ki kawo na gani"
To.
Ta faɗa sannan ta dawo office nata, a nutse ta fiddo su ta shiga dubasu kamar yadda ta keyi nan ta shirya komai ta kammala tsarawa ta ji ana nocking ta bada izinin shigowa Dr Laraba ce ta ke shaida mata OG ya iso an hallara a ɗakin meeting ta fito in ji MD, ta ce da ita tana fitowa.
A nutse ta fito ganin office na Dr Mahmoud da MD a kulle yasa ta sauke numfashi tare da furtawa
Thank God.
Ta iso a lokacin OG ma ya shigo ana gaisawa ta gaida shi, sanye yake da suit baƙi koman shi baki hatta eyes glass dake idanun shi ma baƙi ne, yana da haske ba cen ba ya cire glass ɗin ya ce
"Dr Hamrah lafiya kalau ya kokari"
Alhamdulillah sir.
Ta ajiye mashi komai ta ɗan kalli MD shima ita yake kallo sabar haushi kamar ya shaƙo ta badan OG ne ya ƙirashi ba da ko sai ya karɓi document ɗin ya sauya komai ya tafi daidai da na office nashi kada ya banbanta. Ya sakar mata da harara ta yi kamar bata ganshi ba ta yi murmushi ƙasa² ta ce cikin ranta da saura jira akwai wasan da baka san dashi ba yanzu za a fara buga shi.....
"Godiya ta tabbata ga Allah maɗaukakin sarki wanda yake bamu ikon akan komai, ina mai farin ciki da jin daɗin yanda ku ke gudanar da aikace-aikace a wannan asibitin kuma ina jin yadda jami'a ke yaba ku, Alhamdulillah, musamman ma Dr Hamrah tana na mijin ƙoƙari kuma ina alfahari da ita"
Cewa OG sai da ya kai aya ya yi shuru yana duban su sannan ya kai hannu ya fara duba document dake gaban shi a nutsu ya ke dubawa sai da yazo kan list na staff da partner su sai yaga na list da kuma office dake cikin document da MD ya bashi daban ya ke da wanda ya ke wajen Dr Hamrah, cike da mamaki ya ce
"Ya naga banbanci sakanin list of staff's and there duty's partners ya banbanta me yasa haka?"
Saurin miƙewa MD ya yi ya ce
"With do respect sir, ni ne na sauya sbd ci gaban wannan Hospital ɗin naga ƙanzawa shine zaifi kuma zai kawo cigaba"
Sauke numfashi OG ya yi ya ce
"To ya aka yi yasha banban da na Dr Hamrah, sannan kuma meyasa ka yanke hukunci ba tare da neman izinina ba"
Nan wuta ta ɗaukewa MD ya juyo da jajayen idanuwan sa yana kallon Hamrah ganin haka ta ɗauke kai kamar bata san yana yi ba ya sauke numfashi tare da cewa in kin san wata baki san wata ba, cikin ranshi ya faɗa a fili ya ce
"Eh na manta ne banyi comparing da nata ba but all this ya faru ne sbd rashin bada haɗin kai da bata yi ba"
Sosai OG ya ke kallon shi sannan ya ce
"For what reasons ta ki bada haɗin kai?"
Kai tsaye MD ya ce
"I don't know kawai bata girmama ni ne"
Murmushi Hamrah ta yi bata ce komai ba sai da OG ya kalleta ya ce
"Hamrah meyake faruwa ne, shin gaskiya ne MD ya ke faɗi?"
Cikin girmamawa ta ce
Eh sir amma ina da dalilina na yin hakan.
Ya kalleta tare da cewa
"Menene dalilin?"
Yana da ikon yanke hukunci amma kuma duk da haka ya kamata ya shawarce ni wajen kanza min partner kawai kwasam sai dai jin na yi ya ɗauke Dr Aliyu ya kaishi bangaren yara, sannan kuma ya sauke mishi albashin sa, a kullum neman ci gaba ake ba wai baya ba sannan hakan da ya yi takura ce da kuma jefa shi cikin damuwa shine naga hakan bai dace ba wannan ne dalilin da yasa naƙi bashi goyon baya.
Shiru wajen ya yi ya kalli MD tare da cewa
"Haka ne abin da ta faɗa?"
Ya tsosa keyarsa ya ce
"Haka ne amma.....
"Ya isa haka, na yi cansel na wannan transfer from office to another office dan haka kowa ya koma nashi office ɗin na da sai mun zauna zamu sauya"
Yana gama faɗin haka ya fice, MD ya daki teburin dake wajen yana huce wai always Hamrah, Hamrah, Hamrah. Ya fice a wajen ya wuce office nashi yana huce Dr Mahmoud ya shigo amma ya ɗaga masa hannu alamun ya fita, ya fice ya ci gaba da tunani zuci ya akayi ya faɗi a wannan lokacin amma yasan yanda zai bollowa al'amarin.
Hamrah cikin farin ciki ta dawo office nata, ko ba komai Dr Aliyu zai dawo office nashi ya ci gaba da aikin shi, tana so ta wanke kanta daga ganin cewa da ita aka haɗa baki aka cire shi daga cikin office nashi....
Turo ƙofar Dr Aliyu ya yi ya shigo cikin sanyin jiki, bata ɗago ba jin turo ƙofar yasa ta ke tunanin Dr Mahmoud ne ko MD har yanzu idanuwanta a lumshe suke ....
"Dr Hamrah"
Jin muryar Dr Aliyu ne yasa ta buɗe idanuwanta ta kalle shi, bata yi mamakin zuwan shi ba dan tasan zaizo amma kuma bata yi farin cikin ganin shi ba, har ya ƙaraso kusa da teburin ya zauna tare da cewa
"Dr Hamrah....
Dr Aliyu i don't need any word from you, please step out.
Sauke numfashi ya yi kamar zayyi kuka yana bukatar ta saurare shi amma yasan abu ne mai wuya sbd irin ci mata mutunci da ya yi, cikin sanyin jiki ya miƙe a hankali ya fice da nufin da ta sauko zai sake dawowa.
(Ji na da ku kayi shuru 2days rasuwa aka min naje na dawo. Masu addu'oi da kuma waɗanda suka ƙirani da waɗanda su ka yimin magana duk ina godiya, Allah ya bada ladan ta'aziya) littafin MUJARRABI labari ne mai ɗauke da sakonni daban daban ta ko wanne fanni kuma tafiya ce mai ɗan tsawo sai dai ina tabbatar muku cewa baza kuyi nadamar bibiyar labarin ba. Har yanzu muna cikin shinfiɗa asalin labarin na nan zuwa.
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 25 & 26
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
________Ganin ya rufe min baki yasa na waro idanuwana ina kallon sa sbd farga da tashin hankali cikin kankani lokaci na haɗa uban gumi a lokacin da na yi la'akari da ganin babu kaya a jikin shi sai gajeren wondo, ya sake janyo ni jikin shi na haɗe da ƙaton tumbi shi ya yi magana cikin dashesheyar murya tare da zaro min idanuwan shi alamun gargaɗi da kuma tsoratarwa ya ce
"Kada ki kuskura kimin gardama dan za ki sha baƙar wahala kuma ba kyaleki zanyi ba, dan haka is better for to accept me for the hours, bazamu jima ba amma kin kin bini yadda na ke so in kuma ba haka ba zan aikata miki abin da har ki mutu ba zaki dawo daidai ba"
Zuciyata taci gaba da bugawa na tsorata at the time na saduda dan na sadaukar babu mai ceto na a wancan ranar, jikina na rawa, sai zazzaro idanuwana nake sbd rufemin baki da ya yi babu yadda zanyi nayi magana balle kuma nayi mashi magiya, ganin babu sarki sai Allah na soma karanta duk adduar da tazo cikin zuciyata, ina neman tsari daga azzalumin mijin mahaifiyata.....
Fincikoni ya yi ya tadani zaune tare da yaga min rigar dake jikina daman doguwar riga ce, ganin haka yasa na kurma ihu ina rokon sa da ya kyaleni amma kuma sai ya yi kamar baijiba ya hankaɗe ni na faɗi ta baya kan bed ɗin ya danneni yana huce ya ce
"Kinci sa'a kina period ni kuma ina ƙyanƙyamin mace wacce ta ke cikin al'ada, amma ba komai zamu gamu nan da kwanaki"
Ya miƙe ya fice, na sauke numfashi na sake fashewa da kuka cikin ƙuna da takaici ace mijin mahaifiyata yaga jikina, wannan wane irin ƙazamin mutum ne mara imani da tsoron Ubangiji, sam ya manta da cewa akwai mutuwa. Na jima ina kuka sannan na miƙe na faɗa toilet na watsa ruwa na sauya kaya a daidai lokacin Mommy ta dawo gida, na fito palour duk na ka sa nutsuwa, ya fito ya tadda mu a zaune ya dubeni tare da cewa na kawo mashi tea na saka suger kaɗan a ciki. Da farko na ƙi amma kuma ganin Mommy ta bata fuska sbd ganin naƙi tashi yasa na miƙe na wuce kitchen na haɗa, tun daga wannan ranar ya sanya min ido duk motsina a kan idanuwan shi ko me yake dubawa oho, sai dai kuma indai ya aike ni ɗakinshi bana zuwa, da ya fuskanci hakan shine ya ƙirƙiro cewa yana meeting a guest House nashi dan haka Mommy ta dinga aika mashi abinci, a tunanin sa ni zata dinga aika amma kuma sai yaga driver ne yake kaiwa, ranan ya yi waya akan ta turoni da kulolin abincin akan na zanyi serving baƙin, da farko naƙi amma ganin Mommy ta ɓata fuska yasa nabi driver na tafi, a lokacin da muka iso sai ya sallame driver ya rage daga cikin sai shi, rarrabe idanuwa nakeyi ko zanga baƙin amma kuma babu kowa, shuru banji motsin shi ba na soma tafiya, na iso kofar palour na murɗa handle door amma sai najisa gam a rufe, nayi² na buɗe yaƙi sai naji motsin fitowa na juya muka haɗa 4eyes da da daddy ɗaure yake da towel a kugun shi, cikin tsoro da firgice na fiddo ita waje ganin yana yimin murmushin mugunta, a tsorace na ci gaba da murɗa handle door ko zai buɗe dan na fahimci plan ya hada amma yaƙi, cikin sauri ya finciko ni na faɗai kasan tyles na buga kaina nan ta ke ya fashe bai ko tausaya min ba ya janyoni a hakan ina zubda jini yana jana har ta kusa ƙofar ɗakin shi muka jiyo an danna door bell, cike da mamaki yake dubana ina cikin mawuyacin hali bazan iya tashi ba balle kuma nayi magana, ya wuce baƙin ƙofar ya leƙa ta maleƙa ganin wacce ya gano ne yasa ya yo kaina a guje cikin tashin hankali ya yi cikin ɗakinshi tare da ɗauko wani kyalle ya ɗaure min bakina baibi ta jinin dake malale kan fuskata ba ya buɗe ɗan wani karamin ƙofar ya sakani cikin sannan ya wrgani ya fice bayan ya ɗaure min hannayena, ina jin motsin shigewar sa ɗakinsa da kuma goge inda jinin ya ɓata, sannan ya buɗe ƙofar palour sai jin muryar Mommy nayi tana
"Ikon Allah, ya naga gidan shiru ina ɓakin ne?"
Da ƙyar na miƙe ina bin jikin garu na leƙa ta wani rami ina hango su, gani nayi ya tsosa keyarsa ya ce
"Ai cewa su kayi sai yamma zasu iso"
"To ina kuma Shatu tayi gashi bata nan ɗin ma?"
"Ai bai jima ba ta tafi gida"
"No driver kaɗai na gani na tambaye shi yace ya barota anan, to daman miyar kuɓewar ce ta tuwan shinkafar suka manta shine na fito dashi daman unguwa zan wuce"
"Ai Shatu bai jima ba ta fice, nayi mamaki ma da baku haɗu ba"
"To daman wucewa zanyi ga miyar nan"
Ta ajiye ta juya da niyyar tafiya kuma ta tsaya tare da cewa
"Jini........
Ringing na wayar Hamrah ce ta katse labarin da Shatu ke bata, ta kalleta tare dayi mata alamun bari na ɗaga, Daddyn su ne ta ɗauka cikin girmamawa ta gaida shi ya amsa yake tambayar ta, ya su kayi bikin, ta amsa da komai lafiya sannan su kayi sallama, ta kalli Shatu dake zaune dirsham kan carpet sai a wannan lokacin tayi la'akari da ciwon dake goshinta ta sauke numfashi tare da riƙe hannun Shatu ta ce
So sorry bestie ashe kina cikin mawuyacin hali banne meki ba, meyafaru bayan Mommyn ki ta kalli jini?.
Sauke numfashi Shatu tayi tare da share hawayen dake kan fuskar zatayi magana sai suka jiyo an turo ƙofa an shigo, Zeenat ce suka gaisa ta ce
"Yaya Hamrah dangin mijin Ayshe sun shigo injita wai ki tarɓesu"
Ajiyar zuciya Hamrah tayi tare da cewa
Ina fitowa.
Zeenat ta fice, Hamrah ta ce da Shatu
Ƙawata ina zuwa ɗan bani muntuna bazan.....
Wayar Shatu ta hau ruri ta ɗauka tare da cewa
"An gama kenan zan iya tahowa?"
Ba tare da Hamrah taji mai aka ce ba sai jin Shatu tayi ta ce
"Ok on my way"
Ta katse wayar tare da kallon Hamrah wacce itama ita ta ke kallo ta ce
"Lawyer na ne ya ƙirani, zan tafi, zuwa gobe zan tafi gidan ku na ƙarashe miki labarin"
Lawyer kuma?.
Cewar Hamrah tana takewa Shatu baya suka fito ganin jama'ar dake palour yasa Shatu ficewa ba tare da sunyi sallama ba, Hamrah ta hau hidima dasu sai bayan la'asar ta huta shima a lokacin ake shirye shiryen shigowa da Amarya wajen uwar gida ta shige ɗaki ta kwanta sbd kanta dake tsara mata, lallai Shatu na cikin bala'i wannan wane irin tashin hankali ne, sai 4:30pm aka shigo da Amarya sukayi buɗan kai sannan aka watse.
8:00pm ta kammala shirin tafiya gida suka fito ita da Zeenat da kuma Maryama, Ayshe tayi² su sake kwana amma suka ce zasu tafi Hamrah kuma tana da morning duty gobe kuma Monday ne sai ta koma gida ta shirya Ba zayyu ta kwana anan ba da safe ta wuce, a haka ta hakura suka fito Maryama mijinta ne yazo ɗaukanta ita kuma Zeenat driver ya tura, Hamrah na ƙoƙarin fitowa bakin layin unguwar su Ayshe taga call na Abuja kamar bazata dauka ba ta ɗauka cikin sanyayyar tayi sallama ya amsa tare da cewa
"Baby nah, kwatantamin unguwar da kike yanzu zan iso"
Ta sauke numfashi tare da cewa
Oh yanzu haka na fito zan koma gida.
"Ba damuwa gani nama iso faɗa min layin?"
Ta sanar dashi, aiko babu jimawa sai gashi ya iso da kansa yake tuka motar yayi parking a kusa da ita ya fito tare da sanya mata kayanta cikin boot na motar ya buɗe mata ta shige ta zauna, sanyi da ƙamshin dake cikin motar yasa ta lumshe idanuwanta tare da sauke numfashi, ya shigo ya tada motar suka fito daga layin sai dai kuma sai taga ya ɗau wata hanyar ba inda ta ke tunanin za taje ba, cikin sauri ta kallesa ya sakar mata da murmushi ya ce
"Yi hakuri baby zan bada saƙo ne sai na maidaki gida"
Ta ɗan sauke numfashi ba ta ce komai ba suka wuce Hotel ya yi parking a bakin gate ɗin ya kalleta tare da cewa
"Baby nah yi min rakiya na bada saƙo sai mu fito"
Kai tsaye ta ce
A'a ka shiga ka fito.
Ya yi murmushi ya ce
"Kamar kina shakka a kaina, na yi tunanin yadda na yarda dake haka kema ki ka yarda dani, amma ba komai jirani na shiga na fito"
Ya fice, tana zaune tana kallon yadda ake shigowa da ƴan mata da kuma fita dasu tana mamakin meyasa Alhaji Sama'ila ya sauka a hotel, kuma ace duk faɗin garin Maiduguri yarasa masauki....
"Sorry baby na jima ko?"
Ta kalleshi bata ce komai ba har ya tada motar ya kawo ta ƙofar gida, zata fito ya yi saurin cewa
"Baby nah kamar kina fushi dani, Please faɗamin laifina sai na bada hakuri"
Tayi ajiyar zuciya tare da cewa
Ina so muyi magana amma ba yanzu ba duk na gaji ina so na huta, sai dai ko gobe.
Murmushi ya yi yana mamakin irin kaifin brain nata ya ce
"Ba damuwa gobe zan zo da yamma ko kuma bayan ishai sai muyi magana"
To Allah ya kaimu.
"Amen"
Ya faɗa tare da saukowa ya cire mata kayayyakin ta sai ganin Ammar ya yi ya zuba masa na mujiya ya ɗaga masa hannu tare da cewa
"Ɗan saurayi taho mana ka taimakawa yayarka"
Ammar ya cika ya yi tam kamar ya haɗiyi zuciya, kut lallai wannan mutumin.....
Ammar zo ka taimaka min kaji.
Ba zaiƙi taimakawa yayar shi ba ya iso ba tare da ya kalli inda Alhaji Sama'ila yake ba ya ja luggage na Hamrah ya yi ciki dashi, ta bi bayansa yana ganin ta shigo ya kalleta ya ce
"Hamrah ki jawa wannan tsohon kunne ya fita cikin harkata ya kuma iya bakin sa dan kin bashi dama bazayyu ya yi duk yadda yake so ba damu"
Murmushi tayi ta ce
Ammar mijin da zan aurane so yana da daman ya aiki ƙanina sanan kaima ai ƙanine gareshi.
"Kai ina wannan tsohon ya yi ɗa dani wallahi, kina gani duk ya kusa sheƙewa"
Bata kulashi ba ta wuce ciki ta barshi yana ta huci, ɗakin Ammie ta shige ta ajiye mata sakon da Ayshe ta ce a bata, ta amsa tare da yi mata tambaya akan komai ya tafi daidai ta bata amsa da eh Alhamdulillah, sannan ta wuce ɗakinta tadda Ammar zaune ya kunna tv yana kallo ta ajiye jakar hannunta ta faɗa toilet ta watsa ruwa sannan ta fito ta shirya ta zauna bakin bed ta kalli Ammar ta yi murmushi ta ce
Ammar jibi warhaka baka nan.
"In shaa Allahu, ina cen ABGANISTAN ina shan snow"
Murmushi tayi ta ce
Zanyi kewarka zan kasance ni kaɗai cikin gidan nan.
Jikin shi ya yi sanyi ya juyo ya ce
Ai zan dawo, kuma zamu dinga waya.
Hakane kam.
Sun jima suna fira ya tashi ta fice ita kuma ta kwanta bacci. Washegari tunda ta tashi ta shirya ta fice kada ta makara, ta iso a daidai lokacin ƴan night duty sun fara tafiya ta buɗe office nata ta shige ta shirya komanta ta sanya white coat nata da kuma white eyes glass nata tana ƙoƙarin fitowa Dr Aliyu ya shigo ya gaidata babu yabo babu fallasa ta amsa ta ce zata wuce general ward nan ya bi bayanta, sun jima acen yana taimaka mata sannan suka dawo. 5:00pm na yi ta shirya ya fito ta dawo gida, ta wuce ɗakin Ammie ta gaidata tare da sanar da ita akan Alhaji Sama'ila zaizo anjima, amma harda murmushi ta ce
"To sai kije ki shirya mashi snacks ko, to Allah yayi albarka"
Amen.
Hamrah ta miƙe cikin farin cikin ganin Ammie ta saki fuska, ta faɗa toilet ta watsa ruwa kamar yadda ta saba ta shirya ta gabatar da sallah tana kan dardumar sallah har aka kira ishai ta idar Alhaji Sama'ila ya kirata akan ya iso ta sanya hijabinta ta fito taci karo da Ammar dake ƙoƙarin shigowa ɗauke da niƙe² kaya ya ce
"Ya kamata yau muyi fira dan gobe zan tafi"
To Ammar na yi baƙo sai na shigo.
Ya haɗe fuska ya wuce ciki, ta fito ta taddashi zaune, ta yi masa sannu da zuwa ya amsa tare da kura mata idanuwa ko ruwa bata kawo mashi ba ballantana snack tasan ba ci zayyi ba ya ce
"Ranki shidaɗe na iso ina sauraronki, da fatan ba laifi na yi ba?"
Ta sauke numfashi tare da cewa
A'a ko kusa ba laifi kayi ba, daman so nake nasan waye kai, tunda kasan ba zayyu mu gina rayuwa cikin duhu ba.
"Alhamdulillah hakan yana nufin kin amince dani, to na gode da wannan karamcin. Sunana Alhaji Sama'ila kamar yadda ki ka sani, mazaunin garin Abuja kuma ni ɗan siyasa ne kuma ita ke kawoni nan Maiduguri, ina da mata ɗaya da kuma ƴaƴar 7 ina so ne na aureki sbd na yaba da hankalinki kuma naji inason na haɗa zuria dake"
Ganin ya yi shuru yasa ta ɗago, ya sakar mata da murmushi ya ce
"Is that enough?"
Ta sauke numfashi ta ce
Eh.
Daddyn ta ne ya shigo ya yi parking, ganin haka yasa Hamrah miƙewa tsaye tana sudda kai, ya iso inda suke cikin girmamawa Alhaji Sama'ila ya gaida shi nan ya ce ta shiga ciki za suyi magana, ta wuce ciki, sai ganin Ammie ta yi a tsaye a palour ta ce da ita
"Ya na ganshi da Daddyn ku?"
Eh Ammie magana zasu yi.
"To madalla abu ya yi kyau"
Umm Ammie ina so muyi magana.
"To bismillah zauna mana"
Hamrah ta zauna tare da cewa
Daman akan Alhaji Sama'ila ne, bakon nawa akwai abin da ya ɗaure min kai game da shi.
"To menene kuma?"
Ammie a hotel ya sauka kuma ya ce dani yana da mata ɗaya da ƴaƴa 7 sannan shi ɗan siyasa ne, to amma ni zaman hotel ɗin ne bai kwanta min ba....
"To sannu ƴar iya, tun da mu bamu sani ba ke ce masaniyar komai ko to ki sani aure babu fashi bari Daddyn ku ya shigo naji ya su kayi zan sake tabbatar mashi da cewa wannan karon dole sai anyi in yaso da kunyi aure ya dafa ki ya cinye ki, mutum ya tako ya bar iyalin shi ya taho domin neman aurenki amma ki ce wai kina tantama shi baice yana tantama a kanki ba da ki ke kwana wajen aiki sai ke. To ki sani wannan karon ba zan lamunta ba, ya zama dole ki amince"
Jikin Hamrah ya yi sanyi ta ce
"Ki yi hakuri Ammie"
Ammie ta shige ciki, cikin fushi Hamrah na zaune ta shiga zurfin tunani ta ji muryar Daddyn su na cewa
"Hamrah jeki baƙonƙi na jiranki kuyi sallama"
Jiki a sanyaye tare da jin kunya ta miƙe ta fito ta tadda shi yana tsaye ta ce
Zaka wuce ko?
"Au korata ma ki ke to ki sani yanzu na zama ɗan wannan ahalin ne"
Murmushi ta yi ta ce
To da wuri haka.
"Yes Daddy ya ce na turo da manyana"
Daddyn kenan, to ya yi kyau.
Ta mai rakiya ya tafi ta dawo ciki ta wuce ɗakin Ammar, yana zaune yana shirya katanshi ya ki kallonta, ta fahimci fushi ya ke ta zauna kusa dashi tare da sanya hannu tana maimaka mashi suna shiryawa tare ta ce
Fushi ka keyi?
"Eh kinsan daga gobe ba zamu sake zama muyi fira ba har sai na je na dawo shine ki ka jima"
Murmushi tayi ta ce
Daddy yazo ya tadda ni da Alhaji Sama'ila sun tattauna kuma ya ce ya turo magabatan shi.....
"What?"
Cewar Ammar yana zaro idanuwana waje..........
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 23 & 24
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_______ Horn ya yi a daidai ƙofar gidan Ayshe bai fi 2 minutes ba gate man ya buɗe suka shige ya yi parking a area park/ parking space sannan ya kashe motar Hamrah ce ta fara fitowa tare da ƙoƙarin sauke kayan dake boot na motar, ya matso ya taimaka mata, sbd nawinsu da kuma yawansu, kasancewar gidan yana da gate 1 and 2, one ɗin shine side na Ayshe two ɗin kuma na patients na mijinta, dan haka gate 2 abuɗe yake sai kaiwa da komowa mutane keyi, Ammar ya dauki kayan ya yi bangaren Ayshe dashi gate man ya taimawa Hamrah su kayi ciki da ragowar. Da sallama Ammar ya shiga ta bi yansa yaran na ganin su su kayo kansu suna oyoyo Mommy Hamrah and Uncle Ammar, ya ajiye kayan ya rungume su, suna dariya ya ɗaga little Hamrah yana cillata sama tana dariya sauran suka je ga Hamrah sukayi mata barka da zuwa, ta wuce ciki bayan sun ta amsa ya tsaya suna ta yi mashi fira, ya riko hannun little Hamrah dake ƙoƙarin bin namecynta, itako Hamrah a gajiye ta ke tashige ciki ta tadda ɗakin da akwai baƙi ta shiga ƙawayen Ayshe ne da kuma wasu daga cikin dangin mijinta, suka gaisa a lokacin Ammar ya ƙaraso ganin da baƙi yasa ya koma ɗauke da little Hamrah sauran yaran ma suka bishi waje, Hamrah ta dawo palour ta zauna Ayshe da Zeenat suka fito, murmushi Hamrah ta yi bayan ta karewa Ayshe kallo ta yi kyau tayi kitso da ƙunshi, uwar gida...
"Yaya Hamrah barka da zuwa, nayi tunanin sai zuwa yamma za ki shigo in kin tashi a wajen aiki, tun ɗazu zaman kaɗaici nake"
Cewar Zeenat tana ƙoƙarin zama da ƙoton cikin ta, murmushi Hamrah ta yi ta ce
Night duty na yi da safen nan na dawo shine na shirya na taho nan, ya ƙarfin jiki?.
"Hmm kedai bari gashi dai abu yaƙi fashewa duk na gaji"
Da alamu baza ki wuce next week ba in shaa Allahu, ke dai ki dage da addu'a.
"Allah ya karɓi addu'ar ki"
"Yaya Hamrah, sannunki da gajiya?"
Cewar Ayshe, Hamrah ta ce
Lafiya kalau uwar gida, ya shirye shiryen bikin?.
Turo baki Ayshe ta yi ta ce
"Na kula fa kina goyon bayan babanki a wannan abin"
Dariya Hamrah ta yi ta ce
To in ban taya Daddyna ba wazan taya, in kuma ta fiki kulawa da Daddyna sai na so ta fiye da ke?.
Miƙewa Ayshe tayi ta wuce ciki wai a dole zancen ya ɓata mata rai. Murmushi Hamrah ta yi ta juya suna fira da Zeenat Ammar ya shigo ɗauke da little Hamrah ta taho wajen namecynta ta kwanta jikinta Hamrah
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 19