baya dan yin hakan zaisa Daddyn ƙin amincewa da Alhaji Sama'ila ita kuma Ammie bata so ya sani.
Jikin Shatu ya yi sanyi tana jinjina lamarin ta ce
"To ke bestie meyasa baki son shi?"
Ƙawata ba wai bana son shi bane, kinga masaukinsa shine hotel kuma yace dani shi ɗan siyasa ne kuma ita ke kawoshi Maiduguri sannan yana da mata ɗaya da kuma yara to duk irin wa'yannan mutanen baza su rasa wajen zama ba amma zama a hotel ba girmansa bane, rannan fah cewa ya yi naje na samesa a cen to ni bansan me haka yake nufi ba.
Sauke numfashi Shatu tayi ta ce
"Bestie shawarar da zan baki shine yadda kika ga Ammie ta ɗau zafi wannan karon ki amince ki auri Sama'ila, tunda da zancen aure yazo tunda niyyar sa mai kyau ce ki yarda ayi kawai a wuce wajen sannan kuma you have to find out who is that Hajara bcoz Ina da tabbacin tana da dangantaka da wannan matsalar da kike tare da ita maybe muji wani abin daga wajenta"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce
To nagode ƙawata na amince zan auri Sama'ila sbd hankalin kowa ma ya kwanta to amma batun nemo wannan matar Hajara bansan wa zan fara tambaya ba Daddy ko Ammie dake fushi sani?.
"Daddy za ki tambaya ko ki tambayi Zeenat tunda kinga maybe ta sani dan suna tare da dangin Daddy"
To zan yi.
Suna fira tare da baiwa junansu shawa suka jiyo sallama daga bakin gate suka ɗago cike da mamaki suke kallon su tare da amsa sallama suka ƙaraso.
"Hauwa'u Jibrin!"
Cewar Shatu ceke da mamaki ganin ɗayar yasa tace
"Wai tab in ba a mutu ba za a haɗu, Zainabu Abu mai tagwayen suna"
Dariya sukayi suka haɗa baki wajen cewa
"Aishatu muktar ashe rai kanga rai, to har yanzu ana nan ana ƙawancen kenan ya yi kyau"
"Uhm ai ni da Hamrah aminya mutu ka raba ne"
Dariya sukai Hamrah tayi musu barka da zuwa tare da ce musu su shige ciki amma suka ce anan ɗin zasu zauna ta basu kujerun roba suka zauna, nan aka shiga gaisawa Hamrah ta ce
Zainab Ayuba kina nan a gari ikon Allah ko matsin ku ba a ji.
"Uhm pretty kenen ina nan fah harkoki ke riƙe ni"
Ikon Allah, ya yaran naki da mai gidan?.
Dariya Hauwa'u da Zainab sukayi lokaci guda sanan Zainab ta ce
"Ai banyi aure ba har yanzu"
Cike da mamaki Shatu ta ce
"Kai da mamaki kenan yawancin ƴan set namu da muka kammala secondary School bamu yi aure ba ikon Allah"
"Uhm fah shine ma abin da ya kawomu sbd mu tattauna akai though we have already talked about it me and Hamrah Amma kuma she didn't respond to me, maybe bata fahimce ni bane shine muka zauna dani da kuma Zainab muka sake shawarar zuwa mata da zancen sai kuma gaki to hakan ma yayi kyau sai mu tattauna kan batun"
Hamrah ta miƙe tare da cewa
Let me find you some water.
"Ai daga Restaurant meke bamu da yunwa da kuma ƙishirwa, ki zauna muyi magana wannan karon da babban batu mu kazo"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta zauna tare da ƙurawa Hauwa'u idanu wacce ke cewa daga Restaurant suke sanye take da riga da wondo tashi kitson Attachment mai colour hulace wacce bata rufe gashin kan ba. Ta juya ta kalli Zainab wacce ta ke sanye da doguwar riga itama tasha cikon gashin Attachment ta yafa ɗan ƙaramin mayafi duk sun sha mai kamar ba ƴaƴan Musulmai ba, tayi ajiyar zuciya ta ce
Hauwa'u muna jinki.
"Da farko dai kamar yadda kuka sani ni ce hauwa'u ƴar goal mai lakaɓi da bini a hankali in kayi gardama kasha ƙasa, ina da kungiyoyina na kaina sun kai 7 amma kuma uku ne suke tashe wato ina da fannin ƴan mata waɗanda basu taɓa aure ba sannnan ina da na zaurawa da kuma matan aure. Zainab shugaba ce a ƙungiyata ta ƴan matan da suka jima basu yi aure ba to ita ke riƙe da duk yadda za ayi kuma adace akwai Rahama ita kuma ke riƙe da na zaurawa, ni kuma ina riƙe da na matan aure, sannan akwai masu tallafa mana manya manyan ƴan siya da nan gida Nigeria da kuma wasu daga cikin shahararrun ƴan kasuwa sai kuma ƴan outside.....
Tayi shiru ta sauke numfashi tana dubansu suma sun zuba mata na mujiya suna kallonta cike da mamaki da kuma son sanin shin wane irin kungiya ce wannan mai dubban mutane. Kamar tasan me suke tunani tasa ta cigaba da cewa
"Bari na tafi kai tsaye kan batun so muke mu haɗa kai daku wajen sake bunƙasa wannan kungiyoyi guda ukun musamman ma ke Hamrah pretty ba ƙaramin ƙaruwa zamu yi dake ba ina tabbatar miki karon farko ma Saudi Arabia zaki tafi acen za ku fara shan iskar ku"
Shiru da ta yi ne yasa Hamrah cewa
"Ƴar goal har yanzu ban fahimce ki ba wacce irin kungiya ce wannan wacce kuke taimakon ƴan mata, zaurawa da kuma matan aure kuma wane irin tallafi kuke bada har da kuna da masu taimakon ku"
Sauke numfashi Zainab ta ce
"Haba Hamrah pretty kada ki ce min kina da duhun kai mana, harkar ce baki sani ba zaki ce min ko kuma gwadamu ki ke son yi, to naga ita ɗinma taimako ce tunda tamkar business ta ke do me i do you ne, harka ce ta ƙaruwa da wannan zaman da kuke yi a gida ana matsa muku duk da ba sai kun faɗa ba nasan haka abin yake kuna cikin damuwa to duk wacce ke cikin irin wannan matsalar muke warware ta, yanzu waɗanda suka samu abin yi ta hannun mu suna da yawa dan zan iya cewa last 3month mun ya yi mutane dubu ɗari biyar daga cikin su akwai ƴan mata wasun su kuma akwai zaurawa sannan mata masu jinkirin aure yanzu haka suna da manya manyan shops su ke riƙe da kansu wasu ke riƙe da iyayensu, shine muka zo kema ko ince kuma ku shiga wannan harkar sbd mu faɗaɗa abin musamman ma ke Hamrah pretty da ki keyi...
Ya isa na ce ya isheku ƴar goal da Zee, lallai kun cika ƴan ta'adda masu cutar da al'umma amma to ku sani ko bamu da komai ko da yunwa meke kwana baza mu taɓa shiga cikin kungiyar ta ku ba Allah wadaran da da ƙungiyar ta ku.
Cewar Hamrah cikin ɓacin rai da tashin hankali.
Shatu ko tsuman zaune ta yi tana kallonsu kamar mutum butumi cen ta numfasa ta ce
"Inna lillahi wa inna ilaihi rajiun, Allah yasa mafarki na keyi"
"Uhmm meyasa kuke bada mata ne abu kun sani mun sani amma kuna son wahalar damu, in zaku saki jiki muci arziki mu barshi a inda yake to ku amince kawai ba wai ku tsaya kuna wani nuƙunuƙu ba"
Cewar Hauwa'u Jibrin tana murmushi sbd ganin wannan karon za tayi nasara akansu.......
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 33 & 34
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
______ Ajiyar zuciya ta sauke a hankali taci gaba da kankare carrots ɗin cikin sanyin jiki ko kaɗan bata ji daɗin abin da Maryama ta ce ba, bai dace ta zubar musu da mutunci ba a bainan nasi ko ba komai iyayenta ta. Su faɗi duk abin da suke so su faɗa akanta bazata damu ba sbd tasan watarana zai zamo tarihi. Ayshe dake zaune gefen ta taci gaba da yanka cabeji tayi murmushi bayan taji abin da kanwarta su ta faɗa sun santa sarai ba a gasa mata baki ba duk abin da yazo bakinta faɗa take kuma ba wannan ne karonta na farko da take musu hakan ba duk cikin su anayi musu abu suna shanyewa amma banda ita, sam bata barin takwana kanayi take maida maka, murɗaɗɗiya ce ba a iya gane mata yanzu zakaga kamar mutuniyar kirki ba a wuce wasu lokuta kuma ta sauya kamar mai juju take, cikin sanyin jiki Ayshe ta ce
"Uhm Maryama ko za ki duba abin da na bari akan wuta a cen cikin kitchen please"
Tasan sarai korarta Ayshe ke son yi shiyasa ta faɗi hakan....
"Ke Maryama kada kiga kina tsula tsiyarki uwarki na ɗaure miki gindi ko kuma kina takama da wani guntun arzikin da mijinki ke dashi kina cin mutuncin ƴan'uwanki yau ko uwarki Ammie bata raye su zasu rike ki amma shine kike buɗe baki kike faɗa musu haka waye baisan rayuwar yanzu ba kowa lallaɓa gidansa yake yi yaga ya rufawa kansa asiri in batayiwa ƴaƴanta ba wa zataiwa naga kayi hidima a gidan ka ai ba laifi bane, kuma ai gaskiya ta faɗa dubi fah kiga yadda shekarun ta suka ja she has almost 35yr mai kuma ya rage mata na jin daɗi yanzu bayan tabar kuruciyarta. To ki sani ba abu mai wahala bane na dirza bakinki da jikin garu yanzun nan yayi jini mara kunya kawai"
Cewar Baba Uwani tana huce takaici taƙi jinin Maryama duk ƴaƴan Ammie itace ta fito mara kunya ba a isa a faɗa mata taji ba.....
"Kai duniya ina zaki damu, oh ni Maryamu Daso yau naga ta kaina, yaushe akayi dare da har garin ya waye, tab wai kura ce tace da kare maye. To ke Baba Uwani yaushe kikayi auren ina dududu 2yrs ne da yin aurenki kuma kema kina da shekaru 45 kafin kika samu tsoho yayi wuff dake ai gwamma ita Hamrah 35 ne kuma tana da kyaun jiki da kuma baby face, ina kema lallɓa zaman ki ke shi kanshi Alhaji Audu ba zuwa miki yake ba ke kike binsa cen Kaduna da ya gaji ya koroki, mun san komai kawai bamu son magana ne sbd sanin mutumci amma tunda kunki rike girmanku to me yasa mu zamu baku"
Ayshe ce ganin abin na neman girmama ta ce da Maryama
"Maman Waleed ki tashi kijeki ki duba abin da na faɗa miki yana kan wuta"
"Barta Ayshe, barta muci uwar ta Batula tunda bata bata tarbiyya ba batasan ta girmama manyanta ba mara kunya fusararriya kawai dan kinga kinayi ana kyalikine shiyasa ki keyi to ki sani ko shi ubanku bai isa ba ballantana ke karamar alhaki"
Cewar cewar Sa'ade wacce suka tashi gida ɗaya da Daddyn su Hamrah, Hamrah tayi saurin cewa
Maryama kiyi shuru manyanmu ne bai dace kiyi sa'insa dasu ba ki tashi ki shige ciki.
Maryama ta cika tayi fal daman zafin rai gareta an zagi uwar ta da kuma ubanta dan haka bazata kyalesu ba sbd duk taro sai sun tada husuma haka lokacin bikinta sai da suka tada rigimar da yasa aka watse cikin ɓacin rai babu wanda yayi mata rakiya daga dangin Daddynsu dan haka yau zata sauke musu ta kalli Baba Sa'ade ta ce
"Kai mutane na bani mamaki kowa da guntun kashi a suliyarsa baya gani amma yana leka na wani, ke baba Sa'ade har kina da bakin magana keda da haduwarki da walakiri a kabari ba zatai miki kyau ba, ina zaman zina ki keyi a gidanki baki da aure ki ke zaune da mijinki sbd ya yi miki saki yafi dubu amma kika rufe ido kika ce wai cikin ɓacin rai yayi sa kika zauna kike ta haifan shegu, shine har kike wani kuri kina cika kina batsewa to sai ki dakan na gani da yake ni ɗin shukakkiyar bishiyace ai dole na tsaya ki dakeni"
Aiko nan aka hauta da faɗa sunayi tana maida musu da ƙyar Hamrah tasa tayi shuru, a hankali ta ce
Ayi hakuri da abin da Maryama ta faɗi kuruciya ke ɗibarta in kukayi la'akari da cewa har yanzu bata gama mallakan hankalinta ba. Ku ma ku rike girmanku kuja darajarku ku daina biye mata. Babu macen da zata so ta zauna bata da aure har karshen rayuwarta, kyan mace shine ɗakin mijinta, nima burina shine nayi aure na zauna a ɗakina kamar ko wacce mace amma kuma hakan baya yuwa sai da izinin Ubangiji. Bana cire rai wataran nima zanyi, amma zancen da ake yi wai ina zaɓi ne shiyasa naƙi yin aure ba gaskiya bane kowa yasanni ni macece wacce bata da dogon buri sannan ina da rufin asiri na dan haka ba zan ɗaurawa kaina cewa sai mai kuɗi zan aura ba. Babu wacce zata so ta auri mijin da bashi da sana'a ko wace mace tana so tana kuma muraɗi ta shiga gidan da zata sami kwanciyar hankali in ta tsaya ta dirje ta nemi mijin da zatafi samun nutsuwa da kuma kwanciyar hankali ba laifi bane. Ni kawai na ɗauki jinkirin aure a matsayin jarrabawa ce a gareni kuma Allah yana sane yayi haka shine mafi sani akan komai maybe yayi hakanne sbd ya gwada imani na sbd Ubangiji baya ɗaurawa bawansa abin da yafi karfinsa sai dai bawa ya ɗaurawa kansa, Allah shine ke jarabta kuma shike yayiwa sannan hakan yasa na maida dukkanin al'amurana gare shi kuma na ɗauki hakan a matsayin MUJARRABI na.
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ɗago tana kallon su kamar yadda suma suka zuba mata na mujiya suna kallonta duk jikinsu yayi sanyi da bata maida musu da martani mai zafi ba cikin ruwan sanyi take magana, ta cigaba da cewa
"Na rike mutunci na, masu ce ina bin maza ko ina karuwanci shiyasa naƙi fidda mijin aure to ba haka abin yake ba, ban taɓa sanin wani ɗa namiji ba, na kiyaye mutunci na da kuma martaban gidanmu, bazance ban yafe wa masu faɗin hakan ba amma har ga Allah ina jin zafin mummunar shaidar da ake yi min, amma babu komai duk a rashin sani ne. Yin aure da kuma rashin sa duk daga Ubangiji ne, kamar yadda yayi dare haka kuma yayi rana, haka zalika kamar yadda yayi safiya haka yayi yammaci, yayi rayuwa kuma yayi mutuwa yayi mace ya kuma yi namiji, yayi fari ya kuma yi baƙi yayi duhu kuma yayi haske, yayi samu kuma yayi rashi, yayi zafi kuma yayi sanyi, dan haka bazan ɗaga hankalina ba. Shine aure nufi ne na Ubangiji da yanufa za ayi, ba wai dabararmu bace ko wayonmu zaisa ayi aure shi karan kansa menene aure me ake nufi da wannan kalma ta aure?
___.....shin menene ma Auren? Aure shine haɗa wata irin alaƙa tsakanin mace da namiji, wannan yana nufin haɗe rayuwarsu ta zama ɗaya hakan nan kuma makomarsu ta kasance guda ɗaya. Allah (Subhanahu wata'ala) ya halicci mace daga hakarkarin namiji ya kuma sanya soyayya da tausayi a tsakaninsu kamar yadda ya gaya mana a Alkur'ani mai tsarki. Wannan yana nuna mana cewar alaƙa tsakanin mace da namiji Allah ya kullata tun fil azal. Sai dai kuma duk da wannan alaƙa Allah bai halatta Aure ba sai Aure ya zamo Sunnah ce ta Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama
Dan mace ko namiji bai yi aure ba wannan baya nuni da cewar mutumin banza ne ko wani laifi yai wa Allah shi yasa har yanzu bai auruba ko bata auruba. Aure Sunnah ce ta ma'aiki rashin yinsa kuma ba zai hana bawa shiga aljanna ba matuƙar ya kame kansa, tunda muna da sanin cewar daga cikin Sahabbaima akwai wadanda basu yi aure ba kuma muna da tabbacin ƴan aljanna ne kenan aure baya hana shiga aljanna hasali ma wani aure da yinshi gara rashinsa in muka yi la'akari da irin matan da su ke da aure kuma suke aikata zinna wasu ma maɗugo su ke yi da auren su Wa'iyazubillah mace ta mutu a wannan gabar ai itama ta san makomarta
Da yawan mutane suna daukar rashin yin aure ƴan'mace wata tawayace a gare ta basu sani ba jarrabace daga Allah kuma shi Allah yana jarraba bawansa ta yadda ya so kuma ba zai daurawa bawansa abinda ya san bazai iyaba ƙaddara ce kowa da irin ta sa, nawa ake auren amma kuma ana tsaɓawa mahalli nawa kuma ba a auren kuma ake samun rahamar Ubangiji sannan abu mafi ɓacin rai da kuma takaice shine mafi yawan masu gorantawa ƴaƴan wasu suma suna da ƴaƴan basa tunani suma daga cikin ƴaƴansu hakan zai iya faruwa dasu. To ku sani yin hakan tamkar shishigi ga al'amuran Ubangiji ne kuma jayayya da ikonsa kuke yi in kunne yaji to gangan jiki ya tsiri.
Hamrah na gama faɗi haka ta miƙe ta shige ɗakin Zeenat. Har yamma suna shagalin suna sai bayan magrib suka tattaro inasu ina su ko wacce ta watse.
_After 1week_
Kamar yadda Alhaji Sama'ila yayi musu alkawarin zai turo magabatan shi ranar Friday ya tabbata dan haka suka hau shirye shiryen tarɓansu, aladan Maiduguri shine ranar yanke lokacin biki ko sanya rana ko tambaya ana ɗan karamin hidima wa abokan manemin dan haka kusan kowa ya hallara banda Zeenat mai jego, an haɗa musu roban papare dosen biyu kusan rabin da kwatan dosen ɗin kaji ne a ciki sai kuma sauran aka zuba snacks, dibla, cake, donot, greba, garabiya, alkaki da kuma drinks sabar murna da kuma farin ciki karamar biki sukai ita dai Hamrah na daga gefe tana kallon su duk jikinta yayi sanyi gani take kamar ba da gaske bane abin kamar a mafarki, sai kuma da ta tuna da abin da ya faru ranar bikin ta da Deeny sai gabanta ya faɗi tana tsoro kada hakan ya sake faruwa.
Sai yamma suka iso aka sanya rana sunce sati biyu suke so amma Daddy yace a'a sai dai a sanya 2month da ƙyar aka bari akan 1month aka watse Alhaji Sama'ila ya bada sadakin Hamrah a ɗunkule lokacin guda akan 15 million Daddy ya ɗauke dubu ɗare biyar sannan ya maida sauran amma ina dashi da kuma sauran mutanen da suka zo suka ce a'a rabonta ne baza su ansa ba a riƙe ai wannan ba komai bane, da labari ya iso cikin gida kuma nan aka hau guɗa Hamrah najin haka tsoro ya kamata what, menene dalilin sa na yin hakan kai ita abin tsoro ya bata. Daddy yace da Ammie gaskiya ya tsorata da wannan mutumin amma Ammie ta tashi ta dire ta ce ba zayyu ba sai anyi in kuma a abin da danginsa ne suka faɗa shi yake so ya aiwatar to ya faɗa mata tasan nayi amma kuma sai ya hau rarrashin ta ya karɓa ya ajiye to abinda ya sake ɗaure musu kai shine cewa da yayi baya bukatar ko kwandalarsu shi matarsa kawai yake so dan haka komai zayyi mata a cen Abuja inda zasu zauna nan ma hankalin Daddy ya tashi amma da ya tuna aure za ayi sai hankalinsa ya kwanta.
An watse lafiya an bar Hamrah ita kaɗai a ɗaki ta ɗau waya ta kira Alhaji Sama'ila bugu ɗaya ya ɗauka yana cewa
"Matata ya kike da gajiya da kuma ɗawainiya, kai gaskiya abokaina sunyi farin ciki da wannan tarban"
Uhm, ba komai, kuma ai kunyi ɗawainiya amma kuma kuɗin sadakin da ka bada yayi yawa sannan kuma kace kada amin komai a kaini daga ni sai kayana shine ya ɗaure min kai meyasa kayi hakan, meyasa ka ɗaurawa kanka wannan ɗawainiyar shin taimako na ka keyi ko tausayi na ka keji?.
Ajiyar zuciya yayi cikin sanyin murya ya ce
"Hamrah aurenki fah na fito nema dan nayi hakan ba laifi bane kuma ai ko nawa na kashe a kanki ai kaina nayiwa ba ba dawata manufa nayi ba, ki ɗauki hakan a matsayin ƙauna ce da nake yi miki"
Sauke numfashi tayi ta ce
Duk da haka ai sai ka bari in na shigo gidan ka sai kayi min amma ba a gidanmu ba.
Murmushi yayi sosai sannan ya ce
"To ranki shidaɗe daga wannan bazan sake yi ba"
Uhm shikenan nagode.
Sukai sallama akan gobe zaizo su gaisa. Kiran Ammar ya shigo ta ɗau wayar cikin sanyin murya ta ce
Yanzu ko nake son kiranka sai ko gashi kaki rani.....
"Eh Hamrah yayi miki kyau da kika zaɓi wannan tsohon a matsayin wanda zaki zauna dashi kuma har an yanka lokacin biki shine baki faɗa min za ayi ba shikenan kawai ko kinyi aure babu ruwana dake"
Cewar Ammar ya katse ta yana magana cikin damuwa.
Haba Ammar kaima kasan bazan taɓa aikata hakan ba kawai muma mukaji an sanya rana daman tambaya ce za ayi to shine aka haɗa kawai aka sanya lokacin amma ai an sanya shi daidai da dawowarka.
"Ni dai kawai anyi hakan ne dan bana nan"
Uhm Ammar ai ko kana nan ko baka nan dole zanyi aure so, banga wani abin damuwa ba, abu sai kadawo ma za a ɗaura.
"To shikenan sai anjima"
Ya katse wayar, tabi wayar da idanu ikon Allah menene kuma abin fushi ko da shike an fara musu alluran sojoji ai sai a hankali. Har ta kwanta bata ga Ammar ya hau online ba haka ta hakura tayi bacci.
Washegari, tana tashi ta shirya ta fito sbd tafiya wajen aiki ta shige ɗakin Ammie ta taddata zaune hannunta riƙe da takarda da kuma biro tana ta rubuce rubuce, ganin Hamrah ta saki murmushi tare da cewa
"Yauwa kamar ko kin san ke nake jira amma ba dai wajen aiki zaki ba?"
Cike da mamaki take bin Ammie da kallo ta ce
Eh Ammie zan wuce wajen aiki.
"To wannan sai kin dawo sai mu cigaba da lissafin abubuwan da za a siyo to in ba abin surkin nawa ba yaushe zamu ɗauki yarinya mu bada babu kayan ɗaki ai ba zayyu ba sai munyi"
Galala take kallon Ammie rabonta da taga tana fara'a yau kusan 2yrs kenan...........
Comments and share
*MUJARRABI*
By SAYYADA ✍️ Barrister UMMUL UMMU ABIHA
09021706569
PG 35 & 36
*MIKIYA WRITER'S ASSOCIATION*
_________Sauke ajiyar zuciya Hamrah tayi tare da gyara zamanta ta kalli Ammie wacce ke cikin farin ciki kamar wacce akayiwa bushara da gidan Aljanna, mamaki take ganin lokaci guda ta sauko daga fushin da take yi da ita, daman rashin mijin aure ne tunda ko ta samu komai ya wuce. Ta dau alkawarin zama a ɗakinta koman yaya ta tadda zata jurewa duk rayuwar da zata sinci kanta a gidanta indai hakan zaisa Ammie farin ciki, a hankali ta ce
Ammie ba sai mun zauna munyi list na komai tare ba kiyi duk abinda ya dace nima yamin.
"A'a jeki wajen aiki kin tunda da yamma zaki dawo in yaso zuwa dare sai muyi magana, ai wani abin sai anji ra'ayinki kowa da irin zaɓin sa ballantana ku ƴan zamani da son kyalele ai sai ku kuka san abinku"
Sauke numfashi Hamrah tayi ta ce
To Ammie sai na dawon sai mu tattauna.
"A dawo lafiya"
Hamrah ta miƙe ta fito, tunowa da tayi da ta manta da snacks ɗin da zata kai wajen aikinsu na sanya ranan bikinta yasa ta koma ɗakinta ta ɗauko su kamar yadda ta kulle na kowanne su cikin lada. Ta iso kamar yadda ta saba batayi late ba yasa ta wuce cikin office nata ta ajiye jakarta ta ɗauko white coat nata ta sanya sannan ta ɗau wayarta da kuma ledan snacks ɗin ta fito ta riski Nurse ta bata nata ta faɗa mata an sanya ranar bikinta, aiko da jin haka ta karɓa ta dinga bin office by office tana rabawa nan da nan zancen sanya auren Hamrah ya karaɗa Hospital masu mata fatan alkhairi nayi masu zancen ƙasa² ma nayi, tana zaune a office nata Dr zalihat ta shigo ta tadda ta zaune tana danne dannen wayarta ta ɗago sbd sallaman da tayi ta amsa tare da sakar mata murmushi ta ce
Dr zalihat ke da kanki sannunki da zuwa.
Murmushi tayi ta ce
"Eh fah na ce wannan abin farin cikin yakamata na taho takanas ta Kano nazo na sanya alkhairi. Na tayaki murna Allah ya nuna mana lokacin"
Murmushi Hamrah tayi ta ce
Nagode sosai Dr zalihat.
"Ba komai, amma dai da fatan bazaki bar aiki anan ba ko da bayan kinyi aure"
Murmushi Hamrah ta sake yi ta ce
Yanzu dai bana ce komai ba, dan babu tabbacin anan garin Maiduguri zan zauna amma da zan ci gaba da aikina da yafi amma sai yanda yayu.
"To masha Allah, Ubangiji yayi maki zaɓi na gari, muma da zaki zauna da munyi farin ciki"
Sun jima suna fira sannan ta tafi, Dr Hamrah na zaune Dr Aliyu ya turo kofar ya shigo cikin farin ciki ya ce
"Special Doctor sai naji labari mai daɗi, kai na tayaki murna sai ko gashi dani dake duk a sanya lokacin bikinmu"
Murmushi tayi ta ce
Eh fah haka Allah yake al'amuran sa nima lokaci yayi.
"To Allah ya sanya alkhairi, ya nuna mana lokacin"
Amen.
Sun ɗan tattauna akan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 13 Chapter of 19