rayuwar kika zaɓarwa kanki, to ki sani kiji tsoron Allah ki fidda miji kiyi aure in kina so mu shirya a cikin wannan gidan, dubi kannenki duk sun yi aure sun rufawa kansu asiri amma ke kin tona wa kanbki da kuma mu asiri kina duk abinda ki kaga dama, to ki sani ba zan zuba ido naga kina yin haka ba, na baki nan da karshen wata ki fidda miji in kuma ba haka ba daga ni har ke ba zamu ji daɗin abin da zai faru ba, kin sa sai zancen ki a keyi a family da kuma unguwa kin tsaya zaɓe SBD kyawunki na ruɗan ki to ni ba zan lamun ta ba"
Numfashin HAMRA sama² ya keyi hankalin ta ya matukar tashi dajin waɗannan kalaman daga bakin mahaifiyar ta, daman shine dalilin da ya sa take fushi da ita....
"Hajjiya BATULA ba na hana a dinga wa HAMRA irin wannan zancen ba, ina mun riga da munyi magana akan hakan, mesa kuma yau ki ke tada zancen, lokaci ne bayyi ba in yayi za ayi shi kamar yadda a kayi na sauran"
Cewan Daddyn su, ya ƙaraso wajen tare da isowa wajen HAMRA cikin kulawa ya ce
"HAMRA ki shige ciki ki huta, nasan kin kwana aiki duk kin gaji Allah ya bada ladan taimakon da ki ke badawa"
Ameen.
Ta ce, ya juya ya fice, Ammie ma ta shige ciki, HAMRA ta juyo tana hawaye zata shige ciki sai ganin AMMAR tayi yana tsaye cikin damuwa yana kallonta da alamu ya ɗan jima a tsaye saurin buɗe ɗakinta tayi ta shige, a hankali ta ajiye kayan hannunta, ta fashe da matsanancin kukan da bata taɓa yin irin saba, daga jiya zuwa yau ta shiga tsananin tashin hankali sbd abinda taji kuma ta gani, fushin Ammie da kuma kalaman ta sun fi ɗaga mata hankali ina zata waiga taji sanyi ne, mahaifiyar ta ma ta juya mata baya.....
Alhamdulillah ala kulli halin.
Ina godiya ga Ubangiji da ya sake bani damar sake rubuta wani littafin, ina rokon shi kamar yadda na fara ya bani ikon kammalawa lfy.
Tafiyar wannan littafin mai rai ce, kuma ba za kuyi nadamar karanta shi ba. Ƙunshe yake da darussa da dama, kuma zaku ƙaru da su.
Zan dinga skipping rana ɗaya na posting sbd na sami nutsuwar typing.
Comments and share[1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 3 & 4
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_______Ƙirjinta yana mata raɗaɗi da zugi kamar zai fito, a hankali take sauke numfashi tana zubda hawaye, tana tuna irin rayuwa ta farin ciki da gata da ta ta yi tare da Iyayenta da ƴan uwa ta. Taso cikin gata da kulawa bata taɓa sammanin zata riski irin wannan rayuwar ba, ta ƙunci da tashin hankali. Basu taɓa ganin iyayen su sun sami saɓani da juna ba sai akanta, kuma wannan duk yana faruwa ne saboda rashin auren da batayi ba, da farko anyi ribibin fitowa neman aurenta amma sai kuma daga baya shuru babu wanda ya ce yana ma sonta balle kuma a je ga zancen aure, har aka aurar da ƙannenta....
"HAMRA"
A hankali ta ɗago ta kalle shi, damuwa ce kan fuskar shi sosai kamar zai taya ta kuka, yana mai jin tausayin ta sosai kuma baya son ganin ta tana cikin damuwa, shi ya zame mata abokin kukan ta kuma abokin shawaranta, ganin tana kallon sa kuma tana zubda kwallah yasa ya miƙa mata roban swan water tare da glass cup, ta karɓa ta siyaya ruwan ta sha, sannan tayi ajiyar zuciya a hankali furta
Thanks.
Sauke numfashi yayi ya ce
"Kuka baya miki kyau, kin san me ki ke komawa in kina kuka?"
Ba tayi magana ba tayi shuru tana kallon sa ya ce
"Kamar shrunk"
Murmushi tayi ta share hawayenta daman abin da yake son gani kenan, ta ce
Baka fita bane?.
"Uhm sai zuwa anjima, shima saboda ana neman mu ne zamu yi meeting akan tafiya training na sojojin da muka sa gaba"
Ta sauke numfashi tare da sake zuba ruwan ta sha sannan ta sake cewa
Wacce ƙasar ma zaku je?
"ABGANISTAN"
ya faɗa yana kallon ta tare da murmushi akan fuskar sa.
Uhm ya yi kyau, Allah ya taimake ku. Ta faɗa tana ajiye roban swan water da kuma glass cup ɗin
"Ameen"
Sosai ya juyo yana kallon ta ya ce
"HAMRA, ke ki ke cewa mu koyi jure wa ko wacce irin damuwa, mu rufe idanuwan mu kamar bamu gani ba sannan mu toshe kunnuwan mu kamar ba muji ba, amma mesa ke ki ka kasa yin haka, though a baya ki nayi but this time around kuma kin saduda, kin manta cewa duk tsanani yana tare da sauki, in shaa Allahu nan bada jimawa ba komai zai zama tarihi, za ki yi rayuwar farin ciki kamar yanda kowa ke yi, Please kada ki damu da yanayin da Ammie ke nuna miki ita ma zuwa wani lokaci za ta daina"
Ta sauke numfashi a hankali ta sake cewa
Thank you AMMAR.
Ya miƙe ya fice, ita kuma ta tashi ta shige toilet ta watsa ruwa sannan ta fito ta shirya cikin doguwar riga mara nawi, ta hau kan bed tana jin yunwa ga kuma bacci da ciwon kai da take ji...
Da sallama ya shigo ya ajiye basket dake hannun shi ya ce
"Tashi ki yi breakfast, nasan ba abinda kika ci".
A hankali ta sauko tare da cewa
Kamar kasan yunwa nake ji, shiyasa nake kara son ka ɗan KANINA.
Murmushi yayi ya ce
"A'a ya kamata zuwa wannan lokacin ki barmin girman nan daman cewa a ke yi ke ƙanwarta ce"
Murmushi tayi ta ce
Ai koda girgiza kurna tafi magarya girma.
Yayi murmushi ya ce
"Ba haka karin maganar take ba, cewa a ke yi ko da girgiza magarya tafi kurna zaƙi"
Uhm nawa ne daidai.
Suna fira tana cin indomie da kwai da ya soya mata, har ta kammala sannan ya mata sai anjima ya fice, ta ɗan zauna jim kaɗan sannan ta kwanta bacci sai azahar ta farka bayan ta idar ta sake komawa bacci sai bayan la'asar ta tashi ta idar sannan ta wuce kitchen tare da duba menene akwai, gannin Uwale ta kammala haɗa stew yasa ta fere doya ta dafa sa fari sannan ta zuba a plate tare da zuba stew akai ta dawo ɗakin ta, nan ta ci tare da haɗa tea na ruwan zafi ta sha sannan ta tashi ta shirya ta fito. Ɗakin Ammie ta shige tayi mata sai da safe amma bata kulata ba, hakan yasa ta fito cikin sanyin jiki, ta tadda Daddyn su na zaune a farfajiyar gida ta iso cikin girmamawa ta ce
Daddy zan wuce wajen aiki.
Cikin kulawa ya ce
"Likita Allah ya taimaka sai kin dawo, ayi ta hakuri da sha'anin rayuwa"
To Daddy in shaa Allahu, nagode.
Nan ta fito, ta tari ɗan sahu ta wuce wajen aiki.
Tana shiga cikin Hospital ɗin ta wuce office nata, ta kimtsa duk abin da zata buƙata anjima da daddare sai ga Dr Aliyu ya shigo cikin sallama, ta amsa ya ce da ita
"Special Doctor an fito ko?"
Tayi murmushi tare da cewa
Yau kuma harda zolaya?
"Ai gaskiya ce kuma kowa ya shaida ke ƙwararriya ce ta fannin aikin ki"
Uhm to ina godiya.
Ta faɗa idonta a kan system nata, ya ce
"MD ya ce akwai zaman ku dashi bayan magrib"
Ta sauke numfashi tare da ɗagowa ta kallesa ta ce
Badamuwa Allah ya kaimu.
Matukar burge shi take SBD jarumtarta duk cikin Hospital ɗin nan tsoron MD ake amma ban da ita, ya sake cewa
"Amma bakya tunanin ko abin ya shafe abin da ya ce kiyi jiya da daddare kuma...
Dr Aliyu ni in dai a kan gaskiya ta ce ko ina a kaini, meyasa kuke tsoron sa shifa ɗan Adam ne kamar kowa sannan kuma kowa yana da right na kare kan shi so, banga wani abin tada hankali ba, I'm waiting for the hours.
Ya sauke numfashi ya ce
"Well don special Doctor till we meet later, an fara kiran sallah sai zuwa anjima"
Ya miƙe ya fice, ta sauke numfashi tana mamaki sauran likitoci da suke neman gindin zama a wajen MD shi da ba wani aiki yakeyi ba kawai dai yana zagoyowa ne yana taking information akan wasu abubuwan amma duk da haka suke ɓata ta a wajen sa a cen baya tayi tunanin Dr Aliyu ne amma da tayi bincike ta tabbatar likitoci mata ne ke kai masa gulmanta shiyasa ta share su baki ɗaya indai ba sha'anin aiki bane ya haɗasu to bata shiga tsabgarsu, jin ana kiran sallah yasa ta miƙe ta shige toilet ta ɗaura alwala ta fito ta idar sannan ta wuce office na MD tana isowa ta tadda sa yana waya a waje ta shige ciki ta zauna har ya kammala ya shigo cikin girmamawa ta ce
Afternoon sir, an ce kana nemana.
Ya cire white eyes glass dake idonsa ya ajiye sa kan tebur dake gaban sa ya kuramata jajayen idanuwan sa na wani lokaci sannan ya ce
"Jiya saƙo na ya iso ki ko bai riske ki ba"
Kai tsaye ta ce ya riskeni.
Ya sauke numfashi ya ce
"Kinyi yadda na ce ko kuma kinyi abin gaban ki?"
Ta sauke numfashi tasan yaji labarin komai kawai yana so ta tabbatar masa ne ita kuma baza ta yi ƙarya dan ta kare kanta ba ta ce
Ina da patients waɗanda na ke kulawa dasu, kuma na yi musu alkawarin cewa zan basu kulawa har su sami lfy, shiyasa na fara duba su sannan na duba.....
"Who the hell you are da zakiyi abin da ki ka ga dama dake da patients ɗin ai duk a karkashina kuke, daga yau muddin na ce ayi abu kika sauya to ki sani dole ki bar wannan Hospital ɗin, kina ganin tafiyar ki zai sauya komai ne, we'll work even without you, sai me dan kinga OG yana yabon ki shine ki ke wani ganin kan ki kin fi kowa, to ki sani banga wanda ya isa na saka doka ya karya ta ba a duk faɗin duniyar nan"
Sosai ta rumtse idanuwanta SBD tsawar da ya daka mata, ta tsani ayi shouting mata akai, nan take take gigicewa, hankalinta ya tashi kuma ranta ya ɓace bata san lokacin da ta miƙe tsaye ta nunasa da yatsa ba ta ce
I'm not a young girl, kada ka sake min ihu, a kan wane dalili kake faɗa min waɗannan maganganun? da kake cewa zaka koreni ɗin ai ba kai ka bani wannan aikin ba sai dai OG ya koreni ko da kuwa zan bar wanna aikin, to ka sani ba ta dalilin ka ba, kai kan ka kasan abin da kayi bai dace ma, ta yaya muna aiki domin ceto rayukan al'umma zaka ce a barsu su sha wahala kai a duba naka, wannan ba adalci bane.
Tana kaiwa nan ta fito tabarsa baki sake yana mamakin ta, lallai HAMRA bata san waye shi ba, tana dai jin labarin shi ne, amma soon za ta sani. Tana shiga office kanta ya soma tsara mata saboda ihun da yayi mata, maisa MD bashi da imani ne, kowa yana complain na shi a bayan idon sa akan irin zaluntar mutane da yakeyi. Ta sauke numfashi ta shige toilet ta ɗaura alwala ta idar da sallah ishai sannan ta wuce duba marasa lafiya yau kam ta daɗe a wajen su, mutanen MD kuma Dr zalihat ce ta duba su, HAMRA sai kusan 1:00am ta dawo office ta saka key ta rufe kofar sannan ta kwanta.
Da safe ta tashi a makare ta gaggauta isar da sallah ta ɗau jakarta ta fito har ƴan morning duty sun iso, bayan sun gaisa ne ta fice kasancewar safiya ce ana wahalar abin hawa saboda kai yara makaranta, hakan yasa HAMRA takowa zuwa bakin titi, tana tsaye tana jiran abin hawa amma duk wanda yazo wuce wa sai taga cike yake da mutane. Har ta gaji da tsayuwa ta yanke shawarar ko ta sake yin gaba ne sai taga wata bak'ar mota jeeb mai liƙe da bakin glass ta tsaya kusa da ita, kau da kai gefe tayi kuma take shirin barin wajen taji an ce
"Wa nake gani haka kamar HAMRA pretty kece?"
Jin muryar mace ce yasa ta tsaya tare da juyowa ta kalle ta cike da mamaki ita ma ta ce
Hauwa'u Jibrin! Kina wannan duniyan?.
Aiko ba shiri ta fito daga cikin motar ta tana cewa
"Wata sabon gani inji Hausa people, HAMRA pretty ashe zan sake ganin ki, rabo na da saki cikin idanu na tun a secondary School fa, from where?"
Uhm Hauwa'u daga wajen aiki nake.
"What?.
Ta faɗa tana koƙarin gyara parking na motar ta fito sannan ta ci gaba da cewa
"Aiki daman ana aiki ne a wannan zamanin ai zuwa aiki ɓata lokaci ne, yanzu da wannan kyawun naki ki ke aiki"
Uhm kina nan kamar yanda na sanki, daman an ce in dai ka jima baka haɗu da mutum ba to kada ka tambayi halinsa saboda hali zanen dutse ne baya taɓa kanza wa, to in ba abin ki ba Hauwa'u in dai banyi aiki ba me kike so nayi?"
"Shigo cikin mota na ƙarasa dake gida sai mu ƙarasa gaisawa".
A tare suka shige cikin mota da mamaki HAMRA ke kallon ta, ganin ita kaɗai ce a cikin motar yasa ta ce
Kin kai kids naki skul ne?.
Dariya Hauwa'u tayi sosai tana tuki ta ce
"Ki jiki wai na kai yara makaranta, ni da ko auren ban yi ba, ina na ga yaran?"
Cike da mamaki da kuma tausayawa HAMRA take kallon ta ce
Ayya ki ce duk jirgi ɗaya muke.
"Don't tell me HAMRA pretty wai da gaske ba kiyi aure ba duk da wannan kyaun naki, to ina ga mu kuma munana"
Uhm Hauwa'u ai shi aure ba wai kyau ko rashin sa yake dubawa ba lokaci ne, abin da yasa na tambaye ki ko yara ki ka kai skul shine ganin ki da nayi da wannan motar.
Murmushi Hauwa'u tayi sosai ta ce
"Har yanzu a gidan ku na da ku ke?"
Eh a nan ne.
Cewar HAMRA tana kare mata kallo, sanye take da doguwar riga ta habaya baƙa ta yane gashin kanta da gyallen duk da ma tulin kitson Attachment da tayi duk ya baje mata a baya hakan yasa gyallen habayar kasa rufe kanta, farcen yatsun hannayen ta sun sha janfarce, da kuma zobe, ga kuma bleaching da tayi sosai duk fuskar ta fita hayyacinta. Sauke numfashi HAMRA tayi a daidai lokacin da suka shigo layin su Hauwa'u ta ce
"Ni ina Shatu, What i mean Aishatu Muktar?"
HAMRA ta buɗe kofar motan ta fito saboda parking ɗin da Hauwa'u tayi a daidai kofan gidan su ta ce
Shatu tana nan fah amma yanzun tayi tafiya.
"Ikon God kai rayuwa! SUCH IS Life, did she get married?"
No, ita ma har yanzu like us.
Kurawa HAMRA idanu Hauwa'u tayi na wani lokaci sannan ta ce
"To a zaman ki yanzu haka me kike yi ne bayan aikin nan, i mean kina da wanda yake ɗebe miki kewa ne ko kuma in ce masu ɗebe miki kewa"
HAMRA bata fahimci zancenta ba ta ce,
I didn't get you, what do you mean by that, though zan iya cewa aikina kaɗai yana ɗebe min kewa.
Murmushi Hauwa'u tayi kai tsaye ta ce
"Zaki ce bakya harka da namiji duk tsawon wannan shekarun naki, kina wane ɓoye zancen ai yanzu komai a fili ake yinsa, ba a ɓoyewa saboda abin ya zama ruwan dare gama duniya, kuma rayuwar yanzu kowa nemawa kansa mafita yake, kowa ta kansa yake dan haka feel free muyi magana"
Tsayuwa da kyau HAMRA ta yi tana sake karewa Hauwa'u kallo sai yanzu ta fahimce ta, ta ce
Hauwa'u kenan, wannan kwatakwata baya daga cikin tsarin rayuwata, dan banyi aure ba shine zan zubar da mutuncina, ina har abada ko da zan dauwama a hakan ba zan taɓa zubar da tarbiya ta ba da kuma darajan gidan mu ba kuma bazan saɓawa mahaliccina ba, to ita kanta rayuwar yanzu kayi daidai ma ya ka kare ballantana bakayi ba, kin ganni nan ko saurayi bani dashi.
Dariya sosai Hauwa'u tayi tare da ɗaukan goran faro water ta kai baki ta sha sannan ta ce
"HAMRA pretty kada ki mai da karuwa ƴar iska mana, yanzu zaki ce dani ke VIRGIN ce ina, bazan taɓa yarda ba"
Ran HAMRA zuwa yanzu ya fara ɓaci ta fara tantama kan Hauwa'u Jibrin anya ba ƙazamar rayuwa ta keyi ba da take cewa ita ba cikakkiyar mace ba ce, ta san dai duk macen da zata faɗi hakan akan ƴar uwar ta mace to hakan yana nuni da ita ba mutuniyar kwarai ba ce gani ta ke yi abin da ta keyi ne kowa ma nayi, cike da mamaki HAMRA ta ce
Hauwa'u, ni na yarda da kaina, dan haka bana tsoro ko shakka dan wani zaya min mummunan fahimta kuma naji haushi, to ke kuma fa kina nufin ke ba cikakkiyar mace ba ce?.
Murmushi Hauwa'u tayi ta fito da bunch na dubu ɗari guda biyar ta nunawa HAMRA tare da ce mata
"Ɗazo kin tambaye ni akan wannan motar da nake cikinta, ita dai wannan motar ɗaya ce daga cikin motaci na wanda ALHAJI GONI ya bani, sannan yanzu ma daga wajensa nake a hotel muka kwana shine ya bani wannan 500k ɗin nasha ruwa a hanya bayan ban da wanda ya turamin ta account, ire-iren su suna da yawa ke har outside muna fita tare da shi, kai da duk wanda ya nemi yin hakan ina shanawa ta, duk abinda matar aure take yi nima ina yinsa to naga ai wannan normal ne, damu da matan auren duk ɗaya muke.
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, shine abinda HAMRA ke furtawa cikin tashin hankali ta ce
Amma ko Hauwa'u ba kiyiwa rayuwar ki adalci ba, kin cuci rayuwar ki, babu haɗe sakanin kwaɗan rama da zogale, ko ni nan wahala na fiki sau dubu ballanta kuma matar aure. Kiran da zan miki shine har yanzu da sauran lokaci za ki iya tuba ki dawo cikin rayuwa mai kyau ki tsafta ce zuciyar ki.....
"Heeeee HAMRA pretty, do you mean za ki ce min baki san namiji ba har yanzu, bazan taɓa yarda ba. To ki sani wannan rayuwar da nake yi bata karewa bace haka kurum ina cin duniya ta da tsinke baza ki kamin cikas ba, in kina so hanya buɗe take zan iya haɗaki da irin namijin da kike burin samu a rayuwar ki, haka kurum ba zaki sa nayi 2 zero ba, ni banyi aure ba kuma ban san na miji ba har na mutu kai ba zayyu ba, kinga tafiya ta"
Ta shige mota ta yi tafiyarta, HAMRA sabar kaɗuwa da abinda taji yasa ta juyo cikin tashin hankali ta shigo gida nan tayi kicibis da AMMAR dake shirin fitowa, ta daidaita nutsuwar ta dan kada ya fahimci wani abin tasan da ya sani zai dameta da tambayoyi da SBD ganin tana cikin damuwa, ta kwakulo murmushi ta ce
Ina zuwa da safen nan?.
Yayi murmushi cikin kulawa ya ce
"Kin manta ne ina shirye shiryen barin Nigeria, ko da shike tsufa ya fara kamaki, ba dole ki tuna ba"
Tayi dariya ta ɗan bugesa a kafaɗar sa ta ce
Kai kasani, girma dai na fika, to Allah ya taimake ku, zan shige ciki na huta.
Yayi dariya ya fice yana mai farin cikin ganin ta, cikin farin ciki. HAMRA na shiga ta wuce ɗakin Ammie ta taddata tana breakfast ta duka har ƙasa ta gaidata, amma Ammie ko kallon ta ba tayi ba balle kuma ta amsa mata, HAMRA ta miƙe ta fito sai taji muryar Daddyn su yanawa Ammie magana a lokacin ya fito daga cikin toilet.....
"Zamu sami matsala akan wannan abinda kike son haifarwa a cikin wannan gidan, haba hajjiya Batula sai ka ce ba ɗiyar ki ba ce kike mata haka, ya kike so tayi?.So kike taje ta ce da namiji kazo a ɗaura mana aure ko kuma so kike damuwa ta kashe ta, a wannan lokacin ne take buƙatar kulawar ki amma ki ke nuna mata halin ko in kula"
"Uhm ALHAJI na kula kai kake ɗaurewa HAMRA gindi take duk abin da taga dama shiyasa taki fidda mijin aure....
"Ya isa haka, na ce ya isa haka, kuma bana so ki sake maimaita abin da ki kayi mata yanzu"
Sauri HAMRA tayi ta shige cikin ɗakinta zuciyar ta na harɓawa, ji tayi duniyar ta fice mata a rai, ta saki kuka a hankali, tana tuna abin da Hauwa'u ta faɗa mata da kuma faɗan da iyayen ta sukai akanta, ta jima tana kuka sannan tayi bacci da yunwar da take ji, sai kusan azahar ta tashi ta idar da sallah sannan ta samu ta ci abinci ta koma bacci, har dare tana ɗaki, daman ba inda take zuwa, gidan su Shatu ne take zuwa suyi fira ko kuma ita tazo mata, tunda ta yi tafiya bata fita, daman gidan su kawai take shiga sauran duk ta fisu a shekaru sauran kuma sun yi aure.
Ta miƙe ta shige toilet ta watsa ruwa ta sanya doguwar riga mara nawi ta bacci, ta kunna ɗan ƙaramin TV nta plasma dake maƙale jikin garu daman a NTA News yake ta ci gaba da kallon labaran karfe 9:00pm, nocking akayi ta bada izinin shigowa ya shigo tare da sallama ta amsa, sanye yake da jallabiya ruwan ƙasa ƙirar Dubai, ya zauna kan carpet ya ajiye mata ledar da ya shigo da ita ya ce
"Ke kam akwai ki da son labarai, ki kanza ki kai MBC max yau akwai raceling"
Uhmm kaga Ammar kyale ni na kalli labaran duniya, in kana son kallon wasan dambe koma ɗakin ka, ka kalli duk channel ɗin da kake so, to ba za a zo fada ta ba kuma amin mulki.
Dariya ya yi ya ce
"Fira nazo taya ki fa shine ki ke korata tam akwai gobe. To gashi na siya miki roasted fish da banana juice"
Kai ƙanina kana fa ji dani sosai.
Murmushi yayi tasa hannu ta buɗe ladar ta soma ci ta sake cewa
Ka jima a waje ashe dai wajen siyayya ka wuce.
Ya sauke numfashi yana kallon News ya ce
"A'a daga station nake"
Cikin sauri ta haɗiye ragowar kifin dake bakinta ta ce
Kana nufi police station! Me kuma ya kai ka?.
Kai tsaye ya ce
"Na raka abokina Abdullahi, saboda case na ƙanin shi Sadiq"
A hankali ta kurɓi banana juice ɗin ta ce
Iko sai rabbi, me kuma ya sami Sadik ɗin?.
"Uhm wai budurwa sa ce da iyayenta suka kai ƙarar shi, shine Abdullahi ya ce na kai shi da mota ta"
Budurwa? Yanzu Sadiq har wata budurwa gare shi?. Kai wannan zamanin da abin mamaki yake, in ba karshen zamani ba ina Sadiq da wata soyyayya.
Ya juyo ya kalle ta tana cikin kifin ya ce
"Eh wai ciki gareta kuma ta ce sam na Sadiq ne"..
Aiko kifin da bai wuce mata wuya ba ta ƙware, yayi saurin mika mata robar swan water ta karɓa ta kora sannan ta ɗago ta ce
"AMMAR bana son shashanci yanzu wannan yaron Sadiq ne zayiwa budurwa ciki, kai sai dai ko wani cen ya yi mata zata ƙalla masa sharri.
Murmushi yayi tare da girgiza kansa ya ce
"Shi yayi daga karshe ya amsa, yanzu haka ma sun ce dole sai ya aureta"
Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, lallai na tabbata karshen duniya yazo, a ce yaro mai shekaru 20 ya yiwa mace ciki, amma abin da mamaki yake.
Ya sauke numfashi ya ce
"Waye ne mai shekaru 20, Sadiq fa 25yrs gare shi 5yrs muka ba shi, ai wannan ba abin mamaki bane"
Ta kammala cin kifin ta ce
Kai Ammar, kai yanzu za kace 30yrs gareka, haba dai sai dai 25yrs.
Ta miƙe ta shige toilet ta wanke hannunta sannan ta fito, ta zauna tana jinjina al'amarin kai yaran yanzu da karambani suke....
"HAMRAH kina nufin I'm 25yrs to kenan ke 30yrs"
Ta hararesa ta ce
Ka jika I'm 35yrs, kana nufin zaka haɗa kanka dani.
Yayi murmushi yana kallon ta yace
"Shekaru biyar kika bani, kuma suma ai suna ne"
Ammar kenan, girman nan dai na fika, kaga bacci zanyi gobe morning duty nake dashi.
"To babbar yaya a tashi lafiya"
Ya miƙe ya fice ta gyara wajen ta kashe tv sannan ta kwanta saboda kada ta makara wajen tashin safe.
Comments and share
[1/10, 19:31] SAYYADA ✍️ Barrister: *MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 7 & 8
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_________Tun da na baro gida nake ta sake² cikin raina shin nayi amfani da shawarar da ki ka
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 19