kuma ummie wajen bin Dr ɗin.
Sosai Abba ya tsureta da ido ko ƙyaftawa baya yi, ganin yadda Dr ɗin take ta mulmula baki alamun maganar da take son furta wa mai girma ce.
"A gaskiya nayi mamakin yadda aka yi ƴar ƙanƙanuwar yarinyar da bata fi 17 to 18 years ba ace ta kamu da hawan jini ba.
Amma da sauƙi kar ku tada hankalin ku zan ɗorata kan magani In shaa Allah za'a dace"
TundA ta fara maganar suke binta da IDO taya ma har zata yi wani tunanin kwantar musu da hankali bayan tace musu fatimansu na ɗauke da cutar hawan jini. Sosai hankalin su ya tashi hannu na rawa ummie ta ɗauka file ɗin tana yin woje xuwa wurin su yaya jay.
Da sauri suka nufo ummien ganin yadda hankalin ta yake a tashe, yaya jay ne ya amshi file ɗin dake riƙe a hannun ta wani irin ja da baya yayi tare da kaiwa jingine da jikin ginin. File ɗin na faɗuwa ƙasa.
Saurin ɗaukar file ɗin yaya Nurien yayi shima dai hakan ce ta kasance a gare sa domin shi harma yafi yaya jay shiga shock ɗin.
Saurin rufa musu baya sukayi ganin Abba da Dr na shirin shiga room ɗin da aka kwantar da ita. Koda shigarsu kwance suka tarar da ita hannunta ɗaure da kanular ruwan da aka ɗaura mata. Zuba mata Ido suka yi baki ɗayansu cike da tsananin tausayin ta taya ma za'a ce yarinya ƙarama kamar queen ɗin hawan jini ya kama ta.
Suna a tsaye jigum jigum saiga Mama ta faɗo ɗakin ita da fareedah ahujajan, zaune takai raɓas gefen gadon da queen ke kwance hannunta ta kamo tana haɗewa da nata, kafin hawaye irin mai ɗacin nan ya zubo mata na tsananin tausayin fatiman.
Ta sani har yanxu idan da wanda mutuwar Aliyu shureim bata saki ba to mafi ƙololu ita da queen ne, "kiyi haƙuri! Kiyi haƙuri Fatima Allah baya taɓa barin wani dan wani, da yana bari to da ya bar mana Aliyu shureim ɗinmu ya ɗauki tawa rayuwar!" Sharrrrr haka hawaye ya wanke mata fuska tuni.
Jin alamar damshim ruwa a jikinta ya sanya ta buɗe kunburarrun idanunta, Ahankali ta shiga buɗe su duk kuwa da nauyin da suka mata ga kanta da take jin tamkar zai rabe gida biyu.
Da sauri Abba da shine kaɗai ya lura da farfaɗowar nata ya kama hannunta ɗaya cikin kwantar da murya kaɗan yace, ” Sannu fatin Abbanta faɗa min mi ke maki ciwo yanzu? "
Kai ta girgiza alamun babu sai ya cigaba da cewa "to faɗa min minene ya saka ki damuwa har kika shiga wannan hali?Dr tace za ki iya samun sauƙin ciwon"
Da mamaki shiga kallon Abban jin abinda yake cewa, sai kuma tayi saurin duban gefen ta jin kamar motsin wani abu. Ganin Mama ce riƙe da ɗayan hannunta ya sata ɗan ware idon ta kafin ta shiga bin room ɗin da kallo karan kataf ta gama fuskantar komai sai yanxu ne komi ya shiga dawo mata cikin Brain nata lumshe ido tayi. Tana koma wa ta kwanta.
Ganin ta farka kuma daman ciwon da sauƙi ya yazo mata yasan ya Dr laylerh sallamarsu, tace zata na xuwa dubata akai akai sosai suka gamsu da maganar nata haka yasa suka tattara suka koma gida.
Kowa na ƙoƙarin ganin ta dawo normal nata.
__________★★★___________
# New York
Cikin nitsuwa yake tahowa sanye da farin rigar sport designer ta companyn NIKE mai ɗauke da cap da dogon wando alaman daga street warming execise ya ke.
Ko ina ya ɗauki shirun safiyar ranar ga sanyi irin mai ratsa jikin nan sosai don haka a gurguje ya bude ya faɗa bathroom yana sakar ma kansa shower yau kusan 2 Months keñan da zuwan sa amma komai na nan a yadda yake saima ƙara hauhawa da abubuwan suke ya ɗan yi duhu kaɗan ba kamar sanda yazo ba.
*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*
~Heart touching love, with love aside 🤍🤍~
Page 27&28
*BY*
*AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️*
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Yau page ɗin nakine Zainabu mai tagwayen suna, na baki kyautar page ɗin a matsayin gift na tayaki murnar zagayowar ranar haihuwarki.
# Happy birthday 🥳 🎉 to the most wonderful sister in the world!
# I hope your special day is as amazing as you are 🥰. May all your Insha Allah turn to Alhamdulillahi.
Happy birthday once again DEAR 💐💐💐💐💐💐💐
As gifts 🍢🍿🥂
____________________
# _LOVE ASIDE❤️🔥🔥_
♥️🤍♥️
Yau wajen kwanaki biyar keñan da sallamo queen daga asibiti, amma har xuwa wannan loƙacin komi bai sauya daga yadda yake ba. Saima zancen auren dake ta ƙara kusanto kansa a duk loƙacin da zataji ana maganar auren nan ji take Kamar zuciyarta zata faso ƙirjinta ta fito haka take ji a duk lokacin da maganar aurenta zai faɗo mata,ta kanji duniyar ta ƙara mata zafi da baƙin cikin zamanta a ciki, tabbas ta san da Ubangiji shi ke jarabtar bayinsa ta ko wacce siga, tasan tata ƙaddarar mai zafi ce zafin da mutan bazai taɓa tunanin ji ko gani a aikace ba sai har in ƙaddarar hakan ta gitta maka. To anan ne zakafi kowa fashimtar ya raɗaɗi da kuma zafin abin yake.
Wasu zafafan hawayen da suka kuma zubo mata ta share tana kawar da kanta gefe tare da karanta Addu'o'in da zasu sauƙaƙa mata zuciya. Cikin ƙudir ta Ubangijiin Rahama tuni taji zuciyarta tayi sanyi, a take wurin kuma barcin data kwana bata yiba ya ɗauke ta.
Bangaren ummie kuwa ganin shirun yayi yawa ne ya sanya ta miƙewa tana nufar ɗakin nata, tare da faɗin. "Fatima lafiyar kuwa daga shiga ɗaukar...... Sai kuma taja ta tsaya turus ganin ta kwance saman tiles ɗin ɗakin, tana barci irin wanda baka shiryarma zuwansa ɗin Nan, a Zahirance dai zaka iya ƙiransa da barcin wahala, ko daga yanayin yadda ta takure wuri guda, bata tashe ta ba illa binta da ido kawai da tayi, cikin tsananin tausayama rayuwarta.
Fita tayi daga ɗakin tana komawa kitchen nan yaci gaba da aikin ta cikin rashin kuzari, da jin babu daɗi aceñnn ƙasar ranta. Sosae Fatima iya barci na mamaki, koda sallar zuhr da Abba ya shigo yana tambayar ta ina Fatima tace masa rana cenñnn tana barci tun ɗaxun, Haka ma yayyenta duk wanda zai shigo saiya tambaya queen har ɗakin suka bita ganin kuma har loƙacin tana barcin ne ya sanya su barin ɗakin kowa yana kama gabansa.
3:47Pm
A hankali queen ta shiga buɗe idanunta da take jin nauyin su ya ragu sosae har ta buɗe su duka bakinta ɗauke da Addu'ar tashi a barci. ƙafafunta ta fara saƙƙowa ƙasa tana miƙewa sai kuma tayi saurin mutsitstsike Idanunta waiko gizo suke mata, ganin dai cewa da gaske tabbas anyi la'asr ɗin ne ya sanyata shigewa cikin bethroom. Alwula ta ɗauro wasi wasi falllll ranta, ita data kwanta tun wajajen goman safe har ma taya akayi tayi wannan uban barcin.
Da haka tai tarin tunaninnika ta shimfiɗa darduma tana tayar da Sallah, takai raka'ar farko ummie data kuma zagawota wata iriyar ajiyar zuciya ta saki tana zama daga bakin gadon fatiman.
A nutse take yin sallar, kai yadda take sallar ma shi kansa abin burgewa ne. Bayan ta idar ne ta juyo a ɗan sanyaye tana duban ummienta, Ahankali ummien ta janyo kan queen tare da azawa bisa saman cinyarta.
”FATEEMERH!”
Ummie ta ƙira sunanta a raunace, ”Na'am ummie Naaaaaa‘ ta amsa tana mayar da dukkan wata nutsuwa tata wurin ummien tare da ɗago kanta tana fuskantar ummien.Ummieh da ta kafeta da ido ko kyaftawa ba tayi.
Jin yadda jikinta ya ɗauki zafine yasa wasu kyallar tausayin fatiman kama ummieh, Saida ta sauƙe ajiyar zuciya kafin cikin ƙarfin hali ta fara irin ƴan nasihun da ta kanyi mata a ƴan kwanakin nan.
”Mamana har yanzu na kasa yadda da kin karɓi ƙaddarar da Ubangiji ya jarabceki da ita, kin kasa amsar ƙaddararki a yan da ta zo maki Fatima!, ya kamata ki farka komene zaki a cikin wannan duniyar to la shakka Aliyu shureim bazai taɓa dawowa gareki ba, gidan wani zakije Sammm zamanku bazai taɓa iyuwa a haka ba, Idan har kika ce haka zakici gaba da ire-iren waɗannan Abubuwan to tabbas rayuwar aurenki ba zaki taɓa jin daɗin sa!, ba zaki taɓa ɗanɗanar tarin ni'imomin dake cikin auren ba”
Saida ta ɗan dagata kafin taci gaba da faɗin.
”Ni! Uwace Fatima kuma akwai zuciya a tsaƙiyar ƙirgina, taya kike tunanin zan iya samun nutsuwa kina a wannan yanayin?, mun zaunar dake mun tambayeki ko auren ne baki so amma kince a ahhhhh!, to shin wai a ina hasalin matsalar take?, ki tuna da ke kaɗai ce ƴa ɗaya tilo mace a gabanmu da Allah tamu yayyenki biyu maza ne kuma Ni ɗin dai nice abokiyar shawararki.
domin ban yarda ba ban lamunci ɗibar sirrikanki kina baiwa ƙawayen yanxu da ba amana suka sani ba, idan sirrinki ya wuce to kuwa sai ƴar uwar ki fareedatu. Kuma ina so wannan yazam shine maganganun ƙarshe dazan ƙara zama yi miki akan wannan auren.ki cirema ranki damuwar komi ki rungumi Sabuwa rayuwar dake daɗa kusanto kanta gareki, ki rungumi ƙaddararki da hannu bibbiyu a duk halin da tazo mana hakan shike bayyana kwarai kacika cikakken musulmi na kwarai, wanda Ubangijiin sammai bakwai yace ayi koyi da masu haƙuri da kuma masu rungumar ƙaddara da hannu bibbiyu a duk yacce tazo musu, Ubangijiin Rahama da kansa yace Ni! Kuma nayi ma wannan bawa nawa alƙawarin bisanya ƙaddarar sa daga mummuna zuwa kyakyawa!. Ba buƙatar naci gaba Fatima domin zan iya cewa indai a wannan fannin ne Sammm bana da haufi akan ki, ya kamata ki dawo cikin hayyacin ki!, hankalinki ya dawo jikinki, Ubangijii shiya amshi Ran Aliyu shi kuma ya ƙara baki wani ALIEYON! godiya ya kamata kiyi ma Ubangijin talikai.”
Wata iriyar ajiyar zuciya Fatima ta sauƙe tare da ƙanƙame ummienta ƙammmmm, jikinta ya shiga kerma da mukyarkyata. Hawayen da take riƙewa ne suka sami damar zubo mata cikin Muryar da taci kuka sosae ta fara magana.
”wllh ummiena na karɓi ƙaddarata a yanda tazo min zan kasance mai biyayya ga Ubangiji na, kan zan kasance mai tsananin biyayya da umarninku, kuyi haƙuri Insha Allah za kuyi alfahari dani anan gaba, na amshi ƙaddarar rashin yaya Aliyu Naaaaaa!, na amshi ƙaddarar auren da zaku min. Ku yafemin kusakuraina na baya gare ku don Allah”
Da ƙarasa Maganar tana haɗe hannayenta wuri kuda alamar roƙo .
sake rungumota tayi xuwa jikinta Ahankali ta shiga shafa samar lallausar sumar dake baje kan queen. Sosai ta shiga kokawar rike hawayen dake son zubo mata na tausayin ƴar nata.
Abba da tun farko fara nasihar ummien yake tsaye kansu saidai su Sammm Basu ma san da tsaiwarsa a wurin ba.
”Alhamdulliha Ala kulli halin!, Shi yasa ahar kullum nake alfahari da samun Mata ta gari kamarki A'ISHATU, nake kuma alfahari da kasancewar ki uwa ta gari ga ƴaƴayenta.”
Daga ummie har queen baki ɗaya juyowa suka yi suna kallon Abba dake tsaya daga bakin ƙofa. da faffaɗan murmushi kwance saman kyakkyawar fuskarsa da take kaman ceceniya da ta Abban ya ƙaraso cikin ɗakin. Akan stool ya zauna yana fuskantar su duka nan shima ya shiga tashi nasihar cikin tattako da halin girma,sanin ya kamata kafin su fito zuwa cikin parlourn.
Da sauri yaya Nurien ya nufo su yana kamo hannun queen teemah domin yanxu Sammm babu wannan ƴar tsamar tasu, Tun mutuwar Aliyu yaya Nurien ya daina mata duk wata takurawa kamar da, don yanxu Fatima abar a tausaya mata ce. Saida ya zaunar da ita akan ɗaya daga cikin kujerun parlourn, kana ya ɗauƙo ledar magungunan ta yana zama gabanta, ɓata fuska tayi ganin ledar magungunan, kanta ta juyar gefe tana shirin sakar musu kukan taɓara. Da sauri yaya Nurien ya matso gareta yana ɗan ɓata fuskar shima.
Tallafo ƙeyarta yayi yana da ido ya shiga mata alamar roƙon ta daure tasha amma Sammm taƙi fashimtar Yaren. Magiya babu irin wacce baiyi mata ba haka tayi ƙeƙeme abinta.
Ummie da fitowar ta daga kitchen kenan ya sanya ta faɗin, ”ba saika ƙyaleta ba sauƙi taji kuma jikin waye don ubanta!”
Dama haka ummie take akwai ta da saurin hawa haka za kuma bata da wuyar sauƙa, domin ita macece da bata ɗaukar wargi. Shigowar yaya jay kenan yaji suna musu kan shan maganin. Bai ce da kowa komi ya zauna dab da inda take zaune, sakamakon wayar daya shigo yana yi. Maganin kawai ya amsa tare da tsiyanyar ko wanne Saida ya jere wajen kala biyar banta na ƙwaya ma hakan. Taso yin musu amma daya tsareta da kaifafan idonsa haka ta shiga shan maganin tana ta yamusta muska, Saida ta shanye duka tana gama sha ta tashi a guje ta faɗa toilet ɗin cikin parlourn nan ta fara sheƙa amai, duk maganin da tasha Saida ta amayo shi. Murmushi kawai yaya jay yayi Sammm yama manta da wata wayar daya shigo yana yi.
”An daiji kunya ana shirin aurar dake amma kina abu like girl”
”What?”
Aka faɗa da ƙarajin masifar ƙarfin gaske, wanda badon Bluetooth ne a kunnensa ba babu abinda zai hana duka ƴan parlourn jin wannan furucin. Shi kuwa yaya jay da ƙarfin gaske ya cire Bluetooth ɗin yana cilli dashi..........
__________★★★_________
*New York city*
Kamar yadda ya saba yauma yana zaune a cikin hotel ɗin babu inda ya fita hutawa kawai yake sai farin Bluetooth ɗin dake saƙale a kunnensa wanda dukkan alamu suka gama bayyana cewar waya ce yake yi.
Zumbur ya miƙe zuciyarsa na bugun tara-tara bama uku uku ba, sai yanxu yake ganin wannan matakin daya dauƙa shi ne daidai,duk da kuwa ya na cutuwa da sosae da hakan. Amma taurin zuciyar sa ya shanye hakan, tsawon shekaru masu ɗan dama tun yana ƙaryata zuciyarsa ba sonta yake ba yaji yana sonta amma soyayya ba irin ta aure ba. hankalin sa bai sake tashi ba duk kuwa yadda yakai hana zuciyarsa tunani da kuma sukunin matsuguni acikin ta, amma yasan wannan karon tabbas yana neman gazawa, abinda baka taɓa gani a cikin idanunsa a wannan karon kuwa shine abu na farko da zaka fara cin karo dashi. RAUNI tabbas yanxu kai tsaye zaka fashimci rauninsa, Sannu a hankali soyayyarta me shegen ƙarfi taci gaba da faso ƙirjinsa tana ratsa duk wata kafar dake cikin jikinsa da kuma zuciyarsa.
Alcoholic drinks ɗin da suka zama sune abokan rayuwa ya shiga tuttulama cikin sa, jin zuciyarsa na neman yin bindiga ta faso ƙirjinsa ta fito. Shi kansa bai san adadin kwallabar daya shaba, Take a gurbin wurin ya soma fotali da duk abubuwan dake a cikin ɗakin. A matuƙar haukace ya shiga rotsa glasses plasma donation's kai duk komai haka ya shiga rotsa su babu ƙaukkautawa. Baki ɗaya duk ya ji ma jikinsa ciwo hannuwansa sai zubar da jini kawai suke famar yi. Kafin ya zube a cikin a wahalce saman gadon dashi kansa ya fita a hayyacin sa, few minutes saiga manyan ma'aikatun da suka gama ganin komi ta hanyar CCTV footage ɗin dake cikin ɗakin.
Cikin ƙanƙanin loƙaci suka gama gyare ɗakin tare da ɗan sassauta wasu abubuwan da suka tashi a aiki. Shi kuma suka masa treatment na raunikan jikinsa, wayarsa kuwa tayi ratsatsa sanadiyyar uban cillin da tasha a saman tiles na ɗakin. Tamkar wani mutum haka ya ringa buga wayar da da jikin ɗakin, yana bi ta kanta yana ƙara mutsitstsiketa.
Wayar da aƙalla ba kasara ba kuɗinta zai iya kaiwa 1.5million, amma haka ya tarwatse ta ko a jikinsa.
*Few minutes*
A hankali ya shiga saƙƙowa daga downstairs yana tafiya kamar baya son taka ƙasa hannuwansa naɗe da bandejin da akayi treatment nashi.
jikin sa sanye da wando jeans guntu zuwa gwiwar sa, da yar riga mai ƙaramar hannun hakan ya bawa damatsan hannun sa damar bayyana, suna cike tam kamar zasu fashe fuskar nan tasa tayi fayau tamkar wanda yayi jinyar shekara guda,fuskar nan a daure Sammm babu koda ɗigon annuri a samanta. Lallausan gashin kansa kuwa da a ɗaxun ya birkiceta a yanxun kuwa tana tufke a ƙasan ƙeyarsa, sai uban walainiya da ɗaukar Idanu take.
Lumsassun idanunsa da suka ɗan yi zurfi kaɗan yayi tare da ɗan buɗe su, idan har ba gizau idanuwana suka min ba 😮💨 har wata ƴar rama naga yayi. soft skin nasa sai wani irin sheƙi take. All I know is he is fair ALIEY fari ne tass irin caribean white In Nan.
Kalar jikin shi kamar ana goge shi da madara kullum, shi baiyi ɗau har wani irin glowing yake daga nesa.
yana da tsayi da ginannen jikin da duk ɗa namijin da ya mallaka zaiyi tin kaho dashi, yeah shi kansa yasan kyakkyawanr ne saidai shi Sammm ko kaɗan hakan baya taɓa damunsa.
ƙafarsa kuma na sanye cikin wasu haɗaɗɗaun bedroom slippers masu azabar taushi da kuma laushi pitch color.
Cikin tafiyar nan na zaratan mazan da suka amsa sunan su maza yake takun nan nashi, yana bayyana kansa a ƙatuwar harabar hotel ɗin, kuwa tuni escort nashi suka masa caaaaa suna sanya su tsaƙiyarsu kunnensa manye da Bluetooth.
Cikin ƙanƙanin loƙaci motoci wajen biyar suka jere a gabansa, ta tsaƙiyar ya faɗa wacce ta kasance baƙa wuliƙ mai samfurin ƙirar Bugatti Chiron irin narkakkun nan, da iyaka kallonsu ka iya sanyaya zuciyar mai kallon ta. A fisge ya faɗa cikin motorn key sukama mata suna ɗaukar hanyar daya kasance na ƙaton beach ɗin dake cikin hotel ɗin. Tsit kake jin duka motocin, babu abinda ke tashi a cikin ta sai sassanyarn ƙamshim daya bune motar, Idanunsa a Lumshe yayi Relaxing da jikin kujerar motar yana sauraren daddaɗan ƙira'ar almin shawi cikin suratul MARYAM. Cikin ten minutes suka isa katafaren beach ɗin dake da wani irin azababben ƙyau.
Babban Beach ne mai girman gaske daya amsa sunan shi na beach wanda ƴan ƙasar keji Domin kabbb duniyar ne suka bashi World Best Beach.
Gaba ɗaya wurin wani irin blue ɗin haske ne ke ta faman kaida komo a wurin, a parking space suka Parker motocin nasu.
Cike da izzar daya motsa mishi yau ɗin ya fara ziro kyakkyawan ƙafarsa guda, kafin ya ziro ɗayarma. Kowa ka kallah a wurin harkan gabansa yake babu ruwan wani da wani.
Gaban wani haɗaɗɗan Swimming pool yaja ya tsaya da hannu yama escort ɗin alamun zasu iya tafiya, kyawawan sawayensa ya zira cikin pool ɗin da ruwan cikinsa ya kasance blue sosai.tare da fiddo wani irin haɗɗaɗɗen diary yana rungumarsa tsaƙiyar ƙirginsa.
Ga Wata irin sassanyarn sanyin ƙamshim furannin dake kewaye da ruwan qamshine keta faman tashi, irin mai ratsa jikin nan tare da sanya nutsuwa a tattare da ma,abocin wurin.
A duk loqacin da yake cikin ɓacin rai ko kuma bege da kuma kewar abu mafi soyuwa acikin Rayuwarsa, yakan zo wurin ne don yakan ɗebe mashi kaso mafi rinjaye, na daga cikin abinda ke damunsa ya daɗe a wurin sosai. Aƙalla ya ɗauki sama da 40 mints awurin yana jin sassaucin abinda ke son taso mashi, duk da yana qoqarin dannewa tsayin shekaru masu ɗan dama. A hankali ya fara takowa har yafito cikin ruwan lemar ruwan ta kwanta ajikinsa gwanin birgewa.
Jin barci nason fin qarfin sane ya sanya shi tashi yana layi, irin na masu jin barcin nan
hannuwansa riƙe da wannan haɗaɗɗen diary ɗin, cikin sauri bodyguards nashi suka mimmiƙe tsaye, tare da saurin nufar parking space Cikin tafiyar sassarfa ya kutsa kansa cikin lafiyayyar motar. Babu ɓata loqaci suka ja motocin aguje ajere a kuma tsare suke tafiya suuuuuu cikin tsakiyar titin na qasar New York....
*Mu dawo gida 9j*
Mu haɗe a next page.
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
Ya kashe duka wayoyinsa don ma gudun matsala alcoholic drinks kuwa yanxu sune abubuwan da suka fi kusanci a cikin sabuwar rayuwar daya zaɓarma kansa.
★ Gani yake xuwa yanxu tamkar ya gama rasa komai ne, idan yace komai tofa yana nufin komai ɗin ciki kuwa harda Soyayyar yarinyar daya rayu da son ta dade da daƙiƙa ɗaya tunaninta bai taɓa barin brain nashi ba, ko wacce bugun numfashi yana yinsa ne da tsananin ƙaunarta.
Gani yake ko uwar data haifeta ba zata kaishi SO da kuma ƙaunarta ba, duk wasu tarin ƙaddarorin da suka gitta masa SO da kuma ƙaunarta nanan daram acikin Rai da kuma rushinsa.....
_A tunaninku wacce yarinya ce Alie ya ruyu da SOYAYYARTA a cikin rai da kuma rushinsa?_
*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*
~Heart touching love, with love aside 🤍🤍~
Page 29&30
*BY*
*AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️*
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
Sadaukar ga my official Ƴan Amana Naaaaaa mutanen Amana kuyi yadda kuke so da Wannan page, idan kun so ma ku yagalgala abinku nidai na baku kyautar sa🤗🤗🤗
@~♥️ masoyiya
@Amina Muddes
@Aunty bee Naaaaaa
@Free Life With Bbyna❤️🔐💋
@Maman Hanna
@Zainabu Abu
@+Farida yahaya71
Ina ƙaunarku Ma people Naaaaaa 😘😚
_________________________
♥️🤍♥️
*AMMEY POV*
Tun tana ɗaukar lamarin abin wasa har hakan ya fara damunta , ga kuma rigimar Amnah akan lallai ita dole sai ankai ta gun papieyn ta. domin yanxu magana ake ta wajen 3 Months keñan.
Ga kuma wata sabuwar rigimar taga Hajjo, domin yau kwananta uku da xuwa gidan wai a hakan ma don batasan halin da suke ciki da alieyon bane. Shi kuwa Abba zuba musu Ido kawai yayi yaga iyaka gudun ruwansu. Don tunda abin ya faru yana sane amma yaja bakinsa yayi shiru, tunda ya gane jalala kawai alieyn ke nema hakan yasa shima ya share al'amurransu yaci gaba da harkokin sa, tamkar babu abinda ke damunsa.
Tun ummie na ganin hakan me sauƙi ne gashi yanxu hankalin yafi na kowa tashi. $auƙinta ɗaya ma da hajjo bata san asalin abinda yake faruwa ba, tasan da tuni ta tashi hankulan kowa dake cikin gida. Don hajjo irin masifaffun tsoffin nan ce ga kuma alieyn shine ɗan gaban goshinta, ganin tunda tazo babu aliey babu Irfan sosae tasha mitar ta wai suna ƴaƴan musulmai amma su sallamawa masu jajayen kunnuwa ƴaƴansu.
Kasancewar shi Irfan ɗin Immigration ne, shi kuma aliey pilot.
So dama idan yanayin aikin ya sanja musu gashi dai suna gari ɗaya amma sukan sati fiye ma satin basu ganshi ba, saidai suji ta hanyar yin waya, wannan dalili yasa tunda hajjo tazo bata idon kowa daga jikokin nata ba, Wannan keñan.
Wata farar dattijuwa na hango zaune ko ince kishingiɗe saman sofa Idanunta lumshe hannunta riƙe da chasbahanta tana ja, kallo ɗaya zaka mata ka fashimci hutu ratsa ko ina ajikinta ga wani haske da Annauri dake fitowa daga saman kyakkyawanr fuskanta.
Shigowarsa keñan gidan ko bangaren mahaifiyarsa bai nufa ba, ya yi ɗakin daya san na grennyn sune.
Cike da ɗokin son ganin ta ya faɗa ɗakin cikin zumuɗi, Yana faɗin.
"Sweery Where are you?”
Shiru ta masa duk kuwa da cewar tana kallon sa, kafin ta ware large eyes nata wanda da dukkan alamu daga wurin
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 11 Chapter of 23