jiki ya yi sanyi ganin fa abin yazo sai wawwaro idanuwana ta ke tana kallon mutane Hamrah na danne ta tare da bata addu'oin, har yamma kafin nan Hamrah ta samu ta ɗan zauna, da shigar ta ɗaki wayarta ta hau ringing ta ɗauka sbd ganin sunan Bestie a jiki tayi murmushi tare da ɗaukawa ta ce
Shatu kamar kinsan ko kina raina.
"Nazo gida na tadda Ammie ita kaɗai ta ke sanar dani wai kina gidan Ayshe kuna bikin?"
Sauke numfashi Hamrah ta yi tare da cewa
Uhm kiyi hakuri ƙawata Alay BUKAR ne ya ke ƙara aure, na sha'afa ban sanar da ke ba gobe ne ma ranar taron in kin samu sai ki biyo.
"A'a ba zan zo gayyar soɗi ba sai da na kira shine ake sanar dani, in kin dawo nazo mu tattauna"
Sauke numfashi Hamrah ta yi ta san bata kyauta mata ba, ta ce
I'm really sorry bestie abubuwa sun min yawa shiyasa ban sanar da ke ba amma ki zo goben.
Ajiyar zuciya Shatu ta yi ta ce
"Gobe zani wani bikin sai jibi zan je miki"
To bestie godiya nake, da akwai labari ne?.
"Sosai ma"
Okay sai kinzo.
Sukai sallama tana tsinke ƙirana sai ga kiran Abuja ya shigo nan ta ɗauka tare da sallama ya ce
"Busy tun ɗazu da wa ake waya haka Baby?"
Sauke numfashi Hamrah ta yi tace
Uhm da ƙawata ce, ina wuni?.
"Ok lafiya kalau, daman ƙira na yi na ji muryar ki da fatan kina lafiya?"
Alhamdulillah.
"To maybe gobe na shigo Maiduguri"
To Allah ya dawo da kai lafiya.
"Ameen baby"
Sukai sallama tana mamakin yawan tafiyanshi da kuma zuwan shi bayan kuma ya ce bai san kowa ba anan Maiduguri...
"Yaya Hamrah, Alay BUKAR yana neman ki yana waje"
Ta ɗago tana kallon Zeenat da ta shigo bayan ta fita tattaki sai haki ta ke da alamu tana jin labour ne, ta ce da ita
To gani fitowa.
Ta miƙe ta fice, ta tadda shi yana rakuɓe jikin garu yana jiran fitowar ta, ta iske shi tare da gaida shi ya amsa ya ce
"Daughter faɗamin me da me ku ke buƙatar gobe baya tampol da su carpet abin da ya shafi abinci da abinsha"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Daddyna ba mu buƙatar komai ai duk abin da mu ke so ka siyo su sai dai Allah ya bada zaman lafiya.
Ya sauke numfashi tare da ɗagowa ya kalleta shiyasa ta ke matukar burge shi akwai ta da zurfin tunani ya ce
"To na gode, amma kuma ina so na yi magana da Ayshe ta ki saurara ta Please ko za ki yi mata magana ta samu ta fito mu gaisa"
Murmushi Hamrah ta yi ta ce
To Daddy na.
Ta shige ciki Ayshe na zaune cikin ƙawayenta ta yi mata magana, ta miƙe tare da isowa inda ta ke Hamrah ta riƙe hannunta ta ce
Zo nan Ayshe.
Suka shige ɗaki ta ce
"Menene yaya Hamrah?"
Ayshe kenan duk nasiha da kuma ban baki da mu kayi miki ya tashi a banza to naga babu amfanin zaman mu anan dan haka mu watse kowa ya san inda dare ya yi masa tunda baki bukatar mu.
Hankalin Ayshe ya matuƙa tashi ganin yadda Hamrah ta kanza lokaci guda ta riƙe hannunta tare da cewa
"Yaya Hamrah me kuma na aikata da ya sanya ki ke irin wannan maganganun?"
Ayshe come to your sense, ai koda tunani ya gushe hankali baya gushewa, ke ba yarinya bace da za ayi ta maimaita miki abu guda ɗaya, maisa sai da akazo dab da gaɓar kogi za ki sare, kuma ina mai tabbatar miki wannan sarewar da ki ke shirin yi zai sa ki aikata da kin sanin da ba za ki taɓa mantawa dashi ba, kuma hanyar da ki ke ƙoƙarin bi ba mai bullewa ba ce, kaurace masa da kin tsayawa ki saurare shi da ki keyi tamkar sake rushe alakarku da kuma zubar da kimarki ki keyi, tunda ya yi magana ba sau ɗaya ba, ba sau biyu ba to me ki ke so ya yi miki, ya fasa auren ne, bayan ya tara dubban jama'a ko kuma ya ki ke so ya yi?.
Sauke numfashi Ayshe tayi tare da cewa
"Meyasa kowa ya kasa fahimta ta, sai ganin laifi na ake bayan kuma andakeni sannan kuma ace za a hanani kuka kuma ai abin sai ya taru ya yi min yawa, sannan kuma ai munyi magana na faɗa mashi yaje shi wajen ta na bar mata shi"
Ayshe kina cikin hankali kuwa, kin san me ki ke cewa, kada kishi ya rufe miki ido ki kauce hanya fa, to wlh kiyi gaggawar tuba sbd da Allah ki ke jayayya ba da Bukar ba kenan kin karyata ayar ubangiji da ya halatta aure ya basu damar su yi daga ɗaya har zuwa huɗu shine ki ke cewa baki so, to ma a kanki aka fara kishiya da za ki ɗaga hankalinki?"
Kuka Ayshe ta soma yi ta ce
"Ni bana jayayya da ayar ubangiji, kawai ina jin zafi ne tamkar ci min mutunci yake son yi"
Ayshe, qu'rani zancen Allah ne kuma maganar sa ce dan haka kuma shi ya basu damar yin hakan amma ya ce in zasu iya adalci to kinga Bukar ya shirya zai kuma iya yin adalci sannan da ki ke cewa cin mutuncin ki zayyi ya yi ne ai bai aikata ba sai ki bari ya aikata shi tukuna.
Shuru Hamrah ta yi sbd ganin Ayshe tana kuka ta zauna kusa da ita tare da ɗaura hannun ta kan kafadarta ta tausasa murya tasan Ayshe na da zafin kishi tun tana ƙarama, a hankali ta ce
Ayshe gobe ne ɗaurin auren kiyi hakuri ki daure daga yau zuwa gobe zuwa jibi komai zai wuce ki yi ta karanta addu'oin da na rubuta miki za kiji sauke, da ace Bukar yana bin mata a waje ana yawo dashi ai gwamma ace ya yi aure ana daraja shi sannan hakuri da kuma juriyar ki sa kawaicin ki ne zaisa kiyi kima da daraja a idanuwan dangin shi da kuma shi kanshi, kuma zai kawo muku kwanciyar hankali.
"To yaya Hamrah me ki ke so na yi yanzu?"
Yauwa ko kefa, tashi ki wanke fuskarki ki shafa powder sai ki je ki compound na gida mijin ki na jiranki yana son magana dake, kada ki nuna mashi damuwar komai ki yi mashi addu'a da kuma kalamai masu daɗi da zai sanya ya yi farin ciki gobe cikin jama'a.
"To"
Cewar Ayshe ta miƙe ta yi yadda Hamrah ta sanar da ita sannan ta fito ta wuce inda mijinta ne tsaye ta hango shi ya rakuɓe jikin garu yana jiran isowarta, Hamrah na tsaye daga window tana kallon su ta ji tausayin Ayshe, duk wanda yaga irin soyayya da kuma shukwar da su kayi sannan bata son auren ƙanwar ta ya mutu dan haka za tayi komai taga sun zauna a gidajen su. Ayshe na isowa Alay BUKAR ya rungume kamar zayyi kuka, jin tayi magana ba yadda ya saba ji ba tunda ya sako zanjen ƙarin aure yasa ya ɗago ganin tana murmushi yasa ya yi matukar mamaki ta ce
"Honey, ya Hamrah ta ce kana nemana shin kana bukatar wani abin ne?"
Saurin rungume ta ya sake yi yana sauke numfashi tare da shigewa cikin jikinta yana shaƙar kamshin ta, jikinta ya yi sanyi taji tausayin shi to meyasa yake son ƙara aure in dai yana sonta to me yake buƙatar ne haka?. Ta daure ta ce
"Do you need something Honey"
Ya ɗago da ita tare da ɗan lumshe idanuwan shi yana sauke numfashi ya ce
"Kawai ina so naga wannan kyakkyawar fuskar ta ki"
Ta yi murmushi, sun jima a tsaye yana kwantar mata da hankali tare da yi mata tambayoyi ko da abin da ake bukata ta faɗa masa suna da komai sannan su kayi sallama, ta dawo ciki a lokacin kowa ya kwanta, sai Hamrah ce kaɗai tana shiga ta kwantar da kanta kan kafadar Hamrah tana kuka ta yi ta rarrashin ta daga bisani suka shige ciki suka kwanta.
Washegari ranar ɗaurin aure suka tashi da hidimar biki 10:00am aka ɗaura aure Ayshe ba karamin jarumta ta yi ba har suka wuni. Da daddare aka kawo amarya around 8:00pm Hamrah na zaune kusa da kanwarta ganin ta saki ranta yasa ta miƙe ta fito wayarta ta yi ringing ta ɗauka Alhaji Sama'ila ne bayan sun gaisa ya ce da ita
"Baby na shigo gari fah tun 3:00pm shuru ba ki kirani ba ko ƴar sannu da zuwa ma ki min"
Ta sauke numfashi duk ta gaji ta ce
So sorry, muna hidiman biki ne duk bani da nutsuwa, ka dawo lafiya?.
"Ok ayya ya yi kyau, Alhamdulillah. A ina kuke bikin?"
Nan unguwar jiddari polo.
"Ko zan iya zuwa?"
Eh to gaskiya yanzun a gajiye na ke sai dai ko zuwa gobe.
Ya sauke numfashi tare da cewa
"Gashi kuma ina son ganin ki, ko za ki zo inda na ke mu gaisa ne?"
Cike da mamaki ta ce
Ina kenan?.
"Hotel, Dujuma hotel"
Ta sauke numfashi ta ce
A'a.
"To shikenan gobe zan zo"
To.
Nan sukai sallama.
Sunday, shine ranar wunin bikin humaira na kwance bayan sun kammala dukkanin hidima ta gaji ta shige ɗakin Alay BUKAR ta kwanta kasan carpet bata son hayaniya wayar ta ta yi ringing ta ɗauka sbd ganin suna bestie dake jikin, Shatu ta sanar da ita ta iso tana ina nan ta faɗa mata inda ta ke, ta ɗan jima sannan ta shigo Hamrah ta ce
A ina kuma ki ka tsaya?.
"Ina ɗakin Ayshe muna gaisawa"
Bari nasa a kawo miki abinci.
"A'a barshi zuwa anjima yanzu dai na zo muyi magana ne"
Hamrah ta tashi ta zauna ganin Shatu na hawaye yasa ta ce
Ƙawata meyafaru?.
"Daman akan plan ɗin da muka yi ne na aiwata amma kuma an sami matsala"
Subhanallah wacce irin matsala kenan?.
Gyara zama Shatu ta yi ta ce
"Kamar yadda ki ka ce na baiwa Mommy hakuri da kuma shi mijinta a gabanta na yi, kuma ta sauko, muka koma normal kamar yadda muke, da farko Daddy baya shiga harkata amma kuma bayan an ɗau wasu kwanaki sai ya tsiro da hanyar da zaisa na dinga zuwa inda ya ke, ganin a gaban Mommy ya ke aike na yasa nake zuwa, har ya kaiga ko bata nan yana kirana ɗakin shi kamar yadda ya keyi a baya nake haɗa masa tea. Ranan ina kwance babu kowa a gida duk sun tafi skul Mommyn ta tafi gidan bikin suna naga ni kaɗai ce yasa na shige cikin ɗaki na kwanta bacci ya ɗauke ni, cikin bacci naji hannu na yawo a jikina a hankali na buɗe idanuwa na sai ganin Daddy ne kwance gefena ya zubamin manya manyan idanuwansa waɗan da suka sauya kala lokaci guda su kayi jajir dasu yana fuzgar numfashi yana kallona, zanyi magana yasa hannu ya rufe min baki............
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 31 & 32
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_______ Kura mata fararen idanuwanta tayi tana kallonta cike da mamaki da kuma al'ajabi tabbas tayi nesa, kuma nesan da bazata taɓa jin kira ba, ko baza su taɓa jin kira bata yi mamakin yadda sauran matan suka basu haɗin kai lokaci guda. Matsalar mace ita ce, rabin rayuwar mace duk a kuɗi suke tafi, rayuwar mace na tare da kuɗi sbd mace ƴar kyalkeli ce da za iyaye ko miji zai daure ya ɗauke kaɗan daga cikin bukatur mace da ɓarnan bazata yi yawa ba, da kuɗi ƙalilan ake siyan zuciyarta, sbd duk bukatarta da ta ke so duk suna da alaka da kuɗi. Matan aure da suke zina a waje alhali suna da miji shima yana da alaka da son zuciya da kuma rashin basu kulawa100% ba dole ta sami 100% ba amma aƙalla ta sami 50 to 70 percent ɓarnan zata ragu. Da wannan hanyar Hauwa'u Jibrin da Zee sukayi amfani dashi suka ci galaba akansu sannan su karan kansu daliline ya sanya su cikin wannan harkar dan haka bazata gaza ba har sai ta sanya sun janye wannan tallafin sun ganu gaskiya sun dawo kan daidai. Zata fara ta kansu manya sannan kuma ta hanyar su za a samu su idda sako......
"Ku keda duhun kai, kune dai baku san me kuke yi ba, tir da wannan harkar taku in dai ta wannan hanyar ce zanyi arziki Allah ya tsareni, yanzu har wani abin alfahari ne da yaye ɗalibanku har kuna wani kuri da kuma farin ciki. To ki sani ko ince ku sani kun aikata babban kuskure kuma kuna kan aikatashi, kun cuci ƴan'uwanku mata shawarar da zan baku shine Ubangiji gafururrahim ne duk girman laifi zai yafe muku muddin kuka nemi yafiyarsa ku ka kuma watsar da wannan harkar ta iskanci"
Cewar Shatu cikin ɓacin rai ta katse Hamrah daga tunanin da ta ke yi.
Mun amince da abin da kuka zo mana dashi Hauwa'u Jibrin ƴar gold amma zaku amfana dani ne na wata ɗaya kacal kuma muna roƙon Ubangiji ya bamu nasara......
"Bestie, are you out of your mind, kin kuwa san me kike cewa kin amince da buƙatar su kina nufin za ki sanya hannu a yaɗa alfasha. Come to your mind and wake up from your deeply sleeping, a tunani na za kiyi musu nasiha amma shine ki ke so ki jefa rayuwar ki dumu² a ciki never, that'll never ever happen"
Dariya Zee ta yi ta kalli hauwa'u Jibrin suka tafa suna farin cikin samun nasa tabbas sun kusa mallakar makuɗan kuɗaɗe, Hamrah zata zame musu mukullin arzikin su.
Murmushi Hamrah tayi ta dubi a gogon dake ɗaure a hannunta ta kalli Hauwa'u Jibrin tare da cewa
Da kaina zan nemeku yanzu zan tashi na wuce ciki na shirya zan wuce wajen aiki ina da night duty.
"To pretty mungode da bamu haɗin kai sai mun jiki Please kada ki ɗauki lokaci mai tsawo wajen yin tunani"
Cewar Hauwa'u cikin farin ciki, murmushi Hamrah tayi ta ce
I promise you za ki jini nan da kwanaki.
Cikin farin ciki suka tafi, Shatu cikin ɓacin rai ta ce
"Bestie me ki ke nufi da hakan?"
Murmushi Hamrah tayi ta ce
I want to help.
"Which kind of helping is that, kina so dai ki sanya rayuwar ki cikin hatsari wajen taimakon wasu Please let them do whatever they want and ke ma ki yi rayuwar ki"
Shatu yin hakan da ake yi ne yake sanya bamu taimakawa, taimako yayi ƙaranta kuma hakan shine ke jefa yawancin mutane cikin wani hali. I'll do my best naga na ceto wasu daga cikin matan.
"May Allah be with you bestie, amma gaskiya ina tsoro.
Allah ya taimake mu dai dan tare zamu gudanar.
Tare suka shige ciki Hamrah ta shirya suka fito ta wuce wajen aikinta. Bayan ta idar da sallah ishai ne tana zaune kan dardumar sallah tana addu'a taji wayarta na ringing ta shafa addu'ar ta ɗauka sbd ganin Zeenat ke kira sai dai kuma da tayi sallama sai taji muryan mijin Zeenat yayi magana cikin sauri
"Dr Hamrah kina cikin Hospital ne?"
Ta amsa masa cikin sauri da
Eh, lafiya?.
"Zeenat ce jikin babu daɗi maybe haihuwa ce"
Ok to sai kun iso.
Ya katse wayar ta mike ta sanya white coat nata ta fito ta wuce labour room ta sa a shirya bed ɗin kafin su iso suna ko isowa aka shigar da ita baifi 30 minutes ba ta haihuwa cikin murna da farin ciki Hamrah ta shirya baby boy ɗin ta kwantar dashi babu jimawa yayi bacci. Zeenat jiki da sauki ta tashi ta zauna kamar ba itace wacce ta haihu ba, Hamrah na ta tsokanarta har Aunty maimuna ta shigo suka gaisa Hamrah na mamakin waya sanar da ita nan ta ke faɗa mata mijin Zeenat ne, babu jimawa Ammie ma ta iso nan Ayshe ma ta iso sai kusan 10:00pm suka koma gida amma Aunty maimuna yayar Zeenat wacce suka fito ciki ɗaya sune suke kanta har gari ya waye. Gari na wayewa Zeenat ta ce a bata sallama tunda bata jin komai da ƙyar Hamrah ta bata sallama suka wuce gidanta, nan ko baƙi suka dinga zuwa wunin ranar Hamrah a nan ta wuni sannan ta wuce hospital ta kwana. Sai da ta jera kwana biyu tana sintiri sakanin gidan Zeenat da kuma hospital da gidansu duk sai ta gaji.
_Bayan kwanaki biyu_
Tana kwance a ɗakinta kasancewar bata da aikin safe shiyasa ta kwanta tana hutawa, sai da tasha bacci sannan ta miƙe ta watsa ruwa ta shige kitchen ta haɗa breakfast mai sauki ta fito tana ci kuma tana chatting sai ga kiran Ammar ya shigo ta voice call ta ɗauka cikin sanyin muryar ya ce
"Nayi fushi tunda an daina kulani"
Murmushi tayi ta ce
Ammar iyayen rigima ina ni ina kiranka ai sai a zuƙemin kuɗina, da fatan kana lafiya?.
"Au ta kuɗinki kike bata ni ba shikenan na gode"
Uhm da wasa nake Ammar aikine ya sani gaba ga kuma Zeenat ta haihu shiyasa ka jini shiru.
"Masha Allah, ta sauka lafiya?"
Alhamdulillah, lafiya kalau, ta sami baby boy.
"Wow kice soja ta haihu to saura taki sanya min takwara tun haihuwar ta na fari ta ke min alkawari"
Kama cire rai ba zaka samu ba.
Nan ko yayi tayi mata fira daga bisani sukai sallama ta sauka a online ta miƙe ta maida plate ɗin kitchen ta dawo taji wayarta na ringing ta ɗauka cikin sanyin murya tayi sallama ya amsa tare da cewa
"Ina kofar gidanku ki fito"
Ok to Alhaji Sama'ila amma kashigo cikin gida.
"To"
Ta miƙe ta yafa gyalle ta fito ta taddashi zaune ya sakar mata da murmushi ganin yadda tayi kyau cikin shigar da tayi ta doguwar riga ta atamfa cikin sanyin murya ta ce
Sannu da zuwa.
"Yauwa likita, na kula yanzu ba a yina"
A'a ba haka bane aikin ne.
"To ai ko kirata a waya za ki iya yi ai mu gaisa"
To na amshi laifina zan gyara.
Murmushi yayi tare da cewa
"Ai bakya laifi, nazo ne na sanar dake next week on Friday zan turo magabatana suzo su saida ranar biki, naga gwanda ayi a wuce wajen kawai kada ina ji ina gani a kwace min ke"
Murmushi tayi ta ce
Allah ya nuna mana.
Ameen.
Sun jima suna fira sannan ya miƙe yace zai wuce nan ya ajiye mata envolope cike da kuɗi ta ce bazata ansa ba amma ya dage sai ta ƙarɓa haka ta karba sai dai yawansu yasa ta kasa kirgawa ta shigo ta ajiye ta shirya ta wuce hospital. jiki a sanyaye ta shige office nata ta ajiye komai kamar yadda ta saba ta zauna ta kunna system ɗinta tana dubawa Dr Aliyu yayi sallama ya shigo bata ɗago ba ta amsa ya ƙaraso cikin kusa da ita ya ajiye mata leda tare da cewa
"Special Doctor ki sanya min albarka ga snacks da kolanut and sweet na sanya ranar bikina"
Cikin farin ciki ta ɗago ta kallesa ta ce
Na tayaka murna Allah ya sanya alkhairi ya kuma nuna mana lokacin.
Cikin farin ciki ya ce
"Amin thanks"
Samun wajen zama yayi ya zauna nan suka shiga tattaunawa akan aikin da zasu gudanar a daren yau kiran magrib ne yasa ya miƙe ya fice. 11:00pm ta dawo office nata ta cire white coat ta rataye sa ta dawo kan resting chair ta zauna tare da cewa
Wosh na gaji, ba a gama wancan wani sai ya biyo baya gashi jibi sunan Zeenat kuma morning gareta ko ya zatayi....
Ya turo ƙofar ya shigo cikin sanyin jiki ya ƙaraso tare da yi mata sallama ta amsa ta ɗaure fuska ya zauna kan kujera yana kallonta itama shi take kallo ya sakar mata da murmushi ya ce
"Wai damman babu wata alaƙa soyyayya a sakaninki da Dr Aliyu, niyi tunanin saurayinki ne sai gashi ya kawo min chewing gum da auren sa shine nace bari na shigo na sake tabbatar da cewa ba to yaudararki yayi ba"
Murmushi tayi ta ce
In kuma yaudara ta yayi fa what are going to do?.
Murmushi yayi ya ce
"Sai na mai dukan cin amanar ki da yayi har sai ta gane kuskuren sa sannan na kyalesa"
Ah lallai naga alama, da fatan dai ba kwayar kasha ba kashigo min office.
Dariya yayi yace
"A'a ai yanzu ban cika shanye² ba kuma ina so na daina ko zaki dinga ganin mutunci na"
Uhm Dr Mahmoud Allah yasa ba tuban muzuru kayi ba, Allah ya kara shiryarwa.
"Amin Dr Hamrah bari na tafi ko"
To Dr Mahmoud.
Ya fice tana mamakin sa lallai wannan mutumin to Allah ya sake shiryar dashi.
Washegari da safe ta tattaro ta dawo gida ɗakinta ta shige saboda jin shuru gidan kamar bacci suke basu tashi ba tana shiga ta faɗa kan bed ta kwanta dan ta huta bacci ya ɗauke ta sai 10:30am ta farka ta miƙe ta watsa ruwa sannan ta fito ta shige ɗakin Ammie nan ta taddata cikin sanyin jiki ta sanar da ita sakon Alhaji Sama'ila akan zai turo da magabatan shi nan ta ce da ita taje ɗakin Daddynsu ta sanar da shi. Ta shigo ta riskesa yana danne² cikin laptop nasa ta duka har ƙasa ta gaida shi ya amsa cikin kulawa yake dubanta cikin sanyin murya ta ce
Daddy, daman wancan mutumin ne yace zai turo magabatan shi nan da next Friday.
"Wane mutumin kenan likita?"
Ya tambaye ta ba tare da ya ɗago ba yaci gaba da abin da yake yi.
Ta sudda kai dan kunya abin da ya dace Ammie tayi shine ita zata yi kuma nawin hakan take ji, jiki a sanyaye ta ce
Alhaji Sama'ila na Abuja.
Yayi murmushi tare da sauke numfashi yace
"Allah ya nuna mana"
Amin.
Ta faɗa ta sake duban sa a hankali ta furta
Uhm Daddy.
"Na'am likita, da akwai damuwa ne?"
A'a daman tambaya ce nake so nayi daga cikin babanninmu mata.
"To likita ina jinki"
Daddy wacece Baba Hajara?.
Chak ya dakatar da abin da yake yi cikin sauri ya ɗago ya kalleta yana mamakin meyasa ta tambaye shi, yace
"Hamrah a ina ki kaji ana ambaton wannan sunan kuma menene dalilin ki na tambaya"
Ajiyar zuciya ganin yadda ya tashi hankalin sa lokaci guda sanan ya jima bai kirata da sunanta kai tsaye ba sai yau cikin sanyin murya ta ce
A'a Daddy kawai na tambaya ne.
"A'a Hamrah haka kurum bazaki tambaya ba sai da dalili"
Ta ɗago ta kallesa kamar yadda yake kallon ta tace
Da gaske Daddy na komai.
Ya sauke ajiyar zuciya tare da cewa
Wannan maganar ki barta anan kada kowa yaji sannan kada ki faɗawa Umar ma ya sani kuma ki cire ta cikin zuciyar ki, kin ji"
To Daddy.
"Tashi ki tafi"
Ta miƙe ta fice, jiki a sanyaye ta wuce ɗakinta tana mamaki meyasa Daddy baya so tasan wannan matar Hajara, meyasa da
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 19