Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ta aliey ya gada, zuba masa su tayi na ƴan wasu sakanni kafin ta sake wani kayaceccen smile tana ware masa hannuwanta. Jikinta ya faɗa ita kuma ta shiga shafa samar sumar kansa "OYOYO my na robar I miss you so much 😍 my yaron kirki ɗan albarka" "Nima nayi missing ɗinkin hajjo na!, amma nifa gaskiya bana son kirana na robar da kike, nima kice min na ƙarfen kawai wannan shine magana uhummmm”. Ummie ce ta shigo ɗakin hannunta ɗauke da lunch na yamma da takawo hajjo, Sammm bata yi tunanin ganin Irfan ɗin ba tunda bata san da xuwan sa gidan ba. “sannunki Fatsimatu Ubangijii dai ya biyaki wannan ɗawainiya da kike dani a gidan aljannatul Firdausi” ”Ameern” Ammiey ta amsa tana gaida ta cike da girmamawa, da fara'arta take amsata. Leƙen bayan Irfan ta shiga ganin shiru shiru babu aliey babu labarin sa, haƙuri ta gaza tace. ”Na robar wai ina na ƙarfen yake tun ɗazun se famar leƙar bayanka nake!, naga ta idda zai ɓullo” Cike da mamakin jin hajjo na tambayar sa aliey yakai dubansa kan ammiey, kafin ya juwo da kallon sa kan hajjo. A take Brain nashi ta hasko masa wani abu. Duk irin yadda ammiey ta shiga ƙyaftama Irfan ido amma yai tamkar bai fashimta, har Saida ya zayyanema hajjo komai daya faru. Domin shi nan a ganinsa ai hajjo zata iya hana auren kuma idan ta hana ya fasaya keñan har gaban abada, ”Innalillahi wa'inna ilair raji'un, yanxu Ni zaki munafurta fatsima?, duk kallon masoyiyar da nake miki ashe keɗin ba ƙaunata kike ba, tunda har zaku iya ɓoye min Alieyo ya faɗa” Cikin son ammey ta kwantarma da hajjo hankali tace. ”pls don Allah hajjo ki tsaya kiji taya ma za'a ce me sunan manya faɗa yayi, kada fa ki manta shi pilot ne babu ƙasar da baya keta wa har inda bamu tunani shi yana ratsawa” ”yo ba dole nace an sace min mijina ba!, ki naji fa abinda Irfanu ya faɗa yace tun da ya ya tafi kowarsa ba'a samu, to Wllh zai haɗu dani. Kuma aure ne babu fashi saidai ya mutu ƙarewar zuciya, ɗan me ƙaton kai da tsayi yawa daren mutuwa!, sai zuciya yawa ta kafuran farko, kai Irfanu zo nan zoka ƙiramin shi don uwatata” Ɗan ɓata fuska Irfan ɗin yayi kafin yace ”haba Hajjo kina jin fa abinda nace miki sammmm woyarsa baya tafiya bara ma ki gani” Yayi maganar tare da zaro wayar sa daga aljihun gaban rigarsa, tare da dialing na NO ALIEY yana sakata a handsfree. Daga Irfan har Ammiey wani irin zaro Idanu suka yi waje ganin abin al' ajabin daya faru yanxu yanxu, (NO na Aliey kuma ya shiga yau?) Shine kaɗai abinda suke faɗa acikin zuciyarsu. ___________★★★___________ Cenñnn ɓangaren ALIEY kuwa yana kwance tsakiyar lafiyayyan gadonsa yana barcin daya ɗan samu ya ɗauke sa, tamkar a mafarki haka yaji wayarsa na ringing. ”Ohhh my God!” Shine kaɗai abinda ya iya furtaw domin sammm yama manta ashe fa bayan ya gama wayar sa da Jay ya kotsa woyar nashi, kuma da yamman nan ya fita ya sai wata ya zuba sima siman sa, ya kuma manta shafff baiyi switch na wayoyin nashi ba. Wannan shine dalilin da ya sanya su Irfan samun sa. Batare daya buɗe ido ba yasa hannu yana lalubar wayar da ƙyar ya iya ɗakko wayar don har ƙiran ta kusan yan kewa, da ƙyar ya iya ware lumsassun idonsa da barci ya fara cin ƙarfinsu. Ba tare daya duba mai ƙiran ba yayi picking na call ɗin, tare da manna wayar da kunnensa yayi shiru yana jiran yaji wayo. ★★★ Wani irin kallo Hajjo ta shiga bin ammiey da kuma Irfan dashi, duk cikin su babu wanda ya Iya cewa ƙala, har sanda ta fusge wayar daga hannun Irfan. Tana faɗin ”ashe dama ku munafukai ne kuna son ku rabani da jikina don kunga ina son shi!, to Wllh ashir ɗin ku babu me rabani da Aliyu gadangana saidai mutuwa mutum yayi duk abinda zai yi. A fusace kuma ta dawo da hankalinta kan wayar jin anyi pick call ɗin, tamkar a mafarki haka yaji sauƙar Muryar hajjo cikin hargowa. ”To wllh maza maza ka haɗo naka ya naka ka dawo gida, domin duk gudun ka da Wannan auren sai anyi shi babu fashi!, tunda a istiharar da nake maka kullum wannan auren ya gama bayyana min akwai tarin Alkhairuka a cikin sa, don haka babu fashi koda idan anyi zaka mutu!, to kuwa sai bayan an kai ma matar sannan saika mutun” Shima a fusacen yace "bazan dawo ba ɗin idan kuma kin isa sai kizo ki dawo dani naga ƙarfin ikon ki rikitatta kawai, ki fata a harkana fa ina haka ba Wllh zaki haɗu dank” yana kai ƙarshen maganar batare daya jira amsar da hajjon zata bashi ba ya katse ƙiran, yayi wurgi da wayar yana jan tsaki tare da maida kansa yaci gaba da barci abinsa. Wani uban salati hajjo taja tana fashewa da kuka. ”dama haka ɗan Adam yake ai tara yake bai cika goma ba, yanxun nan na gama faɗa da uwarka da ɗan uwanka amma abinda zaka saka min dashi kenan?, to Wllh bara ubanka yazo a yau ɗin nan saina saka shi ya dawo da kai, yo in banda lalacewa ma ace aure sauran shi baifi sati biyu ba, amma babu ango babu alamunsa dani kake zancen dan banza da faka faka kunnuwa irin na ƴaƴan masu jajayen kunnuwan cenñnn” (Shi kuwa Irfan a cikin zuchiyar sa yake faɗin wlh yau Aliey da nine yayan ka da sai nayi maganin ka wallh) Ammiey kuwa baiwar Allah ta mayi Shiru ta rasa abin cewa dan baga san mene zata ce ɗin ba, Saima tsintar kanta da tayi tana kunyar haɗa ido da hajjon. Sosae tayi ƙasa da kanta kafin cikin aro jarumta tare da tattare nutsuwar ta wuri guda ta furta. ”Don Allah Hajjo kiyi haƙuri wllh kusan kullum saimun ƙira me sunan manya amma sammmm woyarsa baya tafiya, ki tambayi abbansu ma kiji harda shima” dafa kafaɗarta Hajjo tayi tana faɗin ”karki damu Fatsimatu nasan halin ki gaba ɗaya don haka kada ki damu da wulaƙancin da gadanga yamin, Ina zaune zai zo ya sameni a mazaunina. Ƙyaleshi ya gama guje gujensa aure dai na faɗa babu fashi, Ina nan kuma Bama zan koma har sai anyi wannan auren Insha Allah” Ajiyar zuciya ammiey ta saki tana cewa ”Na goɗe hajjo Allah ya ƙara girma” ita kuwa hajjo kallonta ta dawo kan Irfan tare da ɗaure fuskarta wai kar shima ya e zai rainata kamar yadda yaji yayansa yayi. Har wani hura hanci sama take kafin cikin izza fuskar nan babu wasa tace. ”Maza Abdul Malik ƙira min Muhammadu yanxu nan ka haɗani dashi” Jiki a sanyaye Irfan ya amsa da ”toh” yana dialing NO na Abbansu.ring ɗaya Abba ya ɗaga wayar, yana faɗin ”A Malik lafiya dai naji ka haka, ko duk damuwar ALIEYN ne ya sanya hakan?” ”A ahhh Abba da dama dama Hajjo ce tace wai na ƙiraka mata kai” ”To! to bata wayar mana” ”toh Abba!” Hajjo ya miƙama wayar tana amsa ko gaisuwar da yake kuma mata bata amsa ba cikin bada umarni tace. ”Muhammadu Nasiru!” Cikin bada attention nashi baki ɗaya ya nutsu jin ta ƙirashi da cikakken sunan shi. ”Na'am Hajiya” Wura hanci tayi sama tare da sake cewa "shin na Isa dakai?, zan kuma baka umarni ka ɗauka?" Daidaita zamansa yayi tare da zare hular kansa yana ajje ta gefe, Saida ya furzar da iska mai ɗan zafi kafin cikin tsantsar biyayya a gare ta ya furta. ”Kin wuce duk waɗannan Abubuwan da kika lissafo a gareni Oummu Naaaaaa,umarni kawai zaki bani kai tsaye ba tare da kinsha wahala wajen tambayarta matsayin ki gareni ba!" Wani ɗan Lumshe idanu tayi kafin cikin kwarin gwiwa kuma ta furta. ”§O nake ka ƙira aliey a cikin daren nan nake son ganinsa a gabana a yau ɗin nan idan har da gaske na Isa dakai ɗin, kamar yadda kake ikirari ” Wata zufa ce ta shiga karya kowa Abban cikin tsananin tashin hankali kuma yace. ”Oummuna duka fa wayoyinsa basa tafiya duk ya tare duk wata hanyar da yasan zamu neme shi Oum ” ”karka damu Muhammadu yanxu nan na gama waya dashi har ya gama zageni tasssss har da cemin munafaka muguwa algunguma , kai zagi dai babu irin wanda wannan tijararren yaron nan bai yimin ba yau” A fusace Abban yace "shi alieyon ne ya zagemin ke haka?" "Tasssss ma kuwa Muhammad" ta faɗa tana ƙara fashe masa da kuka. Jikin Abba har rawa yake wajen rarrashin Hajjo kafin ya katse ƙiran, yana dialing NO na ALIEY. Yana tsaka da barcinsa Ring na woyarsa ya kuma tada shi, a fusace wannan karon ya janyo wayar da shirin ya bugawa wannan masifaffiyar hajjon worning, akan ta fita a rayuwarsa. Cikin rashin sani ba tare daya duba waye mai ƙiran na,domin samm ko a idon zuci bai taɓa zaton ƙira daga abban nashi ba ya manna wayar da kunnensa, cikin wannan dakakkiyar muryansa ya furta. ”Wai bana miki ki ƙyaleni ba, aike ba uwata bace da zakina bani umarnin kai tsaye, idan kuma kin isa saiki zo ki jani, ki dawo dani ki daura min auren!” Ba tare daya bari ko hutawa yayi ba ya kuma faɗin, ”Saura kuma ki haɗani da ammiey ko Abba Wllh saina....... ”Saika kashe ta ko?” Da wani irin bala'in ƙarfi yakai zaune yana gyara zaman wayar a kunnensa, jin Muryar da sammm bai kawo ta ko kicin lissafinsa, cikin Abba har rawa yake wajen furta. ”Ni idan na Isa dakai to ayau ba sai gobe b Ina son ganin ka a cikin ƙasar, tunda ita bata Isa dakai ba!, Ni data Isa dani ta bani umarnin Ni ma kuma ina mai baka umarni, dade da second ɗaya ban yarda ka ƙara ba mara kunyan banza kawai” kittt Abba ya yanke ƙiran Sosai namomin jikinsa suga shiga rawar razani da tashin hankali, gumi kuwa tuni ga wanke shi sharkafff. Tsananin tashin hankali ya gama bayyana a tare dashi. (Kai wannan tsohuwa anyi ƴar haddasa bala'i) Ya faɗa acikin zuciyarsa, Kafin kace A tuni harya shiga tattara tarkacensa dangin su system wayoyinsa sai kuma sauran muhimman abubuwan sa, xuwa loƙacin kuwa 6:15pm. Tuni yayi boking na flight wanda zaije 9j kai tsaye, domin sammm a yadda yake cikin tashin hankalin nan baya jin zai iya tuƙi. Kasancewar sa sannan tuni har an kammala mashi komi cikin abinda bai wuce 15 minute ba Aka gama shirya masa komi. Around 20 minutes Sai gashi ya fito sanye cikin jallabiya gold color mai masifar kyau da tsada, Tsintsiyar hannunsa ɗaure da agogon Rolex, Jikin sa sai fidda ƙamshi tularensa yake mai masifar ƙamshi da daɗin shaƙa, fararen sawayensa sanye cikin Black cover shues masu masifar ƙyau da tsaɗa, fuskarnan babu ko ɗigon annuri a samanta, tafiya yake cikin hanzari abinda ba ɗabi'arsa ba kenan tafiya da sauri yana tafe yana duba watch ɗin dake ɗaure saman hannunsa ganin zaiyi lett flight nashi. Tun da ya fito harabar hotel ɗin escort ɗin dake tsaron hotel ɗin suka zagaye shi suna daidaita rantsatstsun motocin da zasu masa rakiya zuwa airport. A jere a kuma nutse lafiyayyun motocin ke tafiya suuuuuu suuuuuu suuuuuu akan shimfiɗeɗen titin dake luwai luwai. Cikin abinda bai wuce 10 mint ba sai gasu a cikin airport na Hamad International airport. 7:12pm jirgin sa ya lula daga New York zuwa ƙasar NIGERIA. ★★★ Duk inda ka gilma acikin harabar airport ɗin na malam Aminu Kano sojoji ne kawai ke kai da komo, Tamkar rana haka wurin ya kasance an zuwa wasu uban jami'amai tamkar wanda shugaban ƙasa ne zai sauƙa. A cenñnn gida kuwa babu wanda yasan da batun zuwan na ALIEY kuma dama hakan ɗabi'ar sane, saidai kowa ya buɗe ido ya ganshi a washegarin ranar. Wasu shimfiɗaɗdun motoci ne guda uku suka ɗauke shi zuwa gida, Abba da har zuwa wannan loƙacin ya gaza runtsawa ne ya ɗage labulayen window na ɗakinsa dake upstairs, jin motsin taɓa get ɗin da get man yayi. Wata iriyar ajiyar zuciya ya sauƙe yana sakin labulayen tare da komawa yana kwanciya. Wata nannauyar ajiyar zuciya mai ɗan qarfi shima alieyn ya saki, drictly part nashi ya nufa bathroom ya shige yana watso ruwa few minutes sai gashi ya fito ƙugunsa ɗaure da towel, sai kuma mini dake hannunsa yana tsane tattausan gashin kansa. Daidai saitin bangaren gefensa na hagu na gano wani irin azababben zanen tatto machine. Wanda aka yi sa cikin style Wanda da dukkan alamu zanen na haruffan suna ne, saidai sammmm na gaza gane ko minene ainihin sunan, domin da yaren Italiyanci ne akayi kun ga kuwa babu damar fahimta. Washegari bayan duka sun gama hallaruwa a cikin dining area suna yin dinner na safe. Wani irin daddaɗan ƙamshim da suka san mutum ɗaya ne mamallakin sa ne ya bune baki ɗaya parlourn. Kafin Ahankali takun tafiyarsa ya fara ratsa kunnuwansu, tamkar wanɗanda aka ba umarni haka baki ɗaya suka juyo zuwa bangaren saman upstairs. Da wani irin gudu Amnah ta miƙe tana nufar papieyn ta sama ya cirata duk da baya cikin mood mai daɗi. Cikin tafiyar nan nashi yaci gaba da tunkaro parlourn, zuciyarsa naci gaba da bugu, Amma ya danne hakan yaci gaba ta tafiyarsa xuwa garesu, wani irin wagaje baki Hajjo tayi tana miƙewa tsaye tare da faɗin. ”oyoyo na ɗan albarka, yaron kirki" ta faɗa tana sakin murmushi. Kallon ikon Allah Abba ya tsaya yi wato idan kace zaka shiga faɗan Hajjo da alieyo sai kaji kunya a take a gurbin guri, Shi kuwa nan gashi an barshi a sama jira yake Alieyn yazo yaci mutuncinsa. Shi kuwa Boss In ma wani irin ɗauke kai yayi ba tare da ko ya kalli inda take ba ya kauce mata, zama yayi tare da Amnah a jikin sa ya shiga gaida iyayen nashi, kadaran kada han haka suka amsa shi sosae ya damu ya kuma ji babu daɗi. Bayan sun kammala breakfast in tsabbbb yana shirin tashi yaji maganar Abba kamar daga sama. ” daga nan inason ka zarce gidansu Jabeer ka gana da matar da muka ma” Dammmmm haka gabansa ya bada sautin bugu, ji yayi zuciyarsa ta dunƙule waje guda ba tare daya ko ya iya cewa komi ya daga kansa yana ficewa a parlourn bayan ya ajje Amnah. Cikin ɗaya daga cikin rantsatstsun motocin sa ya ɗauka har maƙalallun nashi zasu take masa baya ya dakatar dasu ta hanyar ɗaga musu hannu, cikin soft voice nashi ya furta musu. ”Hi guys wait for me at home, I'll be back” Aikuwa Cikin bin umarnin uban gidan nasu suka juya zuwa cikin ƙaton harabar gidan, buɗe mai door ɗaya daga cikin securityn wurin yayi shi kuma ya sanya kansa cikin moton yana janta da wani irin mugun gudu. _______*Ina zaune bayan mun kammala breakfast Alqur'ani ne a hannuna ina karantawa. Yaya Nurien ya shigo yace inada baƙo a sitting room, da sauri na ɗago ina binsa da idanuna da suka ciko da ruwan hawaye tare da faɗin. ”Ni! Kuma yaya?” Kansa ya gyada min yana yin gaba sama da ten minutes na gaza koda motsa wa ne ganin bana da alamun tashi ne ya sanya ummie yimin magana, don dole na miƙe ina rufe Kur'anin, ba tare dako gyara fuskana ba na nufi sitting room namu jiki a sanyaye. Da wani mayataccen ƙamshi na fara cin karo, ƙamshin dana rasa ina ne na taɓa jinsa, gabanane ya ɗan faɗi amma haka nayi ƴan mazanci na kutsa kaina cikin qaton ɗakin saukar baƙin mu. Kyakkyawar sumar dake kwance saman ƙeyarsa ne ya fara min welcome, yana kishin kiɗe ya bada baya. Sallama na kuma yi a karo na biyu nan ma shiru, na buɗe baki zan kuma yin wata sallamar ya juyo baki ɗayansa. Wata iriyar zabura nayi ganin mutumin da nake fatan ko a hanya kada ƙaddara ta kuma haɗamu, ina shirin barin ɗakin naji yasha gama na saurin rumtse idanuna nayi domin ban manta marukan da nasha daga gare shiba. Ranƙofowa yayi kaina tare da dago fuskana cikin wani irin sautin daya nemi hautsinani yayi amfani wajen furta. ”Shawarar da zan baki itane kawai kice ke baki sona, domin kinsa ke bakiyi color da matan aure ba kibi komai a hankali, ki kuma saka a ranki wani ramin rijiyar yafi gaban tsallakawar yaro bane saboda faɗin bakin gareshi, kuskure kaɗan zaka iya afkawa ciki ka halaka” A fusace Nimaaaaa......... Hhhhhhhh tofa Chakwakiya nidai kawai nace mu haɗe a page na gaba *BY AMMEY LAYLERH ✍️* *💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘* ~Heart touching love, with love aside 🤍🤍~ Page 31&32 *BY* *AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️* ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* __________________________ ___ Afusace nima na juyo tare da buɗe masa girman idanuna duka wai ko zai ɗanji tsorona LoL 🤩. "uhummmm to da kyau amma kai mine zai hana kaje kace ka fasa a farke wannan ƙaddararren auren naka, ko anfaɗa ma niɗin ina sone uymmmm dubi ka gani a sanadiyar auren ka dubi yacce na koma!” Tayi maganar tana ɗaga hijab nata. A take tsayayyun breast nata suka ɗan bayyana ta samar rigar ta, wanda ita harga Allah tayi hakan ne domin ta nuna masa yadda ta rame over. Saurin kawar da kansa gefe yayi yana wani irin taune ƙasar lips nashi da ɗan ƙarfi. Tamkar wanda aka fusga ko irin ya kwato maganar nan yace. ”Da dukkan alamu harkin tsorata kenan? Tun ba'a je ko ina ba, ina mai ƙara baki shawarin ki sanja ra'ayin ki a kaina, domin Ni ba tsaren aurenki bane kana ina da wacce nake SO ki fashimta” Ya ƙare maganar wasu irin ruwa ruwa na tarun masa cikin idanunsa, hasalin blue ɗin cikin su na ɓoye wa. "Bani da loƙacin ɓata ma laƙaci loƙacinsa zanyi biyayya wa wa iyayena ne kawai wajen AURENKA, Kana bana jayayya da mahaliccina akan abinda ya tsarama rayuwana, Amma ka sani tunda na rashin Aliyu shureim na zare duk wata alaƙa da ya shafi komi ma na wannan duniyar bawai iyaka auren ka ba!” sharrrrr ruwan hawaye tuni ya wanke mata saman kyakkyawar fuskarta, da Allah bai amshi rayuwar nurul qalb ba da tuni nasan, ina ɗauke da cikin sa koma na kusa haihuwa, duk wanda ya zaɓi rayuwar aure dani to ya sani zai rayu ne kawai da iyaka gangar jikina!, amma zuciya da ruhina suna tare da nurul q......... Wata iriyar razananniyar tsawa ya buga mata cikin ainihin zafin zuciyarsa ya kaima wuyanta uban shaqa da dukkan alamu ya fice a hayyacin sa, cike da tsananin ɓacin rai cikin hosky voice nashi yace. ”Ance miki Ni! ɗin sonki nake?, uhm-uhmm to ma za ki farka daga nannauyar barcin daya dauke ki, Bana jin akwai wata halitta acikin duniyar da zanso zata kuma birgine bayan Matana *SOFEEYERH* ,therefore, if you hope to find a husband, you should remove it, because I am stronger than you, I passed the class of a girl like you” Ɗago kanta ta yi ta zuba masa narkakkun idanunta, sai kuma ta ɗauke kai ba tare data furta komai ba, saima ƙoƙarin janye jikinta da take daga yadda ya haɗeta da jikin ɗakin. Da wani irin azababben kallon ƙasarn ido ya shiga bin ta dashi, idanunsa har wani sheƙi suke na ruwan da suka tara a cikin sa, jin yadda sautin fitar numfashinsa ke sauƙa gefen wuyanta shi yafi komai ɗaga mata hankali, jinta take a mugun takure ga wasu abubuwa da taji suna neman tafiya da numfashinsa. ganin yadda take ta ƙoƙarin janye jikinta a nashi ne ya sanya shi ƙarasa haɗe gab ɗin dake tsakanin su ta haɗe jikinsa da nata, haɓarta ya ciro tare da zuba mata sexy eyes nashi, yana binta da wani kallo masu tarin ma'anoni. Idanunta ta shiga kif kiftawa, tana kare matse jikinta dake manne da nashi jikin. Wani irin kafirin murmushi ya sakar mata loƙacin da yake raba tazarar dake tsakanin su, yana mata wata alamar da bansan mene yake nufi ba da yatsun hannunsa. Har ya fice a sittin room ɗin, durƙushe wa tayi a wurin tare da sakin kuka me azabar ƙarfin gaske, ”na shiga uku na lalace Ni Fatima, me wannan azzalumin yake nufi dani ne?, Ni kuma haka salon tawa ƙaddarar take daga wannan sai wancen Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un” Fareedah ce ta faɗo sittin room ɗin jin kukan queen, ilai kuwa ita ɗin ce ta gani durƙushe tana rera kuka, cikin tashin hankali fareedan ta nufe ta tare da faɗin. ”sweetyn meya same ki, meya hfaru dake? Mene aka miki?” cikin sheshsheƙar kuka tace. ”lovie mine ma bai same ni!, tabbas nasan Nima na kusa mutuwa, tamkar yadda yaya Aliyu ya tafi ya barni ina gab da bin bayansa” a ɗan ruɗe fareedan ta shiga faɗin, ” sabo dame zaki ce hakan?, bayan muna ta murna kin sami lafiya kana zamu sha bikin ki kuma, ke nifa yanxu ma xuwa nayi mu shiga koda kasuwa ne. Kinsan loƙacin bikinku da yaya Aliyu ma tun iyazu muka fara shiga kasuwa” Kanta ta shiga girgiza mata kafin cikin kukan taya kuma kufce mata ta shiga faɗin. ”Da ban banci tsakanin wannan auren da kuma wance fareedah, ke a tunaninki har akwai wani abu daya saura a cikin rayuna da kike tunanin zan yi shi don nishaɗin kaina, bayan mai bani farin cikin baya raye!” loƙaci ɗaya ta kuma fashewa da wani irin raunataccen kuka, tsayawa fareedah tayi tana kallonta girgiza kanta tayi jin yardar queen ke kuka tamkar ranta zai fita, tabbas tana matuƙar tausayin ƙawar nata kuma ƴar uwarta domin kuwa abar a tausaya ma ɗin ce, tabbas ƙaddara ce mai ƙarfi tazo ta gitta rayuwarta. Loƙacin da take tsaka da nishaɗantuwarta. jiki asanyaye fareedah ta ƙaraso gareta tana zama kusanta, murya a raunace a kuma tausashe tace. "Kiyi haƙuri sweery ki ɗauki wannan ƙaddarar kamar yanda kikayi abaya don Allah don Annabi karki saka abin nan aranki ki jawoma kan ki wani sabon ciwon, bayan wanda kike a ciki ki taimaka kiyi haƙuri pls sweetheart, Insha Allah ba zaki mutu ba domin kuwa akwai dubinki wanda tarin ƙaddarorin su suka zarce naki, kuma suke rayuwa, ke fa iyaka saurayi kika rasa, wasu faiɗe ake musu da ƙarfin masifa daga ƙarshe ciki ya bayyana amma kuma hakan bai hana su rayu da abinda suka haifa ɗin ba har suyi rayuwarsu cikin farin

Chapter 12 of 23