Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
boot cikin sanyin jiki ta fito ya kira yara su shigar mata da kayayyakin ciki, nan suka soma jidansu suna kaiwa cikin. Da mamaki take kallon yadda suke shigar da kayan ita dai siyayya kaɗan tayi yana nufin duk waɗannan kayayyakin nata ne, ta kallesa tare da cewa Wannan ai ɗawainiyar tayi yawa bansan mani kayiwa waɗannan shopping ɗin ba da ban bari ba. Murmushi yayi ya ce "To ikon Allah, laifine dan nayiwa matata siyya, ai kin wuce hakan ma" Thank you. Ta faɗa, tana kokarin shigewa ciki ya ce "Ba komai ki huta gajiya" Ya shige motar ya tada ta ya tafi, ta dawo ciki ta tadda yaran sun ajiye kayayyakin a palour Ammie na tambayar su waya aiko su, ta ce Ni ce fah Ammie, ta sallami yaran Ammie ta ce "To ashe tare kuke tun yau kika fara siyayya haka?" A'a Ammie Alhaji Sama'ila ne ya min siyayya. "Yazo kenan, to yayi kyau" Eh. Ta faɗa shige ciki itama Hamrah ta wuce ɗakin ta da sauran kayayyakin sannan ta sake fitowa ta jidosu zuwa cikin ɗakin. *Bayan 1 week* A nutse ta shigo cikin hospital kamar yadda ta saba ta iso office nata ta buɗe ta shiga, duk jikin ta a mace a hankali take tattara duk abin da ya dace. Dr Mahmoud ya turo ƙofar ya shigo cikin sanyin jiki ya ƙaraso kusa da ya jin gina da jikin garu a hankali ya ce "Good morning Dr Hamrah" A hankali ta ɗago ta kallesa cikin sakin fuska ta ce Morning too Dr Mahmoud, how was your morning?. "Not good at all" Uhm but why?. "You are going to leave us" Ta dakatar da abin da take yi, jikinta yayi sanyi tunowa da yau za tayi handle off na aikinta, bata so ba tana son aikinta da Alhaji Sama'ila zai amince da ya barta anan garin Maiduguri sai ta dinga fitowa, amma ina last zuwan sa da yayi wajenta sunyi magana amma ya nuna sam a wannan ranar ta bar aikin, sbd shirye shiryen bikin, a hankali ta sauke numfashi ta ɗago ta kallesa tare da kwakulo murmushi ta ce Dr Mahmoud ai indai ana raye wataran za a haɗe, ai ba a rabu ba. "Uhmm baki san yadda zamu ji bane indai baki nan, we are going to missed you, much our special Doctor" Murmushi tayi ta ce Nima ina jin duk wanda yake cikin wannan hospital ɗin tamkar ƴan uwana na jikina nima zan yi kewar ku. "Humm a bar zancen haka kawai, karfe nawa OG zai shigo?" Ya ce 10:30. Ya jinjina kai tare da sauke numfashi yana ci gaba da kallon ta har ta kammala tattara duk abin da ya dace ta ɗauke ta ajiye su cikin drower nata kuma ta maida shi gefe ta ajiye ta juyo ganin Dr Mahmoud kusa da ita yana tsaye ta tsaya tare da ɗan jada baya yayi saurin cewa "Dr Hamrah ke mace ce wacce ke da kyawun zuciya da kuma kyaun hali da kuma kyaun fuskar maybe all this be the last in you, you are so special, duk wanda ya mallake ki yayi dace, ina miki fatan zama a ɗakin aurenki ya albarkaci rayuwar ki da ƴaƴa na gari. Because of the zan zamu mutumin kaina zan dawo cikin hankalina, you changed me thanks for that. Daga karshe ina neman ki yafe min duk abinda nayi miki a baya" Sauke numfashi tayi ta Nagode da yabona da kayi, kuma nayi farin ciki da sauyawan da kayi. Ni ban taɓa ko da kwana da kai ba ban iya ba bansan yadda ake yi ba, Allah ya shige mana gaba. "Ameen, thank you for the understanding till we meet at the meeting room" Ya fice kamar zayyi kuka, ta shirya ta fito ta wuce general ward nan tayi sallama da wasu patients nata wasu har da kuka, cikin Doctor's da kuma Nurses ɗin ma sun zubda ƙwalla wasu kuma na farin cikin tafiyarta, dan Adam sai Allah. Ta dawo zata shige office MD ya kirata, ta juyo ta shigo ya washe jajayen hakwaran sa da zata iya cewa wannan fara'ar tun farkon dawowar aiki cikin Hospital ɗin dan haka batayi mamaki ba ta gaida shi ya amsa tare da cewa "Komai yayi farko zayyi karshe yau zaki bar Hospital, to sai a yayyafe mana zaman tare ban sani ba ko na ɓata miki" Murmushi kawai ta yi bata ce komai ba kanta na kallon gefe shi kaɗai yana ta surutan sa, ta ce "Ba komai" Ta miƙe ta fice, ta dawo office nata ta ɗan kishingiɗe jikin kujera tana sauke numfashi, Dr Aliyu ya shigo cikin sanyin murya yayi sallama ta amsa ya zauna tare da cewa "Our special Doctor tun yanzu muka fara kewarki" Uhm Dr Aliyu ya za ayi ai kuma bazaku so ku ganni cikin wannan yanayin na rashin aure ba, tun da yanzu Ubangiji ya nufa sai muyi masa godiya. "Haka ne amma kinsan sabo akewa kuka, mun zauna dake lafiyar kamar kema kin zauna da kowa da zuciya ɗaya baki damu ba duk abin da za ace you still help people, masu irin wannan halin kaɗanne basu da yawa. Ina miki fatan zama a ɗakinki na har abada. Allah ya albarkace da zuriya ɗayyiba" Amin Dr Hamrah much appreciated with your dua. Thanks. Kiran OG ya shigo a tare suka tafi meeting hall nan yayi dogon jawabi ya fara da yabonta da kuma irin cigaban da ta samar a wannan Hospital ɗin sannan yayi mata kyauta ta musamman na kuɗaɗe masu yawa bayan ya bata award na special Doctor kamar yadda yaji ake cewa kuma ya tabbatar, anan tayi handling aikin tare da bashi files da ya taɓa cewa ta haɗa masa na ci gaban wannan Hospital ɗin, bayan ya dubasu ya ce nan gaba duk kuɗaɗen da zasu shigo ta account nashi zasu shigo, aiko nan hankalin MD ya tashi what OG da kansa ya koma accounter shikenan ta kare masa yana murna bayan tafiyan Hamrah zai ci karensa babu babba ashe ma gwamma tana nan ɗin ma. A haka dai har aka fito daga meeting Dr Zalihat da kuma Nurse Laraba sukayi mata rakiya har bakin titi, tana fita sai ga Alhaji Sama'ila yayi parking ya fito ya buɗe mata alamun ta shigo duk jikin ta a sanyaye tana masa kallon mamaki bata ce komai ba ta shiga ta zauna ya shigo ya tada motar suka dawo gida a kofar gidan yayi parking bata ce komai ba, duk sai taji ta wani iri da tabar aikin duk da ta taɓa yin hakan a baya amma bata taɓa jin irin wannan ba, cikin sanyin murya ya ce "Baby nah ya dai ko dai baki jin daɗi ne muje muga likita" A'a, I'm doing well. "To ki shige ki kwanta zuwa anjima sai muyi waya" To. Ta fito ta shige gida, ta tadda Ayshe da Zeenat sun iso suna ganin ta suka saka murna suna sukananta amarya, murmushi kawai tayi ta zauna a kan kujerun da suke palourn ta sauke numfashi tana bin kayan da ke jibge a zube ta ce Na menene kuma waɗannan?" Ayshe ta ce "Wannan kayayyakin da za ayimiki gyaran jiki na aurenki da abubuwan da zaki amfani su, wadannan kuma ankon biki ne na family anko tunda kince ba zaki cire na kawaye ba shine mu mun siya yanzu haka mutane 70 muka sayawa ga kuma kuɗin mutum 40 ta dangin Daddy. Yanzu ma munzo ne zauna muga su me dame ya kamata a shirya" Uhm ga Atm nawa kuyi duk abinda ya dace Please ku barni zanje na ɗan kwanta. Cike da mamaki suka bita da kallo har ta shige ciki ta kwanta abin ta, duk sai take jinta wani abu haka to ita dai ba murna ba bakuma bakin ciki ba har bacci yayi awun gaba da ita. Sai bayan la'asar ta farka ta watsa ruwa ta fito ta tadda har sun kammala duk abinda suke so suna shirin tafiya su kayi sallama. Biki saura 1week Hamrah ta shirya ta tafi gidansu ƴar gold ita kaɗai wannan karon, ta tadda rahama ce ita kaɗai a zaune a palour ƙasa da alamu shigowar ta kenan, tana ko ganin Hamrah ta saki murmushi tare da yi mata sannu da zuwa ta kawo mata ruwa, sun taɓa fira take tambayar su ƴar gold ta ce da ita ai suma suna hanya ba zai jima ba zasu dawo. Shuru ne ya ratsa sakaninsu a hankali Hamrah ta ɗago ta kalli Rahama dake ta danne dannen wayarta ta ce Rahama da son jin karashin labarin ki na tafi kuma ina tabi a rai, in zayyu ko zaki ƙarashemin ne meya faru ne a lokacin da iyayen mijinki Ahmad suka shigo suka tadda Fateemah wacce mijinki ya kawo ta a matsayin ƴar uwarsa. Ɗagowa Rahman tayi ta kalli Hamrah tare da cewa "Uhmm ki bari kawai pretty, ai Ahmad ya cuceni ko ince ya cuce kanshi, a lokacin da mahaifiyar sa da kuma ƙannensa suka shigo duk sai ya ruɗe jikinsa har rawa yake yana musu barka da shigowa, Fateemah bata palour suka zauna har suka sha ruwa sannan ta fito cikin shiri zata fita cike da mamaki suke binta da kallo tare da cewa "Ah bakuwa ki kayi Rahama ya mutun Kaduna?" "Uhm daman jira nake so aje wajen na ce Ah Ummah ai Fateemah ce ko baki ganeta ba. "Fateemah ta ina kuma?" Ahmad dake sugune duk ya jike da gumi ya ce "Kuci abinci zuwa anjima sai a tsaya tambaye² teemah ki gaidasu mama" Mamah?. Na faɗa a fili tare da miƙewa na tare ta na ce Zo kiyi musu bayani daga gidan uban wa ki ke munafuka, kin ɗauka mahaukaciyar ce ni ko bansan me nake yi ba. Ummah Ahmad ce ta miƙe take cewa "Wai meke faruwa ne Ahmadu, me nake gani wacece kuma wannan?" Tsilli² yake yi da idanuwa ya rasa abin cewa, na ce "Ummah cewa yayi ƙanwarsa ce ƴar baffansa ce satin ta biyu a nan gidan" Wawan mari umman sa ta ɗauke da dashi ya rage tsawo yana hawaye nan yake sanar da ita marainiyace an korota daga gida matar ubanta ce ta koreta sbd babu uwar ta.... Kan ya karasa ta sake wanke shi da mari ta ce "Ah ka manta a kanta aka fara maraici, meyasa ka ɓoyewa matarka sai da ta bincika ta sani to ka sani ta tattara ta fice ta koma gidan ubanta" Aiko Ummah bata tafi ba sai da ta tabbatar Fateemah ta tafi sannan ta fice cikin ɓacin rai ta ce kada Ahmad ya sake zuwa inda take. To sbd wannan abin da ya faru yasa ya ce tunda na haɗa sa da iyayensa babu shi babu ni kuma ba zai sakeni ba sai ya gana min azaba kuma ko ƙwandalansa ba zai kashe min a matsayin kayan abinci ba. Na jikata ya fice yayi tafiyarsa sai da ya ɗebi 3 month kafin nan ya dawo daman ba sana'a ce dani ba, nayi complain a gida suka ce ina tunda naji na kuma gani na zaɓesa bayan sun ce a'a na eh to na zauna dashi ko a wane irin hali nake ciki ni na sani. Shine na faɗa cikin wannan harkar har zuwa wannan lokacin" Sauke numfashi Hamrah tayi ta kalli Rahama da take zubda ƙwalla. Lallai akwai darussa da dama cikin labarinta, a hankali ta ce Mu matsalarmu mu mata munayin abu ne da dawo mana dashi, akwai mu da hakuri da kuma juriya da kwallafa rai akan abu, duk da cewa shi yaba kyauta tukuici ne, amma bai dace a dinga kwallafa rai akan kinyi sai anmiki. kuskuren ki na faro shine bijirewa iyayenki da ki kayi tun farko akan cewa ke Ahmad ki ke so in ba a baki shi ba sai dai a rasaki, su iyaye suke da hangen nesa akan ƴaƴansu suna nema miki farin ciki ne na har abada amma ki kayi kunnen uwar shegu wai ke ga mai miji, to shine Allah ya barki da Ahmad ɗin kuma ai kinga aya. Sai kuma kin rufa masa a siri kina tunanin ba zai taɓa cutar dake ba kin miƙa masa dukkanin yardan ki sbd abinda ki kayi masa ya wadatar ba zai kyalla ido yaga wata ba sai kuma gashi yayi shine hakan ya sanya ki cikin depression. Nan gaba in zakiyi abu ki yi dan Allah bance Ahmad yayi daidai ba, yayi kuskure amma da yake shi na miji duk abinda yayi ado ne, nashi ya ɓoya naki kuma duniya ta sani, bakya tunanin makomar ƴaƴanki ko kina nufin ba zasu taɓa yin aure ba, sannan ma da wane irin idanuwana zaki kallesu a lokacin da suka mallaki hankalin su suka fahimci irin abin da ki ke aikatawa. Shawarata anan shine ki goma gida ki zauna kiyi nazari ki nemi mafita tun kan lokaci ya kure miki, sannan ki nemi mijinki ku sasanta da yanzu dake dashi kun zama daya tunda da kin aikata ma fiye da abinda ya aikata....... "Hamrah pretty daman nemanki nake, mu zaki rainawa hankali ki ce zaki shigo cikin kungiyar mu ashe kina cen kina shirin yin aure to ki sani wallahi baki isa ba kinyi kaɗan" Cewar ƴar gold a lokacin da ta shigo ta tadda Hamrah a zaune a palour nsu daman nemanta take ruwa a jallo.......... . Comments and share *MUJARRABI* By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA 09021706569 PG 43 & 44 *MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION* _________ A hankali ta maida rinannun idanuwanta masu yi mata zafi da zugi ta rufe jinsu take kamar an zuba mata ruwan borkono a ciki take ji, zazzaɓi mai zafi ya ratsa dukkanin jikinta, yunwa ciwon kai rashin karfin jiki suka haddasa mata jin jiri duk da tana kwance ne kan bed amma tana jin duniyar na juyawa da ita. A hankali tayi yunkurin tashi ta gagara ta koma ta kwanta ba tare da ta buɗe idanuwanta ba, sbd jin raɗaɗin da kasanta ke mata, buɗe idanuwanta tayi ta sake duban wannan ma'aikaciyar da take sanar da ita cewa mutumin da ya kama ɗakin ya rigada ya sake tun safe, to wa take nufi ne, cikin rashin fahimta ta yi magana a hankali da ƙyar muryarta ke fitowa ta ce Inaga ba wannan ɗakin bane aka turoki, wannan ɗakin mijina ne ya kamma, ki duba maybe next room ne ko kuma room kafin wannan. Sauke numfashi wannan ma'aikaciyar tayi tana mamakin abin da take cewa, ita dai tasan babu wasu mata da miji da suka shigo wannan hotel ɗin dan cin amarci, an kwan biyu gaskiya. Tayi magana tana mai sake kallon Hamrah ta ce "Baiwar Allah ba ɓatan kai nayi ba wannan room ɗin ne aka sake wani ya kama har anbiya kuɗin ma, manager ne ma da kanshi ya ce nazo na kimtsa shi. To amma ki kace da mijinki kuka shigo ina mijinki yake?" Sai a lokacin kuma ta tuna rabonta da Alhaji Sama'ila tun daren jiya, to ina kuma ya tafi ba tare da ya sanar mata ba ko dai ya tafi sallaman bakinsa ne ya dawo su tafi cen Abujan. Ta dubeta cikin sanyin murya ta ce What the time now?. "To 11:00am" Cewar ma'aikaciyar, daram ƙirjin Hamrah ya buga har 11:00am yayi basu tafi ba to ina ya shiga ne?. A hankali ta sake cewa Please miƙamin wayata. Ta nuna da hannu kan bed side. Nan ma'aikaciyar ta nufo wajen ta sa hannu zata ɗauka sai tayi arba da wasiku guda biyu, ta dauki wayar tare da cewa "Kinga wasiku biyu a ajiye a kan bedside" Wasiku kuma?. Miko min su. Ta miƙawa hamrah su, ƙaramar Hamrah ta buɗe arɓa da abin da ta gani ne a rubuce yasa ta saki kara a wajen ta sume nan take kan bed ɗin. _3 hours left_ Da ƙyar ta buɗe dishashun idanuwanta a hankali tana bin ɗakin da kallo, idanuwanta suka sauka kan drip ɗin dake makare jikin window dake kusa da bed ɗin zuwa hannunta, tana son tuno maisa aka sanya mata drip ne, mai kuma ya faru da ita?. ... "Kin tashi sannu kinji" Muryar da taji ne yasa ta juyo ta ɗayan bangaren ta kaleta, ma'aikaciyar hotel ɗin ne zaune kusa da ita tana kallon ta cikin tausayawa ta sake cewa "Just rest you'll feel better soon" A hankali ta fara tuna abin da ya faru da ita wasu zafaffun hawaye ne suka zubo mata, ta sauke nauyeyyen ajiyar zuciya tare da rumtse idanuwanta tana addu'ar Allah yasa mafarki takeyi, duk wannan abin ba a zahiri ne yake faruwa ba a hankali ta buɗe idanuwanta ganin a zahiri ne yasa tabi jikinta da kallo ganin doguwar rigar ce irin na marasa lafiya a jikinta yasa tayi saurin kallon wannan ma'aikaciyar ta ce Bayan na suma mai ya faru dani? Sauke numfashi wannan ma'aikaciyar tayi ta ɗan dafe jikin bed ɗin da dukkanin hannunyenta cikin tausayawa tace "Sunana Hadiza Aliyu, ma'aikaciyar a nan hotel ɗin na jima ina aiki cikin wannan hotel ɗin, nasan duk wani shige da fice na wannan hotel ɗin, nasha cin karo da ire-iren abin da ya same ki sai dai banbancin naki da nasu shine ke da aurenki akayi miki hakan, na tausaya miki fiye da yadda ki ke tunani, mutumin da ki ke magana akan shi shine wanda ya kama wannan room ɗin sbd bayan kin suma ne na fita da gudu zuwa reception na tadda manager nan nayi masa bayani cikin tashin hankali, cikin sauri ya biyo ni muka shigo yaga abin da yake faruwa he feel so bad. Hankalin shi ya tashi nan ya kira wata likita ya mata bayanin abin da yake faruwa kuma da alama kamar an sadu dake, jin haka yasa tace mu fita muka fita. Nan ta duba ki ita da kanta ta shirya ki da ta fito ne take sanar damu cewa kin sami buɗewa ta kasanki tayi miki ɗinki, amma kina bukatar drip, aka turani na siyo na kawo ta sanya miki, sannan ta tafi. Abin da nake so dake yanzu shine kiyi hakuri ki kira gidanku ki sanar dasu ga abin da yake faruwa dake sai suzo su tafi dake gida amma maganar gaskiya ya sake ɗakin dan mun duba sunan wanda ya kama ɗakin kuma mun samu shine wanda ya sake kuma yayi tafiyar sa shi da wasu mutane ne ma suka fice" Tunda ta fara magana Hamrah ke kallonta bata ko kifta su ba, jin ta take kamar ma bata cikin duniyar baki ɗaya anya itace kuwa, to me yake shirin faruwa da ita ne me wannan Alhajin ke nufi da yin hakan ne, meyasa ya kashe mata kuɗaɗe in dai sbd ya kwanta da ita na dare ɗaya meyasa yayi mata haka menene tayi masa shin daman ba aurenta yake son yi bane tun asali?. Rashin samun amshoshin wanɗanan tambayoyin da tayiwa kanta ne yasa tasa hannu ta cire drip a hankali ta tashi da ƙyar ta zauna cikin tashin hankali take bin ɗakin da kallo idanuwanta suka sauka kan wayarta ta ɗauka missed calls ya kai 50 ta gani cikin sanyin ciki ta kunna wayar tana kallon waɗanda suka kirata, Ammie 20 missed calls, Daddyn 10 missed, Ammar 15 missed calls, Ayshe 3 missed calls Zeenat 2 miss calls ta sauke nauyeyyen ajiyar zuciya tayi tare da kumshe idanuwanata da suka ciko da kwallah rumtse su da tayi ne yasa suka karasa zubewa, zuciyar ta nayi mata zugi da kuma ƙona, ta yaya zata koma cikin gida ta sanar dasu abin da ke faruwa, mema zata ce dasu tace Alhaji Sama'ila da aka ɗaura aurenta dashi jiya j ya gudu ya barta, ta ina ma wannan maganar zata shige su. Sannan tayi yaya da mutanen dake gidan innalillahi wa inna ilaihi rajiun shine kaɗai abin da take ita faɗi cikin ranta.... "Kiyi hakuri ƴar'uwa ki kuma kwantar da hankalinki ki sami nutsuwa ki bar zubar da kwallah" Cewar Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ɗin, a lokacin da ta dafata Uhm. Shine kaɗai a bin da Hamrah ta iya cewa dan wannan tashin hankalin bata san da meyayi kama ba ita ko a tarihi bata taɓa jin abin da ya faru da ita ya faru da wata ba, sannan duk cikin labaran da ta jisu daga bakin waɗanda suka faɗa cikin jarrabawa ma bata ji makamancin irin nata ba, komawa tayi ta kwanta tana furta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Ta jima a kwance ta rasa mafita a hankali ta sake duban wayarta ta shiga contacts ta rasa wa zata fara kira, wani tunani ya faɗo mata ta kira Shatu mana suyi magana ko zata sami mafita, wata zuciyar kuma ta ta bari ba yanzu ba. Cen kuma ta ce ko ta kira Ayshe ne ta sanar da ita hanlin da take ciki, cen kuma ta ce ko Ammie ko kuma Daddyn su, tana ta wannan tunanin ne Hadiza Aliyu ma'aikaciyar hotel ta sake cewa "Ki tashi ki gabatar da sallah azahar lokacin ma ya wuce la'asar ma ta kawo kai" Sauke numfashi tayi tare da juyowa ta kalleta ita sabar tashin hankali ma ta ma manta da ita a zaune. Ba tare da tayi magana ba ta mike ta shige toilet da ƙyar take iya takawa ta tadda akwai na'urar dafa ruwan zafi ta kunna ta dumama ruwa ta shiga ciki ta jima a cikin sai da taji ta ɗan dama² sannan ta ɗaura alwala ta fito ta sanya kayanta na lace da ke jikinta jiya ta yafa mayafin ta gabatar da sallah. Ma'aikaciyar ta fice dan haka tana sallame wa ta dawo kan bed ɗin ta zauna ganin message ya shigo ne ta duba kuɗi ne daga Alhaji Sama'ila Naira miliyan 10, sai da ta sake dubawa da kyau ta kula ashe tun safe ya tura mata. Tayi saurin kiran layinshi kuma a kashe, ta sauke numfashi ta kira number Ayshe kira na farko ta ɗauka tare da cewa "Amarya ran gida tun jiya nake ta kewar ki aure ya rabamu, amma meyasa ake ta kiran number ki baki ɗaukawa duk hankalin mu ya tashi musamman ma Daddy tun jiya ya kasa cin abinci, haka ma yaya Ammar" Sauke numfashi hamrah tayi ta haɗiye abu mai zafi cikin ranta tare da haɗiye kukanta ta ce Ayshe bacci ne ya kwashe mu, bayan na farka kuma na koma sai yanzu na tashi, ina Ammie?" Dariya Ayshe tayi ta ce "Madallah yaya Hamrah kin shiga system ɗin, ai daga yanzu ko zaki fara rama bacci. Ammie tana nan, tun safe duk ta damu ƴan rakiyar ki sun shirya amma kuma shuru ba a ji komai daga gareku ba" Daram ƙirjinta ya buga, wai tashin hankali yanzu ya za tayi kuma ta san dole sai ƴan rakiyar nan sun rakata hasbunallahu wa ni'imal waƙil, Allah yakawu mata mafita shine abin da take faɗi cikin ranta, a hankali ta ce Ki hau online muyi video call. "To yaya Hamrah yanzu ma ko" Dukkanin su suka hau online Hamrah sosai ta ɓoye damuwarta ta kirkiro murmushi amma ana iya hango damuwa ƙarara kan fuskar da dakuma idanuwanta, cewa Ayshe tayi ta dinga yawo da wayar tana son ganin mutan gida, Ayshe ko ta dinga yawo dashi gida ko cike yake maƙil da mutane, sai kaiwa da komowa suke, wasu a zaune wasu kuma a kwance ana ta fira ana raha ta iso inda Ammie take tana tsaye tana haɗa kayan Hamrah wanda za a tafi dasu ta mota katse video call ɗin tayi ta fashe da kuka, sosai taci kuka jin ringing da wayarta keyi ne yasa ta share hawayenta ta ɗauka ganin sunan Zeenat ta kara a kunne tare da sallama Zeenat ta amsa ta ce "Yaya Hamrah barka da rana, yanzu Ayshe ke sanar dani kunyi waya na ce bari na kiraki mu gaisa" Da ƙyar Hamrah ta ita iya yin magana Eh hakane inna shirin kiranki ma kika kira ya gajiyanku?. "Sai godiya, amma ya kamar kina kuka?" Uhm a'a Zeenat ba kuka nake yi ba. "Kai yaya Hamrah gashi naji har muryarki ta dishe, kada ki damu kaɗaici ne ke damunki kuma zai wuce kewace muma duk munyi irinta kina kaiwa sati ɗaya za ki saba da rashinmu" Haka ne Zeenat thank you. "Yauwa ga Ammie nan ku gaisa tana ma son magana dake" Ta sauke numfashi ta ce To ki bata. Ta mikawa Ammie cikin masifa Ammie ta ce "Haba Hamrah abin da ki kayi bai dace ba yaya za ku shanya mutane tun safe suna jiran ku a ɗau hanya amma sai ku sharesu haka ake yi ne, wallahi banji daɗin hakan ba, yanzu ya za ayi ne goben ne tafiya tun da yau an ɗaga ko kuma kun

Chapter 16 of 19