hakan ba shi zai ba ki dama ki mance da cewar ubangijin daya bamu Aliyu shureim, shi ya karɓi abinsa duk mai rai mamacine kuma mutuwa dolece a wuyan kowanne ɗan Adam Aliyu shureim ya riga mu gidan gaskiya Allah ya gafarta masa!, Ubangijii yasa yayi kyakkyawanr ƙarshe yasa aljannatul Firdausi itace makomarka Aliyu shureim!”
Yaya Nurien yaƙa rasa maganar haɗi da fashewa da kukan tsananin zafi da tausayin kansu da iyayensu, yayinda Fatima ta ƙanƙame yaya Nurien tasaki kuka mai matuƙar taɓa zuciya da ratsawa. Yaya jay ne yayi ƙoƙari yaja ta suka fito daga ɗakin, tana turjewa tana komai haka ya jata kafin ta tafi luuuuuu idonta yana rufe numfashinta na barin gangar jikinta. Rasa taka maiman mene zaiyi mata ya kasa kawai ya shimfiɗe a motar ma ya fice yana komawa cikin asibitin.
Abban aliyu da Abban Fatima suka karɓi gawar Aliyu shureim suna nufar cikin motar yaya jay.
har zuwa loƙacin Fatima bata farfaɗo ba yaya Nurien daya kai zauna ne ya yaƙara rungumota zuwa cikin jikinsa sai a sannan su Abba suka fashimci halin da take a ciki, cikin ƙarfin Abban aliyu yace ” fatimatu suma tayi"? Kansa kawai ya ɗago da rinannun idonsa yana gaɗin, ”nima haka na ganta” gorar ruwan dake gefen motar Abba ya jawo yana yayyafa mata, da wani irin matsanancin kuka Fatima ta farka.
Kukan Fatima keyi kamar ita ma za ta bi Aliyun ne sai faman sanbatu take.
”yaya Vijay” Fatima ta ƙira shi cikin dasashiyar murya, wanda ita a tunaninta yaya jay ɗin ne, a tausashe yaya Nurien ya amsata.
”Na'am queen” shima ya amsa mata cikin murya tausayi.
”Shikenan yaya Aliyu yatafi ya barni!, na tabbata nima nayi ban kwana da farin ciki kenan ko?, wallahi yaya Vijay ba zan iya rayuwa babu nurul qalb ba mutuwa zan yi Nima domin ban ga amfani rayuwata ba in ba ta re da nurul qal......
Da sauri yaya Nurien ya toshe mata baki yahanata ƙarasa abunda ta ke shirin faɗar.
Fatima ta riƙo hannun yaya Nurien ta aza bisa Ƙirjinta tace ka saurara yaya Vijay ka ji yadda zuciyata take bugawa wani duhu nake gani wallahi mutuwa zany....numfashinta ne ya kuma ɗaukewa yaɗauke yarafff ta kuma komawa, da wani irin tashin hankalin ya yaɗago fuskarta ƙara rungume ta yayi domin tashin hankali da yake ciki ya fi ƙarfin tunani sa....
Tuni zancen mutuwar Aliyu shureim ya karaɗe cikin garin na Kano kasancewarsa shahararren mawaƙin Hausa, kafin kace mene har kofar gidan su ya cika Maƙil da mutane kowa ƙyakkyawan yabo ne ke fito wa daga bakin sa game da Aliyu shureim ɗin.
Har suka iso gida kuwa babu wanda ya kuma sanin fatiman a some take, Kasancewa dama Mama da ummie tuni suka dawo gida, kasancewar dole zasu zo su ɗumama ruwan ɗumin da za'a wanki gawar.
Bayan an fito da gawar ne yaya jay ya ɗauƙi queen cilakk Yana nufar gidansu da ita, babu daɗewa da fitar yaya jay Fatima ta kuma farfaɗowa da wasu irin sambatun daya fi na farko. A gigice tayi gidansu Aliyu, loƙacin an gama haɗa shi keñan tsaffff.
Cikin rasa tunaninta ta faɗja kansa tana wasu irin sambatu ta shiga faɗin.
”I hate love na tsani soyayya bazan qara wata aba wai ita soyayya ba!, na gama yin SOYAYYA har abadan gaban abadan abada, baxan taɓa iya auren waninka ba NURUL QALB baxan ƙ...……luuuuuu ta koma baya yarafff alamun ta kara somewa kenan, cikin sauri jay yazo ya ɗauke ta yana mayar da ita cikin ɗakin Mama........
*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*
~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~
Page 17&18
*BY*
*AMMEY LAYLERH*
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
@Alhamdulillah forever and always 👏
عقدة الروح ستؤدي إلى الموت
_____________________________________
♥️🤍♥️
Cikin ƴan mintuna kaɗan ta kuma farkawa, amma wannan karon kammm ko damar sunbatun bata samu ba, Samm bata lura da cewa su ummien ta suna ɗakin ba saida ta ji sautin murya ummienta dake famarn dannar Mama. da ƙyar ta ɗago kanta ta karewa Maman da kuma ummienta kallo sai kuma fareedah, wanda ta zubama guri ɗaya ido babu ko kyaftawa, kallo ɗaya zaka mata kasan cewar Samm bata a hayyacin tane, cigaba tayi da kallonsu ta ga kowane hawaye na zuba daga idanusa, sosae tsoro da zallumi haɗi da tashin hankali wanda tsawon rayuwa Fatima bata taɓa fuskantar irin sa ba ya ziyarce zuciya da gangar jikinta, ji take wani irin mashahuri sanyi yasoma ratsa baki ɗaya ilahirin jikinta . sai kawai jikinta yafara rawa kamar mazari da sauri.
Jin tamkar motsi yasa ummie ɗago kanta tana sauke Idanunta akan fatiman riƙe ta ummien tayi.
Cikin ɓacewar tunani muryarnta na rawa tace ”ummiey meya faru naga kuna kuka"?
Duk cikin su babu wanda maganar fatiman bata girgiza ba, meya faru fa take tambayar su. Mama ce ta janyota jikinta tana ɗora kanta saman ƙirjinta cikin dakewa da shanye ciwon dake sukar ƙirjinta Mama ta dubeta tare da ce mata. ”fatima Aliyu ne ya rasu!, ya tafi ya barni ya barki yabar fareedah yabar kowa da kowa da komai na cikin duniyar na baki ɗaya!, saidai Allah Ubangijii yaji ƙan Aliyu shureim domin ya riga mu gidan gaskiya, gatan da zamu masa shine binsa da tarin adda'oinmu!” wani irin murmushi ta saki irin mai ƙona zuciyar nan tace, ”kin yarda keñan?, dama kema Mama ashe kin yarda da maganganun su na cewar nurul qalb ya mutu, wllh ba mutuwa yayi!, nasan bai mutu ƙarya ce!, ƙarya ne bai mutu ba wllh bai mutu ba!,Nima binsa zanyi idan ya mutu Wllh sai muje cenñnn muyi rayuwar aurenmu a maƙabartar, ai shikenan kooooo Mama?”
Wani irin matsanancin tausayin fatiman ne ya kama baki daya ƴan dakin, cikin son gasgata mata Aliyu shureim kamm saidai wani ba bashi bane Mama tace. ”Aliyu yatafi kamm Fatima wannan abu da kikeyi bashi zai sa yadawo gareki ba, da ana mutuwa adawo Fatima da yanzu mun dawo da Aliyun mu cikin mu muna tare da shi, Amma ina! tsakanin mu dashk sai addu'a kafin mu ma tamu mutuwar ta riske mu, A kullum addu'ar daza mu masa shine Allah yagafartawa Aliyu!, ke kuma ya musanya miki da Wanda yafi shi, Wanda zai ƙauna ceki fiye da yadda Aliyu ya ƙauna ceki!”
A tsorace Fatima ta. ɗago dara-dara idanuta masu kama dana mage ta dube maman, kafin ta shiga girgiza kai hawaye na fita a idonta tace. ”har abada mama ba zan sami Wanda zai maye gurbin yaya Aliyu a zuciyata ba, bazan taɓa haɗa son wani ba bayan yaya Aliyu Naaaaaa, na tsani duk wata kalmar da tayi kama da S/ko/Ƙ na tsani soyayya domin so baiyi min rana ba, tunda mutuwa tazo ta rabani da mafarkina!, burina, muradinah fatana!, taya kuke tunanin zan so ko zan ƙauna ci wata halitta bayan yaya Aliyu?”
Tsammm Mama ta kuma rungume Fatima a jikinta tare da cewa.
”Fatima ɗan Adam baya fidda rai da Rahmar Ubangijii, in ki kayi tawakalli da mika al'amurranki gareshi, sai ki ga yakawo miji wanda zai mantar da ke kafff rayuwar da kike yi da Aliyu yabaki so da kulawa fiye da yadda aliyu ya soki ya ƙauna ceki.”
"Kika ce mene Mama?, don Allah ke yanxu akan kanki idan kika ga naso wani bayan yaya Aliyu baza kiji kishi da kuma haushina ba?, na dai na so!, na dai na so!!, na dai na SOYAYYA!!!”.
Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un kawai suka shiga ambata ganin kamar ma fatiman bata a hayyacin tane.
A cenn ƙofar gida kuma bayan an sallace gawar Aliyu haka aka miƙa shi gidan sa na gaskiya.
(Allahu Akbar rayuwar duniyar kenan haka dai- haka dai loƙacin da kake kan ganiyar jin daɗinta, sai kuma mutuwa tazo ta riske ka, ka shirya ko ba shirya ba taɗauke ka Allah yasa mu yi kyakyawan ƙarshe Ameern ya rabb,Ubangijii yaji ƙan Aliyu shureim)
Bayan su Abba sun dawo daga maƙabarta haka zaratan matasa suka rinƙa shigowa cikin gidan suna gaisuwar Aliyu, kai kawai Mama ke ɗaga musu, ummie cema mai ɗan qarfin amsawa. Ita kuwa Fatima ganin tamkar bata a hayyacin tane ya sanya yaya jay ɗaukarta ya komar da ita gidansa wurin aunty zeey.
Haka akaci gaba da karbar gaisuwar Aliyu shureim bawon Allah, daga ko ina daga ko wacce duniya yabone kawai ke tashi akan Aliyu shureim ɗin, kasancewar mutum na mutane babu ruwansa da girman kan nan irin na mawaƙa, da yanxu mafi aka sarin rayuwarnmu ya sanja, daga inda mutum ya zama wani a fagen yanar gizo Tofa zaka same shi da jin kai da girman kan masifa. Harya manta cewar ɗaukakardai daga Allah take, amma su waɗan nan mutanen sune sanadin daukakar nasa, inda shi Aliyu shureim ba haka yayi tashi rayuwar ba, ya shimfida rayuwarsa ne cikin aminci da kuma ƙaunar masoyansa, baya taɓa wulaƙanta ɗan Adam domin yasan duk wani ɗan adam na cikin duniyar ba wulaƙantacce bane, amma fa baka taɓa gane hakan dole saiya kasance kana tarin ilimin addini, haka dai ya ringa shan yabo daga bakunan mutane maban banta. Rayuwa keñan in nayi dakyau kanka haka za inma akasin hakan ne kanka.
To Saida alhamdulillah Aliyu shureim ya sami tarin shedar mutane sai fatar hamdala kammm.
***********
Tunda ta koma gidan yaya Vijay ta daina gane komai, wata iriyar rayuwa ta koma mai cike da tsananin kunci, da matsananciyar kewa, zuwa wannan loqacin tayi wata iriyar rama ta tashin hankali, ta fita a hayyacin ta, ita kaɗai zaka ga tana zabura, tana wasu irin Maganganun marasa kan gado, Saida su Abba da yayyenta da kuma su Abban aliyu kasancewar babban malamin addini, sune suka ringa taimaka mata da adda'oi shi kuma abban aliyu rubutu ne yake mata, sammmm taƙi komawa gida acewar ta ba zata kuma komawa wannan baƙar anguwar ba. Haka dai al'amurra suka ci gaba da wakana inda anyi sadakar bakwai tare da adda'oi wa mamacin.
Komai na duniyar baya mata daɗi komai ya daina birge Fatima ta zama wata shiru shiru, baza taɓa tunanin fatiman yaya Nurien bace, Wata iriyar miskila ta zama domin takan yina churrrr ba tare da tace koda A bane, Alkur'ani shine ya zama babban abokin ta, sunayen Allah sune mafi yawan kalamanta, zuwa yanxu ta ɗauki haƙurin rashin Aliyu ba kamar baya ba, saidai idan abin ya motsa mata takan firgice.
Tana zaune Yankan farce takeyi abinta da nail cutter,baki ɗaya ta bada hankalinta sosai ga yankan farcen da take . yayin da wani sashe na zuciyarta yayi nisa acikin tunanin nurul qalb nata, ita kanta bata san loƙacin da wasu irin zafafan hawaye suka shiga zubo mata ba, Saida taga sauƙar su akan ƙafafunta da take Yankan farcen. Da sauri aunty zeey ta juwo zuwa cikin tamfatsesen bedroom nata, Idanunta na tara ruwan hawayen tausayin fatiman, babu jimawa sai gata sun fito ita da yaya jay. Tsugunne yakai gabanta tare da ɗago haɓarta, cikin lallami da nutsuwa yace. ”ashe baza ki iya karɓar ƙaddarar data zo miki Fatima!, ashe dama duk tarin ilimin addininki ya tashi a banza?, tunda bai amfaneki ba samm samm baki amfani dashi!, pls TUNENE ki dawo tamkar yadda na sanki a ada ki dawo hasalin fatima abokiyar gwabzawar Nurien, ki kuma dawo min a hasalin TUNENEN YATA VIJAY” wani irin rauni ne ya ziyarce loƙaci guda, tare da wani irin tausayin kanta da kanta, cikin ƙarfin hali taɗan saki murmushin yaƙe wanda akance yafi kuka ciwo tace.
"YATA VIJAY ba” wani irin kukane ya kwace mata tana faɗawa cikin jikin yayan nata, cikin muryan kuka ta shiga faɗin.
”YATA VIJAY sai haƙuri addu'a ya kamata kuci gaba damin, amma samm bana tunanin Fatima zata iya komawa tamkar yadda kakeso, ka tuna Min da loƙacin ƙuruciyana!, a lokacin ina kewaye da tsananin gata da farin cikin da kuke bani, Ka tuna Min da baya ga sosai YATA VIJAY, zanci gaba da ƙiran sunan da nake ƙiranka dashi na ƙuruciya, nasan kana son hakan TUNENEN YATA VIJAY!”
Wata iriyar ajiyar zuciya yaya jay ya saki, domin raɗau tamkar yanxu ne yake kallon komai tarin ƙuruciyarta, samm bata iya ƙiran cikakken sunan shi
JABBER saidai ta ƙira shi da VUJAY kafin ta fara wayo da kuma ƙara girma, ta fara ƙiranshi da YATA VIJAY, idan Nurien ya tambaye ta Fatima ya sunanki!, sai tace TUNENEN YATA VIJAY, shi kuma anan zaita cin zalunta domin bata ƙiran sunan shi Saida tayi wayo take ƙiran yaya Nurien da NURUM.
Numfashi ya fesar mai zafi yana cewa aunty zeey tayo masa gaba da fatiman don zasu je gidane. Kuma a irin yanayin da take ciki samm bazai iya barinta ita ɗaya ba gidan, dole zasu tafe tare ne kammmmm.
Ba tayi mu su ba kuwa ta shiryo kanta cikin farfaɗar duguwar rigar atamfa, zaman kurame na jigum jigum suka yi a haka har suka qarasa gida.
Cikin danne abubuwan dake taso mata ya dake tare da soma ambaton sunayen Allah, loƙacin data ga gidansu ne suka zo, a nutse ta fito cikin ƙaton hijab ɗin ta. Da sauri yaya Nurien dake zaune shi kaɗai ya taso yana kama hannun fatiman domin wani irin bala'in tausayi take bashi. Kai tsaye cikin gidan suka nufa bayan nurien ya gaida yaya jay cikin girmama juna suka gaisa aunty zeey saɓe da julaibeeb a kafadarta. Ummie tana zaune duk abinda duniya yabi ya ishe ta, ga kuma rashin autarta Fatima da tsananin kewar ya dake damunta.
Da sauri har tana neman yin tuntuɓe ta iso ga yaya Nurien tana kama hannun Fatima, ganin yadda fatimanta ta koma ne ya sanya wasu wahayenda bata shirya zubarsu bane suka shiga zubo mata, wai ma hakan acikin hijab ta ganta kenan. Zaunar da ita tayi kusa da ita. Cikin tsananin ƙaunar mahaifiyar nata ta sanya hannu ta goge mata hawayen dake saƙko mata, tare da sakar mata murmushi mai taushi ”ummiena duk hawayen akan kewana da kika yine har haka?” a nutse tayi maganar, ajiyar zuciya ummie ta saki tana cewa ”duk na kewar kine ƴar gatan mamienta”
A girmame aunty zeey ta shiga gaida ummie cikin farin ciki ummie ke amsata tare da amsan julaibeeb tana masa wasa har dare suna nan amma abin mamaki loƙacin da dasu yaya jay zasu tafi ƙin binsu tayi tace ita yau da ummienta zata kwana.
Tafiya suka yi akan gobe Insha Allah ya dawo ha ɗauke ta, da haka suka bar gidan. Bayan anyi sallar isha'i babu jimawa da tafiyar su yaya jay Abba ya shigo, shima sosae yaji daɗin ganin fatiman. Cikin nutsuwar daya zame mata jiki ta gaida Abban nata. Kwanciya tayi akan kujerar parlourn. Ummie ce ya haɗa ma Abba dinner ɗan kallon inda fatiman ke kwance yayi tare da faɗin.
"Ina tausayin yarinyar nan wallahi."
Abba ya faɗa cikin raunin murya
"Adda'a zamuyi mata."
Mama ta faɗa a sanyaye itama tana duban sashen da fatiman ke kwance
”insha Allah zamu ci gaba da mata addu'ar kamar kullum “
Ya faɗa a sanyaye ya shiga cin abincin duk kuwa da ba wani dadin cin yake ba sakamakon karya zuciyarsa da Fatima da ganin fatiman ya haifar masa.
"Allah yayi miki albarka, Allah ya taimake ki, ya kare ki da kariyar sa."
"Amin Abba Naaaaaa."
Ta amsa hawaye na taruwa a idon ta, ”Ina fatan a duk yanayin da kika tsinci kanki ki zama me haƙuri da juriya da amsan ƙaddarar data zo miki a irin ko wanne loƙaci Fatiman Abba kinji,ki amshi ƙaddarar rashin Aliyu domin kada ki butulcewa Ubangijii, shine ya fimu sanin abinda ke ɓoye, Ubangijii ya Miki zaɓin miji na gari!”
Wannan karon ummie ce ta amsa da ameern ɗin. Sun jima a parlourn kafin Abba ya miƙe yana barin parlourn, ummien kuma kai tsaye ta nufi inda Fatima ke kwance inda bacci ya dauke ta akan doguwar kujera, Ahankali ta shiga gashinta tare da adda'oi a bakinta, gudun kada ta farka a firgice, da salati ta farka cikin tsananin jin daɗi ummie ta miƙar da ita tana nufar ɗakinta da ita, sosae ta tofe ta da adda'oin kwanciyar barci kafin ta bar ɗakin bayan ta sakar mata net.
Washe gari alhamdulillah ta tashi da ɗan kuzari, domin itane ma ta shiga kitchen ta haɗa musu kayan karin kumallo. Gefe guda ta ɗebi markaɗaɗɗiyar gyada bayan ta dameta da ruwa ta tace abarta ta ɗora tukunya wuta ya tafasa lafiyayyan kunun gyaɗar ta. Saidai ya ɗan tafasa sosea kafin sauke ƙasa tana kawo hasararta ta ɗaure dashi, tare da matsa lemun tsami guda biyu a ciki. Take kunun ya tubke yayi kauri iyakar yadda take buƙatar shan abunta, sugar ta zuba sama sama domin Samm kunun markaɗaɗɗiyar gyada idan sugar ya masa yawa garɗinsa baya fita yadda ya kamata. Wanke kayan da duk tasan tayi amfani dasu tayi, kafin ta jere musu lafiyayyan yamballs ɗin data musu wanda yaji uban kwai na bala'i. Samm shi yasa ummie bata son Fatima tace zata musu Indai abinda ya danganci suya ne, domin ba ƙaramin ɓarnar ƙwai take mata ba.
( LoL 🤗 wllh ina bayanki ƴar gidana musamman da kike son duk kalan abinci kan dana fi so Nima 😋 ehhhhhhhhh mana My Delicious baaaa ♥️ )
★★★★
***********
*ALIEYO*
Misalin _12:15pm_ flight nashi yay landing na passengers a babban airport na ~Muhammed V International airport Casablanca ƙasar Morocco~
cike da takun nan nasa na izza da ƙasaita tamkar mai tafiya a saman iska tsabar yanda yake wani ɗaga ƙafafun da sauke su a nutse. Fuskar nan samm babu alamar yama san minene yaran murmushi, haka ya shiga saƙƙowa daga upstairs na jirgin a nutse.
Sautin takun sawayensa da ke shelanta ma passengers nashi isowarsa wajen ne yaja hankalun mafi yawan jama'ar dake kewaye da airport ɗin. Ɗan fesar da numfashi yayi loƙacin daya ji rurin woyarsa, hannunsa na dama ya cure guri guda yana harbin iska, kafin cike da ɗan ɓacin rai ya zaro wayar daga cikin aljihun sa yana picking call in.
”You will be booked hotel Sir.” abinda aka faɗa kenen daga cikin wayar, a fusace ya mayar masa da amsa a zafafe yace. ”dake garin na uba nane ba!”
ring na Daimond dake maƙale da yatsarsa ya ɗan shiga murzawa a zafafe, yana jin wani irin ciwo ciwon kai na taso mishi. Directly cikin jirgin ya koma. Abinci bai dameshi ba Sam sam, rabon dayaci abinci tun lunch na safe da yayi sai coffee da yake yawan sha akai akai.Kwantar da kanshi ya yi a jikin ɗaya daga cikin kujerun jirgin yana lumshe rinannun idanuwanshi da suka kaɗa sosae a tashin farko.
*Kewa*
Wata iriyar kewa yake ji lokaci ɗaya yanayin sa ya nemi birkicewa, sabi da wani irin azababben kewar Sofeeynshi daya tuso shi farat ɗaya. Sunayen Allah ya shiga ambata cikin ransa. Ahankali komai ke dayake ji ke raguwa a nutse ya tashi akan kujerar yana nufar VIP na jikin jirgin,zaune yakai kan kujeranshi mai juya wa, yana jan ɗan madaidaicin plask tare da tsiyanyar coffee a mug Ahankali yake yake sipping coffee ɗin dake left hand nashi yana latsa laptop da right hand nashi dake kan ɗan madaidaicin sterm din dake gabanshi.
yanda gaba ɗaya ya tattara hankalinsa ga screen ɗin laptop ɗin zai baka tabbacin abu mai matukar muhimmanci yake yi. Dan sai loƙaci-loƙaci ya kan ɗan ɗauka mug ɗin ya kai bakinsa ya maida ya ajje mug ɗin, hankalinsa kacokam na kan abinda yake yin. Cikin deep saund idanunsa lumshe bayan ya kammala shan coffeen
Ahankali ya shiga motsa lips nashi.cikin daddaɗar muryansa ya fara fitar da wani colorn waƙa irin my sanyin nan a ƙalla ya ɗauki lokuta masu ɗan tsayi daga yadda yake in. Kafin wani irin wahalallen barci ya ɗauke shi anan cikin jirgin. Domin samm yau ɗin kwata² baya da buqatar zuwa hotel don abin ya fara sire mishi. Alerm clock ɗin daya seta wayar da asubahi ne ya farkar dashi. A wahalle ya shiga motsa lips nashi alamun yana addu'ar tashi daga barci ne. Kafin ya fara ƙoƙarin ware lumsassun idanunsa s wahalce.
A gimtse 🫰🫰🫰 🤗 fan's
Nagaji haka nan nima😔
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*
~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~
Page 19&20
*BY*
*AMMEY LAYLERH*
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
@Alhamdulillah forever and always 👏
______________________________
♥️🤍♥️
Ahankali ya shiga buɗe sleeping eyes nashi da sukayi masa nauyi kana kuma suka ƙanƙance, dishi dishin da yake gani acikin su ne ya sashi maida idanun nasa ya rufe, sosai yaji kansa na wani irin bala'in sara masa, dan haka yakejin gaba ɗaya jikinsa yayi weak ga kuma wani irin fitinannen kasala haɗi da ciwon kan da suka sauƙar mishi loƙaci guda.
Hannu yasa yana ɗan dafe kansa dake yi masa ciwo kaman zai rabe biyu,still rinannun idanunsa dake a lumshe ya buɗe tare da sauƙe ganinsa cikin jirgin.
Ahankali ya ɗan motsa jikinsa tare da soma ƙoƙarin ɗaga kansa da yakejin yayi masa nauyi sosai, wanda kuma yasan hakan bai rasa na saba da kewa da kuma tsananin tunanin Sofeeynshi daya kusan kwana yiba.
jingina bayansa da jikin kujerar yayi tare da sakin ajiyar zuciya yana miƙewa da ƙyar tare da nufar bathroom ɗin dake cikin jirgin. Shower ya sakamar kansa tare da tokare hannuwansa da jikin qofar wurin, haka ruwan shower'n ya shiga dukan jiki da kuma kansa.jin numfashinsa na neman ɗaukewa ne ya sanya shi janye jikinsa da ƙyar. idanunsa jajur alamar har yanxu komai nanan daram a yadda yake jin komai ɗin.
bathrube ya saka ma jikinsa ya nufi wurin bag da kayansa ke ciki,sauri sauri ya shiga shirya kansa cikin wasu fararen kaya irin na matuƙan jirgin nan, p.cap ya ɗauka ya saka a saman sumar kansa sosai yayi wani irin azababben ƙyau baka ganin komai sai jajayen laɓɓansa wanda suke fidda wani irin shining na tsantsar ƙyau.
walking slowly yake tafiya fuskar nan babu walwala samm ko kaɗan a saman kyakkyawar fuskarshi, pray made ya shimfiɗa tare da fara nafilfulin daya kanyi wasu luƙatan, bayan ya idar da nafilfulin yayi sallar subhi. 7:15am daidai ya shiga saƙƙowa daga cikin jirgin, wanda zuwa loƙacin tuni passengers da yake da wanda zai ɗauke su daga nan xuwa Dubai har sun fara hallara. Kai tsaye wani haɗaɗɗen eatery ya nufa cikin tafiyar nasa mai kama da ƙasaita. Ko mint 1 baiyi da zama ba wata baturiya tazo dab dashi cikin harshen English take tambayar sa mi yake buƙata, cikin kamewa da kuma basarwa ya amshi ɗan madaidaicin littafin dake hannun ta yam potatoe sai kuma coffee kawai yayi oder domin kafff cikin abinsu iyaka abinda yake iya ci keñan.
Sai kuma pizza dominos in banda su babu abinda yake iya ci daga sauran jagwalgwalonsu. Cikin 3mint wannan baturiyar ta kuma dawowa tana ajje masa abinda ya buƙata ɗin, cikin tsentseni da danne zuciyarsa ya shiga tsaƙurar abincin da spoon. Ko halp baici ba ya ture train tare da ɗaukan coffee ɗin, duk uban turirin da yake haka ya shiga sipping nashi cikin kwanciyar hankali, Atm nashi ya bada suka chaji kuɗinsu kafin su bashi yayi gaba.
10:15am jirgin su yayi landing daga ƙasar Morocco zuwa Dubai.
********
*Queen teemah*
Tunda ta idar da sallar subhi ta gaza koda motsa wa,wasu irin zafafan hawaye ne kawai ke faman zirya saman kyakkyawar fuskarta. Ahankali ummie ta zauna dab da ita cikin tausayawa domin tasan wannan hawayen baya rasa nasaba da Aliyu shureim wanda shidai tashi ta riga tazo ƙarshe, Cikin tausasa harshe ummie tace.
”haba Fatima ashe har yanzu ba zaki ɗauki dangana ba!, ashe zaki zama mai jayayya da mahaliccinmu!?, ya kamata zuwa yanxu ace komai ya wuce
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 7 Chapter of 23