Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
boyayyun dimples nasa fararen hakwaransa suka bayyana ya girgiza kansa ya miƙe tare da yiwa Ammie sai anjima ya fice. Baby kam daga shan nono tayi baccinta nan Hamrah ta kwantar da ita a daidai lokacin kuma ƙannenta suka shigo Ayshe, Zeenat da Maryama suna mata sannu tana amsawa. Anan suke wuni da yamma su tafi har aka sallameta suka dawo gidan Hamrah saboda shirye shiryen bikin suna. Shirye shiryen bikin suna ake yi babu kakkautawa Daddy kam kamar akan Hamrah ya fara samun jika sai hidima yake musu musamman da yaji cewa Alhaji Sama'ila na cen Umrah yana ibada Daddy yace ko yana nan ko bayanan hidima sai anyi nan Hamrah ta kwantar da hankalinta suka sha suna bidia kala kala, gift kam ba a magana kowa yazo taron sunan nan zai koma da goma ta arziki anyi wasan Naira yarinya taci sunan kakarta Fateematul Batula wato Ammie aiko ranar Ammie wuni tayi tana washe hakwara. Washegarin suna ne Ammie ta ce za a tafi wankan jego babu musu suka tafi dan Hamrah cewa ma tayi Alhaji Sama'ila ya amince ya ce ta zauna a gida har sai ya dawo. Satin Hamrah 3 da haihuwa jikinta yayi sumul kamar ba ita ba, sai dai kuma yawan shuru da take yi ne da kuma yawan keɓance kanta ke sanya Ammie mamaki kamar ba Hamrah ba duk da daman bata da yawan hayani amma wannan karon shurun yayi yawa. Ammie ta shigo ɗakin Hamrah ta taddata tana nan zaune tana aikin tunani ta zauna kusa da ita sosai take kallonta cikin kulawa ta kira sunanta "Hamrah" A hankali ta ɗago ganin Ammie yasa ta gyara zama tare da cewa Na'am Ammie, yaushe ki ka shigo?. "Ai baza ki sani ba tun da ki zaɓi ki dinga zama ke kaɗai kina tunani, wai meke faruwa dake ne shin gidanki da matsala ne ko kuma akwai abin da ke faruwa sakaninki da mijinki ne?" Jikin Hamrah yayi sanyi tayi ajiyar zuciya a hankali ta ce A'a Ammie babu komai fah kawai babu ƴan tayani firane shiyasa. Sauke numfashi Ammie tayi ta tsurawa Hamrah idanu tabbas akwai abin da ke damunta, a hankali ta ce "Hamrah akwai abin da ke faruwa sakaninki da mijinki dan na kula tun ranar da kika haihu har zuwa yau baki sake yin maganar da ta danganta dashi ba sannan ko waya ma bana ji ko ganin kuna yi. In dai da matsala ki faɗeta tun kan ya dawo mu sami bakin zaren mu warware ki koma ɗakinki lafiya" Ƙirjin Hamrah ya bada rasss, tab ai abin da ke faruwa ya wuce matsala ai da zata sanar da Ammie dako tafi kowa shiga tashin hankali, sauke numfashi tayi tare da ƙirƙiro murmushi ta ce Lah Ammie ba komai yawancin wayar dare muke yi sbd inda yake ba lallai ne na sameshi a waya ba. Ammie na kallonta jikinta ya bata da matsala kawai Hamrah taki sanar da ita ne amma zata bincika ta gano koma menene. ************************* Ɗauke take da little Ammie ƴar lukuta kwana arba'in da haihuwarta amma kamar ƴar wata 2, yarinya barakallah sai wayyon tsiya ga kuma yawan dariya kamar tasan me ake yi, bata da rigama da ta ƙoshi sai wasa da ƙafafunta. Yanzun ma wanka Hamrah tayi mata ta sanya mata doguwar riga pink color har da headband shima pink gashin nan yasha gyara daman ba ayi haski ba. Daman da pampers a jikinta ta dauko ta suka yi ɗakin Ammar, turo ƙofar tayi tare da sallama ya amsa yana tsaye ne gaban mirror yana shiryawa da alamu fita wajen aiki zayyi sbd kakin uniform na sojas dake jikinsa, iya wandon ne da farar riga ta ciki a jikinsa yayi zanzaro da balt na sojoji, yana taje bakar sumarsa mai sheƙi da laushi kuma kwantacce ganin shigowar ta yasa ya juyo yana sakarwa little Ammie murmushi aiko tana ganinsa ta saki dariya ta wangale baki bubu hakuri, ya bar abin da yake yi ya taho ya karɓeta ya soma cillata kamar yadda yake yi sama da ita yana yi mata wasa. Hamrah ta zauna kan bedside tare da rabka tagumi ganin haka yasa ya zauna bakin bed ɗin ya kalleta ya ce "In ce dai lafiya kinyi tagumi kamar wacce ke cikin damuwa" Sauke numfashi tayi cikin sanyin jiki ta ce Ammar damuwa kam ai ina cikin ta sundum kuma bansan ranar da zan rabu da ita ba. Kaga jiya mu kayi arba'in kuma kasan dole yanzu na koma gidana dan zamana anan ba zayyu ba kuma nasan Ammie ba zata bari ba zata ce na koma ɗakina tunda dai na gama wankan jego shine nake tunanin bansan ya zanyi ina son zama agida bana son tafiya cen ɗin duk kaɗaici zai dameni. Ajiyar zuciya Ammar ya sauke a hankali ya ce "Ni a shawarce kawai ki sanar dasu halin da ki ke ciki in kuma ba zaki iya ba ki bari na zanyi magana dasu in yaso muji ta bakinsu kinga sai kiyi zaman ki anan ɗin" Ajiyar zuciya ta sauke da ƙarfi tare da ginginewa jikin garu ta ce Ammar ta yaya zan fuskanci Ammie da kuma Daddy na sanar dasu cewa AUREN HARAMCI Alhaji Sama'ila yayi dani kuma tun washegarin bikin ya tsallake kafa yayi tafiyarsa daga irin ta wankan ranar har zuwa yau ɗinnan ban sanya shi cikin idanuwana duk wannan zaman da nayi a gidana ni kaɗai ke rayuwa. Ai abin da ciwo zasu ji........ "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun, lahaula wala kuwwata illabillah. Me nake ji haka, me kunnuwa na ke ji haka?. Daman nasan da akwai abin da kuke ɓoyemin amma bansan abin na da girma haka ba girman da kunnuwana ba zasu iya ɗaukansu ba Hamrah me kika aikata haka?" Daga Ammar har Hamrah sai da hanjin cikin su suka kaɗa sbd unexpected suka ga Ammie a tsaya akansu tana rabka salati kuma sun tabbatar taji komai. Hamrah jiki na rawa ta iso inda Ammie ke tsaye, hawaye na zuba ta ce Ammie ki fahimce ni..... Ba abin da zaki gaya min Hamrah naji komai daman irin wannan rayuwar ki keyi kika kuma ɓoye sa a matsayin menene kenan saboda kina son mijinki ko kuma kina son ganin farin cikin mu to ki sani ni ba zan ɗauki wannan abin ba dole Daddyn ku ya san halin da ki ke ciki, kai kuma Ammar yayi maka kyau da ka goyi bayan tayi haka yayi maka kyau sosai" Daga jin yadda Ammie ke magana ya tabbatar musu ta fita hayyacinta dan bata san ma me take cewa ba abin ya matukar kiɗimata basu yi aune ba suka ga ta fice cikin ɓacin rai, Hamrah ta zube kasa ta fashe da kuka shikenan ta faru ta kare yau da bakin ciki iyayenta zasu wuni da kuma bakin ciki zasu kwana. Amma na ganin haka cikin tashin hankali ya kwantar da little Ammie kan bed yabi bayan Ammie sai kuma yaga ta wuce ɗakin Daddynsu kamin ya iso kuma babu ta shige ya dafe kanshi da hannu ya sauke numfashi shikenan Ammie zata sanar da Daddy Kai ko yaya Daddy zai ɗauki batun, har zai juya kuma sai ya fasa ya nufi ɗakin Daddyn su sai dai jin furucin da ke fita daga bakin mahaifinsu yasa Ammar daskarewa waje guda take zufa ta karyo masa hankalin sa in yayi dubu to yau ya tashi what me Daddy yake cewa ne wai me ke faruwa ne, har tsawon shekarun nan basu san wannan sirrin ba, anya kuwa kunnuwansa sun jiye masa, aiko yana nan tsaye duk ya ruɗe nan Daddy ya sake maimaita abin da ya faɗawa Ammie cikin ɓacin rai da tashin hankali sosai Daddy ke faɗan duk maganganun da suka fito bakinshi a kalmarsa ta karshe ne da ya yita yasa Ammar dafe ƙirji ya zube kasan gwiwowinsa yana karanta kalmar innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Lallai allura ta tono garma yau yaji abinda aka jima ana ɓoyewa to daman sbd wannan dalilin ne yasa Ammie ta dinga ɗaga hankalinta akan sai Hamrah tayi aure tabbas kuskure kan kuskure suka aikata lallai Ammie taso kanta dayawa. Yana nan sugunne ne yaji alamun Daddy zai fito yasa ya miƙe ya dawo ɗakinsa cikin tashin hankali. Bai tadda Hamrah a ciki ba dan haka ya soma safa da marwa yana jan numfashi yana sake tuno da abinda Daddynsa yake faɗawa Ammie. Ya soma zancen zuci why all this is happening, why from this to that?. Wai to daman babu wata alaƙa ta jini a sakaninsu ashe kuka yanzu Hamrah ta fara yinsa ashe damuwa bata kare ba, to ta yaya ma zata dauki abin kai anya kuwa ba mafarki ya keyi ba, wai shin da gaske ne tsawon waɗannan shekarun Ammie na kullatan Hamrah duk sbd da wannan dalilin ne gaskiya in har hakanne Ammie ba tayiwa Hamrah a dalci ba to WACECE HAMRAH?. Kamar wani sabon zautacce yake magana cen kuma ya dauki duk abinda ya gani ko yayi arɓa dashi yake makewa da ƙasa yana furta "Why, why, why?. Cikin sauri hamrah ta ƙaraso cikin dakin sbd jin ihun da yake yi yana maganganu duk ya kauraye side nasu da karan fashe fashe yasa ta kwantar da little Ammie dake bacci ta fito ta shigo. Ganinta kuma hankalinsa ya sake tashi yana kallon ta cikin tausayawa ya koma bakin bed ya zauna cikin tashin hankali yake sauke numfashi. A hankali ta rage tsawo ta duka kan gwiwowinta ta ɗaura hannunta kan kafadarta cikin sanyin murya ta ce Ammar kada ka tashi hankalinka please take heart, nima fah nayi shuru kuma na ɗauki dangana kuma duk fushin da Daddy zayyi nasan zai sauko kuma ya fahimce mu kaima ka nutsu kabar zubda ƙwalla. Zuba mata jajayen idanuwansa yayi yana kallon ta yana jin tausayinta har cikin ransa da ko tasan abin da hakan ya haifar da ta gwanmaci tun wuri bata ɓoye musu komai ba gashi garin haka allura ta tono garma. Cikin sauri ya janyo ta ya rungume ta ya sanyata cikin faffaɗan ƙirjinsa ya rike ta gam kamar za a ɗauketa daga gareshi cikin tashin hankali yake cewa "Bazan bari ki tafi ba, ba zayyu araba wannan alakar ba, babu inda zaki je mu ɗin jini dayane dukkanin mu ahali ne babu wanda zai bar cikin gidan nan kamawa daga kanki har zuwa kan Maryama ba zan bari hakan ta faru ba. Dan Allah kada a rabamu" Hamrah cikin rashin fahimta zancen da Ammar keyi yasa ta kwace jikinta da karfi tana kallon sa, ganin yanayin da yake ciki yanzu har yafi wanda ta tafi ta barshi a cikin ha a mai yake cewa ne, ai itama yanzu babu inda zata je tunda Ammie ta san komai abinda suke ɓoyewa ya fito fili dan haka a hankali tayi magana Ammar babu inda zanje ina nan cikin gidan kuma babu wanda zai rabamu tabbas mu ahali ne. Ka kwantar da hankalinka zanyiwa su Ammie bayanin komai kuma zasu fahimce mu. "Mun shiga uku meyake faruwa ne, menene haka cen Ammie kuka Daddy na zubda ƙwalla munzo nan ma haka yaya Hamrah kuka kaima yaya Ammar kuka ya kuke so muyi ne?" Lokaci guda suka dago dan jin muryar da basu yi sammanin ji ba a wannan lokacin, Ayshe ne da Zeenat a tsaya daga bakin kofar ɗakin Ammar sai kuma Maryama wacce ke tsaya daga baya kaɗan. Cike da mamaki Hamrah ta miƙe tana kallon su ta ce Ayshe, Zeenat daga ina haka?. Ƙarasowa ciki su kayi Ayshe ta ce Daddy ne ya kiramu a waya yace duk abinda mu keyi mu bari mu taho gida shine muka taho ganin halin da suke ciki ne yasa hankalinmu tashi sai kuma yace muzo mu ƙiraki ke da Ammar. To shine muka shigo kuma muka tadda kuma cikin tashin hankali shine duk muka sorata, wai meke faruwa ne?" Sauke numfashi Hamrah tayi hankalinta take ya sake tashi duk sai ta kiɗime jikinta ya soma rawa tunda Daddy yasa a kira su to fah abin ba kyau. Bata sanar dasu komai ba har suka fito suka wuce palour inda Daddy da Ammie suke zaune, Ammie rakuɓe gefe guda hankalin ta a tashi daga gani anyi ba daɗi kuma yau ta kure mijinta dan fah a yau ya fito tamkar ba shine ba mai daukan duk shirmenta. Yana ganin su Hamrah ya miƙe yana kaiwa da komowa wa ya juyo ya kalli Hamrah wacce ke zaune duk ta rasa yadda za tayi bata so abin yazo a haka ba, ganin yadda idanuwan Daddyn su suka sauya kala zuwa ja yasa tayi saurin sudda kai ƙasa, ya jima yana kallon Hamrah sannan ya ce "Saki nawa yayi miji?" Jikin Hamrah ya fara rawa muryarta ma na sheking ta ce Kayi hakuri.... Dakatar da ita yayi ta hanyar ɗaga mata hannu tare da cewa Ba zancen ki bani hakuri bane cewa nayi saki nawa yayi miki? Ba...ba...bab... Daman tun farko babu auren. Hankalin kowa ya tashi cikin faro aka jero salati cikin bacin rai Daddy ya ce "Babu aure, sadaki da kuma sanya rana da kuma ranar ɗaurin auren da aka tara dubban jama'a aka ɗaura shi kuma menene?. Ba aure bane ko kuma rufe ido yayi mana. Cikin kuka tashi Daddy matansa huɗu nice ta biyar. Haka ya rubuta a wasika ya ajiye min washegarin bikina ya fice. "Innalillahi wa inna ilaihi rajiun" Dukkanin ƙannenta suka haɗa baki wajen furtawa tare da kaɗuwa da abin da Hamrah ta faɗa. Sauke numfashi Daddy yayi cikin ɓacin rai ya ce "Ina wasikar?" A hankali Ammar ya ce "The letter is with me" Cikin daka tsawa Daddy ya ce "Go and bring it" Jikin tashin hankali ya miƙe ya shige cikin ɗakin sa ya ɗauko duka biyu ya kawo Daddy ya warware ya karanta a fili _Da farko ina mai baki hakuri da abin da zan sanar miki, kuma nasan zuwa lokacin da zaki yi arɓa da wannan wasikar na riga da nayi nesa dake. Sorry to say, i have 4 wives and haven't, not any single child. Ban taɓa haihuwa ba, ma'ana bana haihuwa. Abin da nayi miki ba shine na farko ba a kanki, daman ina yinsa amma nasan ke hakan zai damaki sbd ke ƴar gidan mutunci ne._ _I'm really sorry dear. Take the gift._ Cikin zafin nama Daddyn su ya danƙo wuyar rigar Ammar ya ɗagosa sama ya daidaita tsayuwar su suna facing juna, ji yake tamkar ya sami Alhaji Sama'ila ne, ya wanke sa da wani irin gigitancen mari........ ************************* _Niko Sayyada ganin haka yasa na ari na kare na fice a guje daga palour dan kada a haɗa dani ko ta kalmi ban tsaya sakawa ba, nayi waje road 🤣🤣🤣🤣_ Alhamdulillah anan na kawo ƙarshen book 1 na littafin MUJARRABI, tare suke da book 2 amma zanyi rowarsa paid book ne ga me buƙatar ta ci gaba da karantawa sai tayi payment. On Monday 20th January zan fara sake book 2 in shaa Allahu sbd na ƙarashe sa kafin mu shiga watan Ramadan. Abin da na rubuta cikin book 1 mai Amfani Allah ya bani ladansa kuskuren dake ciki kuma Allah ya yafe min. Allah yasa sako ya isa inda nake son ya iso. Ko iya book 1 nasan ya faɗar amma fah book 2 duniya ne kada ku bari a baku labarin hot love dake cikin. Wai shin ya makomar su ƴar gold ne, ya kuma Labarin Alhaji Sama'ila ne shin zai dawo ne ko kuma ba zai dawo ba. Cewa fah yayi baya haihu to ya akayi Hamrah ta haihu dashi. Menene sirrin da Daddy da Ammie suke ɓoyewa. Shin ya kuke ganin rayuwar Hamrah ta gaba. Wai shin wane irin shaƙuwa ce sakanin Hamrah da Ammar?????Duk amshoshin suna cikin book 2. *Jan kunne zuwa ga iyaye mata, dan Allah a daina matsawa ƴaƴa mata akan sai sun fidda mijin aure ko ta halin ƙaƙa SBD jinkirin yin aure da su kayi, yin hakan kuskure ne kuma shike jefa yawancin ƴan mata cikin mummunar rayuwa. Daga karshe abin yazo yana damin ku da kuma su kansu ƴaƴan. Shi aure lokacine da lokacin yayi za ayi sa mace bata tsufa Age is just a number. Allah to be sincerely ƴan mata na kokawa da iyayensu akan wannan al'amarin, Please a jasu jiki, a kuma kwantar musu da hankali wajen basu shawararwari da kuma yawaita addua.* Duk wacce tayi payment tamin magana na bata link na paid group da kuma comments section. Already daman akwai SBD tun a first pg aka fara payment. Thanks fan's. MUJARRABI 500 only inji Bature, complete document kuma 1k ne. In dai ba zaki siya ba kada kimin raddi mara daɗi dan ko a jiya wata ta turo 5k ire-irenta na da yawa ko da basu kai nata ba amma sun kamanta. *Name: Hadiza Saleh Abba* *Account number 1399826356* *Bank name access Bank* Shaidar biya 09021706569 Sai mun haɗe a paid group. Thanks fan's much love for you 🥰❤️😍👌🙏 Comments and share. An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 19 of 19