coumpaund ya faka motar ko gama daidaita tsayuwar motar baiyi ba haka ya fice a zuciye, idan yace yana raɗaɗi ko zafi zuciyarsa yake to yayi ƙarya. Wani irin bugu zuciyarsa ke masa bibbiyu ya shiga taka step na benen, da ƙarfi ya mirza handle na qofar yana tura kansa jikin babban parlourn sa, sa'ar sa ɗaya ma babu wanda ya haɗu dashi.
yana shiga falonsa ya maida ƙofar ya rufe, kana ya zame tare da zama aƙasan tiles na parlourn ya jingina bayansa da jikin ƙofan parlourn lokaci ɗaya yashiga kokuwa da numfashinsa dake ƙoƙarin ɗauke wa.
Atake ya shiga faɗin, “Allahumma Ajirni fii musibati wa'ahkifli lu Khairan minha , Innalillahi wa'inna ilahi rajiu'n, innalillahi wa'inna ilair raji'un"
Cikin wani irin tashin hankali ya cigaba da karanta duk wata adda'ar da tazo bakinsa.
wani irin zazzafan zazzaɓi mai zafin gaskene ya lulluɓe sa wanda gaba ɗaya ilahirin jikinsa ke rawa.
Samm Alie bai iya ɗaukar abu da zafi ba tsananta ma kansa da yayi ne ya sanya wannan zazzafan zazzaɓin rufe shi a take. Amma ɗan bala'in mai makon ya saduda saima wani irin turirin da zuciyarsa yaci gaba dayi. A haka wani irin wahalallen barci yazo yayi awon gaba dashi.
(Kada ku manta a baya nace ALIEY mutum ne da baiya kin abu ba, haka kuma bai iya son abu ba, idan ya tashi da dukkanin zuciyarsa,jikinsa dama komai nashi yake so ko ƙi, fatar kun fashimta dai🤗)
★★★
★★★
Haka al'amurra suka ci gaba da wakana tare da shuɗewa tuni suka suka shiga watan azumi, inda suke gudanar da ibadarsu cikin kwanciyar hankali. Tuni an sanya ranar auren Fatima da Aliyu shureim ɗinta inda za'a yi bikin su bayan sallah da sati biyu.
Kullum aliey tare da yaya jay yake shan ruwa ko a gidan ummie ko kuma gidan ammiey inda kullum kuma kunun gyaɗar aliey babu fashi, bayan yasha a gidan haka ummie zata kuma bashi wani ya tafi dashi. Shi yasa aliey yake tsananin ƙaunar ummien fiye da tunanin mai tunani, kuma duk xuwan da yake basa taɓa haɗuwa da Fatima kasancewar yawanci data gama ayyukanta gidansu Aliyunta take tafiyarta, kasancewar baba mariya ƙanwa take ga mahaifinta.
Yauma kamar kullum tun wajajen huɗu da mintoci aliey yake gidan, inda suke tare da yaya jay tare da Nurien a main Parlour na gidan baki ɗaya. Shi Alqur'ani mai girma ne a hannunsa yana raira kyakkyawar ƙira'arsa cikin daddaɗan sautin daya karaɗe parlourn, 6:34pm aka ƙira sallar magrib, rufe Alqur'anin yayi tare da ɗaurayo bakinsa dabinon ajjuwa ya ɗiba kwara uku yana ci, suma duk shima yaya jay dabinon yaci. Shi kuwa yaya Nurien tuba yaci tare da kankana, suna ida ci suka miƙe xuwa masjid, ko ka fin su dawo tuni ummie ta jere musu komai inda lafiyayyan kunun gyaɗar da teemah ta dama kafin ta tafi already ummie dama ta juye masa cikin plask na shayi in banda turiri da ƙamshim daɗi babu abinda yake tashi a cikin parlourn.
A jere suka shigo parlourn dukan su Abba yaya jay yaya Nurien sai kuma aliey dake gefen Abba inda da dukkan alamu wata maganar suke taunawa mai muhimmanci. Ummie da itama idar da sallar kenen ne ta amsa su, zama suka yi baki ɗayansu, a nutse aliey yaɗan ɗukar da kansa tare da cewa.
"Barka da shan ruwa ummiena"
"Barka alieyo ykk fatar kasha ruwa Lafiya kaima" tayi maganar cike da kulawa tana tura masa plask na kunun gyaɗar, kasancewar tasan shine abinda yake fara sha, a nutsen sa yaja plask ɗin gabansa cike da kamun kai tamkar wata mace, a junan su suka shiga gaisawa tare da yima kowansu Barka dashan ruwan.
Kurr idanun yaya Nurien akan aliey, wani irin lumshe ƙyawawan idanunsa yayi loƙacin daya kai cup na kunun gyaɗar nan bakinsa. Murmushine ya subcewa Nurien da sauri ya kawar da kansa, tare da zancen zuci acen cikin zuciyarsa ya shiga faɗin.
(Shi kuma babban yaya da irin abokin da Allah ya haɗa shi kenan, ga tsananin ƙyau tamkar ɗan ƙasar indiyawa ko kuma Balarabe nema oho?)
Kafaɗunsa ya daga irin bai sani ɗin nan ba. Daga kunun bai kuma cin komai ba har sallar isha'i, inda daga nan bai koma gidan ba daga masallacin suka wuce tare da jay, inda shine ya maida shi gidan tare da kunun gyaɗar sa.
Daidai ta parkin na motar yayi a tare suka fice suna ƴar fira sama-sama kuma duka akan kasuwancin da alieyn ke taɓa ne, da sallama suka shiga qayataccen palon ammiey, ammiey dake zaune tare dasu Abba da kuma Irfan ne suka amsa sallamar, Amnah dake jikin Irfan ta sake shi tana yin kan jay aguje, tare da cewa, "oyoyo uncle jay"
"Oyoyo my princess Naaaaaa"
Shima ya gaɗa tare da cirata sama yana juyi da ita. Ido yarinyar ta haɗa da papieyn ta. Da ido ya mata alama data zo, maƙe kafaɗa tayi tare da masa Gwalo Ahankali tace masa. "Bana xuwa wurin ka tunda kaƙi bani New Mamie, zanbi uncle jay gidan sane kawai nifa"
Da sauri shida ammiey suka dubeta domin a tare maganar Amnan ta doke su, murmushin manya kawai Abba yayi yana barin parlourn bayan sun gaisa da jay. Zama yayi gefin ammiey cikin ladabi da kuma nutsuwa jay ya shiga gaida ammien. Amsa shi tayi tana tambayar shi ummiensa da kuma iyalansa. Cike da girmamawa yake bata amsa, sosai suka shiga fira ammien wanda yawanci akan alieyon ne. Irfan kuwa sai aikin kare ɗan uwansa yake. Sai wajajen goma da rabi kana jay ya musu sallama yana komawa gida.
Wata iriyar soyayya mai qarfin gaske ta sake shiga tsakanin Aliyu shureim da queen teemah, sosae yake ririta abarsa yake ji da ita fiye da duk wani tunanin mai tunani.
Haka rayuwar taci gaba tafiya cikin aminci na Ubangijii har ana yau sauran kwanaki uku sallah, daidai sunkai azimi na ashirin da bakwai keñan, wanda wannan rana tazo musu da tsananin farin ciki, na samun aikin da Aliyu shureim yayi a babban birnin tarayyar Abuja. Haka familyn Aliyu dana Fatima suka cika da tsananin murnarn wannan aiki nashi, Fatima kusan zance tafi kowa murnarn samun wannan aikin nashi, domin dama samm taƙi jinin waƙar da yake yi, kasancewar ya fara in joining da mata suna harkar videon tare.
Ana ya gobe sallah again Alie ya kuma jibgewa gidan su jay uban kayayyakin sallah, tare da kuɗaɗe masu yawan gaske in banda albarka da addu'a babu abinda ummie da Abba suke bin alieyn dashi. Masallatan da gidajen marayun daya ɗauki nauyin sa kuwa acikin watan azumin Allah ne kaɗai yasan iyakar su. Banda taimakon mara ƙarfi da yake yi, hutu sosae ya ɗauka wannan karon domin shi kansa harya manta irin loƙacin daya ɗauka hutu kamar haka. Gaba ɗaya kowa ka gani sabgogin sa yake, babu ruwan wani da wani haka kowa ke gabatar da shirye-shiryen sallah, inda wasu ke ɗebo kansu da zafi, wasu kuwa zama kaga samm babu ruwansa da irin wannan ƙaryayyakin irin na masu manyan buruka.
Washe garin ranar aka tashi cikin annushuwa na ƙaramar salla, inda aka hau idi lafiya aka saƙƙo lafiya. A wani ɓangaren kuma zaka sami yara suna ta murnar fita yawon Barka da sallah, Suna zaune tamkar yadda suka saba suna firansu cikin tsantsar farin ciki, kallo ɗaya zaka musu kasan cewa Yes lallei ana zuba wata iriyar tsabtatacciyar soyayya a wurin nan. Wata narkyakkiyar Baƙar motar ce ƙiran Toyota Avalon,bugun 2024 ta sanyo kanta cikin gidan. Ji tayi kawai zuciyarta ya bada wani irin sautin bugu amma ta danne hakan, taƙi bari tsoranta muraran bayyanuwa. ALIEY dake driving na motar ne ya Parker a ɗan madaidaicin parking lot na gidan, Ammiey da Amnah ne suka fito domin dama duk shekara sukan ziyarci juna ne tsakanin ammien da kuma ummien. Shi kuwa cikin motar ya koma ran nan haɗe tare dayin reverse yaja motar yana barin gidan, kai tsaye ya shiga zaga garin Kano haka taka nas baima san abinda ya sanya shi haka ba.
Cikin farin ciki queen ta shiga gaida ammiey, cike da matsanancin ƙaunar teeman ammiey ta shiga amsa ta tare da ƴar tsokanarta ashe sun kusa shan biki,ita dai kunya ta hana ta yin magana sai Aliyu ne ke amsa ammien da ameern ameern.
Da hannu teemah taya fito Amnah a take yarinyar ta saki hannun ammien tana yowa baya, wurin teeman tayo ita kuma cike da tsananin qaunar yarinyar ta ɗauke ta. Tana ɗaura ta saman cinyarta itama cike da farin cikin ganin teeman ta shiga wasa abinta.
Cikin ƴar shogoɓar yarinta da shegen wayo na Amnah tace, "Kece New mamien da papiey naaa yace min kin kusan zuwa ko?"
Da sauri ta shiga girgiza kanta tace "a ahhh new Mamienki nanan tare dake baby" domin ita sammm duk xuwan dasu ammien suke yawanci bata gidan suke xuwa, kuma ita bata ma taɓa ganin Amnan ba sai yau.
Wani irin kallo Aliyu shureim yake bin queen teemah tare da Amnah yana ganinnnn
A gimtse 🫰💪🥰
Nima kaina bansam mine yake gani ba sai mun haɗe a page na gaba.
*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*
~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~
Page 13&14
*BY*
*AMMEY LAYLERH*
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
*Alhamdulillah forever and always 👏*
_________________________
*Alhamdulillah forever and always 👏*
__________________________
♥️🤍♥️
Sosae yake ganin wani irin bala'in dacewa da sukai, lumshe idon yayi tare dajan qatuwar ajiyar zuciya sunan new Mamie dayaji Amnah ta ƙira queen dashi.
Ita kuwa Amnah ta sake abinta sai zuba take, babu daɗewa Aliyu ya mata sallama domin yana tattara abubuwansa masu muhimmanci ne, don Acikin satin ake son ganin sa a ma'aikatar da suka ɗauke shi aikin. Sallama ya mata Saida ta rakashi har bakin get kana ta dawo cikin gidan. Directly main Parlournsu ta nufa tare da yin sallama cikin nutsuwa, Ammiey ce ta amsata tana faɗin "har ɗan nawa ya tafi keñan?" Ita dai haka kurum take jin nauyin ammien,kasa amsata tayi ɗan murmushi irin na manya ammiey tayi tare da cewa. "Ubangijii ya nuna mana loƙacin da Alkhairi" ummie ce ta amsa da ameern, kafin su shiga wata firan daban.
Sai dab sallar la'asr ammien tawa ummie sallama, duk da kuwa cewar ummien taso Ammiey ta tsaya tayi Sallar la'asr ɗin, amma kasancewar aliey ne yazo daukar za don dole haka sukayi sallama da juna.
Har zata tafi ta tuno da Amnah da take tare da queen a ɗakinta, ummie ce tayo mata magana ta fito cikin ƙaton hijab ɗin ta, aikuwa Amnah na jin ammiey tace ta taho zasu tafi ne yarinya tace bata san zance ba, sammm taƙi yarda duk kuwa da cewar irin wayon da ammien ta riga mata amma haka Amnah taƙi ya.
Cikin salon wayon da ammien keson mata tace da ita "laaa princess ga papieyn ki cenñnn ya kawo Miki New Mamienki" noƙe kafaɗa tayi tare da cewa. "Nidai bana sonta ga New Mamien nawa a Nan, kuma ramin wanka ta bani abinci a baki ta goye ni, kuma ma kin gani harda kitson irin ƴan gayu tamin"
Tayi Maganar tare da zame band dake kanta, a take kyakkyawanr kitson da teemah ta mata ya bayyana irin me ɗan gaban nan.
"Kai Masha Allah tabarakallahu ahsanilkhaliqeen 😔 inyeeeeee ƴar gatan mamienta ba, to maza taho muje ki nuna ma papiey kitson da new Mamien ki ta miki" da haka aka mata yawo tana faɗin "mamiena ki tsaya anan anxu dan dawo!" Da murmushi kwance saman fuskarta take ɗaga mata hannu itama, da sauri ummie ta dubi ledar dake ajje irin mai salo-salon nan cikin azama tace "maza ɗauki yi maza kada amm aliey ta tafi ki bata", badan taso ba ta ɗauka domin a duniya bata ƙaunar abinda zai kuma haɗa ta wannan mugun.fuskarta ko kaɗan babu annuri ta nufi inda motarsu ke Parker yana shirin tashi, da ɗan hanzari ta ƙarisa wurin yana ƙoƙarin yin reverse ammie ta dakatar dashi, ganin fatiman tana nufo.
"Gashi inji ummieee, wannan kuma na baby" tana miƙa mata ledoji guda biyu, "to kice mata na gode sosai Allah ya ƙara girma yabar zumunci", "Ameern tace da sauri tana barin wurin, " New Mamie Naaaaaa " Amnah ta ƙwala mata ƙira da masifar ƙarfi. A birkice ta juye tana sauƙe idonta masu kama dana mage akan Amnah, murmushi yarinyar ta saki tana ce mata "ke yausheeeee zaki dawo gidan papieyna da zama ki zam...... Tsittttt tayi shiru sakamakon wata razananniyar uwar tsawar da papieyn nata ya buga mata. Kunnuwanta ta toshe tare da fashewa da kuka tana ƙanƙame Ammiey.
Da wani irin bala'in ƙarfi itama taja baya tana jin tsawar har tsakiyar kanta, "banza mugu azzalumi, wato ƴar tashi ma baya raga mata keñan,da sannu sena yi maganinka ne!"
(Hhhhhhhhhh Ni kuwa nace a ina ɗin zaki yi maganinsan, bayan kina dab da zama mallakin wani🤌🤗 fan's kunji fa queen teemah da naiman magana🤣.)
Sosai ammien ta riƙe Amnah a jikin ta, ganin yadda jikinta ya ɗau mazari. Cikin sheshsheƙar kuka tace, "kuma na fasa nuna maka kitson da mamiena tamin, sannan bazan faɗa maka tayi min harda wanka bama, kuma baxan cema ta bani abinci a bakin ba" yana jinta amma yayi banza da ita domin shi kaɗai yasan irin zafin da yake ji na sanya shi da tayi ya mata tsawa. A haka barci ya dauke ta tana ƴan qananun Maganganun ta mara sa kan gado.
Kwanci tashi hasarar mai rai yau ya rage saura kwanaki biyar cifff auren Aliyu shureim da amaryarsa queen teemahnsa, a kuma yaune zai tafi Abuja sakamakon ƙiran gaggawa daya same shi, domin da a satin daya wuce ne tafiyar nashi, sai kuma suka cira zaman sabbin ma'aikatan da za'a ɗina sakamakon wani uziri daya hana shugaban campanyn xuwa, sai jiya da dare ƙira ya same shi ujila daga campanyn.
Duk wasu shirye shiryen biki sun fara kankama kama daga gidansu amarya teemah da kuma gidan su angonta Aliyu shureim. Dede ta akwatuna harsun kai kayan su akwatu biyar cifff aka mata kaya na alfarma aka zuba mata kasancewar Aliyu shureim shi kaɗai ne Namiji gaba da baya a wurin iyayen sa, sai kuma ƙanwarsa fareedah wancce ta kasance ita ce auta.
Ɓangaren queen teemah kuwa uyummmmmmmm tamkar tajayo nesa kusa haka take ji, tana ganin waɗan kwanaki biyar ɗin tamkar shekaru biyar, gaba ɗaya kafff cikin school Meta nata babu wanda bai san da bikinan ba domin abubuwa take shiryamusu na musamman. Ita dasu fareedah ƙanwar ango kuma babbar ƙawar amarya ake shirya komai. Tunda satin bikin su ya kama itada ƙawayenta suka kasa zaune suka kasa tsaye, gyaran jiki na musamman Fatima ke amsa daga ɓangaren ummiey da kuma mamansu Aliyu shureim ɗin domin tace itama ƴarta ce, tunda itada da mahaifinta uwa ɗaya uba ɗaya ne suka aifesu. Sosae suke ji da wannan bikin domin tsabbb suka shirya zuwansa dama, da fatiman zataci gaba da karatun tane sai kuma daga baya iyayen suka sanja shawari suka ce gwamma kawai ayi auren. Daga baya taci gaba a gidan mijinta idan yana da ra'ayin hakan.
Shi kuwa yace daga nan har birnin sin in ana zuwa ya barta taje tayi karatun ta don zama babbar likita shine burinta, shi kuwa ya riga ya yima kansa alƙawarin duk abinda queen ɗin nasa keso, to shima kuwa yana son koma miye take so ɗin da gasken gaske.
A yau ranar Monday Aliyu shureim ya shirya tsabbbb cikin shirin tafiya Abuja, sosea yayi wani irin ƙyau fatarsa ta ƙara haske fiye da yadda ka sanshi, cikin shadda giztner milk color ya shirya inda shigar ta masifar yi masa ƙyau fiye da ko yaushe,ɗakin mahaifinsa ya nufa kai tsaye domin yi musu sallama, bayan sun gaisa yace.
"To Abba Mama ayafi juna zan tafiiiiiiiiiii" yayi maganar a raunacetare dajan fi ɗin sosea. Ajiyar zuciya mai qarfi Mama da sauƙe tare dacewa, "nifa Aliyu sai naji sammm tafiyar nan naka ya fita a raina, daka haƙura anan ɗin ma ai alhamdulillah babu ba sai kayi nesa damu ba!"
Shima ajiyar zuciyar ya saki yana jin baki ɗaya jikin sa yana neman mutuwa, amma babu yadda ya iya dole zai tafi ɗin ai dama. Cikin son ƙarfafa mata gwiwa yace. Babu komai Mamana Insha Allah!, ki sanya wa zuciyarki nutsuwa
kinsan tafiya da ƙarfen nasara babu tabbas ne acikin ta"
Kurrrrr haka Mama ta ƙure shi da Idanunta tanaji tamkar wannan shine kallon karshe da take masa. Abba ne yayi ƙarfin halin faɗin “Kin tsaresa da ido kuma kinƙi kiyi magana”. Shima cikin ƙarfin hali yayi maganar domin da gaske shima sammm bason tafiyar yake ba. Kodan shi kaɗai ne ɗa namiji garesu kuma bai saba irin wannan tafiye-tafiyenba ne Ohhhh.
Murmushi Aliyu yayi tare da cewa,
“mamana kodai na miki kyau ne?” yayi maganar again da murmushin nan kwance saman fuskarsa.
Jinjina kai Mama tayi still Idanunta na kansa tace.
“Sosai ma mai sunan manya sai naga kamar baka taɓa min ƙyau irin haka ba”. Murmushi yayi tare da Wara ido kana yace.
“Iyyeee yau Mamana ina kunyar da ake min dahar ake yabo na har haka”
Ummi kuwa still Idanunta na kanshi, fareedah data shigo gidan yanxu ne jin kamar maganar mamansu da kuma ƴaƴanta ne ya sanya itama ta shigo ɗakin,Ta kalli mamansu kana ta kalli yaya Aliyu shureim data tsirawa Idanu matsawa kusa da Maman nasu tayi tare da cewa.
“uhummmmm yaya Aliyu ɗan gata duk su Abba sunfi sonka akaina, to danma ai ka kusan tafiya ka barni daga Ni saini kaɗaina, kaga shike Nan sai nayi yadda nake so Nima a gaban su".
Sai'a sannan Ummi ta ɗauke Idanunta daga kan Aliyun tare da mayarwa kan fareedan. Kallon fareedan Aliyu shureim Yayi tare da cewa.
“fareederh”
Cike da ladabi ta ɗago kanta kana tace.
“Na'am Yaya Aliyu Naaaaaa”
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da cewa.
“dole ai dama koba ki ce na tafin ba zan tafi dole fareedatu, zan tafi nabarki dake sai su Abba da Maman.
Cikin yanayin damuwa fareedah tayi ƙasa da kanta lokaci ɗaya Idanunta suka ciko da hawaye yayin da taji zuciyarta yana masifar bugawa da ƙarfi tace.
"Nufa yaya da wasa nake maka, wllh nafi buƙatar kullum kullum nayi ta ganinka, domin kai kaɗai ne gata ne, kaine babban yayan da nake alfahari dakai, nufa ba irin wannan tafiyar nake nufi ba, idan kayi auren nefa nake nufi yaya Aliyu!, inason mu kasance a tare muyi kukanmu tare muyi farin cikin mu tare, kamin aure kamar yadda kasha faɗin cewa kaine zaka aurar dani ɗin, babban yaya."
Aliyu kuwa murmushi yayi tare da kallon fareedan kana ya cije labɓansa na ƙasa, tare da lumshe idanunsa yana sauraron bugun zuciyarsa, ajiyar zuciya ya sauƙe tare da buɗe idanunsa akan fareedan kafin yace.
“To ai ita rayuwar dama ƴar haka ce fareedah koda baki ce na tafi Ni san zan tafin"
Girgiza kai Mama tayi tare da kallon Aliyu cikin yanayin tsinkewar zuciya tace.
”wai duk mine ya kawo hakan ma Aliyu? don Allah duk Abar maganar Meyesa kake karya mana zuciya ne!?”.
Girgiza kai Aliyu Yayi tare da kallonsu wani irin tausayinsu da kuma ƙaunarsu na ratsa dukkan zuciyarsa, Iska mai zafi ya fesar daga bakinsa kana yace.
“Ba karya zuciya bane Mama Naaaaaa" ya kuma jannn n ɗin
A hankali Abba ya ɗaga idanunsa tare da kallon Mama da ta tsirawa Aliyu idanu cikin wani irin yanayi ko ƙyaftawa bata yi ajiyar zuciya ya sauƙe kana yace.
“Allah Ubangijii ya kare ka da kariyarsa, Allah ya bada Sa'a Aliyu shureim Ubangijii ya sauke ka lafiya, ya bada Sa'ar zuwa" yana faɗin hakan ya fice a ɗakin da sauri domin wasu irin al'amurra masu girman gaske daya gano dan gane da yaron nashi, kiris ya rage zuciyarsa ta fallasa asirin dake birnin cikinta. Wannan shine ma dalilin daya sa yabar ɗakin cikin sauri. Yana fita wasu wahaye masu zafi duka zubo masa, da sauri ya sanya hannun da yana sharewa.
Ahankali Aliyu ya maida kansa jikin kujerar da yake kai ɗin ya jingina, kana ya miƙe ware lumsassun idanunsa tare da kama hannun fareedah cikin nasa kana ya cije lips ɗin sa. "Ga Amanar ƴar Amana na Nan na bar miki ki kula min da ita, fiye da yadda zaki kula da taki rayuwar!, ki kula min da ita har zuwa sanda zan dawo, ko sau ɗaya kada ki taɓa barinta ta zubar da ruwan hawaye ata dalilin rashin..... Da sauri Mama ta rufe bakinsa da hannuwanta, wani irin sanyi jikinta da zuciyarta keyi cikin wani irin yanayi ta zubawa Aliyun Idanu. Anutse Aliyu ya buɗe Idanunsa dake lumshe ya sauƙe akan mama. Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da furzar da iska daga bakinsa kana yace.
“mama ya dai kike rufe bakin haka kika sani ma ko maganar ƙar.....
Cikin saurin Mama ta dafe ƙirjinta daya buga da ƙarfin gaske cikin raunin murya irin na wanda ke gab da zub da hawaye ta kallesa cikin tsananin rauni tace.
“Haba haba Aliyu ya kake mana haka karfa ka manta yau saura kwanaki biyar AURENKA kaida queen ɗinka, amma kake mana irin waɗan nan maganganun!, tamkar bai barin wasiyya”.
Wani irin murmushi ya saki me ɗan sauti yana cewa, "Mama to ita rayuwar nawa take ma, hmmmmmmm" kawai yaja ajiyar zuciya domin wani irin bala'in bugu da yaji ƙirjinsa nayi tamkar me.
Mama kuwa lokaci ɗaya wasu hawaye masu masifar zafi suka fara bin kuncinta, domin Sakk irin Maganganun da yake faɗa mata cikin mafarkanta na ƴan kwanakin nan.
Cikin yanayin tashin hankali Aliyu ya sauƙa tare da ƙara sawa gabanta ya durƙusa tare da riƙe hannun ta cikin sanyin murya yace.
“mamah kiya femin kiya femin kada ki zubar da hawayenki akaina, me ne nayi miki! dana chanchanci zubar hawayen ki akaina?”.
Damƙe hannunsa Mama tayi cikin raunin murya da alamun tashin hankali tace.“Meyesa kake karya min zuciya nida mahaifinka da ƙanwarka gata nan".Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da yin murmushi yayin da Idanunsa ke sheƙi kana yace.
“Toh yazanyi mamah inada ikon sanja ƙaddarata ne? dole nasan ƙaddara zatayi aikinta, kuwa ruwa, iska, tsanani babu wanda ya isa sanja ƙaddarar dake manne acikin zuciyarsa, da ina da dama da nine mutum na farko wanda zai fara sanja ƙaddararsa daga mummuna zuwa kyakkyawa.
Girgiza kai Mama tayi still Hawaye nabin fuskarta tace. "Babu babu babu Aliyu!, ina tsoron abinda zai faru dakai ne kawai, gaba ɗaya kwanakin nan in yawan mafarkai akan ka Aliyu Naaaaaa marasa fasali, marasa kan gado"
”cike da matsanancin mamaki ya dago kansa jin ashe Mahaifiyarsa itama na ire-iren mafarkan da yake yi akan kanshi.amma saiya danne hakan gudun kada ya kuma tada wa mahaifiyarsa hankali, cikin sassanyan muryansa da tayi sanyi sosai yace. "Mamah Naaaaaa kimin adda'a da fatan Alkhairi zan tafi loƙaci na ƙara ƙurewa" kafin ya dubi fareedah data kasa koda kyakkyawanr motsi ne murmushin itama ya sakar mata tare da cewa "ki cika min alƙawarin da nabar Miki fa"
Cikin ƙarfin hali tace "I promise you yaya nayi alƙawari" tare da ɗamke Hannuwansa ta daura akan Ƙirjinta, sasea yaji yadda zuciyarta ke bugawa da ƙarfi, sai kawai ya sakar mata kyakkyawarn murmushin nan nasa yana turkusa gaban mahaifiyarsa. "Ki min addu'ar Mama ki yafe min duk wasu abubuwa dana aikata Miki na rashin daidai, danne zuciyarta dake Zillo tayi, nan ta shiga masa adda'oin neman tsari da gamawa da duniya lafiya, da nema masa gafarar Ubangijii.
Murmushi yayi cike da jin daɗin Addu'ar ta ya shafa sajensa, bayan ya amsa mata cikin farin ciki sai yake jin kansa sakayau tamkar ɗan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 23