gaji 💆🏻♀️💆🏻♀️💆🏻♀️💆🏻♀️ sai xuwa dare insha Allah
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FZOG6TDjDid2W63LyRn3XP
★★★
____________________________
*💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐*
~💸 THE BILLIONAIRE 💸~
A story of pure love that touches the ♥️
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
Page 15&16
*~Story planning and writing ammey laylerh ✍️~*
DEDICATED to SAPWAN AHMED✨
*JUMA'ART IN ADVANCE 🤝🤝
___________________________
♥️🤍♥️
"Ummana da gaske wai yanxu bikin nawa Za'a yi?, kuma nan da sati ɗayan!?"
Ahankali umman ta sauqe ajiyar zuciya tare da ɗan shafa saman kanta dake bisa qafafun ta, sai kuma ta dube ta da ƙyau cike da kulawa tace.
"To kodai baki shiryawa bikin ba? a fasa" umman ta qarashe maganar tana sakin murmushi, ita kuwa Layla qara gyara kwanciyarta tayi ajikin umman, tare da lulawa duniyar tunani, da wasu abubuwa ke qoqarin dawo mata, sai kuma tayi saurin rumtse idanunta jin kanta naɗan yi mata nauyi, hakan ne taci gaba da maganar zuci dake tabbatar mata da cewa ehhhhhhhhh lallei wannan auren nata babu fashi, domin ganin yadda ummanta keta faman shirye-shirye ba kama hannun yaro, ga wasu abubuwa da umman ta fara bata a ƴan kwanakin nan acewarta wai na gyaran jiki ne, hakan shine yake qara tabbatar mata da cewa lallai wannan aure yiyayyene, to idan har wannan auren yiyayyen ne shi kuma yana a matsayin meye a wurin,
Ahankali ta tsinci kanta ta jujjuya zoben dake maƙale a yatsarta na qarshe, sai kuma tayi saurin dake zuciyarta tare da toshe kunnawanta jin kalmomin daya faɗa mata a wancen loqacin na dawo mata daram a tsaƙiyar kanta.
"Are you marry me?"
Sosea ta qara rumtse idanunta da qarfin masifa, kafin jikinta ya shiga wani kakkarwar ɗari atake taji woni irin zazzafan zazzafi na rufe ta, ummah dake zaune tana tasbihi ce tayi saurin cira kanta tare da faɗin.
"Subhanallahi Maryam zazzaɓi kuma?, yanxu fa anan qalau kike innalillahi wa'inna ilair raji'un, bari malam ya shigo mu tafi kyamis"
"Idan nazo ɗin me zanyi? KEEE keeeee KEEE AMINATU ki fita idona na rufe, na hanaki xuwa kyamis ne? Qofa a buɗe take yanxuma tashi kije, idan har kina da quɗinki".
Umma kuwa baiwar Allah cike da martabawa tace.
"Ehhhhhhhhh insha Allah akwai kuɗi a hannuna bara na miƙata, ko nan bayin layi ne"
"Tom dadai yafi ya faɗi maganar tare da shigewa ɗakinsa, dama daga bayi ya fito gitta wa yazo yi shine yaji batun kuɗi, yake naiman zubama umma tijara.
Ita kuwa Ummah qaton himar nata ta ɗauko, tare da zirawa tana kama hannun LAYLAHN da zazzaɓin ya qara rufeta rumm, "au Bara na ɗauko kuɗin" cewar umma tana shigewa uwar ɗakanta, ganin hakane yasa Layla ɗaukar buta tanufi bayi domin kama ruwa.
Tana fitowa Inna ladiyo ta bita da wani irin kallo.
"Wallahi na tsaneki Layla , na tsani koda jin sunankine, a dole nake rayuwa dake cikin gidannan keda uwarki, kun riga da kun zamemin jaraba, ƴan iska Mayu masu fararen fuska tamkar SADAKA YALLA!"
Inna ladiyo ta faɗi hakan cike dajin tsantsar tsanar Laylan.
Umma ce ta fito cikin hanzari daidai loqacin Laylan ma ta fito a bayin, cikin girmama abokan zaman nata umma tace musu ta tafi ta miqa Layla kyamis, a ɗage Inna ladiyo ta kalli umma haɗi da yatsina fuskarta,wacce tayi azabar muni nan take kuwa, a kaikaice ta kuma duban umman tare da turo ɗan kwalinta gaban goshi, sai kuma tace.
"Allah yasa dai ba abin kunya akayi ake shirin zubarwa ba"
Aukuwa hajjama ta ce zancen tare da faɗin.
"Yo wa ya sani abu a duhu, dan naga dama ƴan kwanakin Nan na ga ta ɗashe da yawa sosae, wallahi"
Cewar hajja
"Ohhhh ikon shi kuma wannan mai kama da aljannun haka Ya gani haka kuma yake so"
Cewar Inna ladiyo ta faɗi maganar tana irin riƙe haɓar nan, alamar dai zancen nan ya ratsa aka dole.
Ahankali Umma taje hannun layla wacce take ta qaqarin amai, ai kuwa su Inna ladiyo me zasu yi inba gulmar da gaske ciki ke gareta kenan, tunda gashi harda amai take qoqarin yi.
Sunje chamist na bayan layinsu a rufe, haka yasa Ummu babu yadda ta iya take qoqarin tsaida abin hawa, don zuwa asibitin gwamnati, can wajajen garin kenan, sai kuma ta shiga qoqarin tsaida abin hawa amma duk wanda ta tare baya tsayawa, hakan yasa suka fara tafiya duk da cewar zuwa wannan loqacin jira ya soma kwasar Layla, Amma bata bari Umma ta fuskanci hakan ba.
✨✨✨★★★
Cikin nutsuwa yake murza steering na motar nashi, wanda umma tun daga nesa ganin wata mota ta taho ta fara irin alamun nan na tsayarda mutum.
Shi kuwa jalaal dake tuƙinsa cikin kwanciyar hankaline da tarin nutsuwa ne yayi saurin yin reverse,ganin wata mata tsugunne kan wata yarinya da dukkan alamu yarinyar bataji daɗi bane, har ya wuce su sai kuma wata zuciyar tace masa ka tsaya ka taimaki waɗannan bayin Allah, sai kuma wata zuciyar tace masa yayi tafiyarsa ina ruwansa da hurumin daba nashi ba, sai kuma wata zuciyar tace masa yanxun laylanka ce a irin wannan yanayin ta rasa mai taimakon ta kuma fa, ya zaka ji.
Dummm kuwa yaji zuciyarsa tayi wani irin bugu tare da tsalle, tamkar zata faso qirjinsa , Ahankali ya fara yin baya Yina qasa da glass na motar, ganin matar dake duƙe bama tasan da tsayuwarsa bane yasa shi ɗan danna hong, ita kuwa umma da tayi tunanin motar bada tsaya bane yasa taci gaba ta riqe qafaɗun Layla da jikinta ya tsananta yafi na ɗazu.
Jin ana hong kusan sune yasa ta saurin ɗago kanta, ganin mota ce fake a gabansu yasa ta soma kiciniyar ɗaga Layla dake kwance cikin rairayin wurin.
Ganin kamar matar bazata iya cira yarinyar bane ya sashi fitowa daga cikin motar,ganin suna son faɗa mashi loqaci, domin sauri yake akwai uzurin daya fito dashi a daren nan, shi yasa ko yaransa baima magana ba ya tuƙo motar ya fito a sace.
Umma kuwa cike da ruɗewa tace.
"Bawan Allah taimaka min mu tada ta tsaye"
Jin Muryar ne da dade da sakan ɗaya bata taɓa barin ransa ne, yasa shi saurin ɗagowa kansa xuwa ga matar, ganin fuskar abu mafi soyuwa acikin RAI da RUHINSA sane yasa shi saurin rumtse idanunsa, wato har gizo kenan yarinyar take son fara kaɗa masa, cikin sauri ya shiga jijjiga kansa tare da ware idanunsa akan matar.
Still kuwa fuskarta ya kuma gani tattare da wannan baiwar Allah, saidai ita tafi laylansa manyanta.
Umma kuwa cikin sarewa tace , "bawan Allah hanzarta kada jinyarta yayi tsanani ko kuma ciwon kanta ya tashi!"
Ta faɗi maganar cikin wani irin raunin murya, da dukkan alamu dai ciwon kan na bata wuya duk yadda akayi.
Ahankali ya sanya hannuwansa tare da qoqarin ɗago matashiyar budurwar dake kwance har yanxun cikin rairan qasar.
"Innalillahi wa'inna ilair raji'un, innalillahi wa'inna ilair raji'un"
Ya shiga nanata wa
Tare da furta. *"LA MIA VITA"*. da qarfin
masifa.
ganin laylansa ce kwance cikin mawuyacin hali,hakan yasa baisan loqacin daya rungumo ta jikinsa baki ɗayanta ba, cikin sassarfa ya miƙe da ita yana nufar cikin motar da ita,ganin hakanne yasa umma saurin bin bayansa, tana shiga cikin motar kusa da laylan daya kwantar mata.
Shi kuwa jalaal 360 yaja motar ko ganin gabansa bayayi sosea, haka yake sharara uban gudu dasu umma, don gani yake idan baiyi gudun ba wani abu ka iya faruwa da ita.
Da sauri umma ta waro idanuwanta ganin suna qoqarin shiga.
*J&L SPECIALIST HOSPITAL*
Asibitin da cikin satikannan akayi bikin buɗesa, hakan ne yasa tayi saurin faɗin.
" Bawan Allah bafa nan zamuje ba ka kaimu government hospital kawai"
Shi kuwa ko jin umma baya ma wani yi, wani mahaukacin hong ya shiga danna wa. Get man ne Yayi saurin buɗe musu qaton Get ɗin asibitin, idanunsa Yaɗan zaro loqacin daya ga wanda yake cikin motar.
Sai kuma yayi saurin sara mishi tare da buɗe masa murfin motorn, jalaal kammm da yake a gigice ne ya fito cikin wani irin sauri, buɗe ɓangaren dasu umma suke yayi, ya suri Layla tamkar wata jajariya, xuwa loqacin kuwa Layla ta tafi duniyar suma.
Kai tsaye ya nufi emergency room da ita, ma'aikatan cikin Asibitin ne sukayi saurin rufa mishi baya.
Ganin oga da kansa ɗauke da mara lafiya, hakanne yasa hankalinsu tashi, Dr Sufyan aliey ne yayi saurin tarar shi Yina qoqarin karɓar patience ɗin dake hannunsa, wani irin mugun kallo daya jifeshi da shine yasa shi saurin ja baya. Tare da shiga taitayinsa, qafarsa ya sanya ya turo qafar ɗakin, dr Deejah dake on duty ce saurin miƙewa tare da nufar shi, tana faɗin.
"Subhanallah *Jey* lafiya kuwa? Meya faru dakai haka? Ka sami accident ne!?"
Haka ta shiga jera masa tambayoyi,ganin dai tasan tabbas baya da kowa acikin garin Bauchin, bare tace family nashi ne. Shi kuwa jalaal saurin shimfiɗe Laylan yayi akan gadon marasa lafiya, yana share zufar dake karyo masa,, kafin cikin sarqewar murya yace mata.
"Don't waste emergency help please!"
Cike da kulawa tace.
You have no problem with that *Jey*"
Nan kuwa Dr Deejah ta shiga bata duk wani taimakon
Data san zata iya bata, atake numfashinta ya dawo, kafin ta fara binciken ainihin abinda ke damunta.
Jalaal kuwa dake ta faman Safa da warwane, ya dubi Dr Deejah ganin tana tambayarshi waye ya kawo wannan patience ɗin, cikin sarqafewar numfashi ya dube ta tare da faɗin.
"Me ne ya faru?, ko akwai matsala ne!?"
"Babu komi kawai dai dama inason ganin mama nata ne ko MIJIN ta".
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da jingina da jikin gadon marasa lafiyar, sai kuma ya fesar da wani zazzafan Numfashi yace .
"Ba komi kawai ki faɗa min yadda ake ciki"
Suna haka ta qaraso wurin tare da duban jalaal da kyau, tace "mene yake faruwa da LAYLAHN"
Kallo ɗaya Dr Deejah tama umma Tasan itace mahaifiyar patience nasu,hakan yasa ta dubeta da kyau tana faɗin.
"Dama hajiya yarinyarki tana da wata damuwane?, Judging from how it was too much for her"
Umma dama ta kasa fashimtar mene take nufi ta ce mata.
"Nidai don Allah Dr. Kawai ki faɗamin abinda yake samun ƴata!"
Ganin duk yadda hankalin umman ya tashine yace tace
"Babu damuwa Hajiya kawai dai mun gano, Her heart is about to be infected with pain. Saka makon abubuwan da dole take son cusawa zuciyarta, ko kuma take son tunano wa, kuma abin ya ma zuciyarta girman da bazata iya tunano koma miye ba. Amma kuma tana son tirsasa zuciyar nata, wannan abin ne ma yayi sanadiyar da kanta ya sara mata matsanancin ciwo, wanda wannan abin shine matakin Heart attack na farko!"
"Innalillahi wa'inna ilair rajiun, ya ilahi ya mujibud da'awati ya hayyu ya qayyum, ciwon zuciya Maryam ɗin? Yanxun MARYAM ɗince take shirin kamuwa da ciwon zuciyar!?"
Cikin kiɗima take tambayar likitar, jalaal kuwa idan da abinda yafi zafi zafin to yaji a wannan loqacin, jin maganar yayi gaba ɗaya tana rugurguza duk wata gaɓa ta jikinsa, jin kalmar yake tamkar an ɗiga masa narkyakkiyar DALMA ne, yanajin kalmar na ratsa duk wata kafar dake sassan jikinsa!, jin kalmar yake a wani irin bahagon yanayi, shin yana inaaaaa? Yana ina har gaba RAYUWAR sa take fama da wannan mugun ciwon daya tabbata la shakka shine sanadin hakan, akansa ne tabbas akan sane komine ya faru da rayuwarsa shi yasa ni.
Dan danan bugun zuciyarsa ya qaru fiye da ƙima, baisan meke faruwa dashi ba baisan kuma a wanne yanayi yake aciki ba, haka zalika ya gaza fashimtar halin da yake ciki bashi kuma da loqacin tantance da yake aciki ɗin.
Tuni yaji qafafunsa na gaza ɗaukar nauyinsa ga kuma zuciyarsa dayaji itama tana naiman tsayawa da aikinta, ahankali ya fara qoqarin maida ruwan hawayen dayaji yana naiman zubo masa.
Jiki a sanyaye ya fito daga cikin ɗakin, yana nufar inda yayi fakin na motarsa, bayan ya tabbatar ya bar musu komi na buqatarsu, batare da sanin umman bama.
♥️🤍♥️
Kwance yake tunda ya baro asibitin ya kasa runtsa idanunsa, ya kuma gaza yin komai.
Ahankali ya soma jin Rington na wayarsa na tashi, jin Rington ɗin daya sanya wa mahaifiyarsa ne , yasa shi ɗan rumtse idanunsa kaɗan tare da janyo wayar yana mannata a kunnensa, ba tare da yace komi ba. Ummie kuwa da taji shiru ne yasa duba wayar,ganin already an amsa qiran ne amma babu magana, hakan yasa zuciyarta bugawa.
"Helo Hello Elooo MODDIBO Naaaaaa lafiyanka kuwa!?"
Ta faɗin maganar tare da qara duba wayar ganin han yarzu qiran na nan ne yasata qara manna wayar da kunnenta.
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da dafe saman goshinsa.
Jin ajiyar zuciyar da yaron nata ya sauqe ne yasa ummie fara magana cikin tsoro da ruɗewa tace.
"Are you okay son, open ur eyes MODDIBO Naaaaaa! Ka buɗe idonka,what's ur problem pls kamin magana MODDIBO! Kana son zuciyana ya buga neeee!?"
Rumtse idanunsa yayi da matuƙar qarɓi , cikin sanyin murya yace.
"UMMIE Naaaaaa!"
Jin yadda ya qira sunan nata ne yasanta qara ruɗewa.
Cike da tashin hankali qarara afuskarta ta qirayi full name nashi tace.
" ABDULJALAAL what's ur problem? Meye matsalar ka ka gaya min. Are you sick ?"
Bude idanuwantsa yayi tare da ɗan jujjuya su sai kuma kawai yace.
" Ki tayani da adda'a UMMIE..... I don't knw, I just can't have rest of mind, may be....". Sai kuma yayi shiru hawaye ya taru a lumsassun idanunsa,
"Ni mahaifiyar kace ABDULJALAAL kana da wacce zaka faɗi ma damuwarka duk fadin duniyar nan wacce ta ficeni, tell me where you've gone wrong , what wrong have u done ka gaya min MODDIBO!"
Share xufar goshinsa yayi tare da fesar da iska mai zafin gaske sai kawai yace.
"Ummiena RAYUWATA!"
'me ne ya faru da rayuwarkan MODDIBO me yasa mu rawuyarka?
Duka cike da zallar ruɗewa take ta faman tambayar yaron nata.
Lumshe idanunsa yayi tare dace mata .
"I will continue praying ummuu, it's not even worth saying kema ki tayani da adda'a UMMIE Naaaaaa"
Bai ma bari yaji amsarta gareshi ba ya kashe qiran, ganin loqaci yaja har hakane ya sanya shi miƙewa a sanyaye tare da nufar toilet yana sakarwa kansa ruwa mai azabar sanyi, wai kozai ɗanji dama dama amma inaaaaa damar nan ta riga ta barshi.
"Umma qirjina zuciya kaina duka zafi da ciwo suke min, umma ina ji ajikina mutuwa zanyi, kuma inaji akwai wani abu muhimmi daya saura acikin rayuwata da ban gama cika wannan muhimmin abun ba"
Saurin rumtse idanunsa yayi loqacin daya daukkota zuwa cikin motarsa, sune Maganganun tada rinqa nanata wa, a tunaninta mahaifiyarta ce.
"Tabbas akwai muhimmin abun da bai gama cike gurbin rayuwarki ba *la Mia vita* tabbas nine gurbin wannan cikin na sashin rayuwarki *vita* bana sake barin rayuwarki acikin garari *la Mia vita*"
Da haka wani irin wahalallan barci yazo yayi awon gaba dashi.
♥️🤍♥️
*Washe garin ranan da safe*
★★★★★★
Tsaye umma take abakin gadon da laylan take kwance, ahankali ta shiga motsa idanunta alamun tana son farkawa kenan.
Da sauri umman ta kuma matsowa gare ta taimaka mata tayi ta samu ta tashi, a bakin toilet ta tsaya ita kuma ta shige cike tare da rufowa qofar.
Bayan ta idar da sallarne ta kishin gida da jikin gadon, ahankali dr.deeja ta tura qofar tare da shigowa, da fara'a a fuskarta ta shiga gaida umman, amsata umman tayi da kulawa.
Cike da nutsuwa Layla ta shiga gaida Dr ɗin, amsa ta tayi tare da tsokanarta lalle jikin yayi sauqi, nan ta kawoma su umma breakfast,ita kuma ta fita ta basu guri don basu guri su karya.
Ahankali ya turo qafar ɗakin tare da kafe Layla da ido domin da ita ya fara cin karo, kanta ta samu da da kasa cire idanunta dake cikin nasa.
Qarasa shigowa yayi tare da fara gaida umman,nan ya shiga gaidai umman cike da girmamawa, da fara'a a fuskarta ta shiga amsa shi, tare da yi masa godiyar nauyin da suka ɗaura masa, qasa yayi da kansa sosae domin bazai iya ci gaba da kallon cikin idanuwanta ba.
"Umma zan maidaku gida, domin Dr Deejah tace ta baku sallama"
"To to amma Aida ka barshi mun tari abun hawa bawan Allah, hakan ma mun gode da ɗauniya Allah ya saka ma da mafificin alkhairinsa, Ubangijii ya baka zuri'a ɗayyaba"
Haka Umma ta shiga gode masa, inda shi kuwa ya miƙe tsamm tare da ya fita yana cewa su fito don Allah, daga cen qasan ranshi yanajin daɗin Adda'ar ta gareshi, sosai yaji matar da burgeshi fiye da tunanin mai karatu.
*Gidansu Layla*
★★★★
*Ikon Allah sannunku da xuwa lallei wannan cikin da wuyar fita yake, harda kwana kuma"
Cewar Inna ladiyo data kasa barci tun daren jiya tsabar masifar dake cinta arai.
Ita kuwa umma kanta kawai ta jijjaga tare da kama hannun LAYLAHN suka shige ɗakinsu bayan ta buɗe, suna jin irin maganganun dasu inna ladiyo suka ringa jifansu dashi.
Haka suka shiru babu wanda yazo ya musu sannu, haka kowa ya shiga harkar gabansa Acikin gidan.
*FADEELAH*
"Innalillahi wa'inna ilair raji'un, Mummy! my mum!! mummy Naaaaaa!!!, zo kiga wani tashin hankalin dana gani"
Momin Fadeelah dake cen saman ta da sauri ta fito, jikinta yana rawa jin uban qiran da Fadeelahn take raraka mata, har tana naiman faɗuwa.
"Ke! Kee!! Ke Fadeelah meya faru irin wannan qira haka na tashin hankali"
"Yo ba qara tashin hankalin ba da wannan mumman abinda naci qaro dashi ayau ɗin nan! Zofa ki gani mum"
Ta faɗi maganar tare da nufar momin nata, tana nuna mata abinda da yasan yata a irin wannan tashin hankalin.
Da sauri mommie taja baya tare da dafe qirjinta.
"Kutubar ubancen mu za'a Ni AYSHA zata yiwa haka?, Ni zata muna furta har haka!?, yaushe ake hakan duk bani da labari, idan harba gizo idanuwana suke minba kamar katin *ƊAURIN AURE NE nagani!, ƊAURIN AUREN MA NA ABDULJALAAL AREEF NASARA! * mijinki kenàn JALAAL AREEF "
Ta faɗi maganar tana juyo wa wurin Fadeelahn, saidai ganin babu Fadeelahn ne yasa saurin kallon wasan tiles ɗin ɗakin zube ta ganta babu alamar numfashi tattare da ƴar nata.
Hakan yasa tayi saurin tsugunnawa zuwa ga ƴer nata tare da faɗin.
"Na rantse da mahaliccinnnnn"
Tofa
Wannan shine ana wata ga kuma wata.
Meke shirin faruwa da fadeelah kenàn?
Shin wayeeeee JALAAL AREEF zai aura? Koma nace ya aura.
🫢🫢🫢🫢🫢🫢😿🙄
Kun san amsar tana ina?
👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻
*JALAAL AREEF*
Saimun haɗu a fejin gaba donjin yadda zata kaya.
💃💃💃💃💃
https://chat.whatsapp.com/FZOG6TDjDid2W63LyRn3XP
_______________________________
*💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐*
~💸 THE BILLIONAIRE 💸~
A story of pure love that touches the ♥️
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
Page 17&18
*~Story planning and writing ammey laylerh ✍️~*
*Yau littafin kacokam sadaukarwa ne ga masu bani comments, basai na ambaci sunanku saidai nace ilahu yabar ƙauna ta har gaban abada*
________________________
♥️🤍♥️
"TALLAH! TALLAH!!TALLAH!!!!
*🤍♥️ƘAUNA BIYU ♥️🤍*
~Heart touching love with love aside🤎~
*PAID book Neeeeee akan farashi mai rahusa 300 kacal account number* *3206656358 Maryam Nasiru first Bank sai a tura shaidar biya ta wannan number 090-65-78-25-69*
*Sai na jiku Kar ku manta wannan fasiyar marubuciyar Nan ce wacce ta nishaɗantar daku acikin littafin ta mai suna KAREN BANA, wohoho ga kuma wani zazzafan wato 💐🌼 JALAAL AREEF THE BILLIONAIRE 💸💐, still kuma yanxu nake tafe da wani haɗaɗɗe kuma qayataccen littafina mai taken 🤍♥️ƘAUNA BIYU ♥️🤍*
*Kai daga jin sunan ma ba sai an baka labari ba😶 ƘAUNA BIYU! ƘAUNA BIYU!! ƘAUNA BIYU!!!*
*Labarine na ban al'ajabi, mamaki, tausayi, Cin amana, zamba cikin aminci, Sanya zukata nutsuwa mai tafe da zazzafar SOYAYYAH*
*KAR Amanta akwai kyautar book ɗina ga duk wanda ya siyi wannan za'a bashi KAREN BANA kyauta ya karanta ina maraba da ku🤝 ta haka ne zangane kalar soyayyaku gareni MASOYA na AMANA💃*
*iya wanda ya sai wannan shi zai karanta JALAAL AREEF a bonus🤓🤓😎 AMMEY LAYLERHNKU ce🤙🏻💪🏻*
*Sai Allah Ubangijii ya kaimu bayan sallah darai da lafiya, da nisan kwana 😌🙃*
_______________________________
"Na rantse da mahaliccin dayake busa min numfashi idan anyi AUREN Nan shegiya nake!, idan har ina da Rai da kuma numfashi wllh sunan wannan auren matacce bama bajajje ba!, kozanyi yawo tsirara wllh saina ga bayan wannan auren!".
Kafin kuma cikin tashin hankali ta kinkimi Fadeelahn tanayin harabar gidan nasu, tun kafin ta qarasa fitowa take kwalawa get man ɗinsu qira. Cikin hanzari ya bayyana gabanta, car key ta bashi gane nufinta da kuma ganin fadeelah riqe a hannun ta, hakan yasa ya gane ba lafiya ba. cikin qanqanin loƙaci ya fito musu da motar tare da mata key ajasu da wani irin matsifar gudun daya sa momi antayo masa wata iriyar ashariya, "Dan kutumar uwarka so kake ka qarasa kashemin ƴar tawa kenàn?" Haƙuri ya shiga bata tare da rage gudun kaɗan. Cikin ƙanƙanin loƙaci suka isa wata private hospital mafi kusa, dan danan kuwa likitoci suka dukufa akanta, ganin sun dawo mata da bugun numfashin ta.
*BAUCHI*
Yau 10/1/ 2024 daya kama ranar juma'atu babbar rana kenan
Aka ɗaura auren jalaal Areef tare da amaryarsa Maryam Yusuf mai kaba, Akan sadaki Naira dubu ɗari biyar tare da mukullin mota. Ɗaurin auren daya samu halartar manyan mutane manyan ƴan kasuwa manyan ƴan siyasa harda mai girma shugaban qasar yanxun dake, wanda aka naɗa bayan rasuwar mahaifinsa, Alhaji AREEFILLAHI MUHD MAI NASARA keñan.
Wanda hakan ya girgiza jama'a da dama, Alh Yusuf mai kaba kuwa ai suman tsaye ne yayi, domin da farko da yaga irin manyan mutane da kuma irin manyan motocin dake fakin a bakin babban masallacin juma'ar Bauchin, yasha ɗaurin auren biyu ne sai sai kuma gashi yaji abinda ya kusan girgiza duniyarsa, domin dakam ma ko harabar masallacin bai nufa fa saida su baffan jalaal waɗan nan tsoffin biyu da suka je newama jalaal auren ƴarsa ne suka kamo hannayensa suna shiga cikin masallacin direct, inda suma ɗin da bai wani gane suba. Ganinsu cikin wasu irin ɗanyun shaddaji wanda in banda maiko da shaning babu abinda suke, saida sukayi da gaske nema kana ya gane su.
Gaba ɗaya ya gama jiƙewa da gumi sharkaf, lalle Ubangiji yayi gaskiya da yace wani hanin ga Allah baiwa ce, ya kuma ce wani jinkirin Alkhairi ne. Tabbas ya yau kam ya yarda kuma ya shaida hakan!, Don ga zahirin abun yau ya faru da ƴarsa, Jama'ar da Alh Yusuf mai kaba ya tara kuwa suma kowa yana cike tabb da mamakin wannan sabon al'amarin, musamman ma mutanen dasu inna ladiyo suka gayyato koma na ce suka turo wai acewarsu suzo suga yadda ɗaurin AUREN ƳAR SADAKA zai kaya, sai gashi sunyi katari da abun daya kusa tashin kansu baki ɗaya.
*JALAAL*
💐💐💐
JALAAL tun yaji ansha fa fatiha ya sauƙe wata iriyar naunauyar ajiyar zuciya, yana jin wani irin daɗi aransa, yana kuma yima Allah godiyaa daya nuna masa zuwan wannan da yayi ta dokon jira tsayin shekaru masu ƴan dama.
Ha haɗe acikin wata haɗaɗɗiyar giztner milk color, wacce tayi matukar amsar jikinsa, malun malun da ƴar ciki komi iri ɗaya ya sanya tun daga kan takalmin qafarsa zuwa agogon hannun sa gaba ɗaya komi iri ɗaya yayi a takaice.
Ga wani irin tashin ƙamshi da yake,
Kife hannuwansa yayi akan kyakkyawar fuskarshi yanajin wata iriyar nutsuwar dake sauqar sa na samun cikon muradin sa, burinsa da komi da komae gaba ɗaya jin wannan ranar yake rana ta musamman agare shi.
MD parouk ne ya saɗaɗo ta baya tare da yiwa abokin nasa kuma ɗan uwansa wata irin runguma ta musamman cikin kunnensa ya shiga raɗa masa wasu maganganun dani kaina bansan miye suba.
Kawai dai naga jalaal na janye jikinsa daga na MD parouk ɗin tare da kai masa bugun wasa. Wana cewa "Wallahi kai kammm anyi ɗan iskan yaro"
Shi kuwa MD parouk cike da ƙyalƙyalcewa da dariya yake faɗin.
"Ƙarya nayi ba itace first love naka ba? Kuma final choice ɗinka!,Sabo da ita aka wulloni Bauchi da zama ta hanyar liqa min aikin Company, yau kimanin shekaru ɗaɗɗai har shekaru goma cifff cifff, nida garinmu saida ziyara to allahamdulillahi nima yau na zama sakakken tsuntsuuuu"
Ya qareshe maganar
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 8 Chapter of 22