idonsa yayi tare da buɗewa yana tuna famarkin sa na daren jiya, "Queen gaba ɗaya zuciyar Aliyu shureim ta daɗe da zama mallakin ki ke kaɗai, saidai ina ji!, ina tsoron na mutu na barki da tarin zallar soyayyata a cikin zuciyar......
"Kada ka sake yi min maganar mutuwa nace ma bana so!, bana so!! Bana so ka daina, kuma mutuwar ta rasa wa zata ɗauka sai kai? Wlh duk sanda aka wayi gari babu kai Tabbas a ranar nima zan rasa tawa rayuwar"
”Mutuwa kike tsoro queen?" Yayi maganar yana sakin ɗan wani murmushi mai ciwo a cenñnn qasar ranshi.
katse wayar kawai Fatima tayi ba tare da tace komai ba.
"I LOVE YOU DRAMA QUEEN" ya faɗa yana manna wayar a kan qirjinsa, bayan ya duba wayar yaga katse qiran tayi.
★★★
★ƘASAR🌆MOSCOW★
*Cosmos hotel's lobby*
P U B ɗaki mai no:1200
*~Singer🎙️🎧~*
Wani bazaraten matashin saurayi ne ke tsaye gaban Singing speed kunnuwansa manne da headphones idanunsa a lumshe, iyaka kwantaccen gashin dake nan kwance saman qeyarsa kawai nake iya hange daga ɗan nesa, in banda walwali da ɗaukar idanu babu abinda sumar take aikin yi, ga wani irin qamshin haɗa haɗen mayuka masu azabar ƙamshi da tsada keta faman tashi.
Yana sanye cikin wasu haɗaɗɗaun buttoned shoulder strip wool sweater na Paco Rabanne, Coffee and white color sai sweater daya ɗaura saman kayan da ya mai wani irin kyau banawasaba, yana sanye dawani Black Merni trouser qafafunshi sanye da wani black boot na Lanvin, wani irin azababben ƙamshi yakeyi tamkar Companyn tularen duka ne a jikinsa.
Tsaiwarsa ya ɗan gyara hannuwansa zube cikin aljihun wandon sa idonsa lumshe, Cikin wani irin Sound wizard dake tashi a cikin iyaka ɗakin ya fara fitar da sautin waqarsa mai wani irin sanyi da sanya nutsuwa a wurin ma'abocin jin waqoqinsa. duk da kuwa cewar shi ɗin *PILOT NE* (matuƙin jirgin sama). Amma yana tsananin ƙaunar yin waqoqi ko yaya iɗan ya sami free ya kanyi waqoqi bawai don ya tara kuɗi ba a ahhh saidan kawai tsananin qaunar son yin waqoqin da yake. Kai tsaye idan yayi baya taɓa fitar dasu saidai yakan yi ɗan short video haka a TikTok INSTAGRAM harma da sauran yanar gizo, da ire-iren waqoqin sa masu azabar daɗin saurara. Kaf tarin mabiyansa babu wanda yau zai iyacewa ya taɓa ganin ainihin fuskar ALIEY A wanda da iyaka ALIEY A ɗin kaɗai yake amfani.
Saidai duk da haka yana da tarin mahaukatan fan's kwarai sosea da gaske, wanda daga sunji ya hau kan ire-iren waqoqin sa sukan rikice su haukace da roqon don Allah ya taimaka ya sakar musu a comment sections, saidai baya taɓa sakar musu ɗin sammmm tunda dama yayi ne kawai don nishaɗin ƙansa, da ɗebe masa kewa da hakan yakan yi a loquta da dama.
★★
★★
_Tu hiye mujhko bata de_
_chaahun_ main _ya- na...._
_Apne ta dil ka pata de_
_chaahun _main_ ya -na..._
_Itna bata dun tajhko_
_chahat pe apni mujhko_
_yun toh nahi ikhtiyaar_
_Pair bhi yeh Socha dil ne_
_Ab Jo laga hun milne_
_Poochun tujhe ek baar_
_Tu hiye mujhko bata de_
_chaahun_ main_ ya- na...._
_Apne ta dil ka pata de_
_chaahun _main _ya -na..._
_Aisi kabhi pehle hui na thi khwahishien ... Oh...._
_Kisi se bhi milne kina kithi koshishien
Uljhan Meri suljha de_
_Chaahun_ main_ ya- na..._
_Ankhon aakhon main jata de_
_Chaahun_ main_ ya -na_
★★
★★
Har wani irin luuuuuu idonsa keyi alamar waqar na hawan kansa sosea kuma duk wannan abin da yake, karkuce da pepar yake roying na waqar a ahhh dama haka cenñnn yake waqarsa cenñnn. Vibrating da wayar shi ya ɗauka ne yasan qirane ya shigo masa cikin wayar. Picking call ɗin yayi tare da manna wayar da kunnensa cikin dakewa da nuna tsantsar izza, daga cenñnn ɓangaren mai qiran kuwa jin anyi picking na call nashi ne ya sanya cikin sauri don ɗaya daga cikin aikin aliey ne ya datse qiran nashi baki ɗaya, cikin hamzari ya daidaita nutsuwar shi tare da faɗin.
"Sir.Our flight will depart from Moscow to Nigeria at around 12:30 tonight"
yatsine kyakkyawanr fuskarsa yayi as usual yana daidai tsaiwarsa "ohk" kawai ya iya faɗi tare da zare wayar a kunnensa yana datse qiran baki ɗaya.
Ajiyar zuciya Obi ya saki yana jaddada tsantsar jin kai da tsananin izza irin ta aliey.
*Nigeria*
KANO
SHARAƊA PHASE 01
★ALIEY MAI MATA ESTATE★
Wani irin qerarre kuma haɗaɗɗen shimfiɗeɗen estate na hanga mai kama da SOLDIER'S HOUSE wanda gaba ɗaya anguwar wasu jibga-jibgan soldier's ne kewaye da ita tako ta ina. Tamkar rana haka tsananin haske ya haskake wannan anguwar. Nan na sami kutsa kaina cikin qaton get ɗin gidan dake zagaye da manyan soldier's da ƙyar domin ɗakkowa masoya mabiyan littafin ƘAUNA BIYU rohoton wannan haɗaɗɗen gidan.
Haka na ringa ratsa SOLDIER'S kawai don samo muku meye wannan gidan ya qunsa🤗🥰
Cikin wani haɗaɗɗen paulour na kutsa kai na, da wata kyakkyawar qaramar yarinyar da batafi ƴar five years na fara cin karo, mai masiyar kyau da tsananin hasken fata, tana kwance jikin wata kyakkyawar farar mata wadda taɗan manyanta kaɗan, amma duk kwakwkwafinka baka isa faɗar shekarunta tashin farko ba.
cikin irin yarintar nan na yara ta shiga doddoka qananun fararen qafafunta, tana faɗin. "Ammey yaushe pa piey naaa zai dawo?, kice ya dawo, kice ya taho min da sabuwar mamien da kika ce zai kawo min tunda kowa yana da mamie amma Ni! Bani da mamien!, idan nace pa piey ya kawo min sabuwar mamie idonsa sai yayi jaaaa, ya fito ni waje ya kulle ɗakin sa!" Tayi Maganar tana ci gaba da birgima jikin matar da data qira da Ammey.
"AMNA papieynki ba kamar sauran mutane yake masu samin freedom na kansu ba, gaba ɗaya ya kanainaye rayuwarsa da tarin busy, don kawai wata rubutacciyar qaddara tazo ta gitta ta cikin rayuwarsa....."
Sai kawai wasu zafafan hawaye suka shiga saƙƙowa daga saman kyakkyawar fuskarnta, alamun ko miye ta tuna haka mai girma ne acikin rai da ruhinta, koda wannan kyakkyawar yarinya da aka qira da Amna taga hawaye na zubowa daga cikin ƙwayar idanun ammey sai kawai ta kwantar da kanta saman jikin ammeyn tare da sakin nata kukan itama.
"Duk lokacin da nayi muku zancen sabuwar mamie keda papiey ba kwaso ke kuka kike, shi kuma papiey ya ya rufe kansa ya koroni waje why?, grenny"
(Ya ilahi ya rahman)
Ammey ta faɗa cenñnn cikin qasar zuciyarta ganin Amna na qoqarin fashimtar halin da suke a ciki. Wani irin rungume yarinyar kawai tayi cikin jikinta tana fesar da wani irin zazzafan Numfashi.....
To masu biye dani shin za'a je? Kuna biye da ALQALAMIN AMMEY LAYLERH ✍️. Don jin yadda tafiyar zata kaya🤗💪🥰
Tafiyar mai zafi ce🔥, salon na musamman ne 🫰✍️ haka ma littafin ƘAUNA BIYU 🌺 na daban ne ba kamar sauran littattafan da kuka saba karantawa bane.
This promise is MIRRAH 💫 AMMEY LAYLERH💪🫰
Shin waye ALIEY?
Shin su WAYE waɗannan bayin Allah? Masu tsananin Bama mutum tausayi, AMNA da kuma AMMEY.
Shin waye papieyn da Amna take qiran sunan ya kawo mata sabuwar mamienta?
Shin wannan wacce irin qaddara ce tayi kutse harta zo ta gitta tsakanin wadannan bayin Allah?
Babu 🖐️🤚🙅🙅 duk kanmu bamu sani ba kai tsaye kun san amsar tana ina???
ƘAUNA BIYU
😳
A gimtse 🫰🙃
*💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘*
~Heart touching love, with love a side 🤍🤍~
Page 5&6
*BY*
*AMMEY LAYLERH*
✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~*
______________
بسم الله الرحمن الرحيم
*Alhamdulillah forever and always 👏*
____________________
♥️🤍♥️
Wasu irin zafafan hawaye ne sukaci gaba da zubo mata, zuciyarta wani irin zafin masifa ke mata, duk yadda takai ga hana hawayen ta sauqa amma hakan ya gagara AMNA, Amna Abar tausayice abar a tausaya mata ce. A kaff duniya babu abin yakai rashin mahifiya ɗaci da ciwo, da tashin hankali.
Sai dai sammm papieyn ta ya gaza ɗaukar ƙaddarar mutuwar matarsa abar sonshi Safiya (Sofeey). Wanda a ranar data haifi Amna a ranarn Ubangijii ya amshi ran safiya.
Ya zam tamkar wani zararre,mara hankali duk sanadiyyar mutuwar matarsa safiya. Saboda da tsananin tashin hankalin mutuwar ta shige shi sosae fiye da tunanin mai tunani,Sabo da wata iriyar zazzafar soyayya yakema matarsa Sofeey, domin shi mutum ne da bai iya so ko qi ba shi kaɗai yasan tashin hankalin da mutuwar Sofeey ta sanya shi a ciki.mutuwar tayi matuƙar bugarsa da kuma gigitar dashi,don saura kadan ya zauce a sannan,tun daga wannan lokacin komai ya tabarbare masa.
Hakan sanya shi killace kansa wanda ko abinda ta haifa ɗinma bai gani ba, saida yakai kimanin sati guda babu wanda yasan ko inda yake,gashi duka woyoyinsa switch off ne, anqira shi, an qira shi amma amsar ɗaya ce switch off. Har sai ranar da safiya taci ka kwana bakwai da rasuwa kana ya kunna phones nashi.yana buɗe wayoyin nashi qira yana shigo mi shi, Saida yayi tamkar bazai ɗaga ba sai yaga ammey ce, yana picking sai yaji ta fashe masa da kuka.
Shi kuma a duniya babu abinda yafi tsana sama da zubar hawayen ammeynsa.da ƙyar da tarin adda'oi aka samu ya ɗan dawo haiyacinsa.
Amma fa ya qara zama miskilan masifa, Tun daga wannan rana ya soke komi da komae idan nace komae ina nufin komae ɗin kuwa na cikin rayuwarsa, inda ya qara zama wani irin miskilin masifa wanda dama cenñnn haka Allah yayi sa da tsabar miskilancin tsiya, sai ga wannan al'amari kuma sune suka taru suka qarasa zame masa jinin jiki.
Wata iriyar soyayya ALIEY yake nuna ma Amnah,wani irin gata yake bata na gaban kwatance,duk wata tarin soyayyar mahaifiyarta ya tattare ta duka ya dawo kanta. Inda yaga duk duniya babu macen da zai iya aura bayan Sofeeynshi, domin ya tabbata babu macen da zata taɓa kaiwa matsayin Sofeeynshi acikin duniyar, Sofeey mutum ce mai tsananin biyayya da bin tsarin dokokin sa, tana tsananin ƙaunar ganin farin cikin sa duk da kuwa cewar shi ɗin mutum ne mai murɗaɗɗen hali da azabar zurfin ciki.
Haka su ammiey da abbansa suna ji suna gani, ayaqi zaman nigeria dama kuma gashi PILOT, haka ammeynsa da mahaifinsa Suke ci gaba da binsa da addu'a da kuma fatan Allah ya kawo qarshen komai.
Wannan shine takaitaccen tarihin ALIEY A takaice.
(Miskilanchi
Idan aka ce mutum miskili ana nufin mutum mara sakin fuska. Mara surutu da yawan magana mutum mai aji wanda baya son raini mutumin da ba kowa yake kulawa ba.
Miskilanchi halitta ce ba girman kai bane wasu mutanen haka Allah yake yinsu.)
"Ya Allah" ammiey ta ambata sakamakon mutuwar safiyan da takejin ta dawo mata sabuwa fil, tamkar yanxu ne mutuwar.
Ita kanta batasan loqutan data ɓata a inda take zaune Amnah kwance a jikinta, sai ajiyar zuciya da take ɗan saki lokaci zuwa lokaci kaɗan. Qiran sallar magrib ta taji ana qira ne ya sanya ta miqewa tare da Amnah, direct bedroom nata ta wuce da ita bathroom ta wuce ita kuma cike da sanyin jiki ta ɗauro alwula tare da gabatar da sallah, ko ta kan dinner bata bi ba tana Nan zaune tana azkar har loqacin isha'i yayi, Nan ma ta gabatar da sallar.
Sai wajajen tara ta miqe tana nufar Amnah domin tashin ta tayi sallah.
Slowly ta shiga tashin ta tare da ambatar sunanta.
"Amnah! Amnah!!takwarana !!!"
Ahankali ta shiga ɗan bude ido cike da magajin barci tace.
"Papiey na ashe dama da gaske kake zaka zo yau ɗin"
Da wani irin kallon tausayi ammiey ta bita dashi, tana jin zuciyarta na qara raunana akan tausayin Amnan. "Cwty ki farka ammiey ce ba papieyn ki bane!" Ɗan kucul bakinta ta turo. "To ki ce papiey na ya dawo gida don Allah ammiey na haka nan na gaji da kallon uncle Irfan kullum" tayi maganar cikin ƴar maganar ta me sanyi. domin sosea tayi missing na mahaifin nata. Sanin surutun Amnah ne ya sanya ammiey daukar ta kawai tana shigewa bathroom da ita wanka ta mata, kana ta sanya ta daura alwula kafin suka fito. Saida tayi sallar magrib da isha'i kana ammiey taja hannunta zuwa main Parlour, tamkar yadda ammien ta tsammata kuwa Irfan na zaune saman sopa laptop daure a cinyarsa yana faman sarrafa ta.
Zare hannunta daga cikin na ammiey tayi, da gudu tayi kan Irfan kai tsaye jikinsa ta faɗa cike da farin ciki,"barka da dare uncle" kanta yadan shafa tare yana faɗin. "Bakiy bacci ba baby?" Kanta ya ɗaga mishi.
"Oya taso kiyi dinner kibar uncle yan aiki ne"
Babu yacce ta iya dole haka ta nufi ammien, don cika umarninta.
★★★
★★
★★★
*ALIEY*
2:20 na dare jirgin su yasauƙa 9j a garin Kano,wani irin numfashi ya fesar me ɗan zafi, loqacin daya fara taka step na mata kalar benen a tsanake. Cikin wani irin zallar izzar da yake da yaci gaba da saqqo wa zuwa babbar harabar airport ɗin.
bodyguard nashi biye da shi wayarshi ya amsa daga hannun ɗaya daga cikin guards nashi, dialog nashi ya shiga kai tsaye domin qiran Irfan ganin har yanxun baizo airport ɗin ba,bayan kuma tun kusan 40 minutes da qiransa ya shaida masa sauqarsa. Ji yay kawai an rungumo shi ta baya tare da cewa "Welcome back my cousin" Saida ya mola dan kansa kafin yace,"Welcome"
Directly wurin daya Parker motornsa suka suna,yana barin guards nashi a Nan kasancewar ruwan sane yawo dasu, ruwansa tafiya babu su. Cikin qanqanin loƙaci suka isa qayatacciyar anguwar SHARAƊA PHASE 01
A tamfatsesen
★ALIEY MAI MATA ESTATE★ motarsu ya Parker ko hong aliey bai bari Irfan yayi ba domin bayasan hayaniyar kowa a yanxun. Yana buqatar ya kaɗaice kansa shi qaɗai, Directly part nashi ya nufa
Hankali kwance cikin nutsuwa da zallar miskilancin haɗi da tsananin zafin nama yake tunkarar ƙaton ploorn nashi.
"ya ilahi" na faɗa loqacin da hancina ya shaqo min wani irin azababben qamshim wanda ya riga da ya gama kama ɗakin, parlour ne haɗaɗɗe domin iya haɗuwa kam ya haɗu komi na palon ya kasance Milk and coffee colour ne.
Paulour ne mae tsananin girman gaske wanda yake ɗauke da da ɓangarori daban-daban, ko wanne ɓangare da irin qawatuwar da yake da kana idan mutum yana tafiya, yana kallon kansa da kansa ne ta cikin glass mirror ɗin da gaba ɗaya shine ya kasance a matsayin gini, wanda shi kuma na ciki kai tsaye yake sanin wanda yake tafen, shi kuma mai tunkarar ɗakin iyaka kansa da kansa kawai yake iya kalla.
***Kadaran kada han ya nufi upstairs nashi.
Tun kamin yakai ga qofar shiga ploorn qofar glasses mirrorn ta fara wani irin rubuta da red and blue colors, inda take rubuta ~welcome back ALIEYO MAI TAMA~
da wani irin style gwanin burgewa ga ba'abocin kallo.
Tattausan Tafin hannun sa ya kifa saman ɗan zagayayyen glasses,kana cikin sillent voice nashi yace.
"I answered"
Zuuuuu glasses in yayi sama baki ɗayansa, subhanallah shine kawai abinda baƙina ya iya furta wa, domin wani irin mahaukacin ploor ne wanda yaci uwar na farkon haduwa da komi da komai, gaba ɗaya ploorn an ƙawatashi da wasu Italian fashion rug farare masu masifar ƙawatuwa da burgewa, ɓangare gudan bangon ɗakin gaba ɗaya anshafe shi da plasma wanda idan har ba sani mutum yayi ba, bazai taɓa cewa plasma bace loqaci guda.
Daga ɗayan gefen kuma wani irin haɗaɗɗan dining area ne inda aka masa adon ƙoyaye masu ɗan girma inda suka ɗan sakko qasa kaɗan da dining ɗin, ɗaya ɓangaren kuwa wani irin azababben beni ne wanda yayi wani irin lankwasa, wanda kai tsaye zai sada mutum da bedroom ɗin hasalin ɗakin kenan, gefe kaɗan da wurin kuma an ajje wani ƙaton dum lightning shima domin bada haske kaɗan, wanda idan ma'abocin wurin baison haske yakan sanja hasken ya zuwa dum light kamar dai da night kenan.wani makeken qaton photone manne da ɓangaren dama wanda wata farar mata mai kama da balarabiya ke jikin photon inda aka rubuta ~SOFIYYA MRS ALIEYO~
da wani irin style akayi rubutun, inda gefen photon kuma again wani photon ne dai amma wannan mutane biyu ne sakamakon wancen da take ita ɗaya. Yana tsaye ita kuma ta ɗaura kanta saman ɗamtsen hannunsa,da ɗan matashin cikin ta daya gama fitowa chass dashi kyakkyawar fuskarta qawace da murmushi, irin ta daga kan nan nata sama tana kallon innocent pace na mijinta.
wanda dukkan alamu suka gama baiyana cewa a qasashen waje ne aka ɗauka photon domin baiyi kama da 9j
A kallon farko mutum yakan iya bama wannan ploor suna da aljannar duniya, domin iya tsaruwa ploorn ya tsaru matuqa.
Kai tsaye aliey yake taka mata kalar benen cikin sassarfa, babban burin sa a yanxun bai fice ace yaji shi cikin ruwa masu ɗumi ba kana ya ganshi yana barci domin hutawa.
yana sanya kansa cikin hasalin bedroom nashi kuwa da wani irin haɗɗaɗɗe lafiyayyan gado naci karo, daga saman gadon kuwa wata haɗaɗɗiyar benc Centre ce mai lokoki wanda samanta akayi wasu qananun sink guda biyu a wurin, sai kuma tsakiyarsu akayi adon wata madaidaiciyar fulawa, ɗaya gefen bedside drawer ɗin kuma wani ƙaton Electric kindle ne, mai bama ɗakin ɗan qaramin haske da night shima irin wanda yake sassanja colors Innan.
Cikin muryarsa wacce ta zama slocoly loqaci guda ya furta "ALHAMDULILLAH" yana jin wata iriyar nutsuwa na sauƙar masa ta Musamman, tare da sanya hannunsa yana shafa lallausan sajen dake kwance akan kyakkyawar fuskarshi.
Sau cikin qafarsa ya shiga zarewa tare da fara ɓalle maɓallan gaban rigarsa, tare da zare dogon wandon trouser shima ya rage daga shi sai boxes da farar vest, direct toilet yawuce ruwa masu ɗumin gaske ya haɗama kansa tare da zuba tularen wanka acikinsa. Iumsassun idanunsa da akoda yaushe suke a lumshe ya kuma lumshe wa, jinsa cikin ruwan ɗumin gaba ɗaya ɗumi da kuma ƙamshim ruwan, suka taru suka kuma sanya mashi wata iriyar nutsuwa.
After 30 mint ya fito yana ƙamshim shower gel, ɗaure da farin towel ya fito fari tasss ,sai uban ƙamshi yake zubawa. clothes nashi yashige ya shiryo cikin tree kwata da riga armles ruwan sararin samaniya, mara hannu a tsanake ya zirah jallabiya, a saman kayan.
dadduma yaɗauko yashimfiɗa yatada sallar nifilfulun sa duk kuwa da cewar tsakiyar dare ne amma haka ya gabatar
Sallolinsa cikin nutsuwa, bayan ya idar da nafilfulin ne ya janyo drower na littattafan sa, Alqur'ani ya ɗauko *SURATUL MARYAM* ya fara karantawa cikin ƙyaƙyƙyawar ƙira'arsa, da zakin murya tamkar Sheikh sudues yake rairawa,bayan yagama karatun nashi...
Tare da bin addaoin da yakan yima Safiyyansa bayan ko wacce sallah, sai wajajen qarfe huɗun dare kana ya a tashi a wurin yana faɗawa saman haɗaɗɗen austra bed nashi.
Alarm clock ɗin dake manne saman gadon ne ya farkar dashi, agajiye ya shiga ware gajiyayyun idonsa wanda samm barcin ba wani isar shi yayi ba, kansa har wani ɗan ciwo ciwo yake masa.
Hakan ya sanya a nan cikin ɗakin ya gabatar da sallar asuba nashi, yau ko azkar bai tsaya yiba ya kuma hayewa saman gadon sa tuni wani barcin ya kuma yin awon gaba dashi.
10: 5am
Gaba ɗaya suna Zazzau ne a dining area ammiey, Abba, Irfan,sai Amnah, hankali kwance suke dinner abinsu domin babu wanda yasan da xuwan sa in banda Irfan, Shima kuwa mugun kashedi yasha shi yasa yaja bakinsa yayi shiru.
Sassanyan qamshi da kuma takun tafiyar da suka jine ya sanya kowa dakatawa, tare da dago kawu nansu a tare.
Akansa suka sauqe idanunsu yana tafe cikin tariyar nan na izza haɗi da qasaita, baki ɗaya da idanu suka bishi, kafin Amnah ta tashi ta nufi papieyn ta da Wani irin gudu da tsananin murnarn ganin mahaifin nata,duk da baya fuskarta dake nan a damke tamkar damammen kunun kanwa, amma hakan bai hana fararen haqiransa bayyanuwa.
Hannayensa ya ware mata yana ɗan sassauta fuskarsa, wani irin shigewa jikinsa tayi shi kuma ya wani rungumeya tsammm yana sakin ajiyar zuciya mai ɗan qarfi. "I miss my princesses" ya ɗan raɗa a cikin kunnuwanta ta yanda iyaka iya ita kaɗai ne taji abinda ya ce ɗin.
"Niya nayi kewar papiey, tambayi ma ammiey kaji ina ta jiranka kuma ma ka kawo min sabuwar......
Saurin manna tafin hannunsa yayi saman bakinta,yana nuna kan saman bakinsa tare da faɗin "Shiiiiiiiiiiiiiii"
don ya riga da yasan abinda take shirin faɗi ɗin, a take yaji wani irin bugun zuciya ya zirayar ce shi.
(Why? yasa nake jin irin haka duk lokacin da princess zata min zancen sabuwar momie?)
A cenñnn qasar zuciyarsa ya ayyana hakan har zuwa loqacin zuciyarsa na ci gaba da beating very fast.
Tashi tsaye yayi kasancewar yaɗan turqusa mata ne, gwiwar shi ɗaya har tana kasa ma. Duk abinda ya waka ne kuma akan idanun abbansa da Ammiey da suka jure shi da IDO tamkar wani sabo ya zame musu.
A hankali ya janye idanunsa da ga kallon su cike da basarwa yana amsa gaisuwar da Irfan ke masa, da idanu ya amsa masa kawai alamar ƴan izzar na kusa. zama yayi akan ɗaya daga cikin kujerun dining ɗin. Cike da risinawa da girmamawa ya shiga gaida mahaifan nashi. Kada ran kada han ammey ta amsa tana ɗauke kanta daga gare shi, duk kuwa da cewar a cenñnn qasan
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 2 Chapter of 23