saura ki yi sake kamar yadda ki ka yiwa sauran suka tafi"
Kanta a ƙasa ta ce
Ammie ba saurayina bane, haɗuwa mu kayi ya ce yana so muyi magana.
"Ah in ba abinki ba haka kurum ai bazai ce zaizo ba, ni dai na faɗa miki kisan irin tarɓar da zaki yi mashi"
To Ammie na gode.
_____ cikin nutsuwa ta ke shiryawa ta sanya riga da skart ta lace mai background pitch da kuma ratsi blue ya yi dai dai da shape nata ta yi normal ɗauri ta fashe Jikinta da turaruka masu ƙamsha tare da yane jikinta da gyalle ta dau wayarta dake ruri ta yi sallama ya ce
"Na iso"
Ok ka shigo ba damuwa.
To.
Ya faɗa ya kashe wayar.
Ta juyo zata fito sai ganin Ammar ta yi a tsaye yana kallon ta, ta ƙaraso ta ce
Meyasa ba kayi sallama ba, kuma kasan bana son hakan.
Haɗe fuska ya yi ya ce
"Ya yi tsufa da yawa, please kada ki bashi fuska wannan kwalliyar ma ki sauyata"
Sosai ta ke kallon shi cikin ɓacin rai ta ce
Ina ruwan ka da sufan shi sannan ma ce maka ya yi yana so na ne?.
Sauke numfashi ya yi ya ce
"Da gaske na ke ni kwata kwata bai kwanta min ba"
Ta raɓe ta gefen shi ta wuce ɗakin Ammie ta sanar da ita yazo, sannan ta fito.
Tun da ta fito Alhaji Sama'ila ya saki baki da hanci yana kallonta har ta iso cikin sanyayar muryarta ta ce
Sorry, na jima ba.
"A'a ai girman kujerar ki ne"
Ya faɗa yana tsosa keyar shi, ta janyo farar kujerar zama ta ajiye mashi ya zauna sannan ta ce ina zuwa, ta shige ciki, ta ɗauko mashi gorar swan water ta fito ganin Ammar ta yi yana yi mashi magana bata ƙaraso ba ta ɗanyi jim kaɗan sannan ta ƙaraso ya bar wajen ta ajiye mashi tare da cewa
Sannunka da zuwa.
"Yauwa"
Duk jikin shi ya yi sanyi ba kamar ɗazu ba ya ce
"Waye wannan wanda yanzu ya fice"
Ta sauke numfashi a hankali ta ce
Ƙanina ne shi.
"Ƙani"
Ya faɗa yana kare mata kallo, ya sauke numfashi, ta ce
"Eh girman jiki gareshi amma yaro ne"
Ajiyar zuciya ya yi ya ce
"Hamrah bazan ɓoye miki, ina son ki kuma da aure, tun a ranar da na hango ki har na tsayar dake muka gaisa na kamo da sonki, in har kin amince min nan da karshen wata zan turo magabata na a sanya ranar biki, kin san ni ba mazaunin nan bane wasu abubuwan ne suke kawo ni amma kuma hakan ba zai hana na tsaya ayi komai dani ba"
Jikin Hamrah ya yi matukar sanyi ta ɗago ta kalleshi kwarjinin shi yasa zuciyar ta harɓawa, bashi da wani abin da za a koshe shi sai dai girma da kuma girman jikin da yake dashi ne ba kowacce mace bace zata amince ya aureta. Ta sauke numfashi ta ce
To zan yi shawara tukuna, bani nan da kwanaki biyu.
Murmushi ya yi ya ce
"Ko dai ganin na fara tsufa ne?"
Ta yi murmushi tare da cewa
A'a.
Ya ce
"To ba matsala zan jira amma kada ki ja lokacin ya yi tsawo"
To.
Sun ɗan taɓa fira ta ce dashi zata wuce wajen aiki, ya ce ta fito ya sauke ta, taƙi amma ya dage hakan yasa ta shige ciki ganin Ammie ta yi zaune a palour tana ganin Hamrah ta ce
"Da me yazo"
Jikin Hamrah ya yi sanyi kuma amma yadda Ammie ta sake fuskarta yasa taji sanyi ta ce
Ammie cewa ya yi da aure ya ke so na.
"Alhamdulillah me ki ka ce dashi?"
A hankali ta ce
Na ce zan yi shawara.
"Ba ga irinta ba hamrah wannan halin naki shine ya sanya saura gudawa, wacce shawara da ta wuce ki amince"
Eh Ammie daman wai muyi magana ne.....
"Ammie gaskiya basu dace ba, kin gan shi kuwa sai ka ce Daddyn...
"Ammar ka ci gidanku, manya na magana kana saka baki, tshoholo ko shi ya kawa tsufa duniya tunda ya ce yana so angama"
Ya turo baki ya shige cikin ɗakin shi. Hamrah ta ce
Ammie zan shirya na wuce wajen aiki.
"To Hamrah a dawo lafiya"
Ta ɗago ta kalli Ammie sbd rabonta da taji ta faɗi hakan a kanta ta manta, ta wuce dakinta ta dauko jakarta ta fito ta shige ɗakin Ammar ta taddashi ya cika sai batsewa ya ke a dole Alhaji Sama'ila bayi mishi ba ta ce
AMMAR.
Ya kalleta da jajayen idanuwan shi bai ce komai ba ya ɗauke kanshi. Ta yi murmushi a ranta tace su Umar hali ya motsa ta zauna kusa dashi tare da cewa
Ammar, dama ce ta sameni bai kamata mu bari ta kubuce min ba, baka ga yadda Ammie ta saki fuska muna magana ba, sannan menene in na aure shi ai ba wani matsala ni ma ai na tsufa.
Ya sauke numfashi ya fisgar da iska ya ce
"Na yi mai tambayoyi daga dukkanin alamu bashi da gaskiya....
Kai Ammar, shiyasa ya ke tambaya ta wanene kai a gareni ashe da abin da ka faɗa mashi, Please tell me me ka faɗa mishi?.
Ban ce komai ba kawai tambayar shi na yi waye shi, menene sana'ar shi sannan menene taka mammen abin da ya keyi anan...
Ammar wannan ba hurumin ka bane, kabar manya su yi magana, stay out of this, abin da ka keyiwa sauran suke gujemin shine abin da ka ke so kayiwa wannan ko kana tunanin ban sani bane, to kasani muddin ka zama dalilin tafiyar wannan mutumin to babu ni babu kai.........
Comments and share.
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 21 & 22
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
________ Bankaɗo ƙofar ya yi ya shigo kamar wanda kura ya biyo shi yana huci tare da zazzare idanuwan shi da su kayi jajir yana kallon ta cikin ɓacin rai, ba a taɓa mashi irin abin da ta yi ba, ta zubar mashi da mutunci a idon ma'aikatan da suke shakkan shi, who is she da za ta ja dashi, tsayawa ya yi a kanta yana sauke numfashi ya nuna ta da yatsa, zuba masa idanu ta yi tana kallon shi duk ya fita hayyacin shi ya ce
"Ke Hamrah ki ke ko what so ever, ki fita cikin idanuwana na rufe har kin isa ki tuɓe min rigan mutunci a bainan nasi, har ma jina haɗa kai da ni to ki sani kin taro match sai kin yi regretting abin da ki ka aika yau sai kin yi kuka da ba a haiho ki duniya ba"
Yana ajiyar zuciya, Hamrah ta miƙe cikin nutsuwa ta ke ƙare mashi kallo sbd su ta ke ta tabbatar da cewa shin a hayyacin shi ya ke ko kuma ya yi marisa dan ba abin mamaki bane zai iya aikatawa ta ce
MD ni bana ja da kai kuma bana haɗa kaina da kai, amma kuma wasan da ka fara ne na ƙarashe shi sannan duk abin da za kuyi ku aikata babu ni a ciki.....
"Hold on Hamrah, mu me ki ke nufi da mu ni da waye kenan?"
Ta sauke numfashi ta ce
MD I have told you, ka aikata duk abin da ka ke so amma kada ka sanya sunana a ci, sbd I hate sharri, ba nayi kuma ban so amin dan haka do what ever you want amma kada ka sanya ni a ciki.
Murmushi ya yi yana zazzare idanuwana yana bin office nata da kallo ya ce
"Na fahimta takamar ki wannan office ɗin ne to ki sani kina ji kina gani sai kin barshi, sai kin zubar da kwallah kina begging ɗina akan na dawo dake amma kash a lokacin kin makaro sbd bakin alkalami zai bushe"
Murmushi ta yi ta ce
MD shi sharri ɗan sako ne, zaka iya aikashi duk inda ka keso amma kasani zai je ne kuma ya dawo, da Allah na dogara babu abin da bawa zai iya yiwa bawa ɗan uwanshi fa ce da izinin Ubangiji, kuma Allah ya haramta zalunci bisa kanshi kuma ya hana ayi shi dan haka ba zai bari ka yi galaba a kaina ba sbd bani da hakkin ka, kuma God forbid na roke ka akan wani abin dunya kai wannan aikin ya dama dan haka kai za kayi ta daga hankalin ka.
Girgiza kai ya yi alamun za ki sani, ki jira lokacin sannan ya fice, ta zauna tare da sauke numfashi ta lumshe idanuwanta kanta ya fara yi mata ciwo sbd tsawar da ya daka mata, ta mike ta wuce general ward ta jima acen sai bayan la'asar sannan ta dawo office nata. Bayan ta idar da sallah ta sake komawa genaral ward har da vip sannan ta dawo nan ta tadda OG da MD suna magana ta shige cikin office nata ta hau tattare kayayyakin ta kammala kimtsasu OG ya shigo cikin girmamawa ta ke welcoming nashi ya zauna tare da duban ta ya ce
"Dr Hamrah lokacin tashi ya yi ko?"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Eh sir, da akwai abin da zan yi maka shine?.
"No, babu kawai na fahimta kamar akwai matsala a wannan Hospital ɗin ne shine na ke so mu zauna nan da kwanaki biyu mu samu mu gano matsalar sai mu san yadda zamu gyara"
Ta sauke numfashi cikin farin ciki ta ce
Ok sir, as you do.
To shikenan, ina son bayanai na wannan Hospital ɗin da kuma ya patients suke ji da abincin da ake girkawa har zuwa kan fitan kuɗi da kuma shigowar shi sannan da sabon list na staff's da matsayin su"
Ta jima tana so ayi irin wannan zaman dan haka abin ya yi mata daɗi ta ce
Ok sir, zan shirya komai yaushe ne zaman?.
"Eh to ko zuwa Thursday haka"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Thursday.
Ya kalleta ya ce
"Ko da matsala ne?"
Akwai biki shine daman zan karɓi hutu na kwanaki biyu zuwa uku sai Monday na fito bakin aiki.
Shuru ya yi na wani lokaci sannan ya ce
"Kamar yaushe kenan?"
Thursday zuwa Saturday, tunda Sunday weekend ne sai na fito Monday.
"Ok ba matsala sai ki yi magana da partner nki na office da kuma na duty"
Na gode sir.
Ya miƙe ya fice itama ta ɗau jakarta ta fito ta sanyawa ƙofar key ta hango MD yana yi mata mugun kallo bata bi ta kanshi ba tayi tafiyarta har ta iso ƙofar fita ta ji muryar Dr Aliyu yana cewa
"Dr Hamrah shigo na kaiki gida"
Ta juyo ta ɗan kalleshi sai kuma ta ɗauke kai ta fice yana kallonta ta hau a daidaita ta wuce. Ta iso gida ta tadda Daddyn su zaune a farfajiyar gidan ta gaida shi sannan ta wuce ciki ta iso ɗakin Ammie nan ta gaidata bata ko amsa ba da safen ma albarkacin Daddyn su yana ɗakin ne har ta miƙe zata fice ta ce da ita
"Hamrah da fatan baki mance da abin da na faɗa miki ba ga me da fidda miji, nan da karshen wata kuma kinga lokacin matsowa ya dan haka ki je ki yi shawara tun kan lokacin yazo"
Kan Hamrah na ƙasa ta ce
To Ammie.
Sannan ta fice jiki a sanyaye ta shige ɗakinta. Ajiye jakarta ta yi ta faɗa toilet ta watsa ruwa sannan ta fito ta shirya cikin doguwar riga mara nawi ta zauna a bakin bed ta yi tagumi tana tunanin abin da Ammie ta ce, to ko dai kawai ta faɗawa Alhaji Sama'ila ta amince ya turo ɗin ba tare da ɓata lokaci ba, wata zuciyar ta ce to ya za ki yi da Daddyn da ya ce sai ya yi bincike....
Ƙirana sallah magrib yasa ta miƙe ta shige toilet ta ɗauro alwala ta idar tana kan dardumar sallah tana ta lazimi har lokacin sallah ishai ya yi ta idar, tana jin yunwa kuma bazata iya tashi ta ɗaura komai ba akan gas duk ta gaji, dabara ta faɗo mata ta ɗau waya ta kira Ammar ya ɗauka tare da cewa
"Yanzu zan iso gida....
In ba kayi nesa ba kazo min da abin taɓawa yunwa nake ji.
"Babu na siyo ma, zan ƙaraso yanzun nan"
Ta katse wayar, Alhaji Sama'ila ya ƙira da ta yi saving da Abuja ta ɗauka tare da sallama ya ce
"Na yi fushi ba a kira anmin ya gajiya ba"
Murmushi ta yi ta ce
Ayi hakuri ina niyya.
Ya sauke numfashi ya ce
"To ya zanyi in ba hakurin zan yin ba, da fatan kina lafiya?"
Alhamdulillah, ka sauka lafiya?.
"Alhamdulillah, lafiya lau, da fatan da zaran na dawo zan ji amsa daga gareki?"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Eh Allah ya dawo da kai lafiya.
"Yauwa likita na gode, zan huta sai zuwa gobe"
Su kayi sallama. Ammar ya shigo yana sauke numfashi ya ajiye ledar tare da cewa
"zan je na watsa ruwa ki ci ki ajiye min nawa"
Tab aiko in ka jima sai dai biri ya ganka.
Ya yi murmushi ya ce
"Yanzu zan fito ki ci iya cin ki"
Ya wuce, ta buɗe ladar chibs ne da roasted fish sai kuma banana juice ta miƙe ta wanko hannu ta soma ci, ya jima sannan ya shigo sanye yake da bak'ar jallabiya wacce ta hasko fatarsa, kunna tv ya yi ya ce
"Yanzu kallon news ɗin ma ba kiyi"
Ya zauna ta ce
Kayya abin kaina ma ya sha min kai, ni mantawa ma nake da kallo.
Hannu ya sanya suke ci a nutse suna fira shikuma yana kallon Ball, ta zame hannunta ta miƙe ta shige toilet ta wanke ta fito ta zauna bakin bed tana kallon shi ta ce
Ammar ranar yaushe ne specific time or day na tafiyanka?.
Ya sauke numfashi tare da cewa
"Next Tuesday by the grace of God"
To Allah ya nuna mana.
"Ameen, me ki ke shirya min ne?"
Don't know amma sai na yi tunani tukuna.
Ya miƙe ya shige toilet na ta ya wanke hannu shi ya fito ya ce
"This coming Saturday ne ko auren mijin Ayshe?"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Eh fah, zuwa jibi ma zan koma cen amma gobe na keso muyi magana da Ammie da kuma Daddy akan batun.
"To hakuri za tayi haka Allah ya ƙaddara, in ba abin Bukar ba me zayyi da mata har biyu wannan ai ɗaurawa kai pressure ne"
Murmushi ta yi ta ce
Baza ka gane bane Ammar you are still young, kai ma da ka kai irin age nasu haka za kayi ku maza ai sai a hankali.
Ɓata fuska ya yi ya ɗago ya kalleta tare da cewa
Ki daina faɗamin ni yaro ne, zuwa yanzu na girma kuma zan iya aure kawai dai baya agenda na ne amma ni nasan ba yaro bane"
Dariya ta yi tare da hararar shi ta ce
Do you know what you are saying Ammar, aure fa kace, ce maka akayi auren abin wasa ne, umm kai yaro ne mana da sauran ka.
Ya sauke numfashi cikin ɓacin rai ya ce
"Wallahi ki daina ce min yaro, zan baki mamaki ai ina dawowa na yi aure ko dan ki tantance ni yaro ne ko kuma na girma, ina su Ayshe ƙanne na ne to ai babba ne ni"
Murmushi ta yi ta ce
Kai da aure sai nan da 10 yrs.
Ya miƙe cikin kulewa ya wuce ɗakin shi, wai me Hamrah ta ɗauke shine da zata ce mashi yaro, zai je ya dawo sai ya bata mamaki, itako ko a jikin ta tayi addu'ar bacci ta kwanta tana mamaki yanda yara maza ke aure a wannan zamanin.
_After 2days_
Zaune ta ke a office ɗinta tana ƴan rubuce-rubuce, sbd so ta ke ta yi arranging komai kamin ta tafi huta da zata yi na 2 days kasancewar daren Thursday night duty ne da ita, ta samu ta kammala ta miƙe ta sanya su cikin loker ta rufe sannan ta ƙimsa kan teburin. Turo ƙofar Dr Mahmoud ya yi ya iso tare da sallama ta amsa ba tare da ta kalleshi ba ya matso inda ta ke zaune ya zauna kusa da ita har tana iya jiyo bugun zuciyar shi, cike da mamaki ta ɗago ta dubeshi ya zuba mata ƙananun idanuwan shi da suka sauya kala, ta ce
What these means, ka sakani gaba kana kare min kallo?.
Ya sauke numfashi tare da damƙo hannunta ya riƙe shi gam cikin nashi yana fidda numfashi on on ya ce
"Bazan iya jure sha'awar da na ke ji a kanki ba, ina son kasancewa dake kuma a daren yau kuma ya zama dole ki bani haɗin kai"
Zuciyarta ta buga cike da tashin hankali ta ke kallon shi, tana tantama abu yasha baya cikin hayyacin shi, tayi saurin ƙwace hannun ta amma ya haɗa duka biyu ya damƙe su cikin hannu ɗaya, ta yadda bazata iya kwacewa ba, hannu ɗayan kuma ya kai ƙan botton na rigar da ya soma cirewa, zara idanuwana ta yi a lokacin da taga ya ɓalle bottonan idanuwan shi sun yi jajir dasu jikin shi ya soma rawa cikin rawar murya ya ce
"Ke kaɗai na ke muraɗi, kuma ke ce wacce zata kashe min ƙishirwar da nake ji yanzu, please kada kimin gaddama nasan kin san komai kawai ni ne ba ki so amma ina mai tabbatar miki cewa sauran samarinki suna suka tara da ƙin ji salona zaki......
Jikin Hamrah na rawa tsoro ya rufe ta sbd bata taɓa kasancewa da namiji ba cikin wannan yanayin, da ƙyar ta tattaro karfinta ta hankaɗe shi ta miƙe tare da nufo ƙofar hannunta na rawa tana ƙoƙarin buɗewa ya yi saurin isowa ya rike ta tare da janyo ta ya haɗata da jikin garu yana sauke numfashi ya ce
"You do like baki san na miji ba alhalin kin san komai kuma....
Tasssss, ta wanke shi da mari da ya sanya shi saurin dafe wajen ta nuna shi da yatsa ta ce
Kayi kaɗan Mahmoud, kuma ka yi ƙarya ɗan iska ka kawai mara mutunci, think whatever you want amma ba zaka taɓa samuna ba.
Duk da jakircewar ta ya tsorata ta, ta dau wayar ta tayi sauri zata bar wajen ya biyota zai chapke ta aka turo ƙofar cikin sauri ta yi hanyar fita Dr Aliyu ganin hakan yasa ya matsa mata ta fice Mahmoud kuma ya tsaya suna kallon juna yana sauke numfashi, cike da mamaki Dr Aliyu ke kallon shi ya jefa nashi da tambayar
"Me ka ke shirin aikatawa?. Are you out of your mind, fyaɗe za ka yi mata"
Dariya Dr Mahmoud ya ce
"Rape, with who?. Bayan kuna sheƙe ayar ku tare shine za kace zan yi mata fyaɗe, gwada sa a ta naƙe"
Hankali Dr Aliyu ya matukar tashi ya ce
"Gwada sa'ah, hakan yana nufin ƙarya kamin ranan da ka ke cewa kasanta, kenan sharri kayi mata?"
Ya isa. Ku fice min daga cikin office, kada ku ƙara shigo min.
Cewar Hamrah tana tsaye daga bakin ƙofar, saka botton na rigar shi ya yi cikin sanyi jiki ya fice, ta sauke numfashi tare da dafe kanta bayan ta zauna
Special Doctor, ki yi hakuri da abin da na faɗa miki ranan nan, ban san cewa sharri ya yi miki ba.....
Please Dr Aliyu ka tashi ka fice, bana son jin komai da kai dashi duk halinku daya ne, tunda kunyi tunani iri ɗaya a kaina.
"A'a Dr Hamrah kada ki haɗani da wancan fasukin, na yi miki hakanne a rashin sani ki ya fe min"
Ta sauke numfashi tare da cewa
I need to be alone, please go back to your office.
Ya miƙe tare da sauke numfashi ya fice. Hamrah ta girgiza da abin da ya faru sakanin ta da Dr Mahmoud tabbas yana cikin maye ne amma za tayi maganin shi da zaran ya dawo hayyacin shi, har ta kwanta bacci ya ɗauke ta. Gari na wayewa ta shirya ta fito sbd da tafiya ta rufe office nata ta wuce office na Dr Aliyu wanda MD ya kwace kuma ya maida mashi abin shi, ta turo ƙofar ta shige ta tadda shi zaune shima ya kammala shirin tafiya ganinta yasa ta muƙe tare da cewa
"Barka da safiya?"
Barka dai, zan tafi sai Monday zan shigo.
"To likita Allah ya nuna mana, amma lafiya ko?"
Lafiya.
Kawai ta faɗa tare da ajiye mashi wasu document ɗin ta fice. Kai tsaye ta dawo gida ta shige ɗakin Ammie ta gaidata a lokacin ma Daddy ya shigo suka gaida ya ke ce mata
"Likita yau za ki tafi gidan Ayshe ko, to ayi ta hakuri fa kada kuyi abin da za ayi ta magana akai, Allah ya yi albarka"
Amen Daddyn, mun gode.
Ta miƙe ta dawo ɗakinta ta faɗa toilet ta shirya sannan ta fito daman kayanta a haɗe ta ɗauko tana ƙoƙarin fitowa Ammar ya shigo ganin haka yasa ya ce
"Zuwa ina kuma naga ko hutawa ba kiyi ba?"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Yauwa taimaka ka fitar min, sai ka nema min ɗan sahu ina sauri jirana suke.
Kallonta ya yi sbd ganin yadda ta ke magana kamar da ɗan 15 yrs wai ya je ya kira mata ɗan sahu, ya ɗauki kayan ya fita dashi ta bi bayan shi sai gani ta yi ya sanya cikin motar shi, ta ce
Kai ni za kayi da ka kiramin dan ɗan sahu, kai kam Allah ya shirya kana na miji baka son wahala.
Bai ce komai ba ya koma ya dauko kayan dake ɗakin Ammie daman ta ce zai kai anjima kawai zai haɗa su tafi tare. Ya fito ya tada motar ya kalleta tare da girgiza kai ta ce
Me kuma?.
"Ba komai, nima daman ina son zuwa gidan Ayshe"
To sai muje ai.
Ya ɗan juyo ya kalleta itama ta ɗago ta kalleshi ya sakar mata da murmushi ya ce
"Kamar kina cikin damuwa, akwai abin da ya faru ne a wajen aiki?"
Daram ƙirjinta ya buga da ta tuna da abin da ya faru da ita daren jiya. Bazata sanar dashi ba dan kuwa zai aikata mashi abin da ya taɓa aikatawa shekarun baya dan haka ta ce
Ba komai, ciwon kai ne.
Ya sauke numfashi ya ce
Ciwon kai, ciwon kai always shine amsa, anyway bakomi.
Sai da suka biya suka yi wa yaran siyayya sannan kai tsaye suka wuce gidan Ayshe.......
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 19 & 20
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
__________ Da ƙyar ta ke iya fidda numfashi tana sauke ajiyar zuciya on on zuciyarta na yi mata zafi sai gumi ta ke haɗawa, tana jin kanta na tsara mata zazzaɓi na neman rufe ta cikin ƙanƙanin lokaci. Ta juya tare da jan blanket ta rufe jikin ta tare da rumtse idanuwanta waɗanda suka kasa fidda kwallah sbd damuwa, a kullum sai tayi tunanin meyasa hakan ke faruwa cikin rayuwarta, yaushe zata ji ta cikin farin ciki kamar yanda kowa ke ji, yaushe iyayenta zasu daina faɗa a kanta, yaushe za a koma cikin farin ciki irin na rayuwar baya, yaushe, yaushe, yaushe?. Amma da ta tuna cewa ko wane bawa da irin ta sa jarrabawar sai taji sanyi cikin ranta, duk abin da ya yi farko yana da ƙarshe kuma duk tsanani yana tare da sauki kamar yadda bata taɓa zaton zata riski wannan lokacin ba haka bazata cire sammanin samun sauki nan gaba ba.
"Hamrah"
A hankali ta buɗe idanuwanta sbd jin muryar Ammar da ya ƙira sunanta, ta haɗiye damuwar ta tare da sauke numfashi ta fito da fuskar ta tare da ɗan kishingiɗe jikin bed ta ce
Ammar, na yi tunanin ka kwanta ai, shiyasa nima na kwanta sbd gobe Monday kuma morning duty gareni.
Ya sauke numfashi sosai ya ke kallonta, duk da tana ɓoye damuwarta kada ya gane amma tun shigowan shi ya riga da ya gane sannan yaji abin da iyayensu suke cewa, ko shi kanshi baya son irin yadda su keyi, sun daina jituwa da juna zaman lafiyar ma yanzu ba sosai suke yin ta ba, abin damuwar ma shine yanda Ammie ta ke ɗauka hot akan maganar, babban tashin hankalin shi shine tafiyar da zayyi ya bar Hamrah, yasan za tayi ta shiga damuwa gashi kuma zayyi nesa da ita babu mai kwantar mata da hankali. Ya sauke numfashi a hankali ya ce
"Ban kwanta ba ina chatting ne muna online meeting, muna gamawa ne na ce bari nazo sbd ɗazu kin ce kina son magana dani"
Ta kwakulo murmushi dole tare da cewa
Ammar, shin menene laifina akan zaɓar Alhaji Sama'ila da nayi, meyasa ka ke ganin bai dace na zaɓe shi ba, shin akwai abin da ya faɗa maka ne?.
Ajiyar zuciya ya sauke tare da kura mata idanuwa na wani lokaci yana jin tausayinta yasan tana yin wannan ne saboda ta sami kulawar Ammie ta samu ta sauko su koma daidai kamar yadda suke a cen baya har ake ƙiransu da ba a shiga sskaninsu sbd yadda suke shawara da juna koman Ammie Hamrah. Sai dai ya
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 19