ce da rabon, tunda itace tayi tuwon!"
"Ni kuma isa da mulki suka sanya ni kasawa ba, bakiji me nace miki ba in kin Isa kizo ki kwata dai nace miki kooooo!"
Shiru kakeji Inna ladiyo anyi tsittt babu bakin magana, dama akace duk iya tacewarka a rashin mutunci dole akwai wanda ya dame ka, mu wacce baƙar wuyar ce ummanmu bata shaba, itama gashi cikin sauqi wata tazo sama taka tana murza ta yadda taga dama.
Haka suka qaraci fadansu dan kansu suka yi shiru, dan da ummata ma ta leqo tana basu haƙuri kuma sai suka iwo kanta, suna zaginta daci mata mutunci aikuwa na zaburo zan fito, ummata ta maidani dana min faɗan babu ruwana da matan BABANA . Haka badan naso ba na koma abincin da ban qarasa cin ba kenan, fitowa nayi jikata rataye a shoulder ɗina zan tafi wajen aiki na.
"An dai ji kunya haka aka taso haka kuma za'a qara babu mashin shini, saidai yawon ta zubar dama shi yafi dacewa da ballagaza irinki!"
Jin irin mugayen kalaman da ya fito daga cikin bakin Inna ladiyo ne yasa Ni jin, wani nauyi ya cakemin a maqwallato na.
Bansan sanda wasu irin hawaye Masu zafi suka fara zubo mini ba, tabbas Inna ladiyo batayi qarya ba tunda nake ko kare bai taɓa zuwa ƙofar gidan mu da sunan yazo wurina, agaban idanuna akayi auren ƙannuwana.....wasu daga cikin suma harda masu haihuwa biyu.
"Idan kuka ne ma baki fara ba YARINYA! Sai anzo an dire mana ɗan shege ko ƴar shegiya acikin gida, sannan zaki san Allah ɗayane"
{To fan's kuji fa dama su Inna ladiyo ansan Allah kenan😳}
Ai bansan loqacin da nayi wani kukan kura ba nayi kan Inna ladiyo agujeeeeee....
"keee keeeee keeeee MARYAMU ashe dama abinda ake faɗamin gaskiya ne acikin gidan nawa kike shirin dukan MATATA Uwar GIDANA"
Naji Muryar mahaifina akaina, ummata kuwa da take ɗaki zaune tayi mutuwar zaune jin abinda nake shirin aikatawa, jin kuma murya mahaifina ya kuma sata a shock sosae, har bata san sanda ta fito a fusace ba tana zuwa babu wata wata, ta ɗauke fuskata da zafafan matuka har guda huɗu, banyi ƙoƙorin kare kaina ba ganin tunda nake da mahaifiyata, bata taɓa kai hannunta jikina da sunan duka ba.
Kafin ta shiga surfamin faɗa cikin ɓaçin r̃aî ta shiga faɗin
"Ashe dama ke ba ƴar mutunci bace MARYAM! Ashe dama baki da tarbiya har da ran nawa a gabana kike shirin dukan matar mahaifin ki! Yanxun duk irin tarbiyyar da nake baki da rashin mutuncin da zaki saka min kenan? Ba laifi na gode ko yanxun kin nuna min matsayi da iyaka MARYAM"
Sai kuma ta juya wurin Inna ladiyo tana bata haƙuri, aikuwa dama kamar jira take nan ta shiga yaɓawa ummana magan ganu marasa daɗi.
Hakan yasan ya cikin kuka shaɓe shaɓe na durƙushe qasa gabanta, na kama hannunta na ɗaura akaina nace mata
"Ki yafe Ni ummata baxan qara ba wallahi na tuba"
Kwace hannunta tayi tana ture ne daga kusanta tare da cewa
"Idan da ke ƴar mutunci ce ko ca akai miki ki daki matan BABANKI kya daka!"
Wurin mahaifina na nufa da rarrafe shima kamar yadda nayi umma shima haka nayi a wurin shi, saidai abinda ya bani mamaki ya kuma baiwa kowa dake wurin a tsaye mamakin Keenan, kai tsaye ya ciro Ni sama daga tsugunnen da nake.
"Share hawayen ki kije Allah ya miki albarka amma kada ki qara koda kwatankwacin hakanne! Idan har na kuma kama ki da laifi irin wannan zaki fuskanci hukunci na mai tsananin gaske!"
Cikin kuka nace
"Naji naji wallahi naji baba, ban qarawa insha Allahu"
Aikin da ban fita ba kenan na koma ɗakinmu ina nazarin abubuwa masu yawan gaske, ummata kuwa ko na bata kuma Yina sai ma haɗe fuskarta da tayi.
{Hakan da umman LAYLERH tayi shine daidai, domin duk irin faɗan da kake da abokin zamanka, kada ka taɓa baiwa yaranka damar raina wasu daga cikin abokan zaman naku. Wannan itace tarbiyya mai ƙyau itace kuma irin tarbiyyar da annabinmu Annabi Muhammad Sallallahu alaihi Wasallama ya koyar da m
u. IYAYE WANNAN ɗan tsokacin na kune}.
Allah yasa mu dace duniya da lahira 🤲🏻👏🏻
Ameern
https://chat.whatsapp.com/EJuEWNnTjRk6AmcQ9FKtLk
_____________________________
*💐🌼JALAAL AREEF 🌼💐*
~💸THE BILLIONAIRE💸~
A story of pure love that touches the ♥️
NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨
Page 7&8
*STORY*
*PLANNING*
*AND WRITING*
*Ammey laylerh ✍️*
DEDICATED TO RABI'ATOU SABITU { *KILISHI* } ƴar ɗakina wannan page ɗin yau nakine kiyi yadda kikeso dashi🤗🤗🤗
✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟
***********
Gaba ɗaya yinin ranar haka nayi shi cikin ƙunci da kuma tunanin halin rayuwa, tabbas nima inason nayi Aure kodan na huta da irin abubuwan danake fuskanta daga cikin gidanmu, saidai waye zan aura? babuDon kamar yadda su Inna ladiyo ke faɗi tabbas baƙin jini gareni,dede da wasa koda kuwa yarone ba'a taɓa aiko wa ƙirana da sunan anzo zance wurina ba!.. hakan yasa na tattara al'amurrana wurin Ubangijii domin shine maganin kuka Naaaaaa.
Sallah ce kaɗai abinda ke fitar dani tsakar gidanmu, gashi har zuwa wannan loqacin ummana taƙi sakar mun fuska bare nasa ran zanyi mata magana ta amsa.
Yanxuma qiran sallar la'asr itace ta fito dani, suna zaune har yanxun a tsaƙar gidan dan bana ce cikin su akwai wacce ta tashi tayi sallar zuhur ne ma, bare kuma la'asr kaina a qasa don dabi'a ta kenan, idan har ina tafiya kaina yana a qasa ne.
"Yo dama ai ɗan nagada yafi ɗan na koya koba haka zancen yake ba Hajja?"
Na tsinkayi muryan Inna ladiyo tana tambar Hajja, idan ƙasar dake dake gabanta tayi magana to itama tayi, kaina kawai na girgiza ina ambato sunayen Allah ƙyawawa acikin bakina. Subhanallah, walhamdu lillah, wala,ilaha illallahu wallahu akbar. la'ilaha illahuwa alaihi tawakkaltu wahuwa rabbil arshim azeem. Lahaula wala quwwata illah Billah.
Haka dai nayi ta kama adda'oi da sunayen Allah duk wanda yazo bakina, ahaka nayi alwalana ina komawa ɗakinmu cike da sanyin jiki,
Sai nakejin ina nasani na fita wurin aiki na.
*************
Cikin sauri sauri gudu gudu yake motsa jikin duk ya haɗa uban gumi sosae, bai tsaya ba saida yaji ya gaji sosai kana ya dakata yana janwo wani farin towel tass mai ɗauke da tambarin L... SPACE PLAZA.
Ya shiga goge saman wauyansa da fuskarsa against ya kuma ɗauko gorar ruwa, daya kafa bakinsa bai diro gorar ba saida ya tabbatar yashan ye ruwan ciki tasss, kana ya yasar da gorar qasa tare da yasar da towel ɗin shima a qasan, wani juye yayi tare da sarqe hannuwansa a qirjinsa yana barin ɗakin games ɗin cikin sassarfa.
Toilet ya faɗa yana sakarma kansa ruwa yana fata abinda ke danƙare a cikin ƙirjinsa ya ragu koda ƙanƙanine, saidai bayajin zai ragun domin aduk irin loqacin da wannan dauwa mammen abu ya taso mashi, yakan tsinci kansa ne tamkar wani zararre Yakan tsinci kansa acikin wani irin mawuyacin hali.
Dan shi kaɗai ne kaɗai yasan abinda yake ji acikin RAI da RUHINSA hakan yasa ahankali yadafe daidai saitin zuciyarsa tare da furta
"RAYUWATA"
In a kind of sound ya furta kalmar dayaji tamkar RAYUWAR nasa na tare dashi ne.
Cikin wani irin Yaren da koni bansan wanne irin yare bane ya furta.
" Cest Elle, lafemme quim'a mis au monde LAY LERH bon nuit".
Sai ya kuma juyewa xuwa harshen English
" I can't live without you LAY-LERH"
Murɗa handle ɗin toilet ɗin yayi tare da fito wa yana takawa ahankali tamkar irin mai koyar tafiyar nan, shirya wa ya shiga yi yana son kammala komi cikin 15 minutes, don ƙa'idar sace yin komi akan loƙaci tamkar yanda ya gindaya konace yari ga ya tsara ma Rayuwar sa yin komi akan time nashi.
Don aganinsa bashi da loqacin ɓatawa loqacin loqacinsa, komi yana yinsa a tsare ne ba tare da wani ya shiga cikin woni ba, donshi mutum ne mai tsananin bin kowacce ka'ida acikin dukka lamuransa.
Wasu haɗɗaɗu kuma tsadaddun track Suit yasanya blue black, tare da sanya SKY blue denim jacket a saman tsadaddun suit ɗin. gaban shoesrug dinsa dake shaƙe da takalma kala-kala ya nufa. Wani haɗaɗɗen white sneakers shoe ya ciro haɗi da sanyawa ƙafafunsa.
Baisan da xuwanta ba kawai dai yaji anfaɗo masa jiki Ahankali yasan ya hannunsa yajan yeta daga cikin jikinsa, don a yadda yakeji ɗin kamm bayajin yana da woni qarfin halin mata magana, bare kuma uwa uba ita mai laifice gareshi. Hakan yasa ko cira kai baiyi ya kalleta ba ya raɓa gefenta ya fice yana barin ɗakin baki ɗaya, tana ganin ya fita tabi bayansa da harara acikin zuciyarta tana faɗin zatayi maganin sane.
Kai kuji woni qarfin hali fa My fan's ikon Allah kenan 🤔, wato ma zatayi maganin sa ba laifi🥰 don ganin kinyi maganin JALAAL HAJIYA FADEELAH🤓
**************
💐💐💐💐💐💐💐
L....IN MY LIFE BEACH RESORT EGYPT 🪐🏞️
←←←→→→
Kansa qasa yana duba woyar sa har baima san sun iso ba, Ahankali ya ɗaga kansa ya ƙure rubutun dake kwance saman babban BEACH ɗin nasa, wanda tamkar anan zai hango maganin samuwar shin.
Da ƙyar ya sauƙe idanunsa qasa yana ziro ƙafafunsa waje, kai tsaye cikin kwaton Beach ɗin ya shiga wanda yakasance babban gaske, cikin tafiyar nan ta cikakkun maza yake taka qafafunsa haɗi da tunkarar haɗaɗɗen office nashi, duk inda ya gilma zaka turawa suna gaidashi cike da girmamawa, haka yake amsa su kadaran kada han ahaka har ya qare sa babban office ɗinsa dake manne da sunan MD J→A
Ahankali yasanya zafin hannunsa ƙofar tayi tampering na zanen hannunsa, saida ƙofar tayi wajen 5 minutes kafin zuuuuu qofar tayi qasa gaba ɗaya, kai baka ce an taɓa halittar wata qofa a wurin ba, yana shiga qofar ta tayi sama tana komawa Yadda take da.
Zama Yayi kan ɗaya daga cikin kujerun cikin ɗakin ɗaya kasance tamkar nan ne office nashi, idan ya tuna maganganun dayaji da kunnensa fadeelah da mahaifiyarta sukayi a waya, yakanji tamkar ana zare masa Lanka ne daga cikin jikinsa.
Sowar da wayarsa ta ɗaukane yasan yashi dawowa daga dogon tunanin daya lula, duba mai qiran yayi ganin qirane daga babban abokinsa wanda kakaf duniyar baya da tamkar sa.
Hakan yasa shi amsa picking na wayar, bayan gaisuwa ban kuma jin abinda ake faɗa mashi ba, nadai ga ya kafe wuri guda da idanunsa da tuni suka sanja launi xuwa jawur, gaba ɗaya ma daina fashimtar komi da ake faɗa mashi daga ɗaya bangaren mai qiran yayi, ganin ji da kuma ganinsa sun ɗauke loqaci gudane ,yasa shi tashi amugun zuciya tare da zare wayar daga kunnunsa yana dokata da qasa, nan take kuwa tsadaddar wayan ta tarwatse baki ɗayanta komi nata saida yayi filla fillah komi yayi nashi wuri daban.
**********
Ji yake tamkar daga yau zuciyarsa ta tashi a aiki, gani yake idan babu ita acikin RAYUWAR sa, shi maye amfanin tashi RAYUWAR?.
YARINYAR daya RAINETA! Yayi dokon jirayinta tare da azababbiyar soyayyar ta mai qarfin gaske haɗi da tsananin qaunar ta. YARINYAR daya RAYU da iyaka zallar tsagwaron SOYAYYAR ta.
***************
♥️♥️♥️♥️
Tsaye yake agaban shower ruwa na dukan jikinsa, hannayensa duka biyu ya sanya ya dafe jikin bangon, idanuwansa wanda suka sha ruwa sukayi jajur ya buɗe tare da furzar da ruwan dake bakinsa.
Kashe showern yayi tare da jawo towel ya ɗaura akan waist ɗinsa, bai damu da yanda jikinsa ke ɗigar ruwa ba, ya buɗe ƙofar bethroom ɗin ya fito, idan yace zai iya baje abubuwan dake danƙare aransa to tabbas ƙwaƙwalwa da kuma zuciyarsa basazu iya ɗauka ba.
Hakan yasa shi fara ambaton sunayen Allah acikin zuciyarsa, duk kan ƙoƙarinsa nason kawar da tarin abubuwan da suke son dakatar dashi da bugun numfashinsa, abun yaci tura kansa ya jingina ajikin da jikin gado, tare da lumshe lumsassun idanunsa, numfashi yake fitarwa ahankali,
Yayinda yake furta kalmar Innalillahi wa'inna ilair raji'un, innalillahi wa'inna ilair raji'un,,Ya hayyu ya qayyum subhanallah.....daga bakinsa ahankali nutsuwa ke zuwar masa cikin zuciyarsa, yayinda yaji samuwar da yake ciki na gushewa, sosae yaji sassauci acikin zuciyarsa.
Miƙewa yayi cikin wani irin tafiya wacce tafi kama data ƴan maye, agaban fridge ya tsaye tare ɗaukar bottle water tare da ɓalle murfin.
Wata ajiyar zuciya ya sauƙe tare da sanya hannu ya dafe saitin zuciyarsa, duk yanda zuciyarshi ta so sanyashi dogon nazari yaƙi aminta da hakan.Haka kuma yaƙi bawa brain ɗinsa damar yin tunanin kamar yadda ya saba a ƴan kwanakin Nan.
🔗🔗🔗🔗🔗🔗
Tsaye take gaban tanƙamemen mirrorn ɗakin ta, inda ta cakare cikin wasu haɗaɗɗun English wears rigar pencil gown ɗin ce mebin jiki, turaruka masu azabar ƙamshi ta feshe jikinta dasu, chingowm a bakinta direct ɗakin jalaal ta nufa cikin son gwada ƙudirin Mum nata, kwass-kwass haka sautin takalman ƙafarta masu azabar tsayi da tsini ke tashi.
Ahankali ta kama ƙofar bedroom nashi ta murɗa tare da sanya kanta cikin ɗakin, sanyi da kuma qamshim turaren daya zama dauwamme a ɗakin ne yasa ta lumshe idanunta, tare da qara baza hanci don sake shaqo mata qamshim da ƙyau.
Ganinsa da tayine kwance a irin wannan loqacin data san idan har yana gida, yana kan system nashi yana wasu ayyukan hakan yasa zuciyarta bata ba ƙalauba, qara sowa inda yake baje akan makeken gadon ɗaya fi kama dana irin qasashen wajen dama,
"D ONLY meya faru? Meya sameka? Qalau kuwa‽"
haka ta shiga jero masa tambayoyi, shi kuma cikin cushewar tunani da kuma zuciya ya ture ta a cikin sa, cikin hosky voice furta mata
"Enough FADEELAH! Enough is enough pls👏🏻 ya kamata ki barni haka nan don Allah"
Dake banzar bata iya wani lallaɓa miji bane ta tashi fuuuuuuuu tayi waje.
Har taje bakin qofar fita ta tsinkayi muryansa yana faɗin.
"Ki shirya by 9:30AM muna da Flight xuwa 9j INSHA ALLAH"
Ko sauraren sa bata tsaya Yiba ta fice abinta
Safiya ta gari HAJIYA FADEELAH 😴😴
✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️✈️
9j. ABUJA
Gaba ɗaya airport ɗin zagaye yake da matakan tsaro, tako ta ina sun zagaye airport ɗin Yaman sunyi mar ƙawanya NE,
Bisa zuwan ɗan tsohon shugaban kasa kuma BILLIONAIRE wato JALAAL AREEF.
A hankali yake saƙƙowa daga matakalen benen cikin jirgin fadeelah biye dashi a bayan sa, wai wani hura hanci sama take taci uban wani spec daya kusan cinye rabin fuskarta
sanye yake cikin wata ɗanyar getzner fara ƙal ƙal da ita, sai ɗaukar idanu take. Ahankali ya shiga ware lumsassun idanunsa tare da buɗe hanci yana shaƙar iskar ƙasar shi daya kusa 3/4 years rabon shi da ita.
Wasu uban jibga jigban motocine da aƙalla zasu iya kai guda goma sha biyar, suka Parker cikin ƙanƙanin loƙaci airport ɗin ya kuma kacamewa da matakan tsaro, na JALAAL da kuma mahaifinsa,, wanda dan danan sukawa JALAAL ƙawanya suka sanyashi a tsakiyar su tare da manyan bindugu a hannun su.
Directly motocinsu suka shishshiga bayan su sanya JALAAL a tashi motar, suka kuma sanya motar shi a tsakiyarsu wanda hakan tamkar sunyi mar garkuwa ne, haka suka shiga tsaka gudu akan babban titin birnin tarayyar Abuja.
Cikin Wata ƙayatacciya kuma fitacciyar anguwa suka nufa Directly,
Wato anguwar GUZAPE ASOKORO DISTRICT ABUJA.
Gaban wani ƙaton Get wanda aka ƙawatashi sosae sojojine birjik agaban ƙaton Get ɗin, riƙe da manyan bindugu kallon farko zaka ɗauka SOLDIER'S HOUSE ne, amma duba da yadda sojojin ke tsaye kuma ga mutane sai faman kaida komo suke, agidan shine kaɗai zai tabbatar maka cewa ba SOLDIER'S HOUSE bane.
ESTATE ne guda na duka familynsu JALAAL, babban gidane sosae mai ɗauke da rassa da yawa, cikin ƙanƙanin loƙaci aka wangale musu ƙaton Get ɗin. Motocin suka shigo abin mamaki wani dogon titine awurin abin sha'awa kallon farko zaka iya cewa wata anguwace, domin titine mai tsawo sunyi.
Sunyi tafiya mai nisa kafin suka Isa wurin wani Get shima babbane sosea sojoji zagaye dashi.
Direct parking space waɗannan gungun motocin suka nufa,wanda aka qawata wurin da shuke ² da wasu decoration masu ɗaukar hankali, kai tsaye suka Parker motocin nasu.
Saurin fitowa bodyguards nashi sukayi , suka buɗe motar da tafi ko wacce mota haɗuwa da ƙyau awurin, Cikin Isa yasanwo ƙyawawan daren sawayensa waje, kafin ya fito baki ɗayansa. Da sauri bodyguards nashi suka zagaye shi harda ma police wanda suke acikin gidan.
"My MODDIBO Bismillah"
Ɗaya daga cikin su ya faɗa yana murmushi,
Shima murmushin yayi ɗan yasan Ko waye baya da buƙatar tambaya.
Ba tare da yace komi ba yanufi harabar gidan bodyguards ɗin sane suka nufa shi da niyar rufa musu baya, dakatar dasu yayi ta hanyar ɗaga musu hannu.
Daga ɗaya gefen kuwa wasu narkakkun motocine na hanga, wasu ma sabbine ko hawansu ba'a taɓa ba sai ɗaukar IDO suke.
*********
Babban parlour ne sosae wanda tsayawa faɗa muku irin tsaruwa da kuma haɗuwarsa, ɓata loqaci ne domin ya haɗu iyaka haɗuwa.
"UMMIE"
Cikin muryar da tayi sanyi sosai ya furta hakan.
Kyakkyawar farar matar da aka qira da UMMIE ta juwo,wanda aƙalla matar zata iya kaiwa irin shekaru arba'in da biyar ɗin Nan,
Juyowa tayi kasancewar da ta baiya ƙofar shigowa ploorn baya ne, ya subhanallah tsarki ya tabbata ga Ubangijin halitta daya halicci wannan Mata, mai cike da zallar ƙyau fuskarta shimfiɗe da hasken addini ma'abociyar fara'a, kana kallon ta kaga ba cikakkiyar Hausa nace .
"MODDIBO NA!"
Sai kuma ta nufeshi tana buɗe mashi hannayenta alamun ya taho, cikin sassarfa ya kai ga mahaifiyar tasa , yana shigewa jikin jikinta.
Aƙalla sun kusan ɗaukar 5 minutes Ahakan dan har sai FADEELAH dake hakimce kan ɗaya daga cikin rug na ɗakin, ta musu gyaran murya kana ummie ta zare jikinta ana ɗan nata , tana saurin juya mishi baya tana goge guntun hawayen daya ɗigo daga cikin idanunta, na tsabar kewar yaron nata shekaru uku xuwa huɗu aiba qarya baneeeee.
Cikin tacewa a rashin mutunci fadeelah ta miƙe tsaye tare da faɗin
"To Umm nima zanyi wajen tawa uwar dan nima nasan tana Nan tayi missing nawa!"
Kunji fa My fan's wai UMMIEN ne bazata qarisa ba shine UMM😕🤔🤔
Cikin tattako irin nata da nuna komi ba komi bane tace.
"Haba FAREEDERHTU ai kin bari koda xuwa dare ne saiki qarasa wajen HAJIYA MARIYAN!"
"A ahhh kamm Umm nima zanje wajen tawa uwar ne kawai"
Ta faɗa tana gyara Rolling nata tare da surar handbag nata da kuma wayoyinta, zuba mata idanunsa kawai JALAAL yaYi tare da son ganin iyaka gudun ruwanta, ganin tabbas da da gaske fitar zata yine yasan jalaal faɗin.
"IDAN har nine amatsayin mijinki ban kamin ce miki fita ko Nan da can bane, idan har kuma k"
Saurin dafe bakinsa ummie tayi tare da girgiza masa kanta cikin fusata yace .
"Amma ai nine nake aurenta UMMIE! Kuma fa kina ji magana ta faɗa miki"
yayi maganar cikin haɗe fuska
"Comedown my soon ka barta taje, sannan kuma Ni babu maganar data faɗa min"
*💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐*
Shin kunji labarin MAIBUZUWA HAIR CREAM?
Ko matso tazo muku da mayukan gyaran gashi da zai maida ki India hajiya babu magana. Ga dai bayanin ta da abunda tallan ya kunsa
👇
Yar 'uwana mata nazo maku da mayukan gyaran gashi masu kyau da inganci Wanda zaisa kanki yayi tsawo da sheki, yayi laushi, bugu da Kari km yayi Baki, sannan kuma yayimaki maganin dandruff yasa kanki ya dinga kamshi a koda yaushe kizama mowar gd kedai ki nemi mayu kanmu tested and trusted ( Maibuzuwa Hair Cream) (Emergency Hair Cream) (Hair oil) (Hair spray) ( shampoo and conditioner). Karki bari a baki lbr wadannan mayukan munada guaranty garesu idan har kikayi amfani dasu basu maki abunda muka lissafa ba ki maida zamu baki kudinki
Ga duk masu neman k'arin bayani ku tumtubemu a wannan number
👇
08131624745
Ko wannan
07066456416
Ku hanzarta ku mallaki naku.
https://wa.link/oa5tnj
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/EJuEWNnTjRk6AmcQ9FKtLk
______________________________
*💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐*
~💸THE BILLIONAIRE💸~
A story of pure love that touches the ♥️
*NA MARYAM NASEER MIRRAH ✨*
Page 9&10
*STORY*
*PLANNING*
*AND WRITING*
*Ammey laylerh ✍️*
DEDICATED to SAPWAN AHMED {Bestyn besty👍🏻}
✯D͟A͟Z͟Z͟L͟I͟N͟G͟ S͟✯T͟✯R͟'✯W͟R͟I͟T͟E͟R͟S͟
_______________________________
**************
"Barta taje gurin uwartata don uban daya haifi UBANTA!, nifa mamaki kike bani AISHA esheeeee dan kiji ma da ƙyau ba gulmarki nayi ba uhmmmmm"
Ta faɗi maganar tana gyara ɗaurin zanin ta dake ƙoƙarin since mata
Tamkar daga sama haka sukaji sauqar balbalin bala'in Hajjiya Mama, gaba ɗayansu suka juyo suna kallon ta da mamaki, don babu wanda yasan da xuwanta cikinsu.
"Ba ita shegiya baaa ƴar yau, yoni zata gayawa yau nida naga jiya naga gobe, haka za inasa ran ganin jibi ma daram, nafa gama fashimta ba tun yauma A'ISHA tsoron duk mutanen gidan nan kike! Yo inba don nima kinkai ma labarine, haka ranar waccen shigiyar safarar mai kama da tsinken bawa tazo ta gama qare miki tacewarta, amma uffan kince mata ne?, gaba ɗaya ayi mutum sai shegen sanyin tsiya"
sai kuma ta shiga kuka tare da face majina tana faɗin
"ALLAH Sarki AREEF nasan da kana raye da babu mai abinda ko wacce mace ta isa koda yiwa A'isha kallon wulaƙancin neeee, ALLAH dai yaji qanka yasa ka huta! Wannan yaro"
Cike da tsananin tausayin Hajiya Mama UMMIEN ta qaraso gabanta, tare da kama hannunta tana zaunar da ita bisa ɗaya daga cikin kujerun ploorn. Cikin taushin murya ummie tace
"Don girman Allah Mama ki rage sanya damuwata akanki! Inajin babu daɗi sosae, domin duk abinda ake min wallahi bana jin zafinsa, kamar yadda kike sanya damuwata ta zama taki Mama"
JALAAL dake tsaye ne ya qara so yana zama kusa ta kakar tashi, tare shima da fara bata bakin kamar yadda yaga UMMIEN sa nayi.
Cikin qara sakin wani kukan Hajiya Mama tace
"Wallahi JALALU sai nasa kayi maganin shegiyar matar nan taka ita da banzar uwarta, da sammm bada hali na gari dan nikam ba'a NoNo na tashayo baƙin halinta ba, kuma nasan maganinta daga ita har sauran matan BABAN naka! Da sannu duk sainayi maganin su"
"To naji amma dai ai haƙuri ake baki ba cewa akayi kita lissafin wanda zakiwa rashin mutunci kiba ko?"
JALAAL ya faɗi maganar yana jin kamar ya make ta.
"JALALU Ni niiiiiiiii uwar UBAN ka kake gayawa magana?, yo dama ai nasan ba sona kake ba, inbanda abinka ba uwarka nake shigarwa faɗan ba! Maimakon kaji daɗi haɗi da yimin albarka, amma sai ka fige da nuna min kaima ɗan yaune! Kodan zamanka da wannan shegiyar matar taka da taƙi AIHUWA , wato ta koya ma
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 3 Chapter of 22