ranta tsananin tausayin sane a danƙare domin shiɗin abin a tausa ma ne. Saidai idan ya zaman basu nuna mishi kuskure sa, to kuwa zaici gaba da zama babu aure ne yau tsayin shekaru ɗaɗdai har shekaru biyar da wani abu amma yaqi ya sammm ayi masa maganar aure. Gaba ɗaya kodan sabo da maganganun Amnah na jiya sai taji ta son tilas tashi wannan karon kammm Dole ya fidda matar aure. Sosae ta kuma tsuqe fuskar ta.
Shi kuma ganin damuwarta kam shine abu mafi ƙona zuciyarsa, dan shi karan kansa bai san irin tarin ƙaunar da yake ma mahaifiyar tasa ba. Kaɗan ya gyara daidai ta zaman sa da yay har lokacin idanunsa na kanta, ya juya yatsunsa da ke riƙe da spoon ɗin dake hannun sa yana ɗan jujjuya coffeen dake gaban Amnah.
Tsahon mintuna bai mula ba Saida ya yaja wasu ƴan mintuna kafin tsammm ya miqe ya dawo inda take zaune. Kansa ya ɗaura akan cinyarta ya kama hannuwanta yana ɗan mirza mata domin yasan hakan dayai shine kaɗai hope nashi akan ta.
Tsohon mintuna suna a haka har ta fara sauke ajiyar zuciya alamar saukar fushin nata. Ganin ta koma kamar yanda yafi buƙatar ganinta ya ɗan sake mata murmushi.
“Nafi buƙatar ganin murmushi akan ƙyaƙyƙyawar fuskarki Ammiena! Ganin murmushinki kan faranta raina Akasinsa kan ƙona zuciyata fiye da yanda wuta ke narkar dalma.
Wata iriyar ajiyar zuciya mai nauyi ya sauqe a tausashe tace, "Amnah na buqatar Sabuwar momie ALIEYO, ka daure ko dan maraichin...
Saurin dafe bakin ammeyn nashi yayi tare da girgiza kansa, "AMMIEY Amnah ba marainiya bace! Amnah tana dani dake da kuba Abba ga kuma Irfan, iyaka mu kaɗai mun ishe princess rayuwa ammeiyyyyy"
Yayi maganar ne kuma yana duban ko wanne a cikin su, shidai Irfan harga Allah tsananin tausayin yayan nasa yake yi. Bayason yaji ana taku ra masa akan maganar auren Nan.
Shi a ganinsa ai idan har yana buqatar auren ba sai sunce yayi ba, tunda ai ba gani suka yi ya gaza riqe kansa ba.
(Hmmmmmmm Ni kuwa nace abar kaza cikin gashinta kawai, yaro yaro ne lallae kammmm malam Irfan)
★★★
★GYAƊI-GYAƊI★
Sama sama ta shiga ɗan jujjuya kanta cenñnn cikin barcinta taci gaba da faɗin, "NOOOOO ALIYU NO NURUL QALB karka min haka pls ka dawoooooo" shine kaɗai abinda take faɗi kafin Kuma ta saki kuka mai azabar qarfi duk a cikin barcin nata.
Fatimah! Ke fati!!, wai ke wacce iriyar yarinyarce haka, ki tashi maza garin ya daɗe da waye wa"
Jin muryarn ummienta saman kanta ya sanyata saurin buɗe rinannun idanunta, da wani irin sauri ta damƙe hannun ummien tana sakin kuka mai matuqar qona zuciya......
To masu karatu mu dakata daga Nan
Karku manta wannan littafin na kuɗi neeeee akan fara shi mai sauqi da rahusa.
Duk mai son ya mallaki nashi yayi gaggawar biyan kuɗinsa ta wannan account NO in.
3206656358
Maryam Nasiru
First Bank.
Ko kuma
8104493215
Opay bank
Maryam Nasiru
Salon na musamman ne tafiyar da daban ce, haka ma littafin ƘAUNA BIYU na mai rabo ne domin bamu sa hannu Bama yanxune, wasan zai fara yanxu muka ɗan tsoma qafafun mu a cikin littafin ƘAUNA BIYU.
Share and comments fisabilillah🤌🤌
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*
~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~
Page 7&8
*BY*
*AMMEY LAYLERH*
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
______________
*Alhamdulillah forever and always*
________________
♥️🤍♥️
"Ummie kice min ba haka bane!,ummie na kice masa karya tafi ya barni dashi kaɗai ne zan iya rayuwa ummie k.......
Sai kuma wani irin kuka mai masifar ɗaci da ƙona zuciya ya sarƙafe ta ta kasa ci gaba da maganar da take son yi ɗin. Ummie da gaba ɗaya samm ta gaza fashimtar inda maganganun fatiman suka dosa ne ya sanya ta faɗin. "Ke da'alla cen ki tashi haka nan, Banson wannan shirmen naki kinji"
Dole babu yadda na iya haka na tashi jiki a mace domin sosea mafarkin danayi da nurul qalb ya kashe min jiki.
(Ya Ilahi meke shirin faruwa da rayuwana ne har haka?)
Na faɗa a zuciyata a zahiri kam ina mai runtse idanuna dake cike da nauyi har yanzu. Na kai tsahon mintuna goma ina faman tunani kafin na yunƙura na tashi da ƙyar.
Saida na shiga cikin toilet na wanko fuskana da bakina kana na fito kasancewar yau Alhamis bamu da Islamiyya, haka na faɗa kitchen domin taimakawa ummiena da wasu ayyukan. Dama duk rana irin haka tare muke ayki da ita, wani bin ma nakan ce tayi zamanta ta huta nine nake aikin gidan duka,da ƴar sallamata na shiga jiki sanyaye amsawa tayi tana ƙoƙarin kunna gas. Amsa nayi ina jin jikina tamkar ba nawa ba.cikin ƙanƙan loƙaci na gama lafiyayyar sakwara da miyar da miyar da ummie tayi niyar mana. Lokacin kuma aka fara ƙiraye ƙirayen sallar magrib, kasancewar ina fashin sallah yasa ban fita daga kitchen ɗin ba saina wanke kayayyakin dana ɓata, na gyara kitchen ɗin tsabbb kana na jere mana ɗinner bisa dining.
ɗaki na koma xuwa loƙacin na ɗanyi dama dama akan da. Wanka nayo ganin inada loƙaci ɗakina na hau gyara sai bayan sallar isha'i, na fito zuwa loƙacin kowa ga bayyana a main Parlour zama nayi kusa da abbana ina gaida shi cikin ƴar shogoɓa na kasancewar nice auta kuma ƴa mace ɗaya tilo a wurin iyayen mu.
★★★
Mu uku ne a wurin mahaifanmu yaya Jabeer Al-mustapha (jay) shine babban yayanmu, sai yaya Nura wanda muƙe ƙiransa da Nurien, sai kuma Ni autarsu dana kanasance mace ɗaya tilo a gabansu. Kasancewar Ni kaɗai ce mace ya a gabansu ya sanya suke min wata iriyar soyayya ta daban.
Amma banda yaya Nurien wanda nake jin shikam yafi kowa tsana ta domin samm Allah bai haɗa jini na da nashi ba, kodan dama ance tsakanin mibiyi da mibiyi akwai ƴar tsama, toshi nashi tsamar yama fi ƙarfin tsamar mibiyi da mibiyi saidai kai tsaye a ƙira hakan da tsana. Amma idan aka cema yaya Jabeer hammm shine kattt domin ina tunanin soyayyar da yake min harya zarta nasu ummiena, saidai kashh sai Allah ya raba ƙaunar mu ta hanyar aikinsa, yanxun haka Bama ya 9j yana cenñnn qasar India shida matar sa aunty zeey da yaronsu daya julaibeeb kasancewar babban likitan zuciya. Amma yana yawan xuwar mana babu laifi.
Wannan shine takaitaccen tarihin mu🤏
★BACK TO LABARI★
Kaina ya shafa yana amsani da kulawa sosae kasancewar sunan Maman shi gare ni. Plate ɗin da ummie ta zuba masa farar sakwarar da jar miyar da taji kifi manya ya turo min gabana. "Eat it mana Mamana" yace dani ganin tamkar hankali na ba'a jikina yake ba, da sauri naja plate ɗin ina kallon yaya Nurien dake min kallon ƙasa ido yana zabga min harara, baki na nurguɗa masa tare da ɗauke kaina a kansa. Na fara kai abinci na zuwa masauƙinsa.
Kayan na tattara na tashi domin nasan duk inda nurul qalb yake yana hanyar zuwa ne.
Ina shiga ɗakin wayar umma na fara Rington, ɗan murmushi kawai na saki ina ayya na (ya iso keñan) a cikin zuciyana. Ban ɗauki wayar ba dogon jalbab ɗina kawai na zira na fito, babu kowa a palon haka na sanya kaina na fice zuwa rumfar da muke fira da nurul qalb. Yana zaune cikin wasu fararen kaya wanda suka masa azabar ƙyau na tashin hankali, tun daga nesa ya yake sakar min ƙayataccen murmushinsa me tsaɗa.
Da sallama a saman laɓɓana na isa gare shi tare da maida masa martanin nawa murmushin nima. Zama nayi a gefen kujerar robar dake pacing nashi, ko sallamana gaza amsawa yayi banda fararen idanunsa kawai daya zuba min, hannuwana takare da saman fuskana Nima idon kawai na zuba masa domin ba ƙaramin ƙyau yayimin ba yau ɗin, duk da kuwa cewar dama cennn shi ɗin ƙyakkyawane,
“Babyna kin yi kyau sosai” naji fitar sautin daddaɗar muryansa ya ratsa har tsakar kaina. "Uyummmm" kawai nace domin Nima abinda neke shirin faɗar keñan ya rigani, "idan ana maganar ƙyau aka zo wurin ka ai angama kaine kattt nurul qalb" wani irin murmushi ya saki mai ɗan sauti yana zare hannuwa na daga tagumin da nayi. Ɗanfareriyar wayarsa ya zaro daga aljihun gaban rigarsa yana cewa "ban da dai son kaiiiii queen,duk ƙyawawan da suke nan a cikin duniya amma ki dubeni kice nine katttt" ya faɗi maganar tare da ce min "ga sabuwar waƙar dana fitar yau queen yau wanda nayi wakar ne sabo dake sarauniya" amsan wayan nayi da tsananin murna domin duka yawancin waƙoƙin sa akai nane yake yinsu. Play na danna wani irin amintaccen taken waƙar ne ya fara tashi,Kafin wakar ya fara tashi cikin Amon muryansa da kuma daɗi.
"SARAUNIYA KIKE"
Sai kuma aka nuno wata wata haɗaɗɗar beb ta nuna shi tare da cewa.
"MAI MARTABA KAKE"
Rumtse idanunta tayi da ƙarfim masifa tana tsayar wa domin bata buƙatar ci gaba da kalla. A take wani irin azababben kishinsa ya rufe ta, itafa dama sammm bata wani yarda ya fara in joining da mata ba, ƙara yayi abarsa iyaka shi kaɗai ɗin sa. (Yanxu miye haka keñan) ta faɗa hakan wanda take tunanin a zuciyar ta tayi zancen. "Babu komi ƴar amshi cefa kawai queen sarauniya mata tauraruwa a cikin taurari" don yaga ranta ya ɓaci alamar hakan baiyi mata daɗi ba keñan. Domin zuciyarta da nashi guri guda suke a tare suke bugu duk yanayin da ɗaya daga cikin su yake to kuwa shima ɗayan koda baya kusa yakan ci hakan a cikin jinin dake gudana a jikinsa.
Wani irin abu yaji yana taso masa na mai kama da rauni rauni haɗi da ganin tamkar ya gaza ne, wajen kulawa da soyayyar rayuwarsa.
Ita kuwa tunda ta kife wayar ko kanta ta kaza ɗagowa balle yasa ran zata mishi magana ma, zullumi kike queen akan tarin soyayyar da nake miki Fatima!, kinfi kowa sanin waye Ni!, mezan iya da abinda baxan iya ba ina tunanin duk duniya idan aka ɗauke mahaifanmu munfi kowa sanin kanmu da kanmu!, da abinda zamu iya da kuma abinda ba zamu iya!, don haka ki daina zullumi ko ɗar akan soyayyata queen".
Ahankali ta dago kanta wanda zuwa loƙacin har idanunta sun ɗan sanja launi xuwa ja kaɗan da suka sirka.
Zullumi na ke da ɗar-ɗar ba!har abada Zaɓin raina shine zaɓi, bani da haufi akan zaɓarka da nayi a matsayin abokin rayuwa , na san bazan yi nadama ko dana sanin kasancewar ka gwanina ba, A duk loƙacin da nake tsara irin rayuwar zamantakewar auren da za mu yi, sai na ji wani abu ya tsaya min, ban san ko minene ba ban san mi hakan ke nufi ba, abinda na sani Kawai shine bazan iya buɗer idanuna ina kallonka da ko wacce mace ba acikin wannan duniyar. Idan aka ɗauke Mama da kuma bestie ba"
{ bestien Farida take nufi ƙanwarsa ita kuma Maman mahaifiyarsa take nufi, wacce ta kasance ƙanwa ga mahaifinta Allah yasa kun gane🤗}
hannunsa yakai kan nata hannun dake a kife
"Kishi ne" ya faɗi maganar idonsa cikin tsaƙiyar Idanunta da suka kaɗa sosae.
“Ba ni da tabbacin ko minene”
Hannuwanta dake cikin nashi Yaɗan matse da karfi, tare da cewa.
“Ko ma minene ya tafi can ya bar min queen ita kaɗai domin bamu san yadda rayuwar gobenmu zata kasan ce ba!", wala Allah da nine zakiyi rayuwar, wala Allah kuma wanda zaki yi rayuwar dashi yana cennn dakon tsammanin juma yin zuwanki cikin rayuwarsa, ba ni baneeee”
Wani irin dokawa ƙirginta yayi a gigice ta ɗago kanta tana kallon sa, domin exctly irin wannan maganar ya faɗa mata cikin mafarkinta na ɗazu ɗazun nan.
(To wai mene yake shirin faruwa dani neeeee? Ina bazan jureeee ba!, baxan iya ba baxan taɓa ɗaukar hakan baaaaaaa NOOOh)
Tayi Maganar acikin zuciyarta tare da dafe kanta da hannuwanta duka biyun.
Tamkar wanda ya karanci zuciyar nata yace.
"Zaki iya ɗauka mana, dole zaki iya, zaki iya domin ba zaki taɓa sanja ƙaddara ba Fatima!"
A take ɓacin ranta ya gama bayyana kansa ta ɗago idanunta da zuwa yanzun suka fara zubar da ruwan hawaye tace.
“Ko da mafarki hakan ya kasance na tabbata ba zan yi zullumi ko ƙaddarar son wanin kaba!, Plsssss ka daina min ire-iren waɗannan wasar"
murmushin dake nan kwance saman fuskarsa ahar kullum ya saki
Yi hakuri wasa nake miki kawai na yi marmarin wannan fushin na ki ne, da tsoro kin san ni komai na ki burgeni ya ke, fushinki dariyarki duk ƙyau suke min, wani loƙaci idan ina gida ko stadio na kan ɗauki wayata nakan dauki loƙaci wajen kallon hotunanki, ina jin nishaɗin hakan sosae, Allah ya shiryaki min ke drama queen ". Sai a yanxu ya samu ta ɗan sassauta fushin dake saman kyakkyawar fuskarta tare da ƙawata ta da tarin farin ciki mara misalta, Cike da tsantsarn ƙaunarsa ta ce.
“Na san nafi ko wace mace a duniyar nan dacen masoyi, haƙiƙa ban yi kuskuren Zaɓenka a matsayinka na wanda zan rayu dakai ba, wani loƙacin na kan yi yunƙurin auna irin son da nake maka, amman sai na rasa silekin da zai dauki iya ɗaukar nauyin tarin son da nake ma, balle har na iya misalta kwatankwacin girman soyayyarka gare ni, sai dai ni kuma ina jin kamar akwai wata rana da son ka zai min illa, zai rufe idona na kasa gani a loƙacin da ganin yake da muhimmanci, ya maida ni kurma a lokacin da jin ke da matukar muhimmanci”
Wani irin azababben tausayin kansu da kansu ne ya kama shi, amma saiya ƙi barin hakan bayyanu gudun kada yaga gazawarsa da raunin dake kewaye da ilahirin gangar jikinsa.
"Rufe idonki"
Ya faɗa yana son kawar da wancen maganar data ɗakko mishi.
rufe fuskar tayi kuwa da tafin hannayenta, sai ya ɗakko baƙar ledar dake gefensa ya mika mata.
“Bude idon ga zuciyar nawa nazo miki da ita"
Ya faɗa yana danna dariyar dake son kuɓce masa, dan yasan halin Fatima da shegen tsoro.
saurin bude idonta tayi jin tamkar ledar na motsi ne, wani irin razananniyar qara ta saki tare da wurgi da ledar dake hannunta. Atake ledar ta tarwatse saiga manyan kifaye suna ta mutsil-mutsil akan interlock ɗin dake shimfiɗe a tsakar gidan su. da sauri yaya Nurien dake fitowa ya ƙari so wurin da sauri jin uban ihun data saki. Yana zuwa bayyi wata wata ya fidda hannu ya ɗauketa da mari. Yana huce tare da faɗin "ke wacce iriyar mahaukaciyar zararriya yarinya ce ne?"
Wani irin azababben kuka ta saki tare da dafe saman fuskarta da take jin tamkar ba'a jikinta take ba tsabar raɗaɗin azabar marin data sha.
★★★
*ALIEY A*
lumshe luhu-luhun idanunshi yayi yana ƙara buɗe su, jin wayarshi na vibrating
bai buɗe idon ba, ya dauka Sannan ya manna a kunnesa.
"Ubangiji ya shirye ka ALIEYO, tafiya babu sallama babu magana kuma, babu cira hannu" aka faɗa daga cikin wayar.
A hankali ya tashi zaune daga kishin kiɗar da yayi yana kunna wutar ɗakin. yana jin wani yanayi, Tattaro nutsuwarshi Saida ya ɗebi wajen mintuna uku kafin daƙyar saman laɓɓansa ya furta.
"Jay I hope you are fine"
Shine kaɗai abinda ya furta domin sammm magana ba ma'abociyar yinsa bane. Daga cenñnn kuwa wanda aka ƙira da jay ɗin yace.
"Tsabar rashin mutunci ina tambayarka ka, amma kana ce min ina lafiya, a aahh bana lafiya, da bana lafiyar zaka jine ne banza miskilin tsiya"
Ɗan janye wayar yayi domin samm baya ƙaunar surutun da jay ɗin ke famar masa, tamkar zai fasa wayar ya fito.
"Ka gama"
Ya faɗi maganar yana datse ƙiran, yana komawa yadda yake wani irin kewar Sofeey ne ke taso masa, sammm a irin wannan yanayin baya da buqatar hayaniya, shi yasan ya yake keɓe kansa a killatancen wuri na daban. Duk ƙoƙarinsa nason kawar da tunanin dake neman addabarsa abin yaci tura, kansa ya jingina a saman sofar tare da lumshe Idonsa. Numfashi yake fitarwa Ahankali yayinda yake furta kalmar. " Innalillahi wa'inna ilair raji'un,² Ya hayyu ya qayyum" daga cikin bakinsa.
Ahankali nutsuwa ke sauƙar masa acikin zuciyarsa, yayinda yaji tarin damuwarsa na gushewa.sosea yaji sanyi da cikakkiyar nutsuwa da salama acikin zuciyarsa.
Gaban fridge bottle water ya nufa kai tsaye tare da ɗauko bottle water ya ɓalle murfin, ya kafa bakinsa Saida ya tabbatar ya shanye ruwan dake ciki tsabbb kana yayi wurgi da gorar. Wata iriyar ajiyar zuciya yake sauƙewa tare da sanya hannu ya dafe saitin zuciyarsa, duk yanda zuciyarshi taso sanya shi dogon nazari yaƙi aminta da hakan, haka kuma yaƙi bawa brain nashi daman yin tunani kamar yanda ya saba.
Ya jima a tsayen da yake kafin ya nufi bathroom, ya sakarma kansa ruwa. Ya ɗebi mintoci kafin ya fito jikinsa na faman ɗigar da ruwa, mini towel ɗin dake riƙe a dayan hannunsa na aikin tsanewa.
Wani farin trouser ya zira da t-shirt ita ma farar directly ƙasa ya nufa. Yana jin wani wasu irin abubuwa masu wuyar misaltuwa tattare dashi......
Shin mene yake shirin faruwa da rayuwar su Aliyu shureim ne da kuma queen teemahnsa?
Wannan wanne irin al'amari ne haka dake sanya ALIEYO acikin irin wannan tension ɗin?
Shin yaya labarin zai kasance?, wanne irin tunani kuke game da littafin KAUNA BIYU?
Kunsan amsar tana ina?
Duka zaku sami amsoshin tambayoyinku ne a yayinda kuka biya kuɗin littafin ƘAUNA BIYU akan fara shi mai sauqi, ku biya ku mallaki naku domin ci gaba dajin daddaɗan labarin ƘAUNA BIYU.
ONLY 400# ta wannan account NO in.
3206656358
Maryam Nasiru
First Bank
Ko
8104493215
Opay
Maryam Nasiru
evidence via 08104493215 whatsapp only*
A gimtse 🫰
08104493215
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*
~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~
Page 9&10
Last typing sai Allah ya kaimu bayan sallah 🤗
*BY*
*AMMEY LAYLERH*
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
نرجو أن يستمر الله سبحانه وتعالى في المشاركة في جميع شؤوننا
_____________
Assalamu alaikum ƴan uwa ina muku fatan Alkhairi, tare da Adda'ar zaɓin abinda shine mafi Alkhairun mu garemu. Tabbas dukkan ayyuka suna tabbata ne da niyya,kuma Lallai ko wanne mutum yana samun sakamako ne na abinda yayi niyya, Ubangijii Allah yaci gaba da zama gatanmu,rufin asirinmu, yaci gaba da haskaka dukkan al'amurranmu cikin amincinsa.
Ina taya ƴan uwa musulmai murnarn zagayowar Watan RAMADAN,wata mai cike da tarin falala, a sabo da murnarn wannan wata na RAMADAN mai tarin albarka, NI! AMMEY LAYLERH nace na sadaukar da littafin KAUNA BIYU daga paid zuwa free. Allah yaci gaba da zama gatan mara gata, yaci gaba da haskaka goben mara gata, mara galihu acikin al'ummar musulmi. Sannan littafin *ƘAUNA BIYU* na mai dashi Free inshallah duba da yadda al'amurra suka tare suka ma duniya ƙawanya, kowa yana naiman abinda zai rufama kansa asiri ne, dashi da iyalansa bissalam🙏🙏🙏.
Sannan pls waɗanɗa suka riga suka yi payment sumin magana, zan dawo musu da kudaden su pls karku barni da haƙkinku, kana kar kuji kunyan yimin magana. Wllh idan har baka min magana ba to kusani nikam nace ba gata kuka min ba😮💨.
Duk wanda yaji daɗin littafin yama mahaifina adda'a, domin ya kai ladan ƙabarinsa👏😭, Allah ya jiƙanka Abba Naaaaaa mahaifin da bana da kamarka acikin duniya😭🤲🤲
__________________________
♥️🤍♥️
Idanunsa ya lumshe da sake buɗewa su akan Amnah dake jingine da jikin Ammiey,tana mata rigima domin bata jin daɗi asthmar tane ya tashi. Shi yasa yau bata wani tashi da kuzarinta da karsashinta kamar kullum ba. Suna haɗa ido yaji wani irin raunin da ganinta ya sanya mishi, na ƙoƙarin taso mar, Amnah da ganin papieyn ta ya sanya ta a farin ciki ne ta taso ya gudu zuwa wurin sa, hannayen sa kawai ya buɗe mata domin ya san mine take shirin yi, tsamm ya rungume princess ɗin nashi zuciyarsa na masa wani mahaukacin bugu. "Papiey" ta ƙirayi sunan shi cikin maraitacciyar murya.wanda hakan ya sanya alieyo ɗago haɓarta ya zuba idanunsa, cikin muryan shirin yin kuka tace.
"Papiey new Mamie"
Yanda tai maganar a hankali cikin rauni ne, yasa kaɗan ya rage zuciyarsa yin bindiga, amma ya daure cike da son nuna jarumta yana ƙara ƙanƙa meta sosea a cikin jikin sa.
Nannauyar ajiyar zuciya ya sauke, gaba ɗaya ji yake komai ya cinkushe masa. dole ne yana buƙatar ƙara ƙadaice kansa, domin gudun kada iyayen sa su fashimci rauni da kuma halin da yake ciki, zare ta yayi daga jikinsa samm baka isa kai tsaye ka fashimci halin da yake a ciki ba, amma a baɗani da zaka ga irin tarin raunikan dake chunkushe a cikin zuciyarsa, da kuwa tabbas saika tausaya masa. Upstairs nashi ya juya cikin domin zuwa yanzu wani irin azababben zafi da ciwo yaji zuciyarsa na masa.
Da kallo Irfan ya bishi yana ji inama ace ana iya ɗauke damuwar wani, da kuma ciwon wani,da shi kuwa tabbas shine zai ɗauke duk tarin abubuwan yayansa bama tare da shi kansa ya san da hakan ba. Idanunsa ne ya ciko da hawayen tausayin ɗan uwansa, yana duban iyayen nashi. Sosea ya fashimta halin da suke aciki suma kasancewar su masu saurin gano damuwowin kowannensu ta cikin idon kowannensu, haka shine dalilin da yasan shi fasa ƙaraso wa palon yin dinner da fito. Kukan Amnah ne yaja wo hankulansu baki ɗaya "duk loƙacin da zan yima PAPIEY Na maganan sabuwan momie kora ni yake a wurin sa!, ya tafi ya barni. Shi kenan ni bani da mamie kenan irin mamien su afnan!"
Da sauri Irfan ya rufe mata bakinta shima yana danne nashi bakin da ɗaya hannun sa domin kuka yana dab da subce masa ne. da sauri Abba ya miƙe a cin abincin da yake yana fita a gidan baki daya, rungume kanta yayi sosea yana tuna da Safiyya mahaifiyar ta, irin tsananin mutuncin ta, kara, kawaici, yafi kowa sanin irin baƙar wahalar data sha a hannun yayansa, bata taɓa barin laifin mijinta ya fita,taci ɓakar wuya sosea kafin taji daɗin zama dashi, domin aliey dama cennn wani irin murɗaɗɗen hali gare shi.
Cikin Amnah shine sanadiyyar sanja komae na zamantakewar aurensu.
Wani irin mahaukacin so yake mata wanda shi abin wani bin har mamaki abin ke basa, idan ya duba rayuwarsu ta baya da kuma yanzu.
Sau tari yasha raya kamar Allah ne ya jarabci yayan nasa da masifar son ta, sai kuma da yay zurfi ason nata Allah ya dauke rayuwar abar sa.sunyi kuka sunji ciwon mutuwar Safiyya domin macece da sammm bata san tashin hankali ba, sammm bata iya koda kwatankwacin hakan ba, kai duk mahalukin daya haɗa zaman takewa da Safiyya dole ta shiga ransa farat ɗaya. Innalillahi ya shiga nanata acikin zuciyarsa domin mutuwar safiyan ba kaɗan ba ta daki duk ahalin nasu.
Yana son yin magana amma ya gaza, ammiey ce tayi ƙoƙarin zare ta daga jikin Irfan ɗin, tana yin bedroom nata da ita.
★★★
Akan kyakkyawan madaidaicin frame ɗin ta ganin sa ya sauƙa, cikin tariyar sassarfa ya isa wurin photon rinannun idonsa da baki ɗaya suka gama rinewa ya zubawa photon, wani irin zazzafan Numfashi ya fesar tare da kifa kansa jikin ginin ɗakin, cikin azazzaben
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 23