Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
acikin zuciyarki. Yanzu ba loƙacin kuka bane Fatima! ninasani zaki samu wani wanda zaifi Aliyu tsananin ƙaunar ki, ki tabbata soyayyarki da Aliyu shine ƙaddararki, rabuwa dashi shine jarabarki. Insha Allah Ubangijii zai baki miji wanda yafi Aliyu shureim zama Alkhairinki.” Saurin girgiza kai queen tayi kana cikin murya kuka tace. ”Har r abada ummie!, har abada bazan taɓa samun wanda ya kai yaya Aliyu sona da kuma ƙaunata ba, saboda ko tantama banayi cewar irinsa shi kaɗaine! Ummie tayaya kike tunanin zan SO wanin yaya Aliyu?, taya kike tunanin zan iya rayuwa irin ta aure tare da wanin yaya Aliyu? That will never happen again, forever and ever!” Ta ƙarashe maganar tana me lumshe idanunta zafafan hawayen sukaci gaba da saƙƙo mata. Tuni itama ummien hawayen suka cika idanun nata, na tsananin tausayin ƴar nata, sallamar da fareedah tayi ne ya sanya ummie saurin tashi domin hana hawayen ta damar sauƙa, da sauri tabar ɗakin tana cewa ”yawwa fareedatu ƙara da kika zo maza ki lallahi ƙawarki”. A raunace fareedah ta zauna tana zubama Fatima Idanunta da loƙaci guda suma suka yi ja. ”yaya Aliyu na gaza riƙe amanar ƴar amanarka!, na gaza yaya Aliyu!” tayi maganar cikin wata irin raunatacciyar murya, kafin taci gaba da faɗin. ”gata nan samm samm Fatima bata jin maganar kowa har yau ta gaza rungumar rashin ka da tayi yaya!, ina tsoron Allah ya kama Ni da laifin gaza cika ma alƙawarin dana ɗaukar ma kaina mai girman gaske!, pls fatyyyy ki taimaka ki daina zubar ma yaya Aliyunki ruwan hawaye haka nan. Roƙan sa na ƙarshe maganarsa na ƙarshe kece!, kece Fatimah yace na kula dake fiye da yadda zan kula da tawa rayuwar!” Dakatawa tayi tare dajan ajiyar zuciya mai ɗan qarfi, kafin cikin sheshsheƙar kuka taci gaba da faɗin, ”saidai kinƙi bani damar hakan! kinƙi bani damar hakan taya kike tunanin idan da yaya Aliyu yana raye zai barki cikin ƙunci haka?, na riƙe ki da girman Allah ya zama wannan shine hawayenki na karshe akan mutuwar yaya Aliyu!”. Cikin kuka sosai ta ƙareshe faɗar maganan tana miƙe wa da sauri don barin ɗakin, Cikin sauri itama fatiman ta miƙe tare da faɗawa jikin fareedah. ”taya wai kuke tunanin zan iya mantawa da nurul qalb!?, taya kuke tunanin zuciyana zata ci gaba da zama cikin farin ciki!?, bayan mai bata farin cikin baya raye! Kowa haushi na yake ji na sani, kowa yana ganin na gaza karɓar ƙaddarar rashin nurul qalb ne. Ta ya ya zuciyana da ruhina zasu mantawa da mutum mafi muhimmanci acikin rayuwata?” ,kafin wani irin kuka mai ƙarfin gaske ya kwace mata. Kafaɗunta fareedah ta ɗago idonta cikin na Fatima tace, ”ba cewa akayi ki manta da yaya Aliyu ba, ba cewa akai ki daina tuna shi ba, cewa akai ki daina masa kuka kin san Mea yace min? A ranar dazai tafi. ” cikin zubda wahaye ta kuma duban Fatiman tace. ” cewar Ga Amanar ƴar Amana na Nan na bar miki, ki kula min da ita, fiye da yadda zaki kula da taki rayuwar!, ki kula min da ita har zuwa sanda zan dawo, ko sau ɗaya kada ki taɓa barinta ta zubar da ruwan hawaye ata dalilin rashina!, Duk da haka bai yi shiru ba duk kuwa da irin yadda Mama ta ringa ƙoƙarin hana shi maganar, bai haƙuru ba har yaje bakin qofa ya kuma duba na cikin muryarn dana kasa tance ta har kwanan gobe yace._ ki cika min alƙawarin da nabar Miki fa_ cikin zubda wahaye na dube shi kinsan me ne ce masa?” Ta dubi tsakiyar idanun Fatiman tace. ”ce masa nayi_ I promise you! yaya nayi alƙawari” cikin ƙunar zuciyar da ɗacin tuno da ƴaƴanta tace, ”saidai kin gaza taya ni cika alqawarin yayana Fatima!” tayi maganar cikin wata raunatacciyar murya. Wani irin ɗamke Hannuwanta Fatima tayi daura kanta a Ƙirjinta fareedah, kafin cikin sauri ta ɗago tana goge hawayen dake kwance saman fuskarta cikin murya mai kama da a zauce take. ”tace waye?" Inji wayeeeee yace Miki na gaza tayaki cikon alkawarin nurul qalb!, Insha Allah wannan shine ruwan hawayen da zai kuma sauƙa ata dalilin mutuwar yaya Aliyu Naaaaaa ” sosai itama fareedah ya rungume Fatiman kamin cikin zallar farin ciki tace. ”alhamdulillah! Alhamdulillah fatyyyy Naaaaaa yaya zai yi farin ciki dajin hakan da yana raye, Ubangijii Allah yaji ƙanka yayanmu” suka faɗa a tare, kafin su kalli juna sai kuma kowa ya shiga nuna ɗan uwansa suna sakin murmushi mai tafe da ruwan hawaye. ___________ *Amnah* Cikin murna da tsantsan farin cikin dake ɗauke a fuskanta ta ce "Ammiey papiey ya kusa dawowa” amnah faɗa tana faɗawa jikin Ammiey cikin tsagwaron zallar farin ciki. jan kumatunta ammiey ta yi tare da cewa "duk wannan murnarn dawowan papieyn kine?, to tsaya ma waina waya faɗa miki?” ammiey ta tambaye ta tare da zare farin siririn glass ɗin dake Idanunta. ”uncle Irfan mana ammiey, kuma murnarn ya kusan kawo min new Mamie ne manaaaaa” ta yi maganar tana sauka daga jikin ammien tare dayin woje a guje tana faɗin. ”ammiey kar nayi let na tafi school” wani irin murmushin tausayin amnah ammiey ta saki. Tana hasaso ranarn da ALIEYON TA zaiyi Aure. da kuwa ita ne wacce zatafi kowa farin ciki da kuma murnarn wannan abu, Irfan dake tsaye tun ɗaxun ya zauna kusa da ammieyn, ”wanne irin farin ciki ne ya sanya ammiey na sakin murmushi ita kaɗai har haka?”, shine abinda Irfan ya faɗa yana ƙarasa zaunawa kusa da ammieyn nashi, still ta kuma sakin wani murmushin tare da kallon sashen da Irfan ɗin ke zaune, cikin tsananin zallar farin cikin haɗin da yanxun yazo mata cikin zuciyarta ne yasa kai tsaye tace da Irfan ɗin. ”yayanka nawa Mata” ba tare da fargaban komai ba ammien tayi maganar still dai murmushin na nan d Shimfiɗe saman kyakkyawar fuskarta. Cikin shiga alamar ruɗu Irfan ya ce ”ammiey me ki kace? Kamar fa jinin jiki naji kina maganar yima mata?” wani irin murmushin baka da wayo ammien ta masa tare da cewa. ”shakku ka cire Irfan yayanka ALIEYO! Na yima mata wacce ta dace daidai da shi Insha Allah” Murmushin ya saki shima domin ya riga da yasan halin yayan nashi cikin bayyana tsantsar gaskiyar sa yace, ”haba ammiey ya kamata kina ɗan jin tausayin jinin jiki haka nan mana, tun dai ba wani mugun abu yake mara ƙyaun da zai bada shaidar kasa riƙe kansa yayi ba!, pls sweetheart Ammeynmu kiyi haƙuri har zuwa loƙacin da yaya ALIEYON zai kawo matar da yake so da kansa har gida mana” , kallon baka da hankali ammiey ta jefi Irfan dashi tare da miƙewa tana barin main Parlourn tare da nufar upstairs nata. Da kallo kawai Irfan yabi ammien yana jin wani irin bala'in tausayin ɗan uwansa yayansa alieyonsa. ______________ *ALIEY* Ahankali ya ɗago kansa wanda ya kwashe sama da 30 min a zaunen da yake, fararen santala santalan sawayensa zube cikin swimming pool ɗin. Ahankali yake karkaɗa qafafunsa cikin ruwan. Tuni kaso mafi rinjaye na daga cikin kewa da kuma tunanin Sofeeynshi yaji yana nemar komai yana rasawa na daga cikin abinda ke damunsa. Aƙalla yafi ƙarfin sama da 40 mints awurin yana jin sassaucin abinda ke son taso mashi, duk da yana qoqarin dannewa tsayin shekaru masu ɗan dama.Cikin yanayin dake bayyana tsantsarn nutsuwar da ƙaton beach ɗin ya bashi, sosea yaji wata iriyar nutsuwa tattare dashi, Idanunsa ya ɗan lumshe kana akasalance ya furta, ”Ya Rahman” loƙacin da yaji mararnsa yayi wani irin bala'in murɗa masa, yana ɗan taune jajayen lips nashi tare da dafe saman mararn. yasa cikin sauƙi zaka fashimci cewar mararsa ne ke ciwo, musamman yanda ya dafe kan marar da tafin hannunsa. sake lumshe tsumammun idanunsa yayi yayin da yaji wasu abubuwa na shirin kassara rayuwarsa, ahankali cikin daure ciwon da yakeji amarar ya taune lips nashi da ɗan ƙarfi tare da nutsa hannuwansa cikin tulin sumar dake kwance luff luff saman kansa.ya shiga chakudawa da duka hannuwansa. Kafin a wahalce ya miƙe yana tangaɗi tamkar ɗan maye yana nufar parking space na cikin Beach ɗin, cikin sauri ɗaya daga cikin yaran shi ya buɗe masa wata narkyakkiyar motor ƙirar Lexus, wacce ta kasance Black mai Black ting. Cikin sassarfa ya kutsa kansa cikin lafiyayyar motar. Babu ɓata loqaci ya faɗa cikin motorn yana yin reverse tare da fita aguje yana cilla hancin motar suuuuuu cikin tsakiyar titin na qasar Dubai. Basu yi wota tafiya mai zurfi ba suka isa haɗaɗɗen hotel ɗin da yayi boking, ko gama daidaita parking drive'rn baiyi ba motorn Ya fito. Qafafuwanshi ya fara zirowa kafin ya fito baki ɗayansa. Eyephone nashi kawai ya iya ɗauka tare da nufar cikin haɗaɗɗen hotel ɗin,baki ɗaya hankalin mafi rinjayen fitsararrun ƴem matan da suke nan tamkar tsura re ne ya dawo kansa, cikin sauri da kuma ƙemƙemin ƴan matan ya kutsa kansa cikin jerin ɗakunan hotel ɗin. Babu zato babu tsammani yaji anyi wani irin faɗo masa jiki, tamkar wanda aka jona ma shocking yayi wata iriyar zabura, tare da juyowa a haukace yana wanke fitsaararriyar fuskar wacce ta iya haɗa ƙazamin jikinta da tsarkakken jikinsa. A zuciye yayi wani irin bala'in buga kanta da ƙarfin masifa. Wata iriyar razananniyar ƙara sadra ya saki lokacin daya kuma yin cilli da ita, cikin bala'in zafin zuciya ya nufi part 0122 yana haɗe baki ɗaya abubuwansa Yana barin hotel ɗin baki ɗaya. Wannan ƙazamammiyar rayuwar yake ƙamata shi yasa sammm ya dena boking ko wanne hotel yafi gane yayi zamansa cikin jirgi Yayi rayuwarsa shi kaɗai. A irin wannan masifaffan yanayin da yake ciki ne yaji ina sammm bazai iya ci gaba da zama a wannan ƙasar ba, baki ɗaya yaji komai da komai na sire mishi yana jin wata iriyar tsana da kuma ƙamatar banzaye masu banzan hali irin haka. Shi mutum ne daya kasance mai tsautstsauran ra'ayi, haka shi mutum ne da yake gudun duk wani laifi na saɓa ma mahaliccinsa, yana bin duk wasu ƙa'idojin dake cikin tsarin mahaliccinsa, yana gudun duk wani abu ko duk wani abin ƙi daya saɓama addinin Musulunci. Hakan ya sanya cikin ƙankanin loƙaci ya buƙaci barin ƙasar duk kuwa da cewar sai nan da 6 days yake da tashi. Baki ɗaya yaji gida kawai yake da buƙatar komawa domin sammm zuciyarsa tana cikin wani irin masifar yanayi mara ƙyan gani, wanda a zahiri da za'a buɗe zuciyarsa da kuwa tabbas kun girgiza da ganin abubuwan dake tanƙare a cikin ta. A loƙacin 1:1pm na dare ne. Amma haka ya keta hazo yana barin kasar masu jajayen kunnuwan Nan, komae da yake cikin jirgin cikin ƙarfin hali da dakewa yake aiwatawa.haka yake sarrafa na'u'rorin jirgin. Cikin talatainin dare jirgin yayi dirar mikiya a cikin ƙasar sa 9j wanda ya ɗan jima rabonsa da kasar. Domin kuwa ana sallacewa yabar 9j gashi yanxu wajajen watanni bakwai keñan da ƴan sati kai ake magana,kamar ko wanne loƙaci irfan ne yazo ya ɗauke sa, cikin tsaƙiyar daren. ******** ”don Allah yaya Vijay da gaske kake?” queen ta faɗa tana marairaice, murmushi aunty zeey ta saki tana faɗin ”idan baki shirya ba mu saimu wuce ai ko julay” tayi maganar tana kallon julaibeeb dake riƙe da hannun baban shi. Rungume aunty zeey tayi cikin farin ciki tana faɗin, ”wllh nasha da wasa yake min rabona da zuwa shop harna manta wllh”. Kafin ta sake ta ta nufi ɗakinta a guje cikin mintunan da basu gaza biyar ba sai gata ta dawo cikin shirin fita, inda ta sanya riga da wando na Pakistan ire-iren waɗannan yaya jay ɗin ta ya siyo mata a India. Sallama sukawa ummie suna fita coumpaund na gidan suna daukar hanya. A wani ƙaton plaza A&A motarsu yayi parking, kana kallon wurin zaka san ba wurin zuwan kowa da kowa bane, kasan sai wane da wane sai wanda yaci yasha kana ya tasa kai ne kaɗai keda hurumin shiga cikin plaza ɗin. duba da irin rantsantstsun motocin dake fake, da kallo kawai queen kebin wurin da kallo domin ita dai tasan bata taɓa zuwa wurin ba, iyakarta shoprite dadai sauran wurare. Dab da wata narkyakkiyar Bugatti Chiron suka faka motarsu, a nutse suka fito yaya jay yana ɗaukar julay a kafaɗarsa, cikin girmamawan dake nuni da alamun sanayya tsakanin sa da ma'aikatan suka suka gaisa, suna shiga cikin hasalin plaza ɗin. A take cikin queen ya bada sautin ƙugi, ganin uban jami'an dake kewaye da wurin rike da manyan bindugu a hannunsu. Wani abu kaɗai da bansan miye ba yaya jay ya nuna musu, a take cikin girmamawa suka yi solid na yaya jay tare da basu hanya bayan an jona musu na'urorin gwaji, kafin su keta cikin ƙaton plaza ɗin. Garin kalle kallenta su yaya jay suka ɓacema ganinta. Tana rike da ɗan keken da take dibar duk abinda ya mata. Bakinta ta ɗan tura gaba tana ƙunƙini ita kaɗai, tare da soma tafiya tana bin gefin dogon benen dake da tsayi da zurfi kenan. Rolex ɗin dake ɗaure a tsintsiyar hannunsa ya yake dubawa a nutse, don ƙa'idar sace yin komi akan loƙaci tamkar yanda ya gindaya konace yari ga ya tsara ma Rayuwar sa yin komi akan time nashi, don aganinsa bashi da loqacin ɓatawa loqaci loqacinsa, komi yana yinsa ne akan loƙaci sa ba tare da wani ya shiga cikin woni ba, donshi mutum ne mai tsananin bin kowacce ka'ida acikin dukka lamuransa. Wasu haɗɗaɗu kuma tsadaddun track Suit ne a jikin sa blue black, sai SKY blue denim jacket daya daura a saman tsadaddun suit ɗin, ƙafafunsa sanye da wasu tsadaddun white sneakers shoe. Baisan da xuwanta ba kawai dai yaji an bangaje shi. ganin ba tare da antsaya ko an bashi Haƙuri bane ya sanya ƙafarsa tare da farɗo ta baya. wani irin gigitaccen ihu ta saki wanda ya janyo hankalin duka jama'ar dake ƙasan benen, sammm baiyi tsammanin ƙasan zataji ba hakan ya sanya cikin sauri ya sanya hannunshi ɗaya ya sanya tallafi daidai kanta, ɗayan hannunshi kuma yakama daidai waist nata yana janyota, kai tsaye saman faffaɗan qirjinsa ta faɗa wata iriyar ƙatuwar ajiyar zuciya ta sauƙe loƙacin data jita jikin mutum, hakan yasa ba tare data tantance ko waye ba ta sanya duka hannuwanta biyu tana zagaye ƙungunsa tsammm, tare da ɗaura kanta saman ɗamtsen hannunsa. Baki ɗaya jama'ar da suka bada attention nasu a wurin suka shiga sauƙe ajiyar zuciya , donba ƙaramin faɗuwa zatayi ba inda Allah bai kiyaye ba,Ciki kuwa har da yaya jay da kuma aunty zeey. Ahankali yazare hannunshi daga kan waist nata yana yanyeta a jikinsa tare da tsayar da ita akan qafafunta, idonsa kan fuskanta yana kallon yanda ta ƙanƙame idanunta gam gam cikeda tsoro pink lips dinta nawani irin shaking dayasa dimples nata na lomawa da ƙyar ya motsa motsa lips nashi wajen furta, ” You again?” Muryan dataji yadaki dodon kunnuwanta yasanta buɗe idanunta don gasgata muryanrn data riga ta zauna a kanta daram tamkar wacce aka naɗe muryan a tsakar kanta. idanun nan nata manya masu kama dana mage ta shiga buɗewa akan kyakkyawar fuskanshi ta sauƙe ganinta, jitay numfashinta ya makale ganin fuskanta dab da nashi ya zuba mata wannan firgitattun idanunsa yana kallonta. Cikin jin tsanar rashin kamun kanta ya ɗauke saman kyakkyawar fuskarta da kyakkyawanr mari, cikin takaici ya furta. ”You are the one who knows the donkeys, and is calm and self-controlled”. da azabar ƙarfi ta dafe saman fuskarta tana sakin wani irin raunataccen kuka, a kuma daidai loƙacin Amnah dake tare da ammiey suka iso wurin. Dai su yaya jay na ƙarasor suma cikin sauri ammiey ta tallafi queen tare da shigar da ita jikinta. Cikin kulawa ammiey ta ce ”Hi Stop crying,what happened to you?" Kanta ta shiga jujjuyawa a jikin ammien tana kuma sakin wani kukan, Amnah da sai loƙacin ta kula da ashe Fatima ce ta ƙarfi tace, ”laaaaa waye ya saka new Mamie na kuka na haɗa shi da papieyna ya rama mata ammiey?” Ta ƙare zancen da tambayar ammeyn, papieyn nata ammiey ta nuna mata tana cewa ”He is ganan a gabanki” ta faɗa a fusace tare da kama hannun Fatiman tana yin wurin motarnta da ita cikin wani irin mugun ɓacin rai. Da sauri yaya jay yabi bayan ammiey da sauri shida aunty zeey. Kama hannun papieyn ta tayi tare da cewa ”da gaske papiey kaine ka doke ta new m… ”AMNAHHHH” ya faɗa cike da wani irin mugun tafasan zuciya yana dunƙule hannun sa tare da kaima iska naushi yana surarta a fusace. Coumpaund na plaza ɗin ya nufa cikin rawar jiki duk inda ya ratsa sai kaga masu tsoron plazan na rusunar da kansu cike da girmamawa. Yana zuwa parking lot motar ammiey na barin wurin, luuuuuu idonsa yayi kafin ya buɗe da tsananin ɓacin ran ganin akan wannan ballazar yarinyar ammien shi tayi fushi dashi, ta tafi ta bar shi. Wayarsa ya ciro yana dialing wata NO, ko mint 1 ba'ayi ba ɗaga daga cikin soldier's ɗin nan ya kawo masa car key na motor jiki na rawa, fisge key na motorn yayi a fusace tare da nufar wata sabuwar bakar Benz yana faɗawa ciki tare da mata key yana janta da wani irin bala'in gudu.da sauri Amnah ta ƙamƙame jikinta wuri guda tana rarraba idanu ganin yadda yaja motar da mugun gudu. Cikin ƙankanin loƙaci ya isa gida a haukace ya shiga dannawa me gadi hong, wanda yasa a firgice get man ɗin tashi yana wangale ƙaton get ɗin, da sauri yaja baya ganin tamkar aliey zai yi ciki dashi. Ko gama daidaita parking baiyi ba a matuƙar zuciya, dade da Amnah baba *💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘* ~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~ *🌠OFFICIAL MIRRAH 💫* *WRITING* *AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️* Page 21&22 *Alhamdulillah forever and always 👏* Wannan page in sadaukarwa ne gareku my fans nawa allah yabar ƙauna 🥰🥰🤎 ________* _________★★★_______ ♥️🤍♥️ Baba mai gadi ne ya fito da ita. Cikin ƙunar zuciya yake taka step bibbiyu ko ganin gabansa baya yi tsabar bala'in ƙunar zuciyar sa ke masa.cikin tafiyar sassarfa yake nufar upstairs nashi, yana shiga bedroom ɗin ya fesar da wata zazzafar iska daga cikin bakinsa, har yanzu bibbiyu yake kallon komai yana jin yadda bedroom ɗin ke jujjuya masa. Lumshe rinannun idanunsa yayi domin har zuwa yanzun itane acikin ƙwayar idonanunsa, yana jin yadda zuciyar sa ke yamusta masa, idan harya hasko yadda ta wani zagaye ƙugunsa ta kuma kwantar da kanta saman ɗamtsen hannunsa, ji yake tamkar an rura masa wuta ne ne a cikin zuciyarsa ne. Kana yana yin yadda zuciyarsa ke harbawa da masifar ƙarfi ne yasa, ya wani irin taune ƙasar laɓɓansa da ƙarfin masifa. Domin kuwa har yanzun ya gaza mantawa da haɗuwarsu na farko, yadda ta faɗar masa saman jiki, ta wani cukuwkuye shi. Sake rumtse idanunsa yayi sakamakon yanda yaji zuciyarsa ta bala'in buga da ƙarfin masifa. Sosai wannan karon ya buɗe rikiɗaɗɗun idanunsa da har zuwa yanzun suke ganin komai dishi dishi, kai tsaye bedroom yana haɗa ruwan wanka acikin babban jakuzzie me tsananin sanyi,wai ko hakan zai sa yaji sassaucin ƙunanr da zuciyarsa ke may. Sassanyar ajiyar zuciya ya saki loƙacin da yaji ruwan sanyi na ratsa gaɓɓan jikinsa. Shiru yayi yana sauƙe ajiyar zuciya akai akai tamkar irin wanda yayi gudun wasan tseren nan. Koda ya fito daga bathroom ɗin kuwa wani farin towel ne ɗaure akan waist nashi,yayin da gaba ɗaya gargasan jikinsa suke a mimmiƙe, Cikin takunsa me ɗauke da wata iriyar izza da kuma zallar ƙasaita ya shige cikin clothes nashi. Da sunayen Allah cikin bakinsa da yake ta faman jerawa, maida idanunsa yayi yana kullewa tare da ware su wanda kuma hakan alamace dake nuna cewar ya sami cikakkiyar nutsuwar da yake buƙata...... Da tarin tunanin nika fall zuciyar ammiey a haka har tayi parking motarta a coumpaund na gidan, zuciyarta naci gaba da saƙa abubuwawa maban banta masu ɗan dama,ga kuma kukan da queen ke faman yi har zuwa yanzun kuwa, idanu ta zuba mata yayinda kukan queen ke ratsa jiki da zuciyar ammien. Domin kai tsaye ta fashimci ko kukan mene queen ɗin keyi tsananin tausayinshi ne ya ƙara kama zuciyarta sosae fiye da tunanin duk yacce kuke tunani. Hannuwanta Ammiey ta kamo tana fitowa da ita waje tare da ɗan jingina ta da jikin ta, tuni dama yaya jay da aunty zeey sukayi nasu gidan directly. Cikin gidan suka nufa suna tafe tunani ya cunkushe ma Queen tarasa wane kalar ma tunani zatayi dan gane da wannan mugun abokin yayan nata, ahankali take taka ƙafadunta har suka kai main Parlourn Gidansu dab da gaban ummien ta ta tazauna. Ganin queen tare da ammiey kuma yasa ummie tambayar ammiey ko lafiya?, ɗan murmushi irin mai ciwon nan Ammiey ta saki tare da zama kan ɗaya daga cikin kujerun parlourn, tana sauƙe ajiyar zuciya. Kafin cikin yanayin damuwa tace. "Ita da wannan ɗan uban zafin ran ne mana ALIEYO!, daga haɗuwarsu a cikin plaza ya kama makarta haka nan kawai”. ”baki bibiyi yadda abin ya faru bane Mom ALIEY! Amma tabbas ni nasan haka takanas ba tare da laifin komai ba alieyo bazai kama Fatima ya dake taba, tunda dama ba xuwan kanki bane, ƙarar ɗana kika kawo kinga tafiyana” ummie tayi maganar tare da miƙewa, da kallo irin na burgewar nan Ammiey tabi ummie dashi. Tabbas bata ma aliey zaɓen tumun dare ba ita kanta tasan da hakan, hankalinta ta dawo dashi kan queen da tunda suka shigo take sakin ajiyar zuciya, duban Fatiman tayi tare da kama hannuwanta cikin sigar lallashi tace ”kiyi haƙuri kinji Fateemerh Ni! da kaina zan sanya ALIEYO Naaaaaa ya baki haƙuri har ƙasa kuma zai turkusa Miki, na Miki alƙawarin hakan koda ba yanxu bane kuwa Fateemerh kinji daughter Naaaaaa” wani irin matsanancin farin ciki ne ya kama Fatima jin abinda Ammiey tace da ita, hakan ya sanya t jin wani irin azababben daɗi mamaye ta har batasan loƙacin data ƙanƙame Ammieyn bama, cike da matsananciyar murna ta furta. ”Da gaske kike Loli Ammiey Naaaaaah” lumshe idanu Ammiey tayi duk Duniya babu me gaya mata wannan sunan face mutum ɗaya. ”ALIEYO!” Ammiey ta faɗa tare da sauƙe Idanunta kan fatima (tabbas kin chanchanta Fateemerh ke kika dace!) aceñnn ƙasar zuciyarta Ammiey tayi zancen. ”Ko zamu tafi tare xuwa dare saina dawo dake” muryarn Ammiey ya daki kunnuwanta a matuƙa firgice ta ɗago tare da duban Ammieyn, tuni Idanunta harya tara ƙwalla kanta ta shiga jujjuyawa kafin cikin danne kukanta dake son kubcewa tace. ”zai kuma duka nane fa Ammiey” ”inji waye yace zai kuma dukanki?, ai yayi na farko yayi na ƙarshe kisa hakan a ranki kinji daughter Naaaaaa” (Na biyu dai ammey) Ta faɗi a zuciyarta. Jin kamar tayi magana ya sanya ammiey faɗin. ”mene kika ce Fateemerh?” . ”bance komi ba ammey” ta faɗa tana ɗan murza hannuwanta, "Okk " ammiey ta miƙe tana faɗin "Ni zan wuce gida na bar Amnah ita kaɗai sai babanta shi kuma a wannan murɗaɗɗen halin nasa nasan ita kaɗai zai barta, tayi ta watan gaririya a cikin gida" jin an ambaci Amnah yasa Fatima miƙewa da sauri tana cewa "ammiey na fasa ƙin xuwan, yanxu zan bikin mu tafiiiiiiiiiii" murmushi ammiey

Chapter 8 of 23