jariri sabuwar haihuwa.
Sosai fareedah ke dariya tana jin ƙaunar Yayan nata, miƙewa yayi tare da yiwa mamah Sallama kana ya fice bayan tayi masa Allah ya tsare.
Kai tsaye gidansu queen teemah ya nufa cikin nutsuwa kai tsaye ya tura ƙofar get ɗin. Shiru babu kowa, harya zaro wayar sa da nufin qiran ta sai kuma kawai ya fasa yana sanya kansa cikin gidan. Saida yayi sallama ummie dake zaune a parlour ce ta amsa sallamar tana faɗin. "Shekarau sai yau akaga damar shigo mana keñan, shigo wa yayi tare da ɗan shafa sajan sa yana cewa, ”Amin afwa ummienmu na daina daga yau insha Allah” ɗan murmushi tayi tare da faɗin. "Allah ya yarda Aliyu" acen qasan zuciyarsa ya amsa da ameern. Tsammm ummie ta miƙe tana faɗin bara na turo maka fatiman, "TO Ummienmu" yace yana jin ƙaunar ummien har cikin ransa, domin shi samm bai ɗauke ta a matsayin surukuwa ba a matsayin mahaufiya yake ɗaukarta.
Babu daɗewa saiga mutuniyar taku cikin zumbulelen hijjab ɗin, zama tayi dab da shi tana tonƙoshe ƙafafunta, idanunsa ya zuba mata waɗan da suka ɗan sanja launi.
”nurul qalb!" Ta ƙirayi sunan shi cikin wani irin sauti mai ɗan amo kaɗan, bai amsata ba kuma baima san ranayi ba. Jin yayi shiru ne ta ta ɗago kanta wani irin karyar da wuyan ta tayi tare da zuba masa nata idanun itama, haka kawai yau ɗin ta tashi da wani irin sanyin jiki.
A raunace ta kuma ƙiran sunan shi”nurul qalb!” aɗan firgice ya ɗago kansa yana sakin ajiyar zuciya mai qarfin gaske, nazo muyi bankwana ne Queen ” da sauri tace "ban kwana kuma qalb?, to ina zaka je da zaka min bankwana?," da sauri ya dawo seti tare da faɗin, "au na manta nazo muyi sallama ne ki yafe ni,na yafe ki Insha Allah yau loƙacina ya cika".
Cikin tsare shi da ido tace "nifa ƴan kwanakin Nan samm bana gane kalamanka yaya Aliyu, wanne loƙacin naka ne kuma yayi?" Tayi Maganar da alamar tambaya.
"Ina nufin loƙacin zuwa wurin aikina ne yayi kinsa da tuni a wancen satin naje, sai aka sami ɗan akasi tafiyar ya fasaya, to shine fa jiya bayan nabar Nan ƙiran gaggawa ya same ni, na lalaaie ana nema na yau!".
Wata iriyar ajiyar zuciya ta sauke tana jin yadda duk wasu nau'o'in jijiyoyin dake jikinta suka mimmiƙe, tsintar kanta tayi dajin wani irin azababben tsoro, tsoro na tashin hankali marar misaltawa, cikin wani irin wahalallen yanayi tace "inajin tamkar kada kayi tafiyar nan, ina jin tamkar kana shirin rabuwa da nine nahar gaban abada, inajin tsoro inajin tsoron wani abu da bansan ko miye shi ba"
”MUTUWA”
Ya bata amsa, a kiɗime ta miƙe tsaye ta soma jijjaga kanta”bana so bana son jin kalmar ka dene min zancen abinda zai nisantaka dani pls, ka dena min batun mutuwa haka nan mana!, ba kaga muna shirin mallakar juna bane!! Ba kaga AUREN mu saura kwanaki biyar suka rage mana ba?" Pls na tsani kalmar ma tsani jin kalmar daga gareka I HATE YOU!” cikin ƙaraji ta ƙarishe maganar tana rushewa da wani irin kukan bala'i irin mai ƙona zuciyar nan. Jikinsa kawai ya janyota yana jin ƙaunar ta tamkar yau ya fara sonta, amma shi ya riga da ya sani ba tun yauba ƙaddara ta riga fata.
Cikin wani irin yanayi yace, ”ya zamu yi da ƙaddarar da ke shirin tunkaro mu!, batun mutuwa kona Miki,ko karna Miki ya zama dolen doliya, tabbas zan tafiiiiiiiiiii saidai yaushe ne?" Yaune?, yanxune?,gobe ne?" Allah ne masani queen, idan yaso kuma sai kiga ya barmu munyi rayuwar aurenmu mai cike da annushuwa da tsantsarn farin ciki, idan ya so kuma ya tanaja miki mijin daya fini nagarta,sanin Chanchanta,wanda zai kula dake fiye da yadda Ni zan kula dake!, wanda zai baki soyayya fiye da soyayyar da xan baki, wanda zai soki fiye da yadda nake SONKI, wanda zai ƙaunaceki fiye da yadda nake ƙaunarki queen!” cikin sheshsheƙar kuka tace,
” babu! Ba 'ayi wanda zai soni ba bayan kai yaya Aliyu, bana son rayuwa da kowa idan harba kai bane, da kuwa daga wannan loƙacin na daina ganin ko wanne Namiji a matsayin miji Saidai na kalleshi a matsayin ƴar uwata mac....
Kukan daya ci ƙarfin ta shi ya hanata ƙarasa magan ganunta, ”kada kiyi butulci ga mahaliccin mu FATEEMERH,Ki sani ruwa Iska tsanani babu abinda ya Isa ya sanja ZANEN ƘADDARAR MU, zaki iya dole zaki amshi baƙuncin wani na bani ba” da wani irin masifar qarfi ta fisge jikinta a nashi tana yin ɗakin ta masifar gudu. Duk yadda yakai ga tsayar da ita amma taƙi tsayawa. Kuka take tamkar wadda aka ce mata ya mutu, bayan kuma gashi a gabanta, gidansu, parlourn ummienta.....
Hawayen da suka cika idon sane suka sami damar zuba masa, cikin raɗaɗin zuciya ya goge yana barin gidan baki ɗaya, a bakin get ya haɗu da yaya jay, bayan sun gaisa yake sanar dashi zai je Abuja ne an ƙira shi akan batun aikinsa, anan yaya jay ya juya kan motarsa tare dacewa suje ya kaishi tasha ya hau mota, har yake sanar dashi badan ƴar fita ce ta kamasu ta gaggawa ba shida aliey daya kaishi, shidai kawai Aliyu shureim murmushi ne nashi, suna ɗan taɓa fira kaɗan kaɗan a haka harya mika shi tasha ya hau mota, kafin ya jiyo gida.
Da addu'ar shiga Mota a bakinsa ya shiga, bayan motar ta gama cika driver yaja motar tare da yin reverse yana ɗaukar hanya. Wani irin murmushi tare da hawaye ne suka saƙka mishi lokaci guda, a daidai sanda suke barin cikin garin na Kano baki ɗayaaaaa.
(Ya Ilahi ya mujibud da'awati) Allah ya saukeƙa lafiya Aliyu shureim, sai mun zo amsar tsara ba🤞🤞👌
A gimtse 🫰💪🥰
*BY AMMEY LAYLERH ✍️*
08104493215
*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*
~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~
Page 15&16
*BY*
*AMMEY LAYLERH*
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
*Alhamdulillah forever and always 👏*
__________________________
♥️🤍♥️
Da sauri Mama ta dafe daidai setin zuciyarta jin wani irin mummunan bugu data mata, zaune takai gefen gadon da take shirin tashi. ”Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” ta furta tana jin yadda gaba ɗaya wata iriyar kasala ta mamaye ta. Acikin jikinta taji tamkar wani sashi na jikinta na dab da rabuwa da ita.
Adda'oi ta shiga gurtawa a ƙasan ranta tana neman tsari da koma meke shirin tunkarota yazo mata da sauƙi. Kasa fita tayi domin bata jin zata iya tashi ma adai yadda take ji ɗin nan.
*Queen*
Zaune takai tana rabka uban tagumi domin wani irin masifaffan da taji zuciyarta na mata. Ummie dake faman zabga mata ƙirane taji shirun yayi yawa ya sanya ta shig ɗakin nata kai tsaye.
”fatimah” ummie ta ƙirata da ɗan ƙarfi ganin tamkar ba'a hayyacin ta take ba, jin ummienta na ƙiran ta ya sanya firgigit tadawo da ita natsuwarta, da sauri tanufi wurinta, jikinta kawai ta faɗa domin wani irin rauni taji mai wuyar misaltuwa tattare da ita, ita kanta bata san mene hasalin abinda ya haifar mata da hakan ba.
”fatimah! Lafiyar ki kuwa? dubi yacce kikai zuru² loƙaci guda, baki da lafiya ne?, kodai period naki ne zai zo?, to kuma ai baki daɗe dayin wanka bama acikin ƴan sati kan nan kikayi al'adarki" haka ummie ta shiga jero mata tambayoyi, domin tasan babbar ciwon dake galabaita Fatima shine ciwon mara yayin period nata.
Bata da takamaiman amsa da zata ba ummienta nata domin ita kanta bata san meke damunta ba, kuka kawai ta fashe dashi tana jin yadda zuciyarta keci gaba da bugun bala'i. Hannun mahaifiyarta ta kamo ta ɗora akan Ƙirjinta tare da faɗin. "Ummie ƙirjina gaba na!, gaba na f...…. Kasa ƙarasawa tayi sakamakon wani irin harbawa da zuciyarta tayi da ƙarfin masifa. Cikin tsananin kiɗima ummie ta rungume yarinyanta tana faɗin, ”innalillahi wa'inna ilair raji'un, meke shirin faruwa damu har haka?"
Cikin fusgar numfashi tace "bah bah ban sani ba Nimaaaaa ummieeeee" a fisge tayi maganar, sunayen Allah ummie ta fara tofe Fatima dashi, tare da duk wasu nau'o'in adda'ar da yazo bakinta.
”Innalillahi wa'inna ilair raji'un” mutane suka shiga faɗa a tare a kuma ɗimauce ganin wani irin mugun accident da akayi tsakani wata babbar mota, irin masu ɗibar fetur ɗin nan wani irin mugun ƙarane ya kuma karaɗe wurin sakamakon sake bi ta kan motar da wannan babbar motar tayi. Wannan Mummunan hatsarin shine ya ja hankulan mutane da yawa harda ma wanda ke nesa da wurin. Tuni bayin Allah jama'ar Annabi suka cika wurin domin ceto rayukan bayin Allahn dake cikin motar, ganin bututun gas ɗin ya ɓalle ya fara fidda wani irin turniƙakken hayaƙi ne ya sa cikin azama da tashin hankali,suka fara kiciniyar fito da mutanen dake cikin motar.
Driver suka fara ciro babu alamun rai tattare da shi, sun ciro na biyun kenan gas na motar ya fashe, ji kake wani irin tushhh rududu, da masifar ƙarfi da kuma son ceto rayukan su mutane kowa ya fara neman hanyar tsira, amma duk da haka waɗan nan mutanen Saida suka sami nasarar guduwa da gawar drivern da kuma wannan mutum ɗayan da suka ciro.
Baki ɗaya gurin ya dauka salatin jama'a da kuma hayaniyarsu. Ganin ɗaya daga cikin mutane biyun da suka ciro ɗaya ƙafarsa na motsa wa ne ya sanya sukayi kansa a guje, tabbas motsini yake kafin jama'ar wurin su cika da al'ajabin gani wasu ƴan raunuka ne kaɗai a jikinsa, daidai Nan kuma ƴan kwana-kwana suka iso wurin. A take suka shiga ƙoƙarin kashe wutar dake ci kamar wacce ake ƙara rurata. Sukuma sauran jama'ar ne suka yi kan wannan bawon Allah da yake motsi sosae zuwa loqacin, Ambulance suka ƙira na kusa da cikin garin dake zaria, cikin abinda bai wuce mintuna goma ba motar ambulance ta iso, kai tsaye suka sanya su duka biyun a motar ambulance ɗin. Bayan sun sami damar cire wayar dake jikin wanda yake motsin nan, acikin aljihun wandon dake jikinsa. Kai tsaye suka shiga cikin contact nashi, *ABBANA* itace numbern da sukayi dialing kai tsaye.
***********
Abba fitowar sa daga masallaci keñan yaji wayarsa na Ring alamar shigowar ƙira, rass yaji gabansa ya buga tare da wani irin tsoro daya ji ya kanainaye shi loƙaci guda. Cikin mazari ya fito da wayar dake gaban rigarsa, *ALIYU* shine sunan daya gani.
Wata irin tsinkewar zuciya ne ya ziyarcesa loƙaci guda cikin jarumtaka yayi picking tare da kara wayar a kunnensa, daga cen bangaren masu ƙiran kuwa bayan sunyi sallama sun gaisa da Abba, a nutse suka ce dashi. "Malam ko kana da alaƙa da wannan me wayar?” cikin mahaukacin bugun da zuciyarsa Abba ke yine ya amsa da.
”Ehhhhhhh! Ehhhhhhhhh!! Nine mahaifin mai wayar. Jin a yadda ya amsa sune a kiɗeme ya san masu ƙiran ƙara nutsuwa da ƙyau kafin cikin son kwantar masa da hankali suka ce dashi, ”wannan me wayar ya sami ɗan ƙaramin accident ne, amma alhamdulillah komai yazo da sauƙi, yanxu haka yana Muslim specialist hospital zaria”
Cike da fawwala Allah al'amurransa ya datse qiran bayan yace musu gasu nan xuwa. Yana ƙoƙarin tafiya domin sanar da iyalinsa halin da ake ciki ne saiga Abban Fatima shima ya fito a masallacin ganin Abban aliyun duk a ruɗe ya sanya shi dakatawa, yana tambayar sa abinda ke faruwa, Cikin tashin hankali yace ”aliyu ne yayi accident a zaria,shine ƙiran da akimin yanxu. "Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un, Aliyu kuma Bashir” kansa kawai ya daga masa yana shirin shiga gidansa, "a ahhh dawo Bashir ba'ayi haka ba, kawai kazo mu wuce zarian! barin ƙira jabiru yazo ya kai mu ” yana shirin ƙiran yaya jay ɗinma saiga shi ya sanyo kansa cikin anguwar. Dawowarsu kenàn da Aliyu daga inda suka je ya biya ya sauke shi a gida, shine shima ya iyo nasu gidan, ganin iyayen nasu a tsaitsane na ya sashi yin parking tare da fitowa da sauri yana tambayar abinda ke faruwa. ”kaga jabiru ba loƙaci muje ka sauke mu a Zaria ƙanin kane Aliyu ya sami accident a yayin tafiyarsa abuja” da sauri yaya jay ya ɗago kansa ba shiri yana duban mahaifinsa da yayi maganar.
”abba Aliyu fa kace naga nine da kaina ɗazu na kaishi tasha ya hau mota!”. kansa kawai Abba ya iya gyaɗa mishi ”jabiru in banda abinka to ya za'a yi da ikon Allah, koda kai ɗin ne kuwa ka kaishi da kanka dole hakan saiya faru!, domin rubutaccen al'amari tun daga rabbis samati wal'arat” Abban aliyun ya bashi cikakkiyar amsa cikin nuna jarumta.
”ba loƙacin ɓatawa loƙaci loƙacinsa bane jabiru muje kawai” Abban Fatima ya faɗi maganar suna shiga cikin motar da sauri shima yaya jay ɗin ya faɗa motar tare dayin reverse yana jan motar da wani irin mugun gudu. Yana ɗaukar hanya ɗoɗar. Ganin shirun yayi yawa ne ya sanya yaya Nurien dake zaune a parlour shida mahaifiyarsa sai Fatima dake zaune dab dashi ya sanyata a tsakanin ƙafafunsa yana bata maganin ciwon kai, domin fatiman taku badai shegen ƙin maganin masifa gareta sai anyi da gaske take sha, kuma dama yaya Nurien shike sanyata sha dole. Kai tsaye dialing Number'n yaya jay yayi daga ce mishi gashi nan yama shigo cikin anguwar amma shine har yanxu shiru shiru bai ƙaraso ba, gashi yana ɗan son fita da motar ne shine ma dalilin zaman jiran nashi da yake. A handsfree ya sanya wayar yana ɗaurata saman cinyarsa shi kuma yaci gaba daba queen magani. Yana tuƙin hankali tashe ƙiran ƙanin nasa ya shigo masa, kai tsaye ya danna picking tare da kara wayar a kunnensa.
Ba tare daya bari nurien ɗin yace komai bayane yace,”hello nurien kana jina yanxu haka muna hanyar zuwa Zaria nida Abba da kuma abban aliyu, Aliyu shureim ne ya sami accident a hanyarsa ta zuwa Abuja!, amma kada ka faɗawa kow....... uban Ihun da fatiman ta ƙwala ne ya sanya shi dakatawa da sauran maganar da yayi niyyar faɗa. Kafin kowa ya ankare tuni Fatima har ta bar parlourn da mugun gudu, don daga ummien har yaya Nurien mutuwar zaune su kayi. (Aliyu!, Aliyun dai da yazo ya mata sallama ɗaxun shine yayi accident) haka ta shiga nanata wa acikin zuciyarta.
Mama da fareedah dake zaune a kan akan darduma mama tasbaha rike a hannun ta ita kuma fareedah Alqur'ani ne a hannunta tana karatu, cikin wani irin sanyi jiki domin daga ita har Maman sun gaza matsawa koda. Nan da cenñnn ne, shigowar Fatima a guje da kuma irin uban kukan da take yine ya sanya Mama miƙewa a firƙice, a ɗimauce cike da tsantsarn tashin hankali ta shiga tambayar ta.
”fati! Fatima!! Ke fati mene ne?, meya faru? Mutuwa akayi!, wani abu y faru da kowa ne” sammm ita kanta Maman ba'a cikin hayyacin take mata duk waɗan nan tambayoyin ba, cikin sarƙewar numfashi tace ”Mah mah Mama Aliyu ne ” a fusge ta ƙwato kalmomin ta haɗe su wuri guda. Take jikin Mama ya shiga wani irin mazari ta ƙara riƙo fatiman tsam a jikin ta tace, ”ya mutu ko, dama naji a jikina wannan tafiyar ba Alkhairi bace innalillahi wa'innah ilair rajiun!, Fatima karki cuceni ki faɗa min mene ya faru da Aliyu na?”.
Cikin galabaituwa tace, ”Mama wai yayi hadari ne shi ne!, shine yaya jay ya ƙira yaya Nurien wai karya faɗawa kowa amma sun tafi daukosa” sakin Fatima maman tayi tare da komawa zaune a sulale. "Shike Nan!, shike Nan, Allahu yaji ƙanka Aliyu shureim, yaron kirki ɗan albarka Ilahi ya karɓi baƙuncinka” sune kawai kalaman da mama ke nanata wa, fareedah kuwa sumewar zaune tayi ba tare da kowa ya san ta sume ɗin ba. ”bafa mutuwa yayi ba A'isha accident ne kawai ya samu, kuma alhamdulillah har ma sunje zarian zasu taho dashi ne gida domin mun fisu kayayyakin aiki masu ƙyau” ummien Fatima ce tayi maganar tana dafa ƙafaɗun Maman. Ita dai ƙala bata kuma cewa ba sai zuru da tayi ta zubawa guri guda ido. Fatima kuwa ajiyar zuciya kawai take sauƙewa a kai akai, da sauri ummie ta shiga girgiza fareedah domin taga tunda ta shigo ko motsi bataga tayi ba. A razane ta ce ”yaya Aliyu Naaaaaa!" Sai kuma a loƙacin ta samu damar fashewa da wani irin kuka mai azabar ƙarfin gaske. Yaya Nurien ne cikin zafin rai ya daka musu tsawa, yana faɗin "ku dallacen ku mama shiru idan bazaku masa addu'a ba ku tashi kuba mutane wuri” tsittt sukayi tamkar anyi ruwan sama an ɗauke.
Anan Mama taci gaba da zama dasu maman Aliyu har zuwa loƙacin da yaya jay ya ƙira nurien yake shaida masa sun ɗau shi, suna asibitin Aminu Kano loƙacin wajajen magriba ne. duba da cewar accident ne a cenñnn ma Saida suka yi ta fafatuka kafin a basu aliyun donma da yaya jay, kasancewarsa sananne kuma ƙwararren likitan dake aiki a waje, badan haka Bama da abin baizo da sauƙi har haka ba. Tuni suka kwaza suka yi asibitin Aminu Kano su dukansu.
Duk idan ka dubi kowannensu zuwa loƙacin yayi wujiga wujiga, sai dab da isha'i aka ba su Mama damar ganinsa.
Wani irin kwantaccen murmushi ne kwance saman fuskarsa loƙacin da hannun na dame ke cikin na Mama na hagu kuma ke cikin na Fatima. Cikin ƙarfin hali da kuma dauriya da nuna jarumtaka ya matse hannun mama dakyau yana dubanta. ”mama kin manta nace banson ganin kukan ki!, kukan ki yana ƙona zuciya ta fiye da tarin raunikan dake cikin jikina a yanxu, Lumshe Idanunsa yayi tare da taune lips ɗin sa da ƙarfi yace.
“Ki daina zubar min da hawayenki Mamana!, ko kinason azabar ƙabari ya tabbata akaina, bayan kuma gashi cennn ina hango irin tarin ni'imomin da aka danatar min?,Mama inaji raɗaɗi da zafin ciwo dako ta ina dake jikina kimin min addu'a, ba kuka ba!” amsa
Cikin sheshsheƙan kuka ta kallesa still hawaye na zuba daga cikin Idanunta cikin wata raunan'niyar murya tace.
”na dai na!, na dai na amma kaima ka daina raunana min zuciya mana da irin kalaman ka wanda suka fi zafi zafi!, wanda suka fi ruwan dalma narka zuciya!, kalaman da nake jinsu tamkar sauƙar mashi acikin ƙahon zuciyata”
inaji raɗaɗi Mama!, Mama ko ina fa ciwo yake min zafi nake ji da zafin ciwo kafin wasu irin zafafan hawaye su zubo mishi, duk kuwa ƙoƙarin sa na son ganin ya hana hawayen nashi sauƙa, amma Saida suka saƙko ɗin.
da sauri fareedan tace, ”Toh Yaya Aliyu me yake saka kuka?, ina da ina ne suka maka zafi da ciwon Idan muna da iko zamu raba ka dashi”
Girgiza kai yayi tare da rintse idanunsa kana yace.
“Ba zai rabu ba fareedah domin Allah ya riga da ya fimu sanin abinda shine mafi Alkhairun mu, kuma bana fatan ɗaya daga cikin ku ya gaza amsan ƙaddarar rashina a cikin ku!, na riga da nasan wa'adin da Ubangijiin sammai da qassae ya ɗibar minne yazo ƙarshe.
Badan faɗa da ƙaddararta ba, a'a saidan dama nasan dole zan mutu!, zan tafiiiiiiiiiii na barku tafiya tahar abada, fatana da burina kowa ya karɓi ƙaddarar rashina data zo muku!,lumshe idonsa yayi yana mai jin wani irin yanayi azuciyar kana ya buɗe su tare da duban Fatima yana damkar hannunta da wani irin mugun karfin gaske, rinannun idonsa ya zuba mata kafin wani irin murmushi ya wanzu saman kyakkyawar fuskarshi yace mata.
”kin gani ko?, dama ai nace miki bai zama lalle Allah ya tsara dani ne kaɗai zakiyi rayuwar aure dani ba, wata ƙila wanda Allah ya tsara Miki zakuyi rayuwar auren dashi nanan na dakon tsimayin zuwansa cikin rayuwarsa” da wani irin bala'in ƙarfi ta fusge hannunta daga cikin nashi. Cikin ƙaraji da masifar ƙarfi ta shiga faɗin.
”No! Ina ba xan iya ba!, ba xan iya, nace Samm bazan iya ba”
Jikinsane ya shiga wani irin girgiza amma dole ya fashimtar da ita cikin fusgar numfashi ya furta mata, ”dole zaki iya!, zaki iya Fatima, kada ki taɓa yarda ki butulcewa Ubangijii, kada ki yarda ki nuna Ubangijiin Rahama bai isa zartar da ikonsa a garemu baki ɗaya ba, kinga Mama ma ta haƙura to kema dol.......
A guje likitoci suka faɗa cikin dakin jin wata iriyar ƙara da na'urorin da aka jona masa a jikinsa suka ɗauka, wannan alamace ta mutum na dab da shirin rasa rayuwarsa. duka suka fitar dasu maman Aliyun suna kuka suna komai, haka suka fitan, suna dab da barin emagencyn ne suka tsinkayo muryarsa cikin ƙaryewar harshe yana faɗin. ” Mama ummie queen fareedah duk ku yafemin ku nai mamin yafiyar kowa da kowa, sannan fareedah kece wacce na barma Amanar Mama Naaaaaa da kuma quee........ Sune kaɗai kalaman da sukaji daga gare shi.
Suka bar tarin likitocin na ƙoƙarin daidaita tsayuwar numfashinsa sa saidai ina tuni rabbi ya amshi abinsa, wanda yafi kowa son abinsa da ƙaunarsa, Baki ɗaya likitocin suka fito daga cikin ɗakin bayan sunja mayafi sun rufe fuskarsa, da sauri Abban Aliyu ya nufi ɗaya daga cikin likitocin yana tambayar yaya jikin nashi kuwa?. Innalillahi wa'inna ilair rajiun ya shiga nanata wa da ɗan loƙacin da likitan ke sanar dashi saidai suyi haƙuri Ubangijii ya amshi abinsa.
Wannan dalili shine jawo hankalin su Mama dake tsaitsaye sun gaza zama. Da sauri cikin tashin hankalin da ba'a saka mishi rana Mama,Fatima, fareedah suka jiyo kalma mafi muni a kaff tsawon rayuwarsu da basu taɓa cin karo da koda de kwatankwacin kalmar ba.
”Innalillahi wa'inna illahi raji'un” kalma da su yaya jay da yaya Nurien ke ta faman mai-maitawa saɓanin Fatima da ke tsaye tamkar an shuka taba,ba ƙaramin jajircewa tayi ba wurin ganin ta dai-daita numfashinta da ke barazana rabuwa da gangar jikinta.
da ƙyar ta iya fusgo kalmar ƙarya ce wallahi!, ƙarya kake yi likita ya za'ayi kace nurul qalb ya mutu!, bayan bikinmu yau saura kwana biyar kacal
Just get back to your composure for now”
Wani irin murmushi Doctor yayi cike da tsananin tausayin ta yace ”I'm sorry to say Aliyu bashir is gone sai Kun yi haƙuri mutuwa rigar kowa ce.ya juya yanufi office nashi,a hanzarce yaya jay ya riƙo fatiman ”ka sakeni yaya” girgiza mata kai yaya jay ɗin yayi cikin hargowa tace ”kasakeni yaya jayyyyy”a tsorace ya yasa keta a hankali tafara ja da baya yanayi ta tamkar mahaukaciya sabon kamu, Kafin ta tajuya da gudu ta afka ɗakin. yayinda Su Mama suka rufa mata baya, cikin tsantsar tashin hankali ta hango tun daga tafin ƙafarsa har izuwa kansa lulluɓe da farin zani da gudu ta ƙarasa daf da gadon hannuta na rawa ta yaye zanin da aka rufa masa, idanun sa na lumshe tamkar mai bacci fuskarsa ɗauke da murmushi kamar ka ƙira shi ya amsa, goshinsa na fitar da wani irin haske Fatima ta riƙo hannusa cikin sarƙewar numfashi da halshe ta fara magana.
”Ba ka mutu ba nurul qalb!, ba ka mutu ba ya ya Aliyunmu!, don Allah ka ta shi karka yi min irin wannan wasa karka tafi ka barni. Please tell them that you are not dead!Get up and deny that nonsense, the doctor is the same one who wants to die ka tashi Plsssss”
Ta ƙarasa Maganar haɗi da rushewa da wani irin kuka mai ƙarfin gaske, yaya Nurien ne ya riƙota ya mannata da ƙirjinsa yace, ”ki daure!, ki nutsu, nutsu fatimaki danni zuciyarki don Allah nasan da matuƙar ciyo hakan dole zakifi mu jin mutuwar Aliyu duba da cewar yau saura kwanaki biyar aurenku dashi,
Amma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 6 Chapter of 23