Join WhatsApp Group Join Telegram Download APK


Share this page
ciki, wasu kuwa zasu rasa uba uba ɗan uwa ƴar uwaa, miji ƴaƴa, wasu zaki same su da tarin kalubalen ƙaddarori iri iri wanda da zakiy gamo dasu da kinji taki ƙaddarar ba a bakin komi take ba. UWAA itace mafi ƙololuwar da idan ka rasata har gaban abada ka rasata keñan, wanda kafff duniyar ko za'a tara dubanta to kuwa tabbas babu kamarta!, haka ma mahaifi, Shine duk wani ginshiƙin rayuwa da ɗawaini ta ƴaƴansa, wanda akace randa babu shi tofa shikenan baka da wani saurin gata saina Ubangijiin sammai, wasu ƙaddarar su barace barace, wasu makafi ne wasu guragune!, wasu kutarai ne, wasu wasu kowa yana da nashi salon ƙaddarar, ke kuwa fa iyaka mijin da ake shirin aura miki kika rasa, wanda ayau idan Ubangijii yaso zai baki fiye ma da wanda kika rasa ɗin, harma ana tafe ki iya mantawa dashi acikin rayuwarki dama duniyarki baki ɗaya, shin ina alƙawarin da kika min kodai kin gaza ne, shin ina nasihun da ummie take miki kina nufin har wasiyyar yaya Aliyu Naaaaaa kin haɗa kinyi fatali dasu Fatima?” Kasa shuru queen tayi dan ji take kamar yanzu ne komai ya faru, ji take zuciyarta na yimata wani irin soya tabbas tasan zafin ƙaddara domin kuwa ta zana mata nata salon ƙaddarar acikin tsakiyar ƙirjinta, wanda tasan har gaban abada hakan bazai taɓa gushewa daga cikin zuciyarta ba. da kyar Fareedah ta samu ta rarrasheta tayi shuru gudun kada wani sabon ciwon ya sameta bayan wanda take ciki, kana bata son kowa ya fashimta halin da take ciki. Tisa ƙeyarta tayi har bakin toilet ɗin dake cikin sittin room ɗin tayi, fuskarta ta wanko tare da tsane ruwan Kafin su nufo hanyar fita. Turusss duka su biyun suka ja suka tsaya ganin yaya Nurien tsaye a bakin ƙofar fitar alamun yaji komai keñan, jiki a mace suka dago kai suna kallon sa. Da ido suke roƙarshi ya fashimci su kar wanda yaji abinda ya faru tsakanin ta ALIEY, shi ina sammm ma bai fashimtar Yaren su, idanunsa yawo kawai suke akan fareedah, jin shiru shiru yaƙi ce musu komai ne ya sanya su ɗan dago kansu, ai kuwa caraff suka kama yayan nasu ido duka biyun kan fareedatu baiwar Allah. Wani irin kasa tayi da kanta tana jin tamkar ƙasa ta tsage ta shige. ”Kin iya lallaɓa soyayyar wasu amma Ni har yanxun kin gaza lallaɓa nawa soyayyar” Sune kalaman da suka shiga cikin kunnuwansu, dake ma har an bashi fareedan tun tuni amma firrr taƙi tace ita ba zata yi aure yanxu tabar queen ɗin ba, wannan shine dalilin jirkinta auren nasu da kuma queen ɗin ta samu shine fa aka haɗe bikin nasu. Nan da sati kai biyu masu zuwa. A kunyace ta zame hannunta dake cikin na queen, kafin cikin fakar idanunsu yiffff ta fice a gidan da dan gudu. Dama kuma tunda zancen bikinta da yaya Nurien ya tashi ta rage shigowa gidan kunsan abinka da kunyar nan irin ta sirikai. Sosai queen ke ƙyakyata dariya don ba ƙaramin dariya fareedan ta bata ba, wannan abu shine dalilin daya sanya queen mantawa da batun wani Aliey..... *A week later* Sosae abubuwa suke tafiya cikin tarin farin ciki, inda aka kai kayan lefen yaya Nurien gidan su fareedah wanda yaya jay ne yayo oder nasu tun daga Indiya, kayane na gani na faɗa akwatuna takwas aka mata kaya kuwa sai kun gansu, aikuwa ranarn mutuwar Aliyu shureim sabo ya dawo musu, haka suka ringa ɗauke kwalla daga saman fuskokinsu. Don sun san da yana nan sai yafi kowa murna da wannan auren Allah Sarki dama haka rayuwa take saidai muce Ubangijii ya jikan Aliyu shureim. Haka dai abubuwan suka ci gaba da wakana, biki nata ƙara kusantowa ƴan uwaa na nesa harsun fara zuwa gidajen biyu ko nace uku. Ɓangaren Aliey kuwa shi har ya manta da wani lamarin aurensa, Sai Ranarn dasu Oum Anum suka sauƙa a ƙasar 9j ita da ahalinsu na Madina, wajen su shidda suka zo Sarki julaideen wanda ya kasance shine babban yayansu sai kuma Oum Anum yaya ga ammieyn sai kuma Oum abiddeen wacce ta kasance ƴa ta uku sai kuma ita ammien wacce ta kasance autarsu, Su huɗu ne suka kasance a wurin mahaifiyarsu AYUSSHA wacce suke ƙiranta da MAH!. Sai ita anun ɗin da suka zo da ita, da da farko tasha bikin Irfan ne zasu zo sai daga baya take jin ashe bikin alieyo ne. Ranarn har rufe kanta tayi a ɗaki tasha kukanta, domin ba ƙaramin so take ma alieyon ba shi kuma Samm bata gabansa, a waya ma data fiye damunsa blocked nata yayi. Yanxu haka bikin ta saura baifi wata ɗaya ba amma duk da ta gaza cire Aliey daga cikin rai da ruhinta. Cikin nutsuwar sa yake saƙƙowa Samm fuskarnan ko ɗigon annuri babu, yana sanye cikin wasu haɗaɗɗaun trouser blue black wanda suka ƙara haskaka fatarsa suka kuma bayyana ainihin ƙyawunsa. hankali kwance yake saƙƙowa hannuwansa zube cikin aljihun wandon sai baza ƙamshi uban ƙamshi yake, Dining ɗin babu kowa sai iyaka Anum data kafe sa da Mayun idanunta tamkar ta cinye sa danye, barka da dare ta mishi amma ko kallon inda take baiyi ba, zama yayi kan ɗaya daga cikin kujerun dining ɗin, ganin ya zaune ne yasa anum saurin jawo pilet tana shirin sarving nashi. Yatsunsa biyu ya ɗaga mata tare dayin ƙasa dasu alamun ta barshi keñan, cike da mayen son dake ɗibarta gare shi cike kuma da kissa cikin sexy voice ta furta. ”LIEYOH! What's wrong with me?and all the things that you do not understand and do not understand, why LIEYYYY?” Tamkar ya shaƙeta haka yake ji saidai sammm bazai iya hakan ba, shifa a rayuwarsa ya tsani mace mara kamun kai, da bayan mutuwar SOFEEYERH ita aka so aure masa, amma rawarn kan yarinyarn da kuma rashin ajinta yasa sammm yaƙi aminta da batun, wanda hakan harya kaisu ga samun saɓani tsakanin family nasu, akan hakan har matsala ya samu tsakanin Abbansa da kuma ammieyn. Tun daga loƙacin kuma basu kuma masa batun aure ba sai akan wannan. A hankali ya miƙe yabar kan dining bayan ya kammala shan coffee ɗin fuskar nan a tamke, parlourn ciki ya koma yana zama kusa da Irfan kan 3 sitter wanda shikuma Irfan yana kan 2sitter yana pressing phone nashi, Da wani irin kallo tabi bayansa tana kammala yin dinner Sannan itama ta miƙe tana dawowa parlourn samun wuri tayi ta zauna kusa da Irfan, hannu Anum tasa ta buɗe ledar dake gaban Irfan ɗin. wanda amfanin da yake da wayarsa ne ya ɗauka hankalin har haka,kayan ciye ciye ne gasu nan chips, bugger sai kwalayen picanto, dominos pizza shawarma da sauran wasu tarkacen kayan maƙulashe, Sai ɗayar ledar dake ɗauke da fried meat (tsiren nama) da yaji kayan haɗi sai uban ƙamshi yake yi, miyan bakinta har tsinkewa yake wajen buɗe ledar baki daya ba tare da neman izini ba ta fara antayama cikin ta. Tsammm ya miƙe yana nufar upstairs nashi tsaye kan windown na ɗakinsa Ahankali ya furzar da iska mai zafi abakinsa, yana jin sammm babu daɗi acikin ransa. A hankali yabar jikin window'n yana komawa kan hadadden gadonsa yana kwanciya flat wasu irin abubuwa masu girman gaske na kai da komo acikin brain nashi, Sai yanxun ma na lura da irin gyare gyaren da aka kuma ƙawata bedroom ɗin dashi, baki ɗaya ɗakin ya ɗauki wani irin azababben kamshinsa tuni ƙamshi da kuma sanyin A/ CN dake ratsa shi wani irin daddaɗan barci yayi awon gaba dashi. Mutuniyar taku kuwa Hajjo hr zuwa loƙacin tana gidan domin dama tace bata tafiya har sai anyi bikin Shalelen ta, ɗaki ɗaya duka tare da MAH wanda akwai tsohon ƙawance dama tsakanin su tun na ƴen matanci, kasancewar mahaifin su hajjo ɗin irin me kuɗin nan ne yake ɗaukar family nashi suje ƙasar Madina suyi hutu, hajjo kuwa daga ƙarshe ma Acen tayi karatun ta, wanda shine har suka aure suna raya zumuncin dake tsakanin su, duk kuwa da cewar suɗin ƴaƴan sarauta ne. Ahaka ahaka ana tafiya harya suka kai ga suma sunyi aure sun hayayyafa har takaisu haɗa zuriya, domin ita ammien ƴar cikin masarautar garin Madina ce ƴar sarki YOUSOUF Jikar Sheikh Abduljabbar. Wannan keñan. Bangaren amare kuwa ciki da woje Mama ke gyaran su, a hakan ma Saida taci uban ta kana ta amince ake gyara tan, takanas Mama ta ɗakko AUNTY AISHA ALIYU GARKUWA take tsuma ƴaƴan nasu cike da woje da irin haɗaɗɗun maganunnuwanta irin nasu sanyi, gyaran breast, na ƙarin sha'awa, na saƙko da ni'ima nan take haka dai aunty aysha Aliyu garkuwa ta shiga gyaransu Queen da fareedah, ko ganinsu ba'a yi duk wani shige da ficen daya kamata ƙawayensu ne ke zirga-zirga tsakaninsu. Gashi yau sora kwanaki uku cifff bikin ta kama yau muna Laraba keñan. Aunty zeey kuwa tun sati biyun bikin ta diro kafin daga baya yaya jay shima ya biyo jirgin ya dawo. __________★★★___________ Malam bahaushe ya kance rana bata karya saidai uwar ɗiya taji kunya, Masu iya magana kance da sannu sannu ana tafiya saidai a daɗe ba'a jeba, to sai gashi yau Allah ya kawo mu ɗaurin auren Aliey da kuma queen fareedah da yaya Nurien. ♥️🤍♥️ Hayaniyar da kuma surutan dake ɗan tashi sama sama ne yasashi ɗan buɗe lumsassun idanunsa tare da yunƙura wa yana tashi zaune Acen ƙasar zuciyarsa ya furta. (Shi keñan yanxu babu damar mutum ya sake, abin ma sai yakai ga anbiyoni har ɓangarena!) Yar ƙaramar tsoki yayi domin yasan cewa, idan ba hajjo da kuma Oum Anum babu wanda ya isa shiga masa bangarensa, dan ko Anum ta san mine take yi dade da wasa bata taɓa gigin shigo masa koda parlour bane. Saƙƙowa daga kan gadon yayi tare da wucewa cikin bedroom nashi kai tsaye, yana tsakar ma kansa shower, Saida ruwan ya dake shi sosae kana ya tara ruwa acikin bathtub wanka yayi sannan yayi brush, duk da cewar kuma yanajin yunwa sosai amma bayajin zai iyacin wani abinci, domin shifa komi tsaya masa yayi cakkk tunda aka fara hidimomin bikin ya killa ce kansa babu ma wanda ya gana bare a dame shi, saima wasu daɗan waƙoƙin ɗaya ringa bugawa wajen guda uku. Ahankali ya murɗa handle na ƙofar bathroom ɗin toilet ya fito, jikinsa sanye da white bathrobe. # Turus haka yaja ya tsaya yana ƙarewa mutanen dake Zazzaune zama irin na sarauta da kallo # MALEEK TOUFIQ, na cikin littafin KAREN BANA, na AMMEY LAYLERH # JALAAL AREEF na cikin littafin (JALAAL AREEF) na AMMEY LAYLERH ABDULMALEEK KUWAIT {AK} Na cikin littafin MIKIYA shi ɗinma dai nawan ne Ni AMMEY LAYLERH ✍️ {REAL MIRRAH 🫰 Sai kuma yaya jay wanda ya kasance babban abokin ango, kana kuma yayan ango Inda ko wannen su yake sanye cikin rantsatstsun shiga ta alfarma, ta masu juya masu gidan rana. Murmushi mai taushi MALEEK TOUFIQ ya sakar masa tare da tasowa ya ƙaraso kusa da shi Hannunsa yasa yaɗan bugi shoulder na Alieyn. Cikin yanayinsa na wanda bai saba magana ba yace. ”Congratulations dude” Kawar da kansa gefe yayi yana mamakin ta yadda akayi suka san da batun auren nashi, (jay ɗin ka) Zuciyarsa ta bashi amsa kai tsaye,hakan yasa yayi saurin kallon sashen da yaya jay ɗin ke zaune, murmushi ya sakar masa tare da gaɗa masa kai alamar aikin sane wannan ɗin. Cikin farin ciki JALAAL AREEF ya Taso cikin hanzari ya jawo Alieyn ɗan sauri yana faɗin. ”Hurry up and get ready, we don't have time malam” JALAAL AREEF ɗin ya faɗa daidai yana daidai tama Aliey tsaiwa gaban ƙaton mirrorn ɗakin. Shi kuwa AK tunda suka fara maganar su A bai tsoma tasa ba, domin duk yadda kuke tunanin zafin zuciya taurin rai irin na Aliey wannan ubansa ne a komai ma, Kuma sau biyu suna haɗa ido ko wannen su ya basar LoL 🤗 Ni kuwa AMMEY LAYLERH nace wannan wanne irin abu ne lafiyar zuciyarsu ƙalau kuwa?. Ganin yadda suka tasa shi gaba ga kuma yadda suna tsatstsare shi da idone yasa babu yacce ya iya haka ya shiga gyara jikinsa, Bayan ya kammala ne kuma ya gyara beautiful beard ɗinsa da kuma tarin tumilin sumar dake kwance saman kansa, wacce ya fake ta a ƙeyarsa. Haɗaɗɗun tsadaddun tularukansa ya shafa ganin kuma yana shirin shigewa cikin closet na kayansa ne zai ɗebi kaya, yasa yaya jay saurin miƙa masa set ɗin wata haɗaɗɗiyar white getzner da aka killacesa cikin wani haɗaɗɗenn kwali. ”Just accept it and complain later” Ya jay yayi saurin tararn numfashinsa domin yasan kaɗan dag cikin aikin alieyonsa ne yaƙi sanya kayan. Ganin irin roƙon da jay ɗin nasa ne masa ta ƙasan idanune ya sanya shi amsar kayan jiki a sanyaye. Ɗan kallon jay ɗin nasa yayi Kamar zaice wani abu saiya fasa kuma, tare da komawa cikin clothes nashi. Lumsassun Idanunsa da yau dama yake jin su kuma sauya yanayin su ya ɗan lumshe saboda ganin wata haɗaɗɗiyar getzner da aka ƙawata ta da ɗinkin riga da wando sai kuma babbar riga, wanda akayima irin wani fitinannen aiki da aiki na musamman. Jiki a mace ya miƙe ya fara shirya kansa cikin wannan rantsatstsiyar getzner nan Yah Ilahi ba ƙaramin kyau kayan suka masa ba wanda shi kansa saida yaji hakan ajikinsa. Aikuwa kyawun nasa bai sake bayyana ba saida ya mirza wata haɗaɗɗiyar hulan dake matsayin ta kayan me ratsin blue colour still itama. Black socks ya sakama fararen ƙafafunsa, tare da zura wasu haɗaɗɗun classic shoe sauki ciki masu kalan blue suma. wanda suka kuma bayyana haɗewarsa da kuma kyaun kwalliyarsa. Still ya kuma janyo wata tsadaddiyar rolax yana ɗaurawa saman tsintsiyar hannunsa. Sassanyan turaren ya ɗauka yana kuma feshe jikinsa, shima harya gaji da wannan abubuwan domin kuwa hakan ba karamin takura sa yayi ba. Kyawawan idanunsa ya ɗan lumshe jin yanayin bugun zuciyarsa naci gaba da sauyawa, Ahankali ya shiga tafiya da takunsa mai cike da tsantsarn izza yana fitowa cikin parlourn. Wani irin fitinannen ƙamshinsa daya daki hancinsu su maleek ne kuma yasa duk suka maida kallonsu ga kofar bedroom ɗin harda AK da sai yanxun ya ɗago yana ɗaura idanunsa masu launin madara akan Alieyn, cikin yanayin isa da kuma izza tsammm ya miƙe tsaye cikin taku ɗaiɗai ya nufo Alieyon, cikin tsantsar zallar miskilancin sa tare furta ”Wow Masha Allah” Ya faɗa yana ɗan rungumo sa zuwa cikin jikinsa kansa ya ɗago wanda sai a loƙacin sukayi ido biyu dashi, ɗan murmushin gefen baki ya sakar masa yana ɗan buga bayansa cikin cool voice nashi ya furta. ”Thanks eagle” Hannunsa ya kamo tare da yima su maleek alama akan su tashi su tafi, haka suka fito gaba ɗayansu kowannensu kallo ɗaya zaka masa kasan cewa kuɗi da Hutu da kuma kyau na kai musu. Cikin Wata haɗaɗɗiyar Bugatti Chiron blue black suka shiga, shida yaya jay da AK ne abaya, sai maleek da kuma Jalaal areef dake gaba wanda shine zai driving nasu. Sai kuma motocin escort nashi dama na sauran abokansa suka rufa musu baya, yadda kasan shugaban ƙasane a ciki haka narkakkun motocin suka jera suna tafe a tsari, bakajin ƙaran komi saina gittawarsu suuuuuu suuuuuu suuuuuu shine kaɗai abinda kakeji a shimfiɗeɗen titin. 11:55am suka isa babban Masallacin da za'a wakilci dauren, Cenñnn na hango mugu ogan fatimanku yaya Nurien cikin wata rantsatstsiyar getzner fara ƙall sai murmushi yake ta famar saki, har wani sauri yake yaji an shafa fatiha. Motocin su na fakawa baki ɗaya kallo ya dawo kansu *💘🌺ƘAUNA BIYU 🌺💘* ~Heart touching love, with love aside 🤍🤍~ Page 33&34 *Na Maryam Naseer Ibraheem* *AMMEY LAYLERH ✍🏻♥️* ✯ *~🌠 OFFICIAL MIRRAH 💫~* _____________________ ♥️🤍♥️ ”Alhamdulillah alhamdulillah alhamdulillah, Allah shine abin godiya Ako mi da komai" suna kalaman da ammey ta shiga faɗa loƙacin da Abba yake sanar mata an ɗaura Alieyon ta, wani irin maɗaukakin farin ciki take jin kanta a ciki, wannan ranar jinta take ta musamman. "Aiyuriri, aure ya ɗauru alieyo saidai ka mutu" sune kalaman da hajjo ta shiga faɗa tare da juyi a tsakar parlourn, Hannuwan MAH! Sama ta shiga faɗin, "Ya rabbi ya mujibud da'awati ka tabbatar da tarin Alkhairukan akan wannan auren, ya Ubangijiin taliƙa ka kaɗe duk wata fitina dake cikin auren nan, رَبَّنَا وَأَدْخِلْهُمْ جَنَّاتِ عَدْنٍ الَّتِي وَعَدتَّهُم وَمَن صَلَحَ مِنْ آبَائِهِمْ وَأَزْوَاجِهِمْ وَذُرِّيَّاتِهِمْ إِنَّكَ أَنتَ الْعَزِيزُ الْحَكِيمُ وَقِهِمُ السَّيِّئَاتِ وَمَن تَقِ السَّيِّئَاتِ يَوْمَئِذٍ فَقَدْ رَحِمْتَهُ وَذَلِكَ هُوَ الْفَوْزُ الْعَظِيمُ Our Lord! and make them enter the gardens of perpetuity which Thou hast promised to them and those who do good of their fathers and their wives and their offspring, surely Thou are the Mighty, the Wise. And keep them from evil deeds, and whom Thou keepest from evil deeds this day, indeed Thou hast mercy on him, and that is the mighty achievement. Ubangijinmu! Kuma Ka shigar da su gidãjen Aljannar zama waɗanda Ka yi musu wa'adi da waɗanda suka kyautata daga ubanninsu da mãtan aurensu da zurriyarsu, lalle ne Kai, Kai ne Mabuwãyi, Mai hikima" "Ameern MAH!" Su Oum Anum da oum abiddeen suka haɗe baki wajen amsata, banda Anum ɗin data chakume fuskarnan yawa irin kunun da yayi barcin nan LoL 🤩🥴🤗. Amnah ce ta faɗo parlourm da murnanta tana ƙiran "AMMEY! Ammey!! Ammey wai papiey ya samo min new Mommah?, inji uncle Irfan" Sammm ba ma ta kula da cewar ammey bata parlourn ba. Mah! Ce ta ta janyota jikinta cikin jin tsananin ƙaunar amnah a cenñnn tsakiyar zuciyarta ta furta "Insha Allah princess papieynki yayi aure!, ya auro Miki New Mamie da zataci gaba da kulawa dake da papieynki" Tsalle tsalle ta shiga shi da murna tana cewa "yeeeeeeee My mother is not dead, I will also have a mother like Afnan, I will also tell them that I have a mother!" Wata kwalla ammey dake tsaye tun farkon ƙiran da taji Amnah nayi mata ta fito, cikin matsanancin tausayin ta taji wahaye na sauƙar mata, Hajjo ce ta gani Idanunta sun cika da kwalla ta janyo Amnah jikinta, cikin karfafa gwiwa tace. "Sosae babyn papiey mommanki na nan tare dake, kema kina da mama kawar kowa ba” Mah ce da tun farkon tsaiwar ammien take lure da ita ne ta yafi to ta da hannunta ta mata alama data ƙaraso. Ƙarasowa tayi tare zama tsakiyar yayyenta. Ajiyar zuciya ta sauƙe loƙacin da taji MAH ta janyota samar jikinta, Allah Sarki uwa mahaifiyar da baka da kamarta har gaban abada, duk girman ka tabbas haƙiƙa kana buƙatar kulawar mahaifiya. A jejjere taci gaba da sauƙe ajiyar zuciyar, Cikin sanyin murya ta shiga faɗin, "Ma muci gaba dama mae sunan manya adda'a, ina tsoron zafin zuciyarsa, ina tsoron wannan auren kamar wancen karon! Kinsan sanadiyyar ƙunci da zafin zuciyarsa SOFEEYERH ta kamu da Heart at" Saurin rufe mata baki MAH tayi ta shiga girgiza mata kai. "Little dooo! Taya kike tunanin cewa ALIEYO shine silar komai daya faru, keñan kin manta da faɗin Allah da yace duk wani abu da zai faru da bawane rubutacce ne tun ran gini tun ran zane, ina tunanin ki?, Ina Ilimin, Ina hankalin da sanin da kike dashi?, Shiiiiiiiiiiiiiii kada na kuma jin wannan maganar a bakinki" Haka dai MAH ta shiga kwantarma da little dooo nata hankali,tare da hajjo ma da ita harda su share kwalla, "Safiya mutuniyar kirki munyi rashin mace ta gari, amma ba komai inaji a jikina Insha Allah wannan yarinyar Alkhairi ne a cikin zuriyar mu" A fusace Anum ta miƙe tana shirin barin parlourn, da sauri ammey tace "A Ni kuwa Anum taimaka ki kaima Me sunan manya koda coffee na shine, don ina tunanin babu abinda ya zubama cikin sa wayewar yau!" Da harta ɓata fuska jin ammiey ta ambaci alieyo ne ya sanya ta ƙarasowa da rawarn jiki, domin ita sammm ammey tama manta da wani zancen aure ya taɓa shiga tsakanin aliey da kuma ita Anum ɗin, shekaru wajen uku kenan ko huɗu. Plask ɗin haɗaɗɗen coffee ɗin ammiey ta miƙama Anum sai kuma wani plate na tangaran wanda ta zuba masa danbum nama me azabar daɗin gaske. Yana Sanye cikin wata kasaitaciyar collection na ƙananan kaya ta kamfanin dior hormes white shirt and a very soft black trosers. Tun da garin Allah ya waye dede ƙofar parlour bai sanyo ƙafarsa ba, kuma baya jin zai iya fitar don baki ɗaya yama rasa hasalin abinda ke damunsa. Idanunsa Lumshe zaka ɗauka ma barci yine, amma kawai yana sauraran bugun da zuciyarsa ke masa ne, saida ta ɗanna doorbell wajen sau uku jin shiru ne kuma ya sanya ta tura ɗakin kai tsaye, jin a buɗe ƙofar take kuwa ba ƙaramin sanyaya mata zuciya hakan yayi ba. Kutsa kanta tayi cikin katafaren parlourn, wata iriyar ajiyar zuciya mai qarfi ta saki, jin wani daddaɗan ƙamshin perfumes da sukayi welcomin nata, Lumshe Idanunta tayi tare da buɗewa tana bin baki ɗaya parlourn da kallo, A nutse ta dubi bangaren damarta da kuma hagu ganin hanyoyin har biyu,kai tsaye ta nufi ɓangaren damarta domin tafi kyautata zaton nan ne ƙofar bedroom nashi take. Nan ma Saida tayi noking doorbell ɗin still nan ɗin ma dai shiru, ita kuwa hakan yasa ta kutsa kanta cikin tsararren bedroom ɗin da kai tsaye zaka iya ƙiransa da aljannar duniya, domin ya haɗa komi da komae na buƙatun rayuwa. Kwance luff ta hango shi saman Italian bed nashi, yana kwance ya nutse cikin lallausar katifar gadon dake shimfiɗe cikin wani tsimammen farin duvet ɗin daya masifar ƙawata gadon. Ganin tayi wajen magana har uku ne bai amsa ta yasa Ahankali takai kanta gaban gadon. Ƙasa takai dab da setin kansa, cikin wani irin murya mara amo ta furta, "MY LEEEYO" Tayi maganar tana sauke Mayun idonta saman kyakkyawar fuskarsa, yana jinta yayi banza da ita hasali ma juya kanshi yayi yana tsime akan lallausan trow pillown sa, kamar da icce take maganar ba tare da ya furta koda E bane. Cikin tsantsarn sauƙin da taji yana ɗibarta akansa ta kuma furta "LEEEYO! Get up pls" Tsimewa yayi bai kula taba cikin a Kasar zuciyarsa yaja ƙwafa, yana jin wani masifar haushinta na nemar halaka shi. Bakinta takai daidai setin bakinsa da nufin ta masa kiss 😘 Cikin hargitsatstsen sauti ya kotsa mata wata uwar razananniyar tsawar data kusan sumar da ita, A kiɗime a kuma gigice take shiga neman hanyar data shigo, tana samun hanyar wucewar kuwa ta fita da ɗan gudunta ga wani kuka na kwace mata. *Queen* A daskare ta tsaya chak kamar wacce akayi freezing nata dan ko iya juyowa ba tayi ba, Wani rumtse idonta tayi for the moment tana sauraran bugun zuciyarta, sharrr kuma hawayen tashin hankali suka wanke samar kyakkyawar fuskarta, A karo na biyu ta yaya

Chapter 13 of 23