wanda suka saba cinsa kuwa "Uhmmmmm" kuma su a al'adar su shine abincin amarya na tsawon sati guda babu sauyi, saiɗan kayan makulashe kawai ake barcinta taci.
Itama Layla tashin farko data ga abin yalele saida zuciyarta ya tashi, amma data ci sai Labarin yasha banban bayan ta gama ta kora da madararta, domin shi idan anci da madara ake korawa mai zafi, bi Ma'ana madarar shanuwa kenàn,.
Daga Nan shiga toilet ɗin ummien wacce ta nuna shi, bayan ta ɗauro ta tada sallarta, tana a Nan zaune AUNTY MARYAM ta shigo ɗakin, hannunta riƙe da wata azababbiyar doguwar rigar kimono robo black blue, sai kuma lafayar data kasance sky blue itama, tana zama gefen gadon wata matashiyar budurwa ta qara shigowa ɗakin tare da sallama, amsawa Aunty Maryam tayi tana faɗin "yowwa fareedah kin kuwa zo a daidai ta idar yi maza kizo ki fara mata,kudin kada loqacin waleemar ya qure"
Da to wacce aka qira da fareedan ta amsa haɗi da fara fito da kayayyakin da tasan zatayi amfani dashi.
Nan ta shiga tsarawa fuskar amaryarmu lite mekeup, domin ba Heavy ta mata ba kasancewar iyaka waleema ce kawai za'ai, tuni aka shirya ta cikin rantsatstsiyar kimono robe tare da naɗa mata lafayar akan doguwar rigar, "W0w" zanso kuga yadda Layla tayi wani irin sihirtaccen ƙyau, sosae abinka da farin mutum gashi lite mekup ɗin da akawa fuskar nata ba ƙarin mata ƙyau yayi ba.
"Masha Allah alhamdulillah, kinyi ƙyau sosae"
Cewar matar data mata mekup ɗin, suna haka UMMIE ta shigo ɗakin.
"Masha Allah ahsanin kaliqin, ƴata kinyi ƙyau sosae" murmushi kawai tayi tare da yin ƙasa da kanta tana wasa da zoben dake yatsarta, hannunta ummie ta kama tana faɗin, muje kada mu makara" suna fitowa ainihin parlourn gidan, lumshe idanuwanta tayi ahankali tana jin wani iri da ita, haka suka rinƙa ratsa parlourka, suna Isa harabar gidan wanda ya cika da jama'a, ta kuma lumshe idanunta tana ganin gaba ɗaya Jama'ar wurin sun kafe ta da idanuwansu, ahankali ummie ta zaunar da ita wurin da aka tanaja dan ita, hannunta taji an kama hakan yasan yata ɗago kanta ido huɗu sunkayi da Rahama, ita kuwa Rahama idanu ɗaya ta kashe mata tare da mata irin alamar kinyi ƙyau ɗin nan, kanta ta ɗauke irin bata yardar nan ba. Aknan ce ta matso dab da laylan wacce take ƙanwa ga jalaal ɗin,uba ɗaya suke ƴar gidan Hajiya Turai ce kana itace autarta tace.
"Hello my auntynmu,I am happy to come into our family's, welcome to JALAAL AREEF JALAAL family house" sai kuma ta sakar wani tattausan murmushi, hannu ta miƙa mata alamar suyi musabaha itama martanin murmushin ta mayar mata tare da miqa mata nata hannun, nafisa dake kallon su tun farko ce ta sakarwa da aknan ɗin woni mugun kallo mai cike da ma'anoni daban, ita kuwa ko ajikinta domin tashin farko taji matar yayan nasu ta birgeta, Ring ɗin da woyarta tayine yasa picking na call ɗin ganin babban yayanta ne Messi mai qiran nata, ahankali ta cira woyar tana karata da kunnenta, "ki fito ina jiran ki a coumpaund yanxun ina tsaye" shine kawai umarnin da aka bata tsam tsamm kuwa ta tashi a wurin bayan ta bankawa wurin da amaryar yayansu take ita da akan wata uwar harara tare da barin wurin fuuuuuuuu.
Cikin nutsuwa aka fara gabatar da taron daya haɗa, dab da magrib aka tashi bayan an raba wasu manyan jakankuna, mai ɗauke da photon amarya da ango wanda ita kanta tasha mamakin photon, domin kamm ita dai da kanta bata ma san tana da wannan photon ba, to ya akayi su suka samu?, shine tambayar dake maqale a cenñnn qasan ranta.
★★★
10:12pm Ahankali yake taka qafafunsa agajiye yake liqis, domin kam yau abokansa basu ƙyale shi haka nan ba, sunce suma dole suyi party badan yaso ba suka zo suka jashi, shi yasa ya shigo gidan a matuƙar gajiya direct ɓangaren sa ya nufa, a wahalce ya faɗa toilet yayo wanka ya faɗa saman ƙayataccen gadonsa, yana ɗan lumshe Idanunsa wani irin farin ciki mara misalta yake jin kansa a ciki, cikinsa daya murɗa ne yasa saurin dafe cikin jin wata azababbiyar yunwa da yake ji, babu shiri ya naimi woyarsa tare da dokama ummie qira, ummie dake kan darduma a zaune taji Ring na woyarta hakan yasa ta dubawa don ganin mai qiran, idanu ta ɗan zaro ganin jalaal ne mai qiran kafin ta yi picking na call ɗin ta manna woyar da kunnenta, sauqar muryar yaron nata tayi cikin ƴar shogoɓar sa yace mata,
"Ummienaaaa yunwa data illata miki yaro fa, pls ki haɗo min da Coffee ☕God bless you, I am very hungry"
"To shikenan MODDIBO kada ka damu bara yanxu kuwa za'a kawo ma",,ummie ta faɗa tare da katse qiran, sai kuma ta juyo kan gadonta inda Layla ke kwance yayi luff gaba ɗaya abin duniya sun taru sun mata yawa, kamar daga sama haka taji sauqar muryar ummien tana ce mata, "ƴata tashi maza ga abincin mijinki ki kai masa part ɗinsa"
Dummm gabanta ya buga, ita kuma sannan miji, ita fa kawai kallon komi take kana kuma take bin komi ɗin da ido, "tashi mana yana cenñnn yunwa na neman illata miki miji, maza tashi"
Kasancewar ita bamai musu bace domin bata iya musun ba, hakan yasa ta tashi zaune tare ɗaukar dogon shimar nata tana zirawa, amsan ɗan madaidaicin basket
ɗin dake hannun ummien tayi sai kuma ta tsaya, tare da sadda kanta qasa ta shiga wasa da yatsun hannayenta, sai kuma tace. "Ummie bansan inane part ɗin nasa ba" ajiyar zuciya ummie ta sauqe tana cewa, "kinga na manta ne muje na nuna miki, gaba tayi ita kuma tana baya suna har suka isa part nashin, da hannu ummie ta mata hala mar ganin ta juya, ita kuma ta nufi bakin qofar a sanyaye. Ahankali ta mirza handle ɗin parlourn tare da sanyo kanta cikin ƙaton parlourn, wani irin daddaɗan ƙamshine ya mata wlcm hakan yasa ta ɗan shaqi numfashi, qafafunta kuwa tuni suka nutse cikin tattausan Italian grass carpet ɗin parlour, ɗan wara idanunta tayi tare da fara qarewa parlourn kallo, wani kyakkyawan qofa ta gani wanda dukkan alamu suka nuna mata cewar Nan ne bedroom na mamallakin ɗakin.
Sai yanxun gabanta ya buga da qarfin bala'i, shin wayeeeee iyayenta suka AURA mata?, ina ina ina abduljalaal ɗinta!?, yana ina tasan dai tabbas wannan ba gidansu bane, riga da tasan shi talaka ne tamkar dai yadda su Inna ladiyo ke qiranta keñan "MATAR TALAKA" shine sunanta a wurin su itafa sai yanxun gaba ɗaya komi da komai ya fara dawo mata, domin dakam Bama tasan halin da ita kanta take aciki ba.
"To wayeeeee mijin nawa kuma?"
Ta furta maganar a fili ba tare da tasan maganar ta fito filin na,
"Ni ne"
Cewar jalaal dake tsaye tun farkon shigowanta parlourn, domin ganin shiru shiru ummie nashi bata aiko masa da lonch ɗin bane yasa shi fitowa don xuwa ya amso da kansa.
A firgice ta jiyo jin muryar da ko a gigin barcine taji sauqar ta ba zata gaza gane ta, "JALAAL AREEF why anan kuma! Kenan shine mij kai a ahhh Bama za'ayi haka ba"
ta katse kanta da kanta ta hanyar qarasa qiransa da mijin da tayi niyar yi.
Babu zato babu tsammani taji anyi mata wata iriyar runguma, irin mai hargitsa tunanin nan azabure take qoqarin juyowa amma jalaal yaqi bata damar hakan.
Saima wani irin kwantar da kansa da yayi saman qirjinta yana kuma qara zagaye qugunta da hannayensa, tamkar dai irin yaran nan da aka raba da uwarsa tun yarinta yanxu kuma ya haɗu da ita, yake tsoron kada a sake nesan tashi da ita haka jalaal ya rungume laylan yana sakin ajiyar zuciya mai qarfi. Sai kuma ya shiga raɗa mata.
" I Miss You my LA MIA VITA, I miss my life more than anyone can imagine, I LOVE YOU MY DOLLY"
Shi kansa baisan kalaman ta yadda suka subce masa ba, Layla dake tsaye tamkar dutsen da aka dasa haka take har zuwa wannan loqacin.
Ahankali ta zame hannuwansa dake zagaye da qugunta kana ta rabashi da jikinta tana barin ɗakin baki ɗaya, cikin wani irin mutuwar jiki, tana barin wurin ya biya da wani irin azababben kallo, "ya rabb" ya furta saman laɓɓansa iyaka wannan ƴar rungumar daya mata wata iriyar nutsuwa ta bashi ta musamman, hmmmmmmm bare kuma aceeee nikam babu ruwana ba'a bakina dakuji ba, kuje ku matsa jalaal ya baku amsarku.
★★★
Yau kwanan su adda fatsima, Inna ladiyo, hajja, mamar Rahmah da Rahamar kanta, kuma yaune suke shirin tafiya BAUCHI, tun daga wannan loqacin ko haɗuwa Layla bata qara yarda sunyi da jalaal ba.
Bayan tsabbbbb su Inna ladiyo sun gama fitowa gaban wata shimfiɗeɗiyar motar da zata kai su airport, inda su hajja Inna ladiyo su kaɗai suka san mugun nufi da kuma quɗirinsu, dangane da wannan aure. Kowa ya hallara a harabar gidan amma kuma an rasa baffa yusif mai kaba sama ko qasa, duk woni lungu da saqo na gidan anbi an duba amma babu shi babu dalilin sa, hakan yasa hankalinsu in yayi billions toya tashi, cike da jimama da alhini ummie tace wa su adda fatsima suje ba damuwa insha Allah ya taho daga baya.
Badan sun so kodan sun yarda ba suka shiga motar aka kai su har airport, ita kuwa hajja tasan wallahi wani wurin mai kaba ɗin ya samu ya ɓoye, tasan wannan NI'IMA daya gani haka shine dalilin da yasa ya ɓoye ɗin ba komai ba.
Ita kanta badan son cikar wani mugun buri nata ba, data ɓoye ɗin.
Haka tanaji tana gani girjinsu ya ɗaga zuwa BAUCHIN Yakubu.
Har dare babu baffa yusif babu dalilinsa, amma ba'a bari zancen yakai kunnen laylan ba, domin ko tafiyarsu addan nata bata sani ba, tana cenñnn ɗakin ummien tana shararar barcinta.
Qiran sallar magriba da akayi ne yasa get man ɗin dake zaune yana sauraron ƴar qaramar rediyon shi, yayi saurin kashe radion tare da nufar toilet nashi dake dab da ɗakinsa.
A guje ya zugo ganin mutum kwance yana barci kashirɓan, loƙacin yayi daidai da shigowar wata jibgeciyar mota harabar gidan, jalaal shi da Messi dake cikin motar me sukayi saurin fitowa suna tambayar ko lafiya, cikin haki yake faɗin "Wallahi mutum, aljanine acikin bayi na!"
"Subhanallahi aljani Kuma a ina muje cewar jalaal Messi dake da masifar tsoro ne, ganin jalaal ɗin ya shige gaba ne yasa shi saurin barin gurin yana yin ɓangarensu.
♥️🤍♥️
Turus jalaal yaja ya tsaya ganin mahaifin matarsa ne, da ummie ta shedamar cewar ba'a ganshi, kwance lake lake acikin toilet. Cikin sauri ya qara shiga tara da fara cewa " baffa! Baffa!! Baffa!!!" Baffa yusif kuwa jin kamar ana magana ne yasa saurin tashi zaune yana faɗin.
" Wallahi babu inda zan tafi, ai dama ana yiwa amarya zaman burganci, to wallahi nine zan yiwa ƴata zaman burgancin da kaina, da kuka naimo nima babu inda zan tafi aini naga wajen zama"
"Innalillahi wa'inna ilair raji'un, innalillahi wa'inna ilair raji'un "
Shine kalmar da jalaal yake maimaituwa,, ganin surukinsa guda da wannan aika aikar gashi ma a gaban qaninshi shine da mai gaɗi, dama ace shi qaɗaine ai da dama dama.
Sai kuwa yayi saurin juyowa bayan nasa dan kuma tabbatar wa shikenan sunji komai, wata iriyar ajiyar zuciya ya shiga sauqewa lokacin daya ga babu kowa a wurin.
Tofa PAN'S na Layla kuna 🗣️🗣️🗣️INAAAAAA
Lallai mahaifinta nason ɓallo muku ruwa😅🥹😂😃
Banɗaki kuma innalillahi hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh hhhhhhhh
Wani yayi abun kunya, duk sabo da meneeeee ?🥲🤓 Hhhhhhhh
Sai mun haɗe a shafi na gaba
More comments more typing.
Esheeeeee naga ruwan comments naku
By AMMEY LAYLERH
Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/FZOG6TDjDid2W63LyRn3XP
______________________________
*💐🌼 JALAAL AREEF 🌼💐*
~💸 THE BILLIONAIRE 💸~
A story of pure love that touches the ♥️
*NA AMMEY LAYLERH*
Page 21&22
08104493215
________________________________
♥️🤍♥️
A nutse ya dube shi tare da fara masa magana cikin nutsuwa da girmamawa yace.
"To shikenan baffa muje cenñnn cikin gidan pls yanxun, Nan ba wurin zama bane acikin toilet muke"
Ba don yaso ba saidan babu yacce ya iyane yasa shi miqewa tare dabin bayan Jalaal ɗin.
BAUCHI
Alhamdulillah su adda fatsima sunje gida lafiya qalau, saidai batun baffa yusif daya ɓata ba'a ganshi ba, koda jin wannan lamari Nan take gaban umma ya faɗi acen qasan ranta ta ringa nanata innalillahi wa'inna ilair raji'un, domin tasan tabbas malam yusif ɗin bawai ɓatan yayi ba kamar yacce suka gaya mata ɗin.
Bayan an gama gaggaisawa ne suka cewa Ummah ganan ta kayan da aka basune daga gidan surukan Laylan, aikuwa tace meye nata a ciki ai kawai su rabe abinsu, Inna ladiyo dake tsaye qerere ce ta dubeta a sheqe tare da cewa.
"Kin santa cenñnn baqar munafika algunguma, dama ai da saninki wllh kinsan komi!,dama ai ance ranan da kukaje zubar da cikin nan!, yara sunzo since a wata qatuwar motane aka kayo ku! Ko kinsha bamu sani ba ne?, to kuwa munsan komi tun daga kan shegun cikunkunan da kuka ringa zubarwa, keda gantalalliyar ƴar tak"
Maganar ce ta maqale mata a maqoshinta sakamakon ganin dije da tayi ta fito a guje, tana zuwa tsakar gidan ta fara kwarara amai gaba ɗaya a jikace tace kafin ta durƙushe a wurin yana murqususun azaba tare da riqe cikin ta, da takejin kamar zata mutu tsabar ciwon da yake mata.
A sukwane Inna ladiyon tawo wurinta tare da nufar ta, tana faɗin "lafiyarki kuwa an dije ko har yanxun zazzaɓin bai bar kiba?, kodai chemist zamuje a karɓo miki koda Panadol ne?"
A jigace ta ɗago tana wa Inna ladiyo nuni da cikinta daya ɗan tasa kaɗan.
♥️🤍♥️
Ummie tana zaune ta tasbaha a hannunta tana ja gaba ɗaya abin duniya yabi yasha mata kai, kai wannan abu da ban al'ajabi yake.
Itafa ganin wannan abu take tamkar al'mara tun tana sa ran za'a zo ace mata anga baffan laylan harta fara cire ran, ga Laylan har yanzun bata san halin da ake ciki ba ta yunqura da niyar tashi keñan, jalaal ya shigo ɗakin hannuwansa zube cikin dogon wandon comfy ɗin dake jikinsa.
Hakan yasa ummien komawa ta zauna shima zama yayi gefen qafafunta, tare da faɗin "ummie Naaaaaa barka da dare".
"Lafiya alhamdulillah modibbo! Amma har yanxun shiru babu zancen ganin mahaifin laylah!"
Ajiyar zuciya ya sauƙe tare da fesar da numfashi kaɗan, sai kuma ya dube ta kamar kuma bazaiyi magana tamkar kuma wanda aka fusgi maganar daga bakin sa yace mata.
"An ganshi!"
"Alhamdulillah, alhamdulillah wallahi harna naji hankalina ya kwanta, amma da gaba ɗaya hankalina atashe yake! A ina aka same shi kuma?"
Sumar dake kwance luff a ƙeyarsa yaɗan shafo, tare da faɗa mata duk yadda akai, domin tsakaninsa da mahaifiyarsa babu irin wannan ɓoyeɓoyen, hakan yasa ya faɗa mata komai.
Itama ajiyar zuciyar ta sauƙe jin babu wanda yasan abinda ya farun, cike da tausayin layla fall ranta tace "Masha Allah dama already ban riga na faɗa mata ba", sai kuma ta dube shi tare da cewa " Abduljalaal ya kamata kaje gidansu fadeelah tunda Ni na jajje amma mahaifiyarta taje sai kaje, ya kamata kaje ka dawo da ita ka haɗe kan matanka wuri guda!"
Dake gaba ɗaya baya jin daɗin yanayin sa kai kawai ya gyaɗa mata tare da tashi yana barin ɓangaren nata baki ɗaya, Nasa ɓangaren yayi abubuwa masu dama cunkushe a qirjinsa.
Inna ladiyo
"Innalillahi Ciki kuma likita? Kadai qara aunawa dijen ce take da ciki yau kuwa dana shiga uku!", shi kuwa likitan ganin kamar zata kawo masa haukane yasa shi tattara ita da ɗiyarta ya koresu daga cikin Asibitin sa, kai tsaye wani Asibitin Inna ladiyo tayi da dije Nan ɗin ma dai sunce cikin ne harna tsawon wata huɗu da ƴan sati kai, again wani Asibitin suka qara nufa nan ɗin madai bata sanja zani ba.
Ganin tabbas da gaske cikin ne da ƴarta ɗin yasa hankalinta tashi, cikin tashin hankali marar iyaka taje wani ɗan madaidaicin asibitin dake wani ɗan surquqin lungu,inda aka mata kwatance da nan ne asibitin da suke ABOTIONS aikinsu keñan kawai ɓarar da cikin dama.
Qara dubanta Dr ema yayi da ƙyau cikin hausar da har yanxun bata gama washewa yace "ajiya zaka bar yaronki Anan sai gobe ka dawo ka tafi dashi", ganin tabbas zai ɗebi gara acikin yarinyar domin dama haka yake wa mutane zaice kaje sai gobe ka dawo ka tafi da yaronka, to kafin yayi aikinsa shima saiya ɗan huta dake na tsawon kwana guda da wuni ɗaya, haka tsarin aikinsa yake kuma sannan a biya shi kuɗin aikinsa, idan kuwa yarinya tayi masa irin sosae ɗin Nan sai tayi fin sati a wurinsa acewar aikinka me wahalane haka jikin rawar jiki da son asirinsu ya ruhu tace ba komai zata barta ɗin ta kuwa yi tafiyar ta ta barta wurin Dr ema babu tunanin komai aranta.
{Ya ilahi ya mujibud da'awati Ubangijiin Al'arshi kaci gaba da tsalkake mana zukatanmu, Allah mun gode da kawomu a musulmi ka bamu iyaye na gari, duk wani mai tsananin qaunar mahaifiyarsa yace ameern kana yamin adda'a koda acikin ransa ne ngd}.
Dr ema da dama kamar jiran tafiyar Innan yake ne yaja hannun dijen yana yin wani ɗaki da ita, dake itama dijen dama ƴar hannuce tuni ta gane nufinsa, kafin ya mata wasu abubuwan ma ita tayi mai, haka suka shiga sheqe ayarsu tare, koda yaga dijen itama A ce tuni yaje ya rurrufe ko ina na gidan tare da rufe shagon ma baki ɗaya, dake dama irin shagon nan ne wanda yake daga cikin gidan mutum.
Haka suka wuni suna sheqe ayarsu.
ABUJA
"Haba bro ya kamata fa kaka ɗaga min qafa, nifa kaina wani sa'in tsanar kaina da kaina nake, amma sammmm kai naga baka gane hakan kuma baka tuna ba daidai muke aikatawa, fahad kuwa dake faman sarrafa Nafisa ne yaci gaba da abinda yake.
Kafin ya jishi on top kana ya sarara mata tare da dubanta yace "baby kina bani mamaki wllh! Tamkar wata baƙyauya ko wacce bata waye ma, kinsan fa akwai alqawarin aure tsakaninmu, kuma ai kinsa dai bazan cutar dake ba lovie, keɗin fa JININA Ce ƴar gidan yayan mamata, kuma ko babu haka ai kinsan irin girman abotar dake tsakanin mominmu da mamaki!,kawai bazam iya jure sha'awanki bane har muyi aure shi yasa ma nake naimanki, kuma fa kada ki manta Sisto Na da nakeji da ita bata da ƙawar daya wuce ki baby! Kinfi kowa sani"
"Hmmmmmmm" kawai ita dai nafisan tace tana jan duvet tare da qara rufe jikinta, fahad kuwa jikin nata ya qara shigewa yana faɗa mata wasu abubuwan da Ni kaina bansan miye yake faɗa matan ba.
Kawai dai naga tana sakin murmushi tare da faɗin, "FADEELAH ai bata da dama kai nifa da ace Bro JALAAL ba Uba ɗaya muke ba da wallahi naga mijin Aure, koda asirine kuwa dan da ganinsa ba qaramin jarumin maza za'a yi ba wajen iya sarrafa mace a akan bed
saidai kashhh!"
Sosae fahad ya tsuqe fuskar sa jin irin maganganun da take faɗa akan wani namijin ba shiba, wanin ma wanda yafi kowa tsanarsa a duniya Wato JALAAL AREEF, kuma mijin ƙanwarsa fadeelah.
Cikin tsananin kishi ko nace mugunta yace mata " ohhhh wato dan ina ɗan jin tausayinki ina ɗaga miki qafa shine har kike tunanin akwai wani Namijin, da zaki iya ambata agaban ido na da sunan mijin aurenki! Har ma kike tunani yadda zai sarrafa ki akan bed! To bari nima na gwada miki hasalin yadda nake"
A fusace ya haɗe bakinta da nashi ya shiga sarrafa ta yadda yaga
dama.
Ɓangaren Messi tunda ya shige ɗakinsa bai kuma fitowa, domin Allah ya yi shi wani irin matsoracine shi.
{amma fa hammmmmm a sannu zaku san halin kowa, kana zaku fuskanci asalin gidan su JALAAL AREEF.}
Ko sallah a ɗakinsa yayi abincin sama waya ya bugawa mominshi yace a ba ɗaya daga cikin ƙannenshi su kawa masa , shi bazai iya fitowa ba domin gudun kada yayi gamo.
(Kunji fa ya manta duk inda yake Allah ne dashi, kuma ya manta indai har aljanine duk inda yake acikin duniyar nan yakan iya gano shi acikin sekon ɗaya😅😃)
Tana zaune tunda tayi sallar magrib ta kasa koda motsine daga inda take, gaba ɗaya a sanyaye take tunda aka kawota wannan sashen ta kuma tsintar kanta cikin matsi, cikin takurawa har qara da aiga ummie Nan amma yanxu fa ita qadaice, kana ko waya bata da bare ta ɗan ɗebe kewa.
Jin kamar ana taɓa qofar ɗakin ne yasa ta faɗin "WAYE?" Jin shiru ne yasa ta komawa jikin gadon tana jin gina.
JALAAL dake tsaye daga bakin qofa ne yaja numfashi shifa a duniya jin Muryar ta kawai nutsuwa yake ji da ita, Ahankali ya murɗa handle ɗin qofar tare da sanyo kansa cikin parlourn, ɗan lumshe Idanunsa yayi wanda suka ɗan sanja launi kaɗan yayi, tare da buɗesu jin wani irin ni'imantaccen ƙamshim da hancinsa suka shaqo masa. Wani irin jan yaji yayi tare kuma da fesar da numfashi mai zafi, shifa har tsoron haɗa Layla da fadeelah yake wuri guda, domin shi harga Allah ma ya mance da wata fadeelah badan ummiensa yanxu data masa zancen taba.
Ya sani Layla itace komi da komae nashi😌 idan yace komai to kuwa yana nufin komai ɗin.
Ya tabbata haɗesu wuri ɗaya ba qaramin tashin hankali bane.
Laylah dake manne da jikin gado ce tayi sauran wata idanunta, data ɗan lumshesu, jin amintacciyar muryarsa har tsakar kanta, wacce yayi amfani da ita wajenata sallama.
Zamanta ta gyara sosae tana son danne abinda ke qoqarin taso mata, cikin sanyin ta da kuma nutsuwa ta amsa masa sallamar cikin kamewa, tamkar wata namiji.
Gefen gadon ya wuce directly yana zama daga ɗan ɗefi, Hannuwansa ya sanya ya ɗagota tare da zaunar da ita kusa dashi, har jikinsu na mannuwa wuri guda, a sanyaye ya sanya hannuwansa yana ɗago kanta tare da zuba mata idanunsa, da zuwa wannan loqacin kammm suka kuma sanja color sosae.
Yadda yake mata a shekarun baya hakan ya mata ta hanyar lumshe idanunsa tare da buɗe mata su, atake taji kanta naɗan soma jujjuyawa alamun tanason tayo zeroying mind nata.
"Waye yace miki zan qara guduwa na barki!?,wa ya ce miki zan yarda na qara nesa dake! Keɗin kece rai da rayuwata LAYLERH!, bazan kuma nesa dake ba tamkar shekarun baya"
A firgice Layla ta ɗago kanta tana qara masa kallo tun daga sama har qasa, jin irin kalmomin da ya faɗa wanda suka dawo mata Daram kamar yau abin ya faru, kamar ma a yanxune a kuma wurin.
Cike dason tuno mata da komai ya zaro wani kyakkyawan zobe daga cikin aljihun sa wanda yake acikin wani ƙayataccen ɗan kit, buɗe kit ɗin yayi tare da zaro wani kyakkyawan zobe mai kama dana hannunta exctly, hatta harufan da akayi amfani dasu na L&J sune manne da wannan kyakkyawan zoben da ɗan girmane kawai zai faɗa wa wancen ɗin.
Girman idanunsa ya ware mata baki ɗaya tare da komar dasu ya rufe ruff,
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 10 Chapter of 22